BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   25 / 61

72K to 75K   out of 180.4K words

da yayi, zaije ya sami auntyn ku
Rahma a nema maka auren ikram ƙanwarka"

Cikin zallar tsorata da abunda mum ta faɗa muryarsa har tana sarƙewa yace"What!?, me kike faɗa haka mum nine zan auri ikram"

Ya faɗa yana nuna kansa da yatsa"wallahi mum kar ma ku soma wannan don wallahi ni bazan aure taba".

"Shikenan idan bazaka auri ikram ba, wannan ba wani abu bane dama bamu riga mukayi wa Rahma magana ba balle ka kunya tardamu, kaje gidan dadyn ku gahees kayi magana da mayah domin ita fannah tanada wanda takeso"

"Mayah kuma mum, sa'ar khulud ce fa. Mezanyi da mayah gaba ɗaya mayah bata cikin irin tsarin matar da nakeso na aura sam, saboda haka a ajiye maganar mayah"

Murmushi irin na wacce tasan abunda take mum tayi kaana ta ɗora da faɗin, anjima ka shirya kaje dalah Street gidan hajiya Balaraba kayi magana da raudha itama ta isa aure ai"

Murmushin takaici turab yayi yana tare da cije gefen lips ɗinsa,

"mum banason raudha, finally ni ban tashi aure ba, saboda duk ƴan matan da kika lissafamin har ma da waɗanda ke zuciyar ki,
da waɗanda kika faɗa da Waɗan baki faɗa ba duk basa cikin tsarina, infact ma mum ni tun dawowa ta Nigeria har yau ban taɓa ganin yarinyarda ta birgeni ba ko inji sha'awar zama da ita matsayin matar aure, saboda haka ki ajiye maganar aure gaba daya beside, ni banada buƙata gaskiya"

"Wannan kuma baka isa ba turab, ya zama dole ka fitarda mata kayi aure idan kuma ba haka ba mu zuba dani dakai shege ka fasa, kana gani a gidan nan za'a shigo da mata a matsayin wacce muka aura maka, tun wuri ma kasan abunyi kuma dole sai ka zaɓi ɗaya daga cikin matan da na lissafa maka, shashasha kawai mara tunani" mum ta fada cikin tsananin ɓacin rai ta baro masa part ɗinsa.

Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara turab ya dunkule hannun sa na hagu yakaiwa bangon ɗakin wawan naushi har saida yayi hakan sau uku kafin ya koma ya jingina da bango, ya furzarda iska mai zafi daga cikin bakinsa.

Idanunsa kuwa sun kaɗa sunyi jajir kamar garwashi saboda ɓacin rai. Domin kuwa kalaman mum na ƙarshe sunyi matukar ƙona masa rai.

Fita yayi daga ɗakin, ba abunda ke yi masa daɗi a yanzu, hanyar garden ɗin sa ya nufa saboda a can kaɗai zai iya zuwa ya zauna hankalinsa ya kwanta a halinda yake ciki yanzu.

Tunda ya shigo wurin ya kejin ƙarar sautin piano na tashi daga can inda yake ajiye kayan kiɗansa. Nan take ransa ya kuma yin baki ƙirin, duk tafiyar da yake da saurin da yakeyi sai yakeji kamar ana mayardashi baya ne domin gani ma yake wurin na ƙara yimasa nisa.



A ransa kuma yana auna irin dukanda zaiyiwa khulud "da alamu jikinta ƙaiƙayi yake yimata shiyasa har ta shigo wurin nan kuma ta rasa inda zata je ta zauna sai........"

Maganar ce ta maƙalemasa sakamakon arba da yayi da leeyana a wurin zaune.

Razananniyar tsawa ya daka mata muryarsa har tana crack saboda ɓacin rai,

"me ya kawoki a wurin nan, kuma ya akayi kikasan da wannan wurin a cikin gidan nan gayamin ko nayi miki dukan tsiya anan ba wanda kika gani balle ya kwace ki a hannuna wallahi"

"Wayyo Allah, na shiga uku dan Allah ya-Turab kayi hakuri, wallahi kaddara ce tasa na shigo nan Ni ban masan kana nan ba wallahi da bazan shigo ba" leeya ta faɗa tana shirin rushe wa da kuka.

"Wallahi idan kika sake kika min kuka saina ɓaɓɓalaki, me aka yimiki da har zakiyi kuka this is the last, last warning, billahil azeem idan na ƙara ganin kafar ki a wurin nan sai na miki dukan da sai ance accident kikayi, kinga tun shigowar ki gidan nan ban taɓa dukanki ba kho, ba dan komai ba saboda ke marainiya ce wallahi da badan haka ba ko hanyarda nabi bazaki ƙara kalla ba"

"Wallahi ko yanzu ma bazan kalla ba, dan Allah kayi hakuri"

"Fita kiban wuri" ya faɗa yana nuna mata Kofar fita.

Raɓewa ta farayi tana tafiyar sanɗa kamar wata ɓarauniya
"Wallahi idan na buɗe idanuna naganki wurin nan....."

Tun bai ƙara saba yaji ta wuce a guje gabansa kamar bullet.

Sharafff kakeji leeya ta zube kan gadonta sai maida numfarfashi take da sauri da sauri.

Tashi tayi zaune tana leƙa ƙofar ɗakin ta a hankali, ta dafe ƙirjinta tana sauke nannauyan ajiyar zuciya "wai Allah Nagode maka, ya Allah ka ƙara tsareni daga dukan ya-Turab, Allah ka ciremin kaunar garden ɗin ya-Turab ya Allah"

Ta faɗa a fili tana ɗaga hannayenta alamar roƙo.

"Leeya garden ɗin turab kikaje?"
Ta jiyo Muryar mum da take shigowa ɗakin.

"Wallahi kuwa mum ƙaddara ce takaini wallahi, amma in Allah yaso ba ƙaddarar da zata kuma kaini wurin nan ko hanyar wurin ma bazan ƙara kalla ba"

"Ai kho daya fimiki alƙairi, yau khulud zata fara zuwa School kuma gashi bata tashi da wuri ba shine nazo ki taimaka mata dan Allah kije ki gyara ɗakin Turab, domin shi bayada uzuri kinsani duk da yasan zataje school idan bata gyara ba bazasu wanye lafiya ba".

"Mum yanzu gyara ɗaki shine abun taimako ai ba komai bane wallahi, Ni tun farko ma naso na dinga gyarawa shine ya dage kan ita dai zata riƙa yi"

"Eh Nima nasan da haka, kuma Ni na bada shawarar a barta tayi da kanta domin kina ganin khulud duk girman nan nata ba ko wane aiki ta iya yiba, idan mu munyi haƙuri da ita a hakan wanda zai ɗauke ta nan gaba shi bazai yi hakuri ba komai sonda yake yi mata. Koda yayi na marmari zaiyi amma daga randa ya lura sosai to zai fara yin magana daga nan kuma matsala zata fara shigowa, kinga daga haka abun sai ya taɓa zamansu"

"Gaskiya kuma fa hakane mum, ba Kowa zai iya haƙuri da wannan ba gskiya, Bara naje na gyara kafin ya kammala shan iska nima kinsan ina cikin laifi banaso ya tarar dani ɗakin"

"Okay tau kije kiyi sauri kuma, kinga idan kika yi sauri kika kammala da wuri kika fito ko ya dawo baisan wa yayi aikin ba a tsakanin ke da kuma Khulud.


"Eh wallahi mum ai shiyasa nake so nayi sauri na isa"

"Okay muje to"

Cewar mum tana wuce wa gaba ita kuma tana bayanta.
Suna fita kowa ya kama gabansa, mum ta tafi sashen ta, yayinda leeya kuma ta tafi sashen turab sai addu'a take a Zuciyar ta.


Ji take kamar idan ta shiga zata ganshi, amma kuma tasan ba kowa a ciki tunda tasan inda ta baro shi.

Da sallama a bakinta ta shiga parlourn duk da tasan ba wanda zata tarar amma hakan bai hanata yin sallama ba domin shiga wuri da sallama nadaga cikin ɗabi'un ta.

Kwata kwata ba datti ko kura parlourn kamar ma ba'a zama cikinsa domin komai tsatsaf. Amma duk da haka bai hanata yin shara da mopping ba.

Bayan ta kammala tayi goge-gogen da zatayi sannan ta saka air freshener da kuma turaren tsintsiya.

Bedroom ɗin sa ta wuce shima tsaf-tsaf kamar yanda ta tararda parlour gadon ne kawai a chakude da alama ya kwanta a kan gadon.

Shareshi tayi sosai shima kaana tayi mopping ta saka turare shima.

Duk inda yakeda glass a ɗakin sai da ta gogeshi yafito tsaf dashi.

Gaban wata HANGER CABINET taje ta tsaya tana kallon soldier's uniform ɗin da ya sarƙafe, wanda zasu iya kai kala goma, kuma ko wane kallar uniform da sunan ƙasarsa, ɗaya daga cikinsu ta ƙurawa idanu masu kalar maroon and green.

Uniform ɗin sun ɗauki idanun ta matuƙa, a hankali ta saka abun ciro wa ta ciro jacket ɗin kayan "maroko" abunda taga an rubuta kenan a kan bottom ɗin da ke kan maroon jacket ɗinsa.


"Kenan wannan uniform sune uniform ɗin sojawan maroko"
Ta faɗa a cikin ranta. Lokacin da take shaƙar kamshin da ke fitowa daga cikin jacket din.

Haka kawai taji sha'awar saka rigar, batare da wata shawara ba kuwa ta ɗora ta kan kayan da ke jikinta. Hular kayan ta ɗakko ta saka a kanta.

Komawa tayi da baya inda yake ajiye takalmansa ta ɗakko waɗanda taga sun dace sosai ta uniform ɗin ta saka ƙafarta.

"Hmmm, ashe ya turab kana da ƙafa da yawa takalman nan ai ko kafata biyu zata iya shiga cikin su, amma dai ɗaɗɗaya zan saka ma ko wace ƙafa"

Bangaren da yake ajiye glasses ɗin sa tayi, bayan takalmansa da jacket ɗinsa dake jikinta, wani farin glasses sol ta ɗakko wanda shi yafi ɗaukar idonta duk a cikinsu, da yake niqab ɗin da ke fuskarta ya bayyanarda ƙwayar idanunta, yasa ta saka glasses ɗin ba tsoron komai.

Hannu ta saka ta janyo agogon hannusa baƙi wulll ta saka shima dai yayi mata yawa sosai.

Ƴar siririyar dariya tayi tana faɗin "ikon Allah, Ni ban taɓa tunani ya-Turab nada jiki kamar haka ba, agogon nan fa ya kasa tsayawa a hannuna hmmmm, yanzu sai me ma" ta faɗa a fili tana ɗan taga kanta sama kamar mai tunani.

Sake ja da baya tayi tana gyara tsayinta sosai kai kace itace turab ɗin "mum na tafi maroko, idan na kammala musu aikin su kuma ba dawowa zanyi ba zanwuce Argentina, nan ma idan na kammala Austrelia zanje zan dai iya ɗaukar 2/3 weeks na tafi ku tayani da addu'a" leeya ta faɗa tana gyara agogon da ke hannunta kamar dai yanda turab yakeyi idan zai yi tafiya.

Tafi taji amfara yimata daga bayanta"BRAVO" DR.TURAB K. WAASIB kinyi ƙoƙari sosai.

Kamar sauƙar aradu haka taji muryar turab ta dira a kunnuwanta, suman tsaye tayi daga inda take tsayen domin kafafuwanta ma ji tayi sun kasa ɗaukar ta, ta bashi bayane tana jira yazo yayi mata abunda zai yi mata kawai domin tasan yau tata taƙare saidai buzunta.............✍🏽😌










BAYAN WUYA.......









By RUMANA M DIGGI









EP.27







______________"kinyi ƙoƙari fa sosai leeya, ashe haka kike actress bansani ba" cewar turab yana tsaye daga bayanta kawai domin shi mamakinta da tsaurin idonta ya hanashi tantance kalar hukunci da zai yi mata.

Zubewa tayi kan gwuiwoyinta ƙasa tun kafin ta juyo gareshi, domin a yanda takejin nan bata tunanin zata iya kallonsa.

"Dan Allah ya-Turab na roƙeka dan Allah kayi hakuri, wallahi indai na ƙara shiga gonar ka kaymin duka duka sai ance nayi accident a jirgin sama, amma dan Allah na yanzu kayi hakuri"

"Hakurin me kuma Dr. Turab, kamar ka Chief military health service zaka durƙusa gaban mace kana bata haƙuri"

"Nidai yaya don Allah da alfarmar annabi kayi hakuri wallahi nidai, nidai in nice wallahi bazan ƙaraba" ta faɗa cikin muryar kuka.

Cikin muryarda ke nuna alamar ba wasa turab yace"idan kika ga na hakura to sai dai idan kin juyo da kanki nan, kin aikata duk abunda kikayi bayan idanuna, ki aikatashi a gaban idanuna yanzu"

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Ni yau na shiga uku, wallahi yaya sharrin shaidan ne. Wallahi bazan kuma yiba dan Allah kayi hakuri"

"Yanzu sharrin shaidan ne ko"

Da sauri ta daga masa kai tana faɗin "eh wallahi, dan Allah kayi hakuri kawai"

Komawa yayi kan sopa ya zauna yana fuskantar ta" lokacin ki ya fara tafiya, ki tashi ki fara ko kuma na naɗa miki dukan jakai a ɗakin nan"

Sosai leeya ta tsorata, danasani kam tafi dubu da takeyi a ranta, "ke nake jira" taji muryar sa ta ƙara shigowa cikin dodon kunnenta.

"Dan Allah ya-Turab kayi hakuri wallahi bazan iya ba"

"Ashe kuwa kinada rabon shan duka"

"Duka kuma yaya, wallahi na rantse da Allah bazan ƙaraba, dan Allah kayi hakuri"

Miƙewa yayi fuskar sa na sauyawa zuwa yanayin fushi sosai, a hankali leeya ta miƙe itama tana zame kayan daga jikinta.

Tana duƙawa da nufin ta cire takalman sa dake ƙafarta taji saukar wani abu a jikinta kamar dai belt. da sauri ta miƙe ta fara zagayen ɗakin tana roƙon shi cikin tsoro da tashin hankali.

"Yau na shiga uku na janyowa kaina, ya-Turab kayiwa Allah kayi hakuri wallahi nidai nace idan na kumayi kaymin fitinannen duka"

Turab kam bata ma gabansa, surutanta kawai take domin shi tama fara damunsa, yana bakin ƙofar ɗakin ne yana jira ta gama zagayen da take ta tsaya wuri ɗaya, domin baya tunanin zai iya ƙyaleta da wannan uban laifin data aika ta masa.

"Zo ki wuce" ya faɗa har idanunsa na rufewa saboda tsananin ɓacin rai da hasala.

"Dan Allah ya-Turab kar..."

"Zo ki wuce nace" da mugun gudu ta biyo ta gabansa zata wuce.
Da sauri ya cafkota ya watsa mata belt ɗin da ke hannunsa har sau biyu, kafin ta wuce.

Kuka kam ba kalar wanda leeya bata sha ba kuma ta kasa gayawa kowa labarin.













RONY COLLEGE OF SCIENCE AND INNOVATION UNIVERSITY SULEJA.

wata baƙar mota ƙirar Ferrari f8, ta faka a harabar makarantar.
Dalibai sai kai kawo suke a harabar makarantar kowa na sha'anin gabansa.

Parking driver yayi inda aka sharɗan ta yin parking a compound ɗin makarantar wato parking space.

Yana parker motar ya fito tare da Zagayawa back sit ya buɗe kofar da faɗin "hajia mun ƙaraso"

Ƙafarta ɗaya ta fara fitarwa, kana ta fito gaba ɗayan ta tana hura hanci.

Sanye take da wando pallazo kalar, baƙi sai wata rigar kuma mai ɗauke da falmara. Rigar a iya cinyoyinta ta tsaya, ta cikin ce fara yayinda ta falmarar kuma ta kasance baƙa ce kamar wandon ta.

jessy veil fari sol tayi rolling akanta, yayinda takalman da ke sanye a ƙafarta suka kasance farare suma Hill masu matukar tsawo.

Wani glasses ne sanye a fuskar ta irin fashion ɗin nan daya kusa cinye rabin fuskarta.

Hannunta ɗaya kuma handback kalar Black. Sai kuma ɗayan hannunta na riƙe da wata karamar takarda wacce da alamu wani abun take dubawa a ciki.

Tafiya ta farayi, kamar batason taka ƙasa domin a hankali take takawa, tana ɗaga kai tana hura hanci.

Saida ta kawo daf da wasu hanyoyi da suka rabu uku, kuma ko wace hanya da inda ta nufa.

Ƴar ƙaramar dakardan da ke dunƙule a hannunta ta ɗago tare da walwaleta ta ƙalla, sosai tayi nazarin wurin kafin ta juya ta koma hanyar da ke nufar gabas a makarantar.

Bangaren ANATOMY classes ta nufa tare da duba number class ɗinta, da taimakon wannan takarda da aka yimata jotting yanda tsarin ginin makarantar yake ta gano ajinda take.

Ƙara gyara zaman glasses ɗin ta tayi kafin ta shiga ajin. Ajin cike yake maƙil da mata da maza kowa nata sha'anin sa.


Shigowa tayi ajin batare da ta kula kowa ba domin ba wanda ta sani. Wani bangaren na cikin ajin ta nufa inda ta hango wata kujera da ba kowa taje ta zauna, waya ta ƙara akunnunta da alama kira taji tace "shikenan, ka tafi na gane class ɗin kuma ka kula da lokacin tashi karka makara, idan kuma kaƙi ji kasan sauran" ta fada bata jira cewar wanda tayi wayan dashi ba ta yanke wayar.

Kamar jira ake kuwa tana zama, malamin da zai yi musu lactures ya shigo.

Nan ya gabatarda lactures dinsa har yayi ya gama ya tafi.

Da haka time by time malamai suka shigo suna yin lactures. har lokacin tashi daga School ɗin yayi.

Yunkurawa tayi da nufin zata tashi, kwatsam taji an dafa kafaɗarta, da mugun fushi ta waiwayo domin ganin wanene ita da ba wanda ta sani a makarantar. Wasu ƴammata tagani su uku da sukaci ado sukayi kyau sosai, kana ganin su zaka tabbatar nera da kanta na magana a jikinsu.

"Malama lafiya dai? kinzo kin riƙeni ko wani abun nayi miki" khulud ta faɗa cike da tsiwa.

Murmushi yarinyar tayi kaana tace"lafiya ƙalau, kuma lafiyar ce ma ta janyo hakan. Munga kamar ke ɓakuwace a makarantar nan kuma idan bazaki damuba munaso mu ƙulla ƙawance dake.
Nidai sunan AMRAH RAFEEQ TIMIA. Mahaifina ne mai kamfanin NBC na ƘASAR nan gaba ɗaya har kuma da ƘASAR Japan"

Dan waro idanu khulud tayi cikin mamaki domin ba wanda baisan NIGERIA BOTTLING COMPANY ba (NBC) Indai a garin suleja yakai.

Bata gama mamaki ba taji ɗaya daga cikinsu tace"nikuma sunana REEMAH RABEEL mahaifina ne commissioner of police na kasar nan".

Ta ukun kuma tace;
"Nikuma sunana RAUDHA MAHEER YASAR mahaifina ne current governor na yanzu"ta faɗa tana kaɗa carkeys dake hannunta.

"Wow nice to meet you, I khulud Khattab waasib mahaifina ne current minister of judiciary. Chief Khattab waasib SAN, kuma babban dan kasuwa ne a kasashen ketare" khulud ta faɗa tana fitar da siririyar iska daga bakinta.

Wani irin tsalle suka daka su duka huɗun suka rungume juna, cikin farin ciki.

Raudha, da amrah duk halinsu ɗaya kamar dai khulud, kwata kwata basa ƙaunar talaka ko kaɗan, ga girman kai da son a nuna su wasu ne, a kaff makarantar basa shiga lamarin kowa sai idan sun fahimci kunada mahaukatan kuɗi, kuma idan suka san mahaifinka sanannene.

Sunjima zaune su biyu kaɗai ba wani wanda yake ɗalibi a makarantar Rooney da bai san raudha da amrah ba saidai idan new commer ne, kuma ko new commer aka samu bazai wuce kwana biyu zuwa uku ba zai sansu a makarantar yanda suke fantamawa da kuɗi da manyan motoci.

Samari kuwa sai chahhh suke musu, amma kuma duk wanda yaje sau ɗaya bazai ƙara kwatanta zuwa ya samesu da wata maganar soyayya ba, domin ko mutum bai furtamusu kalmar soyayya ba sun wulaƙanta shi balle ma ace ya nuna musu.

A cewarsu babu irin tsarin samarin da suke so a Rooney ko akwai kuma basu shigo ba tukunna,

Rooney school of science babbar jami'ah ce a garin suleja, kuma shigarta sai ɗan wane da wane, duk wanda kagani a cikinta to mahaifinsa yayi fice domin kuwa ba talaka bane.

Haka amrah da raudha suke rayuwarsu iya su biyu kadai a Rooney basa kula kowa, kuma kowa baya kulasu.

Haka suke duk lokacin da aka kawo new commer idan mace ce zasuje su gabatar mata da kansu da kuma nasabarsu. Itama kuma sai ta faɗa musu, idan sukaji nasabar ta kuma suka gano mahaifinta ba wani sananne bane shikenan suyi gabansu itama tayi gabanta ba ruwan kowa da kowa. Idan kuma sukaji sunan mahaifinta sannanne ne shikenan sai su kulla ƙawance.

Hakace ta faru lokacin da aka kawo REEMAH RABEEL makarantar, da suka gabatar mata da kansu, itama ta gabatar musu da kanta shikenan sai suka ƙullla ƙawance da ita. Saboda mahaifin REEMAH ma sananne ne sosai a ƙasar, kuma gata da cikakkiyar gata domin ita kaɗai Allah ya

25 / 61