Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
mum ta karɓa masa sallama.
"Mum ki turomin wannan yarinyar inaso na bata saqo, yanzu fa!"
Bata cemasa komai ba ta kashe wayar domin tasan wacce yake magana a kanta, "wannan yaron ya raina mutane dayawa wai "wannan yarinyar" hmmm, Allah dai ya sauwaqe" mum ta faɗa tana murmushi.
Har part ɗinsu taje ta tarar dasu kowa yana sha'anin gabansa, meenal tayiwa alama tazo da hannu domin ba wanda ya lura da shigowarta ɗakin sai ita.
Miƙewa tayi ta ƙaraso gaban mum "mum lafiya dai naganki haka"
"Lafiya ƙalau meenal ina leeyanah"
"Ta shiga toilet wanke takeyi"
"Okay idan ta fito ki gayamata yayanku na nemanta sashensu"
"In sha Allah za'a gayamata da zarar ta fito mum"
"Okay Allah yayi muku albarka"
"Ameeen ya rabbi mum"
Fitar mum ba jimawa leeya ta fito meenal kuwa tagayamata saƙon mum, sosai taji tsoro tana fata a ranta ba laifi tayi masa ba.
Saida da shirya tsafff cikin doguwar rigar ta ruwan azurfa, wacce papu ya siyomusu dawowarsa Saudiyya, rigar tayi kyau sosai irin wacce larabawa ke sakawa, rigar batada yawan ado sai dai tanada ɗaukar idanu kalar rigar ma haka sai wani shining take. Gashinta data gyara ta sako gaba ɗaya ya zubomata har gadon bata ya kwanta lifff a kafaɗarta, sai nigab ɗinda ta ɗaura kusan kalar rigar saidai shi baya walƙiya kamar yanda rigar take amma shima yayi mata kyau, ya ƙara fito da daradaran idanunta data shafa musu baƙin kwallin da ya ƙara fito da ainihin kalarsu blue da ɗan sirkin fari-fari.
Mayafin rigar ta ɗakko ta yafa sannan ta fita daga ɗakin.
gabanta na faɗuwa ta Kwankwasa Kofar dakin.
"Waye" ya faɗa muryarsa a dakile kamar wanda ya tashi daga bacci.
"Ni ce, mum tace kana nemana" ta faɗa Muryar ta na rawa saboda tsananin tsoronsa daya fara ziyarar tar zuciyar ta tun kafin su ga juna.
"Mtswww" yayi tsakin da yakai har kunnenta saidai bata ɗauki wannan komai ba taci gaba da tsawuyar jiransa.
Mintuna Takwas bayan kwankwasa kofar da tayi kuma har yanzu bai fito ba ko motsin sa bataji ba kuma tana nan tsaye kofar ɗakin,
Shikuma yana zaune abinsa kamar bai san da mutum a waje yana jiransa ba, da saninsa yabarta a tsaye tsawon lokaci tana jiransa.
Miƙewa yayi ya fara tafiya kamar bayason taka kasa har ya isa kofar ɗakin, mirɗa handle ɗin Kofar yayi ya fara buɗeta a hankali, buɗewar kofar gaba daya yayi daidai da leeya ta juya zata bar wurin.
"Imagine!, ke dan kin kai isashiyar mara kunya har ni zan aika kiranki kizo ki tafi ba tare da na sanarda ke dalilin kiran ba"
Addu'a ta fara karantawa a zuciyarta ko zata rage jin abunda takeji a duk lokacin da ya-Turab ke kusa da ita.
"Wallahi nayi tunanin kana toilet ne saboda na jima nan a tsaye shiyasa nace bara naje parlour na jiraka kafin ka fito"
"Bazaki iya jiran nawa a nan ba sai kinje parlour, uban me zakiyi a can"
"Ah ah bakomai zanyi ba, zanje na zauna na jirakane kawai kafin ka fito"
"Duk wurin nan bazai isheki zama ki huta ba sai kin fita parlor dan munafunci"
"Kayi hakuri dan Allah, naga babu wurin zama a nan ne"
"Kin fi karfin ki zauna kasan tales ne"
Bata amsashiba sai jijjiga masa kanta da tayi tana kara soke kan nata ƙasa.
Wani wawan rankwashi ya sakarmata aka saida ta rasa abunda zatayi saboda tsananin firgici.
"Ban sanardake idan ina magana da mutum banaso a dinga ansamin dakai ba"
"Kayi hakuri Wallahi na manta ne" ta faɗa tana rufe bakinta da hannayenta dan kuka ke ƙoƙarin suɓucemata.
"Wallahi kika sake kikayi kukan nan sai na miki dukan gaske da zai sakaki kuka da dalili babba".
Ƙara danne bakinta tayi domin kar kukan da take ya fito.
Dan guntun tsaki ja ya ɗauke kai daga gareta yace "ke bashi yasa na nemoki ba da zakizo ki sakani gaba kina kuka kamar kinga wani matacce, girki nake so kiyi yanzu-yanzu kuma nakeson aikin ya fara, egwusi and okazi soup, sai kuma oha crayfish soup, sannan kuma ki haɗa min yam and ginger juice karki saka yajiiii da yawa, sannan kiyishi ba mai kauri ba, bani account number ɗin ki na saka miki kuɗin da zakiyi siyayyar kayan girki"
Amsa masa tayi da bakinta dan dole, duk da ba wata maganar tayi ba amma kuma bata kyale shi ba saboda tana gudun yayi mata wani dukan, account number ɗin ta tagayamasa nan taji alert ɗin shigowar kuɗi, dubawa tayi taga ya tura mata da kuɗi har dubu ɗari uku.
"Kuɗin nan sunyi yawa indai siyayyar kayan girki ne 20k ma zasu isa"
"Idan kinyi siyayyar ki zubar da sauran kuɗin" yana gama faɗin haka ya juya tare da banko kofar ya rufe ta rufff.
Komawa tayi part ɗin su babu bata lokaci tayiwa meenal bayanin komai ba abunda ta ɓoyemata har zancen yawan kuɗin da ya turomata.
"Bara na ɗakko gyalena nazo na rakaki siyayyar idan mun dawo sai na tayiki aikin, muyi saurin kammala wa kho, amma taya zamu girka wannan kalolin abincin, na yi searching a YouTube amma bangane komai ba wallahi". Cewar meenal.
"Karki damu girkawa ba Matsala bane muje kawai bana so na kuma yin wani laifin".
Da sauri meenal ta buɗe closet drawer ta dakko gyalenta, sannan suka shiga part ɗin Mum leeya tayi mata bayanin komai.
Suna fita gate suka kira drivern gidan yazo suka zaɓa motar da zasu fita da ita kaana suka ɗau hanya.
Babbar kasuwar kayan miya masu kyau da kamshi suka nufa, inda suka yi siyayyar komai da komai harma abunda zasuyi amfanin kansu ba iya na ya-Turab ba.
Sa'ar da sukayi ba abunda suka nema suka rasa daga ingredients ɗin girkin da zasuyi, sun ɗauki tsawon mintuna talatin kafin su dawo gida.
Tare suka haɗu kitchen ita da meenal ta fara nunawa meenal duk abubuwan da take buƙatar ta taimaka mata dasu wajen haɗa girkin, ita kuma ta fara aikinta matsayin ita zata girka komai,
Sosai sukayi saurin kammala aikin, tun kan a ƙarasa meenal ke faman sonti, har tana faɗin Igbo sunyiwa hausawa wayo domin abincinsu yafi na hausawa daɗi.
"Hmmm, haka dai kikace amma ai abincin su bazaifi na hausawa ɗadi ba domin su mafi yawan abincinsu ganyayyaki ne kuma su zasu yi matsayin tuwo da miya namu na hausawa".
"Me kike nufi leeyana kina nufin Igbo sunayin tuwon ganye" meenal ta faɗa tana gwalalo idanunta waje alamun mamaki.
Dariya ce ta suɓucewa leeya har saida ta gama tiƙar dariyar ta sannan tace"wallahi meenal kinban dariya sosai taya za'a yi tuwon ganye, nace miki mafi yawan abincinsu ganye ne kuma wani lokacin shi zasu haɗa su girka su ci Matsayin tuwo da miya na mu na Hausawa".
"Okay, sai yanzu na fahimta ai, da zance taya za'a iya yin tuwon ganye ki koyamin nima na gwada nagani".
"Ah ah ba haka nake nufi ba, yawwa meenal nace cikin wace cooler ya kamata mu zuba Abincin nan".
Saidai ta ɗan niiisa kaɗan sannan ta kurawa wata cooler dake jerin kulolin da ke jera a kitchen idanu sannan tace "mu ɗauki ash ɗin can mai glitter kuma set biyar ne kinga zata isa mu saka komai da komai, har Babban jug ma sai a zuba juice a ciki."
"Gaskiya kam kular nan ta dace da girkin nan kinga komai zai samu muhallin sa, yanzu ki miƙomin su gaba ɗaya ki mu fara zuba waɗannan da muka kammala"
Da hanzari meenal taje ta ɗauko kuloli ta kawo mata, nan suka fara zuba Abinci sannan suka rage wanda zasu ci da sauran ƴan uwan nasu da zasu iya cin girkin.
Bayan sun kammala kwashe abincin leeya ta ɗauki Babban farantin da ta jera komai ta juya da nufin taje ta kai masa.
Da sauri meenal ta dafa kafaɗarta tace "me zakiyi?"
"Abincinsa zan kaimasa"
"A haka zakije, ɗazun fa ya ganki da kayan nan na jikin ki kuma yanzu zaki koma masa dasu bayan kinyi girki ga ki nan sai kamshin spices kike kamar an baɗa miki su a jikinki. Gaskiya ki ajiye muje kiyi wanka ki canja kaya sannan ki tafi".
Cikin damuwa leeya ta kalleta da blue eyes ɗin ta masu tsorata wanda duk yayi tozali dasu tace;
"kinga meenal barni naje, yayi min kashedi karna jima fa, kuma tsakanin mu yanzu awa kusan uku ne bansan adadin abunda zai min ba".
"Leeyana!" Meenal ta kira sunanta da kausa-sasshiyar murya, bata jira amsawarta ba tace "Dole sai kin fitar da tsoron ya-Turab a ranki, domin kuwa wannan ɗabi'ar ba inda zata kaiki wallahi. Rayuwa da zakuyi, wata sabuwar rayuwace wacce daga ke harshi sababbi ne a wannan rayuwa, saboda ke baki taɓa yin aure ba shima haka, dole sai kin neman wa kanki girma tun a gidan nan domin bakisan inda zaije dake ba idan kunyi aure, idan kikace komai yayi ya zama abun tsoro wallahi bazakici ribar zama ba, kwata-kwata ma bazakiji daɗin zaman dashi ba. Na rokeƙi leeya dan Allah ki rage tsoron ya-Turab a ranki kinga baya wani kulaki sosai kinsan saboda me?"
Jijjiga mata kai leeya tayi alamar bata sani ba, meenal kuma taci gaba da magana;
"saboda kina tsoronsa sosai yasan bazai shata miki layi ki ƙetare ba shiyasa ko a gaban kowa zai iya yimiki son ransa, yana gani duk ranarda ya bukaceki a rayuwarsa zaki shigo ki manta da komai da yake miki Saboda kina tsananin tsoransa, bawai nace kiyi masa rashin kunya bane, ko ɗaya kawai dai ina gayamiki ne dan kisan irin zaman da zakuyi bayan aure. Ajiye farantin muje ki sake shiri"
Meenal ta faɗa tana karɓar farantin daga hannun ta ta ajiye sannan suka fice daga kitchen suka koma bedroom ɗin su.
Suna isa ta shige toilet tayi wanka, koda ta fito har meenal ta zaɓa mata kayanda zata saka, bata ɗauki lokaci wajen shirya jikin ta ba ta janyo doguwar rigar atamfar da aka fito mata da ita ta saka, sosai rigar tayi mata kyau ga kuma adon da akayiwa rigar na bead and stone work kamar ba nigeria akayi dinkin ba.
Juyawa tayi zata fita bayan ta gama shafa turarukan da take amfani dasu Airah tayi saurin tarota "sis-leeya kinga yanda kika haɗu kiyiwa Allah kibari nayi miki hoto".
"Nima Bara naɗauko wayata nayi miki wallahi kinyi kyau sosai matar yaya" cewar badar.
"Ai kuwa idan kika bari Airah da badariyyah suka ɗaukeki Nima sai na ɗauka wallahi" mayah ta faɗa tana daidaita wayar a fuskar leeyana duk da tana rufe rufff sai ƙwayar idanun ta ake iya gani.
Haka suka sakata dole ta tsaya badan ta soba sukayimata hotuna kala-kala kafin suka barta ta tafi, da gudu-gudu ta shiga kitchen ta ɗauko faranti ta isa part ɗin sa gabanta na faɗuwa tana tsoron abunda zata tarar sakamakon ɓata lokaci da tayi.......................✍🏻
BAYAN WUYA........
By RUMANA M DIGGI
EP.38
_____________________A buɗe ta tarar da kofar bata tsaya shawarar komai ba ta kutsa kai ciki, sallama takeyi a tsorace har muryar ta naɗan sarƙewa.
Daining ta nufa ta ajiyemasa abincin har ta juya zata tafi tajiyo motsinsa, da sauri ta sauko daga step ɗin daining tanaso ta fita kafin ya sameta a ɗakin.
Turusss sukayi lokacin da ta iso tsakiyar parlourn.
"zo nan" ya faɗa fuskar sa a murtuƙe.
Har ta buɗi baki zatayi magana ya kuma faɗin"dan uwarki sai yanzu zaki kawo....."
Dakata ya-Turab, ta tari numfashin sa tana ɗaga masa hannu alamar ya dakata ɗin, da ci gaba da faɗin"ka zageni, kaci mutuncina, kaci mutuncin iyayena duk dan Ni.
Wai baka san Ni marainiya bace banada uwa banada uba, duk sun mutu shekaru Bakwai da suka gabata, ko dan daɗewarda sukayi a ƙasa bazaka raga ba, ko dan mutuncin su musulmai ne kamarka bazaka raga ba, ko dan tausaya min da tunamin da mutuwar Iyaye na bazaka daina ambaton su da mummunan kalami ba, ko dan ni da akeda burin auramaka bazaka ragamusu ba, iyayena sunyi maka komai ya-Turab domin Allah ya basu kyautar haihuwata har iyayenka sukaga dacewar mu dakai suke so su haɗamu, ya-Turab kodan mutuncin wannan bazaka raga ba, ai koda iyayena suna raye bai kamata ace bakada abun zagi da kaskanci ba sai iyayena, Wallahi bakasan yanda nake jinka a zuciyata ba aduk lokacin da ka ambato sunan mahaifiyata ko mahaifina a bakinka da niyyar ka zagesu, bazan iya misilta yanda nakejiba na kasa banbance tsana da ƙiyayya wannene zuciyata take yimaka.
Bawai ina nufin Ni na tsaneka bane zuciya ta ce ta kasa aminta dakai ya-Turab, domin kuwa ita ce takeda haƙƙin yarda da duk wani abu da yanzi idan dai ya shigo rayuwata, domin duk zuciya tana son mai kyautata mata, haka kuma tanaƙin mai munana mata ko ya yake" ta ƙarashe maganar da wani irin kuka da kuma karfin halin tsayawa a gabansa harta amayar da abunda ke ranta.
Sosai mamaki ya kashe turab a tsaye domin tsawon rayuwar bai taɓa sanin leeya zata iya tsawa tayi masa Magana kamar haka ba, bai taɓa tunanin tanada taurin zuciya har haka ba, mamaki bai gama kasheshiba sai da yajiyo karar buɗe kofa da sauri kamar wanda yake gudun ceton rai ne yazo yaga kofa a rufe kuma ba'a saka makulli ba. ya kuke tunanin zai buɗe kofar? To kamar haka ne leeya tayi lokacin da kukan da take yaci ƙarfinta, sai gani yayi kawai babu ita a inda take tsaye kuma baiji fitarta ba domin mamaki ya hanashi faɗar komai, sai guntun tsakin da jaa tare da kowa bedroom ɗin sa dafe da kansa.
Da gudu ta shiga ɗakin nasu tana gunjin kuka ta zube kan gado taci gaba da rera abunta, mayah, Aneesa da badariyyah na zaune suna kwasar abincinda leeya da meenal suka dafa.
Meenal da airah da khulud kuma suna zaune wuri ɗaya, sai dai su ba abincin sukeciba firarsu suke kawai domin sun kammala cin nasu abincin.
"Subhanallah, leeyana me ya faru" cewar Airah tana nufar leeya dake zube kan gado.
"Hummm, ya-Turab ne ko leeya, wallahi ya-Turab ya shiga uku shi ba'a taɓa yimasa abun alƙairi, yanzu kar ayi mamakin dukanta yayi fa" khUlud ta faɗa tana jin babu daɗi.
Miƙewa sukayi gaba ɗayansu sukaje inda take, sosai suka rarrasheta har sai da ta daina kukan, sannan ta sanar musu duk abunda ya faru tsakanin ta dashi bata ɓoye komai ba na game da abunda ya wakana tsakanin su.
Sosai suka bata gaskiya bawai don ganin idanunta ba, domin kuwa duk wanda yakesonka da gaskiya, kai koda ma baya sonka bai kamata gana zagin iyayenka ba koda suna raye balle ma ace basa raye.
"KhUlud da karfe nawa zaki fita" cewar Aneesa.
"Sai karfe huɗu zan fita domin nafiso sai pa yana nan, dan kar mum ta hanani zuwa"
"KhUlud ina baki shawara kada kije gidansu id ya lafiyar kura balle taga nama"
"Hmm, Aneesa kenan wallahi ba ƙaramin abu bane zai hanani zuwa gidansu id ba sai dai wani ikon mahalicci kuma, kamar yanda kikaga saura sunyi kema kiyi haka, kimin addua da fatar alƙairi kawai kinsan ba wanda zai wuce ƙaddararsa Ni id ne ƙaddarata kuma soyayyar sa ce jarabtata in sha Allah sai na cinye jarraba wa"
"Ina yimiki addu'a da fatar alƙairi ƴar uwata, Allah yasa hakan da kikayi shine alƙairi" Aneesa ta faɗa tana dafa kafaɗarta.
Daga haka kowa ya kama gabansa wasunsu suka fita wasu kuma suna zaune, leeya kuma tana zaune duk abun duniya ya isheta gaba ɗaya ta rasa sukuninta tana zaune zugummm kamar ba ita ba.
Da yamma likiss khulud ta shirya da ita da badariyyah da fannah suka fita, sai dai su badar da fannah shopping zasuje ba hanyar su ɗaya ba, sai an ajiyesu zai wuce da khulud gidansu idrak.
"Driver saraki mall zaka ajiye su fannah, nikuma layin ƴan haya unguwar tsohon barikin sojoji"
"Tau yayi hajiya ba damuwa yanzu zamu isa in sha Allah".
Saraki mall yakaisu badar da fannah ya ajiye su, sannan ya wuce da khulud layin ƴan haya. Ba jimawa suka iso unguwar, kuma cikin ikon Allah ta gane gidan domin tun ranarda sukazo da mai taxi ta hardace hanyar tsaf.
Sai da ta ɗan tsaya bakin kofar gidan tsawon mintuna biyar kafin daga bisani ta shiga, da sallama cike da bakinta ta ƙarasa har tsakiyar gidan nasu, saida ta karewa gidan kallo tsaff kafin ta ƙarasa bakin kofar tilon ɗakin da ta gani na cement ɗaya jal a gidan, sai kuma ɗan wani ƙaramin daki da akayi da langa-langa, sai kuma daga gefe banɗaki ne da kuma rijiya.
Sallama ta kuma ko zasuji su fito, saidai sallamar ta maƙale sakamakon arba da tayi da matar da ke tsaye gabanta.
Duk da tsufa da girma sun bayyana a jikin matar bai hanata shaida ko ita wacece ba.
Numfashin ta yayi barazanar ɗauke wa har wani fesoshi take da karfi kamar wacce za'a zarewa shi.
"Dayam-mmah aiki ki-ke a gidan nan" khulud ta faɗa Muryar ta na rarrabewa saboda tsanin razana da tayi da matar.
Sai da tayi maganar ne ta tuna da girman gidan bai isa a ɗauki ƴar aiki ba. Da sauri ta rufe bakinta da hannayenta, sannan ta kuma buɗewa sai faman zare idanu take "dayammah nan gidan kine".
Murmushin dole matar ta ɗauko ta yaɓawa fuskar ta sannan ta ce "hajiya ƙarama yau a gidan nan, ko kinyi ɓatan kai ne ko wani gidan kike nema?"
"Ah ah gidan nazo dayammah, dan Allah ki yafemin duk abubuwan da nayi miki a baya wallahi yarunta ne kuma lokacin bangane gaskiya ba sai a yanzu Allah ya Bayyana min gaskiya, wallahi na gyara halayena dayammah dan Allah ki taimaka ki yafemin" khulud ta faɗa hawaye na wanke mata fuska.
Juyawa matar tayi batare da ta cemata komai ba har saida ta ɗauko tabarma ta shimfiɗa daga nan ta dawo wurinta "hajiya ƙarama muje ki zauna, nasan ba ƙaramin abu bane ya kawoki gidan nan ba amma nayi mamaki sosai dana ganki wallahi dan banyi tunanin zaki iya shigowa unguwar nan tamu ba".
"Dan Allah dayammah ki daina faɗin haka, wallahi na yi rantsuwa da mahalicci na ba khulud ɗin da kika sani a can baya bace, wallahi duk na canja daga munanan halayen da kika