BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   24 / 61

69K to 72K   out of 180.4K words

motsin leeya ba kuma idan ta aika khulud sai ta ce mata tana bacci har a wannan lokacin.

Itama mum da kanta sau biyu tana zuwa dakin amma sai ta tararda ita tana bacci.

"Khulud kije ki duba leeya ta tashi kuwa, idan bata tashi ba kizo ki gayamin domin nasan ba lafiyaba indai har yanzu bata tashi ba"

"Okay mum bara naje na duba miki ita"

Kitchen khulud ta shiga ta ɗakko ruwa masu sanyi sosai, ta nufi ɗakin leeya.

Da mugun ƙarfi ta banko kofar tana isa inda leeya ke kwance ta sheƙa mata ruwan da ke hannunta.

Wani wahalallen numfashi leeya ta sake, tare da sakin kuka mai ban tausayi.

"Tashi baƙar munafuka kinzo kin samu wuri tun ɗazu kin wani kwanta kamar gidan ubanki, ko Ni dayake gidan mu ban kwanta nayi yanda kikayi b......"

Tun kafin khulud ta rufe bakinta taji an wanke ta da maruka har biyu, cikin matukar zafin rai turab ke magana.

"Khulud yaushe kika zama haka, tambayarki nake yaushe kika zama haka, ashe bakida tausayi, kinsan wannan yarinyar batada lafiya, amma zakizo saboda rashin tausayi da bushashshiyar zuciya irin taki, zakizo ki jiƙata da ruwa. Ko mutum mai lafiya aka zubawa ruwan nan zaiji daɗi balle ita da kina ganinta kinsan batada lafiya"

"Wallahi ya-Turab lafiya ƙalau take, munafunci ne kawai irin nata, shine akanta zaka dakeni kho ya Turab, ita da bakowa ba bakuma kowan kowa ba almajira, ƴar bola, ƴar tsintuwa, ƴar talakawa, duk ta kai matsayinda zaka dakeni akanta" cewar khulud cikin kuka.

Wasu marukan biyu ya ƙara wanketa da su a wannan karon kam harda bugu.
sosai ta kuma na fitar hayyacinta, miƙewa leeya tayi cikin ƙarfin hali tana takowa gabansa.

Wata uwar tsawa ya daka mata saida ta ruɗe"wallahi kina ƙaraso sai na haɗa dake, wahalliyar yarinya kawai, Ni da nine ke ko yankata za'a yi bazan kalli wurinda take balle nazo kwatarta"

A ƙiɗime mum ta shigo ɗakin tayi kansu tare da shiga tsakanin su,

Khulud kuwa tana ganin mum ta shigo ɗakin tayi sauri ta koma bayanta tare da sakin wani irin kuka.

"Turab meye haka, me khulud tayi maka data cancanci wannan duka"

"Bani tayiwa ba" cewar turab yana nuna leeya data rakuɓe gefe ɗaya sai rawar ɗari take.

Da sauri mum ta ƙarasa gareta, cikin tashin hankali tace "innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, leeyana meyasameki haka, turab meyake damunta, duba kaga yanda jikinta ya kumbura baki ɗaya gashi kuma duk kalar fatarta ta canja"


"Nina bata magani mum, amma bata shashi a ƙa'ida ba, shine yayi mata haka, inaga overdrogs tayi kuma ba'ayin overdrogs a magungunan da na bata, musamman wanda jininsu bayada ƙarfi. Kuma itama da alama jinin nata ba karfi ne dashiba, amma ki kwantar da hankalinka wannan ba wata babbar matsala bace yanzu dai tana buƙatar drip gaskiya kuma sai an an saka mata su da wasu magungunan daban banda waɗan nan, bara naje na dakko kayan aikin. Wallahi sauri ma nake munzo na dauƙi kayanda zan buƙatane gobe ikeja zamuje tare da zafaran da Fahad kuma morning flight zamubi shiyasa nakeso na kwana abuja"

"Yanzu dai ba wannan ba, Dan Allah kayi sauri ka taimakawa wannan yarinyar"

"In Allah ya yarda kuwa" ya faɗa tare da barin ɗakin.

"Mum yanzu shikenan kun daina ra'ayina a cikin gidan nan, duba kiga yanda ya-Turab ya dakeni a banza kamar wata mara gata, wallahi idan papu ya dawo saina faɗa masa tunda ke bazaki iya yiwa ɗan ki magana ya fita harakata ba a gidan"

"Kiyi haƙuri Kinji khulud, bawai ra'ayin ki ne bamayiba. Halin kine bana ra'ayi kuma kin kasa changer wa, yanzu ki duba kiga yanda jikin baiwar Allahn nan ya dawo duk da bansan me kika yimata ba nasan turab bazai dakeki haka kawai ba"

"Wallahi mum nifa ba wani abu na mata ba, ke kika aikoni nazo na tada ita, kuma tun kan ki aikoni inada ruwan sanyi a hannuna shine na shigo bankula ba santsi ya kwashe ni ruwan ya zubemata a jiki. Kuma fa na bata hakuri amma Ya Turab na zuwa ya rufeni da duka kawai baimasan meye mafarin ba"

"Tau kiyi hakuri Kinji, in sha Allah zanyi masa magana kar ya ƙara shiga lamarin ki a gidan nan"

"Is better for you mum" khulud ta faɗa tana barin ɗakin.

Turab bai wani dauki lokaci ba ya dawo ɗakin da duk kayayyakin da zai buƙata.

Leeya kam har bacci ma ya fara ɗaukarta, domin shikaɗai ne abunda zatayi taji sauƙi a wannan lokacin.

"Basai kin tayarda ita ba mum zan saka matane kawai sai in tafi idan drip ɗin ya ƙare sai a cire mata ko kuma idan papu ya dawo ya cire mata"

"Tau Allah yasa ayi dace"

"Ameen mum, amma na gayamiki wannan ba komai bane in Sha Allah idan aka saka mata drip ɗin nan shikenan angama da matsalar, magungunan ne kawai basu karɓi jikinta ba, amma zaki gani kuma zata wartsake bada jimawa ba"

"Allah ya yarda"

Daga haka mum bata ƙara faɗin komai ba har turab ya kammala abunda zaiyi ya tafi.

Mum ta zauna da leeya ko'ina bata ɗaga ba ko nan da can, kuma ta kira papu ta sanardashi abunda ke faruwa. Shima ya tausayawa leeya sosai kuma yayi mamakin wannan al'amari ace daga shan magani jikin mutum ya kumbura kuma kalar fatarsa ta canja.











Turab na fita daga gidan yayi dialing number Zafaran domin duk tare suka taho, saidai shi zafaran ya raka Fahad gidan su zohal kafin turab ya kammala abunda zaiyi a gida.


"Hello zafaran kuna ina ne haka"

Daga cikin wayar kuma zafaran yace" kafito kawai a first Street na arear ku zamuzo mu dauke ka"

"Ok hurry up please karku barni pending"

"Ahh, mun isa mubar likita bokan Turai a titi yana jiran mu, wane mu, kaidai ka fito kawai"

"Okay ai nakusa na ƙaraso ma"

Katse wayar akayi da faɗin "shikenan sai ka ƙaraso ɗin"

Ba wani jimawa turab ya iso wurin, saidai abun mamaki koda ya iso ya tararda motar su a packed an ajiye ana jiransa ya ƙaraso.

"Har kun iso" turab ya tambaya yana buɗe kofar motar.

"Me zamu jira to, mun iso kai kaɗai ka tsayardamu ai amma mun jima a wurin nan ko zafaran" cewar fahad.

"Ae nasan kunjima anan professional lie-man"

"Ni kake kira professional lie-man, Wallahi kuwa sai zohal taji wannan. Kuma sai ta ɗaukar min mataki"

"Idan zohal ta ɗaukar maka mataki, nikuma zan saka lewar mu ta ɗaukarmin mataki kan ka harma zohal ɗin"

Sai a lokacin zafaran ya shiga maganar tasu shima jin an ambaci rabin ransa. yana amsa maganar tasu jefi-jefi.



Washe gari kuwa tunda sassafe suka yi shirin tafiya, bawani dogon shiri sukayiba domin a ranar zasu dawo.
Tafiyar awa huɗu sukayi, kafin su isa inda zasuje.

Suna sauka kuwa. Basu zarce ko ina ba sai arean da yasan lewarsa take, unguwar da yake gani kamar itace sillar komai, unguwar da aka kashe iyayen leewa, unguwar da aka salwantar da ita, unguwar da Yana shigowa cikinta da yaga komai ya dawo masa sabo. Wasu zafafan hawayene suka gangaro a kwayar idanun sa yayinda ya ƙurawa wani wuri can nesa dasu idanu.

Mai jirgin kwale-kwale ya kira ya shiga dasu cikin Area. Wani gida suka nufa bayan mai kwale-kwalen ya ajiye su, Zafaran ne gaba sannan sai fahad sai kuma turab. daya kasance bayansu gaba ɗaya.

Sallama sukayi baki ɗayansu duk da sunsan abune mawuyaci su sami wanda zai amsa sallamar.

Domin ba gidan musulmai suka shigo ba.

Matan gidan su biyune sai kuma ƴaƴansu da bansan adadin su ba duk dai suna zaune a tsakar gidan nasu.

Mamaki kwance a fuskar mutanen gidan ganin baƙin larabawa da indiyawa a gidansu.

Zafaran ne ya matsa sosai kusa dasu, yayin da turab da fahad ke tsaya daga farkon gidan.

"Barkan ku da wannan lokacin" zafaran ya faɗa da yaren da yasan masu gidan zasuji, kuma shine asalin yaren da zafaran yakeji sosai kafin hausa, saidai shi musulmi ne bakamar mutanen gidan ba.

"Wata matashiyar yarinya da bazata wuce shekaru goma sha bakwai ba, ta amsa masa da faɗin" barkanka dai wakake nema"

"Mai gidan nan nake nema"

"Bayanan amma baiyi nisa ba, jira kaɗan a aika yaro ya kirashi"

"Okay Nagode" amma duk wannan da suke Fahad da turab basa fahimtar komai saboda ba hausa suke ba kuma ba turanci ba.

Kallonta ta mayar kan Fahad da turab tace a cikin Yaren ta.
"Ku shigo ciki ga shimfida ku zauna"

Kallon juna turab da fahad suka farayi, domin ba wanda yaji abunda tace.

Kallonta ta mayar kan Zafaran ta kuma fadi da yarenta domin batajin hausa ko kadan " basajin abunda nake cewa ne?"

"Eh, suba yaren mu bane. Su hausawa ne kawai"

"Okay nagane, to ba damuwa ka gayamusu da yarensu, kace masu ga wurin zama".

"Guys wai kuzo ku zauna akace"

Shigowa sukayi cikin gidan suna nufar inda akayi masu shimfida.

"Masha Allah, wallahi kamar sun san a gajiye nake ina neman wurin zama" cewar FAHAD.

"Tau ai gashi ka samu yanzu kho"

"Eh, nasamu mana, amma ga alama ba gajiya a tattare da man turab domin naga ko magana bayayi"

"bakasan idan gajiya tayi yawa tana saka mutum ya kasa magana ba"

Fahad na shirin yin magana sai ga mai gidan yazo.

Miƙewa sukayi gaba ɗayansu tun kafin ya karaso suka durƙusa tare da gaida shi, duk da sunsan ba Musulmi bane amma hakan bai hanasu yin ɗa'ah ba.

Zafaran ne kawai yayi magana domin shi kaɗai yasan abunda zai cewa mutumin da yarensa.

"Muje ga shimfida can ku zauna sai inji abun da ke tafe daku" cewar dattijon.

Miƙewa sukayi gaba ɗaya suka koma kan shimfida suka zauna.
Shi kuma aka miƙo masa kujera ƴar tsuguno ya zauna.

"Amma kamar ban wayeku ba kho"

"Eh gaskiya baka wayemu ba, muma haka"

"Meya kawo nan, naga kamar ku ba ƴan nan bane, kuma naji mamaki sosai danaji kana yin yarenda mukeyi. Ƴan uwanka basa magana ne"

"Munzo muyi tambaya ne, kuma ni da ka ganni yare ɗaya nake dakai, saidai Ni Musulmi ne. Kuma ƴan uwana sunayin magana saidai basajin yaren nan, abunda kuma ya hana nayi maka magana da hausa nasan yanada wuya ace kanajin Hausa"


"Eh, hakane kam gaskiya, to tambaya akan menene, fatar dai nasani kuma zan iya bayarda amsa"

"Muma muna fatar kasani ɗin"

"Mecece tambayar taku" dattijon ya tambaya cikin yarensu.

"Baba dan Allah ina tambayar wani mutum ne da ake kira ADEBAYO SHOLA"

Gyaran murya kaɗan datijjon yayi kafin yace"bansan Adebayo shola ba, amma kuma nasanshi ta labarai da ake bada wa a unguwar nan tamu. Hasali ma nan ne gidan sa daya taɓa rayuwa"

"Eh, hakane nan ne gidan sa daya taɓayin rayuwa, wannan shine ma babban dalilin da yasa ina shigowa arean nan na fara shigowa gidan nan domin nasan anan zan sami cikakken labarin abunda ya faru dashi, shekaru bakwai baya"

Cikin mamaki dattijon ya kalleshi da faɗin
"kai kuwa yaro ina ka shiga tsawon wannan lokaci, sai a yanzu da aka fara mantawa zaka fito kace kana neman labarin sa"

"A can baya da daɗewa munyi zama a garin nan sai saidai ba'a wannan bangaren muke ba, ADEBAYO SHOLA ƙanin mahaifiyatane sosai. Canjin wurin aiki da aka yiwa mahaifina yasa muka bar garin nan muka koma Abuja da zama, sosai muna jin labarin su, domin suna kiran mu a waya muma muna kiransu ana sada zumunta. Kwatsam rana ɗaya sai muka wayi gari da labarin cewa anzo an tarwatsa wannan area. Kuma ba'a samu mutum ko ɗaya daya rage mai numfashi ba a wannan area.

Labarin ya girgizamu sosai matuƙa musamman ma Ni, domin kuwa harda matata da zan aura, muna cikin jimamin wannan halin ne kuma aka sake yiwa mahaifina canjin matsayi ya koma da yin aikinsa a ƙasashen ƙetare. Duk muka koma can da nufin idan komai ya lafa sai mu dawo mu cigaba da bincike ko Allah zai sa a gano inda wasu daga cikin su suke, domin a zahirin gaskiya waɗan da suka bada rahoto suka ce akwai wasu mutanen da aka gudu dasu saidai ba'a asan inda aka nufa dasu ba.

Hukumomi da dama sun shiga binkicen, da muka koma can ƙasar las-vagers kuma sai naci gaba da karatuna a can. Dama mahaifiyata ke ƙarfafamin gwiwa kan wannan lamarin na ɓatar matata da zan aura, to itama bamu jima da komawa las-vagers ba ta rasu bayan ƴar guntuwar jinya da tayi.

Daga nan mahaifina ya ɗauki soyayyar duniya ya ɗoramin kuma baya barina na ɗaga ko nan da can, sai da na kammala karatuna gaba ɗaya, bayan haduwar mu da bawan Allahn nan"

zafaran ya faɗa yana nuna turab. shikuma turab bai masan wainarda ake toyawa ba

"sai haɗuwar mu dashi ne mahaifina ya aminta na biyoshi muzo Nigeria bayan dogon sharaɗi daya ɗaɗa mana. To kaji ainihin cikkaken labarina kan wannan lamarin da kuma buƙatata agareka................✍🏽

















BAYAN WUYA.......










By RUMANA M DIGGI






EP.26






______________"naji labarin ka yaro, kuma zan baka kaɗan daga abunda nasani game da wannan batun amma bana tunanin za'a iya samun Adebayo shola a raye, saidai baza'a fitarda ran samun matar da zaka aura ba saboda basu kashe mata da ƙananan yara ba. Amma babban abun lura anan shine ba'a san ina za'a fara neman suba tunda kaga abun ba jiya bane ba kuma yau ba magana ce da aƙalla shekaru bakwai"

"Hakane Ameobi, (ma'ana baba) a yaren hausa, Nima wannan abun nake tunawa naji zuciyata ta karaya amma a kullum ina ƙara ƙarfafawa kaina"

Nan datijjon ya kwashe labarin da yasani gaba ɗaya ya faɗa masa. kamar dai yanda ya samu labarin a bakin Muhsin idan baku manta ba.

"Shikenan Ameobi munji abunda kace kuma muna godiya sosai, in Allah ya yarda zanci gaba da bincike idan rabona ce zan sameta, komai wahala da rintsi da wuya idan lewa mata tace zan sameta"

"Hakane ayi ta addu'a kuma kacigaba da hakuri kaji, Bara na kira a kawomuku ruwa kusamu kusha" datijjon yayi maganar yana kallon ƙofar ɗakunan biyu jal dake gidan.

"Ah ah mun gode sosai wallahi, ai Bama sai an kawo mana ruwa ba yanzu tashi zamuyi mu koma kuma, saidai wata rana" zafaran ya faɗa yana miƙewa, ganin ya miƙe ne ya saka su turab suka miƙe baki ɗaya.

Hannu zafaran ya saka a aljihun sa ya fito da ɗaurin kuɗi ya miƙawa datijjon tare da daɗa yimasa godia.

Sosai datijjon yaji daɗi kuma yayita yimasa addu'a irin tasu, da fatar nasara. Haka Zafaran da turab da kuma fahad suka bar gidan zuciyar zafaran ba daɗi.

"Man Zafaran, baka bamu labarin abunda kuka tattauna da wancan datijjon ba, duk da kasan Bama jin abunda kuke faɗa".

"Kuyi hakuri mutanena, haƙika ba wani abu daya sauya a labarin da muhsin ya bani, amma a yanzu bazan iya cemuku komai ba. Ku bari mukoma gida kawai"

Dayake basa son su takuramasa duba da halin da yake ciki yasa suka nuna masa ba komai a bari har a je gidan ya nutsu sai ya basu labarin abunda ake ciki.

Komawa sukayi filin jirgin da suka sauka suka jira next flight ɗinda zai koma Abuja da yamma.










★★★★

BAYAN SHEKARA ƊAYA........FARIN CIKI, BAƘIN CIKI, SOYAYYA, SHAƘUWA, SHIRIYA, NADAMA HAƊE DA KUNYA, BAYYANAR ƁOYAYYEN AL'AMARI, SADAUKARWA, CIN AMANA, TARE DA BAYYANAR AHALI.

A shekara ɗaya data gabata abubuwa da dama sun faru, ciki kuwa harda soyayya mai ƙarfi tsakanin FAHAD GAHEES WAASIB da kuma ZOHAL KHALIL GIRAH.

Tsaftatacciyar SOYAYYA suke a tsakanin su, wanda sukeji tamkar su haɗiye junan su. Babban FARIN CIKIN da wannan ahali suke ciki kuwa shine nemarwa fahad auren zohal da akayi har ma an saka rana nan da wata huɗu masu zuwa.


Babban abin BAƘIN CIKIN da ahalin gahees waasib suke ciki kuwa, a asibitin da suka kai Rukhshanah can BHOPAL INDIA an tabbatar musu da bazata warke daga cutar da ke damunta a ƙwaƙwalwar ba, saidai zata iya samun sauki ne idan taga abunda ta taɓa sani gabanin cutar ta sameta.

Likitocin sun tabbatar musu da cewa idan har suka bi sharaɗin maganin nan, za'a sami waraka ko kuma akasin ta domin maganin bayada tabbatacciyar magana ɗaya, sauƙi ko kuma akasinsa.


Domin ba ko wane mai cutar ƙwaƙwalwa ake bawa wannan maganin yayi amfani dashi ba, sai wanda yayi nisa sosai, ita kuwa Rukhsha za'a iya sakata sahun mutane masu irin cutar nan da suka yi nisa sosai, domin duk yanda akayi kanta ko kuma wani bangare na kanta ya bugu sosai har ya haifar mata da matsala a cikin kwakwalwar ta.

A bangaren ɗaya kuwa, khulud k. Waasib tayi graduation ta kammala karatun ta na secondary a BUSY BRAIN INTERNATIONAL, kuma ta sami good grades saboda mahaifinta nada abun hannunsa. Kuma aka samamata admission a ROONEY COLLEGE OF SCIENCE AND INNOVATION SULEJA. inda zata fara karatun nursing nan bada jimawa ba.

Leeya kuma aka sama mata CATERING SCHOOL inda takeda burin zuwa taci gaba da koyon girke girkenta.

Turab kuwa ya shahara ya goge, ya zama zakaran gwajin dafi a ƙasashen ƙetare, domin kuwa yana aikinsa cikin ƙwarewa. Ga sanin makamar aiki, domin har ɗaukan shi anayi aje dashi wurin yaƙi komai wuya da rintsi kuma zai jure, idan aka tafi dashi yakin kuma baza'a barshi a baya ba domin idan ka ganshi ma zakace shine sojan bawai likitan suba.

Bangaren aikin sa kuma komai raunin da soja ya samu, ko karaya, ko kuma yawan harbi to yana koƙari kuma da addu'a nan take ake warkewa idan yayi aiki, shiyasa suke bala'in ji dashi, a wata ɗaya sai yayi tafiya aƙalla bakwai ko takwas daga ƙasa zuwa ƙasa yaje yayi musu aiki ya dawo, kuma bazai barsu ba har sai yaga wanda yayi wa aiki ya miƙe da kanshi.



Saidai matsalar da turab ke fuskanta a gida, anyi masa tsayin daka kan dole sai ya fito da wacce yakeso a haɗasu su biyu a cikin waasib family wato shi da fahad ayi musu aure lokaci ɗaya.

"Turab mun riga mun gama magana nida justice idan har Allah ya
Mayar da shi lafiya daga tafiyar

24 / 61