YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   46 / 98

135K to 138K   out of 291.7K words

tell me mahaifata ta 6aci kenan kwata-kwata?”
“Gaskiya to be frank with you tunda har kince for six months kike sha zeyi wuya ace zaki iya concieving baby saboda ko bamuyi scanning ba I know ya riga ya miki damaging womb cause there was a lady also data sha for just a month, mahaifarta ta b'aci gabad'aya daga k'arshe surgery akayi mata aka cire aka yasar dan ya zama ba amfani. Amman kinsan kowa da yanayin jikinsa maybe naki baya jin magani da wuri.”

“Innalillahi! Yanzu Dr kana nufin bazan iya ta6a haihuwa ba kenan?” Kasa tare hawayen tayi se zuba suke.
“Zeyi wuya to be frank Ma'am amman kinsan akwai miracles, babu abinda yakai ikon Allah mamaki saboda ba yadda Allah baya abinsa kisa a ranki wataran zaki haihu kema kuma ki dage da addu'a in shaa Allahu you wont be disappointed.”
“Shikenan Dr nagode.” Tayi managing ta fad'a.
“Bakomai sauran muyi scanning muga shape na mahaifar naki ko?”
“No please, bazan yi ba banason inji nima se an yanke min nawa koda ya 6aci ne abarmin shi a jikina.”
“But Ma'am yakamata kiyi scanning d'in still.”
“A'a wallahi Dr tashin hankalin danake ciki ma kad'ai ya isheni damuwa basena k'ara wani akai ba thank you” tana kaiwa nan ta miqe se soaking with tears tissue'n hannunta yake “Ma'am! Ma'am!” Dr ya shiga k'olla mata kira, kasa amsasa tayi ta fita da sauri inda ta nufi motarta ta zauna ta bud'e sabon dandalin kuka.
Takasa tayi shiru, hawayen har kaman so suke su k'are ga d'an banzan yunwan da takeji. Babu abinda yafi bata takaici kaman in ta tuna batada gatan iyaye yanzu, da ace auren mutunci akayi mata da albarkan Baba da Mama aciki da hankali kwance zata je ta irga musu komi da yardan Allah kuma suyi mata tsaye akan case d'in se an k'wato mata 'yancinta. Amman yanzu fah? Ba yadda ta iya haka zata hak'ura kokuwa taja Allah ya isa.

Se 4:36pm Zeezee ta isa gida alokacin har Adeel ya gaji da trying number'nta, jira kawai yake ta dawo ya hauta dan kuwa ya hanata fita bale wai yau bada izininsa ba. Ta bud'e k'ofan parlour ta tarar dashi zaune bisa sofa da remote rik'e a hannunsa. Bata bari idonsu ya had'u ba ta kawar da kanta da wuri. Ji kawai take kaman ta d'au wuk'a ta cakka mai for what he did to her.
“Ina kikaje? Ma tukun ban hanaki fita ba?” Ya tambayeta cike da tsiwa. Ko d'aga kai ta kalli direction nasa batayi ba, hakan ya sake k'ullar dashi. “Zeezee am talking to you, are you deaf?” Nanma shiru hannu ta zira a jakarta ta ciro kwalin maganin sannan ta nufi har gabansa ta ajiye akan centre table. Mamaki ne karara ya bayyana a fuskansa be tsamman zata iya tatso magunan ba a inda ya 6oye don haka jikinsa yayi sanyi, “a ina kika samu wannan?” Ya tambayeta finally.
“Wow! Abinda kad'ai zaka iya tambaya kenan? A ina na samu? Ba dogon surutu nakeso ba just tell me menayi maka a rayuwa da ka za6i daka 6atamin mahaifa Adeel, mena maka?”
“What are you saying?”
“Don't play dumb sarai kasan maganin nada side effect amman dake you are a beast a horrible one you proceeded on and kept me taking it wallahi kasani bazan ta6a yafe maka ba for what you did.” Miqewa yayi ya tsaya, “look at you daman nace ki yafemin ne? Please don't ever forgive me, am not ready to be a father and that was the only decision to make.”
“Ashe maqaryaci ne kai ban ta6a sani ba, waya ta6a cemin we should elude muyi aure and have our own kids?”
“Don na fad'a doesnt mean I meant it and koda wasa karki sake referring d'ina da maqaryaci I wont let it go.”
“Mene inba maqaryacin ba? Me zakamin? Kasheni? I wouldn't be suprised tunda har ka iya ka kashemin mahaifa hakan na nufin zaka iya kasheni nima mugu kawai.”
“ENOUGH OKAYY!!” Ya tsawata mata amman ko firgita batayi ba “its not enough until I say it is kabani takardana this instant.”
“LOL” ya saki dariyan rainin hankali. “In baki takardanki? Sekuma kije ina? Ko kin manta bakida gun zuwa ne? Well if you do lemmi remind you, Babanki yayi disowning naki bakida kowa se ni gomma kin bini a hankali ‘yar sadaqa ma dake ko kin manta a kyauta Babanki yabani ke? Don haka bakida value ko kad'an a idona. Bama wannan ba ajinki akwai na mijin da ze zauna da macen da bazata iya haihuwa bane yanzu? You are nomore a complete woman Zeezee your womb is bad you can't concieve so is better ki bini a hankali nine kad'ai gatanki a duniyan nan. ”

Karyewa gabad'aya zuciyarta tayi, tabbas ba k'arya a zancensa amman sede duk abubuwan da suka faru shine sila da tun lokacin taji maganan Lubiee da Adeel bashida bakin da zai mata gori har yace da ita 'yar sadaqa. Hawaye kawai taji na forming rapidly a idanunta kafin ta hankara taji sauk'ansu kan cheeks nata. “Gomma kukan de shi ze rage miki takaici” yana kaiwa nan ya bar mata parlourn. Sauk'a har k'asa tayi gun tana kuka me tsuma zuciya, tayi nadama, tayi nadaman kawo Adeel rayuwarta.

***
Through out ranan word be sake had'ata da Adeel ba dan tunda ta shiga guest room bata fito ba seda taji k'aran engine na motansa, anan ne ta fito ita ko htl ne ta gwammaci tayi zamanta ciki kafin ta samu permanent place don batajin zata iya cigaba da zama da mugun halitta kaman Adeel, if only tasan true colour'nsa da bata aure sa ba. “Oh Allah! am missing you Ya Al'ameen please forgive me” ta furta a ranta. D'akinsu ta shiga ta had'a akwati d'aya da wuri-wuri tazo da fita ta murd'a handle seji kawai tayi a rufe, “like seriously? Rufeni Adeel yayi?” Rattling k'ofar tayita yi amman ina sam bayi bud'uwa, kuka ta shigayi amman hakan besa ta hak'ura ba seda k'arfin jikinta tas ya k'are sannan ta tattara kanta tayi guest room. Har after 9pm Adeel be dawo gida ba, yunwa ne ya korata ta nufi kitchen ta had'a oats tasha sannan ta sake komawa d'aki gabad'aya tunanin duniya ya sata gaba. A haka har bacci yayi awon gaba da ita.

Adeel kuwa se dab da Asubah ya dawo gida bayan ya idda Sallah ya koma bacci se pass 10 ya tashi yayi wanka tsaf sannan ya leqa parlour. A dining table ya tarar da ita tana had'a tea, gefenta kuwa indomie ne da sardines aciki seda fried egg a gefe, kafin ta hankara kawai taga ya d'aga plate natan “Adeel ya da haka give me back my plate.“ Tayi stating angrily.
“In ke kike siyan abincin seki amsa aikin banza kawai, ki sake girka wani am in a hurry zan fita.”
“Ina ruwana da fitanka give me back my plate.”
“Ki amsa idan kinada k'arfi mschww!” tunkud'eta gefe yayi seda ta kusan fad'i sannan ya k'arasa had'a tea'n nata yakoma d'aki. Hawaye ta soma without knowing how, a hankali ta share ta koma guest room ta baje kan gado ta cigaba da aikin kukan.

15 more minutes taji an bankad'e mata k'ofa which she is sure is no one other than Adeel ko juyawa ta kallesa ma batayi ba “Ke!” Ya kirata cike da raini da nuna isa. “Ke! Baki jina ne? Don't let me repeat myself turn around.” Seda ta d'au tsawon minti d'aya sannan ta juya a hankali tana kallonsa kayan wankinsa dake hannunsa ya zuba a k'asa “gashi do my laundry in kika gama seki girka min spaghetti for lunch, up you go.”
“Nice zan maka laundry?” Ta tambayesa in a low tone cike da mamaki.
“Baki tab'a ganin mata suna yima mazajensu wanki bane?”
“Bana d'aya daga cikin jerin matayan can don haka bazan wake komi ba, ko ka wanke da kanka kokuwa ka kai laundry su wanke maka.”
“What? Me kikace? Come again.”
“Bazan wanke ba nace ai ba 'yar aikinka ce niba.”
“LOL toh ai baki sani ba Zeezee, me aiki ma yafiki min ke k'ima da daraja a ido saboda su atleast da kud'i zan d'auko su kekuma fah? A sama fa na sameki don haka kibar 6ata min lokaci and do as I ask.” Tana hawaye tace, “bazan yiba“ isketa yayi lokaci guda zuwa kan gadon tare da fincikota da hannunta. Wani irin riqo ya mata wanda tuni k'arfin kukanta ya dad'u dan azaba. K'ok'arin kar6e hannunta take amman takasa. “Adeel ka sakeni” ta fad'a in between tears.
“In saki aiki kice baza kiyi ba?” Ya sake dandame rik'on daya matan k'ara ta saki a sanadin haka. Da zafin ya isheta tana kuka sosai tace “zanyi, zanyi ma wankin don Allah ka sakeni.”
“Repeat it again.”
“I'll wash your clothes for you ka sake min hannu please.” Ta qare maganan tana kuka sosai, se anan ya saketa wajen har yayi dark pink colour tsan-tsan azaba.
“Don't try crossing me again” yana kaiwa nan ya fice, kan gadon ta koma ta cigaba da rusa kuka sosai na haqiqa.

Seda tayi me isarta sannan ta tashi taje ta wanke mai kayakin tas ta shanya ta kuma aza mai girki. Dad'i sosai taji ganin be rufe k'ofa ba, nan da nan taje ta d'auko akwatinta sede kash tana isa bakin gate ta tarar dashi a rufe. Kulle idonta kawai tayi se hawaye suka soma fita, abin tausayi ta koma ciki ta cigaba da kuka tana cikinyi taji buzzing na wayarta, Lubiee taga ke kira amman batajin zata iya amsawa haka har ya tsinke tana gani.

*~ *~ *~
Rayuwa kuma haka ta canza, Zeezee kullum cikin kuka ba kalan azaban da Adeel bai galla mata. Ta yini a aiki takuma ta tashi da aiki gashi koda wasa ta gwada cewa bazatayi ba threatening nata yake sosai, daga yasata yimai wanki, se girki, gashi ya tashi dawowa daga yawonsa yanzu da gan-gan se ya taro ambaliyan friends nasa about 5-6 of them suci lunch. Zeezee kullum tsaye bakin gas, da iskancin Adeel ya tashi ma yace shi yabar siyan Gas d'in wai tayi tsada charcoal stove ya sai mata haka kullum tana waje tana mishi girki da friends nasa which she don't get any thanks in return. Se tunawa kawai take da bawan Allah Al'ameen. Shin ma ta ina zata soma neman yafiyansa? Dukkanin rashin hankalin da take mai dai-dai da rana d'aya be tab'a wulak'anta taba ko tsawa bayi mata a kullum cikin missing Al'ameen take se yanzu ta gano the true definition of Love and Adeel was never her true love Al'ameen is amman tasan its too late now maybe yanzu Al'ameen ma yayi aure ya manta da ita.
Abin da yafi bata takaici kuwa shine yanzu koda ta kira Mama, Mama bata picking calls nata ba ita kad'ai ba harta sauran 'yan uwan nata. Inhar ba aiki Zeezee keba toh tana kwance a d'aki tana kuka ne, cikin sati biyun nan ba k'aramin zubewa Zeezee tayi ba don har haskenta ya ragu sosai, gata nan ne kawai kullum cikin nadama take.

****
Yau da safe tana girka breakfast a waje kan charcoal ta baro wayarta a kitchen. A dai-dai lokacin da wani friend nata Imam ke turo mata saqo a dai-dai lokacin Adeel ke shigowa kitchen ganin haske yayi flashing kan screen natan yayi sauri ya leqa kasancewar iphone na reading notifications ya samu ya karanta saqon as “morning dear ya kike?” Wani banzan kishi ne ya tokaresa d'aga wayan yayi yasa a aljuhunsa wanda a dai-dai nan Zeezee ke shigowa da soyayyen doyanshi da sardine sauce. Bata cemai komi ba ta wuce dining ta ajiye ta dawo kitchen d'aukan wayarta taga babu sede kallo d'aya tama Adeel ta gano shi ya d'auka. “Kabani wayata.”
“Bazan bada ba, iskanci zaki soma kawomin gida? Waye Imam and why is he referring to you as a Dear One?”
“Ina ruwanka kai kullum da kake waya da 'yan matanka na ta6a yima magana ne?”
“Are you talking back to me?” Fuskanta ta wajen bakinta ya kama da k'arfi ya maqure, “don't you dare banason raini kina ganewa ko?”
“Let me go you're hurting me” ta iya fad'a kad'ai don azaba seda yaga tana wahala sosai ya saketa. “Mugu, azzalimi kawai Allah ze saqa min kuma ka bani wayana ai ba kai ka siyamin ba don haka you have no control over it.“
“Haka kikace?”
“Yes give it back.” Hannu ya zira a pocket nasa yafito da wayan da mamakinta taga ya tarwatsar dashi a k'asa da duk k'arfin da Allah ya basa “I guess I do have a control over it now.” Yana kaiwa nan ya fice sauqa tayi har k'asa gun tana kuka abin tausayi. Yanzu kuma a ina zata samu wani wayan tunda ko bakin gate bayi barinta ta taka. Seda taji ya fita tayi d'akinta. Landline ta d'au ta kira Lubiee tana kuka sosai gabad'aya hankalin ta ya tashi daman tasan ba lafiya ba yadda taji Zeezee shiru kwana biyu.

“Babe please calm down and tell me meya faru? Kina gida ne inzo right away?” Lubie tayi stating hankali duk a tashe. Hanci taja sannan tace, “ko kinzo ba ta inda zaki shiga locking d'ina yake baya bari na in taka koda bakin gate.”
“Subhanallah shi waye?”
“Adeel.”
“Adeel? Adeel fa kikace kunyi fad'a ne?”
“Kaca-kaca Babe ashe Adeel ba sona yake ba tunda ya ringa bani wani capsules seda na rasa mahaifata.”
”Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!” Labarin komi Zeezee ta bata wanda ya mugun bawa Lubiee mamaki bata ta6a sanin Adeel is as wicked as this ba. Ranta ya matuqar 6aci tayi hanging call d'in tare da kiransa. Se a karo na biyu ya d'aga.

*MIEMIEBEE Team #YGC!*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*Febuary, 2017*
4⃣3⃣

_Its my biggest pleasure giving this whole page to you guys alone *MIEMIEBEE FANS❤* Group, its indeed a blessing having you guys. Funny how you'd spend the whole day talking about Zeezee, Adeel and Mag-Gen LOL well it gives me pleasure going over and over your chats I never get tired of it. God bless you for me AMEN I heart y'all to pieces, a big heart for y'all ❤ #OneLove❤_

“Halo Lubiee?”
“Haba Adeel! Haba what's wrong with you?”
“Kekuma menayi kike scolding d'ina haka?”
“Harma tambaya na kake? Mesa kakeyi wa Zeezee haka? Me tai maka da har zaka riga d'ura mata magani kana destroying mata womb?”
“Oww haka tace miki? Toh nayi kinga please am busy right now I dont have time for this” bejira jin me zata sake fad'i ba ya katse wayar, mamaki ne sosai ya rufe Lubiee shiyasa ita tun farko bata so Zeezee ta koma gidansa ba, mutuncin sa kad'an ne.
Se 9pm Adeel ya dawo gida yana watsa ruwa ya nufi d'akin Zeezee ya tarar da ita zaune a one angle cikin d'akin ta had'a kai da guiwa. Koda taji shigowansa bata d'aga kai ba, “Ke Zeezee!” banza dashi tayi “am talking to you tun ba ayi nisa ba har kin soma kire-kiren waya kina yad'a what's going on between us? Ke kika jawo komi inda kin bini a hankali da duk haka be faru ba, apologise to me and we will be back as how we use to be before.”
“Apologize to you?” Ta d'ago kai finally ta furta da mamaki, “menayi ma da zan baka hak'uri? Ni da kai waya kamata ya baiwa wani hak'uri? Kamin destroying mahaifa an kana expecting d'ina na baka hak'uri? For what? Adeel koda kaine autan maza na yafe ka, na hak'ura abinda kamin ko maqiyi na bazemin ba.”
“Haka kikace? Kece zaki cutu just apologies to me and it'll bygone.”
“Never! Am never apologising to you again wad'an dana maka da a baya suma inda I can take them all back da nayi, ka cinye kanka kaga dama, nayi nadaman saninka Adeel, I wish I've never met you, inda Allah

46 / 98