Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
dashi da gudu na nufi cikin masallacin unguwar tamu ban tsaya ba har sai da nakai gab da mutanen zasuyi sallahr azahar, ban zarce a ko'ina ba, kuma babu wanda yayi yunkurin tsayardani har sai da na isa gaban limamin yana shirin kaffara sallah a dan tsorace ya juyo gareni yace;
"Malama lafiya, meyake faruwa dake?"
Cikin Muryar kuka da damuwa nace "malam dan Allah ka taimakamin mahaifina ne ya rasu, 'yan unguwar nan suna zargin mu da maita wai dan ana yawan mace-mace a cikin danginmu, shine yau Allah yayiwa mahaifina rasuwa kuma nika dai ce a tare dashi, diyansa biyu maza an nemi d'aya an rasa yau kwanaki hud'u kenan, dayan kuma yayi tafiya zuwa barno ina ta kiran number ɗin sa bata tafiya. Gashi mahaifinmu ya rasu ban san yanda zanyi da gawarsa ba, duk Inda naje korata akeyi shine na yanke shawarar na shigo nan na sanar muku da abunda ke faruwa. Dan Allah ku taimaka min wallahi bamu da alaka da maita"
Cikin matukar tausayin da ya bayyana har fuska limamin yace;
"Allah sarki karki damu kinji in sha Allah mu zamuje muyi masa sallah mu tsaftace shi mu suturceshi mu kaishi makwancinsa na gaskiya, kiyi hakuri Allah ya jikansa ya yi masa rahma. Allah ya bashi masauki mai girma"
"Ameen malam Nagode sosai Allah ya biyaka, Allah ya jikanka yanda ka jikanmu malam"
"Ameen ya rabbi" suka fada har sauran mamun da zasu bi limamin sallah.
"Kije wancan dutsen ki zauna ki jiramu kafin mu idar da sallah sai muje gidan ki nuna mana" limamin ya kuma fada yana nuna mata wani dutse dake gefen masallacin daga waje.
Fita daga cikin masallacin tayi sannan taje wurin dutsen ta jirasu har suka kammala sallah.
Yanda limamin ya fad'a haka ta kasance wato su sukayiwa hilwah wanka, suka yimasa sallah Sannan suka binneshi a makwancinsa na gaskiya.
Nasha kuka sosai lokacin da za'a fita da shi gidan, na zama ni kadai ke nan innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me muka aikatawa fairozha da zafi haka, shikenan na rasa kowa.
Idan har da gaske ne abunda fairozha ta gayawa hilwah gabanin mutuwar sa, duk kisan da akeyi itace, hakan yana nuna kenan har iyayena ita ta kashe su.
Wunin ranar ba wani aiki da nayi da ya wuce kuka, sai idan lokacin sallah yayi ne nake tashi nayi, kuma daga zarar nayi sallahr nake ci gaba da kukana.
Na dauki tsawon kwanaki uku a haka, kuma kullum ta Allah sai na kira wayar maharaz amma bana samu, yau ma haka ne ina zaune tsakar gida ni kadai abun duniya duk ya isheni na rasa inda zan saka kaina.
Wayata naji tayi qara, ganin baƙuwar number ya sakani d'an shakku, kuma ban d'aga wayar ba har sai da akayi kira kusan biyar.
Ganin karar wayar na so ya fara takuramin sai ya saka na dauki waya na kara a kunnena.
"Kece dayammah" naji an fada da wata baƙuwar murya da bazan iya shaidawa ba.
"Ninni........Ni....ni ce" na fada muryata na rawa.
"Yawwa masha Allah, sunana inspector Bukar Elyass, dayammah ki kwantar da hankalinki ki saurareni. Wata mota da ta taso daga garin barno ta samu accident yau da safe, amma ba wanda ya rasa ransa a lokacin da aka samu accident din, sai bayan anje asibiti ne dayan da yafi kowa rauni a cikinsu Allah ya karbe shi, kuma shine muka dauki wayarsa muka fara binciken contact dinsa, a yanda muka ga yayi miki saving ya tabbatar mana da ke matarsa ce, kiyi hakuri dan Allah mijinki ya rasu Allah ya karbi abunsa sai hakuri" 'kitttt mutumin ya kashe wayar.
Dayammah ta sake kallon mutanen da ke zaune a parlourn idanunta sharkafff da hawaye tace "Wallahi Hajiya bazan iya kwatanta muku irin kunci, da bakin ciki da tashin hankalin da na shiga ba a wannan lokacin" dayammah ta kare Magana wasu zafafan hawaye na gangaro mata.
Sai a wannan lokacin id yayi magana shima idanunsa sun kad'a sunyi jajir jin irin yanda rayuwar ahalinsa ke tauye.
"Annah kenan maganar fairozha da ta gayawa marigayi hilwah zata kashe Affana gskiya ce? Shine ta kasheshi ta hanyar saka su had'arin mota kuma taji masa rauni da yawa, sannan ta kasheshi ki kaɗai. 'yar uwarsa ce fa, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya labarin dan uwan affana maharaz, sannan kuma ya akayi kika baro garin calaba bata hanaki ba?"
"Wallahi nima duk wadannan tambayoyi ne ke min yawo a kwakwalwa" hajiya fanaya ta fada cikin tausayawa.
Murmushin da yafi kuka ciwo tayi sannan tace "bayan sati biyu na maida komai kamar ba komai ba, naci gaba da nemawa iyayena da mijina da kuma sauran mutanen da suka riga mu gidan gaskiya gafara, ba wanda nake ra'ba kuma babu mai ra'ba ta.
Haka naci gaba da zaman kadaici, wani abu kawai nake tunawa naji sanyi shine cikin maharaz dake jikina, a duk lokacin da na kalli cikin sai naji tsakanin farin ciki naji kamar maharaz nake kallo, naji kamar na fito da abunda ke cikina na ganshi.
Cikina na cika wata tara da kwana biyu na haifi d'ana namiji, cikin taimakon Allah nayi nakuda na gama, akwai dukiya sosai a gidan, kuma akwai dabbobi, a ciki na zabi biyu naje na kai masallaci aka yanka akayiwa yaro suna.
Nayi matukar farin ciki sai dai yaron baya kamada mahaifinsa ko kaɗan, a komai na fuskarsa ni ya biyo hakama yanayin tsarin jikinsa.
Ina rainon d'ana hankali kwance cikin tarbiyyar da naga mahaifinsa na da burin bashi idan yazo duniya, sai kuma Allah bai qaddara zaizo yana raye ba.
Wata Rana da dare Misalin karfe takwas na dare, idrak na zaune tsakiyar parlour ba yanda banyi ba akan yayi bacci amma yaki, a lokacin kuma ya fara girma domin yanada shekaru biyu da watanni.
Kwatsam naji an bude kofar dakin anshigo, a razane na tashi ganin fairozha fuskarta a hade babu alamar rahama a cikinta.
Hannu na d'ora a ka ina kokarin rokonta akan kar ta cutarda mu da d'ana.
Kunsan me tace?"
Dayammah ta tambayi su mum dake zaune jugum-jugum suna saurarenta.......................✍🏻
44.
_____________Bata jira cewar su ba taci gaba da fadin; "Sosai nake kuka kamar hawayena zasu qare saboda ina tunanin shikenan ranar rabuwata da yarona tazo, idan ta rabani dashi ina zan saka kaina, nasan ba raina take da buqata ba, domin dah rai na ne da tuni tayi yanda takeso dani.
Wata gigitacciyar tsawa ta dakamin har sai da hanjin cikina suka motsa, shikuma idrak ya kwallah kara yana shirin fadowa daga kan gado da yake zaune.
Kafin nayi wani yunkuri tuni fairozha ta chafe kafafunsa tayi sama dasu ta mayarda kansa ƙasa, wani kuka na sake ina neman karasawa gabanta na ceci rayuwar yarona, domin yanda nake ji a lokacin zan iya bayar da kaina fansa akansa.
"Bazan cutarda yaronki ba, haka zalika kema bazan cutar da ke ba,,,,,,,Face kin kasa cika sharadin da zan gindaya miki. dayammah! Kinada sanin nasan kinsan da duk asirina dana jima ina 'boyewa kho, kuma nasan kin san komai, a yanzu duk burinki bai wuce ki tona min asiri ba kho, to bara kiji wallahi wannan shine mafi girman kuskure da zakiyi a rayuwarki idan kikace tona min asiri zakiyi.
Zan ida fadamiki wani abu da baki sani ba, a wannan ƙungiya tamu muna da sirruka sosai wanda ba kowa ya sani ba, kuma ba'a fadin koda kalma daya tak ga wani mai rai da motsi da lafiya ba tare da wa'adinsa ya cika ba.
Hilwah da kikaga nazo na sanarmasa, nasan lokacin sa ya riga yayi saboda nayi sacrifice din sa wa kungiya.
Ke kadai kika san wannan, bayyanuwar wani al'amari ko kuma sanarda wannan labarin ga wasu to daidai yake lalacewar kungiya, idan kuma kungiya ta lalace ta dalilina to hukunci zai hau kaina, nikuma idan har hukunci ya hau kaina na rantse miki da Allah bazan barku a rayeba keda wannan d'a naki.
Sannan abu na gaba dayammah ki saurareni, inaso ki tattara komanki kiyi nisa da garin nan, har abada bana bukatar sake ganinki a gidan nan daga ke har yaronki.
Kuma karkiyi tunanin kamar na fita rayuwarki, ah ah....... Ina nan ciki, kuma ina bibiyar duk wani motsi naki, kamar yanda na 'batar da hamraz sannan na kashe maharaz to kema haka.
da wannan d'an naki kasheku yafimin sauqi bisa ga ko wane aiki da zanyi, saboda haka ki kama kanki. Wallahi kwana daya jal na baki idan na dawo na sameki sai dai wata bake ba"
Tana gama faɗin haka ta juya, kamar walqiya na nemeta na rasa, tun daga wannan lokacin na tattara komai nawa na baro garin calaba, sannan tun daga lokacin Sai dai naga fairozha a mafarki tana qara min gargadi akan kada na Bayyana labarin su ga kowa kamar dai yanda nayi wannan.
Tho kunji, wannan shine takaitaccen Labarin da na sani game da iyayenku" dayammah ta fad'a a sanyaye.
Kamar daga sama sukaji muryar dad ƙarami yana cewa"haqiqa akwai qamshin gskiya a labarin nan na dayammah, domin kuwa mahaifin mu yazo mana da wani baqo, kuma har ya shaida mana cewa d'an amininsa ne dake zaune garin calaba, sannan ya gayamana dashi da dukiyarsa amana ce a wurinsa, bayan haka kuma yace mana koda bayan ransa mu nemi waɗan nan mutane mu Mallaka masu dukiyarsa, Wallahil Azeem da kunsan yanda muke neman bayin Allahn nan da sai mamaki ya rufeku gaba ɗaya, ashe bamu sani ba muna tare da su har a cikin gida"
"Yaushe ka shigo dad?" Khulud ta faɗa cikin sigar tambaya.
'Dan murmushi irin na Dattaku yayi sannan yace"tun lokacin da ta fara bada labari ina tsaye jikin kofa ina saurarenta, haqiqa anci amanarku, kuma an zalunceku, amma Allah baya barin azzalumi da haqqi, Wallahi indai fairozha ce bazata gama da duniya lafiya ba, ta dalilin dukiyar maharaz da dan uwansa hamraz da mahaifina ya karba amana shine dalilin da ya saka fairozha ta kashe shi har lahira".
"Yanzu kina nufin kice ku dangin mu ne? Dan Allah ki amsamin kice wancan saurayin da nake gani ahalinmu ne jinin mu daya" leeyana ta fada tana fashewa da kuka.
Itama Dayammah kuka take Aleena ma haka, idrak ne kadai mai taurin zuciya, amma hatta su mum dake zaune da dad ƙarami sai da sukayi hawaye.
Da sauri Leeya ta miqe ta nufo Dayammah ta rungume ta tana kuka, itama Aleena ta rungume su gaba daya tana kukan.
"Leeyana, indai har da gaske kike da kika bamu labarin kinyiwa mahaifiyar ki alqawarin bazaki bude fuskar ki ba har sai ranar da aka daura miki aure, to ki bude fuskar ki yanzu, domin yau andauramiki aure da yardar Ubangiji"
Chak kowa ya tsaya da abunda yake kafin duk suka waiwayo suka kai dubansu ga papu dake shigowa dakin rike da wani farin bowl sabo cike damtsam da dabino da kuma alawa, har gabansu yazo ya ajiye tare da basu umurnin kowa yaci goron daurin aure ne.
Ba wanda yayi wani kwakkwaran motsi a cikinsu, baramma leeya dake tsaye kamar gunki sai zanje take da zuciyar ta.
Tana ji cewa bazata iya cire mayafin ta ba domin ta riga ta saba dashi tsawon shekaru. Tanaji a ranta koda ta cire to bazata iya zama babu shi a fuskar ta ba kwata kwata.
Maganar da ta jiyo Papu nayi ne ta qara dawo da ita hankalinta.
"Amma idan kinji baza ki iya cirewa ba shikenan kiyi zamanki da abunki, wannan ba matsala bane"
Kafin wani yayi magana a cikinsu papu ya kuma kallon gahees cikin tsananin bacin rai yace"gahees kunsan kuskuren da kuka aikata kuwa, kunsan abunda kukayi tauye haqqine? Wallahi kunso kanku da yawa, akan d'a d'aya jal, zuciyoyin mutane nawa za'a 'bata a gyara ta mutum d'aya kawai......"
"Wallahi da kasan Dalilin mu na yin haka da bakayi wannan furuci ba justice Khattab, amma kayi haƙuri idan komai ya dai-dai ta zanyimaka bayani, abi komai a sannu justice please" dad ƙarami ya katse papu da fadin haka.
"Ba wani bayani da zan saurara daga bakinku, amma kusani komai zai zo karshe bazan lamunci wannan ba"
"Justice kanada masaniyar wannan matar dake tsaye....."
"Wacece?, meye had'ina da ita, banada wata alaqa da ita a yanzu, a baya alaqarmu ta aikace-aikacen gida ne kawai da take taya hajiya fanaya sunayi, daga baya kuma tazo ta nuna ta gaji da aikin har ta fara dukan 'yata har cikin bedroom ɗin ta, wannan ne ya saka na koreta domin bazan yarda da hakan ba gskiya" cewar Papu cikin matukar bacin rai.
Mum ce ta kalli dad ƙarami cikin nutsuwa ta tambaye shi "baban twins, Dan Allah me akayiwa justice da zafi haka, wallahi na jima rabon da naga ya shiga yanayi irin wannan"
"Hajiya kiyi hakuri, wallahi wannan maganar ba yanzu Yakamata ayita ba domin ba qaramar magana bace sanin abunda ya faru, amma kiyi hakuri idan mun gama wannan case na Dayammah sai na yimiki bayani"
"Wane case ne ke tsakanin ku da ita Dayammah?" Cewar Papu a kufule.
Jin tambayar nan ya saka dad qarami kallon Papu cikin nutsuwa da son tattaro magana mai ma'ana yace "Justice Khattab waasib, ka mayarda hankalin ka sosai ka saurareni. wancan matashin saurayin da ke zaune d'ane wurin maharaz, waccan yarinyar da kuka riqa tsawon shekaru wato Leeyana ita da qanwarta Aleena 'yar wajena, 'ya'yane wurin hamraz, wannan kuma da kake gani Dayammah mata ce a wurin maharaz mutanen calaba, 'ya'ya wurin aminin abbanmu mai rasuwa"
"Whattt??!" Papu ya fada fuskar sa dauke da madaukakin mamaki, 'yan amana?"
ya kuma fad'a kamar zai yi kuka, Allah sarki ashe muna da rabon haduwa da ahalinku, Wallahi munsha wahala sosai, a kullum addu'ar da nake bata wuce allah ya bayyana muna ku ba a duk inda kuke........"
"Justice me kake nufi Ni fa bangane ba, kana nufin abunda ta fada na batun dukiya gaskiya ne?" Mum ta fad'a da kokonto a ranta.
""Hajiya, haqiqa wannan labarin da ta baki gaskiya ne, domin kuwa dukiyar su na hannun mu.......! ki sani duk kamfanonin da kika san ina ziyarta kasashen waje to ba nawa bane, na leeyana, ne da kuma qanwarta Aleena, da idrak gashi nan zaune.
Sannan kuma kamfanonin jiragen sama gudu shida dake Abuja suma ba nawa bane, sai kuma kasar Kuwait da jordan suma kamfanonin masarufin da ke kasar ba nawa bane nasu ne" papu ya karashe maganar da tabbacin abunda yake cewa.
A rud'e khulud ta miqe sakamakon jin abunda mahaifinta ke fad'a"papu are you serious?"
"Yes Khulud my daughter, kina mamakine kho? Ko kuma kin fara jin kunyar leeya ne irin cin zarafin da kika yimata akan bata da dukiya ita yar talakawa ce, to ki sani leeyanah ba yar talakawa bace, domin dukiyar da suka mallaka a yanzu ta kasa tamu uku, kinga yanzu mune qasa, su kuma suna sama"
Wani kuka ne ya kwacewa Khulud, tana tuna yanda ta dinga wulaqanta leeya, da kuma irin baqaqen maganganu da take mata. ta bangare d'aya kuwa ta qasa had'a idanu da idrak shima yanda ta dinga masa prouding a skul.
Ji tayi an rungumota ta bayanta, jiki a sanyaye ta waiwayo. Sake fashewa tayi da kuka lokacin da taga leeyana ce, itama leeyanar kuka takeyi.
Sake neman gafarar juna sukayi a karo na biyu, inda leeyana ta sake jaddada mata cewa bata taɓa riqeta a rai ba, kuma tun a wancan lokacin ta yafe mata domin kuwa da gaske ta changer halayenta.
Karasowa tayi har gaban idrak ta durkusa cikin matsanancin kuka tace "dan Allah karka gujeni idrak, Wallahi idan baka soni ba mutuwa zanyi. Zuciya ta bata da kwari da dauriyar da zata iya hakurin rashin ka, dan Allah karka barni idrak Wallahi inasonka, karka gujeni saboda kaji kunfimu dukiya"
Ba zato ba tsammani, taji yace "ban ta'ba son wata yarinya ba a rayuwata sai ke, tun ranar da kuka zo inda nake kasuwanci na fahimci halayenki sun sauya, kuma na fahimci kina sona domin kuwa na tabbatar wa kaina ke kika dakatar da Amrah da raudha wajen saka iyayensu su koreni a Rooney. Bazan gujeki ba Khulud k. Waasib, kisani idrak Manaf maharaz nakine ke kadai in Sha Allah" idrak yayi maganar murmushi kwance a fuskar sa.
Miƙewa tayi tana murmushin itama while hawaye na zubowa daga idanunta, "ina sonka sosai id, Allah ya mallaka min......"
"Uhmm, uhmm" badar tayi gyaran murya tun kafin Khulud ta karasa fadin abunda takeda niyyar fad'a.
Ba id ba har ita khulud din sai da taji kunya, shafff ta manta a inda suke.
Sake komawa tayi inda leeya ke zaune ta zabga tagumi Allah kad'ai yasan abunda take tunanowa. Dai dai lokacin da Aleena ta karaso inda leeyana ke zaune.
Janye hannayen leeyana tayi daga tagumin da take tace "Yahya leeya tagumi bai dace dake ba a dai-dai wannan lokacin, ina fata zabin da akayi mana su zama alqairi a garemu, kisani mun fita daga sahun da kika sanmu a baya mun shigo wani sahun da sai mai qarfin hakuri zaici ribar zama a ciki. Kisani gata wadan nan mutane suka yimana,,,,, gata kuma wacce ba kowane mutum ne zai iya yimana ita ba, ba su sanmu ba, ba kuma su san ina muka fito ba, sun yarda da imaninsu ne kawai suka taimakemu, sun zauna damu tsakanin su da Allah, sun saka mu makaranta, sun ciyar damu, sun shayarda mu, sun tufatar damu, muka girma suka nemo 'ya'yayensu suka had'amu aure dasu.
Menene abunda ya rage suyi mana Yahya leeya? Bamuda kamar mutanen nan a duniya sai kuma matar yayan Abbinmu.
Yahya wallahi na rasa kalmomin da zanyi amfani dasu wajen godewa waɗan nan bayin Allah, dan Allah ki tashi muje gaban su, ki tashi muje mu nuna godiyar mu a bisa wannan dinbin alkairi da suka yi mana" Aleena ta fada kwallah na kwararomata.
Kamar wacce kwai ya fashewa a ciki haka leeya ta mike ta fara takowa gaban su mum, Papu, dad ƙarami, mummy-neesah, Khulud, badariyyah, meenal, Aneesa, twins, Dayammah da kuma Idrak duk suna zaune a parlourn.
Kowa ya kasa idanu yana kallon leeya ba wanda yace uffan.
Aleena kuma ganin kowa ya kife leeyana da idanu yasa ta waiwayota.
Daidai lokacin da leeyana ta karasa cire mayafin da ke fuskarta gaba ɗaya.
Wata irin bugawa zuciyar Aleena tayi lokacin da idanunta suka sauka cikin asalin fuskar leeyana.
Su mummy-neesah da su papu kuwa suka ja da baya sosai,. khulud da su meenal kuma har sun kusa fita parloun da gudun su saboda tsanin tsorata da sukayi.
Fahad, turab da zafaran kuma da shigowar su kenan suka rasa me zasuyi.
Ba makawa yau tasu ta qare, dama shi wallahi yana zaton leeyanar nan ba mutum