BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   10 / 61

27K to 30K   out of 180.4K words

doma road tana tsintar kayan bola dana dawo daga daga school ɗin su khulud, wallahi justice dana ganta na tausayamata sosai, kuma yanda ka ganta da mayafin nan yanzu haka na ganta ko jiya ma, na jima ina kallon ta, har sai da khulud taji haushin haka, kuma haka kawai naji yarinyar nan ta shiga raina, naji tausayinta sosai"

Jin an ambaci mayafine yasa papu ya ƙara kallon fuskar LEEYA,

"Ikon Allah" papu ya furta yana jinjina kai.

"Lafiya dai"

"Lafiya lau, amma wallahi karkiyi mamaki idan nace miki nima na taɓa ganin yarinyar nan a haka"

"Ka taɓa ganin ta kaima justice? ikon Allah, a ina?"


"Wallahi a bakin hanya na ganta kwance batada lapiya sati ɗaya daya wuce, na ganta kwance tanata rawar ɗari. Nima saida nayi parking motata na tsaya ina kallon ta domin wallahi Allah Nima taban tausayi"

Duk hankalin ya ɗagu sai mamakin yanda wannan al'amari ya faru suke, kawai sukaji tayi ajiyar zuciya, a hankali ta furta"wallahi ni ba ɓarauniya bace"

Kallon su suka mayar kanta gaba ɗayansu cikin mamakin yanda akayi ta farka, mai gaɗin ne tsaye a kanta da robar ruwa a hannunsa, kana ganin shi kasan tsorace yake.


"Allah ya ceceka ba mutuwa tayi ba wallahi daka yabawa aya zaƙinta domin ni ba ruwana wallahi"

"Alhaji kenan dama na gaya maka ai ba mutuwa tayi ba"

"Kai dai ka kiyaye idan ko ba haka ba kanason aiki gidan nan zaka barshi" faɗin mum dake janye da hannun leeya tana takawa da ita a hankali domin jikin ta duk yayi tsami.

Juyawa papu yayi ya rufawa mum baya suka shige gidan, suka bar mai gadin kaɗai.


Master parlour ɗin gidan suka isa da ita, suna isa kuwa papu ya wuce ciki yabar mum kaɗai da leeya.


"Sannu, ya jikin?"


"Jiki lafiya ƙalau ba abunda yasameni, nidai wallahi bani na ɗauki generator ba. Yau na fara zuwa nan wallahi bani bace dan Allah ki taimakeni sai kema Allah ya taimakeki"


"Uhhhhm kwantar da hankalinki kinji, ba komai bane mun san ba ke kika ɗauka ba shima mai gadin yayi kuskure ne kuma ya gane kuskure yayi,
kiyi hakuri kinji, yanzu kizo ki zauna na kawo miki abinci kici sannan kisha magani domin wannan dukan zai iya saukar miki da zazzaɓi"


"Nagode sosai, Allah ya saka da alƙairi, na gode kwarai da gaske".

Ƙarar buɗe ƙofar da akayi ne yasa mum ta mayarda hankalin ta kan ƙofar domin ganin wanda ke shigowa

"Awwwwn my kid you're welcome"


Cewar mum fuskar ta ɗauke da murmushi, tanayiwa khulud barka da zuwa.

khulud kuma tana shigowa master parlour ɗin jikin ta sanye da uniform ta dawo daga school kenan.


"My sweet mum, wacece wannan? Khulud ta tambaya tana watsawa leeya wani wulaƙantaccen kallo.


"Baƙuwa ce"


"Baƙuwa!?, wurin wa tazo a gidan nan ? Kodai ba gidan nan ba mistake tayi kho naga ba talakawa a gidan nan da wannan yarinyar zatazo nema"

Mum na shirin magana saiga papu ya fito,

"my princess u're welcome, ya school"

"School ba daɗi pa"

"Haba dae mamana school ɗince ba daɗi"

"Ehh wallahi pa, babu daɗi za'a ce ai, karatu kam ae ba daɗi ne dashi ba"

"Humm, mamana kenan karki damu zakiji daɗinsa nan gaba kinji"

Taɓe baki kawai tayi ba tare da tace komai ba.

Kallonsa ya mayar ga leeya wacce ta soke kanta ƙasa, bata san me akeyi ba muryoyinsu kawai takeji, jin kowa yayi shiru ne yasa ta ɗago kanta, ganin papu na kallonta sai kunya ta kamata saboda tasan koba komai yakamata idan taga kamar sa a waje ta gaida shi, balle gata har a gidan shi bata gaidashi ba.


"Barka da rana, an wuni lafiya"

leeya ta faɗa tana durkusawa ƙasa daga zaunen da take.

Ɗan murmushi papu yayi kana ya amsa mata

"lafiya lau, ya kike jin jikin naki, dafatar bai jimiki ciwo ba kho?"


"Ehh ba inda ya jimin ciwo gskiya"

"Tau tashi ki zauna mana durkushen ya isa haka"
Miƙewa tayi ta zauna sannan ta mayarda kanta ƙasa yanda tayi a ɗazu.


"Gashi ko sunan ki bamu sani ba"

mum ta faɗa tana kallon leeya.

"Sunana LEEYANA"

"Masha Allah, nice name LEEYANA, a garin nan kike?"


"Ah ah ba garin nan nake ba, Ni bansan ma wane gari ba ne wannan"

Zaro ido mum da papu sukayi, itako khulud ba abunda take sai aunawa leeya harara duk maganar da zatayi.

"Kamar ya bangane ba, harsu iyayen naki basusan wane gari ba ne wannan?" Mum ta tambaya.

"Ae ni banada kowa"

"Bakyada kowa kuma kina nufin ke marainiya ce?"

"Ehh ni marainiya ce banada kowa"

leeya ta faɗa Muryar ta na cracking.

"Allah Sarki, yi hakuri kinji. Dan Allah zan iya jin kaɗan daga labarin ki?. Cewar mum tana gyara zaman ta.

"Me zai hana" leeya ta faɗa ataƙayce, gyara zaman ta tayi itama kafin da kwashe labarin ta kafff dagayawa mum.

Amma iya labarin Nnene da uchie da kuma Aleena ta gayamasu, kuma bata sanardasu ba su bane iyayenta.


"Allah Sarki gaskiya leeya na tausayamiki matuƙa"


"Uhum hajiya fanaya wallahi bake kaɗai ba nima na tausayawa wannan labarin nata musamman ma yanda mutane ke gudunta babu dalili"


"Ahhh justice ya zakace babu dalili bayan ga dalilin nan a fuskar ta, wannan mayafin da take sakawa"


"Ehh hakane kam, amma meyasa kike ɓoye fuskar ki leeyana?"

Papu ya tambaya yana kafeta da ido.


"Wallahi Alhaji nima bansaniba koda na girma nayi wayo naganni da mayafin nan, kuma a duk lokacin da na tambaya ran mahaifiyarmu yana ɓaci shiyasa nadaina tambaya, wallahi koni kaina bansan yanda fuskata take ba saboda har kallon madubi banayi ta hanani. Tace na ɗaukar mata alƙawarin bazan taɓa buɗe fuska ta ba sai ranar da aka ɗauramin aure, ko kuma idan na tabbatar da aurena da wanda zai aureni ba mahani sai Allah to na buɗe, Ni kuma na ɗaukar mata alƙawarin haka".


Cikin mamaki mabayyani mum ta kalli papu da yayi tambayar, shima ya zuba mata ido kawai tsawon mintuna ba wanda yace kanzil cikin su, sai mum ce tayi magana

"yanzu shikenan aleena ta mutu"

"Ehh" ta faɗa tana sakin wani siririn kuka ta chusa kanta tsakanin cinyoyinta.

"Ayyah, yi hakuri kinji ki daina kuka addu'a kawai take buƙata ba kuka ba Dan Allah ki daina kuka kinji".

"A ina dangin ku suke"cewar papu.

"Wallahi nima bansaniba amma mahaifiyarmu na gayamin mumada dangi muma amma bantaɓa ganinsu ba"

"Idan na fahimta kema bakisan dangin naki bakho?.

Ɗaga masa kai tayi alamar ehhh,
Daga nan papu bai ƙara faɗar komai ba yaje kan sofa ya zauna.

"Zaki iya zama damu a nan tunda bakida kowa?"

A rikice khulud ta kalli papu kafin ta maida kallon ta ga mum da tayi maganar

"WHAT!!!?, mum, you agreed to let her in to this house, papu kaima yarda zakayi ta zauna? Stranger, can't see her dirty mum? Bakya ganin yanda take ne hala? kuma zakice ta zauna damu a nan gidan"

Karo na farko da leeya ta ɗago kanta ta kalli khulud, sannan ta sake mayarda kanta ƙasa.

"Maman khulud zamu iya hawa sama inaso nayi magana dake"

"Me zai hana justice muje saman"

Mum da papu suka miƙe suka bar wajen, wurin yarage daga leeya sai khulud kawai.

Miƙewa leeya tayi daga wurin da take zaune ta nufi inda khulud take,

"sunana LEEYANA HAMRAZ AWAIS and you are...." Leeya ta faɗa tana miƙawa khulud hannu.

Miƙewa khulud tayi itama tare da saukar da back bag ɗin da ke rataye a bayan ta, a tsawace ta fara magana

"NO one case what your name is, and now listing up, let's me told you, who ever you are and what ever plan is, it will never ever work, and won't allow peasant like you in this house. it's the profound innovation of senselessness for you to think, I khulud Khattab waasib na saka mutane da dama sun bar gidan nan kuma waɗanda suka fiki komai balle ke ƙaramar alhaki"


"Haba, it's young for you to do that my sister..."

"I'm not your sister mtswww, taja tsaƙi ta tare da ɗaukar lunch bag da kuma back bag ɗinta ta wuce fuuuu tabar leeya ita kaɗai a wajen kamar an dasata...✍🏼









BAYAN WUYA...










By RUMANA M DIGGI


EP.10











.................Bangaren mum da papu kuma suna isowa upstair papu ya dakatarda mum da faɗin "hajiya fanaya kinyi tunanin abunda kika aikata kuwa, zamu iya yarda da ita a wuni ɗayan nan, kinga Ni ba abunda nakasa yarda dashi tattare da ita yanda take ɓoye fuskar ta.

"Wallahi kuwa justice amma ya zamuyi muyi haƙuri kawai mu riƙeta mugani mai hali ba zai ɓoyuba, kuma Allah yaga niyyar mu ta alƙairi koda tayi niyyar cutar damu Allah zai dubi nufin mu ya kuma kare mu daga sharrinta idan ma ta kasance tanada shi, saboda haka mubarwa Allah komai kawai mu riƙeta da zuciya daya".



"Toh shikenan Allah ya karemu da koma menene, idan kuma alƙairi ce Allah ya haɗamu dashi, amma kuma wata matsala ɗaya yanzu khulud"


"Khulud kuma justice me khulud ɗin tayi?"

"Hmmm hajiya fanaya kenan kardai kice min baki kula da duk abun da khulud keyi ba da wani kallon da take yiwa baiwar Allah nan, na santa sarai zata iya cewa bazamu zauna da ita ba"


"Haba justice to kana nufin me kenan?, idan khulud tace bazata zauna da ita ba shikenan yana nufin bazamu zauna da ita ba"


"To hajiya ta ya zamuyi kin san matsalar fa, yanzu idan na kasa yimata abunda takeso ranta zai iya ɓaci, idan kuma ranta ya ɓaci ciwon ta tashi zai yi. Wallahi kinsan bana son haka ta faru shiyasa nake duk wasu abubuwa dan kiyaye haka, Nima kaina nasan bana kyautawa wani ɓangare amma uzuri kan kauda uzuri"


"Duk da haka a wannan karon baza'a biye mata yanda takeso ba, shikenan saboda tanada ciwon zuciya ta riƙa yin komai yanda takeso gaskiya a wannan karon kam bazatayi haka ba domin yarinyar nan bazata bar gidan nan ba"

"To Allah ya yayi mana alƙairi"

"Amin ya rabbbi"
mum ta faɗa.

Shigewa papu yayi ɗakinsa ita Kuma mum ta sauƙa ƙasa

"leeya lapiya na ganki tsaye alhali kuma zaune na barki"

Da sauri leeya ta durkusa ƙasa

"lafiya lau hajiya bakomai kawai nagaji da zamane na ɗan tashi tsaye"


Ɗan murmushi irin na manya mum tayi ko ba'a gayamata ba tasan akwai abunda khulud tayi mata saboda daga ita sai khulud suka bari a parloun

"amma kuma naji muryarki kamar mai shirin yin kuka"


Murmushin yaƙe mai sauti leeya tayi sannan tace

"wallahi hajiya ba komai"

"Okay tau yayi amma daga yau kidaina kirana da hajiya kinji"

"To mezan dinga kiran ki?"

"Ya kikaji waccan yariyar takirani?"

"Mum"

"Haka zaki riƙa kirani daga yau Ni mum ɗinki ce kinji, justice kuma papun ki, khulud kuma sistern kice, sai kuma babban yayanku dake can Mexico yana karatu, nan ba da jimawa ba zai dawo"

"Okay mum in sha Allah zanyi yanda kikace, Bama yanda kikace ɗin kaɗai ba zan ɗaukeku ƙwatankwacin yanda kuka ɗaukeni domin har fiye da yanda kuka ɗaukeni in sha Allah"

leeya ta faɗa cikin Siririyar muryarta mai cike da nutsuwa.

"Tau yanzu kina jin yunwa sosai?"

Girgiza mata kai tayi alamar bata jin yunwar sosai,

"to idan bakyaji kizo muje sama na nuna miki part ɗinku inda zaki zauna, sai kiyi wanka kiyi sallah daidai an ƙare abincin rana sai ki fito daining area idan kikayi lunch sai ki koma ki huta kinji"


Har ƙasa leeya takai tana yiwa mum godiya, ɗagota mum tayi daga kasan kana ta jata suka nufi inda zata zauna, a part ɗin khulud ne saidai ko a cikin part ɗin akwai ɓangarori daban-daban kowa kuma da ɓangaren sa.

Anan mum ta shiga da ita wani ƙasaitaccen ɗaki wanda komansa iri ɗayane dana khulud, sosai leeya tasha kallo a wannan ɗakin har tana gani kamar mafarki take ba ita bace yau zata kwana a ɗakin nan ba, kuma ita kaɗai

"mum nanne ɗakin?"

"Ehh ko bai yimiki ba a changer miki wani?"


Da sauri tace

"ah ah wallahi ba haka nake nufi ba, kawai dai ina mamaki ne wai nida ba kowa ba, ba kuma kowan kowa ba nice zan kwana a ɗakin nan nikaɗai gaskiya mum bansan da wane baki zan iya gode miki ba Nagode, Nagode sosai Allah ya biyaku".


"Ameeen, yanzu kizo na nuna miki ban ɗaki kije kiyi wanka ki fito, kici abinci kinji"

"Tau muje mum"

Mum gaba, leeya kuma tana baya har suka iso kofar ban ɗakin mum ta nuna mata ita kuma ta shige ciki, ta ɗauki lokaci sosai a ban ɗakin tun mum na jira ta fito har ta gaji da jira ta sarkafa mata towel ta fice daga ɗakin.

leeya na fitowa ta ɗaura towel ɗin ta iso gaban mirror ta zauna, har yanzu dai mayafin na fuskar ta amma ko da kuskure bata yarda ta kalli mirrorn ba balle taga yanda fuskar ta take ko a cikin mayafin.

saida ta kammala shafe jikinta tsaff da mai, sai kamshin takeyi duk da bata saka perfume ba amma kamshin man da ta shafa ya game ko ina cikin ɗakin,

mum ce ta shigo ɗakin da sallama, hannuta riƙe da kaya, doguwar rigar ƙanan kaya mai adon stones ƙanana ta ɗan mayafin rigar da ake ɗaurawa idan an sakata.

"Har kin fito kenan"

"Ehh mum nafito"

"Tau ga kaya nan ki saka idan kin gama ki sakko ƙasa kizo daining kici abinci kinji"

"Okay mum, Nagode sosai"

"Kidaina min godiya kinji, nayine saboda Allah"

"To Allah ya baki lada mum"

"Ameen sai kin fito"

"Okay mum"

Mum na fita leeya ta miƙe ta zura rigar, rigar kuwa tayi mata chif-chif, amma a jiki saidai bata ida kai mata ƙasa ba.

Mayafin rigar ta ɗakko sannan ta cire wanda ke fuskarta, nan take gashin ta ya zubo gaba ɗaya, kama gashin tayi tare da mirɗeshi waje ɗaya, sannan ta laulaya mayafin rigar a fuskar ta,

amma da yake mayafin bayada girma sosai sai bai rufe mata kanta gaba ɗaya ba.


Tafiya take a hankali cikin natsuwarta ta sakko ƙasa, tana sakkowa ta nufi daining area ta zauna koda ta isa ba kowa amma ga abinci nan an jera kala-kala.


A ƙa'idar gidan gaba ɗaya indai ka kasan ce ɗan gidan ne kai ba ɗan aiki ba to tare ake zama gaba ɗaya a ci abinci.

Tana nan zaune a haka tah ɗauki kusan mintuna goma kafin papu ya iso wajen yana isowa kuwa ta tashi da sauri ta isa gaban shi,
"papu barka da rana"

"Barkanki dai ɗiyata ya jikinki"

"Ni ba abun da yasameni papu"

"Ah Masha Allah, idan kinci abinci yanzu kije ki huta kinji, anjima da yamma zaku fita da mum ɗinku tayi miki shopping ɗin kayan sakawa kinji"

Ƙara durkusa wa tayi har ƙasa sosai ta fashe da kuka, a cikin kukan ne take yimasa addu'a da fatar gamawa da Duniya lafiya.

"Tau ki tashi ki zauna godiyan ya isa haka kho"

Komawa tayi wajen zamanta ta zauna, sannan ta soke kanta ƙasa tana murza yatsunta,

"ki tashi kije part ɗin mum ɗinku ki kirata"

"Wallahi papu bansan inane part ɗin ta ba"

"Aww hakane fa"

"Amma ka kwatantamin zan gane in sha Allah"

"Ok tau idan kika hau sama hawa na biyu bangaren hagu nan ne part ɗin ta, dakinyi knocking zatayi fito"

"Tau yayi papu, yanzu kuwa"

Miƙewa tayi ta nufin saman step ɗin sai kusan gab da zata shiga part ɗin na mum saiga mum ta fito

"Ahhh ƴata ina zakije?" mum ta tambaya tana shafa kan leeya.

"Mum papu ne yace na kiraki kizo, kuma khulud ma bata fito ba"


"Ayyah sorry na barku kunata jira kho, gani nan tafe Bara naje part ɗin ku na kira sistern ki yanzu kinji"

"Okay mum a fito lafiya"

Leeya na gama faɗin haka ta juya ta koma ƙasa, ita kuma mum ta bi hanyar da zata sadata da part ɗina khulud, tana Isa part ɗin ta fara ƙwala wa khulud kira har ta iso ƙofar ɗakin ta,

"Khulud!×2"

"Gani nan" khulud ta faɗa a takaice tana fitowa daga bedroom ɗin ta.


Juya kanta tayi gefe ko kallon mum bata ƙara yi ba.


"Gayamin bakya buƙatar leeya a gidan nan ne nasan duk dan saboda ita ne kika ƙi fitowa cin abinci, kuma nasan saboda ita ne kike wannan fushin kho? Gayamin meye matsalar"


"Uhmm first of all mum, she's stranger, and again she's extremely poor girl, she picked the bottles on the street and I will never ever share my father's house with her. Bazan taɓa haɗa wurin zama ɗaya da talaka ba haba dai mum wannan ai raini kika janyomin wallahi" khulud ta faɗa tana huci.

"Ajiyar zuciya mum ta sauke a fili kaana tace

"saboda leeya ta zauna a gidan nan bashi zai saka a dinga kiranta da sunan gidan nan ba, ba kuma shi zai saka dangin ki su ɗauketa yanda suka ɗaukeki ba, na taimakawa rayuwar leeya ne kawai sabida girmanta bakai yanda za'a kyaleta ta riƙa yawo kan titi tana tsince tsince ba, dan haka dan allah ki sakawa zuciyarki salama ku zauna lafiya keda ƴar uwarki kuma yayarki"

"Never mum, bazata taɓa zama yayata ko ƴar uwata ba bazata taɓa zama ba, i was born to be great I'm not being suffer"
faɗin khulud tana ƙara juya kanta gefe.


"Ohh Bara na gyaramiki maganar ki, ba wanda aka haifa domin yasha wahala, yanayi ne kaɗai zai iya mayarda mutum haka, so munada abunda zamu taimaki mutane me zai hana mu taimake su ɗin my kid" mum ta faɗa cikin sigar rarrashi.

"Mum idan taimako zaki bata ki bata taimakon ta tafi mana, amma bazata zauna a gidan nan ba"

"Wai meyake damunkine khulud meyasa kike haka? Meyasa!?? this is not my child, kina ɗabi'arda bata dace ba, wannan halin yayi yawa a shekarunki khulud, meyasa? To bara nagayamiki, ba inda leeya zataje tana nan a gidan nan this is the final".

"Okay mum" khulud ta faɗa tana rolling eyes ɗinta.

"Khulud ni kike yiwa haka, ina yimiki magana kamar bani na haifeki ba..."

"Sorry"
Faɗin khulud tun kafin mum ta idar da maganar da zatayi.

"Hmmm zomuje kici abinci"

"I'm satisfied" ta faɗa tare da juyawa ta koma ɗakinta.


Zuciyar mum kuwa kamar ta zage ta fito waje saboda bakin cikin halaye da kuma ɗabi'un khulud ƴarta mace tilo.

domin kuwa yau ta tabbatar khulud bata tsoronta, a ranta take gani kamar ma ba laifin ita khulud ɗin bane laifin papu ne daya sakkamata komai takeyin yanda taga dama, tana cikin tunanin ne harta sauka ƙasa ta isa daining area, har yanzu kuma leeya da papu na zaman jiranta.

"Ina khulud?"
Abunda yafito daga bakin papu kenan.

"Tana ɗakinta"mum ta bashi amsa

"Meya hanata fitowa?"

"Tace ta ƙoshi da abincin"
Murmushi kawai papu yayi domin yasan abunda ya kawo wannan.

"Leeya!"

"Na'am papu"

"Ki zuba duk kalar abincin da kikeso kici, idan kin gama sai ki zubawa khulud nata ki kaimata ɗakinta".

Da

10 / 61