Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
komai ba, muinda ake packing ɗin mota muka iso ya buɗe kofar ya fito nima na buɗe na fito.
Office ɗin likitan da yakeda duty muka shiga bayan yayi tambaya angayamasa wanda zamu gani, bai nunamin komai ba a asibitin shiya tsaya yayi komai har aka kammala yimin abunda za'a yimin.
Allurai aka yimin, kuma aka aka sakamin drip gora ɗaya, bai je ko ina ba har ruwan ya ƙare domin ni bacci ma nayi bansan abunda ake ba.
Ina farkawa na ganshi a ɗan gefe dani yana danna wayarsa ba abunda ke damunsa, cikin raunananniyar muryata dana keyi a duk lokacin da yake zaune kusa dani ko kuma idan na ganshi nace "ya-Turab dan Allah ka kiramin zohal inaso nayi magana da ita na bar wayana a gida"
"Ki bari idan kin koma gida ki kirata amma bazan baki wayana ba" ya faɗa ko kallon inda nake baiyiba kuma bai fasa danna wayarsa dake hannunsa ba.
"Dan Allah ya-Turab......"
Cikin tsawa da ɗaga murya yace"nace bazan bada ba kho, idan kuma ke kika siyamin wayar kizo ki karɓa" ya faɗa yana miƙa wayar Alamar ta karɓa.
Kamar dai kullum hawayene ya cika mata idanu bata sake cewa komai ba ta mayarda kanta zata kwanta taji yace"kinajin yunwa ne, ko akwai abunda kike buƙata ki faɗa fita zanyi yanzu, kuma ga su mum da haji da sauran ƴan uwanki nan tafe, saura idan sukazo ki faɗa musu wani abu, kindai san hausawa sunce "nuna sani a kasuwar jahillai, wautane" idan kuma kina musu ki faɗa musu kigani"
"Bana buƙatar komai" .
na samu kaina da faɗar haka batare da na kalli gefen da yake ba.
"Hmmm" kawai ya ya faɗa yana barin ɗakin.
Fitarsa ba jimawa kamar da mintuna biyar zuwa shida ya dawo, tun daga ƙofar ɗakin na fara jiyo hayaniyar ƴan gidan mu, sosai raina ya cika da farin ciki koba komai zan sha iska yanzu. Domin zaman ya-Turab a tare da Ni ba abunda yake ƙaramin sai wulaƙanci da tozarci.
Tana tsaka da tunanin tane taji muryar zohal na kwala sallama lunch bag a hannun ta.
Sosai farin ciki ya cika ranta samakon ganin abokiyar ta ɗaya tilo,
Da sauri ta ƙaraso inda leeya ke kwance hankalinta duk a tashe.
"Besty Leeya bakida lafiya har haka kuma baki sanarda ni ba, dan Allah zama yace haka"
Cikin sanyin jiki irin na marasa lafiya leeya ta tashi zaune sosai tana fuskantar zohal tace"zohal kiyi haƙuri Kinji, wallahi nima bansan ciwon zai kai har haka ba. Jiya ne fa da safe kuma wallahi tun lokacin ban ƙara amfani da waya ba balle na kiraki na gayamiki amma kiyi hakuri kinji"
"Ba komai fa, kawai dai banji daɗi bane wallahi, Allah ya baki lafiya".
"To amma waya gayamiki banada lafiya ne"
"Wallahi gobe mukayi niyar mu rubuta invitation kuma kinsan dole sai dake za'ayi komai, shiyasa na kiraki ɗazu da safe na gayamiki ki shirya gobe za'a rubuta, sai kawai naji khulud tana gayamin wai bakida lafiya tun jiya har ma ankai ki asibiti"
"Ina su khulud ɗin suke"
"Tare muke dasu da kuma ya-Turab amma Ni na rigasu isowa gaskiya bansan meya tsayardasu ba"
Leeya na shirin yin magana sai sukaji an buɗo kofar.
Airah ce sai kuma mayah dake bayanta.
Da sallama suka shigo dakin suma suna ɗauke basket food.
"Leeyana ya jikinki"
"Jiki alhmdullillah Airah, ya gida"
"Lafiya lau munata kewarki"
"Ai naji sauƙi wata ƙila ma za'a sallame mu yau"
"Tau Allah yasa, amma inaga kamar hakan zaiyi wuya, dan naga ya-Turab yakai papu wurin likitan da ya dubaki, har likitan ya bashi takardar da za'a shiyo magungunan da allurai".
Airah na gama faɗin haka sai ga mum, haji, meenal, badar da kuma khulud sun turo ƙofar gaba ɗaya suka shigo.
Sosai suka nuna damuwarsu yanda suka ganta duk tayi wani iri kamar ba ciwon kwana biyu ba.
KhUlud ce ta matso kusa da ita sosai bayan tayi mata ya jiki tace "leeya waya gayawa saurayin ki bakida lafiya"
Sai da gabanta ya faɗi ta ɗaga idanuwanta da duk suka jeme har colour ɗinsu ta blue ta ƙara fitowa abun tsoro tace"kamar ya bangane ba, waye saurayin nawa?"
"Samari nawa ne dake?" KhUlud ta faɗa
"Ko ɗaya" leeya ta faɗa a takaice sai dai har yanzu muryarta bata dawo nml ba.
"Hmmm, menene Matsayin Wanda kuke tare dashi a koda yaushe ta hanyar turamasa da saƙo a duk lokacin da kikaga saƙonsa"
"Wannan ba saurayina bane, amma kuma ina jin sa a zuciyata fiye da idan yana saurayina. Sai dai ko za'a tambayeni a Yanzu bazance ga matsayinsa a wurina ba"
"Hmmm, wannan ma wata babbar alamace leeya, yanzu bakida lafiya bamuda lokacin da zamuyi maganar nan har sai kin warke hankalin ki ya tsayu wuri ɗaya, daga nan ne nakeso ki zauna kiyi tunani kan abunda zai fisshe ki, kinga wannan bawan Allah dayake turamiki saƙo a koda yaushe?" Leeya ta ɗaga kanta alamar "ehhh"
KhUlud ta gyara zama taci gaba da faɗin "wallahi na tabbatar da soyayyarsa gareki gaskiya ce, a yanda yake kula dake hakan nan ba kowane namiji bane zai iya yin haka, wallahi daga jiya da aka kawo ki asibitin nan ya turamin sakonni sunfi a kirga da wayanki dake hannuna, kuma ba saƙo ɗaya da ya turamin da number iri ɗaya, kin ma san menene? Wallahi wancan box da kika gani daga gareshi ta fito, kuma sakonsa ne zuwa gareki".
Khulud ta faɗa tana nuna wata ƴar qaramar kyakkyawar akwati wacce da alamu abinci ne a ciki, sai kuma wani gefe daban da akayi wasu ƙananan abubuwan daga gefen akwatin, kamar dai wurin saka ruwa ko wani Abu mai kamada haka.
Da mamakin da ya Bayyana ga leeya ƙarara ta kalli khulud irin kallon nan na bangane abunda ki ke nufi ba.
Kamar khulud ta karanto abunda ke zuciyar leeya tace "baki gane ba kho?"
Cikin son jin ƙarashen zancen leeya tace
"eh wallahi ban gane ba, dan Allah kice min kinganshi kuma kin sanshi Please, wallahi ina so na san waye a tsawon lokacin nan."
"Uhmm--hmmm, ki kwantarda hankalinki nayi miki bayani"
"Ina saurarenki khulud nasan kin sanshi kho!?"
"Ah ah wallahi ko kaɗan Ni bansanshiba, hasali ma ba waya mukayi dashi ba,
kamar yanda kuke magana dashi ta hanyar turo da sakonni, haka nayi magana dashi har wannan sakon ya shigo hannuna, da taimakon wayarnan taki.
Yayi min bayani inda zan sameshi da kuma kalar kayan da ya saka a jikinsa, sannan kuma ya gayamin yanda zan sami saƙon da kuma kalar saƙon wato box ɗin nan dake gabanki, nayi iya ƙoƙarina wajen ganin ba'a sami mistake ba, haka kuwa bamu samu mistake ko ɗaya ba wajen kwatancen da yayi min da kuma yanda nayi saurin ganewa. Sai dai abun mamakin shine koda naje wurin sakon kaɗai na tarar babu shi mutumin, ina shirin tura masa saƙo ne naji shigowar saƙonsa "khUlud k-waasib kho, bravo kinyi ƙoƙari sosai da kikayi saurin gano wurin nan, nasan zakisha mamaki sosai idan kika zo wurin nan baki ganni ba, amma kuma hakan shine daidai domin bamuyi dake zaki ganni ba saƙo kawai nace zan bada kuma ga sakon nan a gabanki ki ɗauka ki wuce, na roƙeki da girma Allah ki kaiwa dream girl saƙon nan kuma kigayamata ya fito daga babban masoyinta mai burin zama da ita har abada ki dauka ki kaimata please kema ina yimiki godiyan ki ta musamman sai anjima".
Wannan shine sakon da ya turomin lokacin da na iso wurin da yace mu haɗu, Ni kuwa ina gama karanta saƙon na tsaya shawarar ɗaukar box ɗin ko na ƙyaleta domin na fara zargin wani abu, bankai ga karasa zancen zuci na ba naki shigowar wani saƙon, "khulud me kike jira naga har yanzu baki ɗauka ba ko kina tunanin Ni mai cutarwarne zan Cutar da ke kho?, to ki daina wannan tunanin domin ko wata bakeba bazan iya cutar ta ba balle ke, idan na cuta muku wallahi amanar so da haƙƙi bazasu barni ba kidaina wani kokonto kinji kho" maganarsa kenan a cikin saƙon kamar mai gargaɗi.
Mamaki ya kamani sosai domin bansan yanda akayi ya gane ban ɗauki saƙo ba, babban abunda yaban mamaki shine yanda akayi yasan sunana har da na papu, "mamakin me kike wata ƙila leeyana ta gayamasa tunda kinga soyayya suke ai" wani bangare na zuciyata ya faɗi haka.
A fili na furta "to ya akayi yasan ban ɗauki saƙon ba, me hakan yake nufi?
Kenan yana nan.
Dube-dube ta farayi hagun ta da dama domin taga ko zata hango wani da hankalinsa ke kanta saidai bata iya gane komai ba.
Durƙusawa tayi ta ɗauki box ɗin ta miƙe zata wuce sai kuma taji an sake turomata da sako "yawwa ko kefa, amma fa ki daina tunani zaki ganni, bazaki ganni ba saɓanin Ni da nake kallonki a yanzu haka duk abunda kike ina gani, hannunki ɗaya akwai shopping leather, ɗayan kuma saƙon da na baki ne da kuma wayanki sai kuma ke kanki da kike rataye da handbag fara da hijab ɗin ki light-blue ko ba ke bace".
"Nice" na faɗa a fili saboda tsananin ruɗewar da nayi domin Ni a nawa ganin wannan mutumin ba mutum bane duk yanda akayi aljanine.
Amma kuma zuciya ta bata karfafa ni wajen cewa shi aljanine domin ko aljanine bai cutarda keba a iya tsawon zamanku, kuma Nima ya ƙara jaddada min bazai cutardani ba saboda haka dan Allah ki kwantarda hankalinki kinji, ki taimakamin na sauke wani nauyi dana ɗaukarwa kaina"
"Wane nauyi kika ɗaukar wa kanki khulud?"
"Nayi masa alqawarin zaki karɓi wannan kyauta tasa da hannu biyu, kuma zaki ci, nasan kin yarda dashi kuma ma ai shi ɗin masoyinki ne akwai soyayyarsa mai girma a zuciyarki nasan da haka saboda haka bama sai nace kici ba nasan zakije".
"Amma kafin nan kibani wayar nayi magana dashi, sannan kuma nayi masa godiya da kyautarsa gareni, haƙiƙa naji daɗin kyautar nan ko ba komai nasan ina ransa tunda har ya binciki lapiya ta kuma ya damu dani har ya kawomin kyauta duk da bansan meye a ciki ba"
"Karɓi to ki yi masa saqon bara na buɗe naga abinda ke cikin box ɗin nan" khulud ta faɗa tana miƙawa leeya wayar da ke hannunta a lokaci ɗaya kuma tana janyo box ɗin da ke gabanta.
Karɓar wayar tayi ta rubuta masa zanzamammen sako mai cike da sanyi da kwanciyar hankali tare da tsaftatacciyar godiya.
"Wow, Masha Allah" khulud ta faɗa lokacin da take buɗe box ɗin nan, daidai lokacin da meenal da airah suka matso kusa da su.
Wani ɗan ƙaramin bowl ne mai marufi fari sol sai sheƙi yake kamar wanda aka shafawa mai, daga gefen box ɗin kuma kyakkyawan cofi ne madaidaici kamar bowl ɗin nan kalarsu da sheƙin su daya, saidai an warewa ko wanne wurin zamansa a cikin box ɗin, a jikin bowl da mug cup ɗin kuma anyi wani tsararren rubuta da aka rubuta sunan Leeyanah cikin salo da kwarewa, sosai abubuwan sukayi kyau kamar ka sace ka gudu.
A tare suka furta "Masha Allah, gaskiya abubuwan nan sunyi kyau sosai"
KhUlud da murmushi tace " ai Ni bazance komai ba idan ana sallah ba'a Magana bari dai mu buɗe muga abunda yake ciki.
Bowl cooler ɗin ta fara ɗauka ta buɗe marufinsa "sweetness" Airah ta faɗa tana lumshe idanun, snaks ne a ciki masu matukar ɗaukar ido ga wani shahararren ƙamshi daya garwaye ɗakin hatta su mum sai da suka kalli inda su leeya ke zaune, jin wannan kamshin ya saka badar da Aneesa tasowa sukazo wurin.
Saida kowa ya gama faɗin abunda zai faɗa kan snaks ɗin sannan suka dauko mug cup, shima marufinsa suka bude nan take ƙamshin fruit ya haɗe wurin da yake akwai air-conditioner yasa fitar ƙamshi ba wuya.
dama can Mayah ce kawai bata ƙara so ba itama ganin duk sun haɗe kai waje ɗaya kamar masu kallon wani abun mamaki ya sakata ta zo itama, domin
Ganin abunda ke faruwa.
"Menene a ciki" cewar meenal
"Niƙakken fruit ne gskiya yaji haɗi sosai sai kamshi yake bugawa" cewar khulud tana saka cokali cikin mug ɗin fruit dake hannunta.
"Lallai ma wannan massager din shi har yanzu bai haƙura ba akwai bala'i kenan tsakaninsa da ya-Turab" Aneesa ta faɗa lokaci ɗaya kuma tana rufe bakinta data tuna cewa leeya batasan da zancen ba.
"Me kike cewa haka Aneesa, mezai haɗasa da ya-Turab balle suyi bala'i ba wanda yasan wani a tsakanin su bala'in me zasuyi"
Aneesa duk ta daburce ta rasa abunda zatace, sai cewa tayi "leeya kin manta kenan ya-Turab yana faɗamana duk wacce ya kama a cikinmu tana kula samari sai ya karyata, kinga ke gashi dan tsaurin ido har a Asibitin nan saurayinki ya kawomiki kyauta, duk wanda yaga kayan nan yasan abun masoyane wallahi. Shi yasa nake gudun kar ya-Turab ya ganki ko kuma wata rana kuna tare da messengern saurayinki ya turomiki massage ki shiga uku" Aneesa ta sauya zancen da haka.
Duk suka amince da maganar ta ana neman yanda za'a ɓoye kayan domin kar ya gani ya karyasu musamman ma ita uwar gayyar da aka kawowa.
KhUlud ce ta bada shawarar zube snacks da fruit wani wurin daban sai a ɓoye kayan idan zasu tafi su wuce da su.
Da wannan shawarar sukayi amfani, nan suka haɗa hannu kowa da kowa banda mum da haji mainah, dama basu san abun da ake ba.
Suka ci suka sha smoothie fruit dinda messanger ya kawo, sosai khulud ta Bama leeya fruit ɗin nan tasha musamman ma da taga yayi mata daɗi sosai.
Fira sosai sukasha har zuwa yamma sallah kaɗai take tada wasu daga cikinsu da suke yinta.
Har sai da aka kira sallahr magariba ko wannensu ya hau shirin tafiya, papu da kansa yazo shima ya qara duba jikin leeya sannan ya haɗa kansu gaba ɗaya suka tafi, haji kaɗai aka bari ta zauna ta kula da leeya kafin taji sauqi.
Leeyana taji daɗin hakan amma ba sosai ba taso duk a barmata ƴan uwanta koba komai zata fi sakewa, domin tana jin nauyin haji sosai bazata iya dogon surutu da ita ba.
Ƙarfe goma da mintuna huɗu na dare leeya ta ɗan motsa da alama ma ta farka.
"Leeyanatu ya jikin kin tashi kenan"
"Eh haji na tashi, jiki alhmdullillah naji sauƙi"
"Allah ya ƙara afuwa"
"Abu-turab yazo kina bacci ya jima kafin ya tafi, amma yazo miki da ferfesu yace ke kikace a zo miki dashi"
Bata tsaya shawarar komai ba ta amsawa Haji da "ehh ninace ina son ferfesu Tun ɗazu ne ma kafin kuzo da zai fita"
"Amma Abu bayada tausayi yanzu tun da rana kika gayamasa amma bai kawoba sai yanzu ƙarfe goman dare, da nasan haka ne ai bazan karɓa ba wallahi saidai ya koma dashi na kira fanaya akawomiki daga gida wannan rashin tausayin har ina ko yanzu ma idan zai dawo da ya koma da abunsa ɗan rainin hankali kawai" Haji ta ƙarashe maganar da faɗa kamar turab ɗin yana gabanta.
"Kiyi hakuri haji, wata ƙila ya manta ne ko kuma wani uzurin ya riƙe shi shiyasa bai zo da wuri ba".
"Zaizo ya sameni ai sai naji dalilinsa nayin haka, yanzu ki tashi kici kinji"
Badan inaso ba na tashi naci kaɗan, ko shi ma dan haji tayi Magana ne da ba dan haka ba Ni ba abunda zanyi da kayansa.
Kwana biyu tsakanin kullum sai mutanen gidan mu sunzo sun wuni su koma, kuma haka zamuyita fira dasu har su tafi.
Washe garin rana ta uku da sukazo ne da yamma aka sallame mu a asibitin domin naji sauƙi sosai na warke kamar ma bani nayi ciwon ba, sosai haji da mum sukayi dawainiya dani kamar nice khulud ko meenal ko wata daga jikokinsu na cikinsu.
Tun ranarda akace ya-Turab ya kawomin ferfesu ban ƙara sakashi a ido ba sai ranar da za'a sallamemu, nida mayah da mum muka shiga motarsa.
Haji da Badar, da Aneesa da meenal kuma suka shiga motar driver, ita kuma Airah suka shiga motar da khulud tazo da ita.
Kusan tare suka iso gaba ɗaya, sashen haji suka wuce gaba ɗayan su, a can leeya tayi wanka aka ɗauko mata kaya ta saka sannan sukaci abinci.
Sun jima a sashen daga nan kuma khulud da mayah, Badar meenal, Aneesa da Airah suka koma part ɗinsu leeya kuma suka barta a sashen haji domin ita tace suje Magana zatayi da leeya.
Tana zaune a parlourn turab ya shigo da sallamar sa, ko kaɗan bai lura da tana zaune a parlourn ba yasa yayi zamansa a ciki, zamansa ba jimawa mum da papu suka shigo a tare, bayan ya gaidasu yaci gaba da abunda yake cikin laptop dinsa, sannu suka yiwa leeya, ta amsa musu cike da nutsuwa.
Sai a lokacin ya lura da ita, nan ya kare daure fuskar sa sosai kamar wanda bai taɓa yin dariya ba a Rayuwar sa.
Suna zaune a haka sai ga haji ta fito daga bedroom itama "ahhh kuce kun haɗu gaba ɗayan ku kenan"
"Eh haji mun fito, amma ai bamu jima da fitowar ba"
"Tau shikenan sai muyi abunda ya kawomu kowa ya kama gabansa kho".
Ita dai leeya tana zaune a wurin kanta a ƙasa gabanta sai duka yake, tana Addu'a a zuciyarta "Allah dai yasa Lafiya" haka take ta nanatawa.
"Leeyanatu!"
Ta tsinci muryar haji na kiranta cikin muryarta mai cike da Dattaku.
"Na'am Haji"
"Leeyanatu menene matsayin fanaya wurinki, domin duk sun bani labarin yanda zamanki gidan nan ya kasance dama sauran wani labari na daga rayuwar ki"
Da mugun ƙarfi turab ya ɗago ya kalli haji da ke Maganar amma yayi saurin mayar da kansa ƙasa domin kar a fahimta.
"Haji da zaki sanardani idan na tambayeki wani abu daga abunda kike faɗa da kin rage min nisan tafiya"
Turab ya faɗa a zuciyarsa yana kara gefawa leeya wani mugun kallo da ta rasa menene ma'anar sa.
Leeyana ta dago kanta