BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   39 / 61

114K to 117K   out of 180.4K words

bazan ƙara aikin ba"

Yana shirin miƙewa ya shiga ɗan ƙaramin kitchen ɗin nasu ne suka jiyo sallamar Sayyid yana shigowa gidan.

Har gaban Annah Sayyid ya durkusa ya gaida ita cikin tarbiyya "Annah to ya jikin?"

"Jiki alhmdullillah Sayyid, ya gidan naku"

"Lafiya qlau, ga wannan a ci da hakuri annah"
Sayyid ya faɗa yana ajiye wata babbar leda daya cikota da abubuwa.

"Har da dawainiya haka sayyid, tho an gode Allah bada lada"

Miƙewa sayyid yayi yaje inda idrak ke tsaye sukayi musabaha, daga nan ya janyeshi suka fita gidan.

"Jiya da safe nazo gida ban tarar dakai ba, sai Annah na tarar ba Lafiya, dana tambayi inda kaje tace baka nan, na gayamata lafiya kake tun jiya ina kiran number din ka bana samu tace min ai ka siyarda wayanka, na ce mata meya sami wayan taka tace min wai magani ka siyamata da kuɗin"

Sayyid ya faɗa lokacin da suke zama cikin motar Sayyid ɗin.

"Eh hakane wallahi mutumina, jiya Annah ta tashi ba lafiya, kuma ba kudi a hannuna shine na saka wayar kasuwa na siya mata magani"

"Amma wallahi idrak bakay min adalci ba, kuma ka bani mamaki, aka daiyiwa wasu mutanen da ba'a sani ba balle kai id, wallahi banyi tunanin haka daga gareka ba. Wai ace muna tare koda yaushe har Annah zatayi zazzaɓi bansaniba sai kaje ka siyarda wayanka ne za'a sami kudin magani"

Id na shirin yin magana, Sayyid ya tare shi rai a matukar 'bace "wallahi nidai na gayamaka idan ka kuma min haka ranka in yayi dubu sai ya ɓaci"

"Tuba nake ur highness" Id ya faɗa yana langwabar ta kai gefe tare da haɗe hannayensa biyu.

Kwalin waya sabuwa filll Sayyid ya miƙe masa "ga wayarda ka siyar, dan Allah ajima naji ance ka siyarda ita".

Id ya rasa abunda zaiyi kawai sai ya rungume Sayyid cikin tsananin farin ciki "Nagode sosai Sayyid, Allah ya ƙara buɗi na alƙairi, ya sa ku gama lafiya da duniya"

"Ameen abokina, kadaina.....! babu godiya tsakanin mu, and kuma dan Allah anjima da yamma ka shirya, mai martaba na nemanka domin na bashi labarin ka da mahaifiyar ka"

"Okay ba damuwa Allah ya kaimu anjima ɗin"

"Ameen"

"Yawwa Sayyid yau khulud tazo gidan mu"
"Gidan ku kuma, yin me?"
Sayyid ya faɗa yana dan gyara zaman sa dai-dai.
"Wallahi kuwa ashe tasan Annah sosai, kuma iyayenta ma sun sanmu"

Nan id ya kwashe labarin ta kafff da suka sani da kuma yanda mahaifiyarta ke taimakon su.

"Aikuwa dai wallahi da badan mahaifiyar ta ba banga abunda zaka nema a wajen ta ba, kenan ita ɗabi'ar ta ce tun a gidansu kho, wulaƙanta talaka, shiyasa tayiwa Annah sharri har aka koreta"

"Eh wallahi mutumna, ai wannan yarinyar da badan ta tuba ba da tayi asara wallahi"

"Kai manta da ita kawai Allah ne ya nuna mata abunta tunda talakan da take gani ba komai ba shine kuma ya zamarmata komai yanzu"

"Hmmm, Allah dai yayi jagora"

Ameen Sayyid ya faɗa daga nan sukaci gaba da labarunsu.



K.WAASIB MANSION.

Tunda wannan abu ya shiga tsakanin leeya da turab ba wanda ya kuma kula wani a tsakanin su, leeya ta zage sai soyayyar ta take sha da messengern ta, kullum tana maƙale da waya har mum ma ta fahimta yanzu, sai dai bata san soyayya take a wayar ba tunanin ta kawai yanzu leeya ta shaku da wayar ne.

"Mum yau inaso naje gidansu zohal, kuma inaso meenal ta rakani"

"Tau ba damuwa ki shirya kuje, lefe zakuje gani kho"
"Eh mum ta kirani ta sanardani ankawo lefen jiya da rana, amma kuma bashi kaɗai bane zanje mu tsara yanda bikin zai kasance"

"Okay nagane, tau idan kin shirya ki sanardani wata ƙila tafiyarku zatayi dai-dai da turab sai ya ajiye ku, domin kaduna zai koma sai an fara programme ɗin shima zai dawo"

"Uhmm--hmmm tau shikenan mum, amma fa mu munshirya meenal ma Ni kaɗai take jira idan nayi wanka nayi sallah sai mu wuce"

"Okay tau sae kun dawo"
"Yawwa mum mun gode"
"Ki gaida ummansu Zohal"
"Zataji mum"

Daga haka leeya ta mike ta shiga part dinsu ta sanarwa da meenal yanda sukayi da mum, ita kuma ta fara shirin tafiyar.

Sai da suka shirya tsaff kaana sukayi sallama da sauran ƴan uwan nasu suka tafi.

Suna fitowa harabar gidan suka haɗu da turab shima ya fito da trollynsa janye kana gani kasan tafiya zai yi.
Jingine yake yana jira a fito masa da motarda zai fita da ita su kuma su meenal suka karaso wajen.

Ta gabansa suka bi zasu wuce meenal ta gaidashi "ya-Turab ina yini"

Cikin sakin fuska wanda bata taɓa gani a tattare dashi ba ya amsa mata "Lafiya lau meenal fita za'a yi"
"Eh zamuje gidansu Zohal ne mu duba lefen da aka kawo"

Sai a lokacin leeya tace masa "ina yini" ko kadan kuma bata d'aga kai ta kalleshi ba hannun ta na kan wayanta tana dannawa duk da ba komai takeyi da ita ba.

"Lafiya lau" ya amsa cikin halin ko in Kula.

Gaba sukayi suka barshi a wajen bayan sunyi sallama dashi yayi tafiyarsa shima.

"Amma gaskiya ya-Turab ya changer kamar ba shiba, ko dai magana akayi masa"

Ɗan murmushi leeya tayi......, meenal kuma na ci gaba da tuƙa mota tace "wa zai yi masa Magana tunda haka tsarin rayuwarsa take, wata kila dai yana cikin mood na farin ciki ne shiyasa kika ga haka, amma Nima nayi mamaki sosai gaskiya"

"Ai da haka yake tun farko da an huta, wallahi banyi tunanin haka daga gareshi ba, sai naji yau kin birgeni da baki nuna masa tsoronsa da kikeyi a fili ba"

"Meenal kenan, ya-Turab yana samun damata da yawa shiyasa yake min komai dayaga dama, amma yanzu gaba ɗaya banajin akwai sauran wani abu mai suna tsoro da ya rage a cikin raina indai na ya-Turab ne, kuma bana tunanin akwai Ranar da wannan zai dawo"

"Lallai kam gaskiya wannan da kika dauka yayi, bawai ina zugaki kiyimasa rashin kunya bane amma a dinga jan girma kawai" meenal ta faɗa lokacin da suke karasowa kofar gidan su zohal.

Mai gadi ya buɗe musu gate suka shigo da motar har cikin gidan, mai gadin ya san leeya sosai kuma yanajin sunanta a bakin mutanen gidan.

Fitowa sukayi sukazo har wurin da yake tsaye suka gaidashi, ya shaidar musu zohal tana nan bata fita ba.

Suna shiga gidan kuma suka tarar da mutane sosai, gidan ya cika da mutane masu duba lefe, ummah mahaifiyar su zohal tayi maraba da leeya da kuma meenal, an karrama su a gidan sakamakon zamansu familyn fahad kuma ga leeya kawar amarya, sai da aka buɗe musu kayan lefen gaba ɗaya suka gani kafin leeya taje inda Aunty zainab yayar Zohal babba tace mata"Aunty zainab ina zohal tunda mukazo bamu ganta ba"

"Lahhh leeya ba'a gayamiki tana dakinta ba, ai na zata kinje wallahi, faruk nace ya gayamiki fa kiyi hakuri karkuga kamar mun barku ne wallahi tana d'akinta ita da sultanah"

"Bakomai Aunty bara naje dakin nata, su sultanah sun zo kenan"

"Eh yau sukazo sai bayan biki zaku koma, maman numrah tazo sai faɗa take wai baku rubuta invitations da wuri ba har gashi saura kwana biyar, sauran families sai ganin laifin mutane suke wai ba'a turamusu invitations ba, da akayi mata Magana akan ta rubuta sai tace sai ranar da kikazo saboda bakida lafiya har asibiti aka kaiki kwana biyu"

"Eh wallahi Aunty banajin daɗi kwana biyu zazzaɓi nake fama dashi, amma naji sauƙi. Aunty ai da kun rubuta tunda gaku nan ba sai ta jirani ba"

"Eh haka mutane suka ce amma furrrrr taƙi yarda wai sai kinzo"

"Tana dakinta kikace kho" cewar leeya.

"Eh fah, tana dakinta ita da sultanah ne a ciki inaga"

"Muje meenal" leeya ta faɗa tana yiwa meenal alama da su tafi.

ZOHAL a dakinta, sai leka window take ko yaya Imran zai fita ta samu suyi satar hanya ta bayan gidan su ta tafi gidan su leeyana, domin ya imran babban yayansu namiji ya hanata fita tun shigowar satin nan indai ba fitar ta gida bace wacce za'a fita da motar gida.

"Yawwa sulteey kinga yafito Gashi chan Allah kasa tafiyar ce" ta faɗa tana daga hannunta alamar roko.

Sultanah dake kwance kan bed tace "zohal ki kirata a waya don Allah, Wallahi Nima ba wani fitar nan nakeso ba kin matsa ne kawai amma ga hanyar sauqi kice bazaki bi ba"

"Ina hanyar sauƙin?"

Sultanah na shirin magana sai ga leeya ta faɗo dakin baƙinta dauke da sallama.

Da gudu Zohal ta dago tsalle daga kan gado ta rungume leeya

"besty ashe kina tafe, wallahi gani nan ina shirin zuwa gidan ku yaya Imran kawai nake jira ya fita nabi ta hanyar baya naje gidan ku"

"Satar fita kuma zohal amarya da akace tsausayine da ita"

"Ke wane tsautsayi, wallahi ba wasa ba da bakizo ba binki nakeda niyyar yi yanzun nan, mutane duk sun azomin baki wai ban rubuta invitations ba har yanzu, kullum sai anyi magana"

"Tau ai gani nazo" leeya ta faɗa tana kokarin zama.

"Ina yini" cewar meenal tana kallon Zohal.

"Lahhh meenal, tare kuke kenan har naji kunya, wallahi Allah Bankula dakeba yi hakuri kinji yasu mum"

"Duk suna Lafiya, ya haƙuri"

"Alhmdullillah, mungode Allah"

"Ya shirye-shirye kuma"

"Uhmm--hmmm yana nan kunayi meenal"

Dan murmushi meenal tayi sannan ta gaida Sultanah itama.
Sultanah da Zohal mahaifinsu ɗaya, kuma kusan girman shekarunsu ma daya, amma ba'a garin suleja suke ba.
Tunda mahaifin su Zohal ya rasu mahaifiyar sultana ta koma gaban iyayenta a Katsina, sai idan biki ya taso ko kuma aure sannan suke zuwa, ko kuma idan sallah tayi sai suzo.

"Lafiya qlau, meenal naji zohal ta kiraki kho? Ykk"

"Lafiya lau alhmdullillah"

"Masha Allah, leeyana kema sannunki, muna shan labarin ko a bakin Zohal"

"Yawwa sulteey sannu, Nima ina shan labarin ki sosai ashe kin iso"

"Eh na iso wallahi tun jiya ma, sai da nazo nake samun labarin wai baku shirya invitations ba har yanzu, amma Yanzu tunda gaki nan kinzo sai muyi sauri a tsara a turawa wanda zai yi printing"

Zama sukayi gaba ɗayansu suka fara tsara yanda events din zasu kasance.
Leeya tace "rubutawa za'a yi ko kuma dai ayi typing a waya a turawa mai printing din"

"Gaskiya yafi, gwanda ayi typing ayi bayani dallah-dallah yanda shi wanda zaiyi printing invitation din zai gane"

"Okay programme nawa za'a yi?"
"Uku" sultanah ta faɗa tana kallon zohal koda an changer tsarin domin ita a yanda ta sani a gidan nasu ba'a yin wata bidi'ah sosai.

"Uku kadai za'a yi dame-dame kenan?"
"Kamu, sai kuma dinner, sannan sai waleemah da akeyi ranar daurin aure da Yamma" cewar sultanah dan ita zohal bata cewa komai. Meenal ma haka suna kallonsu ne kawai da kuma sauraro.


"Okay ina za'a saka venue din wurin day one, kamu kenan kho"

Sultanah tace "Eh kamu ne za'a day one, kuma a gidan nan za'a yi ki saka yanda za'a gane kawai kiyi summarize Kar zancen ya tsawaita"

"Na saka day one:kamu;
Venue: resident of Alh Khalil Adam girah.
Time: 4pm"
Haka dai leeya tayi masu bayani dallah-dallah yanda tayi komai, har akazo kan dinner da waleemah shima tayi kamar yanda tayi day one ɗin.

"Shikenan bara a tura masa tayi wallahi" cewar sultanah da meenal bayan sun gama karanta wa a wayar zohal da aka rubuta.

Miƙa mata wayar akayi itama ta karanta kafin daga bisani aka turawa wanda zaiyi printing invitation din.

Bayan haka kuma sunsha labari sosai inda zohal take gayamata batun fitarda zasuyi gobe su raba katin gayyata idan an kammala aikin zuwa gobe.

Sai Yamma sosai leeya da meenal sukayi shirin tafiya, meenal ma ita ta kuma tukasu da mota har gida domin ita leeya bata iya tuki ba, kuma hakan bai taɓa damunta ba balle tayi tunanin koya.





A bangaren Turab kam tun da ya fita gidan ya dau hanyar kaduna, ya ɗauki tsawon awanni yana tafiya kafin ya iso.
Wayar sa ya laluba lokacin da yayi parking gaban wani babban supermarket.

Number ɗin zafaran yayi dialing ringing ɗaya ya dauka.
"Turab ya akayi ka karaso ne?"
"Yanzu na shigo, na tsaya supermarket ne na siye abu gani nan karasowa"
"Okay, a estate ɗin fahad muke ba gidansu ba"

"Aikuwa gwara da ka sanardani gidansu nayi niyyar zan tafi wallahi, amma dai ko da haka zanje na gaida mommy munjima bamu ga juna ba, idan na gama sada zumunta zaku ganni"

"Okay no wander, sai ka shigo"

Daga haka turab ya kashe wayar sannan ya shiga supermarket din yayi abunda zaiyi kaana ya fito.

Gidan su fahad ya fara zuwa bayan sun gaisa da mutanen gidan ne ya nufi estate ɗin da su zafaran da fahad suke.

Zaune ya tarar dasu a balcony din da ke wurin, kamar shi ake jira kuwa yana zuwa suka tambeshi, bayan sun gabatar masa da abinci yaci ya koshi ya kalli fahad yace "up going groom, yau ba wani deal ne sai shan iska kawai"

Fahad ya dan yi murmushi mai sauti sannan yace "mutumina mukuwa mukeda deal babba wallahi"

"Masha Allah, ina saurarenku ya akayi"

"Batun lewa ne" fahad ya faɗa yana ɗan satar kallon zafaran da hankalinsa yafi karkata da wayansa dake ajiye a gabansa.

"Lewa kuma" turab ya faɗa da mamaki.

"Eh, wallahi batun lewa ya dan sakamu attention shiyasa ka ganmu a haka munyi jugum-jugum"

Har a lokacin zafaran bai kallesu ba kuma bai ce uffan ba, har turab ma ya lura da haka.

"Ya akayi, me ya faru ne kuma"
"An samu labarin Yan bindigan da suka aika aikan basu kashe mata ba, kuma tun a farko munsan da haka"

"Eh dama basu kashe mata ba ayanda muma muka sami labarin, sai dai abun tambaya anan shine ina suka kai matan"

"Basu kaisu ko'ina ba hasali ma duk matan da suka kwaso wasunsu sun tsira"

"Taya???"

"Accident 'yan harin suka samu, kuma da sukayi accident din wasu sunyi kokarin ceton rayukansu, wasu kuma sun mutu, kuma labarin accident ya isarwa jami'an tsaro, har Allah yasa aka cafko wasu daga maharan, sannan kuma aka taimakawa wadanda sukaji rauni daga cikin matanda aka kama, sai kuma wasu da suka rasa rayukansu"

"Allah sarki, yanzu to mecece standard Magana kan lewa"

"Babu" fahad ya faɗa yana Tafa hannayensa biyu alamar babu ɗin.

"Ina kuka sami wannan labarin, kunyi wata tafiyar ne bada ni ba?"

"Ina zamuje bada kai ba seniorman?, kawai dai labarin bincikoshi akayi"

"Waya binciko?"

"Har ma sai ka tambaya man turab" cewar Fahad yana nuna zafaran alamar shi yayi binciken.

"Allah sarki, Ni wallahi zafaran tausayi ma kake bani, gashi Allah ya jarabceka da ƙaunar wacce bakada tabbaci kan tana raye ko ta mutu, ina rokon Allah ya takaita maka wahala idan tana raye ya bayyana maka ita, idan kuma ta mutu Allah ya musanya ta da wata matar daban ya Allah"
Turab ya faɗa a zuciyarsa, a zahiri kuma yace"zafaran a wannan zaka kare ai, Ni ko yaushe idan ka zauna da waya hannunka, kana nan kana search din labaran yan bindiga, Allah dai ya bayyana lewa mu huta"

"Ameen suka faɗa baki ɗaya.











K. WAASIB MANSION.

"Mum ba sai driver ya kaimu ba dan Allah, wallahi zan iya tukin da kaina kinsani"

"Justice yace a daina barinku kuna fita ba tare da driver ba"

"Saboda me mum" khulud ta faɗa kamar zatayi kuka "mum tun dazu fa nake rokonki ki barni muje da yanzu fa na dawo, kunga ma wallahi ilyass sai kirana yake wata ƙila fita zaiyi daga shagon nasa" ta fada tana dagowa mum wayanta dake ta faman ruri.


"Okay shikenan, keda wa zaku fita?"

"Da badariyyah zamu fita, ita kadaice bai auna size dinta ba lokacin da yazo tana bacci"

"Fito da kayan"

Mikewa khulud tayi ta koma bedroom ɗin mum ta fito da kaya niƙi-niƙi a trolly.
Kayane na sakawa wadanda ba dunkakku ba, duk anko ne da kuma sauran kayan fitar biki da papu ya saka aka fita da yaran gaba daya kowa ya zabi abunda yakeso.

Shine ake shirin kai dinki, khulud kuma ta dage kan ita zata fita kai kayan saboda yanzu ba sosai ake bari tana fita gidan ba tunda ba skul an yi hutu.

Dalilinta na son fita kuwa tanaso ta je unguwar tsohon bariki ne ta haɗu da id tun ranar bai nemeta ba gashi kuma batada contact dinsa balle ta nema shi, shine ta yanke shawarar fita yanzu zuwa wurin mai dinki.

Da saninta ta saka badariyyah tayi bacci lokacin da mai dinkin yazo har gida zai aunasu, shiyasa ko yanzu ma mum batayi gardamar fitar ba saboda kar a tauye wa badar haƙƙin ta.....................✍🏻



















EP.40











___________________"badar kama mu fita da trollyn nan"
Miƙewa badar tayi suka d'aga trollyn, ita ta riƙa hannu ɗaya khulud ma ta riƙa ɗaya har suka isa mota.

"Nidai bazan iya driving ba wallahi ke zakiyi tunda kika cewa mum zaki iya"

"Driving kam ai bazai haɗa faɗa ba muje" khUlud ta faɗa tana nufar mota.
Centre ɗin mai ɗinki suka fara zuwa suka kaimasa kayan daga nan kuma suka wuce layin ƴan haya.








Bangaren su id.

"Gaskiya Mutanen nan suna da karamci, kamar ba gidan sarauta ba"

"Annah nifa inaga jinin su sayyid basa wulaƙanta mutane tun haduwar mu da shi na fahimci haka, Ashe abun daga gida ya gani"

Annah zatayi magana sukaji sallamar khulud.

"Annah ina yini" khulud ta faɗa lokacin da ta karaso inda suke zaune id kuma yana yimata tausa.

"Hajiya ƙarama yanzu ake tafe"
Cikin dan jin kunyar abunda Annah tace khulud ta ɗan soke kai ƙasa ba tare da tace komai ba.

"Barkanku da wuni"Badar ta faɗa tana satar kallon akulkin gidan da khulud ke mutuwar son ɗan cikinsa.

"Yawwa Barkanmu dai, ya hanya?"
"Alhmdullillah sai godia"

"Idrak kaje ka dauko tabarma ka shimfida musu mana ah bar mutum tsaye haka kawai"

Sai a lokacin id ya dago kansa sannan ya furta "sannunku" can a kasan zuciyarsa, domin ko badariyyah dake gefensa bataji abunda yace ba, amma ita khulud ta ji maganar. kamar shi kaɗai take jira yayi maganar kuwa ta karɓa masa.

Gaisuwa sukayi sama-sama sannan ya wuce tilon dakin ginin siminti da ke gidan ya dauko musu tabarma ya shimfiɗa masu duk suna tsaye.

Idrak badai ɗa'a da ladabi da tausayi ba, domin kuwa yana taimakawa mahaifiyarsa sosai ta fannoni da dama musamman ma bangaren aikin gida, shara, girki, wanke-wanke, wani lokacin har tufafi yake wanke mata domin ita kaɗai ce ta ragemasa a duniyar nan, kuma shikadai ne ɗa daya tilo a wajen ta.

Idan

39 / 61