Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
na girmama taba kamar yanda kikeso, Ni yakamata ta girmama bawai Ni nazo ina girmamata ba, she's the peasant and the we're not the same class"
"Rufemin baki sha-sha-shar yarinya, saboda tana ƴar aiki shine zaki yimata magana yanda kikeso wannan ba rayuwa bace"
"So mum because of the maid you're talking to me like that, right?" ulud ta faɗa cikin murya kuka.
Dogon numfashi mum ta sauke, kafin ta zauna bakin gadon, a tausashe mum ta fara magana a karo na biyu
"you're my kid khulud, ko kaɗan bana son ganinki cikin damuwa, a koda yaushe addu'a ta ɗayace Allah ya shiryaki, ya rabaki da waɗannan halayen nan. Ki zamo yarinya ta gari wacce kowa zaiyi alfahari da ita, bazan iya jure ganinki a haka ba, bazan iya ba"
"Mum Please, can you leave me alone, I'm so tired, banason ganin kowa kusa dani dan Allah"
Khulud tayi maganar tana juya kanta gefe ɗaya.
Ɗan jimmm mum tayi tsawon mintuna ba wanda ya sake cewa komai acikin su, sai mum ce ta ƙatse shirun da faɗin
"ina home work ɗinda aka baku, bani naga marks ɗinda akayimiki"
"Malamin yace sai gobe zai bamu littafan mu"
faɗin khulud tana sosar wuyanta kamar mara gaskiya.
"Okay Allah ya kaimu goben"
mum ta faɗa tana miƙewa tare da barin ɗakin.
Mum na fita ulud ta janyo school bag ɗinta, tana ɗan leƙa bayan mum a hankali, note book ta fito dashi da kuma red pen, dudduba littafin ta farayi, guntun tsaki taja, sannan ta ɗauki red pen bayan tagama dubawa ta fara yiwa kanta marks yanda takeso, sannan ta maida littafin cikin school bag ɗinta, fuskar ta ɗauke da murmushi.
LEEYA.
Ta ɗauki tsawon awa ɗaya harda kusan rabi cikinta bai daina mirɗa mata ba, tana nan dunƙule gefe ɗaya hannunta dafe da ciki sai hawayen azaba ke zalalomata.
Sunsha tafiya sosai cikin motar ita dai leeya ta saddaƙar, ta barwa Allah ikonsa domin kuwa bata san a inda take ba a halin yanzu, kuma bata san inda suka nufa ba a nan gaba.
"Allah sarki ammi da kinanan da bazan shiga wannan gararin da nakeba, da kinanan baza'a dinga gudana kamar haka ba, da kinanan baza'a dinga min kallon mahaukaciya ko aljana ba, da kina nan, da kina nan"
haka dai tayi ta saƙe saƙe cikin ranta.
Tashi tayi tare da jingina bayanta jikin motar Yayin da taji cikin ya lafa daga mirdawarda yake mata, yunkurin tashi tayi daga inda take domin kuwa tagaji ainun, ƙafafuwan ta duk sunyi mata tsami, koda ta tashi sai taji kayan da ke motar sun hanata miƙewa yanda takeso, komawa tayi ta zauna dafas tare da sakin siririn kuka
"wa ƴannan mutane waɗan ne irin mutane ne da basuda tausayi, ae koda dabbobi aka ajiye ya kamata a kula dasu balle mutum ko mutum ma mace"
koda ta kawo nan a zancen zucinda take wata zuciyar tace
"haba dai kiyimusa adalci kema ko dan sanin baya bata gani, domin kuwa ta baya kika shigo motar nan bata gaba ba, kuma ba wanda yasan dake a cikin mutanen da ke cikin motar nan. Hakuri kawai zakiyi har kiga hukuncin da Allah zai zatar kan wannan lamari".
"Nayi hakurin Allah kasa ba hannun mugayen mutane nashiga ba" ta faɗi a fili cikin muryar kuka, kamar wacce ke magana da wani.
Birkin da aka jaaa daga cikin motar ya dawo da ita hankalinta, ƙara komawa tayi ta kwantar da kanta jikin motar domin yanzu ta fitar da ranta da za'a fito taimake ta.
Motar tasha tsayawa amma haka zasuyi abunda zasuyi har su gama basu zo sun leƙata bayan motar ba.
Shiyasa ko yanzu da suka tsaya bata wani damuba,
"Mezai hana kibi ta inda kika shigo ki fita tunda baki san ina motar nan ta nufa ba".
Wani gefe na zuciyar ta yayi maganar.
A hankali ta janyo jakarta, sannan ta matso daidai da bakin kofar motar inda ta shigo, ta kara kunnenta a hankali domin ta jiyo idan akwai hayaniyar mutane ko kuma cikin daji ne suka tsaya.
Cikin ikon Allah kuwa ta dinga jiro maganar mutane a ɗan nesa da inda take daidai lokacin duhun magariba ya fara, a hankali take yaye marufin da aka rufe jikin motar dashi harta kawo daidai da kofar fita.
ƙafafuwanta ta fara sakowa Kafin ta fito gaba ɗaya, idanun ta ne suka yimata nauyi sosai sakamakon hasken da ya dokesu domin kuwa ta jima rabon da taga haske a idanun ta duk kuwa da fuskar ta na lulluɓe cikin mayafi, a dudduƙe take tafiya domin kuwa ita ƙaɗai tasan yanda takeji ga yunwar da ke damunta sosai.
tafiya kawai take batare da sanin wane gari take ba, bata kuma san inda zataje ba a halin yanzu.
Ta san ta fita Lagos yanzu domin yanayin mutanen da take gani a nan suna giftawa basu yi kamada mutanen da ta saba gani a Lagos ba.
Tafiya kawai take batare da sanin ina zatajeba, duk hanyar da tayimata binta kawai take batare da dogon tunani ba.
A hankali take ganin tana kutsawa cikin gari sosai, domin kuwa inda take nufa yafi inda ta baro mutane.
Tana cikin hakan ne ta hango wata rumfa kamar kuma abinci ne ake siyarwa wajen, sai kawai ta juya akalar tafiyarta zuwa wajen, tana isowa taga a she rumfar mai sayarda shayi ce rumfar kuma tabb da mutane sakamakon ruwan sama ta aka ɗauke bada jimawa ba.
kamar dai yanda mutane suka sabayi idan suka ga leeya suma mutanen nan haka sukayi.
Amma jin tayi sallama yasa ƙalilan daga cikinsu suka tsaya
"ke! Mekike nema a nan?"
"Abinci"
"Ba'a sayarda abinci anan shayi kawai nake saidawa da biredi sai indomie da kwai, wanne kikeso?"
"Shayi da biredi zaka bani"
"Na nawa kikeso?"
Jakarta dake rataye a kafaɗarta ta sauke, hannunta ta saka cikin jakar tana lalubar kuɗinta, sai can ta cirosu sannan ta miƙa masa su gabaɗaya bata ko lissafa ba
"ɗari huɗu ne na duka za'a baki?"
Mai saida shayin ya tambaye ta.
"Ehhh"
"Abis ka bata kuɗinta Ni zanbiya mata"
Cewar wani dattijo dake zaune a wajen, mai saida shayin kuwa ya bata kuɗin ta tare da haɗa mata shayi da biredi a leda ya miƙa mata, zagayawa tayi har gaban dattijon ta durkusa.
"baba Nagode Allah ya saka maka da alƙairi, Allah yayi maka fiye da yanda kayimin"
Dashida sauran mutanen da suka rage a wajen zaune suka amsa mata da "Amin"
Har dattijon ya fito da ɗari biyu ya daɗa mata, hannu biyu ta saka ta karɓa haɗi da yimasa godiya sosai da Addu'oin alkairi.
Tana ɗagawa daga wajen mutanen ta samu wuri a gefen hanya ta zauna, ta buɗe ledar shayi da biredin ta fara sha.
K. MANSION SULEJA NIGERIA.
★*★*★
Zaune suke a daining area anata murnar dawowar papu daga Mexico. Mum, khulud da kuma papu duk suna zaune suna cin abinci cikin nishadi da yanayi mai daɗi.
"Pa, nayi farin ciki sosai da wannan labarin da kazo min dashi, kuma naji daɗin saukarka lafiya gaskiya mun gode wa AZMAFAT AIR TRANSPORT gashi kaje lafiya ka dawo lafiya"
"Bazakice kin godewa Allah ba saidai kice kin godewa AZMAFAT AIR TRANSPORT ai basu sukeda ikon zuwa lafiya sudawo lafiya ba duk Allah ne yakeda ikon, justice kaji mamana kho ɗaukin ganin ka yasa ta faɗi abunda ba daidai ba"
"Hakane kuwa khuludina ki gyara kinji"
"Naji"
"Yawwa mamana, ɗazu ina hanyar zuwa airport zamuje tarbon justice school teacher ɗin ku yakirani, he complain vitally cewa bakya maida hankali a class, yace ko jiya anyi test kinyi filled".
"Mum I'm trying my best, kawai dai malamin ya tsaneni ne, shiyasa komai nayi yace bai yiba".
"My kid ina kika taɓa ganin malami ya tsani ɗalibinsa, ko wanne malami zai koyar tsakani da Allah yake badan a yabashi ba, saboda haka kidaina faɗin ya tsaneki".
"Mum nasan mutane da yawa dana fisu a class ɗin nan amma yana nuna banbanci tsakanin mu"
"Uhhhhm What did you score in class today?" Cewar mum.
"Ten over ten"
"That's my brilliant daughter wow" faɗin papu.
"Ten over ten?" mum tayi tambayar cike da rashin yarda da abunda khulud tafaɗa.
"Yes mum"
"Okay zan iya ganin littafin naki"
"Of course, but mum why not the one that told me that I should always observed table minus"
"Karki damu inaso na ganshi kawai, wata rana idan zan nemi nagani zan faɗa miki, mum bata jira abunda khulud zatace ba ta fara kiran sunan dayammah!" Kiran dayammah mum tayi sau biyu kafin ta amsa mata da sauri ta fito ɗakin da take ta nufosu.
tana isowa wurin da gaida su Sannan ta juya ga mum
"gani hajiya babba me kike buƙata"
"Littafin khulud nakeso ki ɗaukomin a part ɗinta kiyi sauri kizo"
Khulud da ke faman hararar dayammah tun sadda ta fito tace mata
"kikula da kyau akwai cc tv camera a ɗakina karki min sata"
Ba wanda yace komai tsakanin dayammah, papu da mum.
Duk basu ce da khulud komai ba balle ita dayammah ɗin da ba kowa ba, juyawa kawai tayi domin ta aikata abunda aka sakata tayi.
Tura kofan ɗakin tayi yayinda hawaye suka zubo a idanun ta,
"Allah mai juya al'amari yanda yakeso kuma yanda yaga dama, haƙiƙa daba dan karatun ɗana ba da bazan zauna a gidan nan wannan ƙaramar yarinyar na tozartani ba harda ambata min sata. Allah sarki RAWAAN, Allah ya bayyanar da kai idan kana raye idan kuma baka raye Allah ya jiƙanka nasan da kana na da wannan Abubuwan bazasu faru damuba, da babu inda hajiya ƙarama zata ganmu balle ta ɗinga wulakanta Ni kamar haka"
ta ƙare maganar hawaye na gudu a fuskarta.
School bag ɗin khulud ta fara nema bata ganta a bedroom ɗin ba, ta fita a cikinsa sannan ta shiga Library room ɗin ta, achan taga jakar sai ta fito da littafin sannan ta fita ta rufe daƙin ta koma daining area ta kaiwa mum littafin.
Karɓar littafin mum tayi sannan ta buɗeshi yayinda hankalin papu gaba ɗaya ya koma kan mum yana jiran abunda zatace.
"Ten over ten" mum tafaɗa badan ta yarda da marks ɗin ba, kamar ba Malami ne yayi shi ba, amma ta share ba don komai babsai domin tana gudun ran papu yaɓace ne yasa ta faɗi abunda ta gani zane a littafin.
"Wow, five-five" papu yafaɗa yana lalewa da ulud "I'm proud of you my kid, zan baki kyauta"
"Thank you my pa"
"Wannan shine lokaci na farko da naga score ɗinki ten over ten" faɗin mum."but I'm so proud of you my love khulud"
"Millions of thanks my lovely mum, can we continue?"
"Yes" mum da papu suka faɗi.
ULUD
Zaune take a Library room ɗin ta, bayan sun tashi daining area ɗin, littafin tane ajiye a gaban ta sai red pen dake hannun ta, marks kawai take zubawa kanta yanda takeso har sai da takai ƙarshe sannan ta ajiye littafin, murmushi kwance a kan fuskar ta,
"Zanci gaba da cinye kyautar pa indai zanci gaba da haka, uhmmm I'm really proud of myself"
Washe gari, mum ce zaune gaban mirror tana shiryawa, yayinda papu ke zaune kan fabric sofa Yana duba wasu takardu, ƙarar wayar mum ce tacika ɗakin.
(Maman twins)
sunan da ya fito kan screen ɗin wayar kenan.
"Assalamu alaikum" mum ta furta sallama lokacin da ta kai wayar kunnen ta.
"Wa'alaikisalam"
Aka amsa daga cikin wayar
"Maman twins manyan mutane kaduna ta amshe mana ku kho, ba a kiran kowa yanzu kunzama manya"
"Hammmm hajiya fanaya kenan ni na isa in manta daku ah ah wlh wuyana baiyi kauri ba tukunna"
"Gashi kuwa kin manta maman twins, Ina ga ma saida kikaga nayi magana a group ne jiya nace a dinga sada zumunta koda ta wayane shiyasa kika kirani kho?"
"Ah ah Hajiya fanaya duk ba wannan bane ina kawar gidane kawai shiyasa nakiraki mu gaisa"
"Ahhh tho Nagode sosai Allah yabar zumunta, ina twins angirma kho?"
"Twins suna nan ƙalau amma dai ki ƙara da ɗaya akai don yanzu basu biyu bane su uku ne"
Mum na shirin yin magana matar ta kashe waya, ajiye wayar mum tayi kawai tana murmushi domin a zatonta haihuwa matar ta kuma yi.
"Justice Dan Allah idan zaka fita aiki ka ajiyemin khulud a school, bazan samu zuwa kaita ba yau, kasan bata son drivers suna kaita school"
"Okay wannan ba matsala bane kinji, ina khulud ɗin take?"
"Tana daining"
"Okay bara na idar sai mu tafi"
"Thanks a lot" mum ta faɗa tana murmushi.
Zaune akan daining ulud ce sanya cikin school uniform ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya.
"Wai me kike jirane, kefa nake jira kar nayi letting ki kawomin break fast ɗina" khulud ta faɗa cikin Daga murya tana kallon hanyar kitchen.
"Hajiya ƙarama kiyi hakuri yau nima nasan na makara wallahi ɗana ne aka dawo dashi daga boarding school ba lafiya shine Alhaji ya kaini tunda sassafe na dubashi, yanzu dai yaji sauƙi an maidashi a school ɗin amma kiyi hakuri nagama yanzu zan kawomiki"
"Who cares, where is my breakfast? Menene damuwata idan ɗanki bashida lafiya mezan yimiki mtswww"
"Allah ya huci zuciyar ki, ga breakfast ɗin"
Dayammah ta faɗa tana ajiye babban faranti agaban khulud, kayan da ke cikinsa ta ajiye gaban ta ko wanne daban.
"What!!?, what is this?"
"Breakfast ne na kawomiki"
"Ni sa'ar ki ce da zaki bani Wannan wawuyar amsa, me kika dafa anan"
"Toasted bread, da meat pie ne da kuma tea Hajiya"
Tea cup khulud ta ɗauko tare da zubashi cikin meat pie ɗin sannan ta watsawa dayammah sauran a fuska
"next time idan zaki yi girki kizo ki tambayi abunda nakeso bawai kiyimin irin wannan rubbish food ba, idan kuma kinsake haka na rantse sai kin bar gidan nan"
Ta faɗi maganar dai-dai da shigowar papu a daining area ɗin shi baima kula da dayammah dake dosƙare a wajen kamar gunki ba"
"Hey my kid are you ready for school"
"No pa, I'm not"
"Why?"
"Pa bata bani breakfast ɗina ba tun ɗazu ina nan amma taƙi ta kawo min"
"Dayammah by this time why" ya faɗa yana duba agogon da ke ɗaure a tsintsiyar hannunsa.
"Alhaji wallahi ga breakfast ɗin ta nan na kawomata, shine ta haɗe tea da meat pie ɗin nan waje ɗaya ta cakuɗe"
"Pa, wallahi ƙarya take nace mata ta idan zata kawomin break fast ta haɗamin da kwai shine takawomin ba kwai a ciki"
"Amma Hajiya jiya fa cewa kikayi u're lactose intolerant bakyacin ƙwai shine kuma yanzu zakice kina cin ƙwai"
"Karya take pa yaushe na faɗi haka?"
"Enough, dayammah na ajiyeki ne domin ki kula min da yarinya, kibata duk abunda takeso, kuma kada ki takuramata, ina fatar kin fahimta"
"Na fahimta Alhaji in sha Allah zanyi ƙoƙarin yin haka"
"Mamana ki tashi muje restaurant kiyi breakfast kinji I'm sorry".
Miƙewa tayi tare da ɗaukar school and food bag ɗinta suka fice gidan.
★★★
LEEYANA.
Tana nan zaune wurin da tasha shayin har akayi kiran sallar isha, anan ne hankalinta ya tashi domin rashin sanin inda zata kwana.
Miƙewa tayi taci gaba da kutsawa cikin garin da ta tabbatar da koma wanne garine to babban garine domin kuma haske ne ta ko'ina a cikin garin, ta ɗauki tsawon lokaci tana tafiya cikin garin tana bawa idanun ta abinci kafin tafara cimma gidaje.
Wata mata ta hango zaune tana soya waina ga mutane zagaye da ita da sauri ta isa laɓin wani gida ta ajiye jakarta, Sannan ta fito da ɗari biyun da dattijon nan ya bata taje wajen mai suyar wainar ta miƙa mata kuɗin
"abani abinci na ɗari biyu"
"A roba ko a leda"
"A leda zaki sakamin"
Lissafa wainar matar tayi harta ɗari biyu ta miƙa mata Sannan ta bata ruwan pure water ɗaya, leeya tayi mata Godiya sannan ta juya ta koma inda ta fito, zama tayi ta fara cin wainar hankalinta duk baya kanta, yau haka kawai takejin kawar Aleena na damunta.
Harta idar da cin wainar bata daina tunanin Aleena ba,
"shikenan duk kun mutu kun barni. babu Abbi, ba Ammie, babu uchie babu Nnene babu ke Aleena Gashi broth okene ma ya tafi ya barni".
Wani kukan tafashe dashi mai tsuma zuciyar mai sauraro. Haka tayi kukan harta gaji babu mai rarrashi.
Wani zani ta fito dashi, sannan ta sanya ƙafar takalmanta ta share wajen tsafff, sai kuma ta shimfiɗa zanin ta ajiye jakarta ta kwanta ta aza kanta kan jakar ta tayi pillow da ita zanin ta ta kuma lankafewa da rufa jikinta dashi tayi baccinta.
K. WAASIB MANSION.
"Dayammah!
"Dayammah!!" Ulud keta kwala mata kira tana zaune a resting parlour.
"Na'am Hajiya ƙarama gani nan zuwa"
Fitowa tayi daga kitchen ta tazo wajenta
"kina buƙatar wani abu ne hajiya ƙarama?"
"Ke rufemin baki kar na saɓa miki a wajen nan, shine ɗazu da safe kikaso ki haɗani da papu kho, kika ƙaryatani gabansa, wallahi summa tallahi dayammah kin kusa barin gidan nan alo tsiya alo danja, tunda nagane keba tsohuwar kirki bace, Aikin me kike yi a kitchen yanzu?"
"Jar miya nake haɗawa Alhaji yace ita yakeso yaci yanzu"
"Okay kije ɗakina ki ɗauko min tab ɗina ki sameni a parlourn ƙasa"
"Amma hajiya ƙarama da kin bari na ƙarasa don Allah, Alhaji yana jirana yanzu ya dawo office"
"Iyyeee! Yaushe bakin ki ya buɗe harda zan sakaki aiki ki kawomin wata Magana?, wallahi idan baki tafi inda na aikeki ba saina saɓamiki.....✍🏼
BAYAN WUYA...
009
By RUMANA M DIGGI
★★★
______________Da sauri tabar wajen, ta nufi part ɗin khulud. Tayi nema duniya a ɗakin bataga tablet phone ba, sai ta yanke shawarar zuwa ta sanar mata amma tana jin tsoron zuwa tagayamata.
Tunawa tayi da girkin da take a kitchen kuma tasan Alhaji na jira, fita tayi da sauri ta nufi functional electric pot ɗinda ta jona ta kashe ta bayan shigar ta kitchen ɗin.
Tana kashewa kuwa ta buɗeta da fatar red soup ɗinda take bata ƙone ba.
Tana buɗe functional pot ɗin taci karo da abunda ya bata mamaki ƙarara domin kuwa ruwa ne cike a cikin miyar anzubamata ruwa harsaida functional pot ɗin ta cika.
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un"
ta furta kalmar daidai lokacin da taji papu na kwala mata kira a daining area.
Fita kitchen ɗin tayi jikin ta a sanyaye
"Alhaji wani abu yafaru, kuma wallahi bansan waya aikata ba"
"Ban fahimceki ba, menene yafaru?"
"Alhaji wallahi abincin da na dafa aka zubawa ruwa bansan waya zuba ba"
"Kamar ya baki san waya zuba ba kina cikin kitchen, bayan ke akwai mai shiga kitchen ne?"
"Ah ah Alhaji ba wanda yake shiga kitchen amma wallahi bani na saka ruwan ba"
"Karka yarda da ita pa, karya take ita ta zuba ruwan da kanta"
"Da gaske?" Cewar pa Yana kallon khulud da tayi magana yanzu.
"Da gaske kuwa pa, jiya