Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
da bayaso a gani a cikin wajen, saidai shi mutum ne da bayason takura ko hayaniya, kwata kwata bayason zama a cikin mutane, kuma idan yana nan bayada wurin da ya wuce masa wancan warin, domin yana ƙaunar irin yanayin wajen. Daga cikin abunda yasa yake zama a wajen nan yanada wata jita wacce a koda yaushe yana zama yayita kiɗa jitar har sai bacci ya ɗaukeshi.
Idan har kin kula da kika shigo wajen kinga wasu kujeru biyu a can gefe su kaɗai to akwai wani plastic table dake ɗauke da kayan kida, anan ne yake zama koda yaushe domin bangaren yafi ko wane wuri daɗin zama a faɗin balcony ɗin"
Mum ta faɗa tana zube blending ɗinda ta kammala a cikin bowl.
Sosai leeya taji wajen ya ƙara shiga ranta tana ayyanawa a ranta a kwanakin nan zata dinga ziyartar wajen baramma da taji cewa akwai kayan kiɗa, a rayuwarta ba abunda yake birgeta kamar tayi kiɗan piano ita kaɗai.
"Mum to shi Wannan mutumin faɗa yake yiwa mutane ne idan aka shiga wajen" leeya ta tambaya tanason jin ƙarin bayani.
"Hmmm, ba faɗa yake ba duka yake wallahi kuma ba dukan wasa ba. Kafin khulud ta daina zuwa wajen ta daku sosai saida justice ya masa rantsuwa karya ƙara dukanta har ya koma a wannan lokacin".
"A gidan nan yake mum, ko shine ya-Turab?"
"Shine, wallahi sai kunyi a hankali yayan naku ba sauƙi kuma bayason wasa ko kaɗan, duk wannan da kike gani khulud tanayi saboda baya nan ne. idan yana nan sanyi zatayi liƙiss kamar ba ita ba"
"Hmmm to mum Allah dai ya mayarda shi lafiya"
Leeya ta faɗa zuciyarta na ƙara hasasomata har ta fara kiɗa da piano a garden ɗin ya-Turab"
Sosai sukaci gaba da firarsu har suka kammala aikin, daga nan mum ta fita ta bar leeya a kitchen. Ita kuwa mum ta koma daining area.
Bayan Leeya ta idarda komai ta fara jidar abincin tana kai daining. saida ta kammala tsaff sannan ta koma part ɗin ta tayi wanka.
KADUNA, STATE.
ASHMED SPECIALIST HOSPITAL KADUNA.
zaune take gaban wani matashin likita idanunta a kansa, yayinda shikuma yake koromata bayani.
kana ganin ta kasan ba ƴar ƙananan mutane bace. Kalarta irin chocolate color ɗin nan ne amma mai ƙonuwa, ganin yanda fatarta ke sheƙi da walwali zaka tabbatar ƴar manyan mutane ce. Tanada yalwataccen gashin ido dana gira, wanda suka ƙarawa fuskar ta armashi da kyau da tsari.
Yarinyar bazata wuce shekaru sha shida ba a ƙiyasi, saidai zakaji tausayinta idan kasan larurarda ta kawota a asibitin.
"Rankiyadaɗe, dole sai kin fitarda damuwa a cikin ranki fa, kinga yanzu stage ɗin da aka ɗoraki a shan magani yakamata ace zuciyarki na samun natsuwa, kuma kibata lokacin da zatayi tunani"
"Stop saying please Dr. B. Areef" Yarinyar ta faɗa kamar zatayi kuka. "Zuciya ta batada wani time da zatayi tunani, kawai ka faɗamin menene abun yi yanzu, saboda nasan yanzu dad na waje yana jiran fitowata kuma idan na fito zaizo ya tambayeka idan ansamu wani ci gaba, me zaka faɗa masa Dr. Beeshwah Areef?"
Yarinyar ta faɗa tana gyara zaman Glasses ɗinda ke fuskantar ta, cikin tsananin damuwa.
Ɗan guntun murmushi likitan da aka kira da Dr. Beeshwah Areef yayi kafin yace mata
"gaskiya zan faɗa masa mana, Rukhshanah menene dad ɗinku ya rageku dashi da zaki ɗauki damuwa ki sakawa zuciyarki. Bayan Kuma kinsan damuwarki babban tangarɗace a wannan tafiyar tamu. A yanzu mahaifinki da mahaifiyar ki harma da ƴan uwanki basuda wani buri da ya wuce suga kin sami lafiya. To menene abun da zai sakaki a damuwa Rukhshanah? kinsan fa damuwarki kamar damuwar ahalin gidanku ne gaba ɗayane"
Dafe kai yarinyar da aka kira da Rukhshanah tayi, Alamar surutunda yake yafara isarta.
Dr. B.Areef ya fahimci abunda take nufi, hakan yasa shi janyo takarda da biro, yayi ɗan guntun rubutu a cikin ta, ya miƙa mata.
bayan ta ƙarɓa ta miƙe da nufin ta fita daga office ɗin. Harta miƙa hannu zata buɗe kofar, santsi ya ɗebe ta zata faɗi.
Take ta riƙe sopa ɗinda ke wurin amma duk da haka saida glasses ɗin ta ya faɗi ƙasa.
Da sauri ta durkusa ƙasa tana laluben glasses ɗin nata.
Sai a lokacin Dr.B.Areef ya lura da abuda ya faru.
"Subhanallah" ya furta da ƙarfi yana ƙarasowa wajen da gudunsa. Ɗagota yayi, da sauri ya zaunarda ita kan sopa. Sannan ya juya ya ɗauko glasses ɗin ta ya saka mata.
Nan komai ya bayyana a ganin ta. Da murmushi ta kalli Dr.B.Areef tace "Nagode".
"Ahh ba damuwa Allah ya tsare gaba".
"Ameen" ta faɗa tana barin office ɗin.
Tana fitowa daga cikin office ɗin wasu 'yan mata biyu sa'anta suka rugo kanta da saurinsu suka rungumeta.
"Rukhshanah ya jikinki ina fata dai ansamu ci gaba ko sweet sis?.
d'aya daga cikin 'yan matan ta faɗa.
"Hmmm, twiney kin rigani magana ne kawai amma abunda nazo na faɗa kenan"
Dayar ta faɗa tana shafa kumatun Rukhshanah kamar wata ƙaramar yarinya.
Jin tayi shiru bata ce musu komai ba, yasa suka fahimci batason damuwa,
"Twiney muje ta huta kafin dad ya ƙaraso kho".
"Ok muje ga resting sitter ta zauna. Dayar yarinyar ta faɗa tana riƙo hannun Rukhshanah"
A resting sitter suka kaita ta zauna kafin itama ɗayar yarinyar ta zo ta zauna a kusa da Rukhshanah, zaman ta ba wuya sai ƙarar ringing ɗin waya ya fara ruri a cikin hand bag ɗin da ke hannun ta.
"Hello, ya-fahad". Yarinyar ta faɗa tana kara wayar a kunnenta.
"Yes, FANNAH an fito da ita ne"
"Eh, yanzu ta fito muna ƙarasowa tana fitowa"
"Okay ya akayi, ya jikin nata fatar dai akwai cigaba a stage ɗin nan data kai kho, kinsan yaune farko da akayi mata gwaji akan magungunan da aka bata a wannan watan"
Cikin murya mai alamar damuwa yarinyar da aka kira da FANNAH tace
"to wallahi ya-fahad muma abunda muka damu musani kenan amma ba dama, saboda gata a zaune irin dai batason damuwa ko surutu ɗin nan"
"Allah sarki abun ya tashi kenan, gaskiya ba haka naso naji ba, but ba damuwa bara nazo na ɗaukeku a hospital ɗin domin Dr. Beeshwah yakira dad yayi masa bayani, yace masa basai yazo ba tunda gaku kuma da driver kuke, shine dad yace na kiraku idan da buƙatar sai yazo. Idan kuma ba bukatar hakan na sanarda shi domin 11pm zasu shiga meeting da Company A.R.P"
"Wow Masha Allah, gaskiya nayi farin ciki, kace A.R.P zasu fara aiki a shekarar nan kenan"
"In sha Allah" wanda aka kira da ya-fahad ya faɗa a taƙaice.
"Okay To kace masa yaje kawai zamu iya dawowa gida ai".
"Tau nima dai gani nan zuwa a hanya kujirani, amma ki faɗawa MAYAH DA NU'AIM subi driver su koma ke kuma da Rukhshanah sai kujirani nazo na maidaku gida"
"Okay ba damuwa Amma NU'AIM badashi muka zoba mummy tace bazai biyomuba"
"Okay to taje ko kuma ke kije"
FANNAH kamar zatayi kuka tace
"haba ya-fahad taya zakace twiney taje ni natsaya tarefa mukazo, gaskiya bazataje ko'ina ba tare zamu koma gida"
Kitttt ya kashe wayar domin yasan idan dai da wayar ne yake mata magana to bazataje ko'ina ba amma idan ya ƙaraso da kanshi dole zataje ko kuma yar uwarta taje.
"Menene naji kuna gardama da ya-fahad twiney?" Yarinyar da ke zaune a gefen Rukhshanah ta tambaya.
"MAYAH, wai ya-fahad ne yace kije kibi driver ku koma gida, nikuma da Rukhshanah mutsaya mujirashi yazo ya mayar damu" ta faɗa fuskar ta fallll da damuwa.
Kamar wacce aka cewa za'a rabasu har abada, MAYAH ta miƙe cikin tashi hankali tace"No FANNAH meyasa ya-fahad zaice haka, motarsa bazata iya daukarmu gaba ɗaya bane kome? Gaskiya nidai bazanje nikadai ba kuma kema bazakije ba".
"Iyyeee, nine yayan ko kuma kune yayuna. Na riga na gama magana dayar ku taje driver na wajen gate yana jiranta"
Kamar daga sama haka sukaji muryar ya-fahad ya shigo hospital ɗin.
Da sauri sukayi kansa suna rokonshi harda yan guntun hawayen su;
" ya dan Allah karkayi mana haka, munfiso duk abunda zai sami daya ya samemu mu duka biyu tunda aka haifemu mu biyu bamu ta'ba rabuwa ba. Kuma dan wannan bazaka rabamu ba, munfiso komai zai samemu ya samemu gaba ɗaya" Suka faɗa cikin gamin baki.
"Kujimin yara da shashanci ku har yanzu kun girma amma kamar baku girma ba, rabaku nace zanyi? gida fa nace akai ɗaya daga cikin ku dan kada kubar driver nan ya koma shi kaɗai bayan tun ɗazu ya tsaya jiranku amma shine kuke min kuka kamar nace bazaku qara haduwa ba"
Abu ɗan ƙarami kamar wasa, suka qi yarda shikuma ya nace kan baza'a bar driver ya koma shi kaɗai ba dole kuma sai ɗaya daga cikin su tabi driver.
Sosai mutane suka taru a wajen suna kallon ikon Allah, yayinda Rukhshanah ta rasa inda zata saka kanta saboda batason hayaniya a ƴan kwanakin nan har school ta daina shiga saboda irin wannan.
Rigimar bata tsaya ba har saida aka kira dad ya yanke hukunci subi driver su biyu, shikuma ya ɗakko Rukhshanah suzo gida.
"Okay dad ba damuwa, amma wallahi dad Yakamata a daina biye musu kan haka nan gaba kaɗan fa aure zasuyi kowa ta kama gabanta" ya fahad ya faɗa yana katse wayar.
"Ya-fahad mu miji ɗaya zamu aura idan bazai auremu mu biyu ba saidai yaje ya nema gaba" FANNAH da MAYAH suka faɗa suna barin wajen aguje saboda sanin halin ya-fahad zai iya kaimusu duka.
Guntun tsaki yaja yana nufar inda Rukhshanah ke zaune. Da zuwansa ko magana baiyimata ya miƙa mata hannun shi, miƙa masa nata hannun tayi ya tayarda ita tsaye suka fara tafiya.
Har suka isa mota ba wanda yace kanzil tsakanin sa da ita, zagayawa yayi ta bangaren hagun driver ya buɗemata ta shiga, sannan shima ya zagayo ya shiga ta bangaren driver ya fara tuƙa motar.
"Ya-fahad meyasa kace bazamuje tare da FANNAH da MAYAH ba" Rukhshanah tayi maganar kanta a ƙasa kamar ba ita tayi ba.
Cikin mamaki ya kalleta yace" sannu Rukhshanah ya jikin naki, Kina buƙatar wani abune kafin mu isa gida, ko kuma mu tafi kawai". Faɗin fahad yana qoqarin packing ɗin motar.
"No ya-fahad bana bukatar komai inaso mu isa gida da sauri naji ko FANNAH da MAYAH suna lafiya domin bazan iya yin Magana ba lokacin da kuke rigimar da nima zan bisu gaskiya"
"Humm, Rukhshanah kenan ae saboda ke nayi haka"
"Saboda ni kuma ya-fahad?"
Sai a lokacin ya fahimci 'kwa'barda yayi domin yayi tunanin a zuciya yayi maganar ashe a fili ya furta ta "to yanzu ya ma zance mata ta karta fahimci nufina" ya faɗa a zuciyarsa amma a wannan karon zancen baifito fili ba.
"Kayi shiru ya-fahad bakace komai ba"
"Rukhshanah saboda ke nayi haka, nasan da muna tare dasu yanzu zasu isheki be da surutu, kuma hakan zai iya haifar miki da wata illa domin nasan zasu isheki ne da tambayoyi har sai kin gaji da amsa musu"
"Uhmm ya-fahad kenan indai dan wannan ne ai ba matsala, kuma Ni nasan bazan ji sun takuramin ba tunda inajinsu har cikin raina, duk a faɗin gidan idan aka cire mummy da dad ba wanda nake son kasance dasu kamar FANNAH da MAYAH"
Sosai ya-fahad yaji haushin maganar da ta faɗa "kenan duk irin kulawar da yake gani yana bata, shi baya cikin mutanen da takeson kasancewa dasu a cikin gidan, to meya rageta dashi ne, me twins suke mata wanda shi baya yi mata"
"Ya-fahad kayi shiru wani Abu ya faru ne"
Murmushi yayi irin wanda kana ganin shi kasan murmushin yaqe ne yace mata "ba komai Rukhshanah kawai inaso ki daina magana haka kibari ki huta Kinji, ki bawa ƙwaƙwalwarki dama tatunano wani abu".
"Stop ya-fahad menene haka, Ni zan iya magana da ƙwaƙwalwa tane, ko kuma zan iya bata umurni tabi. Bana son maganar tunanin nan Pleaseeeee" cewar Rukhshanah kamar zata yi kuka.
"Sorry our Rukhsha kiyi hakuri bazan ƙara faɗar haka ba Kinji".
Fad'ar fahad dai-dai lokacin da ya karaso gate ɗin makeken gidan nasu wanda ya amsa sunansa gida yasha kyau ya gaji da tsaruwa.............✍🏼
BAYAN WUYA.......
By RUMANA M DIGGI
EP.16
___________K. WAASIB MANSION, SULEJA NIGERIA.
zaune take a ƙayataccen balcony ɗin da ke gefen gidan, sosai takejin daɗin yanayin ƴar siririyar iska na ratsowa tare da kamshin furanni. Piano da ke gabanta take dannawa tanabin kukan tsuntsayen da ke wurin
Gwanin ban sha'awa.
Wayarta ƙirar iPhone 16 ƴar yayi ta fara ƙara alamar kira ya shigo (my whole world) abunda ya bayyana a screen ɗin wayar kenan.
"Mum? Ta furta cikin tsorata da abunda mum zata cemata idan ta ɗauki wayar.
Saita kanta tayi tukunna kafin ta ɗauki wayar, "Assalamu alaikum, mum!!"
"Leeyana ina kika shiga naje part ɗinki bakyanan kinsa fa gobene taron walimar yayanku, kuma kinsan by 2pm jirgin su zai sauka ba'a gyara masa ɗakinsa ba. Kuma ga baƙi sunata zuwa, ga siyayyarda zakuje kuyi amma ban ganki ba har yanzu"
"Lahhhh, mum Dan Allah kiyi hakuri wallahi duk na sha'afa kiban mintuna uku kacal ganinan zuwa"
"Azo lafiya" mum ta faɗa tana yanke wayar.
Cikin gaggawa leeya tabi ta hanyar da ta shigo wajen ta fita ta laundry room inda ba wanda zai ganta ta koma ɗakinta.
Allah sarki Rayuwa, a shekara goma sha Bakwai din nan na leeya gaba ɗaya, ba wanda zai ganta yayi tunanin itace wancan leeya ta baya. Domin kuwa ba abunda bai sauya ba atattare da ita face abu ɗaya zuwa biyu. Niqab ɗin da take rufe fuskar ta dashi, da kuma rashin kallon madubi da take.
Amma idan kacire wannan ba abunda bai sauya ba daga gareta, kama daga jikinta, adonta, tafiyar ta, maganar ta, surarta, wayewarta da sauransu.
Canja kayan da ke jikinta tayi ta sanya doguwar rigar atamfa, sannan ta ɗakko ɗan kwalin rigar ta yafashi bayan ta saka niqab.
Saida ta isa gaban mirror ne da ɗaura ɗankwalin kana ta fita waje.
Master parlour ta nufa domin tasan kowa yana wurin, Saboda duk a gidan parlour yafi ko'ina girma.
Sallama ta furta yayinda take shigowa cikin parlour.
Ancika sosai dangin papu dana mum kamar wani babban taro ake ko family meeting, nan kallo ya koma kan leeya wacce mafi yawa daga dangin basu san da ita ba. Amma dake taro akeyi ba kowa ya damu da sai yasan ko wacece ba sai waɗan suka kware a gulma.
Saida tayi duba sosai kafin ta iya hango mum can gefe ita da wasu bakin.
"Mum gani me za'a yi yanzu"
Takarda ta miƙa mata tare da A.T.M tace
"kasuwa zaku fara zuwa ku siyo Kayan nan. Khulud da driver na mota suna jiran ki"
"Tau mum bara na dakko mayafina saina samesu a gate kho"
"Okay to banda bata lokaci dan Allah kuyi maza ku dawo"
"In sha Allah mum" leeya ta faɗa tana juya ta koma bedroom din ta.
Bayan ta ɗakko ta fita ta tararda su, khulud na gaba ita kho leeya ta shiga baya. Domin duk zasu fita haka suke idan leeya na gaba baya take shiga. Idan kuma leeya na baya gaba take shi ga.
Idan kuma leeya ta matsa ta cimata mutunci tsafff haɗi ta zageta da iyayenta baki ɗaya, shiyasa leeya ta daina faɗin komai akan hakan.
KUDUNA.
Suna isowa gate ɗin tangamemen gidan Fahad yayi horn, take aka wangale gate ɗin gidan. Ya tura hancin motarsa ciki.
A compound ɗin gidan yayi packing ɗin motar sa domin fita zai kuma yi yanzu.
Yana fitowa daga mazauninsa ya koma bangaren da Rukhshanah take itama ya buɗemata, fahad ko kaɗan bashida girman kai kamar sauran masu kuɗi.
Idan ka ganshi alamace kawai zata nuna kanta shi ɗan manyan mutane ne amma idan ta tashi ce bazakayi tunanin haka.
Yana buɗemata ta fito motar, da gudu FANNAH da MAYAH suka yo kanta a karo na biyu kamar dai yanda sukayi a asibitin.
"Twins har kun iso kenan"
Cikin tsananin farin ciki FANNAH da MAYAH suka dubi juna tare da faɗin "Sweet Rukhsha Kinji sauƙi kenan, Masha Allah"
Suka faɗa suna janyeta daga motar suka shige da ita cikin gidan gaba daya.
Ya-fahad kuwa tun tuni ya shigewarsa gida ya barsu a wajen.
Wani haɗaɗɗen parlour mai ɗauke da kayan ado kala daban-daban, anyiwa parlourn gaba ɗaya ado da pakistan furnitures, da sauran kayayyakin adon da ke parlorn duk na india da Pakistan ne sai kayi tunanin ma ba'a Nigeria kake ba. FANNAH da MAYAH da Rukhshanah suka shigo parlour riƙe da hannun juna, bakunan su ɗauke da sallama.
"Wa'alaikumsalam, yan ukun mummy kun dawo"
wata farar mata mai zubin manyan matan india ta faɗa. kamaninta daya da FANNAH, MAYAH, FAHAD da kuma NU'AIM saɓanin RUKHSHANAH da fatarta ke da dan duhu ta ban banta da tasu.
Faɗawa Rukhshanah tayi jikin matarda ke zaune kamar zatayi kuka tace "mummy wallahi babu wani cigaba".
"Subhanallah, duk suka faɗa harda ya-fahad da yake shigowa parlourn. cak ya tsaya da tafiyarsa yace
"mum aje da ita US kawai dan Allah wannan wahalar tayi yawa ki duba kiga fa tun ranar Lahadi har yau laraba bata yin wata isashiyar magana data fara magana daya, biyu shikenan. Zata iya kai 3-4h bata ƙara faɗin komai ba"
Matar cikin tausayawa tace "wallahi kuwa nima shi nake dubawa haka tasha wahala a idanun nan nata, da taimakon Allah da taimakon Dr. Kanal raghib akasamu ganinta ya dawo a cikin glasses ɗin nan.
"Mum to kho Indian za'a kuma kaita"
"Hmmm, Fahad kenan duka duka wannan shine wata na biyu fa da mukayi a hospital ɗin nan, har asibitoci nawa za'a kaita kenan Fahad" matar ta faɗa fuskarta fallll da damuwa.
"Mummy bawai maganar asibiti nawa za'a kaita bane, duk inda mukaje mukaga nasara nan zamu tsaya. Bawai muzauna tayita shan magani ba wani cigaba ba. Ki duba kiga yanda muka sha yawo da ita kan matsalar idanun nan a nan gida Nigeria, bawata nasara. Amma kiga muna fita da ita ko sati ɗaya bamu cikaba ta fara ganin komai da taimakon wannan glasses ɗin"
"To amma ai shi Dr. Kanal raghib ba likitan qwaqwalwa bane, iya idanune nasa taya zamuje masa da zancen nan"
Murmushi mai ma'anoni Fahad yayi kafin yace
"mum shifa Dr kanal raghib haifaffen India ne BHOPAL yake. Yanzu idan shine yazo yace maki kafff faɗin jaharnan waye kwararren likitan fata wazaki faɗa masa" fahad ya faɗa cikin sigar tambaya
"Dr. Ilyass jiƙamahi" mummy ta faɗa a taƙaice.
Murmushi mai sauti yayi kana yace" mummy ki duba fa kema ba likita face amma sbd Dr jiƙamahi yayi suna har kika sanshi haka, kuma ke ba haifaffiyar ƴar Nigeria bace. To inaga wanda aka haifa a ciki"
Shiru mummy tayi tana jiran ƙarin Bayani.
Ɗan gyaran murya fahad yayi sannan yace "mummy likitoci sunsan junansu sosai, ba wai likita kaɗai ba ma mafi yawan