BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   7 / 61

18K to 21K   out of 180.4K words

kin tashi lafiya? Ya gajiyar aiki kuma ke ga yar aiki ga komai amma bakya zama ki huta"
Papu yayi tambayar yana zama kan Pakistan sofa dake gefe.

Mum na shirin bashi amsa sukaji muryar khulud ta fashe da kuka tare da komawa part ɗin ta aguje,

Zaro idanu papu yayi tare da faɗin "subhanallah!, namanta da ƙararki aka kawomin fa"
Bayanta yabi shima cikin sauri, ita kuwa mum murmushi kawai tayi ta tafi zuwa aikinta.

Koda papu ya isa harta rufe ƙofar ɗaya daga cikin ɗakin da ta shiga a part ɗinta domin kuwa ɗakuna ne jere har ɗaki shida ita kaɗai.

waɗanda suka ƙawatu kuma suka haɗu iya haɗuwa, duk a cikin dakunan ba wanda bata shiga saidai akwai wanda ta tsani ta shigeshi wata wato Library room idan take karatu sai idan mum ta matsa mata sosai ne take shiga ɗakin amma badan tanaso ba.

Daga isarsa part ɗin ya nufi ɗakin da yasan tana cikinsa domin kuwa yasan idan aka ɓata mata rai, ko tayi fushi to bazata wuce dakin ba.


shiyasa ko yanzu ma ya nufi dakin domin ya rarrasheta ya kuma bata hakuri.


Amma sai ya tararda ƙofar ɗakin a rufe, yayi knocking har ya gaji taƙi ta buɗe kofar, rarrashin duniya yayi amma ina ko saurarenshi batayi sai ƙarar abubuwan da take fasawa kawai yakeji.

yayi-yayi ta buɗe amma taƙi, shi bama komai ba yanaso ta buɗe kofar ne don kada tajiwa kanta ciwo ne amma taƙi.

Mum kuwa taji papu shiru ya jima bai fito ba gashi har lokacin break fast ɗin yayi kuma 10Am Flight ɗinsu zai tashi.

gashi har 9:20 kuma sai yaje shopping mall, bayansa tabi itama domin ta kirashi suyi break fast gaba ɗaya saboda haka ƙa'idar gidan yake koda yaushe idan za'a ci abinci tare akeci gaba ɗaya,

Shigowa tayi part ɗin ta tarar da papu yana faman rarrashin khulud kan ta buɗe kofa.


Sallama mum tayi tare isowa wurin:"justice lafiya meyake faruwa?"

"Ba lafiya"

"Meya faru? Mum ta kuma tambaya"

"Mamana ce ta kulle kanta a ɗaki tana ta fushi gashi kinga lokacin break fast yayi amma taƙi ta fito kuma kinga inaso na tafi kar nayi missing Flight" cewar papu da damuwa shimfiɗe a fuskar sa.

Murmushi mum tayi a zuciyar ta amma a zahiri sai ta mayarda fuskarta ta kamar wacce zatayi kuka ta isa gaban Kofar
"mamana Please can you open it, badai ni bace na ɓata miki rai I'm really sorry, kiyi hakuri ki buɗe kinji mamanah na daina daga yau" Mum tayi maganar cikin sigar rarrashi.


Daga can cikin ɗakin suka ji muryar khulud tana cewa

"mum please I'd like to be left alone, ku tafi dan Allah inaso na huta"

Khulud tayi maganar daidai yanda zasu jiyota, mum kuwa da papu suna jin haka suka juya domin kuwa sunsan tunda ta faɗi haka to bazata fito ba.


Daining suka nufa, suna tafiya ba wanda yace kanzil, har suka ƙarasa.

daining chair mum ta janyo wa papu tare da masa alama da ya zauna, da ƴar damuwa a fuskar sa ya zauna kan daining chair ɗin sannan mum tafara serving ɗinshi.


Ta kula sosai akwai damuwa a tattare dashi, kuma tasan damuwar bata wuce ta khulud bace domin kuwa yana tunanin halin da take ciki yanzu.

"Justice menene abun damuwa kuma yanzu, kamar dai baka san halin mamana ba, kasan tanada saurin fushi ne kawai amma batada wuyar hucewa, yanzu kasamu kaci abinci ka ƙoshi kawai saina gayamaka yanda zakayi ta fito ɗakin cikin sauƙi. Idan ko akayi haka bata fito ba sai a ɗauko extra key ɗin ɗakin nata a buɗe mana"

Guntun murmushi papu yayi wanda a iya fuskar sa ne kawai sannan yace,

"shikenan amma kada ki zubomin da yawa domin kuwa sauri nake kinsan saina fita shopping yanzu"

Yafaɗa yana duba agogon bangon dake rataye daining area ɗin.

Basu ɗauki tsawon lokaci ba suka kammala break fast ɗin, inda mum tagaya masa abunda zaicewa khulud ta buɗe kofa.

Sake komawa yayi sashen nata cikin sanyi ya fara magana"my kid ki fito mu tafi kar mu makara zuwa shopping ɗin nan kuma kinga by 10 flight ɗinmu zai tashi, idan kuwa bazakije ba sai ki gayamin abunda kikeso na siyomiki"

"Zanje pa, gani nan tafe" khulud ta faɗa daga cikin ɗakin.


Ajiyar zuciya papu ya sauke a hankali domin kuwa yaji daɗin hakan, yana tunanin idan ya tafi khulud ɗinsa na fushi dashi bazai samu yayi abunda zai kaishi Mexico ba, da wahala ma idan zai iya yin tafiya mai nisa alhali khulud na fushi dashi............✍🏻






















BAYAN WUYA...
By RUMANA M DIGGI




Ep.008









_____________IFE ROAD LAGOS NIGERIA.




LEEYA
Farkawa tayi daga wahalallen baccin da ya ɗauketa, jikinta duk ba ƙwari sakamakon yunwar da ta addabeta.


tashi tayi da ƙyar daga inda take kwance sannan ta janyo jakarta ta fito da kuɗin da suka ragemata domin taje ta sami abunda zata ci,

tafiya take da kyar tana jan ƙafa a hankali take takawa, domin kuwa ba inda baya yimata nauyi a jikinta, ciwon da kanta ya fara yimata ne takeji kamar zai tsage,
amma haka ta daure taci gaba da tafiya har ta iso kan wani shago.


Da sauri ta miƙa kuɗinda ke hannuta tana shirin yin magana sai mutanen wurin suka ruga aguje harda mai shagon suka bar wajen gaba ɗaya, dafe kanta tayi da takeji kamar zai tarwatse, durkushe wa tayi ƙasa tare da fashewa da wani irin kuka, hannu tasa zata yaye mayafin fuskar ta.


"Kinyimin alƙawarin bazaki taba bayyana fuskar ki ga kowa ba hatta ke kanki har sai ranar da zan gayamiki, Dan Allah"


Maganar ammin tace taji tana dawomata a kunnuwanta tamkar yanzu ne take yimata ita.

Nan da nan ta ƙara sautin kukanda takeyi tare da janye hannunta daga kan mayafin, kukanta tayi mai isarta har saida ta gaji don kanta kafin ta tashi tabar wajen.


ba wanda ya ƙara kulata har tayi gaba kallonta kawai akeyi idan ta wuce wasu suyi gudu, wasu kuma su kauce su bata hanya domin suna tunanin ko aljana ce ko kuma mahaukaciya.

Tah ɗauki tsawon lokaci tana yawon neman abunda zata ci da kyar ta samu wani shago inda mutane suka cika yawa, wa sunsu basu kula da ita ba har ta miƙa kuɗin da ke hannunta, hatta shi mai shagon bai kula ba harya amsa kuɗin tare da furta "me za'a bada"
Jin anyi shirune yasa shi ɗago kansa yana ƙoƙarin sake tambayar ta, maganar shi ce ta maƙale sakamakon arba da yayi da yanda leeya take da sauri ya juya zai koma can ƙarshen shago, leeya data fahimci abunda yake shirin yi da sauri da cafko hannusa muryarta na rawa tace
"abinci zaka bani, dan Allah ka taimakamin wallahi yunwa nakeji sosai".

Kalmar Abinci kawai ya iya fahimta a kalamanta da sauri ya janyo sandar biredi da ruwa biyu ya miƙamata, sannan ya haɗa mata da kuɗinta ya bata, hannunsa data rike ta sake da sauri tare da juyawa tana jan ƙafar tata, tun kafin ta isa inda ta ajiye jakarta da fara yagar biredi tanaci sosai kamar wacce bata taɓa sanin menene abinci ba a rayuwar ta,
Koda ta ƙarasa kuwa biredin saura kaɗan, tana gama ci kuma ta ɗauki ruwan ta fara sha saida ta shanye ruwan biyu naki ɗaya sannan tayi gyatsa ta jingina sai bacci ya kuma kwasarta.



★★★★★★★★★★★
KHATTAB MANSION.
SULEJA NIGERIA

"mamana kefa nake jira ki fito muje banso na makara tafiyar nan".

"Pa, kaje kaima ka shirya, kaya nake sakawa idan na saka zan fito"


Tana gama faɗin haka papu ya juya yabar wajen, part ɗinsa ya koma tare dayin shiri kamar yanda ulud tace, bayan ya kammala tsafff ya ɗauki car keys ya fita part ɗin nasa.
Yana fita kuwa ya tarar da ita ta shirya ita ƙadai zaune a master parlour tana kurɓa juice a glass cup.
"Pa, har ka fito? Allah banyi tunanin kaine ka shigo nan ba na ɗauka daga cikin made ɗin gidan nan ne wata ta ƙara karyamin doka.

"Mamana Wai wace doka ce kika kafawa made ɗin gidan nan"

Taɓe baki tayi kafin tace:"ba wata doka bace papu kawai dai na gayamusu ne banason ganin kowa idan na shigo parlour nan, kuma banaso naga ko wuce anyi har saina ɗaga, balle idan nashigo nayi kallo, ko idan zan sha juice"

Khulud ta faɗa tana kaɗa idanuwanta, tare da huro iska daga cikin bakinta, ta juya kanta gefe ɗaya tana ajiye juice cup ɗinda ke hannunta.

"Mamana kenan daɗina dake Bakya ɗaukar wasa, kice wannan itace dokar da dayammah ta karya kho"

"Ehh pa, shine kuma mum tayi min faɗa a gabanta, dana gayamaka kuma wai kace zaka yimata warning amma ka ƙi"

"Uhmm mamana akwai son rigima harda mum ɗin taki sai anyimata rigima kenan, Tau a dinga hakuri dan Allah kinji khuludina"
Papu ya faɗa yana shafa kan khulud.


"Muje, ko kaima kanaso ka makarane shiyasa"

Gaba tayi yana biyo ta baya har suka isa parking space,
Suna isowa wajen drivern gidan ya taso da saurinsa ya taryesu:

"Alhaji fita za'a yi ne"

"Me zai fito damu idan ba fita zamuyi ba, ko ka taɓa ganin mu munzo nan haka kawai idan ba fita zamuyi ba. An ajiyeku ne kawai bakusan aikin ku ba, wallahi next time you try this I Will tell my pa, to fired you. What's all this"

Khulud tayi maganar tana sakin tsaki tare da shigewa mota abinta.

Da kallo kawai papu da drivern suka bita dashi ba wanda yace kanzil, kana papu yayiwa drivern umurnin ya shiga motar su tafi.

★★★★


IFE ROAD LAGOS NIGERIA.





A hankali takejin sauƙar ruwan sama a jikinta, tun tanaji kamar mafarki take har yakai ga tafara jinsu sosai suna saukowa ta ko'ina ajikinta.
Miƙewa tayi sosai ta shiga laluben jakarta domin kuwa har duhu yafarayi, cikin Sa'a kuwa takai hannun ta kan jakar, yayinda ruwan suke zuba kamar da bakin ƙwarya.



Da gudu ta fita daga cikin ƴar rumfar karanda ta fake, domin kuwa har a cikin rumfar ruwane ke zuba sosai ba bambanci da wajen rumfar.

Gudu take sosai iya ƙarfinta domin gujewa ruwan karsu jiƙata, babu inda bai jiƙe ba a jikinta gashi ta gaji sosai da gudun da takeyi da ƙyar take iya yinshi sosai.

a hankali ta fara hango wani wuri mai kamar ɗaki, kamar kuma shago, amma bata iya tantance menene, daga nan inda take, hangoshi kawai take sai idan anyi walƙiyane zata ganshi.

Duk da haka kuma bazata iya gane ko menene ba, a ranta tana ayyana cewa ko menene idan ta riskeshi shiga zatayi kawai.

ƙara hanzari tayi wajen yin gudun domin kuwa ta gaji ainun.
Tana isowa bata tsaya ta tantance abunda tagani ba, kawai ta tuma ta faɗa, tare da janyo abunda taga anrufe wurin data shiga itama ta rufe.


Ajiyar zuciya ta sauƙe tare da furta"Alhmdullillah" can a ƙasan zuciyar ta.

Gefe ɗaya ta samu ta rakuɓe domin kuwa sanyi takeji sosai har tana makyarkyata.


Sautin haƙoranta kawai kake iya jiyowa suna kaura da juna, ta duƙunƙune waje ɗaya, a haka wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita batare data sani ba domin kuwa yunwa ce cike fallll a cikinta tunaninta kawai ina zata sami abunda zata ci.

Bata wani ɗauki lokaci tana baccin ba sakamakon ji da tayi kamar ana tafiya da ita. Da farko ta ɗauka mafarki take sai da ta buɗe idanun ta ne ta fahimci da gaske ne ba mafarki take ba

"hasbunallah wani'imal wakil, me hakan yake nufi, badai mota na shigo ba"

Fara dudduba ko ina tayi inda take zaune domin kuwa a yanda takeji ma har an ɗauke ruwan saman, saida ta lura sosai kafin ta fahimci da gaske mota ce ta shigo.

kuma mota ma irin wannan datake safaran kayayyaki daga wata ƙasa zuwa wata ƙasa.

Fara bubbuga bayan motar tayi tana faɗin:

"dan Allah ku taimakeni ku saukeni anan, wallahi bada ganganci na shiga motarku ba, banmasan mota bace nashiga ne kawai dan na samu mafaka da ruwan sama, dan Allah ku taimaka mini"

Faɗi kawai take tana kuka Bama alamar ana jiyota domin kuwa irin dogayen lorry ɗin nan ne, kuma gashi ansaka abun rufewa anrufe motar rufff, haka tayitayi har ta gaji da magana yayinda yunwa ke ƙoƙarin kada ita.


ruwa tagani a cikin gora ajiye a chan gefe, da sauri takai hannunta tare da ɗauko ruwan ta ɓalla marufin gorar takai ruwan bakinta.


Bata janye ruwan abakinta ba saida ta shanye ruwan kafff, bata kai ga ɗauke gorar bakinta ba cikinta ya ƙulle sosai Mirgina tafarayi tare da riƙe cikinta ta fara fitarda numfarfashi.













K. WAASIB MANSION
★SULEJA NIGERIA★

Sun ɗauki tsawon mintuna suna danna horn bakin gate, amma kamar ba kowa a gidan.

Kallon driver side khulud tayi tare da furta

"kai shuraihu me kake jira da bazaka fita ka buɗe mana gate ba, ko so kake ni nafita na buɗe, ko kuma pa kake so yaje ya buɗe?"

Tun kafin takai ƙarshen maganar da takeyi driver ya fita da sauri ya nufi gate ɗin tare da wangaleshi, dawowa yayi cikin motar tare da kunna hancin motar cikin gidan.


Tun kafin motar ta isa parking space ulud ta bada umurnin a dakata da tuka motar, drivern ko yanajin haka yayi saurin take birkin motar.


Tun kan tayi wani abu saiga wani mutumin daban ya ƙaraso tare da buɗemata ƙofar motar, yana buɗewa kuwa sai gata ta fito daga cikin motar bata ƙara waiwayo ba.

Guard room ta nufa, tana tafiya cikin isa da taƙama kamar itace mai gidan ba papu ba.

Kwala masa kira ta farayi da karfinta cikin fushi da ɓacin rai.

uzairu mai gadi dayake toilet yaji Muryar khulud dake kiransa.
Take hantar cikinsa ta kaɗa domin kuwa yasan yau dubunsa ta cika a gidan, da sauri ya fito daga cikin ban ɗaki tare da nufota da aguje.

Idan kuwa aunawa za'ayi uzairu mai gadi ya haifi kamar ta ba ɗaya ba balle biyu, sauran ma'aikatan gidan har mamakin irin wannan tsaurin idon irin na ulud. Mutane dayawa suna da haushin ulud a ransu musamman ma wasu ma'aikatan gidan da tasa aka koresu ba tare da wani ƙwaƙkwaran dalili ba, kuma sun ƙudurta a ransu idan suka sami dama zasu a zabtarda ita daidai da abunda ta aikata musu, kawai dai dama ce basu samuba.

"Gani hajiya ƙarama, don Allah ayimin aikin afuwa, na rantse da Allah cikina ne baya yimin daɗi tun jiya, kuma banyi tunanin zaku dawo da wuri haka ba da bazan rufe gate ba dan Allah ayimin afuwa"
Uzairu mai gadi ya faɗa yana haɗe hannayen sa biyu, alamar roƙo.

Kanta ta ɗauke gefe ɗaya:

"kaje wurin pa, kace masa nace ya baka ladar aikinda kayi, ka ƙara gaba"

Daga haka bata ƙara cewa komai ba ta juya ta barshi wajen hankalinsa a tashe, kuma yasan cewa shikenan zamansa a gidan ya ƙare tunda a gaban idanunsa tasha yiwa wasu ma'aikatan haka.


Kuma shikenan sun koru har abada.
Hannunta ta ɗaga tare da yiwa wani mai aiki alama da yazo, cikin azama ya ƙaraso Wajen jiki na rawa domin gudun kar abunda ya faru da wancan shima ya faru a kansa.

"So nake kaje ka samo cardboard paper kayi rubutu akai muna neman sabon mai gadi wanda yasan aikinsa ba kamar wancan sha-sha-shan ba, sannan kaje wajen gate ka liƙa domin kowa ya gani.

"Tau hajiya ƙarama in sha Allah yanzu zanyi kuwa, wannan ba wani aiki bane. Kuma za'a sami irin wanda kikeso da yardar Allah"
Cewar mutumin.

Juyawa kawai tayi ba tare da ta ƙara faɗin komai ba ta nufi cikin gida.

A parlour ta tarar da mum tare da mai aikin gidan wato dayammah shiga tayi ciki kamar yanda ta saba, ba wanda take yiwa sallama parlourn kawai ta shiga tare da furta "excuse me.
Mum I'm back"
Khlud ta faɗa tana ƙarasowa gaban mum tare da dafata.

"Barka da zuwa my kid, kin dawo lafiya? Ya hanya kuma?'

"Hanya Lafiya ƙalau, ina pa?"

"Yana part ɗinsa Yana shiryawa yanzun nan zai fito ai"

"Okay" kallon ta takai kan dayammah:
"what'd you make, me kika haɗa yau?"

Khulud tayi tambayar ga dayammah daidai lokacin da mum ta miƙe ta bar wajen tare da nufar part ɗin papu.

"Doya da miyar kwai na haɗa"

A tsawace khulud ke magana, kuma a fusace"What!!? You make what!!??, how many times do I need to tell you that I'm lactose intolerant, I don't eat eggs, yet should want ahead and the make eggs for me, do you have something wrong with your hearing?"

"Ulud!!!!, why talking to dayammah in this manner, meyasa a duk lokacin da zakiyi mata magana sai ki dinga yi kamar Sa'arki?" mum tayi maganar a tsawace itama tana shigowa cikin parlourn.

"Mum can You imagine she makes eggs for me, after I told her that I'm lactose intolerant I don't eat eggs"

"Saboda ta dafa miki kwai ne kike yimata haka, it's easy idan bakyaso kigaya mata sai ayi miki wani abincin da kike so ko kuma ki faɗa wanda kikeso da kanki sai a girka miki, bawai kizo kisakata gaba kina yimata faɗa ba"

"Mum I've told her at several times that I'm a began I'm not eat eggs. Milks, little potion. Idan ta gaji kuma ta bar aikin tunda ba dole aka sakata ba, mu kuma ba kyauta take yimana ba biyanta akeyi. Dama haka talakawan nan suke idan sukaga ana sake musu"

"Khulud!!" Mum ta faɗa a fusace.

Juyawa kawai khulud tayi batare da tajira abunda mum zatace ba tayi shigewarta.

"Dayammah kiyi hakuri Dan Allah. Nidai shine abunda nakeso kicigaba dayi dan Allah, kije kitchen kici gaba da aikin ki"

Juyawa mum tayi itama tare da nufar ɗakin khulud, tura ƙofar ɗakin tayi cikin Sa'a ta tarar da ita a buɗe domin a tunaninta ma ta rufe ƙofar.


Tura ƙofar tayi tare da yin sallama sannan ta shiga ciki, zaune ta tarar da khulud gefen gado tana cika tana batsewa

Zama mum tayi a kusa da ita fara yimata magana cikin sanyi.
"Khulud, sau nawa zan gaya miki ki koyi yanda zakiyi magana da manya, dan Allah khulud ki zamo yarinya mai jin maganar iyayen ta, kuma kizamo mai girmama manya kinji"

"Mum she's the maid I have the right talk to her the way that I wanted, ita ɗin ƴar aiki ce ba dole ne

7 / 61