Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
hakan, inaga ita musulma.
share hawayen ta tayi kafin tace "shikenan oke nagode Dan Allah kaima kayiwa su amminmu addu'a idan kaje wajen da kuke bauta"
Tau kawai yace mata kafin ya ɗauki buta ya ɗebo mata ruwa sannan ya kawo mata a gaban ta tare da faɗin: "tashi kije banɗaki ki wanke fuskar, gida zanje amma zandawo, zanje na sama muku abunda zakuci daga nan kuma nasamawa budurwa maganin da zata sha domin ta samu sauƙi"
Godiya tayi masa kafin ta ɗauki butar ta nufi ban daƙi, bayan ta wanke fuskar ta sannan ta tafito ta koma ta zauna tayi tagumi tunani kala-kala na zuwar mata a kwakwalwa.
Bata daɗe zaune a wurin ba sai ga oke yadawo ɗauke da abinci amma ya ɓoye shi ta yanda ba za'a gane abunda ya ɗauko ba lokacin duhu yayi sosai dan har an qare sallar Isha.
Fitilar da yazo da ita ya haska har hasken fitilar ya kai inda leeya ke zaune.
"Leeya! Kuka kikeyi haba dai leeya dan Allah ki daina mana idan nima baso kike nayi kukan ba"
Shafa fuskar ta tayi cikin mamaki tajita da danshin hawaye, A mamakance ta kalleshi tace: "okene wallahi bansan ina kukan ba, nima bansan da zuwansa ba"
Zabura tayi da sauri ta nufi inda aleena take kwance.
Har okene ma saida ya razana da yanda ta miƙe.
shafff ta manta da ita tunani yayi mata yawa, tana isa wurin ta tada ita zaune ta jingina ta daidai lokacin da okene ya iso wajen tare da ajiye musu abinci.
Tare suka dinga bata abincin tanaci a hankali har tayi musu alama ta ƙoshi ba um bale uhm-uhm.
Maganin da ya taho dashi ya balla tare da yiwa leeya umurni taje ta kawo mata ruwa "leeya je ki ɗebo ruwa Aleena ta haɗiye magungunan nan ta samu ta kwanta ko zataji ƙarfin jikinta, zuwa safiya"
Tashi tayi da sauri tare da nufar inda ake ajiye ruwa a gidan nasu, yayin da okene ke haska mata hasken tauch light ɗinda ke hannunsa.
Bayan ta debo ruwan, aka Bama aleena magani ta haɗiye da ƙyar sannan suka kwantar da ita. Sun ɗauki tsawon lokaci a haka ba wanda yake komai,
ba kuma wanda ya sake kallon wani a cikin su, har suka fahimci bacci mai ƙarfi ya ɗauki aleena.
Nan ne okene yayi wa leeya sallama domin shima ya fara jin baccin ''leeya zan tafi gida domin nima bacci nakeji kuma gashi inajin ciwon kai sosai, banso na barki a gidan nan ku kaɗaiba amma kinsan halin iyayena bazasu barni na kwana wani Wurin ba, duk da ko yanzu ma basusan ina gidan ba, ga wannan touch ɗin kiyi amfani da ita sannan kuma dan Allah karkiyi kuka bayan na tafi kinji, ki ƙaddara yanzu kinshigo wata rayuwa ta daban mai matukar wahala amma kisani komai tsanani sauƙi na nan zuwa BAYAN WUYA SAI DADI ki rike wannan a ranki"
Daga haka bai jira abunda zata ceba yafita gidan zuciyarsa nayi masa ɗaci. Bayansa tabi da kallo tana share hawayen da bata san da zuwan suba.
"Hakika wannan ƙaddara ce da ba wanda ya isa ya canjamuna ita, haƙiƙa wata mutuwar wa'azi ce, dan a ƙananun shekauna na fahimci haka, haƙiƙa basai kanada ciwo bane za'a kiraka majinyaci, ko rashin mahaifama babbar jinya ce mai wahalar warkewa.
Wannan itace ranata ta farko da bazan taɓa mantawa da itaba a rayuwata, yau zan kwana a cikin gidanmu ni kaɗai, dagani sai ƴar ƙaramar ƙanwata babu Ammi babu Abbi.
Mutuwa mai raba ƙauna, mutuwa mai tonon asiri, mutuwa mai tarwatsa farin ciki, mutuwa mai razana ƙwaƙwalwa, mutuwa mai yanke zumunta, haƙiƙa mutuwa bakida sabo, ya Allah, Allah ina roƙon ka ya Allah kabani juriyar rashin iyayena"
Leeya ke wannan maganar yayinda fuskar ta ta jiƙe sharkaf da hawaye.
haka sukayi daren ba wani bacci da ta samu saida sanyin asuba ya sauko Sannan bacci ya kwashe ta, bata farka ba saida rana ta faso sosai.
A daren kuma wani mummunan labari ya samu leeya wai jiya da dare ɓarayi sun shiga shagon abbinsu sun kwashe komai ba abunda suka bari, bayan sunyi satarne kuma suka cinnawa shagon wuta ya ƙone kurmus.
Hannu ta ɗora aka ta fasa wata gigitacciyar tsawa wacce ke barazanar fasa dodon kunnen wanda yajita.
nan ta faɗi sharaff a ƙasa kamar wata gawa, haka mutane suka dinga ketareta suna wucewa ba wanda ya kula da ita, mafi yawan jama'ar wasu tsoron ta ma sukeyi, yayinda wasu suke kiranta mayya ta kashe mahaifiyarta da mahaifinta ga ƙanwarta can a gida zata lashe ta, kuma gashi Yanzu ta kunnawa shagon mahaifinta wuta.
haka dai akayita yamuɗiɗi da maganar har ta isa ga kunnen mai gidan, wato wanda ya basu hayarsa, yana isowa wurin kawai ya fara yimusu watsi da kayayyakin su nan tsakar hanya yayita watso duk abunda ya samu a waje kuma har zuwa lokacin leeya na kwance a some bata ma san abunda ke faruwa ba.
Da gudu okene ya ƙaraso wajen kamar wani mayunwacin zaki zuciyarsa a bushe kyamas ba alamar fara'a a fuskar sa cikin wani irin ɓacin rai ya nufi wasu mutane da yaji suna faɗin
"dama an ƙona ta tana a halin suman nan tun kafin ta farka Dan bata da amfani a cikin mutane" har suna faɗin ayi sauri a ƙonata kafin ta tashi ta lashe musu kurwa.
Wasu daga cikin su sunyi na'am da shawarar da aka yanke ta ƙona leeya, wani Christian mai suna taoma ne yayi sauri ya ɗakko fetur tare da ashana a rumfarsa, yana isowa wurin baiyi wata wata ba ya kwalala mata ruwan fetur ɗin tare da kesta ashana.
Daidai lokacin ne okene ya iso wurin.....✍️
BAYAN WUYA......
By RUMANA M DIGGI.
EP.05
___________Da wani irin ƙarfin da baisan yanada shiba ya saka ƙafa ya shuri taoma, nan take ashanar tayi wani gefen daban sake komawa kan taoma oke yayi tare da maka masa wani irin naushi a ciki nan take kuwa taoma ya suma, sai mutanen da ke Wurin ne suka rirriƙe okene.
Leeya kuwa tun da taoma ya zuba mata ruwan fetur ɗin ta farka daga suman da tayi amma nauyin da takeji na jikinta ya hanata miƙewa, sake jujjuya idanun ta take yi yayinda ta miƙe zaune a hankali tana gyara zaman mayafinta, saidai hankalinta ya ƙara tashi matuƙa yayinda taga abunda mai gidan yayi musu, kifa kanta tayi a tsakanin cinyoyinta ta fashe da wani irin kuka mai ban tausayi ga wanda yasan menene tausayi.
Okene kuwa yana Ganin haka sai ya fizge daga riƙonda akayi masa yazo kanta yanata bata hakuri, amma taƙi kulashi taci gaba da kukanta kamar bazata daina.
Taoma da tuni ƴan uwansa sunzo sun ɗaukeshi da sukayi tambaya aka gatamusu abunda yayi niyar yi basu ce komai ba suka ɗaukeshi kawai suka tafi dashi, da haka Mutanen sukayita watsewa kowa ya koma kan lamarinsa sai da wurin ya rage saura su biyar kacal, okene leeya da kuma yaran mai gidan mutum biyu, sai kuma shi kanshi mai gidan da yaketa aikin watso ƴan kayayyakin su.
Har yanzu kuma okene bai fasa rarrashin taba kuma yana ci gaba da bata hakuri, fitowa mutumin yayi daga cikin gidan tare da nufar inda take yana isowa ya busa hayaƙin sigarin da ke bakinsa a fuskar ta sannan yace:
"ke aljana tun tuni kisan inda dare yayi miki, saboda nidai gaskiya bazan iya barinku a gidan nan ba, tun jiya ma naso nazo nagaya muku amma wata sabgar ta ɗaukemin hankali har gashi kin janyomin hasara to wallahi kinci arzikin matsiyatane ku bakuda ko sisi, da badan haka ba wallahi sai an biyani ko jikar ifirito ce ke ba abunda zaki iya yimin,
kuma yanzu-yanzun nan minti ɗaya na baki kishiga ciki ki fito da kanwar nan taki ko itama na watsota waje, kitashi nace"
Ya faɗi maganar a tsawace, yayinda okene ya cika dam kamar ya fashe, hannu yasaka ya rarumo wani dutse da niyar ya faskara masa aka.
Shi kuwa mutumin ya juya yana tafiya bai ma san abun da ke faruwa ba.
Leeya data fahimci abunda yake shirin yi cikin matukar tashin hankali ta riƙe masa hannun daya riƙe dustsin dashi tace
"dan Allah oke kayi hakuri ka barshi ae mu mukayi masa laifi, mune muka janyo masa asara fa kaga ko bazamu hanashi yin Magana ba shida abunshi dan Allah ka kyaleshi"
A zafafe okene ya kalleta sannan yace "An ƙi a kyaleshi ɗin saboda yaganku ƙananu shine zai wulakanta taku haka, leeya duba kayayyakin ku watse a titi kamar wasu dabbobi, sannan Kuma asara dayake faɗi ae ba shikaɗai yayi ba domin kuma......"
tasssss yaji saukar mari ba zato,
babu shiri a tare suka ɗago kai domin ganin wanene da wannan aiki, da sauri leeya taja baya saboda ganin momyn sa ce,
"Okene bakajin magana bazaka fita harkar wannan mayyar yariyar ba ko" momynsa ta faɗa baki na kumfa taci gaba da faɗin "Har iyayenta ta cinye balle kai da ba kowa bane a wajensa, wata ƙilama ta shanye kurwarka shiyasa kake yi muna jayayya kuma ka kasa fita rayuwar ta, sha-sha-sha kawai"
"Ah ah mommy leeya ba mayya bace kuma ba ita ta kashe iyayenta ba Allah ne ya kashesu kuma wallahi kuna dauƙarwa kanku nauyin wannan baiwar Allah..."
Tasss tasssss kakeji ta sake ɗaukeshi da wasu maruka biyu nan take bakinsa ya fashe jini ya fara zuba a hankali.
Leeya na ganin haka ta dafe kunnuwanta tare da fasa wani kuka mai cike da danasanin abunda ta janyowa okene domin dabadan ita ba tasan ba za'a fitar masa da jiniba.
Mommyn shi bata ko kalli inda take ba ta fizgi hannunsa tare da nufar gidan dashi suka bar leeya tsaye a wurin ita kaɗai.
shi kuma zuciya tama hanashi ko ya ƙara kallon leeya domin ya tabbatar idan ya ɗaga idanu ya kalleta bazai iya barinta ota kaɗai a wurin ba, sai dai momynsa ta yankashi, shiyasa kawai ya barta a wurin bai kuma kallontaba.
Ji tayi an rungume ta tabayan ta, a ɗan razane ta waiwayo dan ganin ko waye jikin ta duk a mace,
Suman tsaye tayi saboda ganin abunda batayi zatoba.
Nan da nan itama ta rungume ta cikin tsantsar farin ciki kamar ba ita bace take kuka: "budurwa yajinki!? Ni banmasan fitowar ki a gida ba kinji sauƙi kho? Alhmdullillah Allah na gode maka Allah ya ƙara baki lafiya ƙanwata"
Ta faɗi maganar hawaye na zubowa a idonanunta ga kuma murmushi kan fuskar ta.
''yayata kukan me kake yi kuma, meyasa zaki yi kuka?? saboda an fito muna da kayayyakin mu a hanya kikasan ko gyara gidan za'a za'ayi? yarhyarh kinsan me wallahi ko an gyara gidan nan abbi da ammi bazasu zauna ba suje can inda suka tafiyar su suka barmu, tunda sunzaɓi su tafiya wani wurin ba tare da sun gayamana ba kuma basuje da muba, kuma sunƙi su dawo har yanzu"
Aleena ta fadi maganar idanuwanta na cikowa da kwalla.
Share mata hawayen leeyana tayi tun kafin su zubo sannan tace: "na ɗauki alkawarin bazan taɓa barin hawayenki yayi zuba ba indai ina nan da rai da Lafiya, haƙiƙa ammi da abbi sun tafi, tafiya kuma wacce ba dawo, tafiyar da sukayi suma ba sanar musu akayi ba balle mu su sanardamu kiyi hakuri ƙanwata ammi da abbinmu addua kawai suke buƙata kinji ta faɗi" maganar a raunane.
Cikin jin haushin abun maganar leeya, aleena tace:" to meyasa da aka sanar dasu zasu tafi suƙaƙi zuwa damu?"
"Lokacin mu ne baiyiba, idan lokacin mu yayi muma zamu tafi, yanzu dai abar wannan maganar kinji ta wuce ki dinga yiwa abbi da ammi addu'a kinji budurwa"
"Yahyah-leeya to wazai min aure?"
"Ni zanyi miki aure Aleena kar ki damu, kuma duk abunda kikeso a sakamiki a ɗakinki Ni zan miki shi in Allahn duka ya yarda. Kizo mu kwashe Kayan nan namu daga kan hanya"
Tare suka tattara kayayyakin nasu suka kaisu ɗan nesa kaɗan daga kofar gidan, wajen wasu bishiyu da sukayi wa arean tasu ƙanwanya suka kai kayan suka ajiye, amma har yanzu da saura dan iya abunda suke iya ɗauka suka ɗauka,
''Wai Allah bayana wallahi yarhyarh nagaji dayawa, kuma gashi bamu ida kwashe Kayan nan ba kuma naji kaina yafara min ciwo ga kuma yunwa danakeji."
"Subhanallah kanki yana ciwo kuma, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un yazanyi kinga bara naje nayi bara kozan sami kuɗin da zan siyamiki abinci da magani" leeya ta faɗa tana miƙewa cikin tashin hankali.
Aleena data fahimci hankalin yayarta ya tashi sai ta rasa abunda zatayi nan da nan ta ƙaƙaro dariya mai karfi cikin dauriya duk dan taga hankalin yayarta ya kwanta " to sarkin tsoro wasa fa nake garau nake ƴar yunwa kawai nakeji ko itama ba sosai ba, saboda haka ki zauna muyi fira kawai"
ta karasa maganar tana janyo hannun ta alamar ta zauna ɗin.
Sauke ajiyar zuciya tayi Sannan ta zauna ba dan tayi na'am da abunda tace ba "Amma kuma duk da haka bazan zauna ba kibari na tafi na sama mana abunda zamuci ke kuma sai ki jirani anan kafin na dawo kinji"
"Yarhyarh a ina zaki sama mana abunda zamuci to??"
"Barah zanyi budurwa" leeya ta bata amsa a takaice.
"Allah yaya bazakiyi bara ba, a ina ma zakije bara bayan kinsan a ecocon nan yanda mutane ke harinki, kuma kindaisan yanzu ba ko ina ake zuwa ba ansha faɗa mana a makaranta ƴan satar mutane da ƴan bindiga sunyi yawa yanzu, nidai indai dan nice wallahi kiyi zamanki bazaki baraba akainaba,
bakisan wani zai iya ruɗarki ba ya cuceki da sunan bara zai baki nidai bazaki bara ba idan kuma kikace sai kinje wallahi nima saina tafiya na barki kamar yanda ammi da abbi sukayi"
Rufemata baki leeya tayi tare da faɗin "shikenan ƙanwata wallahi bazanje bara ba shikenan adaina Wannan maganar kinji bazaki tafiba bazakije ko ina kibarni ba"
"Tau idan bakyaso nayi tafiya ta wallahi karki ƙara maganar zuwa yin bara"
"Bazan ƙaraba kanwata"
"Hmmm ka jita wai "bazan ƙaraba kanwata" wacece ƙanwar taki, yanzu tunda ammi batanan shine zaki kirani da ƙanwarki Allah idan ta dawo saina gayamata"
Aleena ta faɗi maganar tana taɓe baki zatayi kuka.
Da sauri leeya ta durƙusa ƙasa tare da faɗin "natuba budurwa bazan ƙaraba"
Dariya suka fashe da ita su duka biyu yayinda sukaji muryar ta uku atare dasu, da sauri suka juya baya Domin ganin waye mai dariyar.
"broth O" da sauri aleena ta isa ta rungume shi cikin murna da ɗoki.
"budurwar amminta kin warke kenan, haka da kikayi ai sai ki karyani" ya faɗi maganar cikin jin daɗin ganin leeya ta fara sakewa hartana dariya.
"Na warke kam amma gaskiya ciwon kai nadamuna sosai da sauri" ta rufe bakinta da hannayenta tare da juyawa ta kalli leeya "wasa nake masa kaina baya ciwo"
"kinga zo ga abinci nan kuci, harda magani ma nazowa budurwa dashi. idan kunci sai Kisha maganin kinji, leeya kizo ki zauna mana, ko laifi nayi miki ne da kika koma gefe kina kallona haka, karfa ki cinyeni da wannan kallon kinga ɗan kyakkyawa ko? kinaso ki ragemin kyau tun ɗazu sai kallona kike"
Ta ɗan ji kunyar maganar da yayi mata saidai ba tana kallonsa bane da wata manufa, ita kallon da take masa na mamakin dawowarsa ne garesu bayan sanin yanda sukayi da momynsa, mamakin ta ya kasa ɓoyuwa har zuwa wannan lokacin da tazo kusa dasu.
ƴar ƙaramar tabarma ta janyo ta shimfiɗa sannan ta kalleshi tace "bismillah zo ka zauna kho"
Da murmushi a fuskar sa ya ƙaraso inda shimfiɗar take hannunsa saƙale dana aleena ɗayan hannunsa kuma na riƙe da abincin, suka zauna tare sannan leeya tazo ta zauna har yanzu dai da mamaki a fuskar ta.
Ta kasa hakuri saida ta furta tambayarta "okene me kuma ya dawo dakai nan baka tsoron momyn ka ta kuma zuwan nan tayi maka abunda tayi maka ɗazun, kaga har bakinka ma yaɗan kumbura dan Allah ka tashi kaje wallahi bana son kana shiga matsala ta dalilina"
Matsowa yayi kusa da ita kafin ya janyo hannun ta itama sannan yace "niba komai yadawo dani wurin kuba Magana ce dani kizauna idan kin gama cin abincin saina gayamiki abunda ke tafe dani"
Abincin ya janyo kusa dasu sosai sanna ya ɗauko ruwan pure water dayazo dasu ya miƙawa ko wannen su ɗaɗɗaya, sannan yace "oya kuci sosai sai kun ƙoshi kunji ƙannena"
Idanun leeya ne suka kaɗa sukayi jawur yayinda, Aleena ta fara auna abincin hankalinta kwance.
Okene ya lura da yanayin leeya daya changer duk yanda yaso ya shareta amma yaji ya kasa, tashi yayi daga inda yake ya nufi wurin da take:
''leeya! Make faruwa? Ba kinyimin alƙawarin ba zaki ƙara zubda hawayenki ga su ammi ba, leeya kin taɓa gayamin fa ba ayiwa wanda ya mutu kuka, hawayen azabtar dasu ya keyi, kinaso ta Dalilin ki Ammi da Abbi su azabtu?"
Dasauri da girgiza masa kai "wallahi banaso kuma basu nakeyiwa hawaye ba okene ka taimaka mana ka zamomuna bangon da muke jingina muji sanyi, ka nuna muna so yayinda kowa yake gudun mu, okene bamuda abunda zamu biyaka dashi ina roƙon Allah ya rabautaka da samun tsira da rahmarsa"
ta ƙare maganar hawayen da ta riƙe suna zubomata.
Murmushi yayi tare da kai hannunsa yana shafa kanta "badai kuka kike ba koh? Wannan bakomai bane kinji ƙanwata nidai abunda nakeso dake yanzu kici abinci kawai ki nutsu magana zamuyi kuma saikin bani hankalinki sosai maganace mai mahimmanci"
Hannunta ya riƙo tare da wanke mata shi sannan ya saka hannun ta a abinci yace " kiyi sauri kici yanzu zanje nadawo kinji"
da "tho" ta amsa masa kafin itama ta fara cin abincin.
miƙewa yayi tare da barin wurin.
Suna nan zaune bayan sun gama cin abincin aleena ta bingire sai bacci,
yayinda leeya itama taɗan kishin giɗa. Okene yaɗauki lokaci kafin ya dawo ya tarar dasu duk suna bacci kuma da alama sunajin daɗin baccin da suke, saboda haka ya juya da nufin barin wajen domin bayaso ya tadasu kuma a ransa abune biyu ke yawo,