BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   26 / 61

75K to 78K   out of 180.4K words

bawa iyayenta.

Sai dai wani abu ɗaya REEMAH da RAUDHA da kuma AMRAH basa jituwa sosai a tsakanin su, saboda halinsu ya bambanta da nata. Ko kaɗan REEMAH bata ƙyamar talaka, kuma bata wulaƙanta mutane kamar yanda su amrah sukeyi.

Amma kuma batajin zata iya rabuwa dasu kan wannan, saidai suyi faɗa su shirya, haka suke koda yaushe.

Shiyasa REEMAH tayi farin ciki sosai ganin khulud tana tunani wata ƙila halin khulud daban dasu amrah shikenan sun zama su biyu a bangaren ta, suma su amrahn su zama su biyu ke nan tunda ba zasu sauya halayensu ba.

"Shikenan ku fito mu tafi kho, wata ƙila ma anzo ɗaukar wasu daga cikinmu" REEMAH tayi maganar tana wucewa gaba.

Su kuwa su amrah sai jan khulud surutu suke, ita kuwa ta sake sai basu labari take kamar da can sun saba.

Fitowa sukayi harabar makarantar suna tafiya su huɗu sunsha kyau sosai da gayu, mutane kuwa sai kallon su suke duk inda suka gifta musamman ma khulud da take baƙuwa fuska bakowa yasanta ba.

"REEMAH kinga fa ke nake nema tun ɗazu" wani farin matashin saurayi ya faɗa yana murmushi.

"Lahhh wallahi Sayyid muna class tun ɗazu, baƙuwa mukayi shiyasa kaga mun jima bamu fito ba, ince dai lafiya".

"Lafiya ƙalau fa, kawai inaso nayi tambayane amma muje daga can" ya faɗa yana nuna mata wasu plastic chair's dake ɗan nesa dasu.

"What!?, ba inda zataje idan bazaka iya yin tambayar anan ba ka ƙara gaba, ko kaje can wurin wanda yayi lacturing ɗin kaje kayi tambayar ka ai ita ba lactures take yiba" cewar raudha tana hararar matashin saurayin da ya tsayarda reemah rabeel.

"Raudha kenan, nasan ba lacturing take ba. Na zaɓi nayi tambayar wurin tane saboda ita tasan abunda take, inaga ga mutane nan da yawa sai ita na zaɓa ta gayamin saboda ita tasan mutumcin jama'a"

Raudha na shirin yin magana khulud ta daga mata hannu alamar tayi shiru. Tafiya ta farayi ɗaɗɗaya har ta ƙaraso gaban sayyid.

Sayyid kuwa ganin haka yasa ya gyara tsayuwar sa, tare ta mayarda hannayensa gaba ɗaya cikin aljihunsa yana jira yaji dame tazo.

"Kai Sayyid naji an kiraka ko wah, Please ka fita sha'anin mu a School ɗin nan gaba ɗaya, naga kamar kanka yana ɗan rawa. So it's better for you to maintain yourself. If not kasan sauran" khulud ta faɗa tare da juyawa ta fara tafiya.

"Hmmm, idan kika tambayi labarin Sayyid Turaki bana shiga lamarin ƙananun yara, musamman yaranda basu san abunda suke ba. Kuma Ni idan kika duba bana kula jahilai kamar ke ɗin nan dama sauran tumakin abokan nan naki raudha da amrah. Idan kika ganni a wuri to nasan inda na kawo kaina, REEMAH RABEEL tasan mutumcin mutane kuma wurinta nazo, inace ma danazo wurin nan bankira sunan ko waje akuya a cikinku ba kho, so kuma ku kama kanku Sayyid baya lamarinsa da dabbobi" cewar Sayyid yana wani shu'umin murmushi.

Kalamansa sun ƙona zuciyar khulud matuƙa, hakama amrah da raudha, saidai nasu duk mai sauƙine tunda su ba yau suka saba ba. Khulud ce ya fara yiwa yanzu, ba ranarda Sayyid zai haɗu dasu AMRAH ba'a sha daga ba, wani lokacin kuma REEMAH ce ke tarewa tun kan a fara.

Khulud na shirin magana, REEMAH ta dafe mata baki da hannayenta tana shirin kuka "dan Allah khulud kiyi haƙuri karki ƙara faɗar komai dan Allah na roƙeƙi, Sayyid kaima ka tafi dan Allah zanzo kaji kayi haƙuri Please " ta faɗa cikin matukar damuwa tana rangwaɓarda kanta kamar zata fashe da kuka.

"Shikenan REEMAH zan tafi saboda ke, wallahi da badan keba bazan je ko'ina ba sainaji ina rashin kunyar wadannan yara ta tsaya" cewar Sayyid yana barin wajen tare da jefawa su amra wani wulaƙantaccen kallo.

Cikin matukar zafin zuciya da ɓacin rai khulud ta bige hannayen REEMAH daga kan fuskar ta"dan Allah tsaya Malama, ashe ke matsoraciya ce, gskiya Ni banason mutane irinki REEMAH na rantse da girman Allah ni banason mutane irinki, kum naga su AMRAH ba wannan tsoron a idanun su ke kaɗai ce, to wallahi Ni bazan iya da wannan abun kunya ba. Duba kiga yanda wani ɗan iska yazo ya cimana mutunci ya tafi ba abunda muka iya yi masa"

"Kedai kibarta kawai khulud, wallahi reemah bakyajin magana kece kike janyo anayimana kallon ƙananun mutane, yanzu ki duba wannan dan iskan Sayyid ɗin da yazo yana cimana mutunci harda kiranmu wai awakai, wallahi da ace munsan yanda zamuyi da Sayyid da tuni mun saka an fitar dashi daga Rooney" cewar amrah cike da masifa.

"Saboda me baza'a iya fitarda shi ba, Ni wallahi zan iya samun mahaifina da maganar nan kuma in sha Allah zai iya saka a sallameshi daga School ɗin nan"

"Hmmmm, kedai khulud rufa mana asiri, Sayyid bazai iya fitardamu a Rooney ba, haka muma baza mu iya fitardashi ba. Sayyid ya zamarmana ƙadangaren bakin tulu ba yanda muka iya dashi ya riga da ya rainamu duk fadin Rooney sayyid ne kaɗai baya shakkun faɗa mana magana"

Ƙwafa khulud tayi kawai tare da barin wurin bata cewa kowa ƙala ba, saboda ranta yayi matuƙar ɓaci............✍🏽












BAYAN WUYA........






By RUMANA M DIGGI









EP.28



_________________________________________K. WAASIB MANSION.


"mum na kammala"

"Kije kiyi wanka ki shirya, fita zakuyi"

"Fita kuma mum?"

"Eh, kije ki shirya turab zai kaiki shopping, saƙo nakeso na
Baki.

"Ok mum, yanzu zanje na shirya, amma dai mum da so samu da sai driver ya kaini ya-Turab yayi zamansa"

"Turab nakeso yaje ya kaiki, kiyi sauri kuma karki ɓata masa lokaci domin shima na faɗa masa ba ruwana idan kika ɓata masa lokaci".

Juyawa leeya tayi gwiwarta duk tayi sanyi, domin rabon da ta saka turab a idanun ta tun ranar da tayi masa laifin a dakinsa.


Daga ranar ne kuma ta toshe duk wata ƙofa dazai dinga ganinta, sun kwashe kusan sati uku basa ganin juna. Dayake shi bai cika zama a gida ba, ita kuwa leeya duk ranarda yana gidan bata taba fitowa ko cin abinci, idan ta fito da sanɗa zata fito tayi duk abunda zatayi sannan tayi tafiyar ta batare da sunga juna ba.


Da sanyin jiki ta ƙarasa ɗakinta, tana isa kuwa wayarta ta fara ɗauka tare da dannawa zohal kira, Bugu ɗaya ta ɗaga.

"Bestie" aka faɗa daga cikin wayar.

"Na'am, zohal barka kina lafiya"

"Lafiya ƙalau, yasu mum"

"Mum tana nan lafiya"

"Masha Allah, bestie kina lafiya kuwa, naji muryarki ta sauya"

"Wallahi zohal da dama dai za'a ce, kinsan tunda na baki labarin laifin da nayiwa ya-Turab koh"

"Eh masani, bestie badai laifi kika ƙara yimasa ba kuma"

"Ah, ah, banyi masa laifi ba amma tsawon wannan lokacin bamu ƙara haɗuwa dashi ba, na kiyaye duk wata hanya dazata sake haɗamu, sai yanzu ne mum takirani tace naje na shirya tanaso ta aikeni nayimata shopping kuma ya-Turab ne zai kaini"

"Tabbb, lallai kam dole hankalinki ya tashi, ke mene ma wani abun tashin hankali. Kedai kawai ki tashi kije ki shirya ki fita kar kuma ki sake masa laifi, amma kuma shawarar da zan baki ki kama kanki karkiyimasa ba daidai ba duk yanda yace kiyi, koda bai miki daɗi ba kiyi don ku rabu lafiya. Naga kamar zaifi da wani tsoro-tsoro da kikeji"

"Tau shikenan zohal, in sha Allah ba wani abu dazai faru indai ta bangarena ne, amma Ni wallahi tsoronsa nakeji"

"Hmmm, yafi ma zaki cire tsoron sa a ranki, idan yaga kin cika tsoransa da yawa wallahi zai ta kura miki ne da yawa shima"

"Shikenan bara naje nayi wanka, sai na dawo"

"Allah ya tsare hanya"

"Ameen thumma Ameen"
Leeya ta faɗa tare da katse wayar.



Ajiye wayar ta tayi a inda take zaune daga nan kuma sai ta shiga toilet da nufin yin wanka.
Bayan mintuna kaɗan kuma sai gata ta fito,
Dressing mirror ta nufa tare da shiryawa tsaff cikin riga da skirt na atamfa ruwan shuɗi mai ɗan haske. Kayan sunyi matukar yi mata kyau, duk da ba'a ganin fuskar ta amma hakan bazai hana mutum ya fahimci irin kyawun da kayan suka yimata ba.

niƙab ɗinta ta ɗauko kalar blue mai duhu, sai kuma ta yafa gyale kalar blue mai duhu shima.

Sannan ta juya da nufin ɗaukar wayanta,

Lokacin da takai hannunta ga wayar da nufin ta ɗauka, babban abunda ya ɗaure mata kai shine shigowar sakkoni uku lokaci ɗaya, kuma ko wane saƙo da lambar da aka turoshi daban.

Amma kuma duk abunda saƙon yake isarwa ɗayane da kowace lamba.

Lamba ta farko abunda aka turo da ita shine, "AMINCIN ALLAH YA TABBATA A GAREKI MY DREAM GIRL, INA FATA KINA LAFIYA, ALLAH YASA HAKA. NASAN KINA CIKE DA MAƊAUKAKIN MAMAKI KHO? KO KAƊAN KADA KIYI MAMAKI LEEYANA, NI MASOYINKI NE NA HAƘIƘA WANDA BANA TUNANIN KINADA KAMARSA A HALIN NAN DA MUKE CIKI YANZU, NASAN KINA MATUƘAR BUKATAR NA BAKI DAMA KIYIM TAMBAYA KHO, HMMM, KARKI DAMU WATA RANA IDO DA IDO ZAKI GANNI KINJI. BYE KI KULA DA KANKI, SAI ANJIMA".

Number ta biyu kuma sai aka turo sakon kamar haka"SORRY MY DREAM GIRL, NACE MAKI SAI ANJIMA KUMA GASHI BAMU KAMMALA MAGANA BA, YANZU NA SAMI LABARIN WAI ZAKI FITA SHOPPING KHO, AMMA KUMA SHINE BAKI GAYAMIN BA, KO DA YAKE MA AI BAKIDA WATA ƘOFAR DA ZAKI IYA SANARMIN DA KOMAI SAI DAI IDAN NI NA ƁUKATA, WELL SAI DAI KIN DAWO ALLAH YA KAREKI DA KARIYAR SA".

Number ta uku kuma saƙonta shine"YAWWA MY DREAM GIRL, BAN GAYAMIKI ABUNDA ZAKI SIYOMIN BA IDAN KIN FITA SHOPPING ƊIN, DAN ALLAH INASO KI SIYOMIN KYAKKYAWAN AGOGON HANNU DOMIN YANA DAGA CIKIN ABUNDA NAKE BUƘATA. KUMA NAJI ANGAYAMIN BAKE KAƊAI ZAKIJE BA, DAN ALLAH KI KULAMIN DA KANKI. KINSAN INADA MATUƘAR KISHINKI. KARKI DAMU KANKI DA SANIN WANDA YA GAYAMIN ZAKI FITA BA, KEDAI KAWAI KISAKA A RANKI INA KAUNARKI KUMA INA KULA DA DUK WANI MOTSI NAKI DREAM GIRL ƊINA.
NASAN ZAKI ZARGI KO ZOHAL CE TA GAYAMIN KHO, HMMMM.
MAGANATA TA ƘARSHE ITACE BASAI KIN WAHALAR DA KANKI DA TAMBAYAR ZOHAL BA DOMIN WALLAHI KO ITA ZAKI TAMBAYA BATA SANNI BA KAWAI DAI TASAN INA SONKI DA ƘAUNARKI SAI ANJIMA".

Leeya nakai nan a karatun da take sai ta sauke wani ƙaƙƙarfan numfashi tare da zaunawa kan royal chair, ta ɗauki lokaci a haka daga bisani kuma ta kira number zohal.

Kwata kwata bata kawo kiran number ko ɗaya daga cikin numbers ɗinda aka yimata saƙo ba, domin kuwa tasan abu ne mawuyawaci ta sami number a kunne, kuma idan ma tayi reply ba respond saboda andaina aiki da number.

A Yanzu kam abunda takeji yafi gaban mamaki domin kuwa wannan bashi bane na farko, kuma bashi bane ba biyu. Domin idan zata lissafa, wannan abun yakai tsawon wata bakwai. Kuma ko sau ɗaya ba'a taba turamata sako da number iri ɗaya ba. Kuma wanda yake turo saƙonnin bai taɓa barin alama ko ɗaya da zata gane shi ba.

Yasha faɗa mata abubuwa yace daga bakin zohal yake samu, sai dai kuma ita zohal tace batasan da labarin ba sam.

Ko yanzu ta kira zohal ne kawai badan tanada tabbacin samun abunda takeso ba.

"Hello, zohal"

"bestie kun fitane"

"Zamu fita yanzu"

"Lafiya, ko wata matsalar ta faru ne?" Zohal ta tambaya da mamaki.

"Zohal maganar mutumin nan ne da yake turamin saƙo a kowace safiya ta Allah, yau ma yace wai ke kika faɗa masa zamu fita shopping, har yace wai na siyomasa agogon hannu"


"Hmmm, bestie bazaki gane bane, abunnan akwai ɗaure kai wallahi. Amma kiyi hakuri yanzu kije ki dawo idan kika dawo mayi magana in sha Allah ki kwantarda hankalinki kawai Allah ya kai ku lafiya" daga haka zohal bata jira cewartaba ta yanke wayar.













*A bangaren turab kuma yana zaune a parlourn sashen sa, sai faman waya yake yana murmushi cikin natsuwa.

Mum ce ta shigo ɗakin bakinta ɗauke da sallama, ta zauna a kusa dashi kaɗan. Shi kuwa turab ganin mum yasa shi faɗin

"shikenan fahad zankiraka in anjima, ga mum ta shigo yanzu"

Daga cikin wayar kuma aka amsa masa da faɗi"well ba damuwa ka kirani ɗin idan kun gama, kuma kacewa mum ina gaida ita"

"Zataji in sha Allah, sai na kiraka ɗin"

Sallama sukayi kafin su katse wayar, turab ya dubi mum da fara'a "mum, barka da warhaka"

"Yawwa, ya aikin ya gajiyar hanya?"

"Hanya alhmdullillah mum, ai bazanyi tafiya a watan nan ba"

"Saboda me!?" Mum ta tambaya da mamaki "ince dai lafiya"

"Lafiya ƙalau mum, Alex zaiyi aiki dasu a wannan watan domin ni na ɗauki hutu, duk da bai taɓa aiki dasu ba. Amma yanzu na sakashi ya wakilceni"

"To Allah ya taimaka, ya tsare ya bada Sa'a"

"Ameen ya rabbil ibaddd mum"

"Dawa kake waya danashigo ne"

"Mum, da angonmu nake waya"

"Yanzu ya kaji da kace ango turab, bakaji kamar kai ake kira da sunan nan ba dan Allah. Wallahi ni dana shigo na ɗauka da wata kake waya har naji sanyi ashe da fahad ne"

"Eh shine mum muna tattauna maganar auren ne"

Taɓe baki mum tayi tana faɗin "katashi ka shirya zaka kai leeya tayi shopping"

Cikin mamaki ya ɗago da faɗin "leeya kuma, ni zan kaita shopping, duk ina driver's ɗin gidan nan mum. Dan Allah mum kinsan banason raini kho, please karkija yaran nan su rainani nine zan kaita shopping wallahi ni har na manta da wata leeya a gidan nan"


"Har ka manta kho? To na tuna maka yanzu saboda haka ka tashi kaje ka shirya idan kuwa haka zaka fita sai ka tashi muje"


"Mum please kije ki haɗata da driver dan Allah"

"Kai nakeso ka kaita turab, idan kuma bazakaje ba sai ka faɗa min kagah idan zan ƙara maka maganar" mum ta faɗa da bayyanannen ɓaci rai.

"Kiyi hakuri zanje" ya faɗa fuskar sa ba annuri ko kaɗan.











(ROONEY)
Zaune suke su huɗu cikin wata ƴar qaramar rumfa da iyakacin ta mutum huɗu sune abunda take iya dauka domin tayi ƙanƙanta ga Mutanen da suka haura huɗu.

Rumfa ce ƙarama wacce akayita domin ɗalibai su ɗinga zama suna shan iska ko kuma suyi karatun su a ciki.

Amrah ta kalli khulud tace "khulud ya akayi jiya naga wata ta tsayardake tana tambayarki, Ni kuma a wannan lokacin driver na yazo shiyasa banzo naji abunda kuke tattaunawa ba, amma dai kinsa ita ba kowa bace kho. Wallahi babanta custom yake yiwa aiki bama shine custom ba yaronsa ne"

Taɓe baki khulud tayi cikin jin haushi tace "ke rabuta shashashar yarinya, wai gayamin take na fita harakar ku a makarantar nan domin ba wanda kuke gani da mutunci"

"Hmmm, ke kuwa me kika cemata" raudha ta tambaya cike da masifa.

"Ai kema kinsan bazan rangwanta mata ba wallahi, nayi mata wankin babban bargo. Tun a wurin saida tayi danasanin tarona da maganar" cewar khulud tana wani makirin murmushi.

"Wama take da suna" cewar raudha cikin sigar tambaya.

"Ni ko menene sunan ta, inaga kamar sunan ta hibbah basheer"
Cewar amrah da tabbacin abunda take faɗa.


"Haaaaa, hibbah basheer kho, ina ga fa Physics class take zata gane ta shigo gonar mu wallahi, ita menene damuwar ta damu to, tunda bamu taɓa yimata komai ba yanzu zatasan ta taɓomu wallahi dan sai tayi nadama"


Da sauri reemah ta ɗago kanta da faɗin
"me zakiyi mata raudha dan Allah karki saka a koreta a makarantar nan kamar yanda kikayiwa husnah, da kubrah. Kinsan har yanzu wasu suna wannan maganar kuma har yanzu wasu suna dubinmu da wannan zaluncin, kinga hibbah ma bamusan yanda mahaifinta ke fadi tashi yana samun kuɗinda yake kawowa ba, ki wama Allah da Manzonsa karki saka a koreta a makarantar nan"

Wawan kallo amrah da raudha suka jefamata yayinda khulud ta daka mata tsawa da faɗin

"wai kekam reemah menene matsalar ki ne dan Allah, Allah ya bambanta tsakanin mu da talakawa amma ke kin kasa gane haka, ita hibbah da ake magana a kanta ita kaɗai ce a Rooney? Ko kuma wani abu ya taɓa shiga tsakanin mu ne. Bata duba bama ragawa kowa ba sai tayi mana kutse kho, kuma ta rasa wanda zata gayawa sai Ni wallahi batayi a banza ba kuma idan kikaga taci gaba da karatu a makarantar nan, saidai idan Bama nan cikinta"

Khulud ta faɗa tare da janye su amrah daga wurin.



Suna nufin fita daga rumfar ne sukaji muryar Sayyid na faɗin "idan kun rabata da School ɗin nan ai ba da ranta kuka rabata ba kho, to wallahi kun rago tunda bazaku iya fitar da rai daga gangar jikin taba, kuma duk irin zaluncin da kuke tafkawa kuda azzaluman iyayenku, Allah yana gani. Kuma ba mantawa yayi dakuba a hadisin Manzo Allah Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa;
"(IN-NALLAHA LAH-YUMLIE LIZZALIMIN, HATTA IZAA AKAZAHU LAM-YUFLIT-HU)",

[Ma'ana] "Allah yana jingitarwa azzalumai, har sai ranarda suka shigo hannunsa.

"wallahi kuyi gaggawan komawa ga Allah domin cin zalinda kuke yiwa mutane yayi yawa"

Sayyid na gama faɗin haka, ya janye reemah daga wajen.
yabar su amrah na binshi da ido baki sake kamar wanda basu saba ganin sa ba.






A zafafe khulud ta kalli amrah da faɗin"amrah wai sayyid ɗin nan dan gidan uban waye dayake yimana yanda yaga dama a Rooney?"


Murmushi irin najin haushi amrah tayi tare da faɗin "Sanin ko ɗan gidan waye bazai yi mana maganin komai ba, domin tun kafin yau raudha da mahaifinta ba yanda basuyiba kan su fitarda sayyid makarantar nan amma abu ya faskara. Koda suke Wannan mahaifin raudha bai san waye mahaifin sayyid ba, sai daga baya ne daya gane mahaifinsa komai ya tsaya domin idan har bai kiyaye ba raudha ce za'a fitar a Rooney ba sayyid ba"

"Saboda me za'a fitarda raudha alhali ko waye mahaifinsa mahaifin raudha ya fishi matsayi"

"Mahaifin raudha bai fi mahaifin sayyid matsayi ba"

"Hmmm, amrah kenan nadai san mahaifin sayyid bashi bane shugaban ƙasa ba, domin kaff ƴaƴan shugaban ƙasa na yanzu ba wanda ban sani ba, saboda suma familyn mune"

"Eh, mahaifin sayyid ba shugaban ƙasa bane"

"To waye Sayyid" khulud ta tambaya cikin ƙuluwa.

"Yarima sayyid ɗan sarki maleek al-shams"

"What!!?".
Khulud ta faɗa cikin mamaki da kuma tsoro.


Amrah cikin tabbacin abunda take faɗa ta maimaita da faɗin

26 / 61