BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   28 / 61

81K to 84K   out of 180.4K words

ce asalin mahaifiyar leeya.

"Kedai kibari kawai, idan na dawo zan kiraki, Bara na tashi naje na fara aikina tun kafin yazo ya naɗamin na jakai"

"Tau yayi, Allah ya taimaka sai kin dawo ɗin" cewar zohal tana yanke wayar.

Miƙewa leeya tayi tare da nufar kitchen area. Aikinta ta farayi hankali kwance, domin kuwa aikin yana bukatar nutsuwa.

Saida ta kammala komai, kafin ta zube ko wanne a wurinda ya dace.


"Leeya me kike dafawa haka naji ƙamshi nata fita a ko'ina"

Cikin mamaki na waiwayo, idan ba mafarki nake ba to Muryar khulud naji tana yimin Magana.

Mamaki bai ƙarasa shigata ba saidai na waiwaya naga fuskar ta ɗauke da murmushi.

"Bazaki amsa min ba leeya, kiyi haƙuri da duk abunda ya faru a baya kinji, ki zo mu zauna lafiya kinji komai ya wuce dan Allah" khulud ta faɗa tana dafa kafaɗuna.

Saboda tsananin mamaki, maganar ma kasa fitowa tayi daga bakina, sai da kyar na samu nace mata "ya-Turab ya sakani nayi masa girki".

"Uhhm khulud tayi murmushi kaɗan "kaga ƴan CATERING SCHOOL gidan namu sai ƙamshi yake, Bara na barki kiyi aikinki saboda nasan halin ya-Turab yanzu zaice kin ɓata masa lokaci"

Ko amsa mata banyiba, ta juya ta fita daga kitchen ɗin. Jikina gaba ɗaya ya mutu da ganin sauyin khulud domin ina tunanin kamar wani abun take shiryawa.......✍🏽















BAYAN WUYA......








By RUMANA M DIGGI








EP.30



_________________da kyar na samu na kammala sauran aikin da ya rage bayan na haɗa masa pimm's juice.

Jido kayan na farayi daga kitchen zuwa sashensa, sai dai har na kusa kammala kai kayan ban ganshiba.

sosai hakan yamin daɗi, na koma kitchen da nufin dakko juice ɗin da na hada masa, ina fitowa sashen nasa sai nayi karo da khulud itama ta fito da system a hannu tana tafiya tana ɗan dudduba wa, da alamu wani abun mai muhimmanci take dubawa.

"Leeya har kin kammala aikin"

"Ah ah juice kawai ya rage na kaimasa shikenan na kammala sannan nayi wanka nayi sallahr la'asar"

"Okay dan Allah idan kin kammala duk abunda zakiyi kizo ki tayani yin assignment saboda naga kin iya mathematics sosai lokacin da muna BUSY BRAIN"

"Okay ba damuwa ki jirani kaɗan yanzu zan kammala" na faɗa ina wujewa batare danaji abunda zata faɗa ba.

Juice jug ɗin da na haɗa masa na ɗakko tare da komawa sashen nasa, kamar yanda nayi tsammani kuwa ban tarar dashi a parlourn nasa ba kuma hakan yamin daɗi sosai, na juya da nufin na fita muka kusa cin karo dashi, da sauri na ja baya da ƙarfi ina toshe bakina gudun kar kuka ya suɓucemin nayi wani laifin kuma.

"Ke! Dan ubanki wari nake da zaki wani toshe baki da hanci"


Jijjiga kai na farayi kukan da nake riƙewa ya suɓucemin

"dan Allah ya-Turab kayi hakuri, wallahi ba warinka nakeji ba, ina jin tsorone kar kuka yazo min kuma nayi maka laifi shine na rufe bakina, amma wallahi bada niyyar komai nayi ba"

"Me zai sakaki kukan, dukanki akayi da zakizo daga shigowar ki nan sai ki fara kuka, daina kallona da waɗannan mayun idanun naki ko yanzu ki gansu a ƙasa, shegiya mai siffar aljanu. Fita daga nan kiban wuri ko yanzu na karyaki wallahi"

Da sauri na raɓe ta gabansa zan wuce, wawan rankwashi ya sakarmin akai naji kamar dutse ne ya dakeni dashi.

"Wayyo ya dan Allah kayi haƙuri wallahi bazan sake kallon ka ba" na faɗa cikin matsanancin kuka.

"Bar nan nace"


Da sauri na fito part ɗin nasa ina cigaba da tafiyata ina share hawayen da ke zubowa, jinayi an dafa kafaɗata ta baya. Ban wani razana ba saboda sanin cewa mum ce, juyowa nayi a hankali na kalleta da sauri ta jaa baya da ƙarfi.


"Khulud lafiya naga kin jaa baya kamar wacce taga wani abun tsoro"
Na faɗa cikin sassanyar murya irin ta wanda yayi kuka ina ƙara tsureta da idanuwa na.

"Ke zanyi wa wannan tambayar leeya meyasameki kike kuka, ya-Turab ne kho"

Da sauri na ɗaga mata kai ina ƙare rushewa da kuka.

Cikin tausayawa khulud tace

"kiyi hakuri kinji, wallahi lamarin ya-Tk sai shi, kinga Ni na huta bana ma wuni a gidan ina school, kuma idan na dawo yamma tayi bana ganinsa sosai sai idan an fito cin abinci, da safe kuma koda nakeyin break fast ɗina bai fito ba, idan na tafiyata bana dawowa sai yamma, kinga ba yanda za'a yi mu dinga haɗuwa".

"Khulud dan Allah wani abun kikeso kiyimin ne"

Dan murmushi khulud tayi domin ta fahimci abunda nake nufi

"me kika gani ne leeya, ko saboda kinga nayi miki magana, wallahi dama can rashin fahimtar rayuwane yasa nake miki irin haka, yanzu dana faɗa tarkone yasa nake ganin nayi babban kuskure a can baya, saboda haka ina neman gafararki kinji"


Khulud ta faɗa har iyakar gskiyarta tana haɗe hannayenta biyu wuri ɗaya alamar roƙo.

"Leeya, wallahi na faɗa ƙaddarar soyayya ne da wani bawan Allah, wanda nasan samun sa zaiyi matuƙar wuya a gareni sakamakon abokinsa"

"Abokinsa kuma" na tambaya da mamaki, "abokinsa ne zai hanaki mallakeshi" na kuma tambayarta.

"Eh, abokinsa zai hana na mallakeshi domin id wani Mutum ne da yake saurin yarda da mutane musamman ma abokinsa, shi kaɗai ne amininsa a kaf faɗin makarantar mu, kuma duk abunda ya sakashi shi zai aikata, idan kuma ya hanashi ya hanu kenan.
Haka shima idan ya umurce shi da yin abu koda bayaso sai yayi saboda ya faranta masa rai kuna idan ya haneshi ya hanu kenan"

Khulud ta faɗa kwalla na gangaro mata. Taci gaba da faɗin "zakiji cikakken labarin in sha Allah, kibari duk ranar da kika nutsu kizo ɗakina muyi magana ko kuma ni na sameki a ɗakin naki"

Tausayinta ne ya kamani sosai ganin yanda take zubarda hawaye akan ɗa namiji,

"kiyi haƙuri kinji, in sha Allah zamu shawo kan matsalar, kuma zan tayaki da addu'a idan hakan alƙairine Allah ya tabbatar miki. Kuma zan kira ƙawata zohal in sha Allah, itama zata bada idea"

"Nagode sosai kinji, dan Allah ki yafemin gaba ɗaya. Wallahi har kunyarki nakeji"
Cewar khulud.

"Allah sarki, wallahi khulud Allah ne shaidata ni tun farko ban taɓa riƙeki a rai ba, saboda haka komai ya wuce kinji"

"Yawwa Nagode, sai kin fito kho gani nan a parlour ina jiran ki"

"Okay" leeya ta faɗa tana barin wajen.

Haƙiƙa khulud taji tsoron ganin leeya a yau, tunda take da leeya bata taɓa haɗa idanu da ita ba balle tasan yanda idanunta suke, asalin pure blue.


Da suka haɗa ido da ita, ta tsorata matuka har takai ga ta jaa baya da ƙarfi, amma kuma sai ta nuna mata ba komai. Saboda karta fahimta.







***

A can ɓangaren leeya kuwa tana komawa part ɗin ta tayi wanka tare dayin sallah, Sannan ta shirya cikin riga da skirt na jumper cotton silk.

Ɗan ƙaramin mayafi ta ɗakko ta yafa, sannan ta saka niƙab ɗin ta.


Wayarta dake a jiye a gefe ta gaban dressing mirror ta ɗakko, number zohal ta lalubo tare dayin dialing number.
Bayan ta ɗaga wayan ne sun ɗan gaisa, da yake ba wata gaisuwar kirki sukayi ba domin basu jima da gama wayar ba.

Leeya kuwa ta fara koro mata bayanan dalilin da yasa ta kirata.
Murmushi mai sauti ZOHAL tayi tare da faɗin "baza'a bata shawarar ba taje can ta ƙarata, wallahi wannan yarinya ta raina wayon mutane, sai yanzu tasan kinada muhimmanci da zata nemi shawarar ki, taje can wurin masu kuɗi irinta ta nema, wallahi amanar ki ce kawai ke fita a kanta, saboda haka mu bamuda abunda zamucemata sai dai Allah ya kyauta, ya kuma bata ƴan uwanta masu kuɗi da zasu bata shawarar abunda ya dace"

"No zohal, wannan ba reason bane kawai kisamu abunda zakice kinji Please. Ai ba duka aka taru aka zama ɗaya ba kuma Ni wallahi ban taɓa riƙeta a raina ba kinga ko yanzu ita ta kawo kanta gareni, wannan alamace daga wurin Allah da yakeso ya jarraba iyakar hakurina, kinga tun muna yara tayi min abubuwa da dama da bana tunanin mantawa dasu, har kuma muka girma bata daina ba ni kuma ban daina abunda nake ba tun a farko wato haƙuri, yanzu kuma ta kawo kanta tana nunamin kuskuren nata ne, kuma bata fahimci rayuwa ba a can baya. Ai kuwa kinga dole nayi mata uzuri kho, ko dan mahaifin ta da mahaifiyar ta zan mata komai Zohal"

Jikin zohal yayi sanyi sosai da jin kalaman leeya saboda haka ne tace

"to shikenan yanzu ki tambaye ta idan har wani abu ya taɓa shiga tsakanin ta da abokin shi wanda takeso ɗin, idan kuma ba abunda ya taɓa shiga tsakanin su nan ma zamu fahimci wani abu"

"Yawwa bestie na haka nakeso naji kin faɗa Nagode sosai"

"Ya batun Private lover ɗin ki"

"Hmm kedai bari kawai, har yanzu ba reply"

"Okay to kiɗan kara haƙuri kadan, ki bada lokaci muga. Ko ki kara kiran number"

"Ke nifa har na gaji da kiran wayarsa domin kona kira ba'a ɗagawa, banaso kuma na cika yawan kiran kuma yazo kashe wayar alhali na tura masa saƙo kuma bai yi reply ba, kar garin neman gira a rasa ido"

"Haka ne kuma fa, to kijira mugani"

"Okay" ta yanke wayar da faɗin wannan.








*****

A can ɓangaren turab kuma;
Tunda leeya tabar sashen gaba ɗaya ya dauki daddaɗan kamshin girkin ta, juice jug ɗin da ta haɗa masa ya ɗaga tare da tsiyayawa kaɗan yasha, yana isa cikin maƙoshinsa kuwa ya lumshe idanun sa ya ƙara buɗewa, ƙara tsiyaya wa yayi yayi fiye da rabin cup ya kuma kai bakinsa ya shanye.

Sosai yayi mamakin yanda ta iya haɗa pimm's juice lafiya ƙalau haka, domin rabonsa da shan daddaɗan juice irin wannan tun a Mexico.


Ƙarar wayarsa yaji Alamar kira ya shigo, a nutse yakai hannu ya ɗauki wayar yayi gyaran murya.

"Hello man fahad ango ya akayi kun ƙaraso"

"Eh gamu a gate"

"Okay ganinan tafe"

Ajiya wayar yayi tare da nufar hanyar fita.








****
Leeya kuma bayan ta gama waya da zohal ta tashi ta fita waje, a parlour ta sameta sai faman aiki take a system.
"Leeya kin fito"

"Eh, na fito wallahi kinga har na kammala nayi wanka shine na fito muyi assignment ɗin idan mun kammala kuma sai naje na ɗora girkin dare"

"Tau shikenan, kiyi sauri mu kammala sai muje nima na tayaki girkin kho"

Cikin mamaki na ɗago zanyi magana ta takatardani da faɗin "Leeyana ya kamata ki daina mamaki a duk al'amurana, kinsani ba abunda yakeda wuya a wurin Allah, kuma wani iko na Allah ya wuce gaban mamaki"

Ban furta komai ba na mayarda kaina kan system ɗinta muka fara aiki.

"Kinsan me" khulud ta faɗa tana kallona.

"Ah ah sai kin faɗa"

"Ki tashi muje Library room ɗin mu muyi assignment ɗin nan, NASAN yanzu ya turab zai shigo kuma naji fakawar motoci ina tunani yayi baƙi ne, dan har waya naji yana yi yanacewa "ku shigo mana ko gidan baƙon kune. Kuma naga kina tsoron sa sosai shiyasa nace kizo mu bar nan kar ya shigo, NASAN su ya fahad da ya Zafaran ne sukazo kinga ba kunyarsu yakeji ba ko a gabansu zai iya cimana uba".

Tunawa leeya tayi da ya cemata tayi girkin mutum uku, nan da nan kuwa ta gaskata abunda khulud ta faɗa mata.
da azama suka miƙe suka bar parlourn.

Suna shigewa kuwa sai gasu turab sun ƙara so parlourn sai sheƙa dariya suke abunsu, Zafaran kam kamardai ko yaushe idan ya shigo suleja, dafe yake da saitin zuciyar sa, sai kiran sunayen Allah yake a bakinsa.


Turab ne ya ɗan dubeshi kaɗan cikin sigar zolaya yace " lewa ta motsa kho"

"Hmm, bari kawai man turab, wallahi duk inda lewa take a yanzu motsin ta yana tafiya da motsina da kuma kowane harbawa da zuciyata takeyi a halin yanzu"

"Iyyeee kaji majnoon a gaskiya wannan yarinyar ta wahalar damu, ina tabbatar maka idan Allah ya ƙaddara saduwarmu da ita saita biyamu ladar wahalar da mukesha wallahi, ko ya ka gani man Fahad" cewar turab yana mayarda kallonsa ga Fahad.

"Eh mana ai shima kansa yasan sai ta fanshe wahalarda mukayi akanta kota hanyar girka mana abinci mai daɗi ne"

Tattausan murmushi Zafaran yayi sannan yace"lallai kuwa zata fansar da kanta har kuma ta fanshe Ni Nima indai ta hanyar abinci ne, domin a ta Wannan ɓangaren kan ta wuce boss"

"Ae dai zamu gani" Fahad ya faɗa daidai lokacin da suka ƙara so sashen nasa.

Zama sukayi a ɗan madaidaicin Centre carpet ɗin da ke tsakiyar parlourn, inda turab ya fara jido musu abincin da yasa aka girka musu, sosai suka ƙagu da su fara cin abincin domin ƙamshin sa ya kaimusu ko'ina.

Bayan ya buɗe abinci ne kowa ya ɗiba wanda yasan zai iya cin yewa, cooler da aka saka bitterleaf soup Zafaran ya buɗe, cikin matuƙar farin ciki ya kalli Turab yace"wannan ai miyar igbo ce, kuma igbo kaɗai suka iya haɗa miyar nan ta fito sharrr da ita kamar haka, dama mum igbo ce ba bafulatana ba"


"Uhmm--hmmm, ba mum ta dafa ba"

"Kunada House-maid igbo ne"

"Ah ah"

"Waya dafa to"
Zafaran ya kuma tambaya.

"Wata yarinya ta dafa, nima na faɗa ne kawai wallahi banyi tunanin zata iya dafawa ba, kuma dana sakata ba musu ta tashi taje tayi kaga alamar ta iya kenan"


"Ita yarinyar igbo ce" fahad ya tambaya yana kai bruschetta bakinsa.

"Wallahi nima bansanshiba, ƴar ƙawar mum ce data rasu shekarun baya, kuma bana tunanin mahaifiyarta igbo ce gskiya, saidai ko mahaifinta duk da bansanshi ba".

"Ikon Allah amma tayi ƙoƙari gaskiya" Zafaran ya faɗa cike da al'ajabi.

Cin abincin su suka farayi cikin kwanciyar hankali har suka kammala gaba ɗaya, aka kira sallahr magariba sannan suka bar gidan bayan sun shiga sashen mum sun gaida ita.

Dayake papu baya ƙasar yasa basu jira dawowarsa ba suka yi tafiyarsu.







*****
A can ɓangaren su khulud kuwa bayan sun kammala assignment ɗin da aka bata, sai suka nufi kitchen domin girka abincin dare.

Khulud ce ta kalli leeya cikin kulawa tace;
"Sis-leeya me ya kamata mu girka"

Ɗan ɗaga kaina nayi kaɗan ina tunanin abunda ya kamata mu girka da daren nan kafin nace

"mu dafa jollof rice da fried potatoes kho, sai kuma muyi fried plantains"

"Wow gud ideas wallahi kamar kinsan ina kwadayin fried plantains, fara aikin ko mr. Chief kinsan ba komai na iya yi ba" khulud ta faɗa tare da laƙato hancin leeya.

Itama leeya ta rama abunda tayi mata, cikin nishadi.


A can kofar kitchen ɗin kuma mum ce tsaye, farin cikin ta ya kasa ɓoyuwa na ganin yaran sun haɗa kansu.


"Allah yasa ku ɗore haka ƴaƴana" ta faɗa a zuciyarta tana barin kitchen area ɗin.

Saboda ta taso ne ta taya leeya aiki kar ta barta da aikin ita kadai yayi mata yawa, ganin khulud na tayata yasa ta koma domin tayi wani aikin duk da ba wani aiki daya rage domin kuwa gaba ɗayan gidan ba inda basu tsaftace ba.

Sai kusan karfe bakwai da rabi na yamma suka kammala aikin komai da komai kaana suka wuce sashensu, ko wacce ta nufi ɗakinta domin su huta.

Leeya na shiga ɗakin nata tayi sauri takai hannu ta ɗauko wayanta jin ƙarar shigowar saƙo.


Sai dai wani abun ban haushin koda ta buɗe saƙon na MTN ne bawai sakon da takeso ta gani ba.

Ajiye wayar tayi tare da nufar ban daki tayi wanka, tayi alwala kaana ta fito ta saka kayanta, ta zumɓula babban hijab ɗin ta ta tayarda sallah.


Tana cikin sallar ne taji ƙarar buɗe kofa, khulud ce ganin leeya na sallah yasa ta juya ta koma bedroom ɗin ta.

Leeya kuwa tana sallame sallar tayi addu'o in da zatayi sannan ta ninke sallaryar ta maida ta inda take ajiyeta tabar ɗakin nata.

Bedroom ɗin khulud ta nufa bakin ta ɗauke da sallama cikin siririyar muryarta.


"Khulud ya dai, ya kike, ya gajiyar aiki kuma"


"Gajiya kam tana nan wallahi, ai naje bedroom ɗin ki kina sallah"


"Eh, wallahi shine na kammala nazo ai"

"Ok tau muje daining, dama shine naje na faɗa miki kuma na tarar kina sallah"

"Da kin bari anyi sallar isha ai tunda kinga saura kaɗan".


"Okay tau ai ba damuwa mu Bari idan aka yi sallar sai muje"
Cewar khulud.

"Yawwa, na kira zohal munyi magana da Ita, kinji yanda tace min" leeya ta kwashe kaff yanda sukayi da zohal ta gayamata.

"Eh, a gaskiya zohal bata faɗi karya ba, wannan shine abunda yakamata na fara dubawa tun a farko, Sayyid maleek al-shams shine cikakken sunansa, kuma shine babban abokinsa na hakiƙa.
tun ranarda muka fara haɗuwa da sayyid jininmu bai haɗu dashi ba, kuma babu rana ta Allah da zata fito idan mun haɗu da sayyid bamuyi faɗa ba, bama ƙaunar Sayyid ko kaɗan haka zalika shima baya ƙaunarmu, mu huɗu ne kawayenmu kuma tare muke komai duk halayenmu ɗaya ba abunda ya banbanta , sai ɗaya daga cikinmu ce da ake kira reemah rabeel, ita kaɗaice ta banbanta damu kuma ita kadaice take shiri da Sayyid duk a cikinmu.
leeyana zakiyi mamaki sosai idan nace miki Sayyid shine babban abokin wanda zuciyata take bege dare da rana, kuma shi wannan danake ƙauna wato IDRAK MANAF, sabon ɗalibi da aka kawo mana a School ɗin mu ne, amma babban abunda ya kamata kiyi mamaki akansa shine shi Wannan mutumin da nake ƙauna wallahi talakane sosai kuma bashida mahaifi mahaifiyarsa ita take ɗauke da nauyi su da taimakon sa shima, da sana'ar faci da yake yiwa babura da motoci.
da Farko da muka ganshi munyi tunani shima mai kuɗi ne kamar Sayyid, ashe ba haka bane yanda mukayi zato domin kuwa wata rana da muka fita ranar weekend nida ƙawayena motarmu tayi faci,
da muka tambaya aka nuna mana inda akeyin faci bamu tsaya ko ina ba sai gaban rumfarsa dayakeyin faci, a razane na kara daga kaina na kura masa idanu domin tabbatarda shine koba shi bane, ban gama tantance wa ba naji raudha ta daki kafaɗa ta da ƙarfi

"ke id nake gani ko idanuna ne"

"Wallahi shine, raudha duba fa kingani" cewar amrah tana ƙara kafeshi da idanu.

Murya na rawa na kira sunan shi

"id, ina mai wurin nan"

Miƙewa Id yayi da murmushinsa yazo har gabanmu da kuma abun yin faci a hannun sa.

"Id tambayar ka nake ina mai wurin nan"

"Wa kika gani anan Hajiya, faci za'a muku?"
Idrak ya faɗa yana durƙusawa gaban tayar motar mu.

Da sauri raudha ta banko ƙofar motar ta fito ta nufeshi ta cewa

"kai wai da gaske kaine anan, faci kake yi kuma kake karatu

28 / 61