BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   40 / 61

117K to 120K   out of 180.4K words

bai mata ba wazai yiwa, kalmar da yake yawan faɗa kenan a duk lokacin da ya ke wani aiki daya kamata ace mace ce take yinsa bawai namiji ba.

Bayan sun zauna ya juya da nufin fita gidan "ina zakaje?"

Ya jiyo Muryar khulud na tambayar sa ba tare da ta kalleshi ba.
"Fita zanyi"
"Munzo duba jikin Annah kuma nazo nayi Magana dakai"
"Ina waje idan kin gama abunda kikazo yi"
"Okay" ta faɗa tana mayar da hankalinta ga Annah.
"Annah Allah ya baki lafiya ga wannan" ta faɗa tana fitowa da kudi masu dan yawa daga cikin jakarta.
"Hajiya ƙarama harda dawainiya haka, to angode Allah ya sanya alƙairi"
"Amin Annah, Allah ya baki lafiya"

Daga haka suka miƙe gaba ɗayan su suka fita, mota badar ta wuce ita kuma Khulud ta zauna kan wani yankakken ice dake kofar gidan inda taga id zaune a yanzu.

"Na dauka kayi tafiyar ka kabarmu ai" cewar khulud tana kallon idrak dake zaune.
"Kin taɓa ganin inda mutum yayi bako ya gudu ya barshi"

"Idan mutumin ya zama mara cika alkawari ai zai iya yin haka"

Haɗe hannayensa yayi wuri ɗaya ya langwabar da kansa ƙasa kamar mai roko yace "dan Allah hajiya ƙarama kiyi haƙuri da alkawarin da nayi bancika ba, idan kin bani dama sai na tashi na miki bayanin abunda ya hanani zuwa"

Wani abu ne taji ya tsarga mata a hankali ta furta;

"idrak.........!"

"Nifa bazan taso ba Hajiya ƙarama har sai kin yarda kin yafe min laifin Sa'ba alƙawari danayi"

"Tun kafin kayi laifi indai a wurina ne ka ɗauka an yafe maka saboda bakayin laifi"

"Kina wasa kenan"
Ya faɗa yana kara kasa da kansa.

"Na yafe maka ka taso muyi magana ka gayamin abunda ya saka ka karya alkawarin mu"

Mikewa yayi ya zauna daidai sannan ya kalleta yace "jiya ne fa kikazo nace miki ina nan tafe gidanku, naga kamar kinyi gajen hakuri, jiya da Yamma bayan kin tafi sayyid yazo duba Annah daga nan ya sanar mana da mai martaba nason ganin mu, shine yau muka shirya mukaje, yamana kyauta sosai bayan sayyid yayi masa bayani akanmu shine ya bamu kyautar gida a wata unguwar daban kuma yace zai sama min wata sana'a idan an duba"

Fuskar khulud dauke da murmushi tace"gaskiya wannan abun murna ne kuma Sayyid ya cika aboki yayi kokari kwarai, Allah ya saka masa da alƙairi gaskiya na tayaku murna"

"Muna godiya, wannan shine dalilin da ya hanani zuwa gaskiya, kuma gobe zamuje duba gidan amma in sha Allah zanzo banda gobe karki damu"

Karar kiran waya da taji yana fitowa ne ya sakata shiru bata ce komai ba har saida id ya fito da wayar tana binsa da idanu ya daga wayar ya kara a kunne.

Mintuna uku yayi wayar ya gama, sannan ya kalli khulud yace "sorry ma"

Ita wallahi har mamaki ma yake bata yanda taga yana wani lallabata kamar ba shiba.

"Kodai a kwai wani abu ne" ta faɗa a zuciyarta.

Tunanin tane ya katse lokacin da taji yace "kinyi shiru bakiyi hakuri bane"

"Ah ah ba komai, amma ka gayamin bakada waya kho"

"Eh jiya sayyid ya siyamin wannan"

"Hummm, kyautar Sayyid kawai kakeso ko idrak"

"No ba haka bane naga ba dadi ne kinzo da waya haka kawai na karfe inaaa.............! abun bazai yiwu ba ai"

"Amma kuma Ni na baka ko?"

"Duk da haka ai, amma kiyi hakuri wannan maganar ta wuce. Yawwa nace dan Allah idan nazo gidan ku zaki bani dama na yi Magana da mahaifinki"

"Sosai, me zai hana, ai mahaifina yasan Labarin ka sosai a bakina, mahaifiyata ce kawai ta fara sani yanzu, yan gidan mu ma gaba ɗaya ba wanda bai san labarin ja a wajena ba"

"Tau shikenan na gode da kauna"

"Uhmm--hmmm, bani number din ka tunda sai na roka"

"Roko kuma, ai ba roko bane kawo na saka miki koda baki tambaya ba inada niyyar na baki ai"

"Amma kuma sai da na yi tambaya ne niyyar tazo maka"

"Ah ah tun dazu surutun da muke ne ya hana in fada, idan bakyason number dina to ga wayana ki saka min taki"

Zatayi magana yayi saurin cewa"dan Allah"

Karɓar wayar tayi ta saka number ɗinta sannan sukayi sallama ya rakata har mota suka tafi.

"Wallahi kinci arziki banyi niyar tuki ba har na koma gida da ji kawai zakiyi na tuka motar nan na yi tafiya ta" badar ta faɗa a kufule.

"I'm so sorry sweet badariyyah wallahi bada niya na jima wurinsa ba kiyi haƙuri wani abu ya dan tsayar da mu amma yanzu mun kammala kiyi hakuri dan Allah, muje gida mum ta fara calling"









*________
A can bangaren su leeya kuma yau tunda sassafe sukayi duk aikin da zasuyi suka gama sannan suka shirya tsaff suka tafi gidan su zohal ita da meenal.

Misalin ƙarfe goma sha daya suka isa gidan su Zohal a parlour suka sauka duk da mafi yawan bakin da ke gidan suna parlourn, nan su leeya suka tsaya suka gaida su.

Sultanah ce ta taso tazo inda suke domin su basu ma lura da ita ba.

"Meenal yanzu ake tafe" ta faɗa tana zama inda suke

"Lahhhhh sultanah ai bamu lura dake ba ma wlh yanzu muka karaso"

"Eh ai na kula baku san dani ba, Zohal na ciki bata gama shiryawa ba inaga kaya take sakawa yanzu ta fito wanka tun dazu muna zaman jira baku zo ba har munyi tunanin zuwa gida mu sameku"

"Sai kuma Gashi Allah ya kawo mu, muje cikin to" cewar leeya tana shigewa dakin zohal su kuma sultanah da meenal suka rufa mata baya.

"Besty sai yanzu, mu nan har munyi Magana da driver idan mun fita gidan ku zamu fara zuwa"

"Kaiiiiii, aikuwa da bazaku samemu ba dan muma tun dazu muka fito biya ta shagon mai tela ne"

"Okay tau ba damuwa, sannunku da zuwa meenal zo ki zauna ga invitations nan ki d'ibai wacce zata ishi su mum da kuma su fannah"

Zama meenal tayi ta fara duba invitation din yanda akayita cikin tsari aka bi komai dalla-dallah gwanin ban sha'awa, bayan ta gama dubawa ne ta cire adadin waɗanda za'a buqata a bangaren gidan maza wato su fahad kenan.

"Leeyana inaga waɗan nan zasu isa kho" cewar meenal tana nuna mata yawan invitations din da ke hannun ta.

"Eh mana ai zasu ishesu in sha Allah, ki ajiyesu hannunki idan mun koma gida sai a isar da saqo"

"Muje" sultanah ta faɗa lokacin taga Zohal din ta kammala shirin da take.

Fita dakin sukayi sannan suka shiga inda umma take mahaifiyar zohal sukayi mata sallama sannan suka wuce da driver.


Sai misalin ƙarfe takwas na dare suka dawo gidan su Zohal bayan su gama raba katin gayyatar, sosai suka d'ebo gajiya kuma sunsha yawo.

Sallar magariba da isha sukayi gaba daya domin basu samu sunyi ba, daga Nan kuma suka ci abinci sannan leeya da meenal suka dauki hanyar komawa gida. Sultanah da Zohal kuma kowa ya nufi bed dan rage gajiya.


Washe gari ya kama ranar talata, kuma yayi daidai da ranar da za'a kamu wanda muka sanshi a al'adance shine saka amarya lalle.

Da yake familyn gidan maza wato angwaye basu cika zuwa wurin kamu ba saidai waleemah ko dinner party, shiyasa ƴan gidan su mum basa wani d'oki, meenal da leeya ne kawai suma kuma don suna kawayen amarya ne.

Kasancewar mummy neesah da kuma su twins da dad ƙarami basuda wasu dangi a garin Kaduna hasali ma aiki ne kawai ya mayar dashi garin yasaka suka tattaro wasu kayayyakin su da zasu bukata suka dawo suleja gidan dad babba wato papu, kuma a chan Bhopal India ma an wakilta wasu familyn su mummy-neesah suzo daura auren fahad yasaka akazo dasu su kusan shida a gidan yau.

Sosai gidan su mom ya fara cika da dangi domin a ka'ida duk wanda yake babba gidan sa za'a yi komai dad'in dad'awa kuma har haji-mainah na gidan mahaifiyar kowa a familyn.

Yau saura kwanaki uku kacal ayi komai a gama har daurin aure, domin yau talata kuma ranar juma'a ne za'a daura auren.

Karfe huɗu saura kwata yaran da ke gidan suka shirya zuwa saloon da kuma gyaran jiki. mayah, khulud, badariyyah, da kuma Airah.

Leeya da meenal kuma suka wuce gidan su zohal suyi attending programme ɗin da za'a fara yau.

Da shirin su suka fita gidan da kuma anko da za'a saka yau ranar kamu, zani da dan-kwali iri ɗaya, sai kuma riga ta roba karama mai dogon hannu kalar baki.

Koda suka isa gidan su zohal din sunyi mamakin ganin mutane rututu har haka, sunsan dai a gayyatar da sukayi basu yi inviting mutane har haka ba.

Har inda aka warewa Amarya wurin zama leeya da meenal suka nufa, Zohal yau ba damar a rugo da gudu a tarbi leeya yasa ta sake mata murmushi mai sauti tana washe haƙora, daga can nesa kuma sukaji muryar Sultanah tana kwala musu kira cikin jin dadin ganinsu tana tare da wasu yan mata kimamin mutum hudu itace cikon ta biyar.

Gaisawa sukayi sosai cikin mutunta juna bayan ta ƙaraso wurin, pictures suka fara dauka bayan wasu mutane sun dauka kafin wasu suzo kuma.


"Besty yau meya sameki dan Allah na ganki sanyi-sanyi kamar akwai wani abu dake damunki"

Murmushi leeya tayi wanda tasan zohal zataji tace"besty ina tunanin yanda zan zauna idan an kammala bikin nan naki Ni kadai, meenal tafiya zatayi can yobe kinsani ke kuma kinyi aurenki su badar duk tafiya zasuyi, khulud kuma kinsan makaranta take itama"

Jikin zohal ne yayi sanyi sosai domin itama tanajin abunda leeya keji a game da haka kusan ma tace tafi leeya jin d'acin haka "karki damu in sha Allah komai zai daidaita ai kema ba dadewa zakiyi ba, fahad yace min da yanzu lokaci daya za'a yi auren mu daku amma kuma aka daga naku domin ba'a saka rana ba ma har yanzu, kuma kinga ai estates daya fahad da ya-Turab suke ai koda aure kukayi wuri ɗaya zamu zauna dan Allah ki kwantarda hankalinki ki daina saka damuwa a ranki"

Duk da ƙarar sautin kidan kwarya dake tashi wurin bai hana leeya jin meeting din wayarta ba alamar shigowar saƙo.

Dan dago da wayar tayi ta duba ko ba'a faɗa mata ba tasan wanda ya turo mata saqo messenger dinta ne sunan da su khulud suka sakamasa.

"Me yace?" Zohal ta tambaya lokacin ta fahimci leeya ta isa kammala karanta saqon da aka turo mata.

Mika mata wayar leeya tayi tana shirin dubawa sai ga wasu mutane da alamu dai duk familyn nasu ne.

Da murna suka gaisa gaba daya hade da yimata pic's ita kadai, sannan suka fara dauka a tare, leeya na tsaye jikinta duk a sanyaye ta rasa meyasa kuma tunda taga messengern ta ya turomata sako taji gaba ɗaya yanayinta ya chanja.

Bayan sun tafi ne zohal ta janyo hannun leeya suka zauna, dago da wayar tayi ta karanta sakon da taga antura mata.

Cikin matuƙar farin ciki zohal tace "congratulations bestie komai zaizo karshe in sha Allah, kinga a nan ne zaki sami duk wata dama da kika rasa akansa a baya, wallahi nayi matukar farin cikin ji da ganin wannan saƙo"

Cikin madaukakiyar karaya leeya tace "hmmm, bestie kinsan na kamu da matsananciyar soyayyar bawan Allahn nan? wallahi besty har ina rasa abunda ke damuna a wasu lokutan idan na tuna irin yanda nakeji akansa, besty koma waye wannan mutumin na kamu da sonsa a lokacin da babu wani amfani da hakan zaimin, domin an katangeni da kula duk wani saurayi, a yanzu banida yanda zanyi kuma"

"Allah sarki karki damu da wannan kinji, idan abu rabon ka ne ko mai wuya da rintsi zaka sameshi, kuma idan ke rabonsa ce zai samu. Idan kuma rabon ya-Turab ce ke babu abunda za'a iya yi domin haka Allah ya tsaro tun kan a halicci duniya da abunda yake cikin ta"

Sosai gaban leeya ke duka jin an ambaci sunan ya-Turab ita harga Allah mantawa take da bawan Allahn nan, hasali ma babu shi a lissafin ta na komai.

"Dan Allah zohal kidaina faɗin haka, Ni ba rabon ya-Turab bace in sha Allah"

"Kiyi sauri ki tuba besty"

"Astagfirullah, Allah na tuba" cewar leeya a sanyaye.

"Dan Allah karki kara kwatanta fadin haka, Allah ba ruwansa da komai, kuma ikon kowa bazai hana Allah nashi ba saboda haka ki roki abun da yafi alƙairi kawai kinji"

"Allah kayi mana mafi alƙairi"

"Ameen besty ki tashi muje kiyi rawa yau"

"Rawa! Hmmmm, kin ta'ba gani"

"Bantaɓa gani ba amma ki tashi muje Ni zanyi idan bazaki min ba"

"Zohal bakida dama wallahi, Amarya ba kunya gasu Sultanah can sai bajewa suke amma ke duk bai miki ba"

"Rawar su bata min ba gskiya" zohal ta fada kamar mai rad'a suka kwashe da dariya baki daya.

Haka akayi komai yanda aka tsara da kuma yanda abun yake a al'ada, sai karfe bakwai na yamma aka kammala taron bikin kamu da akayi, meenal da leeya suka dawo gida bayan sunyi sallama da sauran kawayensu.




KADUNA.
CLASSIC ESTATES.

"Zafaran kayi sauri karka jima dan Allah yau nakeso mu tafi, kuma ina so mu kwana suleja yau domin gobe ne za'a yi dinner, kuma na sanarwa duk friends dinmu na Abuja dana nan kaduna harma 'yan suleja ɗin"

"Sorry our groom, gani hanya fa na kusa na karaso saura kadan, ina turab"

"Yana sama yana shirya mana kaya a trolly"

"Soja da kansa, lallai yau sunanka Sa'adatu fahad, turab ne yake shirya kaya a trolly yau"

"Wallahi idan ka zagesa saina gaya masa bazan rufeka ba"

"In rufe kaina mana idan baka rufeni ba ko banada blanket"

"Kanada, ka zaga ka gani"

"Na zaga"

"Bakasan na zama munafiki ba yanzu, muna gama wayarnan zanje na sanar masa"

"Ai mun gama" Zafaran ya faɗa yana dariya.

Fahad zaune a parlour ya ajiye wayar kan table bayan ya gama waya da zafaran, knocking kofa yaji anayi daga waje.

"Waye?" Ya tambaye da mamaki.

"Bude kagani" aka bashi amsa daga waje.

"Lahhhhh, Zafaran dama kana kusa kenan"

"Malam ka bude min kofa dan Allah idan na shigo kayi duk tambayar da zakayi"

"Kofa a bude take ko kai ka rufe ta da zaka fita"

Mirɗa handle din kofar zafaran yayi yajita a buɗe, cikin haɗe fuska ya karaso gaban fahad yace "ina abincina"

Dariya ta kwace wa fahad ganin yanda zafaran yayi kamar da gaske, dama haka suke ta wasa tsakanin su kullum da shi zafaran, suna iya kokarinsu wajen ganin sun mantarda shi soyayyar lewa da ta zamo masa ciwo a zuciya.

"Sorry rankayadade sir, abincinka na daining"

"Allah ya ceceku wallahi da sai kunyi frog jump"

"Soja kenan" fahad ya faɗa yana toshe bakinsa da dariyar da yake.

"Kuyi duk abunda zakuyi idan na kammala cin abinci mu wuce suleja" cewar zafaran yana wucewa daining.



SULEJA STATE.
K. WAASIB MANSION.

"Mun gode sosai ilyass, shiyasa muke sonka da son aikinka Kanada alƙawari wallahi ba kamar sauran madinka ba"

"Nima na gode hajiya khulud, inason yimuku aiki nima Allah ya kara bamu hakurin zama da juna"

"Ameen, jirani na hau sama na sanar wa da mum zuwanka domin batasan kazo ba"

"Ahh, ai da kin barta kawai wata kila tana tare da baki ne tunda kinga gidan nan mutane ne ta ko'ina"

"No, karka damu bari na kirata kawai dan Allah"

"Okay ba damuwa, ina jira"

Miƙewa tayi ta shiga part din mum ta sanar mata da zuwan ilyass wanda shine yake musu dinki, ko yanzu ma ya kawo musu dinkin da suka bashi ne gaba daya.

"Malam ilyass yanzu ake tafe" cewar mum tana sakkowa da ga step.
"Hajiya barka da dare ina wuni ya jama'a"

"Alhmdullillah ilyass komai lafiya Ƙalau, khulud tace an kammala aiki kho"

"Ehh in sha Allah Hajiya, an gama komai ba abunda ya rage"

"Masha Allah, Allah ya saka maka da alƙairi sannu da kokari mun gode sosai"

"Ni ke da godiya hajia Allah ya sa a more Ni zan wuce"

"Okay ba damuwa, Allah ya kai lafiya ga wannan a sha mai kho"

karɓar kudin yayi yana qara yimata godiya, ya fita daga gidan.

Zama mum tayi ta zube kayan ta fara dubawa daya bayan daya, kayan iri daya ne kuma dinkin da akayi ma iri daya ne sai dai anyi alamar suna a jikin ko wace leda, nan hajiya ta kira kowa, leeya, meenal, mayah, Airah, khulud, da kuma badar kowa ya dauki nashi suka tafi bayan sun da d'a yin godiya.

Tafiyar su ba jimawa mum ta kuma kiran meenal, ita da leeya suka fito suka sami Mum a parlor.

"Yawwa ai gwanda da kukazo ku biyu, kun ragemin tafiya wallahi yau duk na gaji.
Leeya je kitchen ki sakawa haji abincin ta ki kaimata sashenta, sannan ki diba wani daban a babban wuri ki je dashi domin akwai baki a bangaren nata"

Miƙewa leeya tayi ta nufi hanyar kitchen tayi abunda aka sakata.

"Meenal ke kuma kije daining abinci na nan a basket ki dauka kije boss quarter maman twins suna nan ki basu, kuma kar inji kin gayawa mayah sunzo"

Cikin mamaki meenal tace "mum meya sa suka zauna boss quarter su kuma?"

"Wallahi su fannah ne suka dage akan haka wai sai sun rama abunda mayah tayi musu tunda tazo har tsowon sati biyu bata taba kira ba ko a wayane ta gaida su, wai ta manta dasu shine sukace idan sunzo bazasu bari ta gansu ba sai dai idan sun hadu wurin dinner"

Tashi tayi batace komai ba taje daining ta ɗakko abunda aka gayamata sannan ta wuce boss quarter.


Ba jimawa ta dawo tuni leeya ta dawo itama, a can bedroom ɗin su kuma sai fira suke, kowa na ayyana irin kyawun da zai yi a wurin dinner gobe, ganin yanda aka kashesu da dinki na ji da gani.

"Kowa yaje ya kwanta dare yayi muryoyinku kadai suke tashi a gidan nan har wajen gate ana jiyoku"

Murmushi mai sauti Airah tayi sannan tace"kunji mamana nayi muku magana kowa yaje ya kwanta, wallahi yanzu nake shirin gaya musu haka sai gaki kinzo"

"Sameerah bana son karya wallahi ai muryarki tafi ta kowa tashi duk a wurin nan"

Shagwaɓe fuska Airah tayi jin mamanta ta kirata da asalin sunanta sameerah "mama Ni kullum bana abu kice gaskiya ne komai dai karya, ai sai kisa su badariyyah su raina ni tunda ke kika fara"

Wani mugun kallo badar ta jefa wa aira tace"Aunty zainab ki yiwa Allah ki tafi zamu kwanta, kuma idan kin fita ki ja kofar dakin nan kiyi locking, yau sai naga wane irin raini ne ya shiga tsakani na da wannan yar taki wallahi.
Mu fa kannen ki ne, ita kuma yar ki amma sam bata bamu girman mu da Allah ya bamu"

"Zanyi duk abunda kika ce domin ko ni da nake mahaifiyar sameerah ta raina ni balle ku da kuke qannena amma yanzu ku

40 / 61