BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   16 / 61

45K to 48K   out of 180.4K words

ma'aikata sunsan junansu koda ba aikin su ɗaya ba. To balle waɗanda suke aiki ɗaya, kuma agari ɗaya. Kunga zamuje ne mu sami Dr kanal raghib ya faɗamana ƙwararren likitan ƙwaƙwalwa, a BHOPAL INDIA idan ya faɗa mana sai mu gaya masa matsalar mu ko za'a sami waraka"

"Gaskiyane ya-fahad abunda ka faɗa shine daidai Yakamata a koma india da Rukhshanah ko za'a sami nasara domin a gaskiya nan Nigeria babu ƙwararrin likitocin ƙwaƙwalwa domin kuwa da akwai da mun samu, kaga har abuja anje da ita amma ba wani cigaba" cewar MAYAH dake can gefe dasu.

"Gaskiya mummy ya kamata ayiwa dad magana kan shawarnan da ya Fahad ya kawo ko ya kika gani ke" FANNAH ma ta faɗa
Dason jin abunda mummy zata yanke.

"Hakane fahad amma yanzu ku bari idan muka dawo da naija state gobe zamuyi tafiyar, ba'a can Zamu kwana ba idan muka dawo sai a ci gaba da Maganar sake fita da Rukhsha waje"

"Me zamuje yi a suleja kuma mummy inace dai ba gidan dad babba zamuje ba kho" MAYAH ta tambaya tana ƙanƙan da idanu.

"Menene idan chan zamuje".

"A gaskiya mummy mudai bazamu jeba kho twiney" cewar MAYAH tana kallon FANNAH.

"Ehhh mummy gaskiya bazamuje gidan dad babba ba mudai".

"Kuzo nan" cewar mummy ba wasa a idanun ta.

"Mummy kiyi hakuri zamuje" MAYAH ta faɗa kamar zatayi kuka.

Wata uwar Tsawa mummy ta daka musu da sauri suka ƙaraso wajen ta.

"Sai nace ku zauna kho" cewar mummy.

Zama FANNAH tayi tana kama hannun MAYAH suka zauna tare
"Mummy kiyi hakuri idan ranki ta ɓaci da abunda muka faɗa, wallahi bawai bama son zuwa gidan dad babba bane, ko domin mum-fanaya zamuje da kuma dad babba. Amma kinsan yanda khulud ke yimana kamar ba jinin taba, tafison ƙawayenta fiye damu ƴan uwanta. Sai tayita mana abu kamar ba dangi ɗaya ba" cewar FANNAH idanun ta na cikowa da hawaye.

FANNAH da MAYAH ba kamar kowa bane saboda su abu kadan zai sakasu kuka. Ko yakai ayi masa kuka ko bai kaiba, kuma su a rayuwarsu basa qaunar ganin mahaifiyarsu tayi fushi dasu to wannan shine Babban tashin hankalin su. Kuma ko a Yanzu suna gani kamar tayi fushi dasu ne.

"Mummy, wallahi kinji Dalilin da yasa muka faɗi haka" shiru mum batace komai ba.

Rukhshanah dake lafe jikin mummy tun ɗazu, ta kalli mummy tace "mummy dan Allah ki duba uzurinsu mana Please, sai magana suketayi amma kinyi shiru".

Sai a lokacin mummy ta ɗago da idanunta ta kallesu tare da faɗin "shikenan ku tashi ku tafi, amma ku tabbatar kun fara shirin zuwa suleja gobe zamu ɗauki hanya in sha Allah"

"Tau in sha Allah, zamu cika trolly mummy karki damu shekara zamuyiwa dad babba a gidansa" MAYAH ta faɗa tana dariya.

Dariya mummy tayi itama kaana tace"to ai shikenan kuje ku cika trolly ɗin kutafi can wajen hajia fanaya koni na huta ai taje ta ƙara kuzama ku huɗu kenan. Harda Rukhshanah a tafi da ita".

"Mummy!" Fahad ya kira sunan ta a taƙaice

"Na'am fahad ya akayi"

"Mummy naji kuna maganar zuwa SULEJA ne gobe kuma banida masaniya"

"Sannu dad" MAYAH ta faɗa tana taɓe baki. Dayake itace mai neman rigima dama, FANNAH ba ruwanta da irin haka. Haka itama Rukhshanah batada neman rigima amma MAYAH kam ko za'a yankata indai zata tashi to idan taga abun magana sai tayi.

Pillow ya ɗako da gudu ya miƙe da nufin ya jefa mata, ita kuwa tana ganin haka ta tashi da gudunta itama ta fita parlourn tare da janyo ƙofa ta rufe rufff tana ta dariya.

"Da kin tsaya da kinga ikon Allah wallahi" Fahad ya faɗa yana komawa inda yake zaune.

"Ikon Allah kuma ya-fahad na nawa aini tun kafin a haifeni ake ganin ikon Allah, har aka haifeni ba'a daina gani ba, har na girma na fara gani Nima. Menene saura to" cewar MAYAH tana leƙowa ta window.

Sake jefamata pillown yayi daga inda yake ita kuwa ta ƙara fecewa aguje.

"Yawwa mum nace yaushe ne za'ayi tafiyar? Fahad ya tambaya.

"Gobene ya-fahad amma nima bansan me zamuje yi ba, wata ƙila ziyara kawai zamuje kho mummy" FANNAH ta faɗa tana kallon mummy.

"Ehh to, makamancin haka. Amma kuma yayanku Turab ne za'a yiwa walimar kammala karatun sa na likitan sojoji"

"Yaushe zai dawo kenan" fahad ya faɗa yana gyara zaman sa.

"Inaga tsakanin yau da gobe zai dawo domin gobe za'a yi walimar"

"Amma Turab ya rainani mummy yanda nayi missing ɗin guy ɗin nan har zai iya shigowa Nigeria ba tare da nasani ba, wallahi mummy a wannan karon idan kukaji muna masifa karku shiga" cewar fahad.

Wayar sa ce ta fara ruri alamar kira ya shigo.

"FANNAH miƙomin wayana"

Miƙewa FANNAH tayi da sauri ta ɗakko wayar

"lahhhh ya-fahad, ya-Turab ne ke kiranka fa"

"FANNAH miƙomin wayana banason shashanci ci"

"Wallahi da gaske neke duba kagani" FANNAH ta faɗa tana miƙo masa wayar daidai lokacin da kiran ya katse.

"Lahhhh wallahi kuwa shine mummy, kenan yana Nigeria ma kinga ma number Nigeria ce" Fahad ya faɗa yana mayar masa da kiran.

Sai da wayar ta tsinke ba'a ɗaga ba, "mummy yaƙi daga kiran fa"

"Fahad ka rufamin asiri Ni na isa na shiga tsakanin ku da Turab"

Har ya buɗi baki zaiyi magana sai ga wani kiran ya shiga "hello" fahad ya faɗa cikin zumuɗi.

Cikin husky voice ɗin sa ya amsa " Yes"

"Turab yaushe ka shigo Nigeria ne bansaniba. Kuma Baka gayamin ba, alhali ko jiya da dare munyi chat dakai"

"Yanzu" Turab ya faɗa daga cikin wayar.

Fahad yasan halinsa sarai yasan bayason yin doguwar magana ko kuma zance mai tsawo.

"Any problem" fahad ya tambayi Turab.

"Dakai za'a zo airport?"

"Bana suleja, ina kaduna amma yanzu zanzo in sha Allah"

"Ok azo lafiya" Turab ya faɗa yana shirin kashe wayar.

"Amma kajirani zanci uban mota yanzu zan ƙaraso"

Murmushi kawai Turab yayi batare da yace komai ba ya katse wayar.

Fahad kuma da ya fahimci kallonda mummy ke masa tun sa'adda yace gashinan zuwa suleja, ya lura tana masa kallon bakada hankalin ɗin nan.

Setting ya shiga a wayarshi sannan ya kunna phone ringing saida yaɗan jima yanayi kafin ya kara wayar a kunnensa.

"Hello ranka ya daɗe sir, Barka da aiki.
Ya gida ya iyali?"

ɗan jimmm yayi kamar wayar yakeyi da gaske kafin ya kuma faɗin "Ahhh mummy da dad duk lafiya ƙalau suke wallahi alhmdllh" Subhanallah, yanzu kana nufin zaman za'a kumayi kenan. Allah sarki gaskiya shari'ar nan tayi tsawo sosai, nikam nace a zauna kawai ayi komai a gaban kowa. Ni lauyan gwamnati ne bazan tsayawa ƙaryaba, saboda haka ku jirani kawai idan nazo komai za'ayi sai naji da kunnuwana"

Second ɗaya, biyu, uku baice komaiba sai a second na huɗu ne yace" ahhh ba komai wallahi ranka ya daɗe yanzu kam yamma tayi da zuwa Abuja amma bara nakira dad nayi masa bayani inyaso sai nazo na kwana a suleja gobe tun da sassafe kafin masu binciken suzo mu mufara ganin suspect ɗin".

Kamar dai ɗazu yayi shiru kaɗan bai ce komai ba kamar wanda yake wayar da gaske sai da yaɗauki tsawon seconds sittin sannan yace

"shikenan ba damuwa yallaɓae yanzu zanyi shiri kafin karfe huɗu zan kuma kiranka in Allah yaso, Yanzu dai bara na fara shirin tafiyar kho, dan inaga nama fasa weekend ɗinda nazo zan dawo gaba ɗaya"

"Okay rankashidaɗe na gode mu jima lafiya" cewar fahad yana sauke wayar a kunnen shi.

Cikin damuwa ya kalli mummy dake sauraren wayarda yake tun sa'adda ya fara hankalin ta na kanshi yace" mummy, ina labarin shari'ar nan dana baki, wacce akayi kisan kai a makaranta kwana ta maza a abuja".

"Eh na tuna" mum ta faɗa tana gyarawa Rukhshanah kwanciyarta da take ta faman bacci tun ɗazu.

"Shine aka nemi suspect ɗin aka rasa bayan zama biyu da akayi a kotu, amma anyi nasarar kamoshi jiya da dare. Kuma wasu ne aka aika suka saceshi. Su sun tsere amma shi anyi nasarar cafkoshi, shine aka kirani inaso na gana dashi gobe tunda sassafe kafin a wuje court". Fahad ya faɗa kamar da gaske................✍🏼







BAYAN WUYA....










By RUMANA M DIGGI







EP.17

____________shiru mummy tayi tana kallon sa, domin ta kusa ta harbo jirginsa, ta kusa ta gane duk shirine ba gaskiya bane.

Ɗan gyaran murya fahad yayi saboda yaga kamar mummy ta manta dashi zaune a wurin.

"Allah sarki, haka akayi kenan? Yanzu kai meye naka da suspect ɗin kaida kake lauyan gwamnati?".

"Tau kedai mummy ganemin hanya, Nima bansaniba ba amma ai idan naje da kaine zan san ko menene".

Dariya ta kusa suɓucewa mummy ganin yanda yake yi kamar da gaske. "Tau Allah ya tsare ya kaika lafiya".

"Ameen thumma Ameen sweetheart, nifa bana ma son tafiyar nan kawai ta kamani dole ne, nida nazo weekend ma. Naso nayi 2weeks wallahi mummy".

"Fahad kenan ba komai ka tafi kawai, kaida naji kana faɗin ka fasa weekend ɗinda kazo kayi".

"Lahhhh yaushe na faɗi haka mummy" fahad ya faɗa yana ɗan waro idanu.

"Ya-fahad ka manta lokacin da kana waya ka faɗawa ogan naku" faɗin FANNAH itama tana dariya.

"Awwwn, ashema nace haka, kunga Ni ban masan nace ba ai. Bara dai kugani na tashi kar dare yaymin dama kayana na nan parked ban walwale ba".

"Uhmmm" kawai mummy ta faɗa tana barin wajen.

Shima tashi yayi ya ƙaraso inda Rukhshanah ke kwance yace"baiwar Allah, Allah ya baki lapiya Rukhshanah. Zan dowa nan bata jimawa ba muje aimiki magani da iznin rabbi kema kiyi walwala kamar kowa" fahad ya faɗa yana shafa goshinta zuciyar sa cike falll da tausayinta.


FANNAH itama tausayin nata ne ya kamata nan da nan idanunta suka ciko da kwalla tace" wallahi ya fahad nima ina qaunar naga Rukhshanah ta sake kamar dha Ni inaga ma lokacin da muke innovation specialist magungunan sunfi karɓarta bisa waɗan nan na asibitin Dr Beeshwah Areef. Saida ta fara amfani da sune fa ta zamo haka, bata son surutu, batason yawan yin magana, Batason hayaniya ga yawan bacci" cewar FANNAH cikin tsananin tausayin Rukhsha.

"Tau Allah ya bata lafiya ki zauna nan da ita na san MAYAH na nan tana jira na fita ta dawo nan, dan Allah ku kula da ita sosai Please ƙannena, kuma banda damuwa karku sakata surutu Please. Idan kukayi haka gobe zan fita daku shopping idan kunzo naija state"

"In sha Allah ya-fahad zamu kula da komai karka damu, Allah ya kaika lafiya ya tsare hanya. Ammafa kaje kayi sallama da mummy karka tafi"

"Haba dai ke kuwa, ai dole ne naje nayi sallama da ita. Har dad ma sai nabi ta Company nayi sallama dashi tukunna saboda shima nasan zaizo gobe". Fahad ya faɗa yana shigewa sashensa.

Kamar kuwa yasan MAYAH jiransa kawai take, yana fita ta cillo parloun kamar na an harbota "twiney ya-fahad ya tafi kho? mayah ta faɗa kamar mai yin raɗa.

"Waya gayamiki ya tafi, kayansa yaje ya ɗakko fa yace bazai bar gidan nan ba sai kun haɗu dash..... "
Tun kan FANNAH ta idarda maganar, MAYAH ta zabura aguje zata koma inda ta fito har takai tsakiyar parlourn FANNAH tace "to wasa nake ya tafi, sai jan rigima ga kuma tsoro".

Dakatawa MAYAH tayi da gudun da take ta waiwayo itama tace"to waya gaya miki shi nake yiwa gudun Ni, kawai ina exercise ne na rage ƙibar kumatu".

Har Mommy dake shigowa parlourn bata san sa'adda dariya ta suɓucemata ba.















*ABUJA STATE*
Da misalin ƙarfe biyu da kwata jirginsu yayi landing a NNAMDI AZIKIWE INTERNATIONAL AIRPORT ABUJA.
Sanye yake cikin suit bold colour.
Fuskar sa ba alamun fara'ah ko kaɗan, kamar bai taɓayin dariya ba.

A ƙasan zuciyarsa kuma tsaki yake yafi dubu. Sai fama kallon tsadadden agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannun sa yake ƙirar Itali.

Trollynsa dake janye a hannun sa na dama ya sauya mata hannu zuwa hannunsa na hagu ya ci gaba da janta a gajiye.


Hannun sa ya saka cikin aljihun jacket ɗinsa yafito da wayarsa.
"Our boss"

Number da akayi saving da wannan sunan ya dannawa kira.
Kamar jiran kiran nasa akeyi, aka ɗauki wayar da sauri.
"Ko na shigo motar kasuwa na dawo gida ne" ya faɗa cikin muryarsa mai kamada wanda ya tashi daga bacci.

" sorry son, muna airport ɗin yanzu haka" aka faɗa daga cikin wayar.

Katse wayar yayi bayan ya kwatanta masa inda yake, wuri ya samu ya ɗan zauna ya jira isowarsu.

Bai jima zaune a wurin ba ya fara hangosu tafe. Hannu yayi masu tun kan su ƙaraso ya taryesu.

Papu, Aunty Rahma wato ƙanwar papu, da wasu mutum biyu daga cikin familyn su kazo tarbar Turab.

Yana ganinsu kuwa ya ƙaraso wajensu, bai tsaya komai ba ya rungume mahaifinsa, sun jima a haka kafin ya sake shi suka gaisa da mutanen da sukazo tarbashi.

Nan suka ɗauki kayayyakin shi aka saka a mota suka ɗau hanyar komawa suleja.





K. MANSION SULEJA NIGERIA.

"Mum, inaso naje nayi wanka nayi sallahr la'asar sannan na dawo, inaga kafin haka ma duk abincin nan ya ida nina" cewar Leeya tana yamutsa abincin.


"Okay ba damuwa kije, kuma karki jima dan Allah. Idan zaki sakko ki karamin khulud justice yace gashi nan sun kusa ƙarasowa, kuma ba'a gyara ɗakin Turab ba banaso yazo ya sami ɗakin da ƙura duk da nasa ba wani gyara za'a yi masa sosai ba"


"Okay mum , in sha Allah zan gayamata sai muje mu gyara. Yawwa mum ban faɗa miki ba ɗazu da kika je sashen da ɓaki suke ankira wayanki maman twins tace wai suna hanya"

"To Bara na kirasu naji yaushe ne zasuzo yau ko gobe" cewar mum tana danna wayar alamar kira zatayi.

Leeya na fita daga kitchen area ta nufi part ɗinsu hankali kwance take tafiyarta domin ba kowa a parlourn duk suna can sashen su na baƙi.

Bedroom ɗin ta ta nufa direct ta shiga toilet ta watsa ruwa tare da yin alwala ta fito, sallah kawai tayi ta saka wasu kaya sannan ta dubi niqab ɗin da yayi daidai ta kayan ta saka ta fito.

Bedroom ɗin khulud ta nufa duk da ta ganshi a buɗe hakan bai hanata knocking ba "baki ganshi a buɗe bane bane kike min knocking" khulud ta faɗa a tsawace daga cikin bedroom ɗin.

"Sorry sis mum ce ke kiran ki, tace wai kizo muje part ɗin ya-Turab mu gyara sun kusa karasowa"

Da sauri khulud ta wuntsilo daga kan gadonda take kwance ta fito ba shiri "me kikace ya-Turab ya kusa ƙarasowa kuma ba'a gyara masa ɗakinsa ba?"

"Eh haka nace khulud kizo muje mu gyara masa kinga mu biyune ai yanzu zamu kammala"

A karo na farko da Leeya taji khulud tayi mata magana a tausashe"wallahi sis ban iya gyara ɗaki ba, muje dai ke ki gyara"

Mamaki ya kusa kashe leeya jin khulud takirata da sis Yau "hmmmm" kawai leeya ta faɗa tana wucewa gaba.

Gwalo khulud ta fara yimata tana yimata dariya a can ƙasan ranta "sha-sha-sha, wai harta yarda da zuciya ɗaya na kirata da sis, to wallahi ni bazan taɓa zama sistern kiba har abada, idan ma da akwai wacce na tsana a duniyar nan to tana bayanki. Yanzun ma wallahi idan ba aikin ya-Turab bane banga abunda zai saka Ni jerowa dake ba" khulud ta faɗi maganar a cikin zuciyarta.

Har suka ƙaraso ɓangaren nasa ba wanda ya ƙara cewa uffan ulud ce gaba, leeya na bayanta. Dayake khulud tafi Leeyana sanin bangaren.

"Akwai key hannunki?" Khulud ta jefawa leeya tambayar tana watsa mata harara a fakaice.

"Wallahi babu key, amma Bara na je na karɓo, dakin a buɗe yake ga key can a jikin handle ɗin kofar" Leeya da ta lura da key sarqafe a kofar ta faɗa tana shigewa gaba.

Murza key ɗin tayi tare da buɗe kofar ɗakin a hankali kamar mai jin tsoro.

Banketa khulud tayi ta shigo ɗakin, sai bayan ta shigone ta juya kanta tace "sorry, bankula dake a wajen ba, ki shigo ki fara aikin" daga haka khulud bata ƙara faɗar komai ba ta wuce bedroom.

Tsintsiya ta nema ta rasa a part ɗin gaba ɗaya, saida ta sauƙa ƙasa sannan ta ɗakko duk abunda tasan zata buƙata wajen aikin.

Dayake ɗakin baida datti sosai, domin kuwa badan ƙura ba zaka yi tunanin ma akwai mutum a cikin ɗakin.

Share parlourn tayi tsafff, sannan ta janyo mopping machine tayi mopping. Bayan haka kuma ta gyara masa show display ɗinsa tsafff, daganan kuma ta ta gyara masa perfume stand show glass. shima ta sake jeren gwanin ban sha'awa, komai na cikin parloun ta gyara masa shi kamar yana nan.

Sweet air freshener ta ɗakko ta fesa ko wanne lungu da saƙon na parlorn, take ƙamshin parlourn ya sauya gaba ɗaya.

Bedroom ta shiga da nufin shima ta gyarashi ta fito "ikon Allah"
Abinda Leeya ta faɗa kenan yayin da taga khulud kwance a kan gadon da take kyautata zaton shine na ya-Turab.

Kamar yanda tayi a parlourn nan ma haka tayi saida ta gyara komai da komai. Har zata fita taji faduwar wata drawer cabinet kuma ga alamu kayane ciki.
"oh Allah, wallahi drawer nan kinban aiki" cewar Leeya tana ƙarasawa gaban cabinet ɗin.

Kayan da suka zuba a ƙasa ta fara gyarawa tana mayarwa a ciki.

Ƙarar buɗe ƙofa leeya taji. Bata ɗaga kanta ba kuma bata motsaba, domin ita a tunanin ta khulud ce ta shigo.

taci gaba da aikinta. jin anyi shiru ba sallama yasa tayi niyar ɗaga kanta. Amma kuma dataji abunda mutumin yace ta fasa ɗaga kan nata cikin tsoro ta mayar dashi ƙasa gabanta na duka.

Cikin ɓacin rai Turab turab ya sake kai dubansa kan khulud yace "tambayar ki nake uban wa ya baki dama ki kwanta kan gadona har ki iya yin bacci akanshi, wato ke isashiyya kho"
ya faɗa cikin tsawa.

Leeya kuwa zuciyar ta har tsalle take kan tsoro kamar ta fado ƙasa kuma gashi har yanzu ta kasa ɗaga kai ta kalleshi.

Shi kuma bai masan da ita a wurin ba saboda bata Ta-ta yakeba.

"Zaki zo ki wuce ko saina babbalaki" ya faɗa kamar wanda ya gaji da yin magana.

"ya-Turab dan Allah kayi hakuri wallahi nazo na gyara maka ɗakin ne, sai bayan na kammala gyaran ne naji kaina namin ciwo shine na ɗan kwanta nayi tunani gajiyace bacci ɓarawo yazo ya ɗaukeni"
Khulud ta faɗa cikin Muryar kuka hawaye na rige-rigen fitowa.

"Zo ki wuce nace" turab ya faɗa yana nuna mata Kofar fita.

da gudu ta wuce ta gabanshi kamar wacce iska ya koro.

Sai a lokacin ya hango leeya ita ma, dauƙe da sauran kayayyakin cikin cabinet ɗin ita bata saka ba kuma bata ajiyeba

"kan'ubahh!!, ke kuma binkice kike min, dan ubanki tukunna ma wacece ke. Kina

16 / 61