Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
tafiyar su,
"Haƙiƙa gaskiyar mutane da suke cewa idan tashin hankali yayi maka yawa kuka ma neman sa zakayi ka rasa,
Sabida yanda nakeji a yanzu dama zansamu kukan yazo da zaifimin sauƙi, yau ba Abbi, Ammi, da kuma uchie gashi kuma ƴan bindigan nan sun tafiya da Aleena da Nnene, gashi babu okene ya tafiyarsa.
Runtse idanuwanta tayi da ƙarfi, domin ji take wani abu yana taso mata tun daga ƙasan zuciyarta tamkar zai fito ta bakinta, da jan ciki ta isa bakin ƙofar ɗakin gidan nasu tare da jingina kan bangon gini, wasu hawaye ne masu zafi suka fara tsartuwa a fuskarta yayinda komai ya shiga dawomata kamar yanzu akayi.
Gaba ɗaya leeya ta kasa sanin abunda zatayi taji daɗi, ko ta samu nutsuwar zuciya, domin kuwa ko rufe idanuwanta tayi sai taga kamar ana haskamata hoton fuskokin su uchie da Nnene.
Ta ɗauki tsawon kwanaki cikin matsananciyar damuwa, domin kuwa bataci balle tasha ba wanka ba komai,
Sallah ce kawai ke tada ita a inda take zama a gidan nasu, komai ruwa da iskan da za'a yi tana nan wurin bazata ɗaga ba.
Duk ta rame ta fita hayyacinta domin kuwa idan har bakayiwa leeyana farin sani ba zaka iya rantsuwar cewa ba ita bace wannan leeyanar da kasani.
A kwana na tarane da rashin su uchie aka yiwa leeya saƙon mai gidan yana bukatar gidansa domin ya saka wasu masu hayan tun da baza'a bar gidan ba kowa ba.
Lokacin da saƙon ya isowa leeya tayi kuka sosai da baƙin cikin barin gidan, bawai barin gidan ke yimata baƙin cikiba, akwai abubuwa da dama acikin gidan da take gani ta dinga tunawa da su uchie da Nnene da kuma ƙanwarta abar begenta dare da rana.
Bata kwashi wasu kayayyaki ba, domin kuwa bata san inda zata je daga nan ba, shiyasa bata ɗiba kayan komai ba.
Wasu abubuwan da take matukar ƙauna a rayuwar ta ne kawai su ta dauka da suka zamo mata abokan tafiya.
Ƴan kudaden da tagani ne wajen binciken nata ta ɗauka tare da barin gidan, tana fita kuwa ta kira mai jirgin ruwa da zai fitarda ita tekun.
Daga fitarta cikin tekun ta rasa inda zataje kawai sai ta yanke shawarar zuwa AJAH ROAD tashar motoci, ba kuma dan tayi tafiya zuwa ko ina ba, saboda ko tafiyar zatayi ba inda tasani ko a cikin lagos ballantana wajen Lagos ɗin, ko AJAH ROAD ɗinda taje ta santa ne a hanyar islamiyyar su idan zasuje IFE.
Duk nisa da tazarar da ke tsakanin MAKOKO da AJAH ROAD haka tayi tafiyar a ƙafa ko nisan ma bata gani har saida ta ƙaraso a haka.
Wuri ta samu a inda ba mutane sosai ta zauna tare da kifa kanta tsakanin cinyoyinta, ta fara tunano komai daya faru a rayuwarta tun daga farko har izuwa yanzu data baro MAKOKO.
Daga kanta tayi sama yayin da takai ƙarshe a tunanin da takeyi idonta sharkaf da hawaye, while fuskar ta na lulluɓe.
CIGABAN LABARI.
Miƙewa tayi daga zaunen da take, ta samu wuri ta ajiye jakarta data fito da ita, sannan ta nufi wani ƙaramin wuri da ake siyarda abinci domin tanada sauran kuɗin da tasamu a gidan su a makoko.
Tana isa wurin sauran mutanen da ke zaune suna cin abinci suka ganta, dayawa daga cikinsu sun tsorata da ganin ta, wasu ma har sun fita daga wurin cin abincin.
Ganin ta ya tsorata mutane sosai a wajen, domin kuwa kamanninta duk sun chanja, baramma mayafin na fuskar ta, ga gashinta duk ya hargitse gashi da tsawo na wuce misali, gashin ya zubo gaban fuskar ta ya rufe ko ina a fuskarta ta.
Sai idan tana tafiya ne take gyara shi domin taga hanyar da zata bi da kyau.
Kuma idan ta janye gashin maimakon aga fuskar ta sai mayafi kawai ake gani, da manyan korayen idanunta masu matukar razana mutane, sannan kuma ga wani mayafin da ta rufawa jikinta, wanda ya zamo kamar hijab ne.
Sai kuma kayanta da sukayi datti sosai, sabida rabon da tayi wanka tun lokacin da abun ya faru.
Ba takalmi a ƙafarta gashi tana tafiya jiri na kwasarta kamar zata faɗi.
Haka ta iso wurin da ake siyarda da abinci, aikuwa mutane na ganin ta suka fara guduwa domin kuwa basu zata mutum bace, hatta waɗanda suke aiki a wajen da ake siyarda abincin saida suka bar wajen ƙalilan ne masu ƙarfin halin da suka tsaya suji mai yazo da ita.
A lokacin kuma wacce takeda shagon abincin ta harziƙa sosai domin kuwa ta kore mata customer's, gigitacciyar tsawa ta daka mata tana faɗin:
"ke wacece ke meya kawoki nan wurin?"
Leeya kuwa saboda tsorata da tayi da wannan matar bata iya furta komai ba sai kyarma da jikinta yakeyi saboda tsoro
Matar kuwa tana ganin haka ta janyo wani kwano da ruwa cikinsa tare da watsa wa leeya ruwan, ta daka mata tsawa
"bar nan kuma idan kika sake dawowa ruwan zafi zan watsa miki"
Matar ta faɗa fuskar ta haɗe.
Da guda leeya ta bar wajen sai kuka take, inda ta ajiye ta koma, ta rakuɓe waje ɗaya tana ta rawar ɗari.
★★★★★★★★★★★★
NAIJA STATE.
SULEJA NIGERIA..
K. WAASIB MANSION.
durkushe take gaban wata yarinya da bazata wuce shekaru goma sha daya ba a ƙiyasi.
hakuri take bata iya iyawarta amma yarinyar ta kasa ɗaga ko kanta balle ta kalli matar da ke durkushe gabanta.
Matar kuma zata iya kai shekaru arba'in zuwa sama.
"dan Allah hajiya ƙarama kiyi hakuri wallahi bansan kin parlourn nan bane da ban biyo ta cikinsa ba, tunda nasan dokokin ki, taya zan karya da ganganci, kiyiwa Allah kiyi hakuri"
matar ta faɗa tana ƙara sunkui da kanta ƙasa gaban yarinyar.
Har wannan lokacin yarinyar bata ɗaga kanta ba balle tayi mata magana, taci gaba da yin game ɗinda take a wata makekiyar tab dake hannunta.
Wata murya taji ta daki dodon kunnuwanta, wacce tasan mamallakiyar muryar, mum ɗinta ce:
"KHULUD me kikeyi haka, me DAYAMMAH tayi miki ne da zaki sakata durƙusawa a gabanki kamar wata Sa'arki.
Khulud ki kiyayeni ranki zaiyi mummunan ɓaci na rantse miki idan baki chanja halayenki ba, menene wannan tho?"
Matar ta faɗa a zafafe.
Guntun tsaki yarinyar da aka kira da KHULUD tayi sannan ta miƙe a fusace tare dayin cilli da tab ɗinda ke hannuta ta nufi sashenta bata ma kula mum ɗin ta da ke yimata faɗa ba.
Zama mum tayi tare da yiwa dayammah izni da ta miƙe daga durƙushen da take:
"Dayammah dan Allah meyasa kike biyewa khulud, ita ƙaramar yarinya ce fa sa'ar ƴar da kika haifa da cikin ki, saboda me zata sakaki yin abu kiyi, tunda baya cikin ƙa'idar aikin ki, dan Allah ki daina kinji kiyi hakuri kuma"
mum ɗin ta faɗa tare da dafa ƙafaɗar dayammah Alamar ban haƙuri.
Murmushi kawai dayammah tayi bata furta komai ba, tashi tayi daga durƙushen da take sannan tace:
"ba komai wallahi hajiya, ae hajiya ƙarama batada laifi, duk laifina ne, nina ƙarya dokar da ta kafamin. Amma wallahi bada ganganci nayi ba domin kho bansan da ita a parlourn nan ba shi yasa na biyo ta cikinsa"
Ɗan jimmm mum tayi kafin tace:
"kuma nagayamiki ki daina kiran KHULUD da wani hajia ƙarama, da badan kar nayi ƙarya ba da zance kinyi jika da wannan yarinyar amma kina kiranta da wani hajia ƙarama ae dolene yarinya ta rainaki"
"Uhmmm ah ah babu rainawa hajia, ai ko rainawanne nina rainata tunda kinga itace sama Dani"
"A ina khulud zata zama sama dake"
Mum ta tambayi dayammah Cikin jin haushin abun da tace.
"Hmmmm a ko ina hajiya, domin kuwa na dogara ga Allah, sannan kuma na dogara wajenku, da badan ku ba da bansan yanda rayuwar nan zatayi mana ba"
"Toh saboda wannan ne zakice khulud na sama da ke"
"Ehh hajiya ko ba don wannan ba, kin manta saida KHULUD ta yarda sannan Alhaji ya ɗaukeni aiki a gidan nan"
Dafe goshi mum tayi tare da faɗin:" ohh god dan Allah dayammah ki daina tuna abunda ya faru baya, koda haka ta faru kuma khulud batada wayo koda akayi wannan, babu abunda ta sani a wannan lokaci, kawai ta yarda a ɗaukekine bawai dan tasan amfanin da zakiyi mana ba"
"Hajiya kuma a wannan lokacin da khulud bata yarda ba da baza'a ɗaukeni ba, kinga kho dole nane nayi abunda tace na kuma bar abunda tace idan ina son zaman gidan nan"
Murmushi kawai mum tayi
"Tau Allah ya gyara amma dai gaskiya ki rage wannan da kikeyiwa khulud dan wallahi rainaki zatayi a haka, ko babu komai kin haifi kamar ta koma waɗan da suka fita".
"Hmmm hajiya duk abunda nayiwa hajiya karama girmanta ne da Allah ya bata babu kuma abunda zanyi tunda ta shiga gabana, kedai kiyi shirunki kawai komai nada lokaci"
Dayammah ta faɗa tana kallon ɓangaren khulud.
Taɓe baki mum tayi kafin tace:" ɗazu naji justice na tambayarki ayi list ɗin kayan da babu a gidan nan amma dai bakiyi ba ko?"
"Ehh banyiba hajiya, wallahi na ɗan sha'afa ne amma yanzu zanyi in Allah yaso".
"Tau babu damuwa kije kiyi dan Allah Saboda tafiya zaiyi gobe zaije visiting Mexico kuma nasan zaiyi one-week shiyasa nakeso kiyi komai yanzu"
"Tau in sha Allah yanzu-yanzu kuwa zanje nayi"
juyawa tayi ta koma hanyar kitchen taje ta dubo abubuwan da babu a bangaren ta na girki.
domin kuwa hakane ɗabi'ar justice KHATTAB WAASIB a duk lokacin da zaiyi tafiya to sai ya samu duk ƴan aikin gidan suyi list ɗin abubuwan da za'a bukata bayan tafiyar sa,
ummu-hajara ce House-maid ɗin gidan shiyasa aka umurce ta datayi list ɗin kayan kitchen da babu a kitchen
Khulud;
banko ƙofar shahararren part ɗin nata tayi kamar zata karya kofar.
ɗaki ɗaya ta nufa daga cikin ɗakunan da suke part ɗin, daga isarta ta faɗa kan gado sai wani zafi takeji yana fitowa daga cikin zuciyarta, ta jima tana juye-juye kan gadon kafin ta tashi tsaye.
Kai da komowa ta fara a cikin ɗakin tana cije lips ɗinta tare da buga hannun ta ɗaya ƙan ɗaya tana tafawa a hankali tana daga kai tana saukewa kamar wacce ta saka jami'an tsaro a gaba tana yimusu jawabi.
"Me mum tayi haka, gaban wata ƙasƙantacciyar talaka, ƴar aiki mum zatayimin faɗa Alhali banida laifin komai, shine zata yimin faɗa a gabanta but it's well dayammah sai kin gane kuskurenki da kika saka ayimin faɗa kuma alhali kece mai laifin ke kika karyamin dokar da na kafawa ma aikitan gidan nan, dama nayi alƙawari duk wacce ta fara karya dokar nan sai nayi mata hukunci gwargwadon laifin da ta aikata, ke kika fara karyawa sannan kuma kika saka aka yimin faɗa, good"
KHULUD ke maganar tamkar ba ƴar shekaru goma sha daya ba.
Murmushi tayi sakamakon tunawa da tayi da wata shawara da tazo mata a zuciyarta, fita tayi daga part ɗin tare da nufar part ɗin papu wato mahaifin ta, cikin tafiyar ta irin da isa da jin kai tamkar wata ƴar sarki.
tafiya take kamar bataso ta taka ƙasa har ta ƙaraso part ɗin papu.
Knocking kofa tayi tana faɗin:"excuse me"
"Yes"
Wata murya ta amsa mata daga cikin wani master bedroom.
Da fara'ah a fuskar ta, taƙarasa har ciki tare da nufar papu da ke zaune.
"Good morning my kid"
"Morning too pa, how's your night going?"
"So gud mamanah, ina mum ɗin ki take? Yau kin rigata zuwa tadani kinyimata mata wayo"
Papu ya faɗa da murmushi kwance kan fuskarsa.
Wani uban tagumi taja tare dayin mirmir da idanu zata yi kuka,
Da sauri ya sakko daga kan gadon da yake, ya nufi fabric-bed sofa ɗinda take zaune, hannuta ya riƙe tare da faɗin:
"mamana waya taɓamin ke, ki gayamin ko waye nasan dalilin sakaki kuka da yayi"
papu ya faɗa yana rungumota jikin sa.
Kamar wacce akayiwa ɗan karen duka ta fara magana:
"pa, mum ce"
"Me mum ɗin tayi miki?" Papu ya tambaya.
"Pa a gaban House-maid ɗin nan, talaka da ita ƴar talakawa, a gabanta mum tayi min tsawa"
"Tsawa!"
Ya faɗa da kakkausar murya kamar wanda akace masa wuƙa aka yanka mata.
Ita kuwa tana ganin haka sai ta fashe da kuka mai sauti saboda haƙonta ya cimma ruwa.
Tunda tayi kuka a gabansa.
Idan za'a tambayi papu abunda ya tsani gani shine ɓacin ran khulud, balle har takai ga tayi kuka.
"Haba my kid kuma my mum kiyi hakuri ƴar lelen papu da mum ki tashi muje gaban mum ɗin taki naji dalilin da yasa tayi miki tsawa gaban mutane"
"Pa, nifa ba tsawar ce tabani haushi ba inda akayimin tsawarne yasa naji haushi, gaban ƴar aiki fa talaka hmmm"
ta faɗi maganar tana ƙara sautin kukanda takeyi.
Sosai papu ya rikice ganin ulud na kuka har hawaye wasu na izar wasu, rarrashin ta yayi sosai, amma taƙi ta daina kukan har sai da yace zaije da ita shopping idan zai fita yanzu sannan ya samu ta yarda zatayi shiru kuma koda haka saida aka yi sharaɗi kan cewa zai jawa mum uban warning karta ƙara yiwa khulud tsawa ko tsakaninta da ita ne balle gaban ma'aikatan gidan nasu.
Komawa papu yayi kan gadon da ya sakko tare da rufe laptop ɗinda ke ajiye sannan ya dauki phone's ɗinsa tare da barin ɗakin, bayansa tabi tanata dariya a cikin zuciyar ta, idan kaga fuskar ta a fili kuma zakace dukan tsiya akayimata abunka da farar fata har fuskar tata tayi jaaa sakamakon kukan da tasha a ɗakin papu, idanunta kuwa sunyi jajir kamar barkono.
* * *
JUSTICE KHATTAB WAASIB,,,,,,,,
Dan asalin garin kaduna ne, aiki ya kawoshi garin Abuja, amma a suleja yake zaune da iyalinsa, zakuyi mamakin jin cewa a Abuja yake aiki amma kuma yana zaune a suleja da ƴaƴansa da matarsa.
wannan kuma tsarine daya fito daga ƴar autarsa wato KHULUD KHATTAB WAASIB, khulud yarince ƙarama, saboda ko a shekaru ma bazata wuce goma sha daya ba.
amma tanayin abunda ko babba bayayi domin kuwa batada tausayi ko kaɗan.
A duniya babu abunda khulud ta tsana kamar talaka, domin kuwa idan akwai yanda zatayi da saita ɓatarda kowane talaka da yake faɗin duniyar nan.
mahaifinta shine babban gishiƙinda yasa khulud keyin yanda taga dama domin kuwa idan ta aza doka ba wanda ya isa yace takkkkk kan abunda tace.
Mahaifiyarta HAJIA FANAYA wato (MUM) ita kaɗai take takamata birki a wasu halayen nata, kuma koda haka sai idan mahaifinta baya nan ne, ba ita kaɗai bace ƴa a wajen su justice ba, sai dai itace mafi soyuwa a ransa.
Domin kuwa yana matuƙar ƙaunarta har yanda zan kasa yimuku misali, ƙaunar khulud a zuciyar papu dabance data kowa, kuma gashi sunan mahaifiyarsa ce aka sakawa khulud shiyasa papu yaƙi jinin yaga abunda zai taɓa khulud ɗinsa idan ko yana nan sai inda ƙarfinsa yaƙare.
Koda ulud tayi kuskure papu bazai taɓa nuna mata kuskure bane komai tayi daidai ne wajensa, kuma komai tsada da wahalar abu idan ulud ta nema wajen papu sai ta sameshi.
Babban abunda yake damun mum Bai wuce wannan ba, sau dayawa tana yimasa magana akan haka amma basa kwashe wa da daɗi domin kuwa shima kanshi papu yana matuƙar jin haushin azo a gayamasa laifin khulud, shi a kullum khulud bata laifi a wajensa.
"Justice wallahi wannan abun na damuna, dashi nake kwana da shi nake tashi, wallahi wannan ba gata bane justice ace kamar mamana du-du-du nawa khulud take da za'a ce sai abunda tace akeyi a gidan nan kowa bayada ikon kansa sai nata.
A gaskiya justice wannan ba ɗabi'a bace. Khulud macece a kwana a tashi yau da gobe girma zatayi a kaita ƙarƙashin wani, wallahi justice ba namijin da zai ɗauki shashancin wannan yarinyar a haka, kho mu da muke iyayenta hakuri kawai muke, kaga koh ba wani namijin da zai ɗaukar mata wannan, gaskiya ka canja kawai kaima domin kuwa wannan ba gata bane.
"Kin gama! Nace kingama? Tashi ki fita idan kin gama" papu ya faɗa yana nuna mata kofa fuskar sa a haɗe.
Baki sake mum tabi papu da kallo har tsawon wasu mintuna,
Da sauri ya buga mata tsaya: "I Said out, koba zaki fita bane ni na fita na baki wuri"
Miƙewa yayi yana nufin zura takalmansa, mum ta tashi ta fita da sauri tare da dafe bakinta tana shirin sakin kuka, daurewa tayi kawai tayi tare da barin abun a ranta ta fara ambaton Allah a zuciyarta, kafin ta tsaya ta saita kanta sannan ta fita wajen resting-room ɗin.
Sau dayawa idan mum tayi wa papu maganar khulud tayi wani kuskure haka suke rabuwa koma fiye da haka.
~~~khulud kuma Daga fitarsu part ɗin na papu suka nufi master parlour ɗin gidan inda sukeda tabbacin zasu tarar da mum yanzu, tafiya suke ba wanda ya ƙara faɗar komai tsakanin papu da khulud,
"Pa, amma dai bazaka gayawa mum nina kawo ƙararta wajenka ba kho?"
"Kona gayamata me zatayimiki mamana, ae ba wanda ya isa ya taɓaki, kwantar da hankalinki kinji, kibarni da mum ɗin taki kawai"
"Ah ah gaskiya pa karkace nina gayamaka kaga tafiya zakayi wallahi idan ka tafi zata iya yimin abunda yafi wannan"
"Hmmmm mamana kenan, kece kike sakawa ranki wannan kawai amma idan mum ɗinki nason ganin farincikina yayin tafiyar nan da zanyi to dolene tayi miki yanda kikeso kuma kidaina sakawa kanki damuwar komai domin kuwa ina nan''
Wani farin ciki ne ya ziyarci zuciyar ta yayinda taji papun ta yayi wannan maganar nan take taji wani ƙwarin gwiwa ya shigeta.
Suna ƙarasowa parlour sai khulud ta sami wuri ta tsaya domin ta tabbatar wa kanta bazataje ko ina ba sai taga anyiwa mahaifiyarta warning.
"Pa, ka kirata idan batanan saboda banji motsin ta Anan ba kwata-kwata".
"Gani anan, lafiya dai kho my kid meke faruwane" faɗin mum dake ƙaraso cikin parlour tana ɗauke da tea flasks zata kai daining.
domin haka take bata zama sai anyimata aikace-aikacen gida, tare take aikinta ita da ƴar aikin su wato dayammah domin bata yarda da tsarin sakewa ƴar aiki ragamar gida ba.
Juya fuska khulud tayi gefe ta ɗauke kanta daga kallon mum, mum kuma tana ganin haka tayi murmushi domin tasan nufinta tunda ta ganta tare da papunta a wannan lokaci, domin kuwa lokacin yin break fast baiyiba a gidan nasu. Haka yasa ta fahimci khulud ƙara ta kaita wajen papunta.
"Morning justice, an tashi lafiya? Kace yau mamana ce taje ta tasoka kho"
Da murmushi shimfiɗe a fuskar papu ya amsawa mum gaisuwar da tayi masa:
"Lafiya ƙalau hajjaju,