YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   80 / 98

237K to 240K   out of 291.7K words

  Nan fa ya kama Hajiyar red handed tana dariya bama murmushi ba wanda tuni ta tsuke fuska ganinsa amman inaaa ya riga ya gan ta.

    "Princess?" Da wuri ta sauk'e idanunta a k'asa. Komawa yayi ya zauna gefenta "Princess?"
  "Na'am" ta amsa not looking at him.
  "Look at me." Da wuri ta kad'a kanta.
   "Kuma murmushin me kike? Princess anya kuwa?"
  "Anya meh?" Finally ta d'ago kanta tana kallonsa.
  "Anya ba faking rashin lafiyar nan kike ba Princess?"
  "Kaman ya Sweetheart? Dan ba kai keda cikin ba ai dole kace faking nakeyi, ni kad'ai nasan abinda baby'n ka kemin." Ta qare maganan tana zum6uro baki.
  "In haka ne toh dariyan me kikeyi? Wanda bashida lafiya yana dariya ne? Kuma ina juyawa kika sake fuskar."
   "Haaa'a! Ni murmushi nayi ba dariya ba. Yanzu ma murmushi ban isa inyi ba Sweetheart shikenan ya zama abin magana akai?"
  "Yanzu Princess kina kallon cikin idona kina min k'arya koh?" Sekuma taji ta kariya. "Nifa ba k'arya nake ba."
  "Ga jikinki ma ba zafi."
  "Alright alright naji ka kamani ina maka k'arya I'm sorry, I just can't help it and wannan plan d'inne kawai solution gashi yanzu sun k'ara maka hutun sati biyu ai, it worked!" Da mamaki ya tsaya kallonta har tayi fooling nashi haka be gane ba? Lallai kuwa ta fisa wayo, "so duk kuka-kuka da su awch da wash na d'azunnan duk k'arya ne?" Kai ta gyad'a mar a hankali "am sorry."
"Haba! Princess kinsan yadda hankalina ya tashi kuwa?"
   "I'm sorry Sweetheart but kaima inda kaine a shoes d'ina you'll do exactly the same thing bana son ka tafi, I want you by my side."
   "Yanzu kenan duk sharri kikayi ta wa Little Princess d'ina?"
   "Ba Princess bace, Soldier ne kuma nasan ze yafe min kaman yadda Daddy'nsa ya riga ya yafemin ko?" Tayi maganan cike da shagwa6a.
    "Am very mad Princess." Hannunsa ta kama ta had'a da nata tana murzawa soothingly, "Sweetheart please don't be I'm sorry."
   "Kinsan yadda hankalina ya tashi kuwa? Ban nuna miki bane fa kawai, har kai na sanda yamin ciwo bana son ganinki ba lafiya."
  "I'm sorry Sweetheart please forgive me, I couldn't think of a better plan shiyasa, ka gane mana bana son ka tafi ka barni ne."
  "Uhmm" zalla yace.
   "Baka hak'ura ba har yanzu?" Hannun nasa ta sake ta kama kunnuwanta both "I'm sorry My Soldier I won't do it again, please." Kallonta yayi na 'yan seconds sannan ya miqa hannunsa ya sauk'e hannayen nata. "Promise?"
  "I cross my heart."
   "Toh na hak'ura."
  "Thats My King!" Ta fad'a tare da shigewa jikinsa tana hugging nasa, shima hugging nata yayi back yana shafa bayanta a hankali, "but my plan worked atleast you are staying with me for the next two weeks, it isn't bad or is it?"
   It is yake son ce mata dan kuwa idan ya tafi yanzu bai sake zagayowa se nanda 3 months, tafiyan da be ta6a yi ba zeyi wannan karan. Yasan idan har ya sanar da ita akwai tashin hankali.
    "Is it?" Ta sake tambayarsa jin shiru. Breaking hug d'in yayi tare da cupping face nata "it is not Princess actually nima ba son tafiyan nake ba, we get to spend two more weeks together." Hannunta ta aza akan nasa dake rik'e da fuskarta tana shafawa a hankali.
  
   "I love you My Soldier, gani nake like bazan iya rayuwa ba idan ba kai, na gommaci in rasa komi a duniyan nan harta rai na da akan in rasa ka, banida burin da yafi inga muna tare kuma ina sanya ka farin ciki. I love you eternally." Kissing lips nata yayi lightly but with so much emotions, assuring her he is with her forever. A hankali yayi pulling out, "I love you more Zainab, for all my life ke kad'ai ce macen dana ta6a so. Despite all the different types women I met during my time in school, despite all those Mama introduced to me, duk cikinsu ba wacce ta ta6a yimin, but ke? For the first time that I set my eyes on you Zainab, my heart skyrocketed, alokaci guda naji ina sonki even though I've never experienced love I know it was love, alokacin banida burin da yafi in mallekeki and make you happy-"
   Katsesa da wuri tayi sounding disappointed "and a lokacin I failed to see you for who you are, I was dense and stupid and blinded by Adeel's playful love na kasa baka chance."
"Don't talk like that Princess, here we are together today ready to die for each other, it is all that matters right?" A hankali ta gyad'a mishi kai, "I love you Habeebi kasan haka Fannah ke kiran Anas wani love story dana karanta and sunan yamin dad'i sosai."
"I love you more Habibtee, bari in had'o miki tean."
"Muje mu had'a lunch tunda ba rashin lafiya again."
"LOL pretender kawai, You sure about this?"
"Yes Sweetheart." Hannunsa ya miqa mata tasa nata ciki sannan ya mik'ar da ita a hankali suka fice kitchen. Macaroni me rai da lafiya suka girka da minced meat all over se k'amshin girki ke tashi a gidan. Atare suka ci abincin sannan suka fito waje gun garden suka zauna suna shan iska kamin Maghrib ya shiga.






*MIEMIEBEE. Team #YGC🎀*
Beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*March, 2017*
7⃣1⃣

_Where is the Most Sweetest Angel of them all? MY SUPER STYLISH BITCH. Just in a swift motion kika zame YAR GATAN MIEMIEBEE, know that I am head over hills in love with you, ina godiya da kalan soyayyar da kike nunawa ZAIMEEN🔥 and YGC🎀 in whole. You guys are always on my mind Mio 17 Babe Cute Xarah, Ashnur Pyar (indian Babeh) and Queen Meemi. A big shoutout to you Lovers #OneLove💞 Team YGC!🎀_

***
Life moved on, cikin Zeezee se dad'a girma yake a hankali a hankali. Two weeks d'in ya k'ara mata, cikin two weeks d'innan Zeezee ji take just like a Queen se abinda takeso Al'ameen yake mata.
Tun ana saura kwana biyu Al'ameen ya koma Abj Zeezee ta soma kumbure-kumbure, shi kuwa binta yake a hankali saboda condition nata. Murmushi ma ta d'auke yi masa. A ranan da ze tafi ya d'ago akwatinsa dan shirya kayakinsa ciki. Dama on normal basis Zeezee ke tayasa su shirya atimes kan ma ita ke shirya masa ita kad'ai amman banda yau. Juya mai baya tayi tana kwance bisa kan gado Tana game abinta.
"Princess?" Banza da shi tayi sanda ya tako har zuwa gabanta, take ta gwada juyawa wanda tuni ya kama hannunta. "Princess yau bazaki tayani shirya kayakina ba?" Baki ta tura mai tare da had'e rai without saying a word. "Haba mana Princess ke shikenan kullum muna abu d'aya kenan?"
"Ni ka sake min hannu bacci nake ji."
"Bacci? Yaushe kika fara bacci by 8pm?"
"Yau" ta fad'a a takaice.
"Bazaki tayani ba kenan?"
"Eh mana ni banason ka tafi meyasa zan taya ka shiri?"
"LOL toh shikenan zanje in had'a abu na." Har ya miqe seta rik'o hannunsa tare da jansa da iya k'arfinta seda ya fad'a kan gadon a gefenta. "I don't want you to go." Ta fad'a tana lumewa jikinsa, hugging nata yayi gagam.
"And I don't wanna go either." A hankali ta raba jikinta daga nasa ta miqe "muje mu had'a maka."
"Kin huce?"
"Nop kawai zan taya kane bana son ka gaji kai kad'ai is better mu gaji together." Pecking forehead nata yayi sannan suka k'arisa gun wardrobe d'in. Sede wani hanzari ba gudu ba yau Zeezee ta lura da yawan adadin kayakin da Al'ameeen keta iba.
"Sweetheart kayakin nan na zuwa ina ne?"
"Abj of course."
"I know I mean sunyi yawa."
"You think so?" Yayi maganan chan ciki ciki wane me 6oye abu yana susan back head nasa.
"Sweetheart you're hiding something away from me." Ta fad'a bayan dogon nazarin da tayi.
"I'm not Princess."
"Toh mesa kake iban kayaki dayawa haka? Shekara zakayi ne achan d'in?"

"Shekara kuma Princess? Saboda incaseties ne kawai."
"Ban yarda ba, zaka jima ne ko? Maybe dan k'ara maka sati biyun da sun kayin ne sukayi demanding prolonging stay naka achan d'in am I right?"
"What are you talking about Princess kin d'auka wai ni tafiyan nan dad'i yake min ne? 2 months kawai zanyi in dawo."
"Are you sure My Soldier?"
"In shaa Allah." Murmushi kad'an ta saki masa a yayinda shima ya miyar mata but deep inside tunanin ya zeyi ya 6ullo mata da al'amarin yake yasani shi da ya sake dawowa se nan da 3 months ko fiye da haka ma. Suna hira suna shirya kayakin har suka gama suka watsa ruwa sannan suka kwanta cozy under the blanket.

Kamar yadda Zeezee ta saba ko wani tafiyan Al'ameen se tayita kuka haka wannan karan ma, ko rakosa waje ta kasa, everlasting kiss ya bata sannan wa baby'nsu ya fice. Tun safiya ta kama kuka har seda bacci 6arawo yayi gaba da ita se bayan Azahar ta tashi inda ta tarar da several missed calls nasa. Seda ta idar da Sallan ta dawo ta kirasa.

"Hello Princess?"
"Na'am Sweetheart kunyi landing lafiya?"
"Lafiya, kinbar kukan haka ko?"
"Ai zan soma sabo yanzu."
"Yi hak'uri Princess banason ki samun little Princess d'ina a damuwa."
"Shine ni ka tafi ka barni, akwai damuwan daya kai wannan ne?"
"I'm sorry kinji? Zan dawo soon enough."
"Wallahi gidan ba dad'i inba kai."
"Ko zaki koma gun Mama ne toh?"
"Nop no need mun kusa resuming school ai probably next week."
"Oh god no! School ze sake stressing min ke out."
"Toh ya muka iya?"
"Allah bada sa'a okay? I love you rananda bakiya jin dad'i ba sekin fita lectures d'inba stay at home and rest."
"Okay My Soldier zan fita gidan Lubiee, am I permitted?"
"Ina kika kai kunneki d'azu da nake ta ce miki na baki izini kije duk inda kikeso just don't stay late at night?"
"Ina ta kuka zaka barni ina kuwa na jika."
"Uhm toh ni na baki izini kinji?"
"Toh thank you, bari in shirya."
"Toh ki gaishe min da mother in law na."
"Toh Afrah zata ji bye, I love you."
"I love you more" ya fad'a tare da hanging. Nan da nan ta shirya ta wuce gidan Lubiee, chan suka had'u da Omar ma inda suka ta hira kaman ba gobe se kusan Maghrib ta dawo gida.

Life moved on, in a week time su Zeezee 'yan 300level suka koma school, sosai ta miyar da hankalinta ga karatu, anytime she is less busy kuwa zata kira Al'ameen nata ko tayi mar video call suta hira. Baby'n su na nan cikin k'oshin lafiya sam bata wasa da appointements nata. Ahaka fa har sukayi spending 2 months apart nan Hajiyar ta soma matsawa Al'ameen da yaushe ze dawo at first k'arya ya mata yace zuwa next week ze shigo saboda besan ta ina ze soma sanar da Zeezee ba. Haka har satin ya cize be dawo ba nan ma ta sake kiransa harda 'yar k'wallarta, and again ya sake yi mata k'aryan in 5 days time ze dawo. Kuka ta fashe mar dashi ita she can't take it anymore she needs him, shikuma ya sanar da ita sauran masa 3weeks infact 4weeks saboda 'yan gun aikin nasa sun mai prolonging zaman nasa for a week more ya kasa. Da k'yar ya samu ya lalasheta ta yarda akan cewa in five days time d'in ze dawo.
Al'ameen ya shiga damuwa sosai saboda besan kuma wani k'arya ze sake shiryawa Zeezee ba next time if she calls, he don't think he can keep on the pretense also, is better ya sanar da ita su yita ta k'are.

_5 days later... exactly ranan da Al'ameen yace ze dawo._
Sanin daman idan har ze shigo yana sanar da ita kokuwa idan beyi bama bayi wuce 3pm be dawo gida ba yasa Zeezee ta yafe lectures na ranan, even though ta tashi ba seti saboda leg cramps dake ta kamata kasancewar cikin nata yayi girma ba laifi getting to 6 months now. Hakan besa ta kwanta ba aiki sosai tayi ranan abinda ya kama kan shara, mopping, goge-goge sannan ta girka favorite na Al'ameen tuo da miyan ganye, tayi setting dining itama ta d'au wankanta tasa wata doguwar rigarta daya mugun amsan figure'nta da d'an k'aramin cikinta dake 6ullowa idan tasa loose kaya. Rabonsu da waya tun jiya, bata damu da kiransa ba saboda tasan mostly rananda ze dawo ba'a cika samun wayansa ba. Tun 2pm data idar da Sallah tayi zaune a parlour tana jiran dawowan Al'ameen sede shiru. Abu fa kaman wasa har 4:30pm Al'ameen be shigo ba by now kam tayi giving up tasan baze dawo ba he just tricked her daya ce mata ze dawo yau, toh why? Duda Tasan zargi zunubi ne kuma ba halin Al'ameen bane kula mata amman se raya mata shaitaan ke da Al'ameen ya fara cheating ne akanta. Time da zeyi tafiya yace 2 months zeyi, yazo yace ze k'ara sati yazo yace 5 days yanzu gashi yau d'inma ba alamansa. With this thought running on her mind kawai seta fara kuka a rayuwa bata son tayi sharing Al'ameen da wata, tasan its so selfish ta fad'i hakan amman she can't help it, tana sonsa fiye da tsammanin kowani d'an Adam. Wani sa'in har kishin 'yan uwansa Aysha da Salmah ma take ganin how they are free with him, barin Aysha dake auta har cinyansa tana d'alewa to talk more of side cheeks she can't handle them. Kuka ta shiga yi sosai tana shessheqa, in the process wayanta dake gefen ta ya shiga ruri kaman karta duba don haushi amman ta dage ta leqa gani tayi Al'ameen na kira.

Shima tun safe ya kasa samun peace of mind, ko aiki ya kasa fita yau saboda beyi fulfilling promise daya d'au wa Princess tasa ba, yasan sarai she is mad shiyasa tak'i kiransa har yanzu thats why yayi calling nata instead. Tana ganin call d'in har ya tsinke bata d'aga ba, video call next ya shiga yi mata nan shima tak'i d'agawa, again ya shiga calling nata wanda in the process ta kashe wayar nata kwata-kwata. Nan fa hankalin Al'ameen ya sake tashi, guards nasa biyu da ya bar mata a gida ya kira ya buk'ace sa daya kai wa Zeezee wayar. Tana zaune kan kujera ta since d'aurin data sha ta ajiye a gefe se kuka take shark'af shark'af ta jiyo knocking. Sanda ta share hawayenta ta tambaya.
"Waye ne?"
"Sadiq ne Madam."
"Lafiya?" Tayi maganan tana clearing voice nata.
"Uhhm Madam please ki bud'e." A hankali ta mik'e ta bud'e mishi k'ofan. "Lafiya?" Ta sake tambaya. Wayansa yake miqa mata "Boss ne ya kirani yace in had'aku ta nan gashi yana kan wayan." Duk anan Al'ameen na sauraronsu.
"Princess yi hak'uri ki amshi wayan kinji?" Ya fad'a cikin zazzak'ar muryansa me narkar wa Zeezee da zuciya ta speaker phone. Shiru tayi wane me nazarin abu.
"Princess? Am sorry yi hak'uri ki kar6a kinji?" Ganin bata ko motsa ba and bata da niyyan hakan Sadiq yace, "please ki kar6a Madam Boss is so worried." Kallonsa tayi sannan ta miyar da k'ofanta ta rufe. Me kuma Al'ameen ze sake ce mata bayan evidence sun nuna he is cheating on her. D'aki ta wuce ta cigaba da kuka abinta hannunta rik'e da cikinta.
"Am sorry Sir, ta rufe k'ofan she is not ready to talk."
"Its okay Sadeeq thank you."
"No please don't thank me again Sir, its my job."
"Good" ya fad'a tare da katse wayan. Yau ina zesa kansa? Tunda yake Zeezee bata ta6a yimai fushi kaman na yau ba meke faruwa haka? Shi da yasani da tun da a baya ya yi maning up ya sanar da ita actual

80 / 98