Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
BAYAN WUYA...
*By*
💫RUMANAH M. DIGGI💫
(Star writer's✨)
*GODIYA*_ Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga buwayi gagara misali, Sarkin sarakuna, shugaban shugabanni, ubangiji makaidaici mai Kowa mai komai. Tsira da Aminci su tabbata ga shugaba ja gaba dan gata annabi Muhammad (s.a.w) da ahalinsa da sahabbansa da dabi'ahn sa baki Daya.
*GODIYA TA MUSAMMAN, FARIN WATA WRITER'S ASSOCIATION 🌙✍️🥰 ALLAH YA ƘARA BASIRA MUTANE NA INA ALFAHARI DAKU AKODA YAUSHE💫*
*SADAUKARWA* na sa daukar da wannan littafin gabadayan sa ga tashar EL_NAJEEB PRODUCTION YOUTUBE CHANNEL. Allah ka karamusu daukaka da nasara Ameen thumma Ameen 🙏🏼
*Godiya* godiya ta musamman ga abokanan arziki da 'yan uwana na gari bazan taba mantawa dakuba koda ina bakin kura 🦬❤️💫🥰
*Bismillahirrahmanirraheem*
BAYAN WUYA...
EPISODE 001.
*****AJAH ROAD*****
*LAGOS NIGERIA*
Duniya darasi!!! Hakika duniya darasi ce ga Wanda zai tsaya ya fahimta, rayuwa juyi-juyi ce yayinda tamu rayuwar tayi mana juyin kwado daga ruwan sanyi zuwa ruwan zafi, hakika ƙaddara abace mara tabbas, babu mai iya sauya ƙaddara face ɗayan taccen sarki, kaddara kamar zanen dutse ce da babu wanda ya isa ya goge, a haka tamu kaddarar ta zo, Kuma a haka muka ɗinga binta dalla-dallah kamar zanen kan taswira.
Rayuwa mai ƴanci ma gata ne, ganin iyaye a kusa dakai babban gatane koda basuda ko sisi, Iyaye ko ya suke rahma ne, kuma wani sashe ne na jikin ka wanda idan ka rasa kamar ka rasa komai. nayi rayuwata cike da rashin ƴanci da rashin tausayi, ga ƙyama ga kuma cikakkiyar wahalar da ta amsa sunanta.
Maraici bashida daɗi ko ya yake, sannan rashi ma bashi da daɗi ko na menene, balle ma ace rashin iyaye gaba ɗaya. na tausayawa marayu kamata, na tausayawa marasa galihu kamar yanda nake.
★★★
Shekaru biyu da suka shuɗe rayuwa mukeyi mai cike da ƴanci da so da ƙaunar juna irin wacce iyalai suke yiwa junan su.
Mu biyu ne awajen iyayen mu Ni, sai kuma ƙanwata.
mahaifiyarmu itakataice wajen mahaifinmu ma'ana ita kadaice matarsa.
Mahaifinmu ba talaka bane Haka kuma baza'a Kira shi da mai ƙudi ba, sabida ko gidan da muke zaune ba gidan mu bane gidan hayane.
Mahaifinmu ABBIE HAMRAZ AWAIS yanada karamin shago Wanda yake hade da gidan da muke zaune ma'ana an gina shagon kofar gidan mu.
A cikin shagon zuba kayan masarufi sosai da baza'a rasaba, kamar dai Kayan Miya irinsu magi, mai, bushashen danƙwa, da sauransu.
Haka Kuma ana siyarda shinkafa, spaghetti, indomie, da Toka, clean, slippers, dadai sauran kayayyakin amfani.
Alhamdulillah mahaifinmu yana samun ciniki sosai sabida kayansa sunada arha ba Kamar na sauran 'yan unguwar ba. Haka ma mahaifiyar mu AMMIE FAHEEMA ba'a barta a baya ba tanayin ƴan Sana'oin ta cikin gida a rufawa juna asiri.
Kanwata Aleena shekarunta goma ne zuwa sama sabida a wannan shekarar ce zata kammala karatunta na primary, yayinda nikuma nakeda shekaru goma sha biyu kuma ina jss one a wannan lokaci duk muna tare cikin rufin asirin Allah.
Iyayen mu na matukar nuna ƙauna garemu ko kaɗan basason abunda zai damemu, domin duk abunda muka nema muna samu a wajen su idan dai baifi karfisuba.
★★★
Yara biyu ne suka shigo gidan, bakunan su dauke da sallama, jikinsu sanya da uniform din islamiyya.
Karamar ce ta rugo aguje kan Wata mata Dake zaune tana gyara shinkafa wacce da alamu ana shirin dafawa ne,
"Amminmu sannu da gida" yarinyar ta fada tare da ɗalewa bayan matar ta sarƙabo hannun ta kan kafaɗun ta
"so kike yi karyani budurwa" matar ta faɗa da fara'ah.
"Ahhh amminmu idan na karyaki na hau ƙafarwa toh?"
Matar na shirin bata amsa ne sai ɗayan yarinyar ta ƙaraso inda suke zaune "Ammi inawuni ya aiki"
"Lafiya kalau LEEYANA ƴan makaranta andawo lafiya, da fatar dai anyi karatu kho" matar ta faɗa tana kallon yarinyar da najie ankira da LEEYANAH.
"Ehhh Amminmu nayi karatu sosai kuma na iya harda ta har kyautar littafi aka bani" yarinyar ta fada tana nufar tilon dakin su Dake can gefen gidan.
bayan tashiga ta cire hijab dinta ta Kuma ajiye Jakarta Sannan ta fito waje ta dawo inda matar nan ke zaune.
ta karbi tiren shinkafar tana faɗin
"Ammi bara natayi, wallahi ammi yau nagaji sosai fa nayi tunanin ma an kare abincin nan".
"To gara sarkin ci ba'a kareba'" Yarinyar da ke kan ƙafar matar nan ta fada tare da yiwa LEEYA gwalo.
Hannu leeya ta ɗago da niyyar ta rankwashi yarinyar sai matar ta rike mata hannu
"kullll karki yarda ki dakammin yar budurwata wallahi"
Turo baki leeya tayi duk da fuskarta na lulluɓe da mayafi hakan bai hanawa mahaifiyar ta ta gane abun da tayi na, sannan tace,
"Ammi kibari nayi mata rankwashi ko ɗayane dan Allah ko zan rage haushin ta danake ji".
Leeya faɗa tana yamutse fuska duk da ba ganin fuskar ta nakeyi ba domin a rufe da ke da wani mayafi.
" Subhanallah!!" leeya haushin me kikeji nata kuma me tayi miki har da zakiji haushinta? sabida ta kiraki gara sarkin ci ae gaskiya ta faɗa" Ammi ta fada tana shirin miƙewa zata tashi daga inda take zaune.
"Ammi wai kinsan yau kasa muka dawo daga IFE AREA kuwa?
Komawa tayi zaune daga niyyar tashinda take sannan tace "ƙasa kuma leeya meya hanaku shigowa taxi yau?
"Wallahi Ammi Aleena ce ta kashe mana kudin taxi bayan kuma ta kashe wadanda Abbie yabata, kinsan ba class dinmu dayaba Saida aka tashemu sannan take gayamin wai kar ma na tara taxi domin ita ta kashe kudin taxi din, Ammi haka inaji ina gani muka dawo gida a kasa".
Aleena da tunda aka fara magana hannunta ke dafe da gabanta tace "Wallahi amminmu wasa nake ban kashe kudin ba nayi hakane kawai sabida mu koyi tafiya a kasa, mukoyi maintaining, Kinga yanzu ni budurwa ce, idan Bana tafiya a kasa Ina miji zai ganni balle nayi aure, ko so kike in wuce lokacin aure kamar yanda yahyah leeya ta wuce?"
Ta fadi maganar cike da yarinta tana ware hannayenta alamar tambaya.
A yarinta irin na Aleena duk wacce ta kammala primary to itace budurwa kuma idan batayi aure a wannan lokacin ba har wata shekara ta zagawo aka kuma yaye wasu ɗaliban to shikenan ƴan waccan shekarar sun tsufa kenan sun wuce lokacin aure.
To ita yanzu take shirin zama budurwar, shiyasa kowa a gidan yake kiranta da sunan.
Idan kuma baka kiranta da sunan budurwa to bakaibane wanda kuke shiri da ita ba.
Dariya suka kwashe gaba dayansu, sai yanzu na kula da Wani dattijo Dayake shigowa gidan daga can kofar gida.
Dattijon ba baki bane, haka Kuma Kai tsaye bazaka kirashi da fariba.
yanada dan tsayi, Haka kuma yanada matsakaicin jiki.
A ƙiyasi zai iya kai shekaru 45 zuwa sama HAMRAZ AWAIS kenan datijjo mai kamala da haiba.
Tun sa'adda Aleena ta fara magana yana jinsu Shima maganartata ce ta bashi dariya.
"Assalamu Alaikum" Abbi ya furta sallama yana ƙarasowa cikin gidan.
Tare suka amsa masa sallama a lokaci ɗaya.
Leeya ce ta fara gaida shi sannan sai Aleena.
"ummu-aleena barka da gida"
"yawwa barka dai Abu-leeya ya shago?"
"shago alhamdulillah mungode Allah".
Dubana na Kaiga wacce aka kira da ummu-aleena matar nan ce dake zaune tana gyara shinkafa tun a farko wato Ammi.
Naganta macece guntuwa mai faffadan jiki,
duk da kasancewarta guntuwa a kallo daya bazaka kirata da guntuwa ba haka zalika ba doguwa bace, gata fara sol zubin fulanin maiduguri wato kanuri Ammi faheema kenan mahaifiyar Leeya da Aleena, mata wajen Abbi Hamraz Awais.
"Ke! budurwa kike ko wa?? ki tashi daga kafar matata karki karya min ita" Abbi ya faɗa yana kallon Aleena dake zaune kan kafar Ammi.
Maƙe kafaɗa tayi Alamar bazata yi ba, sai ta sauya zancen da faɗin "Abbie yau kasaka kudi a asusuna kuwa?"
"batun matata nake, bata asusun kiba"
"Abbie nifa bazan tashi ba sai ka gayamin amsar tambayata"
"to ban sakaba Amma kizo muje yanzu na baki ki saka da kanki".
zabura tayi da gudu ta isa gun Abbie ta miƙa masa hannu alamar yabata, sunkuyo da kansa yayi ya raɗa mata Magana a kunne, sai ta jijjiga Kai alamar ta gamsu da abunda ya faɗa mata sannan tace to "nagane Abbi".
Duk abin nan da suke da Ammi da leeya na kallonsu,
leeya kam ta ƙasa hakura saida tazo inda Abbi ke tsaye da Aleena tace "Abbie wai asusu akeyiwa Aleena ita kadai ba daniba" ta faɗi maganar kamar zatayi kuka.
har Abbie ya buɗe baki Zaiyi Magana Aleena ta karɓe da faɗin
"Ehhh asusu yake min ya ranki daɗi ko bakin ciki, nace daɗi ko bakin ciki? To koma dai menene Abbie asusu yakemin kuma kayan aure za'a siyamin tunda ke kinƙi yin aure Ni bazan zauna ina haɗa kafaɗa dake ba, Muna gwada tsawo a gidan nan da ni dake ba ehee"
Aleena ta faɗa tana rike kunkuru tana juya idanu kamar itace yayar ba ƙanwa ba.
Leeya da taji dalilin da yasa akeyin asusun ta juya tabar wajen, ba tare da tace uffan ba.
𝙇𝙀𝙀𝙔𝘼𝙉𝘼 itace yaya wurin 𝘼𝙇𝙀𝙀𝙉𝘼 ƴaƴan Abbie 𝙃𝘼𝙈𝙍𝘼𝙕 da Ammi 𝙁𝘼𝙃𝙀𝙀𝙈𝘼.
basu kadai bane ƴaƴan su ba amma su kaɗai ne araye,
idan da za'a lissafa, leeyana ita ƴa ta huɗu wajen su kawai dai yaran basa tsayi ne da zarar an haifesu wasusunsu ko sati basa yi suke mutuwa.
A haihuwar su ta biyu ɗane namiji yaron saida yakai wata biyar sannan ya rasu.
haihuwar su ta uku ma ɗane namiji saidai ya fara girma domin yana taka ƙafarsa ko ina shima yazo ya rasu ba ciwon wuni babu na kwana.
Shiyasa koda aka haifi leeyana basu wani ɗaura mata soyayya ba saboda suna tunanin itama zata mutu ne kamar sauran ƴaƴansu.
Saida sukaga kwanaki na tafiya, satuttuka nata tafiya, watanni sunata gudu, shekaru kuma suna shudewa hardai takai anyimata ƙanwa wacce aka sakawa Aleena murna da godiya ga Allah kam bazan iya faɗi ba kawai Ku misalta da kanku.
Kodayake basa saka rai ga ƴaƴan nasu har dai sukazo suna sakin jiki dasu a yanzu.
Hamraz na matuƙa ƙaunar yaransa yayinda ammi FAHEEMA ke kokari wajen ganin ta tarbiyantar da yaranta.
Leeya dabance da Aleena komai na rayuwarsu ya bambanta, kamar tsarin zubin halittarsu da kuma halayensu.
IAleena ta kasance rigimammiya ta ƙin ƙarawa,
Yayin da leeya ta kasance mai sanyi a halayenta,
Aleena batada hakuri ko kadan bata yafiya,
yayinda leeya ta kasance mai hakuri sosai da yafiya, bata shiga harakar mutane balle ta tsokano rigimar su saidai ita a tsokaneta.
ko a hakan kuma Aleena ce take karɓewa ta tare mata faɗar, Leeya ta kasance tanasamun tsokana a wajen mutane da kuma hantara da ƙyara saboda wani banzan dalili na mutanen.
A kaf faɗin unguwar tasu ta ECOCO,
LAGOS NIGERIA ba wani mahaluki daya taɓa ganin fuskar leeya hatta ita kanta leeyana bata taɓa ganin fuskar ta ba ko a mafarki.
Idan ka cire Aleena, Abbie, da kuma Ammi. Tun tana ƴar ƙaramarta ammi ta saba mata saka mayafi ta ɓoye fuskar ta ga kowa shiyasa koda da fara girma sai bata sha wahala ba wajen ɓoye fuskarta ta domin ta riga ta saba.
Sau dayawa in suka fita aka aikesu ko kuma zasuje makaranta, idan har basu sami abin hawa tun a layinsu ba, yanada wahala suje inda zasuje leeya bata haɗu da masu barazanar cire mayafin da take rufe fuskar ta dashiba, tun sa'adda taga mahaifiyarta bataso ana ganin fuskar ta, itama take ƙoƙari wajen ganin ta hana aga fuskar Tata.
Wannan kenan..................✍️
Bayan wuya....
*By*
💫RUMANAH M. DIGGI💫
EPISODE 002.
**********
Sun jima zaune madaidicin filin gidan nasu kafin Ammi ta kammala Abinci.
Bayan mintuna kaɗan aka sauke girkin aka zubawa kowa nashi, saida kuka kammala cin abincin ne Ammi ke tambayar leeya,
"leeya kina ganin okene kuwa, nadaina ganin shi kwana biyu"
okene wani makwabcinsu ne kuma igbo ne saidai shi ba musulmi bane saɓanin su leeya dasuke cikakkun musulmai. Mahaifinsa shahararren mai kuɗi ne na bugowa ga jarida.
Ko kaɗan mahaifan okene basason alaƙarsa da mutanen gidansu leeya, suna gani kamar zasu canza masa ra'ayi, Yace zai fita daga addinin sa ya koma nasu.
shiyasa gaba ɗaya suka hana masa fita koda yaushe yana nan gida baya fita ko'ina.
Jinin okene ya haɗu dana leeya sosai hasali ma duk zuwan da yakeyi gidan nasu saboda itane, idan zasuje islamiyya tare suke zuwa ko taxi zasu shiga dashi ake shiga.
Haka idan suka iso islamiyyar yana nan bazai matsa ko ina ba har sai an tadasu daga makarantar.
Okene yakan zamo mai basu kariya ne musamman ma leeya wacce ko yaushe fuskarta ke lullluɓe cikin mayafi, hatta shi okene bai taɓa ganin fuskar ta ba.
iya karsa ganin fitinannun idanunta masu razana mai kallonsu, suma idanun nata ba kullum yake ganin su ba sai idan ta saka mayafi wanda zai bayyanar da su.
Duk da Yawan mutane suna kiranta da Kowane suna suka samu, saboda Yawan saka mayafin da take,
hakan baya damunta sosai dan tasan ba illa bane, domin kuwa da illa ne da amminta bazata riƙa sakamata mayafin ba.
bawai okene bayason ganin fuskar ta bane shima, idan za'a tambayi wanda keson ganin fuskar ta wata ƙila shine na farko dazai ɗaga murya domin a fara yayemasa fuskar tata ya gani.
"Leeya bakyajin ina tambayar ki, ko kina ganin sa gidan nan ne ya daina zuwa?"
Sai yanzu leeya ta ɗago kanta da ke rufe da mayafi sannan tace
"Ammi wallahi nadaina ganinsa nima, jiya fa har bakin gidansu naje nasamu wurinda baza'ayi saurin ganina ba na fake domin naga ko zai fito amma ban ganshiba".
"To idan kin gama ki duba shi ko lafiya yake kinga ba'a zama haka saboda nasan dakece okene bai gankiba kwana biyu da yanzu ba haka ba" Ammi ta faɗa tana dan murmushi.
Da "tohhh" leeya ta amsamata tana miƙewa tare da nufar inda randar Ruwa take.
"Ammi wai nace ina Aleena ne?" Cewar leeya bayan tasha ruwa.
"Aleena tana bacci tun ɗazu kinsan ai aikin tane bacci kam"
Ƴar dariya leeya tayi kafin tace "Ammi ki matsa dai budurwar taki taji kina faɗin batada aiki sai bacci kigani duk shirin nan da kukeyi da ita zai wargaje saboda kinsan bataso ana kiranta sarkin bacci"
ammi tace:"
"Aikuwa wallahi zamu ɓata da ita nasani, kuma nasan haka kuke so kiji daɗi keda abbinki idan kinga nayi faɗa da budurwa kho, abunda kikeso kenan tho bazamuyi faɗan ba"
"Ehh wallahi ammi gayamata ba mu ba faɗa Nida ammi takalmin kaza mutu karaba baza'a ganmu a rana ba ko aure nayi ammi dake zamuje ga ɗakina ga ɗakin ki"
can a bakin ƙofar tilon ɗakin nasu suka tsinkayo Muryar Aleena na faɗin haka.
Dariya suka kwashe da ita jin abunda budurwa ta faɗa domin basuyi tunanin tana jinsu ba.
Cike da son tsokana leeya tace,
"Ni idan inaso kuyi faɗa nasan abunda zanyi, injiku tsakar gida Nidai ina ɗaki kinji ko ƴar yarinya"
"kam matsifa ammi kinjita ko!? yau ni budurwa Yahyah leeya ke kira yarinya fa ammi, dubeni sama da ƙasa nayi mata kamada yarinya?" Aleena ta faɗa tana karasowa gaban amminsu cike da shagwaɓa
Abin ya bawa ammi dariya sosai matuƙa amma sai ta kanne gudun ɓacin ran budurwa tace "inahhh ko kusa. ai ba wanda zai ganki yace miki yarinya, kuma duk wanda yakiraki yarinya shine yaro bai saniba".
"Babban yaro ma kuwa" ieeya ta kuma faɗa tare da juyawa ta fita gidan aguje.
Tana fita tabi wata babbar hanyar da zata sadata da gidansu okene.
tana tafe tana saƙawa da kuncewa domin tasan halin iyayen sa sarai, basa ragamata ganin tanaso ta sauya musu tilon ɗansu wajen binta da addinin ta.
Tana tsaka da guntun tunanin da take taji an cafko wuyata ta baya, da sauri ta waiwayo domin ganin wanda ya kawo mata hari.
Waiwa yowar da zatayine wani daga cikin yaran su biyu ya fizgi mayafin da ke lullluɓe da fuskarta!
Da mugun sauri ta rike masa hannu tare da gantsara masa cizo a ɗan yatsarsa,
Yaron ya fasa uban ihu yayinda ɗayan ya juya aguje da nufin yaje gidansu abokin nasa ya sanar.
Tana ganin ya saketa ta juya da gudu ta nufi gida tana rushewa da wani irin kuka na bakin ciki da takaici.
A ranta take aiyana cewa idan ta koma gida yau saita tambayi Ammi dalilin da yasa take ɓoyewa mutane fuskarta alhali ba ita kaɗai bace a gidan ga Aleena nan tana sakewa kamar kowa saboda ba'a sakamata mayafin a fuska.
Tana fita lafiya ƙalau ta kuma dawo ƙalau.
saɓanin ita da take fita tana haɗuwa da irin waɗan nan abubuwan ta zama kamar ɓera a tsakanin yunwatattun mage, ba yaune lokaci na farko da aka taɓa yimata hakaba.
Idan ma da sabo ta saba kawai dai jurewane bazata iya yiba.
Domin kuwa sauda yawa sai ankai Ruwa rana kafin ta iya ƙwatar kanta a hannun mutanen da ke barazanar ganin fuskar ta, a hakan Ba yara kaɗai suke yi mata haka ba, hatta manyan ma da kansu suna yimata haka, wani zubin kawai dai Allah ne yake ƙwatarta hannunsu ba tare da sun idda nufinsu ba.
da gudu ta shigo gidan batare da ta kalli kowa ba ta zarce ɗakinsu ɗaya tal tare da banko ƙofar ɗakin ta rufe tana rizgar kuka.
A tsakar gidan kuma Ammi ce da budurwa ke zaune suna ɗan taɓa fira kamar yanda suka saba.