Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
mutum haka da ciwo ne"
Meenal ta kalli mum cikin damuwa da halin da leeya ke ciki tace "Wallahi mum, mun aike Airah taje ta sanar miki amma ba'a sameki a part ɗinki ba, sai dai tasha magani yanzun nan.................✍🏽
BAYAN WUYA........
By RUMANA M DIGGI
EP.35
_______________mum ta kalli leeya cikin kulawa tace" ko muje asibiti?"
"Ah ah mum kinsan banason zuwa asibiti dan Allah wallahi yanzu ma nasha magani kho meenal, ke kika bani maganin da hannunki nasha"
Mum ganin hankalin leeya ya tashi yasa tace mata"shikenan kiyi kwanciyar ki kinji ba inda zamuje, amma da sharaɗin idan baki walwale daga zazzaɓin nan ba gobe ba abunda zai hanaki zuwa hospital"
"Tau mum, in sha Allah zanje idan bansamu sauqi ba"
Daga haka mum bata ƙara cewa leeya komai ba, ita kuma tayi kwanciyar ta har bacci ya ɗauketa.
A ɓangaren turab kuma tunda ya shiga ɗakin sa ya zube kan gado ko wani dogon motsi bayayi, domin tun da aka faɗa masa maganar kansa ke bala'in ciwo, hannusa ya saka ya fara lalubo wayarsa, ɗaga idanunsa yayi da kyar waɗan da suka rine suka jajir saboda azaba, number fahad ya lalubo tare da danna masa kira ringing ɗaya ɗaga.
Banji abunda ya faɗa daga cikin wayar ba saidai shi turab ya buɗi baki da kyar yace "ka fasa kenan", shikenan goben ku shigo kawai sai muyi magana"
Daga haka bai jira cewar fahad ba ya kashe wayar.
Ya jima kwance a wurin ko motsin kirki baya yi, sai kamar Bayan mintuna arba'in tsakani ya miƙe hannun sa dafe da kansa yana tafiya a hankali yana cije gefen lips ɗinsa na ƙasa tare da runtse idanun sa duk taku ɗaya da zaiyi.
Har gaban akwatin da yake saka magunguna ya isa tare da buɗe a akwatin yafito da wani magani nannade a farar yana, sannan ya kuma ɗauko wani daban a cikin kwalli ya ɓalla ɗaya, daga nan kuma ya ɗauko wani syrup yasha marufi ɗaya, tashi yayi da sauran a hannunsa ya isa har gaban fridge ya buɗe Sannan ya ɗakko robar ruwa ya haɗiye magungunan da ke hannunsa.
Komawa yayi kan bed ya kishin giɗa, har kuma lokacin kansa bai sassauta ba.
★
Washe gari tunda asuba meenal ta farka daga bacci, ganin kamar lokacin sallah ya kusa yasa bata maida kwanciyar ba,
Waya ta janyo tare da kunna ɗan hasken screen ɗin wayar, ganin saura mintuna goma sha ɗaya akira sallah yasa tayi niyyar tada su khulud suyi sallah,
side lamp ta kunna daga nan kuma ta kai hannu kan wuyan leeya dake kwance ta taɓa,
Sosai tayi mamaki jin jikin nata raɗau kamar abunda aka zubawa ruwan zafi "Allah sarki leeya har yanzu ana ta fama da ciwo Allah ya baki lapiya"
Airah kuwa jin ana magana ne yasakata buɗe idanunta a hankali domin batada nauyin bacci ko kaɗan "meenal lafiya!?"
Ta faɗa a ɗan tsorace ganin leeya kwance ita kuma meenal ta sakata a gaba tana haske ta da touch.
"Da dama dai Airah"
Da sauri Airah ta sakko kan gado ta nufo gadonda su leeya suke tace;
"meenal zazzaɓin ne har yanzu"
"Eh wallahi Airah, ki taɓa jikinta kiji yanda yakeda zafi sosai"
Hannu Airah takai tare da taɓa wuyanta "Ah'uzubillah, meenal kinji yanda jikinta yayi zafi, gaskiya meenal zanje na gayawa mum tazo Wallahi tsoro nake ji kar ƴar mutane ta mutu a hannun mu"
"Bazamu gayawa mum a Yanzu ba, mu bari idan safiya ta waye sosai sai muje mu sanar musu, kuma nasan mum zatazo part ɗin nan domin ta dubamu idan mun samu Sallar asubu, ko batazo dan haka ba zatazo dan tabar mara lafiya jiya, saboda haka muyi hakuri tazo kawai, daga nan ma sai suje asibiti gaba ɗaya, amma yanzu idan muka gayamata zamu tada mata hankali ne kawai, kuma zatace sai anje asibiti kuma koda anje asibitin kinsani ba likitoci saidai masu shara"
"Haka ne meenal, amma haka zamu zuba mata ido har sai mum tazo ai abun da tausayi wallahi"
"Yanzu darena Airah da kinje parlourn ƙasa kin ɗauko min maganin rage zafin jiki, dana sani jiya da nah ɗauko sachet ɗin gaba ɗaya"
"Bara naje na dauko kawai meenal, bani fitilar wayanki wayana ba chaji"
"Ah ah karki fita yanzu kinji Airah, kije toilet ki jiƙa towel da ruwa masu sanyi sosai ki kawomin saina rage mata zafin jiki da shi"
"Okay tau jiran mintuna biyu gani nan zuwa" Airah ta faɗa ta ficewa ɗakin da sauri.
Haka kuwa akayi da taimakon towel ɗin zafin jikinta ya ragu, kuma ba abunda ya rage na game da ciwon saidai ma abunda yayi gaba domin jiya Bata yin amai, amma daga wayewar gari zuwa yanzu tayi amai yakai sau huɗu.
KhUlud na zaune a gefen ta, ita kuma tana daga kwance. Sai meenal, badar, Airah da mayah duk suna zaune kan gadon, Aneesa kuma tana daga gefen damanta ta riƙe hannunta cikin tausayi, "Ki tashi muje sashen haji idan zaki iya ta aiko tace kizo kiyi breakfast sannan kuje asibiti"
Miƙewa tayi da kyar suka taimaka mata har ta tashi gaba ɗaya, miƙewar ta keda wuya amai kuwa ya bijiromata da gudu ta isa toilet ta nufi sink,
"Yau ta wahala wallahi Ni har tausayi ma take bani"
"Gaskiya kam ko wannan aman wahala ne balle kuma ga zazzaɓi, Allah dai ya bata lafiya"
"Ameen" khulud ta faɗa daidai lokacin da leeya ke fitowa daga toilet.
Hannunta meenal ta rike har sashen haji, da kyar leeya ta iya ƙarasawa da kanta duk da tana tsayawa ta hutawa, da yake ba wata tazara tsakanin sashensu dana haji, suna sashen meenal ta wuce bedroom ɗin haji, ita kuwa leeya ta kwanta kan sopa duk da ba daɗin kwanciyar tayi ba amma zafin ciwon ya sakata kwanciya bata damu da rashin jin dadin ba.
Haji ta fito daga bedroom tare da meenal har suka ƙara so inda leeya ke kwance.
"Leeyanatu ashe bakyajin daɗi mu bamu sani ba"
"Haji ina kwana"
"Lafiya lau leeyanatu ya jikinki"
"Naji sauƙi haji zazzaɓi ne kawai"
"Allah sarki Tau Allah ya baki lafiya, Bara na zubomiki koko mai zafi danayi yanzu sai kisha, kafin na kira Abu turab yakaiki asibiti"
Gabanta ne ya yanke ya faɗi sakamakon sunan turab da taji haji ta furta "Nagode sosai" ta faɗa da dusashshiyar murya.
Koko mai zafi haji ta ɗebo ta har gabanta ta kawo mata, ita kuma meenal tunda ta rako leeya ta fice daga sashen domin tayi aikace aikacen da ya kamata ace tayi.
Haji kuma ta fita zuwa sashen turab domin gayamasa, tana fita sukaci karo da papu shi kuma yazo ya gaida ta da safiya
"Haji ina za'aje haka"
"Wallahi zanje sashen Abu ne na gayamasa yazo yakai leeyanatu asibiti aduba ta"
"Leeya batada lafiya ne"
"Eh wallahi tun jiya akace batada lafiya ta kwana tanayin amai"
"Subhanallah, amma da ciwo a jikin mutum tun jiya ba'a faɗi ba, ai da ankira ko dr.jif ne yazo ya dubata"
"Wallahi Nima bansaniba sai daren jiya nakejin fanaya na sanardani"
"To Allah ya sauwaqe"
"Ameen ya rabbil ibaddd"
Haji ta faɗa daidai lokacin da suka ƙara so part ɗin turab.
zaune yake kan darduma ya kammala Sallar walha yana tazbihi yaji ƙarar kwankwasa kofa, miƙewa yayi yaje har gaban ƙofar ɗakin ya buɗe ba tare da yace komai ba, ganin haji harda papu yasa ya faɗaɗa fuskar sa da murmushi "haji yau ziyara aka kawomin kenan, pa barka da safiya" ya faɗa yana ɗan rusnawa a gabansu.
Shafa kansa papu yayi shima fuskar sa ɗauke da murmushi yace"son barka dai, ka tashi lafiya"
"Eh pa lafiya ƙalau nake stress kaɗai ke damuna"
"Uhmm--hmmm tau ayita hakuri kaji, Allah yayi maka albarka ya kuma baka ladar biyayya"
"Ameen pa" turab ya faɗa har haji ma ta amsa da faɗin ameeen.
"Ku shigo daga ciki"
"Ba shigowa zamuyi ba nabar mara lafiya a sashena kuma ba kowa a tare da ita"
"Subhanallah, waye ba lafiya kuma"
"Leeyanatu" haji ta faɗa.
Wani abu yaji ya tsargamasa tun daga tsakiyar kansa har tafin ƙafarsa"Allah ya bata lafiya"
"Ameeen, kazo muje ka fara sauke nauyin ta dake kanka"
"Muje nayi mata me haji" ya faɗa fuskar nan tasa babu yabo ba fallasa.
"Ka kaita asibiti"
"Haji dr.jif fa"
"Baya gari"
"Okay gani nan tafe idan nayi wanka"
"Turab karka jima kaji, kasan ciwo ba daɗi tun jiya take fama wallahi"
"In sha Allah bazan jima na papu zanyi ƙoƙari naga na kammala komai yanzu"
"Yauwa Allah yayi albarka"
"Ameeen pa"
Komawa yayi cikin ɗakinsa haji da papu kuma suka koma sashen mum.
Yana shiga ɗakin nasa ya mayarda ƙofa ya rufe, wayansa ya ɗakko ya ɗan dudduba kafin ya ajiyeta a gefe ya shiga toilet.
Ba jimawa yayi wanka ya fito, a nutse ya yi shirinsa cikin plain cotton yard, violet Ash color.
Kalar yadin yayi masa kyau sosai ga dinkin da ya zauna tsaf dashi a jikinsa.
Farin gilashin da ya ƙarawa fuskar sa cika da Haiba ya ɗakko ya saka sannan ya saka hularsa plat cap dark ash ya zura takalmansa ya fita ɗakin.
A can ɓangaren leeya kuma,
tana kwance har yanzu kamar yanda haji ta barta, bata sake dawowa ɗakin ba domin a tunanin ta turab ɗin yazo dan bataga dauɗa a jikinsa ba balle tayi tunanin ko sai ya ƙara yin wanka.
Leeya kwance a kan Centre carpet ɗin tsakar parlorn duk ta jeme da ita, ba abunda yake tada ita daga kwancen sai idan taji amai na batun kwace mata.
Ƙamshin turarensa ne ya bugi hancinta yayinda yake shigowa parlourn, sallama yayi da tunanin ko haji na parlourn.
Daidai lokacin da ya shigo tsakiyar parlourn, leeya ta zabura da ƙarfi ta dafe saitin bakin ta daga cikin niqab, da gudu ta biyo ta gabansa zata wuce take ya kara mata ƙafarsa tayi tuntuɓe da kafarsa har saida ta faɗi ƙasa. Ƙara miƙewa tayi da nufin ta tashi ya damƙo gashin kanta ta gabansa yana fuskantar ta kuma babu wata tazara sosai a tsakanin su, juya kanta tayi gefe still hannayenta na rufe da bakinta sai zare idanu take tana wani yunkuri tun daga ƙasan maƙoshi.
"Ke! Dan ubanki shine zaki ganni ki nemi guduwa harda wani toshe hanci da baki ga dodo ko, wai wace irin mai kunnen ƙashi ce ke? Ban faɗamiki karki ƙara yin irin haka idan kika ganni ba, shine zakije ki liƙewa mum da papu har haji kin asirce su da wadannan mayun idanun naki kika saka aka tauyeni ko, wai za'a haɗamu, Ni in aureki, hmmm, God forbid bazan taɓa haɗa inuwa dakeba leeyana, kuma kada ki saka ranki zan aureki domin hakan bazai taɓa faruwa" rufe bakinsa keda wuya yaji saukar amai da ya fito da karfi daga bakinta zuwa jikinsa.
Suman tsaye tayi ba abunda zaka gani a idanun ta face zallar tsoro da fargaba, tunani take kan maganganun da ya gama faɗa mata yanzu, me yake nufi da aure kuma, me asirin da ya faɗa yake nufi wai nayiwa mum, da papu da haji asiri da idanuna, idanuna kuma, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un bazamu taɓa zama inuwa ɗaya ba, ya-Turab duk ina kalaman nan naka suka dosa.
Tayi nisa a cikin tunanin da take domin ita bama aman data lalata masa jiki dashi ne damuwarta ba, sarƙaƙƙun maganganun da yayine keyita dawo mata arai haƙiƙa da zai bata dama da ta nemi ƙarin sani daga waɗannan maganganun nasa.
Saukar wani kafirtaccen bahagon mari ne da taji ya sauka a fuskar ta ya dawo da ita hankalinta "dan kinga an nuna ki a matsayin wacce zan aura bashi yake nuna cewa Ni sa'an ki bane wallahi idan baki shiga hankalin ki ba sai na nuna miki na wuce da saninki kuma wallahi rigarnan da kika ɓata sai kin gyarata.
Gata nan kije ki wanketa ki busarda ita da dryer sannan ki gugeta ki kawomin gani nan ina jiranki, kuma da hannu zaki wanketa banason wankin machine na baki mintuna goma sha biyar kije ki dawo idan kuma ba haka ba jikinki ne Zai gaya miki wallahi"
Turab saboda fitina irin tashi ya ma manta da batada lafiya, ya rufe ido rufff yana zabga mata rashin mutunci.
Duƙawa tayi da kyar ta dauki rigar da ya cillo mata, a hankali take iya ɗaga ƙafarta tana takawa har ta shiga toilet.
Tana shiga kuwa ta durkushe tare da sakin wani marayen kuka mai cike da ban tausayi, sai da tayi kukanta ta gaji ba mai rarrashi daga nan ta wanke fuskar ta ta koma laundry room ta wanke masa rigarsa da daddafe ta fita, tana fita ta sakata dryer ta bushe sannan ta goge masa ita kamar yanda ya buƙata.
Sosai tayi ƙoƙarin yin aikin domin ta galaɓaita.
Fitowa tayi da rigar a hannun ta tana dafa bango a hankali tana tafiya har ta shigo parlourn, babban abunda ya bata mamaki shine ganinsa a zaune har ya canjo kaya ya saka wasu kayan daban.
Har gabansa ta ƙara so tare da durkusawa har ƙasa, bata iya ɗaga kanta ta kallesa ba domin ita a ko yaushe tsoron sa da takeji yana ƙara ninkuwa a zuciyarta.
"Allah sarki ya jikin naki da sauƙi ko, kinga Ni harma na chanja kaya ki ajiye waɗannan a wurinki kinji, Allah dai ya baki lafiya ki tashi muje kar muyi letting muje da wuri a dubaki, sannu kho"
Turab ya faɗa da sassanyar muryarsa mai cike da kwarjini.
Mamaki ne ya kusa kasheta da mugun sauri ta ɗago kanta domin ta ganewa idonta shine ko kunnuwanta ne suka fara samun matsala.
Tana ɗago kanta kuwa sai taga mum da haji da sukayi turusss a bakin ƙofar shigowa ɗakin su a zatonsu duk soyayyarce haka.
"Ki tashi muje kinji, ko na ɗagaki ne"
Da sauri na zabura ganin da gaske yake "ki ajiya rigar har mu dawo mana, ke duk da bakida lafiya bazaki huta ba gaskiya sai naje na sami su mum a daina wahalarda ke wallahi zai iya yiwa ma gajiyace ke sakaki zazzaɓin nan" ya faɗa yana karɓar rigar daga hannunta cike da kulawa.
"Muje" ya faɗa yana juyawa, "lahhh, mum yaushe kuka shigo ne"
"Ina zakasan mun shigo kana ta shan soyayyarka"
"Wane soyayya kuma haji, ana soyayya ba lafiya"
"Ko ba'a yi kaikam gashi nan kanayi"
"Ah ah nikam ba wata soyayya wallahi"
"Dallah wuce ka bamu wuri mu bama son shashanci mara kunya kawai"
"Mum har da su kora lallai ma, idan bakya buƙata akwai masu bukata indai nine'' cewar turab Yana rufe fuskar sa da tafin hannun sa tare da fita parlorn da sauri yana dariya.
Sai yanzu na fahimci duk wannan abun da yayi saboda yaga su mum ne, Allah ne ya tausayamin ya kawo su mum domin da badan su ba bansan wane kalar hukunci zai yimin na sakamakon na haura lokacin da ya ɗiba kansa zan gama aikin da ya sakani.
Muna fita ɗakin ya ɗaure fuskarsa tamau kamar wanda aka aikowa da saƙon mutuwa, parking space ya nufa Ni kuma na tsaya gefe ina kallon sa kafin ya fito da motar.
Sake matsawa nayi kusa sosai domin har ya fito da ita fili, gaban motar na buɗe na shiga na zauna, wata Uwar tsawa ya dakamin "ke dan uwarki baki iya sallama bane da zaki shigo wuri ba sallama"
Baki na rawa nace masa"kayi hakuri dan Allah, wallahi na zata nayi sallama ne kayi hakuri wallahi zafin ciwo ne ya sakani"
"Sannu asibiti, ciwo kho? Nace sannu asibiti wallahi kika sake shigowa wuri idan ina nan baki yi sallama ba sai na saɓamiki wawuya kawai daƙiƙiya"
Kamar saukar tafasasshen ruwan zafi naji a zuciyata irin munanan kalaman da ya-Turab ke min.
Da sauri na ɗago kaina domin in gayamasa Ni ba ɗakikiya bace kuma Ni ba wawuya bace, amma sai na kasa mayar masa domin rashin kunya ba halina bane kuma bansaba yi akan kowa ba balle nayi akansa.
Mayarda kaina nayi ƙasa bance masa komai ba, sai hawayen dake faman zuba a idanuna kamar ana izosu da karfi.
Hannun sa ya saka ƙasan wuyanta tare da ɗago haɓarta ya saka tissue ya fara goge mata idanunta da hawaye ke zuba, a hankali yake goge mata idanunta kamar yana tsoron tissuen ya taɓa ta "kiyi hakuri kinji Yanzun nan zamu ƙarasa, ki daina kuka kinji Allah ya sauwaqe, ya baki lapiya"
Dosƙarewa tayi tana kallonsa saidai ba shi take kallo ba idanun ta ne kawai a kansa ko kaɗan bata iya kallonsa na seconds biyar domin yana yimata kwarjini sosai a duk lokacin da ta kalleshi sai tsoronsa ya ƙara nikuwa a cikin ranta.
Bai gushe ba har yanzu yana goge mata hawayen tare da kalamai masu kwantarda hankali.
Daga can wajen motar naji muryar papu da fara'a yana faɗin "turab har kun fito"
Shima ya kalli papu da alamun jin kunya yana ɓoye tissuen da ke hannunsa yace
"lahhh papu har ka fito, Ni bankula dakai na ma ashe har ka fito, ga ƴarku nan sai kuka take wai batason allura".
"Leeyana my daughter kiyi hakuri kinji, ciwo sai anyi haƙuri kinji.
Kuma ciwo ne yake shiga da sauri Lafiya a hankali take shiga saboda haka kiyi haƙuri kuje Allah ya kai lafiya kuma ya baki lapiya kinji".
"Ameen" ya Turab ya faɗa nikuma na ɗaga kaina kawai hawaye na ci gaba da fitowa a idanuna ina mamakin ya-Turab a ƴan mintunan nan tsakanin sa da mum, da haji da kuma papu.
To meyake nufi..........................✍🏻
BAYAN WUYA.....
By RUMANA M DIGGI
Ep.36
____________har muka fita gidan bai ko kalli inda nake ba balle yayi min magana, a haƙiƙanin gaskiya na kasa gane manufar ya-Turab kan wannan abun da yakeyi.
Cikin nutsuwa yake tuƙinsa yayinda ya saka karatun Alkur'ani mai girma a speakers ɗin motar, duk da zafin ciwon da nake ji bai hanani bin karatun a zuciyata ba.
Har muka ƙaraso asibitin bai cemin