BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   29 / 61

84K to 87K   out of 180.4K words

a Rooney"
Ta faɗa cike da cikin tsiwa da masifa.

"Hmmm" kawai idrak ya faɗa yana ƙoƙarin fara aikinsa.

Da sauri amrah ta fizge abunda yakeyin faci dashi tayi cilli dashi gefe ɗaya

"malam magana ake maka kayi banza da mutane, ko dai bakai bane IDRAK MANAF ba na Rooney.

Cikin tsananin ɓacin rai id ya kalli amrah da raudha yace.............................✍🏽





BAYAN WUYA........












By RUMANA M DIGGI








EP.31






_______________"malamai idan kun tashi ku ɗaga nayi muku aikin ku, idan kuma ba aikin kukeso ba dan Allah ku tafi daga nan"

Dariya amrah da raudha suka sheƙe da ita harda yin tafi,duk abunda su raudha da amrah keyi a zamanmu dasu ban taɓa yin haushin su ba sai a yau ɗin nan da sukayiwa id, kuma bansan dalilin da yasa haka ba.

"Amrah Dan Allah a taimaka masa da abunda zai ja jari"
Raudha ta faɗa cikin izgilanci.

"Gaskiya ya kamata a bashi jari kuma fa tunda kin ga sana'ar faci ba sana'a bace"

Dawowa raudha tayi mota ta ɗauki hand bag ɗinta, nidai inata kallonsu ban cemusu uffan ba. Domin kuwa jikina yayi sanyi likiss kuma bansan dalilin haka ba.

Komawa tayi inda id ke tsaye, tare da buɗe handbag ɗin ta taciro bandir uku na ƴan dubu dubu, ta ɗan juyasu kaɗan a hannun ta.

"Amrah ai kuɗin nan zasu ishi mai faci ya ja jari kho"

"Sosai kuwa raudha, har jarin wankin mota ma zai samu, kinga ya haɗa biyu kenan da faci da wankin mota"

Sake sheƙewa sukayi da dariya ita kuwa raudha ta watsa masa kuɗin da ke hannunta "gashi nan, ka dauka kaje ka....."

Tassss taji saukar mari a fuskar ta, tun kafin ta gama tantance ko waye taji an sake saukar mata da wanda yafi na farko zafi
.
Da kyar ta ɗaga idanunta ta iya furta

"id! sayyid ku kuka mareni, to wallahi baku mari banzaba musamman kai idrak na rantse daidai da wannan rumfar taka sai tayi maka wuyar zama balle makarantar Rooney kuma kajira ka gani" raudha ta ƙarashe maganar tana sakin kuka.

Da sauri na fito daga cikin motar ganin id da Sayyid sun mari raudha lokaci ɗaya, babban abunda yaban mamaki shine ganin sayyid a wurin alhali kuma koda mukazo wurin bayanan.

Cikin matsifa na ƙarasa gabansa da sauri na ɗaga hannu na mareshi nima domin na ramawa raudha marinda yayi mata.

Caraffff naji an riƙe hannunta. Ba kowa bane ya riƙemin hannu face id.
"Wallahi karki sake wannan ƙazamin hannun naki ya taɓa fuskar Sayyid, idan kuma kikayi kuskuren aikata haka wallahi sai dai kici gaba da ganinta yashe a ƙasa domin san na rabata da gangar jikin ki"

Cikin mamaki naji na kasa mayar masa da martanin abunda yayi min, sayyid kuma inda yake shiga ba nan yake fita, amrah da raudha har ma Ni ba wanda ya ƙyaleshi, haka mukaci gaba da ɗauki ba daɗi tsakanin mu dasu, hardai wasu dattijawan da ke sana'a a wurin sukazo suka rabamu dasu ko wa ya kama gabansa, yanzu kwana biyu kenan da mukayi abun nan. Kuma tunda muka samu misunderstanding dasu nidai ban ƙara sakasu a idona ba, kuma tun a wannan lokacin soyayyar id ta kamani ta hanini sukuni, wallahi leeya bana ganin kowa sai shi.

Khulud ta faɗa tana saka yatsa tare da goge hawayen da suka zubo mata taci gaba da cewa "Babban abunda yake bani tsoro taya zan tunkareshi da maganar, kuma ya su raudha da amrah zasu ɗauki maganar. Wallahi akwai kunya gskiya ace kamar ni na rasa wazan faɗa a soyayyar sa sai talaka mai faci a titi"
Khulud ta ƙarasa labarin nata cikin rauni da gazawa.

"Khulud kenan, kin manta da Allahn da yayi ki mai kuɗi shi yayi id talaka mai faci a titi, ko kuma kin manta da Allahn da yayi ki ƴar ministan shari'a shi ya saka soyayyar mai faci a zuciyarki wanda ba kowa ba, ba kuma ɗan kowa ba, sannan kuma.kisani ita soyayya bata shawara balle ta zaɓi mai dukiya ta hadashi da mai dukiya, ko kuma ta zabi talaka ta hadashi da talaka dan uwansa,. soyayya ikon ta take ba shawara take ba"

"Duk nasan da wannan leeya amma wallahi Allah bai ƙaddarceni da gane hakan ba saidai na faɗa soyayya"

"Haka Allah yake al'amuran sa khulud, dama a rayuwa kana naka ne Allah na nasa, kinga ke ko kaɗan a rayuwarki baki taɓa tunanin akwai rana ɗaya da zatazo ki haɗa inuwa da talaka ba, kuma rayuwarki ma ta baya ba abunda kika fi tsanar gani da kuma ji kamar talaka, sai gashi Allah ya nuna miki ƙudurar sa cikin sauƙi ya saka kin faɗa soyayyar talaka, a maimakon ace talakan ne ya faɗa soyayyarki. Amma yanzu duk ba wannan ba, dha nayi tunanin lamarin nan mai sauƙine ashe yafi gaban tunanina, domin kuwa ba babban kuskuren da kika aikata kamar yunkurin marin Sayyid da kikayi a gaban id, kuma ta dalilin sa sayyid yaje wurin, da yazo kuma yaga ana cimasa zarafi har gaban kasuwancinsa sai ya shiga maganar domin kare abokinsa da wulaqanci da kuka yi niyyar yi masa. Kinga tun a farko dama baki fito motar ba, tunda kinga ko da sayyid yazo baiyi tunanin ku uku bane saboda su biyu kadai yagani ke bai ganki ba, sai kuma kika fito da abunda yafi wanda su raudha sukayi, domin su basuyi yunƙurin bugun kowa ba, ke kuma kinyi. Babban abun haushin ma kuma wanda kikeso ɗin shi ya riƙe miki hannu har yana ikirarin zai rabata da gangar jikin ki. Kinga kuwa ba yanda za'a yi kije masa da maganar soyayya yanzu kuma ya amsa miki, amma dai kuma baza'a fasa ba saboda ba'a fitar da rai daga Rahmar Allah"

leeya ta faɗa cikin tausayawa halin da khulud ta tsinci kanta.

"Wallahi nima wannan ne tashin hankali na, domin nasan ba yanda za'a yi id ya karɓi soyayya ta, koda ya karɓa kuma sayyid bazai barshi ya zauna dani ba nasani, duk a cikin mu sayyid yafi tsanata da yawa. Nima kamar yanda yake nuna ya tsaneni haka nake nuna masa harma nawa yafi nashi"

Dafata nayi cikin son kwantar mata da hankali, domin kuwa duk wanda ya tsinci kansa cikin halin da take ciki abun tausayawa ne, duba da yanda hawaye ke faman tartsuwa a idanunta.

"Ki kwantarda hankalinki kinji, in sha Allah zamu sami mafita zan kirawo zohal tazo gidan nan sai muyi Magana baki daya. Kuma abun da nakeso dake kibar wannan zancen a matsayin sirri tsakanin ki da zuciyar ki, karki bari amrah ko raudha suji har ma ita kanta reemah domin hakan zai iya janyo wata matsalar daban, kuma kiyi saurin dakatar da raudha cikin hikima da matakin da takeso ta ɗauka game da Id, domin kuwa idan kika kuskura kika bari ta ɗauki matakin sanya mahaifin ta ya koreshi daga Rooney wallahi kinyi Babban kuskure kuma kin rasashi, domin kuwa a kullum zai dinga dubin harda saka hannun iyayenku a ciki, saboda haka kisan yanda zakiyi ki hanata aikatawa"

"Hakane leeya, zanyi ƙoƙari daga yau zuwa gobe nayi tunanin abunda zan sanar da ita".

"Tau shikenan yanzu ki tashi kiyi alwala muyi sallah, sai mu tafi daining kho".

"Ke dai kije kiyi sallah nikam ina cikin jar mota"

Siriyar dariyar ta tayi domin ta fahimci abunda khulud ke nufi.
Bedroom ɗin ta ta koma sannan tayi alwala tayi sallahr isha kaana ta fito suka haɗu da khulud suka wuce daining.

Sosai mum ta nuna farin cikin ta da wannan sasanci da aka samu tsakanin leeya da khulud, haka suka ci abincin su cikin nishaɗi da wasa da dariya. Su uku ne kacal a gidan domin kuwa dad yaje ƙasar NAYAH tun wancan sati, shi kuma turab ya fita dasu ya-fahad baya nan.


Bayan mun kammala cin abincine muka koma parlour, sosai mukasha fira da mum da khulud, haka mukayi firar mu cikin farin ciki da nishaɗi har sai ƙarfe goma da kwata kafin mum ta sallami kowa, bayan mun koma sashen mu saida muka tattauna batun id, dayake kuma da muka koma sashen namu sai da nakira zohal na sanya speaker tare da bata labarin duk abunda yake faruwa tsakanin khulud da sayyid da kuma id.


Sosai zohal ta tausayawa khulud kuma ta bada shawarwarin da khulud zatayi amfani da su wajen janyo hankalin id, da kuma yanda zata kyautata zamanta da sayyid koda yana wulaƙanta ta karta daina hakan zai janyo id yayi magana koda baya sonta ɗin zai iya yin magana kan Sayyid yadaina abunda yake, daga nan kuma ta samu wata hanyar shiga rayuwarsa. Haka dai muka dinga bata wasu shawarwari da muke gani za'a sami nasara idan akayi amfani dasu.

Miƙewa nayi da nufin in tafi, khulud kuwa ta riƙeni wai na kwana a ɗakinta ta sami abokiyar fira.
nayi nayi tace ba inda zanje sai dai idan ɗakina zamuje mu kwana, haka muka fita muka koma ɗakina a can muka kwana.
Can cikin dare misalin ƙarfe sha biyu na dare, naji ƙarar shigowar saƙo a wayana,

Khulud kam tuni tayi nisa a baccin ta da alama.
miƙewa nayi da kyar domin baccine a idona, dan gefen pillown da nake kai na ɗaga na fito da wayar.


Da sauri ta miƙe zaune ganin number nan ce da ake tura mata saƙo da ita, cikin matukar ƙaguwa ta bude saƙon da aka turomata da shi kamar haka;

Barkan ki dai my dream girl, ina fata kina cikin ƙoshin lafiya kho, wallahi ina kewarki sosai na kasa bacci da nutsuwa ne, ina so injiki koda kaɗan ne, a game da tambayar ki kuma, sanin waye ni a yanzu bayada wani amfani.
Zaifi kyau abi tafiyar a hankali yanda tazo kar ayimata garaje, domin kuwa idan muka saka sauri mun tafka babban kuskure, kuma zaki gane amfanin hakan nan gaba kaɗan. Nidai abunda nake roƙonki don Allah ki taimaka ki dinga bani lokacinki mu dinga magana dake anan a kuma Hakan nan, idan nace a nan ina nufin nan, wato ta hanyar turamin da saƙo, nima kuma na turamiki, banda tsananta bincike dan girman Allah.
bazai yiwu na kiraki ba ko kuma ke kinkirani, ah ah duk wannan zai faru ne idan komai ya tashi bayyana. Wallahi ko contacts ɗin ki kawai na tsurawa ido zuciyata na samun sauƙin raɗaɗi da azabar wutar sonki da ƙaunarki da take daɗa ruruwa a duk wani lungu da saƙo na rayuwata baƙi ɗaya, idan kikayimin wannan kin taimake Ni sosai, kuma kin ceci zuciya ta daga faɗawa hallaka, bye bye I love you more than words can describe wallahi daga zuciya ta komai ke fitowa Leeyana ina sonki da ƙaunarki da muradin ganin kin zama Uwar ƴaƴana, sai da safe ki huta lafiya. Amma kuma dan Allah inaso zuwa gobe da safe ki yanke shawarar da zata zama mafita ga ko wannen mu. yarda Dani, ko akasin haka. Duk wanda yayi miki a ranki zaɓinkine, kuma ra'ayin ki ne, kuma bazan hanaki ba, tunda ke kika ɗauka. amma ki tuna da girman so da masoyi a duk tsawon lokacin da zaki ɗauka kina tunanin mafita".

Nannauyan ajiyar zuciya ta sauke a fili tare da miƙewa ta tashi daga kan gado, wayar ta fara jujjuyawa a hannunta cikin wani yanayi da ita kanta batasan wane yanayi bane domin kuwa zuciyarta ta tsaya chakkk!! ba komai dake aiki a cikinta hakan kuma ya bada gudunmawa sosai wajen dakatarda duk Wani abu da zatayi tunani a cikin ƙwaƙwalwar ta. A daren ranar kasa runtsawa tayi domin kuwa tunanin wannan bawan Allah ya hanata saƙat, ko wane second da minti shi take tunawa da kuma saƙonsa da ta karanta ba adadi. Domin kuwa idan tambayar ta za'a yi ba abunda zata manta a cikin massage ɗin kamar wacce aka ce mata hardace shi zatayi.

Haka tanaji tana gani idon ta ya ƙeƙashe kyam ba alamar bacci sai saƙawa take da kuncewa take a ranta har akayi assalatu.
ɗan hasken screen ɗinta ta kunna sannan tayi amfani da shi ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito.

Kayan baccin da ke jikinta ta sauya zuwa doguwar rigar jalabbiya ta mata, tare ta janyo ƙatoton hijab ɗin ta
Ta zura.

Batayi ƙoƙarin tada khulud ba Domin ta faɗa mata period takeyi a kwanakin Nan.

Sallahyarta ta ɗakko tare da shimfiɗata, Sannan kuma ta juya ta ɗakko Al-qur'ani tare da hisnul-muslim ɗinta ta ayije.

Raka'a biyu ta farayi kafin a tayarda sallar asuba wato raka'atanil-fajhr, bayan ta sallame ne ta ɗakko qur'ani ta fara karantawa a nutse cikin sanyin muryarta.

Ta ɗauki lokaci kadan tana karatun kafin taji an tayarda sallah, miƙewa tayi tabi jam'in Sallar domin tanajin duk abunda ake faɗa har aka kammala, tasbihi ta soma yi, bayan ta yi iya gwargwadon abunda zata iya ta ajiye, kaana ta ɗauko qur'ani shima ta kammala ayoyin da suka rage mata saura ta ƙarasa karatun suratul-ahzab.

Tana kammala karatun ne ta ɗakko hisnul-muslim shima ta ɗan dubbuba kafin ta mayarda hankalin ta wajen azkar.

Saida ta kammala tsaff kaana ta roƙi Allah ya tsare ta ya kuma bata kariya da kuma sauƙin duk abunda zai tunkaro ta Indai na cutarwa ne, daga Nan kuma tayi addu'a tare da neman zaɓin Allah kan lamarin mutumin nan da bata san ko shi waye ba.

Tana gama addu'ar ta tofe ta shafe Sannan ta tashi daga wurin, duk abunda tayi amfani da shi ta mayardashi muhallinsa kamar darduma da kuma ƙur'ani.

Komawa tayi ta zauna tare da zabga uban tagumin tana neman abunda ya kamata tayi, domin harga Allah ita tanajin wannan bawan Allah a ranta, amma ita a ganin ta bazata iya miƙamasa yardar taba tunda ko saninsa ba tayiba kar tayi abunda zai saka tayi dana sani daga baya.

"Leeya, me yake damunkine tun ɗazu kin tsurawa wuri ɗaya idanu"
Sai da ta dan bugi kafaɗarta tana kuma maimaita abunda ta faɗa.
Kamar wacce ta farka daga bacci haka ta kalli khulud dake tsaye akanta tace"ulud yaushe kika tashi?"

"Nima bansaniba amma ba yanzu natashi ba na ɗan jima da tashi amma tun sanda na tashi na ganki a haka har na shiga toilet na fito kuma kina a haka, me ya ke damunki ne"

"Ba komai kawai"

"Haba sis-leeya taya zaki ce ba komai Alhali duk wanda yaga yanayinki yasan akwai abun da ke damunki"

"Uhmm--hmmm, ba komai ke damuna ba"

"Hmmm, a tunani na daidaiton da muka samu zai iya mayarda mu kamar yaya ta ƙanwarta ko kuma ƙawaye ko kuma ƴan uwa, kuma waɗan da zasu dinga faɗawa juna sirrinsu ko kuma wani abu dayake damunsu, sai yanzu na gane sha-sha-shan tunani ne yake bani haka ba gskiya bane, kiyi haƙuri Kinji nina shiga lamarin da ba nawa ba"

Ta faɗa lokacin da take miƙewa zata tafi cikin yanayin ta mai kamada fushi.

Da sauri leeya ta riƙo hannun ta da lafazin mai taushi tace "zauna muyi magana ƴar uwata, kiyi min uzuri Please wallahi abun nan yanada mamaki ne bansaniba ko zaki iya fahimtar abunda zan faɗa miki, amma kiyi hakuri kinji wallahi ba haka bane duk abunda tunanin ki ya baki gaskiya ne munzama ɗaya yanzu, kuma zamu dinga faɗawa juna matsalar mu"

Zama khulud tayi jin kalaman da leeya tayi amfani da su wajen bata haƙuri.

Leeya kuwa ta kwashe labarin komai ta faɗa mata kan batun wannan mutumin da ke turamata sakonni kuma bata sanshi ba, da kuma tsawon lokacin da ya ɗauka yana turomata da sakonni tsawon shekara ɗaya kenan kuma harda ƴan satuttuka kuma duk tsawon wannan lokaci ba rana ta Ubangiji da zai gaza da turamata sako ba, kuma kullum safiya zai zai turamata saƙo fiye da uku, har tsawon shekara ɗaya kuma ko tayi masa reply ko kar tayi masa bai damuba hasali ma bai damu da reply ɗin ba domin yana turawa yake fitarda sim ɗin a wayarsa idan ta kira bata samu kuma ko da tayi reply baya tafiya sabida layin baya aiki. Komai da komai dai ta kwashe ta gayamata harda batun saƙon na jiya da kuma abunda ya ce mata a cikin sakon.

"Hmmm, gaskiya wannan lamarin akwai ban al'ajabi, amma kuma ke baki taɓa tambayar wani bayani daga gareshi ba, kamar a ina ya sami number ki, ko kuma inda ya taɓa ganinki"

"Khulud kin manta a cikin bayanin da nayi miki na faɗa miki bai taɓa ban wata dama da zan iya yimasa tambaya ko kuma nasan wani abu daga gareshi ba. Sai a wannan karon kuma jiya-jiya, a saƙonsa da yayi min ya sanarmin da kar na damu da komai zan sani daga baya, kuma ya ce karna tsananta bincike"

"Yanzu wace shawara kika yanke kan batunsa da yace ki yarda da soyayyar gaskiya yake yimiki"

"Wallahi khulud shine sillar tunanin nan da kika sameni inayi saboda Ni bansan ma mezanyi ba"

"Nidai gskiya a ganina ya kamata ki yarda ki amince domin kuwa a labarin da kika bani tsawon shekara ɗaya kenan yana bibiyar rayuwarki, idan da wani abu yake nema da ya wuce soyayya tsawon wannan lokaci ya kamata ace ya samu. Nidai ina gani kamar soyayyarsa gaskiya ce a gareki dan haka kisan abunda zakiyi idan kinji zuciyar ki ta amince masa"

"Alamar hakan nakeji khulud domin tun bana kula saƙonsa har nazo na fara duddubawa ina karanta wa, har takai ina ɗan shiga wani yanayi mai kamada damuwa idan naga saƙonsa ɗaya takk zuwa biyu a wuni, sai inga kamar wani abu ya sameshi ne ko kuma bayada lafiya domin kuwa abune mawuyaci ya turamin saƙo daya ko biyu a wuni"

"Uhmm--hmmm, sis-leeya albishirin ki" khulud ta faɗa da wani shu'umin murmushi a fuskar ta.

Cikin matukar mamaki leeya ta ƙara ɗago kanta ta kalli khulud tsaff har kallon ya bayyanarda mamakin ta. Haka kawai ta tsinci kanta da faɗin "goro fari"

"Bana son goro, goro yanada ɗaci sosai ki sauya da kishiyarsa"

Kaɗan leeya ta ɗaga kanta sama kamar tana tunani kafin tace

"to zuma"

"Yawwa na karɓi zuma, kinsan me"

"Ah ah" ta faɗa tana ƙara dalleta da idanunta masu kamar kwan fitila saboda girma da faɗi.

"Kin faɗa soyayya, ki yarda Dani kawai wallahi kin faɗa soyayya"


"Taya zakice na faɗa soyayya da Wanda ban taɓa gani ba kuma bansan shi mutum bane ko aljan. Bansan ko cutar dani zaiyi ba, bansan daga ina ya fito ba, bansan, bansan....."

"Ya isa haka sis-leeya wallahi ko ki yarda dani ko karki yarda kin faɗa soyayya, ina da dalilina na faɗar haka, ki duba kiga tsawon wannan lokacin da ya ɗauka yana

29 / 61