Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
ta fara wankin without knowing how. Kujera yaja ya zauna gefenta yana kallonta tare da instructing nata da zaran tayi pausing kuwa ya d’aga mata belt tana kuka tana jan Allah ya isa ta samu ta gama wankin sukaje gun shanya ta shanyasu tas har takama hanyan d’akinta tana tafiya tana kallon yadda omon yaci mata faracu tana gun-guni Ibraheem ya kira ta “ke! Where do you think you are going? Baki fa gama aikin naki ba.”
“Ni wallahi ba jaka bace, dubi wankin dana maka kawani ce ban gama ba” seta rushe da kuka “wuce site d’ina nace kinada minti d’aya kiyi hakan” banzan kallo ta bishi dashi “shegen jan fuska sekace tsuliyan biri, mugu kawai” tafad’a a hankali sannan a hankali ta soma bin bayansa suna isa d’akin ya jata toilet “so nake ki wanke mana bathroom d’innan tas! Banason naga slightest dotti ga harpic da hypo off you go.” Kuka tasa tsakaninta da Allah “bazaki tashi bane?” Still sprawled a k’asa tace;
“Ya kayi hak’uri wallahi na tuba zan kira Aunty Fateemah na bata hak’uri.”
“Aww kinsan dama abinda kikayi ba dai-dai bane?”
“Eh nasani wallahi na sani sharrin shaid’an ne.”
“Kinsan ba kyau mesa kikayi?”
“Wallahi sharrin shaid’an ne na tuba.”
“Zaki k’ara?”
“Wallahi bazan k’ara ba ko wayanka bazan sake tab’awa ba.”
“Kai inaaa tashi kije ki wanke toilet d’in by then kayan da kika wanke sun bushe kihau gogewa ban yarda da tuban da kikayi ba.”
“Ya wallahi na tuba bazan sake ba, na sake kamin duk abinda kaga ya dace.”
“Maza tashi ki bani waje ki sake tab’amin waya kiga” har da cin tuntub’e agarin fita, d’akinta ta nufa straight taje ta mik’e kan gado.
A week later Mariam ta haihu ta samu ‘yarta Zeezee najin haka ta hau had’a akwatinta zata gun me jego kodan cin kazan jego, itama Yasmeen na jin haihuwan Mariam ta hau had’a akwati. D’aukan abu ya kawo Zeezee d’akin Yasmeen ganin tana had’a akwati ta dakata, “Yasmeen ina zaki haka?”
“Bakiji haihuwar Adda Mariam bane? Zanje tayata zaman jego.”
“Chab! Ke asuwa? Wallahi na rigaki ni zanje mata.”
“Se mu gani ai! Keda ko aiki bakison yinne zaki tayata zaman jego?”
“Wannan kuma keya dama wallahi ni zanje dani za’a ci kajin jego ehe!” ganin Yasmeen ta cigaba da shirya kayakin nata ta fice zuwa d’akin Baba kai masa k’orafi ai kuwa ya goye mata baya just as expected, yace sam ita zataje ta taya Mariam zaman jego ba yadda Mama batai dashi ya bari Yasmeen meh son aiki taje ba yak’i, bayan Zeezee ta gama had’a akwatinta Omar yayi dropping nata a motan Baba.
Mariam dake expecting Yasmeen kawai se ganin Zeezee tayi. “Ya haka ina Yasmeen?”
“Tana gida” ta bata amsa a takaice.
“Tana hanya ko tana gida? Ba ita zata tayani 40 days ba?”
“Baba yace ni zan miki.”
“Ke! God help me wallahi aiki zaki zage kiyi kina jina koh?”
“Ai nasani ina baby’n take muga kota kwaso muninki.” Da yamma Mama da Yasmeen suka iso tayi ma baby wanka.
Zeezee de tun daga ranan ba aikinta se ciye-ciye dake ba abinda Uncle Mahmoud bai siyowa kowani rana kuwa se Mama tazo tayi ma jikarta wanka atimes su taho da Yasmeen atimes nahh. Ba wani aikin arzikin da Zeezee ke yiwa Mariam banda in an kawo kaji ta baje taci ta had’a tean ta me kauri tasha se in taga Uncle Mahmoud ne tage zagewa tayi aiki saboda kud’in katin dayake bata anytime yaga tana aiki. Ahaka har aka samu akayi suna yarinya taci sunan Ramlah (mom na Uncle Mahmoud.)
30 days Zeezee tama Mariam ta tattara kayanta tabar gidan saboda gajiya da tayi da wanke panties na kashi, Mariam se aukin barin ‘ya ba pampers dalili wai ana zafi ga Ramlah se aukin pupu any minute. Ganin haka Zeezee tace zata koma gida Uncle Mahmoud da kansa yayi dropping nata ya bata 3k ai kuwa mutumiyar ta raina ta manta d’ari biyu zuwa biyar da yake bata almost after every 3-4 days nasa kati a waya.
D’akinta ta wuce direct tayi whats needs to be done sannan ta fito tayi d’akin Yasmeen, mik’e kan gado tana karatu ta tarar da ita “Yasmeen ina Baba?”
“Har kunyi arba’in d’in ne?”
“Su gama arba’in nasu lafiya wannan Ramlah take ko meh se aukin kashi minti-minti na gaji da wanke pant na gudo.” Dariya sosai Yasmeen ta tsaya yi da k’yar ta samu ta tsaida dariyan tace, “amman bakida mutunci wallahi sam!”
“Niba wannan ba ina Baba ya bani dubu biyu in cika in sai wani porche dana gani a Jumia 5k.”
“Baba yayi tafiya ai yau.”
“Tafiya!” Tayi exclaiming “shine be fad’a min ba wallahi ya kyauta.”
“Ji mata! matarsa ce ke da seya sanar dake in zeyi tafiya, lallai kam.”
“Ni yanzu ki ranta min 2k, na gama sa rai Uncle Mahmoud ze ban 5k yakama yawani ban 3k mschw!”
“Baki gode ba kenan.”
“Iyi kuwa ko bakin kasuwa naje na zauna zan tara dubu ukun, ranta min 2k d’in kinji?”
“Dalili? Ke d’inda baki biyan bashi.”
“A da ba, da dabansan meye bashi ba amman Allah yanzu zan biyaki.”
“Tsakaninki da wa?”
“Da da tsuntsu ne? Da Allah mana.” Kallonta Yasmeen tayi taji kaifa bazata iya rantawa Zeeze kud’i ba. “Kai! Ban yarda ba kije kice Mama ta baki.”
“Tana gida ne? Kai aiko tana gidan ma ba bani zatai ba ‘cause time da Uncle Mahmoud ya ban 10k ban bata ko k’wandala ba.”
“Kinga erin halin naki ai, nide kije ki rok’eta kokuwa kije gun Ya Ibraheem ko Omar nide na koyi lesson ban sake baki bashi.”
“Ya Omar? Wancan marowacin? Ko dubunsa ban tab’a ci ba, dama-dama Ya Ibraheem d’inma de shikuma yanzu da naje ze kama min suratai please ki bani Allah zan mayar miki nan da 2 weeks” da k’yar tasamu tayi convincing Yasmeen ta bata kud’in nan ta biya buk’atar ta.
* ~ *~ _Few days later_...~ *~
_Wednesday night 12:46AM_ Zeezee ce miqe kan gadon d’akinta tayi ruf da ciki se chatting take a wayarta not minding gobe tana da school ga kuma test da suke dashi a Maths. Bacci ne yazo yayi gaba da ita batasan when and how ba. 5:00AM as usual Mama tazo tayi knocking bisa k’ofar d’akintan gbam! Gbam! Gbam! “Zeezee tashi Sallah” shiru ba response “Zeezee!” Se anan ta amsa uhmmm.
“Tashi Sallah ko kin manta da akwai school yau?”
“Ni banayi.”
“Yaushe ne kikace baki Sallah? Yauma kice bakiyi?”
“Toh date d’ina ya rikice ne” tayi stating sleepishly.
“Banson k’arya fa bud’en k’ofa!”
“Mama dan Allah ki tafi naji zanyi.”
“Kar ma kiyi ba yarinya ce ke yanzu ba ai” tana kaiwa nan ta fice Zeezee bata tashi ba se 6:00AM alwala tayi, tayi Sallah ta koma gado ta mik’e a cewarta wai 6:30AM seta tashi tayi wanka ta shirya.
Kasancewar baccin da bata samu jiya ba tayi sleeping off 7:10AM Ibraheem ya gama shirinsa tsaf yazo fita ganin ba Zeezee yayi ficewarsa yaso seta bi su Nanah (maqotansu) bacci Zeezee tayi tasha se 9:06AM da Baaba tazo share mata d’aki ta tashi sanadin knock da Baaba ke. Firgit ta miqe se yanzu ta tuna tanada Maths test, agogo ta kalla taga 9:07AM “innalillahi! Maths test!” bayi ta fad’a tayi brushing ko wanka batai ba har a yanzu knocking Baaba ke.
“Nikan dan Allah wa me cika min kunne? Koma waye ne ya koma seda na gama makara zaku wani zo kuna wani min knocking mschw!” Ta k’are maganan tana zipping school bag nata, drawer’nta ta bud’e taga ba uniform ciki duk sunyi dotti, jiyan daya kamata ta wanke batayi ba tana ta chatting. Ihu ta qurma ta zarce d’akin Mama, suprisingly Mama ta d’ago kai tana kallonta “ya haka? Ba school ne yau?”
“Ai dole kice haka” tayi maganan almost crying “Baba kad’ai ya damu da naje school koko a’a wallahi sena kirasa na irga mai komai, tun tafiyansa nike tashi na shirya kaina baku assisting d’ina gashi a banza yau nayi missing Maths test kuma teacher’n bayayin make up test.”
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
www.beeenovels.blogspot.com
PAGE 16
*December, 2016*
“In kin fasa, banje na ta dake Sallah kika k’i tashi ba? Fice min daga d’aki da Allah!” tsaye tayi gun tana mata mugun kallo ledan bread dake gefen ta Mama ta d’aga ta wurga mata “ficemin nace!” Kuka Zeezee tasa ta nufi d’akinta ta kira Baba a waya tana kuka cike da tashin hankali ya tambayeta ko lafiya nan ta irga masa komi. “Haka suka yi maki? Kai wa Maman naku wayar” ai atapir Mama tace bazata amsa wayan ba saboda tasan ita ta tada Zeezee itace tak’i tashi “Hafsah fa ina jinki amshi wayan nace!”
“Wallahi bazan karb’a ba duk Alhj kabi ka b’ata yarinya se aukin rashin kunya nan gaba aka tayar da ita zata tashi ai.”
“Aww haka kika ce koh?”
“Eh ai hakan ne.”
“Da kyau, Zeezee...”
“Na’am Baba” ta kashe speaker.
“Bari in na dawo zanje in samu teacher’n naku in shaa Allah ze baki makeup d’in shi kuma Ibraheem zan kirasa bar kukan haka kinji K’anwata.”
“Toh Baba nagode ba-bye” yana katse wayan ya kira Ibraheem ya dinga balbalesa da masifa. Da azahar Mama ta shigo d’akin Zeezee ta tarar da ita mik’e kan gado tasa earpiece a kunne tana jin music tana kad’a kai.
“Laa’ilaa! Kid’a kikeji haka?” Earpiece d’in ta zare “ni wayace miki wak’a nakeji shikenan mutum be isa yasa earpieace ba ace yana jin wak’a.”
“Toh me kike ji dashi?”
“Voicenote aka turon a whatsapp nake playing.”
“Yayi kyau mik’e kije ki share min d’aki ki kuma gyara kan gado kiyi mopping zan shiga nan mak’ota.”
“Toh ba Baaba tazo ba”
“Baaba bata da lafiya bazata iya duka aikin ba.”
“Ni wallahi da erin wannan aiki gwara an sallameta mutum sekace me aids kullum batada lafiya-” kafin ta hankara taji sauk’an mari fas! A bakin ta, “ki iya bakinku kina jina koh?”
“Allah ya-”
“Mawa?” Mama tayi saurin katse ta dama cike da ita ta ke, nan ta rufe ta da duka seda tayi mata lik’is sannan ta barta “marasa kunya kawai kuma ki kira Baban naki yanzu ki cemasa nayi maki duka kiga in bansa Omar ko Ya Ibraheem sun k’ara miki ba.” Kuka sosai Zeezee ke tsakaninta da Allah ana cikin haka Omar ya dawo gida inda yaji hanayaniya ya zarce “ya haka Mama? Meke faruwa?”
“Barni da maras kunyan nan Omar zan fita ka tabbata ta share min d’aki tayi mopping in bahaka ba kamata dukan tsiya nina baka izini.”
“An gama Mama sekin dawo” nan ya dawo da kallonsa kan Zeezee dake harararsa “me kike jira har yanzu da baki mik’e ba?” Bayan fitan Mama yasa Zeezee gaba taje ta d’au tsintsiya ta shiga sharan cuwa-cuwan data saba duk ta tuttura dottin k’arkashin gado tanayi Omar na mata dariyan mugunta itako se zaginsa take a ranta.
Da La’asr Yasmeen ta dawo gida taci broke kona kati bata da, remembering tanada 2k gun Zeezee ta mik’e taje ta sameta a d’akinta oya ke bani 2k na, ai ba haka mukayi dake ba.”
“Ai nice zan ce ba haka mukayi dake ba, ce miki nayi se Baba ya dawo.”
“Lallai kuwa! Yaushe mukayi haka dake? Kinsan yaushe ze dawon nema? Kiban kud’ina Malama”
“Seki d’auken ai tunda nima kud’i ne” tana kaiwa nan ta juya mata baya. K’arisawa cikin d’akin Yasmeen tayi ta wanke ta da mari a baya “Allah ya isa kuma bazan bada kud’in ba.”
“Haka kika ce?”
“Eh” kafin ace me suka b’arke da fad’a tun daga d’aki Mama takejin hayaniya “ya haka? Meke faruwa?” Tayi maganan tana k’ok’arin rabasu, ko a babu Zeezee taci k’aniyanta da k’yar Mama ta samu ta raba sun “wai kashe kanku kukeson yi neh?”
“Mama wallahi kice ta biyani 2k na” cewar Yasmeen tana huci.
“Meya faru tukuna?” Nan Yasmeen ta labarta mata komai bayan da Mama ta gama jinta tace, “toh kema meya kaiki baiwa wannan bashi? Sekace bakisan halinta ba.”
“Wallahi tsautsayi kuma ma seda ta rantse kafin na bata.”
“Oya Zeezee nasan kinada kud’i pay her back her money.”
“Aiki nake da zan samu kud’i ta bari Baba ya dawo.”
“Sarai nasan kina saving break money naki ki d’au dubu biyu ki bata or else.”
“Or else what? Zaki cire mata daga cikin pocket money na da Baba ke baki?” Tayi maganan unbelievably.
“Tabbas! Tun wuri ki d’au kud’inta ki bata.” Kuka Zeezee tasa “wallahi Allah ze sak’a min ni se Baba ya dawo na bata.”
“Taho muje Yasmeen na baki a pocket money’n ta.” Ba kalan darun da Zeezee batayi ba amman hakan be hana Mama d’au dubu biyunta ta bawa Yasmeen ba, yini tayi ranan tana kuka gashi kota kira line na Baba bai shiga.
The following day tasa alarm nata da kanta ta tashi, koda taji Mama na knocking k’in amsawa tayi bayan ta gama shirinta ta fito ta leqa dining wayam taga ba breakfast nata daman aikin Yasmeen ne had’a mata breakfast Baba yayi appointing nata.
Gbam! Gbam! Gbam! Knocking take bisa k’ofan d’akin Yasmeen wane zata b’alla, sauti cike da gyangyad’i tace “wallahi kika sake knocking kinji na rantse zaki school kina kuka yau.”
“Sekisa d’in ai muga iskanci kawai ina breakfast d’ina?”
“Cook d’inki ce ni da zaki tambayen?”
“Eh mana ai aikin kine Baba yasaki kina min breakfast.”
“Toh banyi ba yau saboda Ya Ibraheem yace baze karya ba danke kuma bazan yanke bacci na ba.”
“Kutcee! wallahi bari Baba ya dawo zakiga!” Kitchen ta nufa ta fiddo da three eggs da nufin soyawa sede sam ba ta iya ba at last ta k’ona k’wan itama ta k’one a hannunta a takaice da coco pops tayi breakfast ranan sannan ta koma d’aki tagama shiri ta nufi na Mama dan amsan break money’nta.
N200 d’in ta d’aga kan chess of drawer “Mama” ta kira sunanta “meh?” Ta amsa not minding ta juya. “Ance fa mu sayi Evergreen solution na junior waec namu.”
“To ba seki jira Baban naki ya dawo ya baki ba.”
“Ai bansan ranan dawowan sa ba kuma yaune deadline d’in.”
“Yayi kyau seki tambayi Ya Ibraheem.”
“Ni wallahi a’a nasan ba bani zeyi ba kibani in tafi please zan yi latti” se anan Mama ta mik’e zaune ta juyo tana kallonta “wai ma tsaya anya ba k’arya kike ba? Anya kuwa ance kusai textbook d’in?”
“Eh mana da zan miki k’arya ne.”
“Nawa ne?” ta tambaya finally tare da mik’ewa.
“N2,000 ne.”
“Ke wai ni zaki raina ma wayo? Wato jiya dan na cire 2k daga kud’inki shine kema zaki dampareni koh?”
“Allah ma sheda nane kibani wallahi kona kira Baba na sanar dashi.”
“Inma k’arya kike keda Allan ki” nan ta mik’a mata 2k d’in kwatsam ta amsa ba godiya “dawo, dawo nan.”
“Menace miki duk lokacinda aka baki kud’i?”
“Inyi godiya” tayi maganan tana sa kud’in cikin jakarta.
“Mekuma kikayi yanzu?”
“Toh kud’in kashewa ne kika bani? Bana school bane? Kuma naga in nayi karatun kema ze amfane ki mena godiyan?” Buge bakinta Mama tayi da k’arfi seda ya fashe ya soma jini take idonta ya ciko da hawaye “karki iya bakinki ki koyi kalmasa kalamunki kiga kullum inban riga bige bakin naki ba, kiyi godiya ko kiban kud’ina?” Shiru tayi chan tayi mumbling “nagode” sannan ta fice rai a dak’ule “Allah ze sak’amin kuma ko a babu na amshi kud’ina wallahi ba Evergreen da zan siya” garriage ta nufa tana jiran fitowan Ibraheem ayayinda bakin nata ke tayi mata rad’ad’i idanunta kuwa se cikowa suke da hawaye. 3 minutes more Ibraheem ya fito kallo d’ai ya mata yagano da akwai matsala “meh haka kuma kike wani turo baki?”
“Ba Mama bane ta bigen a baki na.”
“Eh ai dai-danki kenan bake rashin kunya ba.”
“Ni tunda ba sannu zaka cemin ba save your wa’azi ka bud’e motan.”
“Meh kikace?” yayi maganan in a serious tone.
“Nace kad’an bud’en motan kar nayi latti.”
“Da yafi maki kam.” Bayan sun isa school d’in kafin ta fito daga motan ya kashe mata warning “sauran kuma idan nazo d’aukanki ki shanyani like the other day kiga abinda zan miki yau” bata ce komi ba seda taga yaja motarsa tace, “mugu kawai” sauk’an mari tajiyo abayanta cike da tsiwa ta juyo ready to insult who ever it was kawai setaga Lubiee.
“Ohh Lubiee!” Ta fad’a a bit startled.
“Ahhhh! ‘yan mata yau ma a tare muka iso kenan! Ya haka meya sameki a baki?”
“Hmm sekin tambaya ne? Mama ce mana anga Baba baya gida kowa secin zali na yake wallahi Allah ze sak’a min.”
“Me kikayi mata?” Lubiee tayi tambayan tana dariya.
“Hmm kede bari! I’m taking you guys for a treat today” nan ta curo 2k d’in ta nuna mata.
“Wannan ba kud’in Evergreen da akace mu saya bane?”
“Wannan kud’in kashewa zan ba Evergreen da zan sai se Baba ya dawo zan sake tambayarsa” nan ta labarta wa Lubiee abinda ya faru jiya alokacin har sun isa class suna zaune.
“Chab! Lallai Zeezee baki jin tsoron Allah, kina wuta ina binki da nuclear bomb!”
“Ke bazaki gane bane ‘yan gidan namu ne seda haka wallahi kawai dan Baba yafi sona suke min bak’in ciki shima