Author : MIEMIEBEE Category : Romantic Hausa Novels
necktie dai-dai tazo basa goodluck kiss kenan Zeezee ta bankad’e k’ofa yau harda ‘yar kukanta. A firgice Ibraheem da Fateemah suka juya suna kallon ta, duk kunya yabi ya ratsa Fateemah “uhm Zeezee lafiya?” tayi saurin tambaya. Kuka tasa gun ta k’arisa wajen Ibraheem da gudu tare da hugging nasa tana kuka. “Wai meke danunki ne? Ko aljanu sun shige kine bamu sani ba.” Ibraheem yayi maganan a bit confused. “Sakeni toh!” Sake matsesa tayi ajikinta “Ya tell me its a dream Baba be mutu ba tell me please” ta hau rusa kukan munafirci.
“Mutuwa kuma?”
“Maybe mafarki tayi” Fateemah ta amsa shi.
“Toh sakeni mana Baba be mutu ba da Allah mafarki ne.”
“Tsoro nakeji” ta cigaba da sobbing, hannu Fateemah tasa zata jata daga jikin Ibraheem ta bata warm hug instead aikuwa Zeezee tak’i, haka ba yadda Ibraheem ya iya yayi hugging nata back yana caressing bayan ta nan munafukan ta b’ullo da rabin idonta tana kallon sauyin yanayin fuskan Fateemah dan dole taji tokari a zuciyarta dukda tasan siblings nesu amman kishi irin namu na mata baze barta ba. Sun kusan minti uku a haka sannan ta d’ago daga jikinsa “shikenan?” ya tambayeta
“Eh nagode.” Kai yayi nodding “koma kije ki kwanta toh ba abinda ya samu Baba, zan tafi office if you need anything else ga Fateemah.”
“Toh Allah ya kare.” Nan ta fice tana murmushi ita kad’anta tana isa d’aki ta baje kan gado “right timing nayi ashe, wannan Fateemah ta fiye iskanci wallahi kullum cikin kissing Yaya shikuma sekace zombie yata biye mata mschww! Ai wallahi muddin ina gidan nan sekun dawo salihan dole. Ko a babu nasan na sosa miki rai.” Bacci takoma se 12noon as always ta tashi tayi wanka ta shirya tsaf sannan ta fita, breakfast nata ta tarar a dining ta bud’e ta gama ci sannan ta shiga k’wala wa Fateemah kira, daga d’akinsu ta amsa nan Zeezee ta bud’e ta shiga ta sameta zaune a k’asa tana gyaran wardrobe nata.
“Sannu Aunty, gyaran drawer kike?”
“Eh wallahi Zeezee harkin karya?”
“Eh bazan tayaki.”
“A’a bari karki damu.”
“Allah kibari na tayaki” nan suka shiga gyara mata. Ashe dekam Zeezee da biyu tace zata taya tan don tun kafin ayi bikin, cikin kayan lefen taga wani lace daya mugun mata kyau ba yadda batayi da Ibraheem ya bata ba yak’i gakuma koda ta duba shagunan Baba duk babu.
Tana cikin had’a mata wardrobe d’in taci karo da lace d’in ko d’inkawa ma Fateemah batayi ba “wow!” Tayi exclaiming. “Aunty Fatee wallahi wannan lace ya had’u gashi favorite color na black and red kap Bauchi na duba ban samu ba.”
“Haba kina so ne?”
“Sosai ma wallahi.”
“Toh shikenan ki d’auka na baki.”
“In d’auka?!” tayi maganan unbelievably bata d’au Fateemah is as sweet as this ba. “Eh ki d’auka ba kina so ba? Na baki.”
“A’a Aunty ai naki ne.”
“Banason haka fah, nace ki d’auka.”
“Wow! To nagode Allah saka da alkhairi” nan ta cigaba da ninke mata kayakin tana cikinyi taci karo da wani white blouse daya mugun mata kyau again gashi always same as her size nanma tayita zuzuta shi haka Fateemah ta d’au ta bata a takaice seda ta kwashi kayakin Fateema har hud’u da shoe and bag guda d’aya sannan taji dad’i. Cike da jin dad’i taje tasa cikin akwatinta. Kitchen Fateemah ta zarce ta shiga had’a lunch sede tun d’azu kasala ke damunta tana cikin soya kaza ta soma jin amai take ta nufi sink ta shiga kwararowa, nan fa uwar gulma ta shigo kitchen d’in a 360 a ranta tace _bade ciki ba!_
“Aunty Fatee lafiya? Subhanalli me kikaci haka? Sannu” nan ta tayata ta d’auraye bakin ta.
“Dama bakida lafiya ne?”
“Kar ki damu am fine something just came over me.”
“Ahakan ne you are fine? Bari na kira Ya.”
“A’a barshi karki tada mishi hankali a off-” bata k’are maganan ba tasake juyawa sink ta cigaba da kwararo amai tana iddawa Zeezee ta d’au waya ta kira Ya Ibraheem kan gida ba lafiya. Not long enough ya iso hankali a tashe, Fateemansa ya tarar zaune a kasalance kan kujera. ”Omg! Sweetheart whats wrong?”
“Babu nifa seda nacewa Zeezee karta kira ka tak’i jina, am fine.”
“Wallahi batada lafiya Ya amai tayi sau uku fitanka.”
“Baby kinci wani abu ne?”
“Wallahi I don’t know I keep on feeling nauseatic and weak.”
”Humm kinci wake kenan” cewar Zeezee. Sam Ibraheem be gane me hakan ke nufi ba, ita Fateema data gane se kawai tayi shiru.
“Wake taci ya b’ata mata ciki?” Ibraheem ya tambaya.
“Ai bama ita taci ba Ya, kai ka bata dan haka se kuje asibiti.”
“Nikuma? Yaushe?”
“Yo ina zan sani abu acikin duhu kuje asibiti de kafin jikin nata yayi worse.”
“Uhm Zeezee d’an kashemin gas d’in muka dawo zan gama soya chicken d’in.” cewar Fateemah.
“Ga Zeezee seta k’arisa ai kafin mu dawo.”
“Wallahi karna k’ona kace zakamin duka gomma na fad’a maka tun yanzu ban iya soya kaza ba wallahi.”
“Ko kunya bakiji ba da girman ki mschww”
“To meh abin kunya aciki? Wanda taci wake bata ji kunya ba seni, ko ince wanda yabada wake beji kunya ba seni?” kai kawai Fateemah ta kad’a.
“Wai me kike fad’a nekam? Wuce kije ki kashe gas d’in useless kawai. Kinsan gomma kin nutsu kin fara koyan girki ko?”
“Ai nagama secondary school zan fara koya bari na d’au ma Aunty Fatee mayafinta nima zan biku.”
“Kina gida ba inda zaki.”
“Allah sarki mana Ya.”
“Baby ni kawai kabarta taje jeki d’aukomin mayafi na akan gado Zeezee.” Da ‘toh’ ta fice. In less than 30 minutes suka isa asibiti nan akayiwa Fateema gwaji, not long enough result ya fito nan aka tabbatar musu juna biyu ne d’auke da Fateema. Dad’i kashe wannan happy couple banda Zeezee dake binsu da kallon tsiya “kome abin murnan oho? Dama kam akayi ai dole sakamako ya fito mschw kunada aiki wallahi.” Se anan Ibraheem ya fahimci zancen Zeezee na d’azu batun wai shiya bawa Fateemah wake taci oh! Allah ya shirya masa Zeezee yarinya sam ba kunya. Haka suna isa gida Fateemah tad’an huta tace zata cigaba da suyan sam Ibraheem ya hanata shida Zeezee suka k’arisa suyan nan ma seda ta k’ona kanta ta k’ona shi duka.
Tun daga nan fa rayuwan Zeezee gidan Ibraheem ya soya. Wani irin d’an banzan laulayi ne da Fateemah, ko tsayuwan kirki bata iyayi dan haka bata iya aikin komi, duk wani aikin gidan Zeezee keyi banda girki saboda daman bata iya ba dan haka Ibraheem ke cikin siyo abinci ba dafe ba dare. Zeezee kullum cikin k’orafi ita wallahi hutun ma ya isheta zata koma gida.
*~ *~ *~
“Zeezee! Zeezee!” Ibraheem ya kira ta daga ciki.
“Na’am” ta amsa tana zaune a parlour seda ta gama d’ura ashar sannan ta mik’e ta nufi d’akin nasu “gani.”
“Ki had’awa Fateemah custard.”
“Ni ban iya ba.”
“Baby she don’t have to kabarta please.”
“Had’a custard ma baki iya ba? Cinki za’a zo ayi ne?”
“Ni wallahi zan koma gida nagaji da ni nace tayi cikin.”
“Me kike ce?” yayi tambayan in a serious tone daya razana Zeezee.
“Babu nace barin je na had’a mata sannu Aunty Fatee” tana kaiwa nan ta fice in less than 15 minutes ta had’a ta dawo kad’an Fateemah tasha Zeezee ta miyar da sauran, ga wanke-wanke nan tun na jiya da rana bata wanke ba. Da yamma Fateemah tad’an warware ta fad’a kitchen se gani tayi wanke-wanke nayi mata sallama. Kai kawai ta kad’a ta shiga wankewa tana cikin yi Ibraheem ya shigo “Sweetie wanke-wanken meh kuma bayan kinsan you’re sick, kibari Zeezee zatayi.”
“Naga kaman muna tak’ura mata dayawa kabari yanzu zan gama.”
“Kibari nace, Zeezee zo nan!” seda ta gama b’ata lokaci ta fito “gani.”
“Oya karb’i wanke-wanken ki gama.”
“Allah sarki Ya kabari ko zuwa gobe mana, yau fa nayi shara.”
“Meaning? In anyi shara ba’a wanke-wanke kenan?”
“Ni wallahi zan koma gida nagaji.”
“Ai tunda kika kawo kanki sekun kusa fara Neco zaki koma gida.” K’afa tahau bugawa amman kota kanta beyi ba yaja Fateemah suka fice. Harara tabi wanke-wanken da sannan daga bisani ta d’aga wuk’a ta yanke yatsanta dagangan nan jini yahau bulbula. Wani irin rikicaccen ihu ta saki Ibraheem besan a lokacin da yafito ba “amman lafiyan ki kuwa?”
“Wayyo Allah yatsa na, jinin jikina ze k’are na shiga uku!”
“Meya sameki?” yayi maganan yana k’arasawa gun sink d’in, kawai gani yayi hannun Zeezee na jini sosai.
“Subhanallahi! ya akayi kika yanke haka?” Tap ya bud’e yasa yatsantan nata underneath, se ihu take bayan daya gama mata dressing ya kalleta “dagangan kika yanke hannun naki dan karkiyi wanke-wanken ko?”
“Mahaukaciya ce ni da zan yanke hannu na da kaina? Ni wallahi yana min zafi.” bakinta ya bige paw! “Nikuma me nace? Wayyo Allah hannu na, wallahi yana min zafi”
“Toh dama ba dole ya miki ba mschww!” shi da kansa ya k’are wanke-wanken ranan. In 2 days time suka samu meh aiki dan duk yadda zasuyi sun san Zeezee bame aiki bace.
One more week ta musu Yasmeen ta haihu ta samu d’anta. Nan fa Zeezee ta had’a akwatinta har airport su Ibraheem suka kaita ya sallameta da 10k Fateema kuma 5k da kuma turmin zani d’aya. Daga Abuja ta wuce Kaduna inda ta had’u dasu Mama, d’an Yasmeen kyakkyawa kaman Babansa anyi suna yaro yaci sunan Kakansa (baban mijin Yasmeen) Sulaiman. Bayan suna su Zeezee suka dawo Bauchi. Ko nunawa Mama kud’in dasu Ibraheem da mijin Yasmeen suka bata batayi ba seda ta gama kashe kud’in tukunah ta fad’a mata.
Kowa na preparation na Neco banda Zeezee data sa yawo a gaba, yau ma as usual by 11am ta gama shiri ta fita, ta shiga cikin gari tana ta driving da gudu kamar yadda ta saba ta k’ure music, wayanta ne ya soma ringing d’agawan da tayi don ganin waye kawai the next abinda tayi noticing shine wani Baba tsoho dake dab da gabanta. Kafin ta ce zata danna brake harta bigesa. Kan motan ta juya da wuri hakan yasa ta buga kanta jikin wani pole. Kaca-kaca gaban motanta yayi, wani irin ihu ta saki daga nan bata sake sanin meya faruwa ba. A sume kanta na jini aka ciro ta daga motan, ita da tsohon data mai k’ariya biyu dakuma fashewan kai aka tattarasu se Teaching Hospital. Baba aka fara kira aka sanar dashi halin da ake ciki.
_45 minutes afterwards, Teaching Hospital..._
*© MIEMIEBEE*
👄👄👄👄
beeenovels.blogspot.com
PAGE 24
*December, 2016*
Tsaye Mama da Baba suke a corridor’n k’ofan da Zeezee ke ciki, kallo d’aya za’ayi musu asan suna cikin babban tashin hankali sam sun kasa zama gu d’aya se safa da marwah suke wajen. Ana cikin haka k’ofan d’akintan ya bud’u, kusan da gudu su Mama suka nufi gun “Dr. How is she?” Sukayi tambayan in unison.
“You two must be her parents, am I right?”
“Yes” Baba ya amsa a yayinda Mama ta gyad’a kai.
“Karku damu she is in a stable condition, alhamdulillah bataji wani ciwo ba kanta kawai tad’an fasa ta gefe wanda a sanadin haka glass ya samu ya shiga amman mun cire har anyi d’inki yanzu haka ma zaku iya shiga ganinta.”
“Alhamdulillah” kawai ke tashi wajen “mutumin data bigen fah?” Baba ya tambaya.
“Eh an kawo min report nasa d’azu, kariya biyu ya samu a k’afa seda gefen kansa daya fashe shima bayan nan alhamdulillah.”
“Toh alhamdulillah mun gode Dr. Bari mu duba ‘yar tamu.”
“Excuse me” yana kaiwa nan ya basu waje. D’akin sukayi rushing kwance suka tarar da Zeezee kan gado ta rik’e gefen kanta da hannu “sannu k’anwata sannu” Baba yayi maganan yana dafe kafad’arta.
“Sannu Zeezee how are you feeling?” asked Mama. Kuka tasa musu, da k’yar suka samu tayi shiru “Baba kaina ciwo.”
“Ai dole ne dama Zeezee mugode wa Allah ma anan abin ya tsaya beyi gaba ba.”
“Baba mutumin dana bigen fah? Ya mutu?”
“A’a yana raye be mutu ba.”
“Alhamdulillah” tace.
“Hmm aini shiyasa ban goyi bayan wannan motar da aka siya mikin ba, yanzu da tsohon ya mutu azumi sittin (60) ya hau kanki, kai kuma inhar danginsa suka k’i yarda seka biya diyya, duk wannan wani irin tashin hankali ne?”
“Qaddara bata wuce ranarta Hafsah, koni nan zan iya yin hatsari nakai mutum lahira, bawai zancen dan Zeezee is too young to drive bane.”
“Ai dama kai bazaka tab’a shiryuwa ba inba wai kuka da hawaye Zeezee ta saka ba.”
“Toh ya isa, yarinya batada lafiya ba suratai yakamata muyi ta mata akai ba, godiya wa Allah ya kamata muyi tunda anan Allah ya tsaida qaddaran. Sannu ko K’anwata kina jin yunwa?”
“A’a ni akaini gida banason zaman nan.”
“Karki damu bari jikinki yayi k’arfi.”
★*★*★*★
5 days Zeezee tayi a asibiti akayi discharging nata. Kusan duk friends nata including Adeel sunzo sun gaisheta, shida Lubiee kanma kusan kullum suna kanta. 2 weeks ya d’auketa kafin nan ta warke gabad’aya, bada jimawa ba suka fara neco. Motarta kuwa tuni Baba yakai aka gyara mata yadawo sabo k’al ba kalan jan kunnen da Mama bata mai ba kan yabari se in sun gama makarantar yaso ya gyara mata amman inaa yak’i. Zeezee kuwa ko bayan incident d’in bata shiryu tabar speeding kan hanya ba, ana gama paper zata tara su Lubiee and others su fita yawo. Ranar da suka yi Geography Adeel yazo school ya d’auketa daga school bayan sunci abinci a Mr. Biggs suka wuce chan bayan gari ya nemi waje yayi parking se hirarsu suke sha gwanin sha’awa. Wayarta ya d’aga yayi entering sunansa as password sannan ya shiga cikin photos yana kalla, yana cikin haka yayi coming across pic na wani d’an saurayi ai take ya fusata “waye wannan?” Ya tambayeta harshly. Koda ran Mama ne ya b’aci Zeezee bata rikicewa haka se in na Adeel ne, “Very Own wani pic?”
“Wannan!” Ya nuna mata wayan. “Ko zakice baki san shi ba.”
“Nasan shi but Very Own calm down wallahi ba komai a tsakani na dashi.”
“Then meh pic nasa yakeyi a wayanki? Ban hanaki barin photos na maza a phone naki ba? You’re cheating on me with him right?”
“Omg No! Am not, wallahi ba komai tsakani na dashi, he’s just a friend-” ya barta tayi explaining kanta nma yak’i, ita kanta ta manta dalilin daya hanata goge pic d’in.
“You are lying!” dan banzan zuciya irin nasa besan a lokacin da yayi wurgi da wayan nata ba seta k’ofa yayi, raga-raga yayi kan kwaltan. Hannu Zeezee ta aza kan bakinta in shock, hawaye kawai tasoma zubarwa, wayyo iphone 7s nata!
“Adeel wallahi ba saurayi na bane kaima kasan I only belong to you be kamata ka fasa min waya ba.”
“Na fasan do something about it if you can, just shut up and get out, dama tun ba yau ba nasan am not the only one.”
“Adeel idan ka sauk’eni anan a ina zan samu abun hawa kayi hak’uri please.” Wai shi ya fasa mata waya amman ita ke basa hakuri while actually she can’t remember when last ta bawa Mama hak’uri amman in Adeel ne kullum cikin basa hak’uri take.
“I said get out!” Ya tsawata mata sekace wani mahaifinta.
Gefen titi guda ta nufi ta tsuguna tana me cigaba da kuka abin tausayi, tafi minti goma haka sannan daga bisani Adeel ya fito ya nufi inda take tare da mik’ar da ita har a yanzu kukan take. A hankali ya share mata hawayen nata “am sorry kinji?” Hugging nasa tayi tana kuka sosai “wallahi ba saurayi na bane, am not cheating on you Adeel please believe me.”
“Is okay I trust you, am sorry kinji?” Har mota ya sata sannan ya tattara broken pieces na wayar nata ya cire sim d’in cikin, yaja mota ya kaita gida. Tun shigarta gida take addu’a Allah yasa kar ayi noticing yau wayanta bayi tare da ita. Da Maghrib Zeezee na zaune a d’akinta abin duniya sun mata yawa ita yanzu in Baba ya tambayeta ina wayanta me zata ce mai? Tana cikin wannan tunani Mama ta kirata zuciyarta na harb’awa ta mik’e a sanyaye ta fice, “na’am Mama, sannu Baba” ta gaishesa.
“Yauwa K’anwata sannu, yau lafiya dai koh najiki shiru?”
“Lafiya Mama kin kirani.”
“Eh wayanki zaki aramun nawa airtime ya k’are.” Nanfa Zeezee ta shiga raba ido, “baki jini bane?”
“Naji Mama wayana ya fad’a a ruwa d’azu so na shanya.”
“Shine baki fad’amin ba akai miki gyara?” Fad’in Baba.
“A’a karka damu Baba ze farfad’o in shaa Allah.”
“No wonder yau ba’ayi ta d’aukan selfies na asara ba, jeki shikenan.” Kwana zaune Zeezee tayi ranan as tana nazarin ina zata sake samun wani iphone d’in.
The next day Adeel ya kirata ta d’ayan line nata wanda duk ‘yan gidansu ma basu san tanada wayar ba kan taje ta samesa a so so place, suna gama paper’n taje ta samesa da motar ta. Kallo d’aya ya mata ya gano da akwai matsala murmushi ya saki sannan ya tambayeta ya paper.
“Lafiya qalau” ta amsa sama-sama “why did you call for me?” hannu ya mik’a a seat na baya ya fito da wani packaged leather jikin attached with a small card.
“Meh wannan?”
“Naki ne open it.” Amsa tayi ta karance letter’n amar haka;