Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
yanzu, dan Allah ki dan jira kadan ko Allah zai saka yanzu"
Da mamaki lulluɓe a fuskar Aunty Rafa'at ta kalli leeya tace"waye kuma zafaran leeyanah"
Cikin zuciyar leeya kuma cewa tayi "wanda aka d'aura mana aure dashi mana" a zahiri ma hakan ta so ta fad'a, amma gudun kar Aunty Rafa'at tace batada kunya yasa tace "wanda zamu zauna dashi a gidan nan"
Ko kusa Aunty Rafa'at bata gane abunda leeya ke cewa ba tana shirin yin magana kuma sai ga kira new number ya shigo wayanta.
Tana ɗaga wayar ta gane ashe drivern da aka turo ne yazo ya dauketa, Bayan sun d'an gaisa ya gayamata daidai inda yayi packing.
"Zan tafi Leeyana, ki jira kaɗan kinji, ba laifina bane wallahi baban twins ne ya bada wannan umurnin. Amma zanzo gobe tun da sanyin safiya"
"Ok Aunty ba damuwa sai kinzo goben, Allah ya bamu ikon taahi lafiya" leeya ta faɗa a sanyeye.
Miƙewa Aunty Rafa'at tayi ta fice daga gidan bayan sunyi sallama da mai gadi.
Leeya kuma bayan fitar Aunty Rafa'at da kamar mintuna goma tana zaune inda ta barta.
Ta rasa abunda zatayi ga yunwar da ke addabar cikinta, ga kuma gajiya, sannan ga alama tana ji kamar zazzaɓi yakeso ya kamata.
Tashi tayi daga parlorn ta shiga bedroom dinda zai ci gaba da amsa sunansa nata halakh malakh.
Tana shiga ta cire dogon hijabin da ke jikinta da riga da zane na atamfa.
Wurin da aka ajiyemata akwatunan kayanta da suka zo dasu ta nufa ta dakko riga da wando na yadi mara nauyi ta ajiye akan bedsofa, sannan ta ninke wadanda ta cire ta bude closet zata saka.
Ido ta zaro waje ganin yanda aka zauna aka jera uban kaya na sakawa dunkakku, sake bude wuri na biyu tayi anan ta kuma cika da mamaki ganin wasu kayan daban da ba dunkakku ba. Da sauri ta bude ta gabanta, qananan kaya ne na bacci da kuma na shan iska na roba dana yadi mara nauyi colours kuma masu kyau da daukar idanu.
Wata gown ta hango pitch mai matukar kyau, da sauri takai hannu ta janyota, abun ban sha'awa kuma tana janyo rigar cikin ledarta sai ta ganta har qasa kuma ga wani dan qaramin tsararren hijab da hula mai kyau.
Murmushi ne ya subucemata babu shakka rigar nan ta shiga ranta, kuma ita zata saka yanzu. Ji tayi kamar tazo ta zube kayan gaba ɗaya taga yanda suke.
Fitarda rigar tayi sannan ta mayarda riga da wandon da ta dakko bayan ta gyara kayan yanda ta samesu.
Toilet ta wuce ba jimawa ta fito da wanka ta kuma yi alwala.
Sai da tayi duk sallolin da tasan suna kanta kafin ta isa gaban mirror.
Ta bata lokaci sosai gaban mirror domin cikakkiyar yar kauye ta zama lokacin da ta ganta gaban mirrorn da ke bedroom ɗin ta, kayane jere a wurin birjit wasu bata san yanda zatayi amfani dasu ba, wasu kam ko ganinsu bata taba yi ba hatta shi kanshi mirrorn abun kallo ne balle kayan da aka jera kamar babie bedroom.
Zama tayi a wurin ta dan gyara jikinta ta shafa abunda zata shafa sannan ta saka kaya ta nufi inda ta hango perfume display, tana isa wurin ta bude cabinet din ta fito da wani turare mai sanyin qamshin furanni ta fesa ko ina ajikinta, sannan ta juya ga show glass shima ta buɗe ta dakko roses bottle shima ta shafa humrah kamar yanda tayi da turare.
Nan take kuwa kamshi ya garwaye dakin kamar zai danwama a haka.
Hular kayan ta saka bayan ta gama cumbing gashinta sannan ta sanya hijab.
Shafff ta manta dare ne take irin wannan shiri kamar wacce zataje biki.
Gaban mirror taje ta tsaya, tanaso ta kalli fuskar ta. Amma kuma tanajin tsoro ganin yanda halittar ta take sanin cewa har yanzu ba'a daina jin tsoron ta ba domin ko ɗazu da ta fara bude fuskar ta sai da aka gudu.
Rumtse idanunta tayi sosai ta lalubi lamp side dinda ke gefen mirrorn ta kunna, nan take kuwa haske ya kuma bayyana tarrr kamar da Rana tsaka.
A hankali take bude idanunta kamar batason amfani dasu har ta bude su tarrr akan fuskar ta dake zane kan tangamemen mirrorn ta.
Gaban ta ne yayi wani azababben faduwa da sauri taja baya ta rufe fuskarta da tafin hannunta biyu tana mayarda numfashi.
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me zan gani? Wazan iya yiwa wannan tambayer. Ni mutum ce ko kuma aljan? Idan Ni aljana ce ya akayi ban gane ba, idan kuma Ni mutum ce taya zan kasance haka"
Saurin fadin "Astagfirullah" tayi sanin ba abunda zai gagareshi yasa tayi shiru ta zabga tagumi kawai tana jinjina Al'amarin a ranta.
Duk abun zan gayamuku Dangane da halittar kyau da tsari da Allah yayiwa leeyanah dole sai na ragemata wasu abubuwan domin ba yanda za'a yi mutum ya iya siffanta ainihin kyawun da Allah ya bata.
Babban dalilin mahaifiyar ta na sakata rufe fuska kuwa shine; tun ranar da aka haifeta mutane na cike da mamakin irin kyau da Allah ya bata, tun tana yarinya qaramarta, kamar hawainiya ce dake chanja kala, ba rana ta Allah da baza ka ganta kaji ta shiga ranka ba, sau shida ana yunkurin kashe iyayen ta domin a saceta a gudu da ita, da suka fahimci haka sai suka tattara nasu E nasu suka bar garin gaba ɗaya.
Da suka dawo lagos kuma sai suka dinga boyeta sosai amma kuma hakan bai yiwu ba domin tuni mutane suka ankara da haka, abunda ke faruwa a nan kuma duk mai sauki ce bisa da inda suka baro domin nan iya hoto ne kawai ake zuwa ana yimata, har takai ta kawo anfara zuwa ana fita da ita unguwa ko wani biki ko taro.
Ranar da wata mata tazo ta fita da ita har dare basu dawo ba, tun suna ganin abun kamar wasa har ya kasance abun ya fara damunsu sosai.
Basu san inda zasuje su nemi matar ba Bayan gidansu,
gidansu kuwa sunje yafi a qirga sai ganin suke gidan sanye da key.
Sai misalin ƙarfe goma sha biyu har da mintuna arba'in na dare matar ta dawo gida hankalin ta duk tashe, leeyanah kam tayi kuka har ta gode Allah.
Da sauri suka rungumeta suna kuka itama leeya kukan take a lokacin bazata wuce shekaru uku zuwa hudu ba.
'Dagata sama abbinta yayi ya d'orata akan kafadar sa yana qoqarin yiwa matar sallama su shiga gida, sai a wannan lokacin ya lura da ammi dake magana da matar gefenta kuma wasu jami'an tsaro ne su kusan hud'u.
Da yayi tambaya kuma aka gayamasa wai abinda ya tsayarda matar shine a hanyarsu ta dawowa wasu mutane suka tare su da motoci guda biyar suka sakasu tsakiya, wai leeyanah suke nema ta basu ita ko kuma harbeta.
Tasha kuka da roqo amma ko kallon ta basuyi ba, sai da ta ga kamar da gaske suke zasu iya harbe ta ya saka ta miqamusu leeyanah.
Daga chan bayan su kuma qarar harbin bindiga suka fara jiyowa yana dumfarar wurin. da sauri barayin suka fara neman gudu amma inahhh sun makara domin jami'an tsaron ne sukayi musu qawanya.
Karbar leeyanah sukayi daga hannun mutumin da ya dauketa, sannan suka yiwa matar magana aka wuce da ita office ayimata wasu tambayoyi.
sukuma barayin aka tafi da su matsayin masu laifi.
Sai da akayi musu tambayoyi kafin aka sakosu suka dawo gida.
Wannan shine dalilin da yasa suka jima sosai basu dawo ba, Ammi tayi kuka har tarasa yanda zatayi.
Anan ne suka yanke shawarar boye fuskar ta ga kowa har sai lokacin da zatayi aure domin idan tayi aure zata zama a qarqashin kulawar mijinta da kuma tsaron sa.
Mayafi aka fara rufemata fuska dashi sannan sukayi nisa sosai da unguwar da suke suka koma IFE inda babu wanda suka sani kuma ba wanda ya sansu...............✍🏼
45.
______________Babban dalilin da yasa ake zargin leeyana da maita shine wata rana sun fito da amminta zata rakata islamiyya sai suka had'u da wani saurayi dan mai unguwar da suka da suke zaune.
Tsayardasu yayi yace don dole sai ammi ta budewa leeyana fuskar ta ya gani, ammi na kuka ta ke rokonsa akan yayi hakuri da wannan quduri nashi domin tana gudun abunda zai sami leeya ko ya yake, qoqarin fizgar leeya yayi daga rikon da ammi tayi Mata, cikin Rashin Sa'a ya fizgo mayafinda ke lullube da fuskarta.
Wani irin mugun ja da baya yayi yana qara kureta da idanu a hankali kuma idanun sa suna lumshewa har ya fadi qasa, ko motsi bai baiyiba lokacin da ya fadi shikenan rai yayi halinsa sakamakon bugawar tsoro da zuciyar sa tayi lokaci ɗaya.
Haka aka tabbatar wa mahaifinsa bayan gwajin da aka yimasa asibiti, ga mutanen qabila ne basuda dangana yasa suka ce sai sun kashe leeyana da amminta tunda suka kashe babban yaron mai unguwa Abiola.
Babbar sa'ar da sukayi shine gidan da suke ciki ba nasu bane da tun a ranar da abun ya faru zasu iya qona gidan gaba daya, da kyar da sudin goshi da sasancin ƴan sanda aka shiga tsakaninsu sukaci gaba da zama unguwar, amma kuma kowa tsoronsu yake yana gudunsu, qalilan ne suke mu'amala dasu.
Ammi kuma bata fasa da horar da leeya akan saka mayafi ba domin hakan babbar kariyace a wurinta.
Ammi ta hana leeyanah kallon madubi kuma. domin hakan zai iya zama illa a wurinta, ko kuma tayi amfani da kyawun da Allah ya bata ta lalata rayuwar ta.
Shiyasa ammi ta hana leeya duk waɗan nan abubuwa tsawon shekara da shekaru.
Wannan shine takaitaccen tarihin leeya da kuma babban dalilin da yasa take boyewa kowa fuskar ta.
*
Tun daga farkon shigowar sa parlourn wani sassayan kamshi turaren roses ya tarbeshi, a zahirin gaskiya da ace yana cikin asalin mood dinsa ne da babu abunda zai hana masa tsayawa ya shaqi qamshin domin ya tafi da imaninsa sosai.
Bakinsa yayi masa nauyi sai tunanin abunda ya dameshi yake tun daga gate da yayi sallama bai qara yi ba sai da ya shigo tsakiyar parlourn kuma ko a parlourn sau daya yayi, idan ma mutum baya kusa da shi sosai bazaiji abunda yace ba sai dai yaga vakinsa na motsi kawai.
Tana cikin baccin da ya shareta taji qarar ajiye wani abu mai nauyi dai-dai inda saitin kanta yake.
Tun kafin tayi yunkurin wani abu ya fara magana da muryarsa mai kamada wanda ya tashi daga bacci yace "ko wacece ke to kisani ba dan ina sonki zan zauna da ke ba, kisani zama ne kawai zakiyi matsayin matarda aka dauramin aure da ita batare da sona ba, karki taba tunanin zan soki, domin zuciyata ba taki bace na riga na sadaukarda ita. Karkiyi tunanin wulaqanci ko tozarci daga gareni akanki, wallahi bazan taba wulaqantaki ba tunda akwai haqqinki akaina, kuma zan sauke miki duk wani haqqinki daya rataya akaine, ke kuma ruwanki ne ki sauke haqqina da yake kanki, ruwankine ki qie saukewa wannan tsakanin ki da wanda ya rataya miki haqqin ne, kuma wannan da nayi karkiyi tunanin so ne ko wani abu mai kamada haka, wallahi ko kadan ba digon sonki cikin rainah, kinji na gayamiki.
Nasan kinyi wanka, kuma kinyi sallah. Good gara da kikayi haka domin kin haqiqance bazan yi wannan dake ba kho, kamar yanda ake kawowa ko wace mata abinci a first night kema ga naki nan ki tashi kici tsirai ne da fresh milk kuma ki tashi idan kinci ki kwanta sai da safe.
Da wani matsananci kuka ta mike tsaye ta kunna electric LED din da ke kusa da ita domin hasken bedside lamp kawai ta bari saboda bata iya bacci cikin haske, ba tare da ta waiwayo gareshi ba take magana domin a iya qamshinsa da taji ta gama gane shi, balle kuma ga muryarsa da takeji na sauka a kunnuwanta.
"Dama kai aka auramin! kaine aka auramin? Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Wallahi ba dole bane sai ka soni.....!
kuma dama nasan ba sona din kake ba, menene soyayya ta zata amfane ka idan ka soni, koda baka faɗi da bakinkaba,
na riga nasan baka sona, balle kuma gashi ka faɗi, kamar yanda kasan biyayya tasa ka aureni nima wallahi rashin sani ne da biyayya ta sa na aureka duk da bakai nayi zaton aura ba.
Kaje kayi rayuwarka a Cikin gidan nan nima nayi tawa, duk da sanin da nayi cewa zamanmu zaiyi wahala tare a gidan nan domin bama zama inuwa d'aya hakan bazai saka na sare tun yanzu ba, na rokeka kaje kayi rayuwarka nayi tawa har zuwa lokacin da Allah ya iyakance mana" leeya ta faɗi maganar cikin gazawa da karayar zuciya.
Turab da yayi suman tsaye ya kasa cewa uffan, ko a cikin zantukan ta ba komai yake iya fahimta ba. Ko kusa bai yi tunanin haka ba, bai taɓa kawowa a ransa wai leeyanah zata tsaya kusa dashi har haka ba balle ma ace ta zama matarsa, mallakinsa, muharramarsa.
Sharaff yaji ta zube kan gado, qarar fad'awar ta kan gado ne ta mayar dashi hayyacinsa daga tsunduma kogon tunanin da yayi.
Da sauri ya isa kan gadon ya fara jijjiga ta amma ko motsi batayi ba, sunanta ya fara kira da qarfi yana jijjiga ta amma har a lokacin tana nan yanda take.
Da sauri yayi hanyar toilet ya ɗibo ruwa ya ajiye ruwan sannan ya kamata ya sauketa qasa ya fara zubamata ruwan da ke hannunsa, kusan sau uku yana dibo ruwa yana zubamata amma ko yatsarta bata motsa ba balle ita kanta.
Addu'a ya fara yi a bakinsa yana tofamata hadi da shafa mata addu'ar kowane sashe na jikinta.
Bakinsa ya kafa kan hancinta ya fara hura mata numfashi da qarfinsa.
Ya kusa mintuna biyar a haka kafin yaji tayi ajiyar zuciya mai nauyi.
Hamdala yayi yana godewa Allah a ransa, a fili kuma kiran sunan ta yake tun tana bude idanunta a hankali har ta budesu tarrr a kansa.
Wani wawan zabura tayi lokacin da ta ganshi kusa da ita sosai, da azama da kuma sauran qarfin da takeda ta tureshi kusa da ita bayan ta tashi.
"Sannu leeyana, bansan abunda ya sameki ba haka kawai naga kin faɗi, Allah yasa da sauqi" turab ya fada yana matsowa kusa da ita.
Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassara leeyanah ta daga idanunta da takeji kamar zasu fado qasa Saboda tsananin nauyi da zugin da suke mata Sakamakon kukan da tasha tace "na rokeka ya-Turab dan Allah ka fita rayuwata, wallahi kamar yanda kace baka sona nima bana sonka, kuma bazan taɓa sonka ba, kada ka yarda ruɗaɗɗiyar zuciyar ka ta vaka zan soka wata rana idan kuma kaji hakan kayi gaggawan cire shi a ranka domin bazai taba faruwa ba".
Kamar ya fashe da kuka haka yake ji zuciyarsa nayi masa raɗaɗi, cikin kwantar da kai da nuna nadama yace "dan girman Allah leeyana ki tsaya ki saurareni, wallahi ba ina nufin abunda ke kike nufi bane. Kamar yanda kikasan baki san mijin da aka auramiki ba, Nima bansan matar da aka auramin ba. A tunanina wata matar daban ce aka auramin wacce ba ke ba, banjin zan iya rayuwa a wuri ɗaya da wata matar sabanin ke. duk a tunanina bake aka auramin ba domin banyi zaton na mallakeki har haka ba, shiyasa dana shigo gidan nan bankula da ke bace ko kuma bake ba har na fara magana kawai, amma wallahi ko cikin mafarki kika ji Ni nace bana sonki yakamata ki qara qaryata mafarkin har a zahiri domin kinsan wannan bazai ta'ba yiwuwa ba, dan Allah kiyi haƙuri, ki yafe min kura kurainah dana miki wanda kika sani da wanda baki sani ba, dan Allah kinji na roƙeki" turab ya faɗa yana durƙusawa kasa da gwiwoyinsa.
Wani irin haushinsa take ji mara misali, ya bata tausayi sosai amma kuma zuciyarta taki bata hadin kai wajen nuna masa yafiyarta gareshi. Wani kallo ta jefa masa dana kasa gane nufinta.
"Ya-turab inaso inyi bacci dan Allah ka fita ka koma parlour ko kuma Ni na fita na baka wuri, sorry kuma ka fita da wannan tarkacen naka domin ko yunwa zatayi sanadina bazanci wannan abun da ka kawo ba"
Kamar turab ya dora hannunsa aka yayita rusa kuka yakeji, muryasa na cracking yace"dan Allah leeya.........."
Katseshi tayi da faɗin "in fita in barmaka dakin ne?"
Cikin taurin zuciya da juriya yace "shikenan zan tafi in baki wuri leeyanah, sai ki saka wani abu a space din da na tare miki, na miki alqawarin nisanta dake kamar yanda kika buqata, dole nasan wata rana ko babu raina ki tuna irin son da na ke miki, sannan ku tuna yanda kike wulaqantani, ki tuna yanda nake rokonki akan ki zauna dani, ki tuna komai da ya shiga tsakanin mu tun ganina dake na fari, dole nasan zaki tuna da haka idan kika juya idanunki gabas, da yamma. Kudu da Arewa na wannan duniyar bakiga mai kamada Ni ba balle ki gani. Nagode da sakayyarki gareni. Inaji kamar bazan sake kai gobe ei war haka da rayuwa ta ba, a yanda nake maganar nan sai naji kamar wasiyya ce kawai nake gayamiki. Leeyana ki dauka kamar da gawa kike magana yanzu domin bana tunanin zankai labari bayan babu ke a cikinsa. Nagode sosai ina fatar samun kwanciyar hankali da kyakkyawan dare a gareki dream gurl, Allah ya sada mu Da alƙairi" turab ya faɗa wasu zafafan hawaye na sauka daga cikin idanunsa.
Juyawa yayi ya kalleta, ya kusa seconds talatin a haka kafin ya juya ya tafi ba tare daya sake kallonta ba.
Zama tayi jagwabbb kan gado ta fashe da wani rikitaccen kuka. Kalamansa sun saka zuciyarta saqa sosai, ta rasa wane mizani zata ɗora zancensa wajen gane abunda yake nufi. Tausayinsa ya kamata sosai tanaji kamar ta bishi parlour ta bashi hakuri amma sai taji bazata iya yin hakan ba.
Tunani kala-kala ta dinga yi a daren ko isasshen bacci bata samu ba har aka kira sallahr asuba.
Miƙewa tayi jiki a sanyaye ta shiga toilet ta ɗora alwala ta fito tayi sallah, bayan ta idar ta d'akko hisnul Muslim ta fara dubawa har sai ta alfijir ya keto.
Fita tayi parlourn domin ta samu ta tsaftace shi duk da tasan Lafiya qalau yake.
Tasha mamaki sosai na rashin ganinsa da tayi parlour.
"Maybe ya biya wani wurin daban da aka tashi daga masallaci" ta faɗa a fili.
Knocking taji anyi, bata ankara ba sai taji tayi murmushi, babbar tambayar da tayiwa kanta sanin