BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   35 / 61

102K to 105K   out of 180.4K words

a hankali ta kalli mum, sannan kuma ta mayarda kallonta ga haji tace "mum uwace a gareni, a kaffff faɗin duniyar nan banida uwa kamar mum, kuma mum ce matar da Allah ya wakilta ta zamo gatana a Duniyar Nan. Idan akwai wani matsayi da daraja daya take mahaifiya to na kira mum da wannan sunan saboda ta wuce haka a wurina, tayi min abunda ba kowace mace bace zata iya yinsa, mum ta kauna ceni lokacinda kowa yake guduna, mum ta soni lokacin da ba wanda zai yarda a kirasa masoyina, mum ta fito dani daga kunci ta saka na zama mutum kamar kowa. haƙiƙa babu kalaman da zanyi amfani dasu wajen fassara matsayin wannan baiwar Allah a wurina, amma kiyi hakuri da wannan dana bata saboda ta wuce haka a wurina"
Leeya ta karashe magana da hawaye a fuskar ta har ga niqab ɗin ta.




Kan Turab na laptop dinsa sai dai ba aiki yake da ita ba, ya.kofa kansa ga laptop din ne kawai saboda bayason yana kallon ko inuwar leeya idan ta fito ɗakin balle ita kanta.
Maganar da tayi ne ya sake jefashi wani yanayi "me wannan sha-sha-shar yarinya take faɗa, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Allah ka taimakeni ka saka peace of mind a zuciyata kada kalaman mum, da haji, da kuma wannan munafukar yarinya su tarwatsa min kwanya" ya faɗa a zuciyarsa da ta ke yawan wani suya mai Kanada ɓacin rai.





Allah sarki!. Cewar haji cikin tausayawa.
Duk wanda yake zaune wurin saida jikinsa yayi sanyi sosai da ji furucin leeya, ga kuma kukanda take mai ban tausayi shima.
Mum dai kallonta kawai take tana ƙarajin soyayyar ta ta daban a cikin ranta.
Ita dai tana kallon ta kamar ƴar cikinta.

"To menene matsayin Khattab a wurin ki?"

"Haji matsayin papu dana mum duk ɗayane a wurina, kamar yanda na ɗauki mum shima haka na ɗaukesa, wallahi haji kunyi min komai a rayuwa banada abunda zance muku, ladarku tana wajen mai duka. Ina rokonsa ya saka muku da mafificin alƙairi"

"Ameen thumma Ameen leeyanatu, ba komai Allah yayi albarka kinji".
"Ameen ya rabbil ibaddd"
"Kenan zaki iya yin komai saboda ki faranta musu"
"Wallahi haji a kullum tunanina mezanyi na farantawa mum da papu"
"Shikenan, kwanan baya kafin zuwanku asibiti mun zauna munyi tunanin, kuma fanaya ta bada shawarar haɗa aurenki da yayanki gashi nan zaune abu turab, kuma mahaifinsa ma ya bada goyon bayansa ɗari bisa ɗari, sanna shima abu-turab ɗin anyi Magana dashi kuma ya amince, ke kaɗai ake sauraro munyi alƙawari bazamu taɓa miki dole ba, idan bakyaso wallahi baza'a baki ba sai kin kawo wanda kikeso saboda haka ki faɗi gaskiyarki ba wanda zai miki dole sai kin yarda".

Wani abu mai Kanada tsoro da fargaba taji ya dira a zuciyar ta, daga nan kuma taji wani ƙololo ya tokaremata maƙoshi wanda ya hanata cewa uffan sai bin haji take da idanu kamar bata taɓa sanin ta ba.

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" ta furta a hankali cikin zuciyarta, nan taji komai ya tafi kamar ma ba maganar akayi ba.

"Wallahi haji kar Allah ya nuna min ranarda mum da papu zasuyi iko akaina na ɗaga murya, nasan gata sukayi min kuma a yanzu na ƙara tabbatar da soyayyarsu gareni gaskiya ce kuma ta tsakani da Allah tunda har suka ɗauki ɗan su na cikinsu suka haɗani dashi a matsayin wanda zan aura, papu mum Nagode Allah ya bani ikon yimasa biyayya, Allah ya sanya alƙairi a tarayyar mu, ya kuma bamu ikon hakuri da junanmu, Allah yasa hakan shine mafi alƙairi a cikin Rayuwar mu, Allah ya baku ladar haɗin zama da kukayi, Nagode sosai" har ta gama Magana hawaye bai daina gudu a fuskar ta ba, ita kanta bata san ma'anar hawayen nan dake fuskar ta ba. ko tambayarta za'a yi akansu batada amsa.

"Allah yayi muku albarka LEEYANA"

" Turab!" Papu ya kira sunansa yana kafe shi da ido, sai yanzu ya ajiye laptop din da ke hannunsa ya mayarda hankalinsa gaba ɗaya kansu, domin duk rabin abunda ake hankalinsa baya kansu.

"Na'am pa" ya amsa kiranda akayimasa.

"Kaji abunda ƙanwarka kuma matarka nan Gaba kaɗan ta faɗa kho"

Sai da ya runtse idonsa da karfi yana cije bakinsa yace "naji pa,. Ameen Allah ya bamu zaman lafiya"

"Yawwa, haka akeso Allah yayi muku albarka baki ɗayanku"
Nasiha papu da mum harma haji suka yi musu kafin daga bisani ya sallamesu suka fita ɗakin tare.

Bai cemata komai ba, ita ma haka har suka kawo inda zai bi ya shiga sashen sa, yayi tafiyar sa itama ta shigewarta, ikon Allah ne kawai yasakata ƙarasa sashen su domin kukanda yaci karfin ta, Sa'arta ɗaya mum na sashen haji.

Da karfi ta banko kofar ɗakin nasu tare da zubewa kan gado ta saki kuka.

Dayake duk sun san abunda take yiwa kuka yasa hankalinsu bai wani tashi ba sai dai sun rarrasheta sosai, har suka samu kukan ya ɗan tsaya.

"Haba matar yaya dan Allah kidaina haka mana, yanzu yasu haji zasuji idan ɗayansu yasameki kina irin wannan kukan, Ni shawarar da zan baki idan bakya sonsa kije kawai ki faɗa"

"Haba badar ya zakice haka, kindai san ya-Turab ɗan mum ne kho, wallahi duk yanda kike gani mum bata damuwa dashi sosai ba, ba hakan yake nuna idan anyi masa abu bazataji haushi ba ɗanta ne na cikin ta fa, kawai dai kunyar nan ne ta fulani da suke nuna rashin kula ga ƴaƴansu na fari, wallahi idan leeya tace bata son ya-Turab mum bazata taɓa mantawa da itaba kan wannan abun, kuma wallahi mum sai ta kalli tsantsar butulci ne leeya tayi mata"

"Gaskiya meenal kinada kyakkyawar zuciya, wallahi da wata ce kamar ke yanda kikeson ya-Turab yaƙi amince wa dake, da dabakinki zakice leeya taje tace bata sonsa Allah dai ya baki mafi alƙairi a rayuwarki"

Dago d blue eyes ɗin tayi da sukayi wulu-wulu saboda kukanda tasha ga kuma colour ɗinsu ta blue ta sake fitowa gwanin ban tsoro ta kalli meenal tace "Allah sarki ke kinaso Allah bai baki ba, sai ni da bamtaɓa kawo hakan a raina ba"

"Kedai leeya kidaina faɗin haka, kici gaba da addu'a kawai idan hakan ne alƙairi Allah ya tabbatar, kuma da kikaga haka Allah ya fiki sanin dalilin sa nayin haka"

"Wallahi ni duk ba wannan bane araina, a rayuwata naso sanin bawan Allahn nan daya damu dani ina mafarkin zama dashi, amma kaddara ta riga fata, in sha Allah zan gaya masa komai, amma wallahi naso nasan wani abu daga gareshi har sunansa ma ban sani ba balle nasan garin da yake dama Asalin fuskar sa gaba ɗaya"

"Leeyana kina nufin kice ko sunansa baki sani na"

"Kwarai kuwa khulud bansan sunansa ba a kullum idan na tambayeshi sunansa sai yace na kirashi da komai nakeso, domin ba abunda zan iya sani akansa sai lokaci yayi, wallahi Nima bansan na damu dashi ba kuma ina qaunar sa sai yau danaji zancen nan, yaa Allah ka taƙaitamin wahala"
Da faɗa da Muryar kuka.

"Ameen" duk suka faɗa suna ci gaba da rarrashin ta..............✍🏻





BAYAN WUYA.....



















EP.37
















___________________tayi shiru kamar ba abunda ya faru har fira mai daɗi ta ɓarke a tsakanin su, sai tsokanarta suke matar yaya ko matar soja, ko kuma sucemata matar likita. tun tana yimusu magana bataso har ta ƙyale su ko sun faɗa sai dai ta murmusa bata ko kulawa.

Yau Monday yau kuma khulud zataje duba result ɗinta kafin ayi closing ceremony na karshen kowace shekara da akeyi a Rooney.

Sosai suka bata shawarwari yanda zata tunkari id da Sayyid da kuma yanda zata ƙanƙan da kanta ƙasa wajen nuna nadama kan abunda tayi musu, cikin shawarar da suka bata kuma harda nuna mata tayi masa ƙayatacciyar kyauta.


Gaba ɗayan su suka shirya suka rakata tayi masa shopping, sosai suka kashe kuɗi kamar me, duk abunda suka gani indai maza na amfani dashi sai da suka siyawa id.








KADUNA STATE.
"Mum yaushe zamuje dan Allah? Tun wancan satin fa twiney ta tafi har yanzu ko leƙe bata leƙomuba, kinsan wallahi dai ta jima da yawa kuma gashi maganar tafiyarmu ba'a ce komai ba"

"Gaskiya mum ya kamata muje muma musha suleja kafin a tashi bikin, zama wuri ɗaya ba daɗi tun da nan ko fita bamayi"

"Ko can kukaje bazaku fita ba Rukhshanah, nasan halin dadynku Babba bazai bari ku fita ba. Amma kuyi hakuri tun da saura kwana takwas, idan muka tashi zuwa sai muje ba dole sai munbi tafiyar mayah ba tunda kho tunawa da mutane batayi"

"Eh wallahi mummy kinga idan mukaje muce a saukemu bisa quarter tunda ba kowa a ciki idan zamuyi wani abu zamu yishi har mu gama ba wanda zai ganmu a cikinsu kar mu fito mu bari sai idan an fara programme ɗin bikin sannan muyi shiri mu fito, kinga ma a lokacin zata gane kuskurenta domin sai ta yita kiran number ki don a aikomata da kayan da zata saka na fitar biki. To a lokacin da ta kiraki tana tambayar kayan a lokacin zamu rama abunda tayi mana mu daina ɗaukar wayanta itama taji idan da daɗi"

"Yes!!, gskiya kin kawo shawara Sweet fannah haka za'a yi amma dai nasan mum bazata bari ba gaskiya"

"Mum wai bazaki bari mu rama abunda tayi mana ba?" FANNAH ta faɗa da alamar tambaya.

"Zan bari mana, me zai hana ai harda ni aka yiwa kinga kho nima dani za'a yi mata".

"Mummy ana kiranki a waya amma kin saka wayar silent shiyasa bakiji ba" cewar Rukhshanah tana miƙawa mummy-neesah wayar.

Karɓar wayar mummy-neesah tayi tare da picking call ta kara wayar a kunnen ta "okay ku shigo kawai, kuma ki turo account number na turomiki sauran two millions ɗin, gobe kikace za'a kawo sauran kayan kho, ok gani zuwa bara nazo na buɗe muku Ni banji knocking ba ai da bazan barku tsaye a waje ba kuma da kaya" cewar mummy tana katse wayar.

"Rukhshanah"
"Na'am mummy"
"Waya rufe sashen nan su hajiya Aƙeesah sunzo sun tararda kofar a rufe"
"Wallahi mummy bani bace sai dai kho fannah"
"Tunda ni kika raina kho, to bani bace junior ne daya dawo daga islamiyya ya rufe na jishi lokacin da yake saka key wallahi" fannah ta faɗa tana nufar kofar sashen.

"Rukhsha ki tashi ku taya su shigo da kayan".
"Wane kaya mummy, yanzun nan fa muka dawo nidai na gaji gaskiyar Allah".
"Ki tashi bana son ragwanta, Rukhshanah bakyason aiki kho wallahi ina guje miki ne baki san inda Allah zai kaɗa ki ba nan gaba kadan".
"Bansaniba mummy amma kiyi min fatan inda zanje na huta" .
"Ita ake yimuku kullum Safiya" faɗar mum yayin da mutane suka fara shigowa da wasu manyan akwatuna masu matukar ɗaukar ido.

Ihun murna Rukhshanah ta farayi, da gudu ta nufi kofar parlourn taje itama a jido akwatunan da ita, domin ita da aka ce kaya bata yi tunanin akwatunan lefen ya-fahad bane.

Masu gadin gidan su uku aka kira sai kuma hajiya Barira da ƙawarta hajiya Aƙeesah wanda su suka haɗa lefen har Dubai sai FANNAH da kuma Rukhshanah su suka shigo da kayan gaba ɗaya akwatin sets biyu ko wane set yanada akwatuna takwas sai kuma hand bag ɗaya da travelling bag itama.

Sosai aka cika akwatunan da kaya kala-kala kamar kayan zasuyi magana da kansu, ba jaka ko akwati da ba'a zubamata kaya ba a cikin akwatuna, sosai naira ta koka ba sauqi.

"Gaskiya kayan nan sunyi kyau sosai, kuma qualities ne daga gani".

"Kedai bari kawai hajiya neesah, ai indai mune wallahi zaki samu kayan ki yanda ma bakiyi tunani ba, domin mu tsakanin mu da Allah muke kasuwancin mu ba cuta ba cutuwa".

"Hakane hajiya Aƙeesah ai naga alama wallahi, kuma muna godia sosai domin kaya sunyi kyau Masha Allah, yanzu ku bada account number na cika muku alkawari"

Account number ɗin su suka bata ta tura musu 2 millions ɗin da suka rage harda ƙarin dubu ɗari biyar sama na godiya da alkawarin da suka cika mata da kuma gaskiyar da suka yi mata.
Sosai hajiya Aƙeesah da Hajiya Barira suka ji daɗin haɗuwar su da Hajiya neesah wato mummy, sun ɗan jima a gidan bayan sun ci sun ƙoshi suka wuce.

Fannah da Rukhsha kuwa sai videon kayan suke suna haɗa pics ɗin zohal da Fahad suna ɗorawa a status.

Kayan sunsha Magana sosai inda kowa yake yabawa, sai sakawa kayan albarka ake, kan kace me magana duk ta karaɗe families sai zuwa suke suna dubawa aka saka ranarda za'a kai kayan gidan su amarya.
















*SULEJA STATE*
ROONEY.

sanye take cikin hijab abaya har suna ja ƙasa kalar maroon da powder colour.

Wasu daga mutanen dake harabar makarantar sai kallon ta sukeyi cike da mamaki ganin ta da hijab.

Hango motar AMRAH tayi tana tahowa, wuri ta samu ta raɓe har motar ta karaso kusa da ita.

"KhUlud kece haka da wannan shigar kamar wata ƙasaitacciyar Malama"

Sosai khulud ta Haɗe fuska tace "bansaba yin shigar bane da zakice haka"

"Maida wuƙar mutuniyar bani na kar zomon ba rataya aka bani"
"Kanki dai ake ji amrah, ina raudha?"
"Raudha suna capteria tun ɗazu ita da reemah"
"Okay muje musamesu nayi missing ɗinku"


Fitowa AMRAH tayi daga motar taci ado cikin blue T-shirt ta mata mai adon kore, sai black Tony skirt da kuma ƙaramin mayafi iya kafaɗarta kamar dai yanda suka saba fitarsu.

Tare suka jera har suka isa, sosai mutane suka cika a wurin da yake safiya ce mafi yawan mutane basu fara lactures ba.

Basu wani sha wahalar ganin su ba domin raudha ma data gansu ta kira wayar khulud ta gaya mata gefen da suke, suna isa wurin khulud ta zaune kujerar da ke kusa da ta reemah.

Har khulud ta buɗi baki zatayi magana aka kira reemah rabeel da waya "sallamu alaikum,
Yawwa barka da safiya,
Okay har kun shigo kenan,
Kuna wane gefe,
Eh na gane jirani kaɗan gani nan tafe"
Reemah ta faɗa tare da yanke wayar, handouts ɗin ta ta ɗauka da handbag da carkeys ɗinta "friend's kujirani ina zuwa yanzu zan dawo abu nakeso naje a nuna min"

"Okay sai kin dawo" amrah ta faɗa hankalinta na kan wayarta da take Street a Snapchat.

"Ina zakije reemah"
"Baya zanje yanzu zan dawo jirana ake naga kamar kinada magana kho khulud, ki bari idan na dawo sai muyi maganar kinji"
"Okay sai kin dawo, kar ki manta saura 30mns mushiga lactures kiyi sauri karki ɓata lokaci, kuma kinsan result ya fito kho"

"Eh nasani idan na dawo sai muje mu duba" cewar REEMAH tana barin wurin.

Bayan mintuna goma sha biyar da tafiyar reemah su khulud sukayi order din abinci, suna kammala cin abincin basu jira komai a capterian ba suka koma ANATOMY. Har zata saka waya ta kira reemah sai ta hango ta zaune a class.

Bayan wasu awanni, block ɗin da ke kallon ANATOMY suka nufa cikin fara'a kowa yana fata a ransa result ɗinsa yayi kyau, khulud sai rarraba ido take a harabar wurin ko zata hango id domin ko a class bata samu ganin shi ba kyau.

Numfashin ta ne yayi ƙoƙarin tsayawa sakamakon hango shi da tayi gaban notice board inda aka liƙa result ɗin, wani irin fitinannen kyau yayi mata baƙar shaddace a jikinsa da aka yiwa adon kwaɗo ruwan zuma, sosai kayan suka yimasa kyau inda kwantaccen sajensa ya kara kwanciya lif a fuskar sai wani sheƙi fuskarsa take ga hasken fatarsa ya fito daidai misali.

"Masha Allah" ta furta a zuciyarta "ina ma inada damar da zan faɗa maka kayi kyau" ta faɗa ƙwallah na cikowa a idanun ta.

Wayarta ta fito da ita ta fara ɗaukarsa hoto ta yanda ba wanda zai gane photo take yimasa, tuni su AMRAH da REEMAH da RAUDHA sunyi gaba basu san ma me take ba.
Sai da tayi masa hotuna masu isarta sannan ta mayarda wayarta jaka ta ƙarasa wurin, bata nemesu ba ta fara duba sunanta, sai da tayi godiya sosai ga Allah bayan ta ga sunanta kuma taga result ɗinta daga nan tayi snapping shima domin ta nuna idan taje gida.

Sai yanzu ta lura da su amrah basa wajen, kuma da taje inda suka ajiye motocin su taga motar AMRAH bata nan ita raudha driver ne yake kaita shiyasa bata gane tana school ba ko kuma ta wuce gida.
Sai dai reemah ita motar ta na nan alamar tana nan kenan, Boot ɗin motarta ta buɗe tare da fito da manyan ledojin da tayiwa id siyayya guda biyu ta nufi cikin makarantar dasu, domin ta ɗauki alwashin yau sai anyi duk wacce za'a yi tagaji da dakon soyayyarsa a ranta tana wahalarda ita.

Dayake reemah tasan da batun kuma duk a cikinsu ita kaɗai khulud ta labartawa kan soyayyar da take cinta a zuciya, number ɗin reemah tayi dialing ringing biyu ta ɗaga wayar "hello khulud, kin duba result ɗin"
"Eh wallahi na duba kuma alhmdullillah ba abunda zance saidai in ƙara godewa Allah".
"Kice anci baza kenan".
"Meye banza reemah?"
"Uhmm--hmmm kaidai bari kawai wallahi result ɗin nan yayi banza da yawa wasu mutanen kam basu ma je dubawa ba saboda sunsan sun cinye".
"Wallahi kuwa, kina ina haka"
"Yanzu haka ina hango ki amma ki biyo hanyarda kike strect idan kikaci gaba da tafiyi zaki ganmu"
"Okay" khUlud ta faɗa wayar na kunnenta.
Cigaba sukayi da maganar har ta fara hangosu daga nesa, saida ta hangesu sannan ta kashe wayar ta ƙarasa wajenda suke zaune

Sallama tayi lokacin da ta iso wurin, su uku ne a zaune a wajen reemah da sayyid suna zaune wuri ɗaya, sai kuma id dake zaune gefe dasu kaɗan amma duk cikin rumfa ɗaya suke zaune.
Reemah kawai ta amsa sallamar id da Sayyid kam kamar badasu take ba damar ma shi id ya amsa sallamar amma a yanda ya amsa ko da kana kusa dashi bazakaji ba balle kuna nesa da juna.

"Ina wunin ku, sayyid ya karatu"
Nan ma bai amsa ba.
Cikin jin ɗacin abunda ya faru reemah ta kalli sayyid tace "sayyid bakaji khulud ba gaida ku ba"
Fuskar sa a tamke bai ko dago da kansa ba muryarsa a dakile yace "sorry banjibane, lapiya alhmdullillah" ya faɗa bai ko kalli inda

35 / 61