YAR GATA CE COMPLETE HAUSA NOVELS BY MIEMIEBEE.txt

Author :  MIEMIEBEE Category :  Romantic Hausa Novels

Chapter   44 / 98

129K to 132K   out of 291.7K words

ta tsana shine tashin hankalin Adeel, wannan kenan!
Zuwa 9pm na dare tana maqale jikin Adeel ta d'aga wayanta for the 1000th time don ganin ko Mama ta kirata, da Adeel ya lura da frequent duban screen da take se yayi deciding da bazi ya tambayeta. “Babe?”
“Yes Very Own?”
“Are you expecting a call?”
“Nnn... No” ta fad'i finally.
“Are you trying to lie to me?” Ya tambaya a hankali.
“Am sorry is just that na d'au ko Mama zata kirani amman shiru Very Own Mama dont care about me anymore.”
“But I do Sweetest Love, you have me, I shall never turn my back against you I promise.”
“I know Very Own but it still isn't enough she's my mom.”
Gashinta ya shiga shafawa a hankali in a soothing manner “I know Babe am sorry kinji?”
“Its not at all your fault.”
“I can be anything for you Babe, a father if you need me, a mother, a brother and also a sister so kidena tada hankalinki let them be and move on okay?” Kai ta gyad'a tana share hawayenta “should I call her instead?”
“You don't have to ita da kanta zata kiraki idan ta jiki shiru.”
“Are you sure Very Own?”
“You don't trust me then , idan na samu misunderstanding da Mami ko Papa before he died da kansu suke nema na ko suban hak’uri ma so karki damu, or dont you trust me?” Take ta d'ago daga jikinsa tare da rik'o hannunsa “stop saying that you know I do alot.”
“Thats my woman get some sleep zuwa 12:00 zamu wuce airport.” Har ta miqe sekuma ya riqo hannunta “but first your medication.”
“Very Own am really okay no more pain.”
“I insist” kad'ai yace mata sannan ya b'allo capsules d'in ya bata yauma kaman jiya seda ta had'iye yabar wajen. Kamar yadda ya fad'i 12am d'in ya tasheta suka shirya zuwa airport kafin su fara boarding Zeezee taso kiran Mama atleast ta sanar da ita amman duk tsoro take kar Adeel ya kamata idea'n tura text message sam bezo kanta ba haka tana ji tana gani ya amshi wayan nata ya musu switching off tare da nasa.

*****
Few days later, jin shiru Mama ta saci jiki ganin Baba na bacci tayi site na Omar ta gwada kiran layin Zeezee don jin ko lafiya tunda tun ranan da aka bata wa Adeel bata sake jin motsinta ba. Abun mamaki kota kira switched off takeji Lubiee ta kira a k'arshe inda take sanar da ita ai Zeezee na Florida ayanzu haka. Mamaki ne ya ziyarci zuciyan Mama, har Florida? Ta tambayi kanta. Shin Zeezee wacce irin d'iya ce ace zata tafi har Florida amman bazata sanar da ita ba, ba k'aramin b'aci ranta yayi ba wanda yakaiga koda da Lubiee ta tura mat digits na Zeezeen ma k'in kirarta tayi, aga wanda ze nemi wani.

*~ *~
Life moved on, Maj-Gen yakasa moving on se a hankali al'amarinsa ya soma dai-daita ya fara rage tunanin Zeezee if not ata farko-farko har Mama Babba ta soma regreting sasa sakan Zeezee da tayi saboda ita sheda ce akan kalan son da Al'ameen keyiwa Zeezee but tasan hakan is for the best shiyasa koda yasamu ya kar6i leave a office tasasa ya dawo gida a wajenta ita da sisters nasa ya zaun suna kula dashi, alhamdulillah yanzu an samu massive improvemet physically tunda har ya koma office amman psychologically kullum seyayi tunaninta always all the time saidai bayi nuna musu.

Adeel de a kullum be fasa baiwa Zeezee capsules dayake bata ba wanda koda zatayi mar tambayan duniya ba fad'amata zeyi ba ganin ransa na 6aci anytime tA tambayesa maganin menene yasa tama dena tambayar nasa yanzu ita wai she trusts him. Duk wani abinda tasan yana iya had'asu ma hasali avoiding take, bata chatting kap dakowa inbanda friends nata mata sanin kishi irin na Adeel. Hakan yasa basu ta6a samin wani understanding dashi Adeel ba, kullum saidai suyi wanka su fita yawo shikenan, duk abinda yagani me kyau ne yana k'ok'arin siya mata suna zaman lafiyansu lau, ahaka har suka samu 3 months Zeezee bata sake ji daga gida ba.
Koda Mama ta bawasu Ya Ibraheem labarin abinda Zeezee tayi mata fusata sosai yayi yace sam se Mama tabasa digits na Zeezee ya kirata yaci mata mutunci amman Mama ta hanasa surely one day she'll need them saboda jini ba abu bane na wasa.

Su Adeel sun samu 3 months 1 week a Florida yace shi zaman chan ya ishesa yanason ya dawo gida. Zeezee tafison zaman chan sabida gabad'aya ta manta da problems nata har wani kauri ta k'ara, tanason cemasa sud'an sake prolonging zaman nasu amman tasan halinsa bayi son ana questioning actions nasa. Haka cikin kwanciyar hankali suka shirya suka dawo Bauchi, Nigeria inda ya d'au musu d'aya daga cikin 2 of his inherited houses as duk sauran ya siyar dasu ya k'arar da kud'in a hosting parties, siyan motoci and other useless expences. Bayan sunyi settling Zeezee ta samu time ta kira Mama a waya suka gaisa ko nuna mata abinda tayi ba dai-dai bane Mama batayi ba saboda there is no point ai ba yarinya bace. Lafiya k'alau suka gaisa sukayi sallama.

*MIEMIEBEE*
www.beeenovels.blogspot.com
👄👄👄👄
🎀🎀🎀 🎀🎀🎀
🎀❣🎀
❣❣
•°•★•°• •°•★•°•
°• •° °• •°
°•° °•°
*‘YAR GATA CE!*👸🏻
•°•★•°•
°• •°
°•°
*_written by miemiebee👄_*

*Febuary, 2017*
4⃣1⃣

_One week later..._
Da dawowan su Zeezee from Florida one week kenan. Tun dawowansu Mami ce ta d'auki nauyin kai musu breakfast, lunch and supper, tayi haka na sati na marmari wato itama ta gaji.
Yau da safe bayan su Zeezee sunyi wanka fes sun shirya sukaji shiru fa yau ba alaman Mami zata kawo abinci ba tare da 6ata lokaci ba ta shiga kitchen ta musu frying chips da omalet komi yayi suka karya. Sun gama breakfast Adeel ya fita ya rage Zeezee kad'ai a gida, chatting suke da Lubiee ganin Lubiee nason cika mata kunne yau ma da zancen da bayi wuce na bata kyautawa Ya Al'ameen ba ta kashe datan nata ma gabad'aya. D'an goge-goge tayi sannan ta sake wanka tahau jiran dawowan Adeel. Bata aza girki ba a tunaninta in Mami bata kawo musu ba shi Adeel ze siyo a hanyan dawowa gida shiko Adeel tunda Mami bata kawo breakfast ba it shows that ba lunch kenan dole Zeezee zata yi musu girki don shi ya gaji da cin abincin waje he is fade up with it. Kusan 2:15pm ya dawo gida as always tayi welcoming nasa da kisses and hugs. Kasa 6oye mar yunwan da takeji tayi ta tambaya a hankali “Very Own baka siyo mana lunch ba?”
“Sayan lunch kuma? Baki gaji da cin abincin waje ba kullum nikam am fade up, Mami bata kawo ba?” Kai zallah ta kad'a mar. “Wow meaning ta gaji kenan so da kikaji shiru you didnt cook anything for us? Am hungry.”
“I didn't, I thought zaka siyo mana its what Ya Al'ameen normally does” ta fad'a a hankali ashe kuwa ya jita.
“What?!” Yayi maganan a fusace “Ya Al'ameen kowa kika ce?”
“Very Own calm down” ta gwada rik'e hannunsa ja yayi da k'arfi “seki je ki samu Al'ameen d'in tunda shi haka yakeyi bullsh*t kawai a gidana kina kiramin sunan wani mschww!” A fusace ya miqe ya shiga d'aki tare da shutting door d'in gbam! Hawaye ta shigayi a yayinda take binsa da kallo. Share hawayenta tayi tabi sahunsa “thank god” ta furta a ranta jin besa lock ba, miqe kan gado yana fuskantan ceiling yana chatting ta samesa wanda yana ganinta yawani juya mata baya. Har gabansa tajeta ta zauna bakin gadon sede banza da ita yayi tamkar besan da halitta gun ba.

Da abun ya isheta a maraice tace, “Very Own am sorry please don't be mad I didn't mean it in a bad way” har anan be tanka taba “am sorry kaji I can't take it you being mad it wont ever happen again kayi hak'uri” anan ne yayi gefe da wayan yana kallonta “pleaseee...” tayi pleading se anan yayi magana “its okay” yace da ita. Dad'i taji sosai wanda koda Allah yi miki albarka Mama tace mata baza taji kalansa ba “you are no more mad?”
“Am not” ya amsata cike da ji da kai. Kwanciya tayi a jikinsa “I love you so much Adeel.”
“I know Babe and I love you too.” Sun jima a haka sannan ta d'ago a hankali “so me zakaci?” Seda yad'an 6ata lokaci yace, “spaggetti da minced meat akai.” Anzo wajen tace a ranta tunda take bata ta6a girka jollof na spaghetti ba ina ma fari yace seta masa heating stew na jiya so take tace masa zata dafa musu fari amman tasan halinsa yanzu seyace ta raina sa tana gaya mai abinda zeyi. “Kinyi shiru Babe am starving.”
“Uhmm I was carried away by something don't worry gimmie an hour” pecking nata yayi lightly a lips sannan ta miqe ta fice.

A kan centre table dake parlour ta d'aga wayarta tare da kiran Lubiee dan guiding nata kan ya ake dafa spaghetti.
Seda Lubiee tamata iskancin duniya sannan tayi agreeing zatayi helping nata out haka da prescription and describtion na Lubiee ta samu ta dafa sede gardaman da tayi mata, Lubiee ta bata amount na maggi da amount na red sauce sam tak'i ji ta k'ara nata akai abincin yayi wani irin d'an banzan zak'i da yaji seda ta sauk'e ta d'ana taji tukun “omg!” Ta fad'a tare da kiran Lubiee.
“Babe am dead I should have listened to you wallahi abincin yayi zaqi da yaji over what am I gonna do?”
“I told you.”
“Shut up and give me a solution” ta katseta a fusace.
“Jimin mata nina 6ata miki girki ne kike neman had'iye ni sede kuci haka kokuwa ku hak'ura.”
“Awww ma haka zakice good!” kafin Lubiee tayi magana Zeezee tayi hanging. Eating up nails nata ta shigayi totally out of idea ta zubar ne ta girka sabo? “Kai! It will take long Adeel can't wait for long me zan yi to?” Ba kalan karkataccen shawaran da bata bawa kanta ba amman duk it aiint working daga k'arshe tace kawai zata zubar ta girka sabo zat using ruwan heater. Ta kaiga d'aukan tukunyan kenan Adeel ya fad'o kitchen yunwa yaci maza mehn!

Firgita tayi har tana neman cin tuntu6e “Babe easy!” Yayi exclaiming “abincin beyi bane? am starving“ yayi maganan hannunsa rike da cikinsa.
“Uhm... Ermm...” Ta shiga kame-kame next abinda taji kawai hannunsa akan nata yana neman amsan tukunyan kafin tayi wani k'wararren motsi har ya amsa ya aza kan cooker ya bud'e. A ido abincin soo yum! Yum! Gabad'aya yawunsa ya tsinke ga k'amshin curry'n dake tashi. Fork kawai yayi grabbing shi bek'i yaci a tukunyar bama.
“Ade-” kafin ta qarisa kiran sunansa harya kai baki within seconds count kamannin face nasa ya sauya, kansa ya juya ya zubar dana bakin nasa a sink sannan hurriedly ya nufi dispencer ya tsiyaye ruwan sanyi ya kora yajin dashi duk anan binsa Zeezee ke da kallo tana kakkarwa tana jiran masifa kawai. Seda ya kora yajin hankalinsa ya dawo dai-dai tukun ya nufi gabanta “what is this?” Ya tambaya a tsawace. Shiru tayi danko batasan na cewa ba
“Yes... Am talking to you what is this? Dagangan kikayi kome? Saboda you weren't in the mood to cook, is that it?”
“No Adeel ba-”
“Then yayane?” yayi saurin katseta still a tsawace, tana shaking hawaye na forming a idonta tace, “am sorry ban iya girkin bane this is my first time.” Dala-dalan idanunsa ya zaro waje unbelievably “like seriously?” ya tambayeta still not believing. Kai tayi nodding a hankali. Dariyan rainin hankali ya saki “LOL baki iya girki ba? And you call yourself a lady? How is that even possible? Me amfanin auroki danayi then if you cant make me a dish inci?”
“Ver-”
“Shhh!” Ya katseta “dont Very Own me kingannin nan bana wasa da cikina you know that inhar you cant make me a meal to eat then bazamu shirya dake ba inada mata I can't depend on buying meal always a waje its two of one, its either ki koyi girki or I should figure out what to do with you.” Tana share hawayenta tace, “like how figure out what to do with me Adeel?”
“Yes Zeezee you give me no choice how can I depend on buying food always bayan I have a wife?”
“To da ban iya bafa?”
“Seki koya its never to late.”
“Adeel in cire kud'i ne baka sonyi I have lots of money zan na saya mana.”
“Owww haka kuma table d'in yayi turning into? Ni zaki nunawa kinada kud'i? You mean to say banida kud'i kenan right? Saboda kinga kina hawan wancan so called Ford jeep ko? For a record kisani Genesis G80 na yafi naki taada way much its just the size, you've got some nerves you know” ya k'are maganan yana watsa mata harara. Gabad'aya hankalinta ya tashi se hawaye kawai take “omg! Adeel yaushe nace haka? Thats not what I mean believe me.”

“Oh you're even asking me again? Kin kyauta bravo super woman” be sake jiran jin me zatace ba ya fita yabar mata gidan gabad'aya. Har k'asa ta sauk'a tana kuka gun tafi minti ishirin se tuna time da Mama zatace mata tabi Yasmeen kitchen tana ganin koda abinda takeyi ne amman haka zata ki ga irinta ai yanzu girki nason shiga tsakaninta da Adeel nata, kukan ta cigaba dayi seda tayi me isarta ta sake aza sabon tukunya tana cikinyi ta manta wani step again ta kira ta tambayi Lubiee kuma bataso ta 6ata mata rai d'azu haka tayi kwa6an ta shima bayi cuwuwa. Tana kuka ta zuba duka a leather bag ta zubar a dustbin sannan t had'a golden morn tasha.
Har 5pm Adeel be dawo ba, wayarta taja ta shiga kiransa haka har ta tsinke bai d'agawa haka ta rufe kanta a d'aki ranan ta yini tana kuka. Abu fa kaman wasa har 8-9-10 kai har 12 na dare Adeel be dawo b gashi yanzu ma kwata-kwata kashe wayan nasa yayi. Ba inda Zeezee batasa kanta ciki ba gabad'aya baccin dake idonta ya watse tayi kuka har ta godewa Allah. A parlour bacci ya risketa se 6:30am ta tashi nanma bataga Adeel ba. Ta shiga d'akinsu donyin alwala taji kaman motsin mutum a bathroom in seconds count k'ofan ya bud'u revealing Adeel, binsa da kallo ta shigayi ma'ana ya dawo ya wuceta kwance a parlour be damu ya tadata ba koya d'agota ya kawo ta ciki ba kenan. Ganin kallon bana k'arewa bane ya d'aga towel dake a wuyansa ya shiga goge gashin kansa ahaka har yazo ya wuceta ya nufi wardrobe yana neman kayan sawa. Guiwowi suna kakkarawa ta juyo direction nasa sannan cikin wani erin murya me nuni da tsan-tsan damuwa tace, “Adeel ina ka kwana jiya?” Banza da ita yayi yana me cigaba da harkan gabansa.
“Adeel am talking to you” yanzu kam ta soma hawaye.
“Somewhere better than here” ya amsata in an I-dont-care tone.
“Baka fa kwana a gida ba Adeel, I waited for you for so long har kusan 1am baka shigo ba.”
“Ke kika so dan ni bance ki jirani ba” anan ya ciro kayan da zesan ya juya kenan da gudu Zeezee taje ta fad'a jikinsa tana wani irin kuka me tsuma zuciya, hugging nasa gagam tayi se kukan take, kayan nasa ya wulla kan gado amman yak'i hugging nata back. Tana kukan ta soma cewa;
“Adeel am sorry, am so sorry dan Allah kayi hak'uri that wasn't my intention please stop being mad in girki kakeso na koya I'll but stop staying mad please I beg you...” Ta k'arasa da kuka kaman bazeyi hugging nata ba sekuma ta basa tausayi shi kansa yasan punishment daya bata yayi tsauri, a hankali ya d'aga hannayensa ya zagayesu a bayanta tare da sake kwantar da ita a jikinsa “its okay stop crying am sorry also just dont try it next time okay?”

44 / 98