YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   22 / 98

63K to 66K   out of 291.7K words

a goben ze zo.

***
Washegari around 10:00AM Zeezee ta shirya tsaf cikin electric blue lace tasha had’ad’d’en makeup sannan ta fito Mama na ganinta tace, “ina kuma zaki yau da safen nan?”
“Gidansu Lubiee mana.”
“Kullum gidansu Lubiee? Jiya bakije bane? Anya kuwa chan kike zuwa bawani yawon banza ba Zeezee?”
“Yawon banza? Toh me zan zauna inyi a gida ba Adda Mariam ba Yasmeen?”
“Wallahi inma yawon iskanci kike kina bin samari gwara tun wuri kin dena.”
“Baba! Baba!” Nan da nan ya fito daga d’aki “na’am K’anwata ina zuwa da safe haka?”
“Gidansu Lubiee zanje shine Mama wai sam yawon banza da iskanci zani.”
“Kamar ya yawon iskanci? Hafsah baki yarda da tarbiyyan da kika bawa ‘yarki bane da zakice zata yawon banza?”
“Ina kuwa na yarda dashi? Kullum ace wai se ‘ya ta fita kuma gidan su Lubiee wallahi k’arya ne inma saurayi kike bi ranan da kika d’auko abinda yafi k’arfinmu nan gabad’aya ke kika sani.”
“Kai! Meh haka?! Ya isa da Allah, kidena yima K’anwata baki in shaa Allah ba abinda ze sameta” hannu yasa a aljihu ya zaro 1k ya mik’a mata “gashi ko Allah ya kare.”
“Ameen Baba na tafi.”

Dai-dai ta fito bakin k’ofa kenan sukayi bumping into each other da Aleeyu. “Awch!” Tayi exclaiming in pain.
“Sorry Zeezee didn’t mean to bump into you.”
“Is okay sannu da zuwa” tayi maganan tana wuce sa.
“Ermm... Zeezee can I have a word with you?”
“Ya Aleeyu right now am heading somewhere kabari in na dawo.”
“Just a minute will be okay.” Waje ta lek’a taga ba motan Adeel sannan tace, “toh ina jinka kayi sauri please” nan fa gaye ya hau suburbud’o mata love words shi yana sonta, kuma so na aure ba da wata manufa ba. Dai-dai ta bud’e baki tace mai ita batayi kenan ta hango furious Adeel tsaye gefen motansa. B’ari ta shiga yi tama rasa nayi.
“Wayyo Allah! na shiga uku!” ta aza hannayenta saman kai. “Ya Aleeyu dan Allah ka shiga ciki, ka gama dani yau.” Sam be gane me take nufi ba se daya leqa wajen yaga inda take kalla ya fahimci komi. Kafin tace zata k’arisa inda Adeel yake tuni ya shige motansa ya fice not minding calls da take mai sending. Kuka ta shiga yi wajen tasan koda zata had’a sama da k’asa Adeel will never listen to her, ai dan dolenta ta fice zuwa gidansu Lubiee ba shiri, thank God Ummi bata gida.

“Ya haka Babe? Meya faru kike wannan kuka?” Lubiee tayi maganan tana caressing bayan crying Zeezee ita a zatonta ma ko rasuwa akayi ma Zeezee.
“Lubiee am in trouble, nasan Adeel baze sake min magana ba.”
“Mschww! Yanzu akan Adeel kike wannan kuka? Oh ni Lubabatu! Wallahi da nasan da haka da tun farko banyi hooking naku up ba.” Shiru Zeezee tayi se kuka take chan Lubiee tace, “meya had’aku?” In a crying tone tayi ma Lubiee narrating komi. Bayan data gama sauraronta tace, “yo ai wannan ba abin damuwa bane, call him up and explain everything to him is all you’ve got to do.”
“Ke kina ganin ze saurareni neh? Fa bakisan Adeel bane, mugun kishi ne dashi ko magana da mazan class namu ya hana ni, bale ace ya ganni da wani bakin k’ofan gidanmu yau, kema kinsan da akwai babban tashin hankali, please help me out.”
“Dan Allah kibarsa da kansa ze sauk’o ni wallahi haushi kike ban idan kina ma Adeel haka, sekace shine autan maza mschw!”
“Ni a wajena shine auta, wallahi I can sacrifice everything for him dan Allah help me out.” Kallo Lubiee ta galla mata sannan ta d’au wayarta ta shiga kiransa. Seda call d’in ya kusa tsinkewa ya d’aga nan ta hau mai tsiwa, “kai kuma sarkin zuciya haka akace maka akeyi ne? How can you just jump into conclussion saboda kaga Zeezee da wani bakin k’ofan gidansu? Baka tunanin ko friend na yayanta ne yake bata saqo?”
“Ko d’aya, ni zakuyi playing? Inhar what you are saying is true why didn’t she call me up herself and explain to me? Daman tace min she have a suprise for me and I guess that incident was the suprise anyways tell her I enjoyed every part of it. Am hanging.”
“Adeel don’t! Ade”- karap ya katse abinsa. Jin haka Zeezee ta sake rushewa da sabon kuka haka ta tayi Lubiee na bata hak’uri har ta samu tayi shiru.

“Babe wallahi it hurts me seeing the way you can die for wannan useless Adeel d’in, Allah yaga kina sonsa ne yake miki wannan iskanci. Forget him karki sakeyi ta kansa believe me da k’afafunsa ze dawo.”
“Babe only if I could, wallahi bakisan yadda nake feeling Adeel ajikina bane, I’ve never felt like this with anyone. Sonsa a jinina yake.”
“Naji amman please kidena tayar da hankalinki haka, ke bakisan hawan jini yana iya kama ki a haka ba? Please ya isa don’t call him up zan kira shi anjima inya sauk’o kukan is enough.” Se bayan La’asr Zeezee ta koma gida ba annashuwa ko kad’an a tattare da ita. Miqe take bisa gado amman hankalinta sam baya jikinta. Daga bisani ta miqe zaune, “wallahi wallahi Ya have to share this burden with me also, duk laifin wannan mayen Aleeyun ne wama ze sake ce mai Yaya? Mschww! Kuma harda na Ya aciki tunda friend nasa ne” trying Adeel’s line for the last time baya shiga taje ta samu Baba da Mama a d’akinsu. Ba sallama ta fad’a tana kumbure-kumbure.

“Ya haka K’anwata wani abu ne?”
“Ke wai bazaki koyi yin sallama bane? Wawiya kawai.” Mama tayi scolding nata. Ai dama a cike Zeezee take seta sa kuka unstoppingly “haba Hafsah! Yanzu ai kin huta da kika sata kuka, zo K’anwata” har kan gado yayi beckoning nata over ta zauna gefensa sannan ya share mata hawayen, “yi hak’uri kinji? Allah Hafsah kika sake cema yarinyan nan wawiya you’ll answer to me.”
“Yo inba wawanci ba yarinya is sixteen (16) years old amman ace har yanzu barging into our room take ba sallama.”
“Ba ruwanki, kiyi abinda ke gabanki. Ehem ina jinki K’anwata meya kawo ki? Ko kinzo tayani hira ne?”
“Ba d’azu zan fita gidansu Lubiee ba?”
“Ehemm... Ina jinki” ya bata full attention nasa wanda ko Mama bata samun irinsa. Itama Mama kasa kunne tayi tana sauraron Zeezee’n.
“Nazo zan fita kenan kawai sega friend na Ya Ibraheem Aleeyun nan, dana gaishe shi seya cemin wai yanason min magana nace yabari anjima yata insisting then nace masa ina jinsa, kawai ya hau cewa wai yana sona. Son ma wai na aure Baba bayan ni ka hanani yin saurayi se after secondary school.”
“Haka shi Aleeyun yace?! Lallai yaron nan baida hankali, har gida na zezo ya nemi K’anwata ba tare da ya tambayi izini daga guna ba? Allah kaimu rananda ze sake zuwa!”
“Uhn-uhn Alhj don’t just jump into conclussion.”
“Like how Hafsah? Ke bakiji abinda Zeezee ta fad’a bane? Mu godewa Allah ma Zeezee nada wayo in wata sakariyan ne ba sede ta bisa ba suzo su mana abin kunya.”
“Kai yanzu how sure are you Zeezeen naka ba k’arya take ba?”
“Wallahi wallahi ba k’arya nake ba kuma tun kafin yau dama ranan na jisu da Ya suna maganan. Ya yake cemai wai ya basa go ahead.”
“Shi Ibraheem d’in? La’ila! Jeki kiramin shi.” Nan ta fice, “hmm Allah kyauta de amman dekam I don’t believe this girl, itan da tun a Ss1 take kula samari dan yanzu Aleeyu yace yana sonta wai take kawo ma k’ara? Akwai abinda ke cikin duhu.”
“Haka kuwa zakiyi ta nema ki gaji saboda ba abinda ke duhu, samari kuma tun Ss1 dana mata magana ta denayi” dai-dai nan Ibraheem yayi sallama “wa’alaikum salam” suka amsa a tare. Wucewa Zeezee tayi taje ta zauna gefen Baba.

“Yanzu kai Ibraheem ka kyauta kenan a matsayinka na babba? Ina ganinka da hankali amman seka tafka sakarci haka?”
“Gaskiya wannan bayi bane, taya a gaban K’anwarsa zaka tsaya kana mai magana haka?” Mama tayi maganan a fusace.
“Ke dama ai tanan kika fi kauri, d’aure ma k’arya gindi. Dake Ibraheem ne me sunan Babanki dole kik’i ganin laifinsa ai to ni kimi shiru.” Har anan Ibraheem bece komi ba.
“Ehh Ibraheem? Hakan da kayi ka kyauta kenan?”
“Baba nifa ban fahimce kaba.”
“Batun friend naka Aleeyu nake magana. Taya zakayi haka? Kai bakasan a rashi na kaine uba ga Zeezee ba? Seka kama ka bawa d’an iskan can go ahead, wato yayi komi da k’anwarka kai baka damu ba ko?”
“Ni!” Yayi pointing kansa. “Yaushe na bawa Aleeyu go ahead? Infact ni koda yacemin gashi gashi yana sonta ma ban yi backing maganan ba ce masa nayi Zeezee is still a girl yabari ni ba ruwa na kuma ko ke Zeezee banje na sameki nace miki duk wanin dana sani inya ce yana sonki kisan ba bakina aciki ba?”
“Ni! Yaushe akayi haka dani? Nide baka cemin komi ba.” Ibraheem was left dumbfounded, lallai Zeezee!





*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com

PAGE 22

*December, 2016*



“A’a barshi K’anwata, toh wallahi Ibraheem ka bud’e kunnuwanka ka saurareni sannan kuma kaje ka samu d’an iskan Aleeyun can kace mai ya fita daga harkan K’anwata banason ya rabawa yarinya attention nata, waec nata ne a gabanta and nothing else. Kuma this should be the first and last inhar kasan ka gayyato friends naka ma kadena kiran Zeezee side naku da Omar kana jina ai?” Shiru... “Ba da kai bane?”
“Naji” yayi maganan harshly “zan iya tafiya?”
“Tashi ka tafi” seda ya galla wa Zeezee harara cike da horo sannan ya fice.
“Kuma Baba kace mai kar ya daken.”
“Barshi bare tab’a kiba, if he does ma let me know.”
“Toh Baba nagode.”
“Yauwa K’anwata Allah miki albarka.”
“Ameen” tana kaiwa nan ta fice.
“Hummm!” Mama ta numfasa, “Allah de kyauta ana ganin gaskiya amman ayita takewa.”

*~ *~ *~
Washegari around 9pm Mama tayi d’akin Zeezee ta sameta se bacci take sha. Bargon data ruhu dashi Mama ta kwaye “oya mik’e kije ki had’a mana breakfast.”
“Wai shikenan sede ba’ayi hutu ba mutum barena samun bacci ba?”
“Tashi nace kona kira Ya Ibraheem ya zane min ke.” Seda tayi wasting several minutes sannan ta mik’e finally tayi toilet. After a while tafito still Mama na tsaye a d’akin nata tace, “chips zamuyi breakfast dashi” shiru tayi taqi amsawa, “ko baki jini bane?”
“Naji.” Bayan fitan Mama ta gwada line na Adeel har sau biyu amman baya picking, morning text message me dad’i tamai sannan ta fice. Nan da nan ta gama fere dankalin ta aza mai kan wuta ta dawo d’aki ta hau chatting da friends nata. Twelve (12) more minutes Mama ta dawo d’akin nata furiously “sekin mana setting gidan on fire zaki samu sukuni ko?! Kin d’aura man gyad’a tun tuni kinzo kinyi zamanki anan kina chatting? Mik’o wayan nace!” Zatayi magana Mama ta daka mata tsawa “miqo nace!” Badan tanaso ba ta miqa mata ta fice se tura baki take gashi Baba bai gida.

Gishiri ta zabga wa dankalin tana sawa cikin mai yayi chaaa!! Kad’an ya rage be zube mata a jiki ba. Dan yadda man yayi zafi da minti goma dankalin ya gama soyuwa ya dawo bak’i k’irin. A garin kwashewa ta k’one kanta a hannu, nan fa tahau disco a kitchen d’in ana cikin haka Mama ta shigo. “Ya haka Zeezee?”
“Ni dan Allah abarni, abanza ansa mutum ya k’one yau wayyo Allah na!” fridge ta bud’e ta ciro k’wai tare da fasawa kan burnt hannun nata. Idon Mama na tozali da k’onannen dankalin ta saki salati “meh wannan!”
“Dankali mana!” Zeezee ta bada amsa in an I-don’t-care attitude.
“Shine bak’i k’irin haka?” D’aya ta gwada d’agawa takai baki aikuwa bai tonuwa, ciki ko alaman soyuwa beyi ba amman ga waje nan ya k’one k’urumus! Bayan nan kuma ga uban gishirin data zabga. Wani abun se girkin Zeezee!

“Ji gishiri! Dagangan kika yi hakan koh? Daman tunda na saki aikin kiketa gunguni, dagangan kika k’onan koh?”
“Kamar ya dagangan? Ni dan Allah kibarni, zanji da k’unan danayi ne kokuma masifar ki.”
“Aww! rashin kunya zakimin akan asaran da kika min? Nasan maganinki, Ibraheem! Ibraheem! Zo Babana.” Ba tare da b’ata lokaci ba yafito “na’am Mama.”
“Yauwa kalli abinda Zeezee tayi da breakfast namu ina mata magana kuma tana gayamin maganan banza.”
“Meh wannan d’in wai?” ya tambaya dan kuwa ya kasa tantance ko dankali ne kokuwa a’a.
“Wai dankali nace ta soya mana tayi wannan abu.”
“Ke bakida hankali ne?” yayi snarling at Zeezee, banza dashi tayi se hura ma hannunta iska take.
“Dake fa nake magana!”
“Dama abinda ka iya kenan, toh dagangan nayi ne ai kuma kunsan ban iya soya dankalin ba kuka sani yi” dama cike yake da ita gashi yasamu another reason na mata duka. Waje ya tura Mama ya shigo kitchen d’in ya mata dukan tsiya, Mama dake waje tana “ya isa haka Ibraheem” dan yadda Zeezee ke ihu amman ina se kaman k’ara mata Mama tace yayi, kirb’anta yatayi seda ya huce haushinsa kap akanta sannan ya barta. “Nan gaba ki sake had’amin waje gun Baba kiga inban miki wanda yafi wannan ba.” Ball da ita yayi sannan ya umarce ta data mik’e abin tausayi se kuka take ta mik’e duk jikinta zafi yake mata batasan da wanne zata fara ji ba.

“Oya d’iba dankalin ki sake ferewa ki soya me kyau kuma ko wallahi na miki wanda yafi wannan.” Gabad’aya taci k’aniyanta yau ko bakin rashin kunyan ma babu “badake bane?”
“Dani ne” nan ta nufi gun basket d’in ta d’iba yana tsaye a kanta ta gama ferewa ta tsaga tasa mai, yana d’an yin zafi tasa gishiri dai-dai ta juye cikin man. Ibraheem ya barta ta fita daga kitchen d’in kafin dankalin ya soyu ma yak’i haka tana tsaye gun har dankalin ya soyu ta kwashe suka karya. Gabad’aya Zeezee ji take dama ba’a k’addaro mata da wannan rana ba, gashi har yanzu ta gwada line na Adeel koya shiga baya picking.

*~ *~ *~
Seda Azahar Baba ya dawo nan Omar daya gama tara kud’in siyan motansa yaje ya samesa ya mai sannu da zuwa. “Baba dama cikon naira dubu d’ari biyar (N500,000) nake so zan sai mota.”
“Iyyeh! Umari nawa ya girma harka tara kud’in sai mota? Wani model ne?”
“Honda DC ceh.”
“Ahh Honda nada kyau, so kanada gurantee na motan?”
“Eh duk mun gama magana komi is in place.”
“Toh bari zan maka transferring kud’in a account naka.”
“Toh Baba nagode Allah ya k’ara bud’i.”
“Ameen Allah maka albarka ya kawo mace ta gari” bayan yafita Mama tace, “oh! Yau wata rana Alhj anyi abin kai toh Allah k’ara bud’i.”
“Ameen” yace mata “ina Zeezee nekam? ”
“Tana d’akinta tana bacci.”
“Ayyah K’anwata yayi kyau toh.”
A ranan Baba ya sawa Omar kud’in as promised, a washegari navy blue discussion continue na Omar ya iso kowa ya taya sa murna barin ma Mama, ita deh Zeezee ko fita taga motan ma tak’iyi dan bak’in ciki. Shikenan Ya Ibraheem, Adda Mariam da Ya Omar suna da mota Yasmeen ma tace mijinta yace ze sai mata mota ita kad’ai ce bata da mota. Kanta ta rufe a d’aki tayita kuka kaman ba gobe, tana cikin yi taji knocking bisa k’ofar d’akinta kamar bazata amsa ba tace, “waye?”
“Baba ne Zeezee” jin shine ta mik’e ta bud’e mai “bade kuka kike ba K’anwata?” Yayi maganan yana scruitinizing face nata. “Wani abu ne?”
“Babu” tace sama-sama tana share hawayenta.
“In shigo toh?”
“Ka shigo Baba” akan kujera suka zauna, “meya faru kike kuka K’anwata? In matsala kike dashi bazaki sameni ki fad’amin ba seki rufe kanki a d’aki kiyita kuka? Ko kinada gatan daya fini ne Zeezee?”
“A’a Baba.”
“Then why won’t you tell me your problem?”
“I’m sorry.”
“Then fad’amin mesa kike kuka?”
“Babu.”
“Kina son muyi fad’a ko?”
“Duk su Ya Ibraheem dasu Adda Mariam suna da mota Yasmeen ma tace min mijinta yace ze sai mata mota ni kad’ai ce banida mota.”

D’an dariya ya saki kalan ta manya, “shine abin kukan K’anwata? Allah kaimu ki gama secondary school mana kiga, kowani kalan mota kikeso zan saya miki.”
“Har sena gama Baba? Bayan ga ‘yan ajinmu su Sumee, Lieeymarh, Nafeesat, Billy duk suna da mota, Lubiee ma Abbansu ya sai mata ita da yayanta.”
“Hakane?”
“Eh wallahi Baba.”
“Toh share hawayenki kinji? Muddin ina raye ba abinda zaki nema ki rasa, in shaa Allahu nan da 2 weeks zan sai miki motanki kema.”
“Dagaske Baba?!” tayi maganan sounding thrilled.
“Eh mana K’anwata in ban farinta miki ba mawa zan farintawa?”
Tsalle ta daka ta d’ale cinyansa tare da hugging nasa “I love you so much Baba.”
“I love you too K’anwata” bata jima ba ta koma gefe ta zauna, “yauwa kuma banason ki fad’awa kowa wannan magana kinji ko? Ko Mamanku ne karki fad’a mata.”
“Bazan fad’awa kowa ba Baba amman wani iri zaka sai min?”
“Don’t you trust me? Its a suprise.”
“I can’t wait! Allah ya k’ara bud’i Baba. Yauwa ance zamu iya fara kawo kud’in neco registration namu.”
“Toh bari in kuka koma school ko a gobe kikeso kikai?”
“Eh a gobe.”
“Toh Allah kaimu.”

22 / 98