Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
zahirin gaskiya na nuna rashin amincewata amma a badini naji farin ciki da sauyin da bantaba ji ba, wallahi leeyana da zaki sami lokaci ki tambayeni zan iya sanar dake dalilin da yasa na ke nuna miki tsana, kuma har ga Allah bazaki kamani da laifi ba idan kikaji dalilina, ki yarda dani leeya zan iya gayamiki komai idan kin bukata"
Cikin muryar kuka leeyana ta waiwayo gareshi tace da karfi "bana sonka turab, ba kuma zan taba sonka ba, meyasa bakada adalci a rayuwarka, Meyasa? Sai da kaga masoyina mai sona da gaskiya mai jin tausayina ya fito, shine kake so ka yaudareni da kalaman banzan ka, bazan taba yarda dakai ba kuma wallahi bazan aure ka ba turab, okene shi nakeso! Soyayyar sa ce kadai a zuciyata a halin yanzu"
"To amma meyasa kika yaudari zuciyata kikace kina sona, kin yi min alqawari da dama leeyana, meyasa kika kasa cika ko daya, wallahi banyi tunanin wannan daga gareki ba"
Wani irin kakkarfan numfashi ta saki a wahalce har idanunta na rufewa suna budewa, baki da hannunta dake nuna shi duk suna rawa ta furta "da....da...kai...!...nake chattinga.....kuma muke magana ta messages, dama kaine?... innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" leeya ta faɗa tare da durkushewa kasa tana gunjin kuka.
Wani abu zafaran yaji ya tokaremasa a makoshi, sai dai baiyi yunkurin aikata komai ba, sai meenal ce taje tana rarrashi, turab kuma bai kara fadar komai ba ya juya ya tafi, kamar wanda kwai ya fashewa a ciki haka zafaran yabi bayan turab shima fahad haka.
Haka leeya ta Karachi darenta babu komai a ciki sai kuka da tarin bakin ciki da nadama, bata taɓa sanin ta tsani turab ba sai ayau, ko sunansa bata so taji an ambata, kalmar sunansa ma idan ta tuna wani abu ne yake tokaremata makoshi.
Har akayi assalatu idanunta biyu bata runtsa ba sai faman zubarda hawaye take kamar wacce akayi wa babbar mutuwa, meenal ma tayi aikin ban hakuri da rarrashi har ta gaji amma leeya taki.
Bubbuga gadon leeya ta farayi da karfi meenal ta mike zaune;
"Leeya, lafiya dai kho"
"Lokacin sallah yayi" leeya ta fada da muryar da tayi kamada mai mura saboda tsananin azaba da muryar tasha.
"Leeya kina nufin har anyi asuba baki daina kukan nan ba, na gayamiki wallahi kuka ba ya maganin komai, dan Allah yanzu ki tashi muyi alwala kiyi sallah, sannan ki samu abinda kika karanta daga cikin Alkur'ani mai girma"
"Bazan iya komai ba a yanzu meenal"
"Don darajar fiyayyen halitta ki tashi kiyi abunda nace leeyana,. wallahi bana kaunar ganinki cikin damuwa"
"Zanyi meenal, kuma Nagode da kokarin da kikeyi akaina"
Mikewa su kayi gaba daya, leeya ta fara shiga toilet tayi wanka sannan ta dauro alwala ta fito ta tada sallah, tana kammalawa ta d'akko Kur'ani ta fara karantawa.
Sai misalin ƙarfe bakwai na safe ta rufe Kur'anin, hakan kuma yayi daidai da shigowar haji ta tada su suyi sallah.
"Haji barka da safiya, antashi lafiya ya tsufa kuma" meenal ta faɗa da sigar wasa.
"Lafiya qlau Amiiina, jiya baku shigo da wuri ba har nayi bacci ban san shigowar ku ba"
"Eh, wallahi mun dan tsaya waje ne kafin mu shigo nan"
"Ah to babu damuwa ba dai kun tashi lafiya ba"
"Lafiya qlau faa alhmdullillah"
Miƙewa leeya tayi ta ninke sallahyar tana gaida haji da kwana itama.
Bayan ta amsa mata tace, "koko nayi da kosai idan zakuci, kunsan ni ba wani son kayan turawa nake irin yanda kuke so ba, idan zakuci muje na saka muku idan kuma bazaku ci ba sai ku kira a kawo muku abin karyawar ku daga can gida"
"Zamuci mu sha kuma basai an kira gida ba muje kawai"
Fita sukayi gaba ɗaya suka koma parlon haji suka zauna, koko da kosan ta zubo musu suka fara ci, sallama sukaji an turo kofar parlon, fahad ne ya shigo bakinsa dauke da sallama.
Gefen haji ya zauna yana gaida ita mu kuma muka gaida shi,
"Fahad ya maganar auren?" Haji ta tambaya domin yau ne aka saka date din daura auren, sai dai rikitattun al'amurran da suka ɓullo ne ya saka ake ganin auren kila-wa kala.
"Aure yana nan in sha Allah haji, amma inaga sai idan an taahi sallar juma'a ne za'a daura"
"To Allah ya kaimu lokacin"
"Ameen" Fahad da meenal suka fada daidai lokacin da turab da zafaran suka shigo parlon.
Wani mugun faduwa naji gaba na yayi nan take naji na koshi da komai da nake ci, mikewa nayi zan tafi naji haji ta min magana.
"Leeyana ina zakije"
Jin wannan tambayar yasa na bata amsa ba tare dana shirya ba nace "haji ba nisa zanyi ba, ina so naje na gyara dakin da muka kwana ne"
"Da kin barshi ma idan na tashi zan gyara da kaina"
"Haji mu kuwa mene amfanin mu idan muka bari kina yin aiki da kanki, Bara naje na gyara kawai"
"Ohhh 'yar nan, Allah ya miki albarka ya baki 'ya'ya na gari masu albarka wanda zasu yi miki kema"
"Ameeen ya rabbil izzati haji" daga haka na wuce da sauri ban jira cewar kowa ba, sai da na kusa shigewa sai naji muryar haji tana cewa;
"Idan kin gama da wuri kizo mahaifinku naso yayi Magana da ku"
Ban kawo komai ba domin nasan maganar bazata wuce na gayamusu alaqata da Aleena, wanda rud'u da tashin hankalin da nake ciki sun hanani zumud'in ganin ta.
Ban jima ba na kammala aikin da nake,,,,, na fito, ban samesu a parlourn ba, haji ce zaune akan sopa sai kuma meenal a kasa tana yimata tausa, zama nayi mina na kama muka ci gaba da yimata, ba jimawa da zaman da nayi sai ga mutane sun shigo parlon, Papu, dad ƙarami, mum, mummy-neesah, Aleena, ya-Turab Fahad sai kuma zafaran da yayi shigowar karshe.
Tsoro ne ya kamani ganin har su ya-Turab a ciki, a raina ina fatar Allah ya sa ace an fasa bawa turab ni sai dai zafaran domin shi ne ya cancanci zama dani.
Bayan sun zauna aka gaisa da kowa papu ya kira sunana.
Amsa masa nayi ina kara yin kasa da kaina "leeyana kinsan meya tara mu anan"
Na amsa masa da faɗin "ah ah"
"To kaso chasa'in na taron nan saboda mu gana da ke ne, kuma kema mu baki damar sanin abunda ya shige miki duhu"
"Wacece wannan a wurinki" papu ya faɗa yana nuna Aleena.
"Kanwatace, mahaifi da mahaifiyar mu daya da ita"
"Masha Allah, amma ita labarin da ta bamu yanada banbanci da wanda kika bamu a farko, amma a karshe labarin ku ya zama daya da ita, amma ita har yanzu bata gaya mana asalin sunan iyayenku ba, kawai dai tace mana Abbi da Ammi"
"Eh hakane papu, na zabi boyemuku labarina ne kawai dan kar ya tsawaita kuma bana son tuna irin wuya da kuncin rayuwarda na shiga"
"Ai koda haka ba laifi tunda baki yi mana karya ba, kuma mun gode da haka wallahi kin cika har halak a shekarun da mukayi dake baki taɓa cutarda mu da komai ba"
"Ni ce da godiya papu, Nagode sosai Allah ya baku ladar kyautatawa Maraya"
"Ameen ya rabbi"
"Amma papu, inaso in san yanda Aleena ta tsira daga mugayen mutanen can, kuma ina so nasan inda mahaifiyar mu ta biyu take"
"Nasan da haka leeya amma ga dan uwana GAHEES WAASIB shi zai bada labarin komai yanda akayi Kanwarki Aleena tazo hannunsa........................✍🏼
42.
_____________shiru ya ratsa na wani seconds kafin dad ƙarami ya fara magana;
"Shekaru shida zuwa bakwai da suka shuɗe wata rana da nida iyalaina baki daya mun dawo ziyara daga Maiduguri zamuje kaduna, anyi ruwa sosai masu karfi har bama iya hango abunda ke gaban mu duba da yanda ruwan ke sauka kasa da mugun karfi.
Packing ɗin mota mukayi kafin ruwan su tsagaita, munfi awa uku muna jiran ruwan suyi sauki amma sai abunda ya karu, ganin haka ya saka matata Neesah taimin magana akan mu tafi mu lalla' ba kawai domin muna cikin daji kuma gashi dare ne sosai bamusan abunda zaizo ya samemu a inda muke ba duba da yanda tsaro yayi karanci.
Na karbi shawarar da sosai haka muka ci gaba da tafiya gab da zamu shigo garin lere ne a cikin dajin muka kusa cin karo da mutum yana nufomu da gudu har sai da ya shiga gabanmu ya giftamana muka bige shi da mota, babban abunda ya tayar mana da hankali shine bayan mun bige mutumin motar bata tsaya ba har saida muka jingina shi da wani katoton iccen bishiya mutumin ya fadi a rigingine kansa ya daku da iccen, mummunar buguwa yayi domin har mu da muke zaune a mota sai da mukaji karar buguwar.
Da gudu na fito motar na nufi mutumin da ke kwance a kasa kamar gawa, ganin haka yasa matata da 'ya'yana gaba ɗaya suka fito.
Wani irin tausayi ne ya kamani ganin karamar yarinya kwance cikin jini, karamace sosai domin bazata wuce Sa'ar Fannah da Mayah ba, sai dai ko tafisu jiki da tsawo kaɗan. Ruwa duk ya jikata.
Da zallar tausayi Neesah ta dauketa amma bazata iya dagata ita kadai ba Saboda tayi mata nauyi yasa na kama mata muka shigarda Yarinyar mota muka dauki hanyar Kaduna da sauri. fahimtar yarinyar tana cikin mawuyacin hali tsakanin rai da mutuwa yasa nake gudun fitar hankali da motar har bana tunanin abunda zai faru gaba.
Direct asibitin kudi muka wuce bayan shigowarmu Kaduna, inda nakeda tabbacin za'a sami kwararrun likitoci a tsakar daren nan domin kuwa karfe biyun dare ta gota.
Karɓar ta likitocin sukayi aka wuce da ita emergency, a lokacin tuni 'ya'yana sunyi bacci, a mota muka barsu muka shiga asibitin.
In takaice muke zance daren da abun ya faru tsakanin Ni da Neesah ba wanda ya rumtsa har asuba kuma duk yarana suna mota a can sukayi bacci gaba dayansu, har kuma wannan lokacin yarinyar da muka bige bata farfaɗo ba.
Sai kusan karfe hudu na yammacin rana ta biyu da abun ya faru sannan yarinyar ta farka, a lokacin ma Ni bana nan amma na bar Neesah tana kula da ita.
Tashin hankali da tausayi ya shigeni sosai lokacin da labarin abunda ya faru da yarinyar ya sameni,
Likita ya gaya mana buguwa da yarinyar tayi da wani abu mai karfi ya haddasa mata matsala a kwakwalwar ta har tayi loosing memory dinta komai ya goge a kwakwalwar ta babu abunda zata iya tunawa, haka kuma an gaya mana cewa buguwar ta taba wata jijiya ta idanunta sosai har bata iya ganin komai a halin yanzu.
Nayi bakin ciki sosai da jin haka domin kuwa yarinyar ko sunanta bata iya tunawa bata cewa ummmm bale umm-umm, mu kwashi tsawon sati uku a haka kuma ana yimata magani sosai kafin aka sallamemu tare da bamu shawarar sosai game da lafiyar ta, ta samu saukin idanunta a hankali domin tana iya gani kadan kadan da rana amma idan dare yayi bata ganin komai.
Likitan da muke karɓar magani wurinsa ya kwatanta mana wani likitan daban saidai shi bangaren idanu ne kawai, haka mukaje muka sami likitan aka yimata wankin idanu aka yanka mata glasses, a lokacin ne ta fara ganin komai tarrrr idan ta saka glasses din, amma daga zarar ta cire shikenan bazata kara ganin komai ba har sai ta mayar da shi a fuskar ta. Wannan shine dalilin da kuka ga tana sanya glasses ko yaushe kuma yana fuskarta a kullum"
Dad ƙarami ya faɗa yana mayarda kallonsa inda Rukhshanah ke zaune, haka ma sauran mutane suka kalleta cikin tausayawa Leeya kam har da kukanta.
Dad ƙarami yaci gaba da faɗin; "haka muka kwashi tsawon shekara daya da watanni tare da ita, a nan ne muka sauya mata suna zuwa Rukhshanah domin babu wanda yasan abunda zai kira sunanta dashi tunda ba wanda ya santa a cikinmu kuma itama kanta bata san wacece ita ba.
A bangaren ciwonta daya kuma muna iya kokarin mu aƙalla mun kaita asibitoci sunfi a kirga amma maganar daya ce.
Mun dauki Rukhshanah kamar yar da muka haifa da cikinmu domin bama taba nuna wani bambanci a tsakaninta da 'ya'yamu ba, su harma suna gani munfi sonta amma duba da larurar da take ciki yasa basa wani damuwa har dai sukazo suka girma suma suka daina damuwa da wannan.
A kwana a tashi girma yana zuwa shekaru suna shuɗewa har mukaje da ita India akayi mata magani aka kuma bamu wannan allura da akayi mata yanzu, a nan ne kuma Allah ya kawo mata karshen wahalar ta kunga yanzu ta warke ta sami lafiya har muka gana da ita, ta shaidar mana da asalin sunanta da kuma labarin ta gaba daya" dad ƙarami ya karashe maganar sa da faɗin haka.
Cikin Muryar kuka Aleena ta taso tazo gabansa baki na rawa ta fara yimasa godiya, haƙiƙa sun yi mata namijin kokari, kuma samun mutum kamar dad ƙarami a halin yanzu ba karamin aiki bane.
Tayi masa godiya kwarai da gaske haka ma Mom Neesah har suka rungume juna da ita, sannan ta mike taje ga yayarta itama suka rungume juna tare da sakin kuka mai ban tausayi.
"Aleena ya akayi kika tsira daga yan bindigan da suka tafi daku" Leeyana ta tambayeta.
"Kamar yanda dad ya fada muna a bangaren mu ruwa akeyi sosai.
Amma hakan bai saka sun dakata gudu da motar ba. Ina cikin tashin hankali sosai matuka ganin yanda Nnene ke wani abu tana gu kamar mai aljanu har tana yagar kayan jikinta,
sai kuka nake ina kokarin dakatar da ita daga abunda take.
muna cikin hakane naji motar mu ta daku da wani abu mai karfi kamar dutse, take motar ta birkice da kowa dayake cikinta.
Nnene tayi kukan kura ta fito daga motar tana kokarin guduwa, da sauri na riko hannunta ta janyoni nima na fito, amma ina fita daga motar ta fizge hannayenta daga gareni ta shiga daji da gudu tana ihu, ganin haka ya tsoratani sosai har nayi kokarin na bita, amma ganin tamin nisa sosai ya sakani hawa titi da gudu ina kuka da kiran sunan mutane koda akwai wani akusa yazo ya ceceni, wani haske naga ya fara tunkaroni gadan-gadan nima na tunkareshi ina d'aga hannayena domin ruwan da ake basu bani damar ganin abunda ya shigo gabana ba, ji na nayi na bugu da wani abu mai mugun tauri da karfi.
Daga haka ban qara tunawa da komai ba sai daren jiya"
Sai a lokacin Zafaran yayi magana yace "Allah sarki kenan Nnene hauka tayi?"
"Ba mamaki domin a gabanta aka kashe mijinta" cewar Leeya batare da kalleshi.
"Ya zama dole na nemo ta idan tana raye, domin tayi min hallaci kuma ta rike amana, a wannan lokacin ne ya kamata na nuna mata godiya ta da abunda tayi min"
"Nima inada fatar haka okene, domin kuwa Nnene ta rikemu kamar ya'yan ta bata taba nuna mana kyama ko bambanci ba saboda mu ba Christian bane"
"Ba Okene bane sunana Lewa, yanzu ni ba Christian bane na musulunta sunana Muhammad Zafaran"
"Lewa!" Ta maimata sunan a bakinta.
Tunawa tayi da lokutan baya idan zai rakasu unguwa ko kuma islamiyya ko idan taje gidan su zata dawo, sau dayawa yana kiranta da wannan sunan. Mafi yawanci ma yafi kiranta da haka ko kuma ya kirata Ifunanya, idan kuma ta tambaye shi sai yace mata zata san meye fassarar haka idan ta girma, bata iya ganewa ba sai da ta koma Makoko gidan kawunsa da ta fara jin yaren igbo sannan ta fahimci"lewa" yana nufin masoyi ko wacce aka bawa wani matsayi na daban, "Ifunanya" kuma yana nufin matar da ake da burin aure.
Tun daga wannan lokacin ne taji a duniya ba wanda take so da kauna kamar Okene, amma kaddara ta riga fata domin kuwa shekaru shida kenan rabon da ta sakashi a idanun ta, sai dai yana nan a zuciyarta koda bata ganinsa.
Turab ma wani abu yaji ya tokaremasa makoshi, a hankali ya fara kiran sunayen Allah domin bayaso yaji sauyi game da zamansa da abokinsa saboda mace, yayi imani da zai iya kyaleta wallahi da ya barta da Zafaran ko zai samu peace of mind, sanin yanda yake fama da soyayyarta a zuciyarsa tsawon lokaci.
Dan gyaran murya papu yayi sai kuma hankalin Leeya da sauran mutane suka dawo kansa, tun kafin papu yayi magana Leeya tayi saurin yiwa Zafaran tambaya.
"Ya akayi ka musulunta Alhali nasan ku katafawa ne bakwason addinin Musulunci ko kaɗan, kuma ko a Cristian ku na daban ne?"
"Lewa wallahi kin bani mamaki da kike maganar ki kuma kike sakawa hardani, wallahi sanin kanki ne banada wani buri da ya wuce na musulunta, da inada akidar katafawa da bazan taba zama musulmi ba. Ke kanki zaki karyata idan aka ce miki banason musulunci da musulmi amma ba komai tunda kince haka na d'auka"
"Kayi hakuri" ta furta a sanyaye, "nasan iyayenka ba sa so ne shiyasa, amma inada tarin tambayoyi akan haka"
"Tambayar ki itace ya akayi na tsinci kaina a musulunci kho?, to zan gayamiki yanzu kuwa.
Bayan barina garin Ikeja sai mukazo Abuja, mun kwashi tsawon watanni tara muna Abuja kafin akayi mana biza muka wuce kasar Mexico, a can ma na dauki lokaci kafin na fara karatu sakamakon halin jinya da mahaifiyata ta tsinci kanta a ciki, in takaice miki banshiga makaranta karin karatu ba har sai da komai yazo karshe ma'ana mahaifiyata ta mutu, daga nan kuma mahaifina ya dauki hutu a wajen aikinsa muka dawo Nigeria kasarmu wato Delta akayi bikin binne ta aka gama muka koma Mexico kuma.
Guntun lokaci da faruwar wannan mahaifina ya dauki soyayyar duniya ya ɗora min har baya iya yimin musu da abunda nakeso saboda tsanin so da kuma tausayina da yake, anan ya bani damar za'bar makarantar da nakeso nayi karatu, nikuma na shiga binciken makarantar da Musulmai suka fi yawa a 'kasar , bayan dogon binciken da nayi kuma na samu sai na sanar dashi makarantar da nakeso.
Ya gane makarantar mafi akasarin ɗaliban da ke ciki Musulmai ne amma bai nuna min damuwarsa akan haka ba, bayan nayi register da komai na fara zuwa, ranar zan fara shiga school din na hadu da Turab kuma muka k'ulla abota mai ƙarfi da shi, bayan wasu lokaci kuma na nuna masa ra'ayina akan addininsu, wannan kuma bai wani bani matsala tsakanina da mahaifina saboda abunda nakeso shi akeyi, ya yarda na shiga addinin Musulunci bisa son raina amma kar nayi tunanin shi zai fita addininsa ya shiga wanda na shiga, naji bakin ciki sosai da furicinsa kuma na nuna rashin jin dadi na akan rashin shiga da yayi addinin musulunci.
Shikenan na shiga