Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
Ya Ibraheem sena tambayeshi kud’in”
*** During break Zeezee ta had’a friends nata both maza da mata ta kaisu school kiosk nasu tayi musu siyayya kowa se hailing nata yake ana tashi taje ta tsaya bakin gate yadda zata iya hango motan Ibraheem koda yazo, bada jimawa ba yazo ya d’auketa suna isa gida ta zarce ciki Baba A’ee da Mama ta tarar zaune tsakar gida suna shan iska daga lungu guda “sannu Mama” tace sama-sama “sannu Baaba.”
“Zo nan!” Mama ta kirata, ba gardama tajeta “gani”
“Baki iya gaisuwa bane kokuwa bakiga Baaba bane?”
“Ba nace mata sannu ba? Ko beyi ba?”
“Sannu gaisuwa neh?”
“Nikam da Allah daga dawowan mutum ko abinci beci ba ahau shi da surutu ina wuni Baaba shikenan?”
“Ki cigaba kinji wallahi ba inda rashin kunya ze kaiki sannan kuma ina reciept na textbook da kika siyan?” Kai tahau sosawa tana tunanin wani k’aryan zata had’a “ehemm dake fa nake ina receipt d’in?”
“Ji Mama sekace school fees aka biya da za’a bada reciept.”
“Uhn-uhn fah!”
“Toh kije makarantar mana ki tambaya in baki yarda ba ni yunwa nakeji” tana kaiwa nan ta bar gun.
“Oh!” Baaba da tun shigowan Zeezee bata iya tace komi ba ta sauk’e ajiyar zuciya “abinda Zeezeen namu ta koma kenan muna ji muna gani? Gaskiya Alhj be kyauta ba ko kad’an kuma kema da naki Hafsah bazan b’oye miki ba.”
“Kamar ya da nawa Baaba? Da ace ita kad’ai ce ‘ya a gabana se ya damen amman inada wasu hud’un wanda ko a ina nasan za’a yaba da tarbiyyansu wallahi ko Allah baze kamani ba, nayi magana har na gaji, tun yarinyan nan bata kai haka ba nake yiwa Alhj wa’azi amman never once did he ever listened to me, me zanyi toh? Akanta sena lalata rayuwar aure na? Inma zanyi sena bari sena aurar da Yasmeen. Ai munanan tare wallahi wataran Alhj seyayi kuka da hawaye akan Zeezee tunda ya miyar da ita *_YAR GATAN_* da batada flaws.”
“Amman haka zaki zuba ma ‘yar da kika haifa ido tana lalacewa?”
“Toh ya kikeso inyi? Daman duk inda aka tara mutan arziki ba’a rasa na banza cikinsu, haka haihuwa ma wata nata gabad’aya haihuwan ma na asara tayi ba na arziki cikinsu kuma bawai Allah yayi hakan bane dan bayi sonta sedan ya jaraba ta, ni kuma da Allah yaban har hud’u masu hankali da tarbiyya se ink’i gode masa nayi hauka sabida d’aya ta tab’arb’are min? Wannan ma jarabawace kinsan kalan halin Alhj towards Zeezee a banza bazasu samin hawan jini ba wallahi is better in fita daga harkansu khalas! Muna nan shi da kansa wataran zeyi regretting ba shi kad’ai ba harta ita.”
“Allah shige mana gaba toh ya ganar dashi gaskiya since before its late.”
“Ameen deh da yafi mai dan wallahi in Zeezee ta cigaba da haka banga na mijin da zezo ya iya da ita ba.”
★*★*★*★
_A week later..._
Sosai Zeezee ta gogu da bak’in wahala cikin sati biyun da tayi ba Baba, muguntan yau daban na gobe daban take samu gun yayyunta gashi ko uffan Mama bata ce musu, ita kuma ko yankata zasuyi bakinta baiyin shiru, Allah Allah take Baba GATAN ta yadawo. A hanyan dawowa daga Lagos to Bauchi armed robbers (‘yan fashi) suka tari motocin d’iban kayan Baba guda biyu daya cika su dim da kayaki suka gudu dashi basu barshi da komai ba. It was such a great lost saboda gabad’aya kud’in account nasa yayi emptying yayo wannan siyayya, abinda yarage a account d’insa sam baida yawa ko kiran Mama ya sanar da ita wannan k’addaran da Allah ya turo mai ma be iya yayi ba sede still kamar yadda Allah yace kowacce k’addara na tare da sauk’i, Allah yayi armed robbers basu k’wace mai motan dayake ciki ba Subhanallahi! What a great lost.
_Three weeks later..._
A takaice kusan rayuwan kowa ya soya a gidan especially na Zeezee da batasan meye k’addara ba balle ta rungumeshi, wai ahakan ma don da taimakon Ibraheem da Mama atimes. Gatsau! Kamar yadda ta saba shiga d’akinsu Mama ba sallama ta fad’a yau ma, direct wajen sa ta nufa, “Baba a canza min waya Abban Lubiee ma ya canza mata nata”
“Zeezee ina zan samu kud’in da zan sai miki sabon waya? Aiint you aware of what happened to me? Na rasa komi fa Zeezee, ki cigaba da sani a addu’a Allah maido min da arzikin da yafi wancan ba waya ba ko jirgi kikeso zan sai miki.”
“Har se yaushe kenan Baba? Haka zan yita zama da akwalan waya?”
“Zeezee sata kikeso inje inyi ne in sai mikin? Kema kinsan inda akwai zan saya miki ko bakisan babu bane?”
“Ni wallahi a canza min waya” nan ta hau bubbuga k’afa.
“Zeezee nace babu kiyi hak’uri mana ke bakisan in babu bane?”
“Ina kuwa ta sani?” Mama dake zaune kan Sallaya tayi maganar bayan sauraronsu datayi, “yarinya tun tana ‘yar k’arama ka saba mata da getting whatever she wants whenever she’s in need, never once did you showed her akwai state of emergency, baga irin ta ba yanzu yarinya is thirteen (13) years old amman batasan meh ake nufi da babu ba, kad’an ka gani ai wallahi. Malam bahaushe beyi k’arya ba kaso d’anka duniya tak’i sa, kak’i naka duniya ta sosa.”
“Kai! Kai! Kai! Meh haka da wannan zance? Meyayi zafi? Meya kawo zancen wani kak’i d’anka duniya tak’i ta, me hakan?”
“Ai gaskiya d’aya ce Alhj kuma daga k’in jinta se b’ata you know right what I mean kuma ka cigaba, kar fa ka manta Zeezee ‘ya mace ce in Allah ya barta rai da lafiya dole wataran zatayi aure ka gayamin wani mijin ne ze iya taking halinta, ace ance wa yarinya babu sarai tasan abinda ya sameka weeks back amman dake batada wayo tazo tana ce maka ka sai mata waya ko ni zaka sai ka siya mata wayan bansani ba.”
“Toh ya isa haka! Zagin ya isa haka, ce miki akayi haka zata cigaba da zama ne? Ai tana girma tana dad’a wayo yanzu ada da take k’arama har zagi batayi neh? Yes tanayi yanzu kuma fah? Tun da ta shiga primary one ta sake d’aga hannu ta zageki ko nine a gidan nan? Hak’uri duk zamuyi amman dekam karki sake cewa K’anwata batada wayo.”
“Wannan kuma ku ya dama dan ni bazan cigaba da zama anan ‘yan unguwa suna zagi na ba, ina aurar da Yasmeen zan koma garinmu incigaba da zama na kai da K’anwarka se kusan inda dare ya muku gare ya waye muku” tana kaiwa nan tayi excusing kanta.
Sosai words na Mama suka ratsa jikin Baba amman sede shi bayason ganin fault in Zeezee, hannunta ya kama ya zaunar da ita gefensa “karki jita kinji K’anwata? Ki tayani da addu’a ina samun kud’i zan canza miki wayan kinji?”
“Toh” tace “zan koma d’aki.”
“Yauwa K’anwata kiyi hak’uri kinji?”
“Toh Baba Allah kawo kud’i.”
“Ameen K’anwata, ameen ameen.”
~* ~* ~*
D’akinsu Ibraheem ta wuce tayi sallama kaman ba ita ba “wa’alaikumus-salam” ya amsa.
“In shigo Ya?”
“Eh shigo” bayan ta shigo tanemi gu a k’asa ta zauna for the first time, “Ya ance mu sayi Evergreen solution na junior waec namu.”
“Nawa ne?”
“N2,000 ne.”
“Toh naji Allah ya kaimu gobe.”
“Ameen nagode” tana kaiwa nan ta mik’e ta koma d’akinta dubu biyun da ta karb’a gun Baba jiya ta ciro sannan ta murmusa wayarta taja ta kira Lubiee bayan sun gaisa tace, “ke yanzu na damparo Ya Ibraheem gobe yace ze bani.”
“Ohh! Zeezee yanzu bayan abinda yasamu Baba still sekinyi masa cuwa-cuwa.”
“Toh ai dubu biyu ne bawani kud’i dayawa ba kuma da nasan zan biya na Ya Ibraheem kashewa zan.”
“Uhn-uhn fa Zeezee, atleast kid’an ji tausayin Baba kiga yadda yake sonki fah.”
“Ke! Dake da wa’azin uwaku kinji ba! Semun had’u a school gobe, bye!” Tayi hanging.
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 17
*December, 2016*
_I dedicate this page in honour of my dear supporters and huge fans *Amyna Malam, Baby Amrah* and *Haleema Abdullah* ILY'ALL💕 #OneLove❤_
_Several weeks later..._
Rayuwa de ta canza daga dad’i zuwa rashinta. Ba abinda ke tafiya wa Baba da iyalansa dai-dai komi ya tab’arb’are more especially ma Zeezee da batasan me k’addara ba bale ta rungume sa. She is used to samun duk wani abinda takeso at that very moment amman yanzu ko kud’in kati setayi dagaske take samu, kullum a cikin complaining take ita tagaji da rayuwan talauci ita kaza ita kaza, harta ipad nata sanda aka siyar danyi mata cikon school fees. Ibraheem na iya k’ok’arinsa dan har na terms biyu kusan dubu d’ari biyu kenan yake biya wa Zeezee as school fees. Without his help da anjima da cire Zeezee daga LYS.
A yanzu haka tana Ss1 tanayin sciences, Zeezee tana girma kyanta na ta dad’uwa, doguwa ce dai-dai, ta kuma k’ara kauri kad’an kan sirantakarta wanda hakan ya mugun fito da dirinta. Tun shigarta Ss1 ta rage karatu se aukin kula yeye samari, kullum seta yini tana waya kokuwa chatting. Kasancewar ayau friends na Baba daga Yola zasu zo yasa akayi lunch like no other, kap ‘yan gidan sun manta when last akayi miya yaji nama kaman na yau stew ne had’ad’d’e wanda yasha nama tako ina da coconut rice. 3:23PM Ibraheem ya dawo da Zeezee from school tana shiga ciki tayi kitchen Yasmeen tasamu tana d’an d’auraye used plates babu ko sannu ta ja plate ta shiga d’iban abinci, da wuri Yasmeen ta dakatar da ita.
“Ke wayace miki wannan namu ne? Ko bakisan Baba zeyi bak’i bane yau?”
“Semeh dan zeyi bak’i me had’i na da bak’insa? Nikan matsa min in d’iba abinci.”
“Mama! Mama! Kiga Zeezee wai abincin friends na Baba zata d’iba.” Daga ciki Mama tace da Zeezee karta tab’a ga nasu na gida can agefe amman dake Zeezee banda maganan Baba bana wanda takeji haka ta d’iba na friends nasan ta sa nama bakwai (7) akai ta k’ara mai. Baba na dawowa gida Yasmeen taje ta fad’a mai, masifa ya shiga yi mesa Mama bata hana Zeezee d’iba ba, “yanzu ina zan samu kud’in sai wani naman?”
“Toh kana blaming waye? Tana jin magana na ne? Bakai ka b’ata taba ai nace mata karta d’iban tak’i jina se kasan nayi yanzu.”
“Aww haka ma zakice ko? Instead kija mata kunne.”
“Ai kai da ka b’ata ta kai zaka gyarata saboda haka ni kabar cika min kunne.”
“Kin kyauta Hafsah, dake yanzu kinga bani samu kaman da dole ki zauna kina gayamin magana iya san ranki, kisani ba ahaka zan gama zama ba in shaa Allahu Allah zemin bud’i”
“Aini ba haka nake nufi ba don’t misinteprete my words” D’akin Zeezee ya nufa ya sameta secin abincin ta take tana chatting “sannu da zuwa Baba” tace dashi.
“Haba! K’anwata taya zaki kwashe nama har bakwai (7) ke kad’ai bayan kinsan halin da muke ciki a gidan nan.”
“Shikenan Baba nama d’aya kakeso in d’auka?”
“Eh mana ai babu ne yanzu lokacin da akwai ba na miyan nake baki duka ba?”
“Nikam gaskiya ban saba ba.”
“Kikace meh?”
“Nace kayi hak’uri.”
“Naji amman karki sake yin hakan yanzu me kikeson na bawa bak’in in sun iso?” Bayan Baba ya fita taja k’aramar tsuka “shikenan sekace ni na d’aura mana talaucin da za’a hanani cin nama, wallahi sede in ba’a siya ba in bahaka ba senaci.”
~* ~* ~*
Ana cikin haka promotional exams nasu Zeezee ya zagayo sam batta karatu se chatting da samari a daren da suke da Chemistry Mama tashigo d’akinta unexpectedly kawai ganin Zeezee tayi ta baje kan gado rungume da pillow tana waya da saurayi daman bata tab’a kama ta red-handed ba seyau, koda Yasmeen ta kawo mata k’orafi cewa fa ga abinda Zeezee keyi bata yarda ba saboda bata d’au rashin hankalin Zeezee har yakai ga haka ba. Wayar ta katse da wuri ta jawo littafinta ta soma karatu.
“Dawa kike wayan?”
“Kamar ya da wa kuma? Da Lubiee man na tambayeta formula ne.”
“Ni zaki raina ma hankali? Nace da wa kike wayan?”
“Da Lubiee mana nikam haa’an!” K’arisowa cikin d’akin Mama tayi a fusace “dawa kike wayan nace? Da saurayi koh?”
“Nide bada saurayi nake waya ba.”
“Oya miqo min wayan naki keda shi sekun gama exams.”
“Haka kawai se kimin siezing waya saboda Yasmeen tace miki da samari nake waya ni wallahi bazan yarda ba” nan ta b’arke da kukan munafirci ta miqe ta nufi d’akin Baba don kai mai k’ara, a hanya ta lab’e tayi deleting call nata da Ammar “ya haka meke faruwa?” Baba yayi saurin tambaya.
“Mama ce wai zata min siezing waya bayan ina browsing stuffs na school dashi.”
“Wallahi Alhj k’arya take kamata nayi tana waya da saurayi.”
“Saurayi?!” Exclaimed Baba.
“Laaa! Wallahi Baba sharri ne ni danake Ss1 ina naga ta kula saurayi, Yasmeen ce taje ta sameta wai inada saurayi alhalin k’arya ne.”
“Wallahi kar ka saurareta in tasan tanada gaskiya ta mik’o wayanta a duba.” Confidently Zeezee ta mik’a mata wayar, sede tayi duban duniya bataga kowani waya dana miji a call log dinba “ina number’n kinsamu?” Baba ya tambaya.
“Wallahi Alhj nina jita da kunne na sede in gogewa tayi.”
“Wallahi Baba sharri ne, yaushe ne na gogen? Ni Allah banida saurayi.”
“Ai nasani K’anwata, ba kalan tarbiyyan dana baki ba kenan.”
“Aww ka yarda da k’arerayin nata kenan? Kuma ma wani tarbiyyan ka bata?”
“Why not? Zeezee tayi k’araman da za’ace tana kula samari she is just four-teen (14) years.”
“Ba komai ka cigaba da d’aure ma k’arya gindi kamar yadda ka saba wataran zakayi nadama” tana kaiwa nan ta juya tana kallon Zeezee “kekuma Allah na kallonki” gwalo Zeezee tayi mata ganin Baba bai kallon direction nata, batare da Mama tasake cewa komi ba tafice.
“Ungo wayarki nasan sharri ne bazaki tab’a watsa min k’asa a ido bako? Keda saurayi sekin gama secondary school, promise?”
“Yes Baba nagode” ta amshe wayan tare da ficewa zuwa d’akinta tasa lock sannan ta haye gado ta cigaba da wayarta daga inda ta tsaya. Ahaka har suka gama exams Zeezee bata rubuta wani abin arziki ba kuma abin takaicin ma wai school mate nata take dating tana Ss1 yana Ss2 sunansa Ammar, irin millonaire school bad boy d’innan ne.
_One week later..._
A yau su Zeezee zasu karb’i result nasu, 9pm tagama shiri Omar yayi dropping nata, hira da selfie sukata sha da friends nata da kuma Ammar, yau ya kasance 3 months anniversary’n su da Ammar, shopping na k’in k’ari ya mata sannan suka d’anyi small party’n su. Not long enough form teacher’n su Zeezee ya raba musu results nasu, shi kansa sakamakon Zeezee ya mugun basa mamaki average nata daga 70.+ ya dawo 49. Sam yace seya kira Babanta yace bata karatu, da k’yar ta iya ta shawo kansa ya fasa. Correcting fluid ta nema ta gyara 49. d’in zuwa 69. Isarta gida ta zarce ciki da gudu da ledojin da Ammar ya bata gudun kar Mama ta ganta, ai tuni Mama taganta tabi sahunta da sauri “Alhj! Alhj! Kazo da kanka kaga yau” tayi maganan tana tare Zeezee daga rufo k’ofar d’akinta. Nan danan Baba ya fito ya samesu “meke faruwa? Har Zeezeen ta dawo ne, ya results d’in?” Tana kame-kame tace, “yayi kyau.”
“Wad’ancan ledojin fa daga gunwa?” Mama ta tambaya, stammering Zeezee ta shiga yi, “nn... Nna..”
“Na saurayi ba?” wabje ledan Mama tayi daga hannunta sannan ta zazzage komi a k’asa. Sega prefumes da chocolates masu heart shapes “ka yarda? Nace ka yarda yanzu aiko? Inba saurayi ba waze mata wannam siyayya? Ina result nakin?” kafin Zeezee tayi k’wararren motsi Mama tasa hannu ta wabje side bag nata tare da ciro result natan sede koda taga 69 gun tagane fake ne, ga kuma correcting fluid data gani gun tuni jikinta ya bata Zeezee ce ta gyara, “yanzu Zeezee har kinyi kaurin canza result naki kikawo wa iyayenki fake one gida? Innalillahi!” Result d’in Baba ya amshe yaduba sosai yasha mamaki jikinsa ya mutu lik’is, yama kasa cewa komi se kallon result d’in kawai yake ayayinda Zeezee tagama tsurewa se raba ido take. Daga bisani ya d’ago kai yana kallonta “kin kyauta kenan Zeezee? Abin naki har ya kaiga ki d’au correction fluid ki canza result naki ki kawo wa iyayenki gida saboda kin rainasu basu je boko ba? Cikin yayyun ki kin tab’a jin wanda yayi haka?”
“Baba nifa ban canza result d’ina ba-”
“K’arya kike” Mama tayi interrupting nata “meze kawo correction fluid kan printed result inba canzawa kikayi ba?”
“A’a barta Hafsah, barta” cewar Baba. “Mesa kikayi hakan?”
“Nifa ban canza ba Baba.”
“K’arya kike sake min? Laifi akan laifi, nace mesa kika canzan? Kuma what was your actual average?” Shiru tayi bata ce komi ba “dake nake magana Zeezee, meh average naki? Karki sa na kira form teacher’nku na tambayesa.”
“49.” ne tayi stating in a slow motion.
“49!” Mama da Baba sukayi exclaiming atare.
“49. Out of 100? Meya sameki Zeezee? Shin baki karatu ne? Kinsan fa da yaya ake samu ake biya miki school fees kika kawo min wannan sakamakon, acireki a LYS d’in a kawo ki Havardth kikeso?”
“A’a” tayi saurin amsawa tana kad’a kai.
“Then mesa kikayi failing woefully haka?”
“Seka tambaya ne?” Mama tasa baki, “samari take