Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
take tsaye ba.
"Kizo ki zauna idan na kammala sai mu wuce kinji, kiyi haƙuri sayyid yace baiji kin gaida shiba"
"Uhmm--hmmm bakomai" cewar khulud tana ƙaƙaro murmushin.
"Zauna" reemah ta maimaita mata.
"Okay" khulud ta faɗa tare da zagayawa inda ɗayan kujerar da ta rage wurin take, kuma kuma kusa da ita ne id ke zaune.
Yana ganinta ta nufo wurin ya hau haɗa kayansa dake baje kan plastic table ɗin da ke tsakanin kujerun biyu zai tashi.
"Idrak me kake shirin yi, Saboda ka ganni ne zaka tashi"
"Mtswww" yayi tsaki sannan yaci gaba da abunda yake.
"Id Yakamata kagane adadin ƙaunar da nake yimaka a raina, dan Allah kaji tausayina wallahi ina sonka, duk abunda ya faru a can baya tsausayine kuma ƙaddara ce wacce Allah ya riga ya tsara saita faru, kuma Wannan ya riga ya wuce dan Allah kayi haƙuri ka soni idrak wallahi ina sonka da ƙaunarka so na tsakani da Allah, kuma ba ranar dainawa muddin ina numfashi a wannan duniyar" ta faɗa tana haɗe hannayenta wuri ɗaya idanun ta duk sunyi jajir ga kuma hawaye kwance a cikinsu.
Bai kalleta ba kuma bai cemata komai ba, yabi ta gabanta zai wuce.
Gefen rigarsa ta riƙe tare da durkusawa gabansa "dan girman Allah id kaymin Magana dan Allah Wallahi idan bansamu soyayyarka ba rayuwata na cikin haɗari ka taimakamin wallahi ina sonka"
Cikin zallar ɓacin rai ya fizge hannunta daga riƙon da tayi masa yayi gaba zuwa wurin da su Sayyid ke zaune.
Duk abun nan da suke Sayyid da reemah basu sani ba domin sun juya musu bayane.
Miƙewa tayi tana share hawaye ta ɗauki kayan da ta siyomasa ta bishi har inda yake, yana magana da sayyid da alama dai yana gayamasa ne gida yakeso ya tafi.
"Ga wannan dan Allah karkace bazaka karɓa ba" khulud ta faɗa zuciyarta na bugawa bataso yaƙi karɓa duk da tasan zai yi wahala ya karɓi kayan.
Miƙewa Sayyid yayi da sauri gaban kayan ya ɗauki ledojin biyu ya zubarda su a ƙasa ya fara ball dasu ko wanne yana yin gefensa kwalin waya sabuwa kirar Apple 15 yake ball dashi har gaban ta.
Cikin kasaita irin ta jinin sarauta ya fara magana"Ya faɗa miki yana buƙatar kayanki ne, ko angayamiki shi matsiyaci ne irinka, this is the first and last, wallahi idan kika ƙara siyo wani abu kika kawo masa saina wulaƙantaki daga ke har kayanda kika zo dasu"
Har ya tafi ya dawo kamar mai raɗa yaje kusa da kunnenta"fool"
Ya faɗa yana yimata murmushin tsana.
KhUlud da ta rasa abunda zatayi sai kawai ta durkushe ƙasa tare da riƙe kanta ta fashe da matsanancin kuka.
Cikin wani irin ɓacin rai reemah tazo gaban sayyid "sayyid me ka aikata haka, me khulud tayi muku da ta cancanci haka daga gareku kalla! Kalla kaga yanda kuka maida ita, idrak kalla kaga yanda tunanin ka ya sauya mata kamanni, idan bakwa buƙatar kyautar da tayi muke it's fyn ku mayar mata da abunta a mutunce kamar yanda ta yi muku, duk abun nan da ka gani a nan da kuɗi aka siyeshi. Wallahi tallahi sayyid kaban mamaki ban taɓa zaton haka daga gareka ba ko a wajen wata ba khulud ba balle ita kanta khulud ƙawata, dan Allah bakaji kunyar idanuna ba ? kome ta maka yakamata taci albarkacina a wurinka sayyid, alhmdullillah, alhmdullillah Sayyid na godewa Allah daya fara bayyana min yanda halayenka suke tun a yanzu.
wanda yayi wa mace haka a gaban wacce yakeda burin aura to karta fitarda tsammanin itama wata rana zai iya yimata haka ko a gaban kowa, shikenan mungode" ta faɗa cikin wani yanayi da sayyid da idrak har ma ita kanta khulud basusan reemah nada irin wannan zuciya ba domin idanunta har rufewa suke saboda tsananin masifa.
Sayyid kam kamar dasashi akayi wurin sai bin reemah yake da kallo domin yama manta da tana wurin kuma bai taɓa ganinta a yanayin nan ba wannan abun ne ya kara bashi tsoro da mamaki.
Inda khulud ke durkushe taje ta tada ita ta riƙe hannunta ta kaita har inda tayi parking motar ta ta buɗe mata mota "ki zauna ki jirani naje na kwaso kayanda suka watsar kinji kiyi haƙuri kuma dan Allah".
KhUlud bata ce komai ba ta kifa kanta kan steering motar tana hawaye a hankali, ita duk wannan abun da sayyid yayi mata bata ji soyayyar id ta fita daga zuciyar ta ba saima abunda ya ƙaru.
Reemah kuma tana zuwa wurin bata cemusu komai ba ta fara haɗa kayan da suka watsar "sayyid karka taɓa kayan nan idan ba so kake na nuna maka asalin kalata ba wallahi" reemah ta faɗa lokacin da Sayyid ke ƙoƙarin tayata haɗa kayan.
Bayan ta gama haɗa kayan zata tafi sayyid ya tareta ta raɓa gefensa ta wuce, da sauri idrak yasha gabanta "karkace min komai id wallahi kunban mamaki, da kanku kuke wulaƙanta mutane wannan halin ne fa yasa kuka ɗauki karan tsana kuka ɗorawa ƙawayena ashe duk halin ku ɗaya dasu kaicona, kaicona danayi tunanin ku daban ne da kowa musamman kai*" ta fada tana nuna Sayyid.
"Dan Allah reemah ki tsaya ki saurareni, banyi tunanin haka sayyid zaiyi ba, da farko ya birgeni da yayi mata haka koba komai zataji yanda akeji idan idan tayiwa wani ko wata haka, harga Allah abun nan da yayi mata yamin daɗi, saidai abunda baimin daɗi ba da wannan tunkiyar yarinya ta kasance daga cikin ƙawayenki, reemah gaba ɗaya ƙawayenki basu dace dake ba, amma kuyi hakuri mun tuba" cewar id.
"Hmmm" kawai ta iya yie kafin tayi tafiyar ta.
Suna gani,
motar Sayyid ta fita makarantar, har ta fita daga Rooney khulud na kallon motar. Ji take kamar ita da id ɗinta ne a ciki zasuje gida bayan sunyi aure.
"KhUlud zaki iya zuwa gida ko na kira drivern gidanmu yazo ya kaiki".
Murmushi mai ciwo khulud tayi tana kallon reemah tace"zan iya karki damu kinji kije gida kar a nemeki".
"KhUlud dan Allah na roƙeki kicire soyayyar id a zuciyarki, wallahi id baya sonki domin duk wanda yakesonka bazai jure ganin ana wulakantaka ba"
"Reemah da akwai yanda zanyi na cire zuciya ta gaba ɗaya, dana cireta ko zan huta na sami bacci cikin kwanciyar hankali kamar yanda kowa yake yi, fitar da soyayyar id a zuciyata babban abune wanda banmasan ta inda zan fara ba amma zan gwada na gani ko zan iya duk da nasan ba lallai ba"
"Shikenan Allah ya sauwaqe kinji, kuma kiyi haƙuri"
"Ameen Ya rabbil alameen, kuma don Allah abunda nake roƙonki kada ki kama sayyid da laifi domin bashi bane mai laifi nice babbar mai laifi da halayena basu kasance haka ba da baza'a min ba.
dama hausawa sukace alhaki kuikuyo mai shi yake bi, kuma abunda ka shuka shi zaka girba, kije gida reemah Nagode".
Sallama sukayi reemah bata gushe ba tana bata haƙuri itama tana bawa reemah haƙuri kan abunda yafaru tsakanin ta da Sayyid.
Anan reemah ta fita daga motar ta khulud ta nufi inda ta ajiye tata, itakuma KhUlud ta fara tuki.
Tana cikin tafiya ne ta hango motar sayyid tayi parking gaban wani babban mall.
Wuri ta samu inda take hangosu sosai daga inda take, saidai su basa ganinta kamar yanda take ganinsu. Fitowa tayi ta jingina da motarta tana fata a ranta Allah ya bata Sa'ar abunda take kuɗuri a ranta yanzu.
Wayar ta ta kashe gaba ɗaya domin kar a dameta da kira daga gida tanaso sai tayi solution ɗin matsalarda ke gabanta kafin ta koma gida.
Tana jinginen ne ta ga fitowar su da sauri tayi locking motar ta ta tare taxi.
"Hajiya ina zamuje"
"Dan Allah so nake ka bi waccan motar, kuma cikin dubara nakeso kayi yanda bazasu gane su muke bi ba"
"Bakida matsala hajiya shigo muje"
Da hanzarin ta shiga motar drivern taxi ɗin ya fara bibiyar motarsu sayyid cikin kwarewa da ɓoyon sahu, sosai sukayi tafiya, da zarar direban ya fahimci hanyarda zasubi sai yayi short cut ya taresu a gaba, haka sukayi har suka iso unguwar ta su idrak.
Sosai khulud tayi mamakin ganin wai mutane ke rayuwa a wannan wurin, ita harga Allah idan da motarta taje bazata iya shiga wannan unguwar ba domin a ganin ido bazace akwai hanyar da mota zata bi ta wuce ba.
Mamaki bai gama tafiya da imanin ta ba sai da taga inda motar sayyid tayi parking, bakin wani ɗan ƙaramin gidane wanda bulon da aka ginin dashi ya gaji da duniya har wani baki-baki ginar gidan tayi, gata guntuwa sosai wani wuri ne da tsawo sauran duk ya faɗin saida aka saka laka aka tada ginin, kofar gidan sai dai aka saka wani tsohon turmi aka tangaleta dan karta faɗi.
"Allah yasa ba gidan bane gidansu id"
Ganin sa ya fito waje ya saka kansa a motar kamar yana magana ne da Sayyid yasa ta ƙara gasgata nanne gidansu, tana kallonsu har suka gama maganar ya juya ya shiga gidan, shi kuma sayyid ya tada motar ya bar unguwar.
Nannauyan ajiyar zuciya ta saki ta kalli drivern taxi ɗin tace "menene sunan arear nan?"
"Tsohuwar bariki" Drivern ya bata amsa.
"Ikon Allah, amma Ni bantaɓa sanin unguwar nan ba"
"Aikuwa unguwar nan a sane take Hajiya, kuma wasu mutanen sunfi sanin ta da suna layin ƴan haya, domin kaf faɗin unguwar nan ba wanda yakeda gidan kansa duk na hayane".
"Kana nufin har wancan gidan" ta faɗa tana nuna masa gidan da taga id ya shiga.
"Ehh sosai hajiya ina yimiki maganar layin nan ne gaba ɗayansa"
"Kana nufin gidajen da ke layin nan na haya ne kuma mutanen da ke ciki suna biyan haya".
"To idan basu biya ba ya zasuyi, ai dolensune su biya, da babu ai gwara ba daɗi".
"Haka ne to muje ka mayardani inda ka ɗaukoni"
"Okay hajiya" cewar drivern yana tayarda taxi ɗinsa.
Saidai ya kaita har gaban mall ɗinda ya ɗauke ta sannan yayi packing ta fita, kuɗi ta ciro wanda bata san ma adadin suba ta miƙawa Drivern taxi ɗin.
baki buɗe yabi kuɗin da ke hannusa da kallo wanda ko a cikin sati ɗaya bazai sami irinsu ba "hajiya na wah ne gaba ɗaya?" Ya faɗa yana washe baki.
Bata bi ta kanshi ba ta buɗe motarta ta shiga sai gida.
Babban abun da ya ɗaga mata hankali shine hango cincirindon mutane da tayi a ƙofar gidansu harda police da kuma dss, "innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta furta a tsorace zuciyarta na matsanancin bugawa "me yake faruwa a gidan ya rabbi kasa naji alƙairi" ta faɗi maganar a fili dai-dai lokacin da motar ta ta Parker bakin gate ɗin gidan.
da gudu meenal da Aneesa sukayo kanta, basu jira komai ba suka rungumeta meenal ta saki kuka, nan zuciyar khulud ta daɗa tsinke wa tuni ruwan hawaye sun cika mata idanu itama tana tsoron jin abunda ke faruwar a zuciyarta.
Kallonta takai ga kofar gidansu inda taga mutane suna fitowa suna nufota, papu tagani ta sauri kamar ya kifa har tuntuɓe yayi saboda tsananin tashin hankali, kana gani fuskar sa zaka san akwai babbar matsala a ransa.
"La-ila-ha illa antah subhanakah inni kuntu minaz-zalumin" ta kuma maimaita wa a Zuciyar ta domin ganin papu yasaka ta manta da tambayar da takeson yiwa su Aneesa, da sauri ta fizge kanta daga garesu ta isa ga papu cikin tashin hankali tace "papu meya faru a gidan nan"
"KhUlud ina kika shiga, alhmdullillah Allah" papu ya faɗa yana lumshe idanu, ya kuma maimaita mata tambayar da yayi mata"ina kika fito?"
"Unguwar tsohuwar bariki layin ƴan haya"
"KhUlud yaushe kika fara min karya ki gayamin abunda ke faruwa"
"Wallahi pa can naje, wani abu na dubo na dawo kuma ina sane na kashe wayata dan kar na tada muku hankali"
"Kashe wayar da kikayi shine zai hana hankalin namu tashi, mum ɗinki da turab tun ɗazu suna abuja domin bada jigiyarki, leeya da haji da badar ma driver ya kaisu gidan television dana Radio, yanzu haka an rufe school ɗin ku sai an gama bincike, haka da kikayi kin kyauta mutum nawa kika tadawa hankali yau ɗin nan KhUlud, karfe biyar na yamma fa keda kika fita gida tun karfe takwas na safe ina hankali zai kwanta tunda baki kira kin sanarba, kindaisan duk inda zakije ba hanaki za'a yi ba dan Allah karki ƙara irin haka kinji"
"In sha Allah pa bazan kuma yin haka ba nayi kuskure na tuba, kuyi haƙuri kuma ku yafemin da haƙƙin ku dana ɗauka"
" ba komai Allah ya ƙara tsarewa, kuma a kiyaye. Amma kamar naga idanunki sun kumbura kuka kikayi?"
"Ah ah pah Nima haka kawai nagani bansan me yake faruwa ba ina kyautata zaton ciwon ido ne keson kamani"
"Subhanallah, to muje gida idan kinci abinci kin yi wanka sai muje asibiti a duba idanun"
"Okay pa muje" khulud ta faɗa tana tafiya.
"Yallaɓae idan kun gama tattaunawa da ita munaso muyi mata wasu tambayoyi" police ɗinda ke tsaye kusa da wurin suka faɗa.
"Ohh sorry, inspector fargab raji, kuyi haƙuri harna sha'afa inaso nazo nayi muku bayani, yarinya dai gata can tana tafiya Allah ya dawo mana da ita duk da ba ɓata tayi ba", papu ya faɗa yana nunawa inspector fargab raji khulud dake tafiya. Yaci gaba da faɗin "amma mu a zaton mu ta ɓata ne tunda anje school bata nan, ankira wayanta kashe kuma an tambayi abokan ta gaba ɗaya sunce sun barta School, ɗayan kuma tace a gabanta ta fita da motar ta, kaga kho dole ne hankalinmu ya tashi tunda lokacin dawowarta gida yayi har ya wuce amma bata dawo ba.
Ashe ta biya wata unguwar ne daban kuma bata sanarwa kowa ba, idan kunje kuyiwa inspector Agu Clement bayanin komai"
"Okay ba matsala yallaɓae za'a gaya masa in Allah yaso, Allah ya ƙara tsare gaba"
"Ameeen, Ameeen mungode sosai" papu ya faɗa yana ciro kuɗi aljihunsa, no yallaɓae, sir Agu yace kar mu sake mu karɓi ko kwandala taka, mu mun tafi"
godia sosai yayi musu sannan ya rakasu har inda sukayi packin mota daga nan ya dawo gida, ya kira kowa ya sanar masa yanda akayi.
Dama su mum kam suna hanya har sunje an fara aiki.
Hakama su haji har sun bada nasu suma.
Bayan shigarta gida ba jimawa su haji suka dawo sunyi farin cikin ganin ta da ganin tana lafiya sosai, sai a lokacin aka fara ƙoƙarin shirya abincin dare domin basa cikin kwanciyar hankali da tuni an kammala komai, ana kiran sallar magariba ne su mum da turab suka ƙara so sai sam barka ake.
Daren ranar khulud batayi bacci ba saida ta labartamusu abunda ya faru tsakanin ta da Sayyid harshi kansa id da yanda suka yimata wulaƙanci.
Airah kamar zuciyar ta zata fashe dan haushi da bakin cikin kyalesu da khulud tayi sukayimata haka, da yawansu sunga dacewar abunda khulud tayi domin ta hakane id zai gane tana danasani da abunda tayi musu.
Duk wannan bai saka Airah taji a ranta ya kamata khulud ta basu dama suyi mata abunda ransu keso ba "kenan da babu reemah dukanki zasuyi"
"Badai duka ba Airah ai ko zan shanye komai bazan taɓa bari id ko Sayyid yakai hannusa jikina da sunan duka ba, kuma ni duk abun nan da sukayi min gaba ɗayansu koda dama aka bani banaji zan iya mayar musu da martani, shiyasa ma na ƙyalesu sukamin abunda sukaga dama mai so baya fushi".
Taɓe baki Airah tayi tace "Allah dai ya kiyayemu da faɗawa kaddararren so irin naki ɗin nan"
"Ameen" suka amsa gaba ɗayansu daga nan kowa ya nufi makwancinsa.
**********
Washe gari kuwa tun karfe tara na safe zafaran ya kira wayar turab ya sanar masa da zuwansa, kuma ya gayamasa idan yazo bazai tafi ba har sai an gama bikin fahad da zohal. Shima turab ya kuɗuri niyar barin gidan su koma can kaduna inda gidan Fahad ɗin yake. Domin bayason hayaniyar jama'a kuma yasan danginsu na kusa dole zasuzo gidansu tun a yanzu ma mutane sun fara yawa gidan koba komai ga ƙannensa nan su meenal su kusan biyar ko shida, shima kansa zafaran ɗin bazaiji daɗin zama gidan ba idan da mutane sosai domin shi kwata-kwata ma baya son zama cikin mutane saboda bai saba da hakan ba yana dubin hakan babbar takura.
Ɗan murmushin turab yayi wanda ya bayyanar da fararen haƙoransa lokacin da ya tuna da maganar da zafaran yayi "yawwa man-turab albishirinka"
"Goro" turab ya amsa masa da son jin abunda zaice, domin harga Allah shi abunda ya faɗo masa a rai daidai wannan lokacin shine zafaran ya haɗu da lewa ko yaji labarin inda take.
"Fari ko ja?" Cewar Zafaran.
"Fari sol mutumina, me ya faru gayamin naji"
"Da yunwa zanzo gidanku yau"
"Ban,,,,,,,gane ba me hakan ke nufi" turab yayi Maganar a rarrabe.
"Ina nufin tun taga yanzu har nazo suleja bazan ci komai ba har sai nazo gidanku, dan Allah ina so ka saka wannan yarinyar da ta taɓa yimana abinci ta sake yi magana ko yanzu ina missing ɗin girkinta".
"Wace yarinya?"
"Wannan yarinyar daka ce ƴar ƙawar mum ce mai rasuwa, wacce ta taɓa yimana girkin nan na igbo kwanakin baya"
"Uhmm--hmmm, okay nagane wane kalar abincin kake so?"
"Egwusi and okazi soup, sai kuma oha crayfish soup, sannan da yam and ginger juice ba mai kauri ba sannan kar a saka yajiiii yawa"
"Mutumina duk kai kaɗai zaka ci wannan"
"Nida kai da ango dai"
"Wah, Allah ya kiyaye Ni bazan iya cin jagwalgwalen abincin nan naku ba ya rikitamin ciki bara na kirata na gayamata ta haɗa maka kafin ka ƙaraso"
"Godiya nake man turab sai na karaso"
Daga haka sukayi sallama ya katse wayar ya zauna, gaban television duk da ba ita yake kallo ba tunanin da yake daban, shine tunanin maganar da sukayi da zafaran ya faɗo masa arai har ta sakashi yin murmushi.
Number mum yakira bugu ɗaya ta ɗauka "Assalamu alaikum"
"Wa'alaikasalam"