Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
yanda kika faɗi haka abun yake ko bamuyi magana ba Allah zai saka mana da abinda sukayi mana a da hakan in Allah yaso"
Ƙarar saƙo ne ya shigo wayar mum tana dubawa kuwa bata furta komai ba ta fita bedroom ɗin na leeya.
Ita kuwa leeya mum na fita ta cire hijab ɗinda ta saka, sannan ta ɗauko kayan da ta cire da mayardasu jikinta, fita daga bedroom ɗinta tayi Sannan ta nufi kitchen ɗin gidan, tana shiga kitchen ko bata tararda kowa ba.
taji daɗin hakan sosai domin tasan ma ba wanda zai shigo kitchen ɗin face mum kuma yanzu suka rabuda ita.
Tunanin girkin da zatayi tafara yi, a cikin kalaluwan abincin da daga mum nayi wanda akeci da dare.
Dogon tunani tayi kafin ta yanke shawarar yin tuwon doya da miyar ganye.
sanin mum nason miyar ganye papu shima ba'a barshi a baya ba, uwar gayyarce kawai bata san yanda zatayi da ita ba domin kuwa a yanda take ganin khulud na kyamatar talaka to ko zinare ta girka mata da hannunta tasan bazata ciba shiyasa ta share maganar kawai ta fara aikinta.
Ta ɗauki tsawon mintuna ashirin, tana haɗa miyar gaba ɗaya kafin da kunna gas Cook, sannan ta fito da doya ta fara gyarata wacce zata tuƙa sakwara da ita.
tana cikin hakane kuwa sai ga mum ta shigo a gaggauce, ganin kamar ta makara a aikinta na yamma.
Baki sake take kallon leeya lokacin da ta buɗe functional electric pot, taga miyar ganye sharrr da ita sai kamshin spices take bugawa
"leeya haka kika iya girmi dama!?, bara na fara sonti tun kan naci nasan zatayi daɗi sosai, masha Allah"
Mum ta furta tana yamutsa miyar.
Murmushi kawai leeya keyi batare da tace uffan ba, duk yanda leeya tayi ta hana mum aikin amma furrrr mum taƙi saida suka ƙarasa aikin gaba ɗaya tare.
leeya ta fita da abincin daining, kaana ta koma bedroom ɗin ta tayi wanka domin mum ta ce mata taje tayi wanka tayi sallah ta fito master parlour akwai Maganar da papu zai sanar musu domin itama ta zama ƴar gidan yanzu.
Buɗe kofar bedroom ɗin ta tayi sannan ta furta sallama duk da tasan ba kowa a ɗakin.
Da mugun mamaki take bin kayan da tagani jibge kan gadon nata, "ikon Allah"
Ta furta a hankali tana isa ga kayan, saida ta iso daf dasu sannan ta gane sune kayan da mum ta gayamata zatayi mata online shopping kenan.
"Allah sarki mum, Allah ya biyaki da aljanna, Allah ya shirya miki ƴar ki yanda kike buri albarka kacin taimako na da kuke yi".
Ta ƙarashe maganar hawaye na zubowa a idanun.
Kayane da zasu iya kai kala ashirin, kuma a ganin ido kayan ba ƙanan kuɗi bane dasu, sosai tayi farin cikin ganin kayan, bakayan sakawa kadai ba harda takalma dasauran tarkacen kayayyakin kwalliya, ba ƙaramin mamaki tasha ba ganin niqab kala daban-daban kusan ma ko wane hijab dake wurin akwai niƙab kallarsa.
Kayan duk ƙananan kayane masu kyau ba atamfa ko leshi a ciki duk ƙananan kaya ne.
Dogayen riguna, riga da skirt, da kuma riga da wando.
Miƙewa tayi cikin tsananin farin ciki ta nufi bathroom a gaggauce tayi wanka ta fito, zama tayi kan dressing mirror ta shirya tsaff amma har ta gama shirin bata ɗaga kanta ta kalli mirrorn ba balle ta hango fuskar ta ko wani abu makamancin wannan, domin rashin kallon mirrorn shima yana cikin alkawarin su ita da amminta.
Body lotion mai ƙamshin ta ɗakko ta shafawa jikinta kaana ta duba wasu turaruka daga cikin waɗan da mum ta siya mata masu sanyin ƙamshi ta shafa.
Tun sanda take duba kayan ta fito da wasu riga da wando, waɗan suka birgeta sosai.
rigar kalar pitch ce yayinda wandon tazama kalar pink, sai kuma hular kayan itama kalar Pink da ta kasance ƙaramace mai kyau da akayiwa adon ƙananan stone iri ɗaya da yanda akayi adon rigar.
Kayan sunyi mata kyau sosai abun sai wanda yagani. Farin niqab ta ɗauko sannan ta cire kyallen da takeyin mayafi dashi kaana ta ɗaura niqab ɗin a fuskarta, sosai taji daɗin wannan siyayya da mum tayi mata, sai addu'o in alƙairi take yimata a zuci da baki.
Sakkowa tayi ƙasa ta koma master parlour ɗin ta zauna, bata tararda kowa a ciki ba saboda hakane ta zauna ta jira su har su iso, wuri ta samu ƙasa ta zauna ga kujeru da yawa a cikin parlourn domin kuwa parlourn babbane sosai yanada girma.
set biyu aka saka na kujeru bayan kuma akwai sofa's.
Tana cikin zaman ne tajiyo muryan mum da papu suna sakkowa, ƙara daidai ta nutsuwarta tayi kaana ta gyara zamanta tana jiran sakkowansu.
Tun suna kan steps ta miƙe da azama ta isa gare su cikin ladabi ta gaida su "mum naga kaya nagode, Allah ya biyaku, ya sakamuku da alƙairi, Allah ya baku abunda kuke nema duniya da lahira"
Mum kuwa murmushi kawai take bayan"Amin" da take faɗa.
Shima papu murmushi yayi kafin yace "Allah yayi muku albarka ki tashi kije daining ki jira mu gamu nan isowa, idan aka gama cin abincin sai kowa ya dawo idan aka faɗi maganar da za'ayi shikenan kho"
Da "tho papu" leeya ta amsa shi itama.
Sannan ta tashi ta nufi daining, takun khulud sukaji tana sakkowa daga part ɗinta, domin ita haka ƙa'idarta take duk inda za'a je sai kowa ya rigata zuwa wajen.
Wucewa kawai tayi ko sallama batayiba, kuma bata cewa kowa komaiba.
Sai papu ne yace"mamanah lafiya kike kuwa?"
Da murmushi ta waiwayo papu sannan ta bashi amsa "lafiya ƙalau nake my lovely pa, ai banyi tunanin kana nan ba, na ɗauka kana daining ɗin".
"Ah ah ai bazan isa daining ba idan baki fito ba"
"Tau muje kho pa, mum ki tashi muje".
Fuska a haɗe mum tace"Ashe kin san da zamana wurin nan, amma da kikazo justice kawai kikayiwa magana kho"
Dariya khulud tayi mai sauti har saida leeya ta waiwayo, domin batayi tunanin khulud na dariya har haka ba.
"Mum kice kinji haushin na fara yiwa pa, magana kenan humm, tho pa, kaji kho mum ta fara kishin mu"
Dariya shima papu yayi sannan yace "barta kawai ai tasan tsakanin ƴa da mahaifi sai Allah. five-five yarin yata".
Papu na faɗar haka khulud ta miƙo tafin hannunta papu ya haɗa da nashi suka lale cike da nishadi.
Hannun papu haɗe da na khulud suka isa daining, nan suka bar mum sake da baki tana binsu da kallo har suka zauna.
Kallon sama da ƙasa khulud keyiwa leeya lokacin da suka ƙaraso daining, ita kuwa leeya bata masan tanayi ba, Hankalinta na wurin papu da take yiwa sannu da isowa, sai kuma mum da itama ƙarasowarta kenan.
"Mum me kika girka muku hakane? naji sai wani ƙamshi yake".
Khulud tayi tambayar.
Tun kafin mum tayi magana Papu ya karɓe da faɗin
"wallahi kuwa mamana kinyi saurin tambaya kawai Nima na ƙagu naji abunda mumman ki ta dafa mana haka gaba ɗaya arean nan sai ƙamshi yake".
Murmushi mai sauti mum tayi Cikin murmushin tace "leeya kinyi shiru bakya cewa komai, har yanzu kin kasa sakewa sosai yanda nakeso"
Martanin murmushi leeya ta maidawa mum kana tace"tho mum nayi magana yanzu, haka yayi miki?"
"Yayi dama dai amma inaso yafi haka".
" mum Please ki kyaleta don Allah, tambayar ki fa mukayi amma kikayimana banza, kina amsawa waccan peasant ƴar talakawa".
"Mamana abar maganar nan Please kinji"
Cewar papu yana kallon yanayin leeya, idan taji haushin maganar da khulud tayi duk kuwa da yasan zataji haushin.
"Okay pa, na daina. Mum me kika dafa wai??
inaso nasani ne idan bazan iya cinshi ba kinga Sai a dafamin wani".
Girgiza kai kawai mum tayi kaana ta amsata da faɗin
"tuwon doya ne da miyar ganye".
"Haba dae mum, shikenan ko yaushe a dinga yin abu daya a gidan nan, gaskiya bazan iya cinsa ba".
Da ƙarfi papu ya ɗago ya kalli khulud da faɗin
"haba mamana ki daure ki ci wannan kinji, kinga ma jiya aka siyo sababbin spices ba irin waɗan da muka saba amfani dasu ba".
Kamar wacce ke magana da sa'anta haka ta kalli papu Sannan tace
"ba ruwana pa, Ni bazanci abincin nan ba this is final"
Ta karashe maganar cikin tsiwa.
Shiruuuu! Kakeji ba wanda ya ƙara faɗar komai a cikinsu, sai bayan wasu mintuna kaɗan mum ta fara zuba abincin ba wanda ya kuma yi takan khulud.
Ita kuwa khulud daddaɗan kamshin miyar na isar mata har wani lumshe idanu take a fakaice tana ajiyar zuciya a hankali
"okay pa, zanci abincin amma gaskiya bazanci da yawa ba saboda ma na fahimci ranka ya ɓaci da maganata ne shiyasa zanci, amma da badan haka ba ni bazan iya cin wannan kalar abincin ba. Kuma ko yanzu ba dayawa zanci ba"
cewar khulud tana janyo abincin gabanta.
Papu kuwa kallonta kawai yayi bai furta komai ba.
Abincinsa mum ta kawo masa gabansa, itama ta ɗiba wanda zata ci sannan ta kalli leeya tace
"gashi ki ɗiba wanda zai isheki kinji"
Murmushi kawai leeya tayi batare da tace komai ba.
ta janyo kular abincin gaba ɗaya da plate da kuma serving spoon ta ɗiba abunda zata iya ci.
Wawan tsaki khulud taja kuma ta na auna abincin kamar ba ita ba ce tace bazata ci ba.
Abincin suka ci sosai domin kuwa ba wanda bai ji daɗin abincin ba har gogan taku.
"Alhmdullillah leeya gaskiya abincin nan da kika girka yayi daɗi sosai masha Allah, kinyi ƙoƙari sosai da sosai har waɗanda basa ci yau sunci".
Faɗin mum tana kallon khulud da kanta yake a ƙasa tana cin abincin ta hankali kwance.
Cikin mamaki papu ya ɗago kansa fuskarsa cike da annuri ya furta
"Hajiyata kina nufin leeya ta girka abincin nan!?"
Ya tambaya da zaƙuwa.
Mum kuwa ta bashi amsa da faɗin
"ehh wallahi ita ta girka justice bakaji chanji ba?".
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un mum Dan Allah kice ba gaskiya kike faɗi ba, kice ba wannan ƙazamar ƴar talakawa tayi girkin nan danake ci ba"
Faɗin khulud hankali a tashe tana kakarin amai.
"Ahhh subhanallah menene kuma haka manana Please ki daina kar ki wahalar da kanki dan Allah, Abincin nan ya riga ya shiga ciki shikenan kuma sai a jirayi gaba".
Cewar papu yana yowa kanta a gaggauce domin dakatarda ita daga shirin aman da takeyi....✍🏼
BAYAN WUYA...
By RUMANA M DIGGI
EP...12
____________Leeya kam ko ajikinta domin kuwa ita har ta fara sabawa da halayenta.
a zatonta Yanzu komai khulud zata yimata bazata damuba tunda ta fahimci halayen ta.
Mum kuwa dariyar ta taketayi ƙasa-ƙasa dama da gayya tayi maganar saboda taga khulud taci abincin sosai har sai da tayi mamaki shine dalilin da yasa tayi maganar.
Cikin kuka da danasani khulud ke magana tana faɗin;
"wallahi ba'a yimin adalci, shine dan Rashin adalci Irin na Mutanen gidan nan baza'a iya gayamin ƴar tsince-tsince a titi ce ta dafa mana abinci idan zan iya ci sai naci, idan kuma bazan iya cin sa ba shikenan.
Amma za'a zo a kyaleni naci wannan Abincin wallahi sai Allah yamin sakkaya"
Khulud ta ƙarashe maganar tana ƙara sakin kuka.
Hawayen ta papu ya share sannan yace "kiyi haƙuri my kid hakan bazata sake faruwa ba kinji in sha Allah komai za'a yi a gidan nan za'a sanarda ke ba wanda zai kuma yin abu a gidan nan batare da sanin kiba ƴar gatan papu da mummunta"
"Ƴar gatan pa, dai mum kam ai ga ƴar gatan ta can waccan ƴar talakawa da ba'a masan dangin ta ba"
Cewar khulud tana jefawa leeya wani wulaƙantaccen kallo.
Leeya kam bata masan tanayi ba.
Da sauri papu ya furta muje daining mum zata biyomu nayi miki wani kyakkyawan albishir kinji"
Papu Yayi hakan ne domin bayaso leeya ta fahimci maganar da suke tsakanin su, kuma yasan idan bai janye khulud ba zata iya yiwa leeya wani Abu mara daɗi, haka kawai yakejin tausayin leeyana sosai shiyasa ita ma yakeso ya kwatanta qaunarta data khulud ya riƙeta tsakani da Allah amma yake Ganin haka bazata yiwu ba tunda khululud bataso.
Parlour suka wuce khulud da papu, daining kuma ya rage saura mum kaɗai da leeya.
Bayan sun kammala ne mum ta tafi tabar leeya daining area ɗin domin ta tattare kayan wanke wanke.
Kitchen ta kai kayan, bata fito kitchen ba saida ta gama wanke kayan kaffff.
Kafin tazo ta tsaftace daining area, kana ta wuce master parlour.
Da sallama ɗauke a bakin ta ta shiga parlour yayinda ta sami wuri a ƙasa ta zauna,
Papu ne yakai dubansa kan leeya sannan yace
" ke! Tashi ki zauna".
Jin yanda papu yayi maganar ne ya saka ta miƙe da hanzari ta zauna kan wata one sitter sofa dake gefe.
Sosai khulud taji daɗin abunda papu yayi da jin yanda yayi mata magana cikin tsawa, har take ganin jirgin ta ya hango mata dalilin zamansu wurin, domin tana gani kamar koran leeya papu zaiyi yau.
itama mum ta ɗan tsorata amma ta dake domin tasan yanada wuya justice ya aikata abunda take tunani.
Gyaran murya kaɗan papu yayi domin hankali kowa ya dawo jikin shi.
Haka kuwa akayi papu na gyaran murya kowa ya nutsu yana saurarar maganar da papu zaiyi.
Sosai papu ya ɗaure fuska kamar bashiba, fuskar sa kamar bai taɓayin dariya ba ya kalli kowa sannan yace" Assalamu alaikum".
"Wa'alaikasalam"
waɗanda suke iya amsawa suka amsa masa.
Ba wani babban dalili yasa nace mu taru anan muyi magana ba sai dan na shaida muku cewa a daren yau muna cikin maɗaukakin farin ciki mara misali. Wanda duk masoyin mu dayake ƙaunarmu ya kamata ace shima yana cikin wannan farin ciki.
Babban abin farin cikin da ya samemu shine Turab Khattab waasib ya zama Chief of military health service a safiyar yau aka gaba tardashi gaban kowa da kowa"
"Alhmdullillah, alhmdullillah". Mum ta faɗa kwallar farin ciki na sakkowa a idanun ta, yayin khululud keta ihu tana tiƙa rawa
Itama leeya hamdalah take kawai duk da batasan akan wa ake magana ba.
"Sai magana tagaba" cewar papu.
Nan hankalin kowa ya dawo jikinsa a karo na biyu.
"Leeyana!" Papu ya kira sunan leeya idanun sa na kanta.
Anan wani sabon farin ciki ya sako khulud gaba Saboda tasan ƙarshen zaman leeya yazo a gidan.
"Na'am" leeya ta amsa masa kanta a ƙasa gabanta sai dukan uku-uku yakeyi domin itama ta fara tunanin haka.
Sosai hankalin mum ya tashi da abunda papu yake shirin yi, domin itama ta fara gane nufinsa.
"Leeyana kinyi makaranta?"
Chakkk komai ya tsayawa khulud yayinda taji tambayarda papu yayiwa leeya, nan fuskar ta changer yanayi sosai. Domin kuwa indai mutum yanada fahimta dole ya fahimci tsantsar hasada data bayyana a fuskar khulud
"Eh papu nayi makaranta" cewar leeya kanta yana ƙasa har yanzu.
"Okay a ina kika tsaya a karatun?''
"Ss2"ta bashi amsa a takaice
"Okay" papu ya faɗa daga haka leeya bata kara furta komai ba.
Cikin tsananin bakin ciki khulud ta kalli papu tare da faɗin;
"What!? Mekakeso kace pa, kana nufin school zaka saka wannan yarinyar, meyasa pa, meyasa? So kawai kake in fita ana nuna ni ana faɗin akwai ƴar government school a gidan mu kho?. So kake ka hanani shiga cikin abokaina kho pa, meyasa haka pa? Kaima ka fara yimin irin abunda mum take min kho? Wallahi nidai bada fatar bakina ba pa.
sai dai kaje ka sakata ɗin nagani.
Munafukar banza ƴar talakawa kawai ƙazamar yarinyar mai tsince-tsince a titi wallahi bari ya-Turab ya dawo nasan sai kinyi danasanin zama a gidan nan ko kwana ɗaya bazaki ƙarayi a gidan nan ba idan ya dawo".
Khulud ta ƙarashe maganar cikin kuka, a guje tabar parlourn ya rage saura mum da papu da Kuma leeya.
Miƙewa tayi itama tanufi part ɗinsu harga Allah yau kam kalaman khulud sun ƙona mata rai amma haka ta danne domin bataso mum ko papu ɗayan su ya fahimci haka.
"Allah ya sauwaqe" shikaɗai mum ta furta bata ma jira cewar papu ba ta juya ta tafi.
Washe gari tunda da sassafe bayan sun kammala break fast papu kuma yafita aiki sai mum dake part ɗin ta tana gyarawa.
Zaune a parlour leeya ce ta kammala gyara parloun itama tana zaune ita kaɗai tana kallo abinta.
Banko ƙofar parlourn da akayi da ƙarfine yasa ta miƙewa da sauri tana jiran ganin wanda zai shigo.
Khulud ce ɗauke da kaya wanki niƙi-niƙi.
Saida takai daidai fuskar leeya ta watsa mata kayan tare da faɗin;
"ga kaya na nan ki wankesu sai sun fita fes, idan kin gama wanke su da hannunki kuma kije ki sakasu a washing machine ki ƙara wanke su dan bazan iya saka abinda ƙazaman hannayen nan naki zasu wanke ba batare da an sake wankewa ba"
Murmushi mai sauti leeya tayi cikin murmushi nata take faɗin "yar uwata wannan ba komai bane kinji, Ni a rayuwata Bama abunda nafiso a aiki kamar inga inayin wanki. Saboda haka Ni kin faranta min rai ma da kika bani aikin nan"
leeya ta faɗa tana tattare kayan wankin.
Cikin jin haushin abunda leeya tace ka kalli fuskar ta a yatsune tace
"well, I don't care if you love to Wash cloth, Nidai na gayamiki wallahi karki sake kimin kuskure idan kho ba haka ba zaki yabawa aya zaƙinta, kuma ki tabbata bayan kin gama duk wannan ki goge kayan Gaba ɗaya sannan kizo ɗakina ki jeramin su closet drawer".
"Karki damu zanyi komai kinji sister khulud".
A tsawace ulud tace "ke! Wallahi karki ƙara kirana da ƴar uwarki, Allah ya kiyaye yamin tsari na zama ƴar uwarki kina talaka, mummuna, kaskantacciya dake ƴar tsince-tsince a titi sannan zaki kirani da ƴar uwarki".
Wawan kuka leeya ta saki tare da barin wajen ta nufi part ɗin ta ta mugun gudu ko gabanta bata kallo harta isa part ɗin ta.
Ƙofar ɗakin ta janyo ta rufeshi rufff tare da murza masa makulli ta dawo kan gadon ta zube tanata rizgar kuka.
Shekaru biyu zuwa uku da suka gabata ta tunano. Wata rana suna zaune ita da amminta da Aleena, lokacin Aleena tana zaune tana wasa da ƴar tsana. Ita kho leeya tana gyara wake a faranti tare da ammi, sai taga kawai ammi ta cire hannunta cikin farantin tayi tagumi idanuwanta na cikowa da kwalla.
Cikin matsananciyar damuwa ta ajiye farantin tazo ta durkusa gaban ammi tare da janye hannayen ammi daga tagumin da tayi tace
"amminmu lafiya meya faru ne naga yanayinki ya canja yanzu nan, wani abu akayimiki ko kuma kin tuna da wani abu mara dadi ne ammi?.
Share hawayen da suka gangaro a kumatunta tayi sannan ta kalli leeya da fuskar Tausayi tace "leeyana inajin tausayinku ne idan na tafi na barku, ina jin tsoron barinku kuyi maraici leeya musamman ma ke da mutane ke farauta. Wallahi