Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
bayan sallar isha idan kowa ya kammala aikin da zaiyi sai yazo a haɗu anan"
Haka kuwa akayi bayan sallahr isha duk mutanen gidan nasu suka hadu a Babban parlourn da ke gidan wanda shine parlourn mahaifinsu marigayi Hahmeed abbansu mum.
Bayan gaisuwar mutumci da sukayi mum ta fara koro musu bayani akan leeyana da kuma qanwarta Aleena, mum ta kwashe labarin su kaff da kuma irin wahalar da sukayi da yanda ake nunawa leeyana kyama da kuma irin rayuwarda suka gudanar akan haka.
Ba wanda bai zubarwa da labarin nasu hawaye ba, hatta aunty Rafa'at da take qanwar Papu sai da labarin su leeyana ya sanyaya jikinta.
Hannu umma ta ware musu cikin muryar kuka tace "kuzo gareni jikokina, nice mahaifiyar faheema. Na yafe mata har lahira, Allah ya jiqanta ya sanyaya makwancinta"
Da gudu suka faɗa jikin umma suka rungumeta suna sakin wani marayen kuka.
Tun a cikin daren aka fara nunasu ga sauran families dinda ke kusa, har mum na sanar dasu cewa za'a yiwa leeya aure, domin ita Aleena da aurenta aka, itama dai keeyaba da auren nata sai dai za'a qara daurawane saboda ba kowa yasan da wancan ba, kuma nan da wata ɗaya mai zuwa ne auren.
A gidan kuwa kowa so yake ace wurinsa su leeyana zasu kwana, cikin ɗan qanqanin lokaci yaran suka shiga ran mutane, domin wata irin kulawa suke samu daga dangin nasu, soyayya da qauna ake nuna musu ta kowane bangare.
Hajiya ummasalima babbar aminiyar Ammi ce Lokacin suna 'yan mata, yarda ce mai qarfi a tsakanin su. Ko a lokacin da labarin guduwar Ammi da saurayinta suka sami ummasalima sai da tayi zazzaɓi na kwana da kwanaki, kullum bata da aiki sai kuka da tunani.
Sai da abun ya dan lafa ne ta sami sauqi, tun daga lokacin bata qara jin wani labari daga Ammi ba.
Sai kawai rana ɗaya aka je mata da Leeya da Aleena sune 'ya'yan fanaya.
Hmmm zo kaga Gata, ummasalima ji take kamar ta hadiyesu saboda tsananin qaunar da take yiwa mahaifiyarsu.
Da taji labarin auren da za'a yimusu tace "hmmm ina da rayuwa ina numfashi zan bar yaran nan a garin nan a gyarasu, hajiya fanaya ina so ki bani passport dinki da na yaran nan in sha Allah zuwa ranar lahadi zamu wuce Thailand ayi musu gyaran jiki mai kyau"
Mum kam ta rasa da wane baki zatayiwa ummasalima Godiya baki har kunne ta isa gida ta gayawa umma, sannan ta kira gida ta sanarwa da mazajen yaran ta kuma sanarwa da papu da dad ƙarami.
Ranar Lahadi kuwa suka dauki hanya sai kasar Thailand, mum fanaya da kuma ummasalima da leeyana da Aleena.
Satinsu biyu a Thailand, suka dawo tare da uban siyayyar da ummasalima ta yimusu.
Maiduguri suka dawo kwanan su daya suka tattara suka koma suleja.
Ranar kamar turab yayi hauka, shidai zafaran a ranar da suka dawo a ranar aka mayar masa da matarsa.
A wannan karon ma haka akayi domin turab ya kasa idanun sa ko zai yi tozali da ita amma inahhhh.....,,,,,.
Duk ya shiga damuwar akan haka, itama leeyana tayi kewarsa sosai. Wani lokacin ma tanaso ta kirashi amma kuma sai ta fasa. tuno da gargadin mum.
Yau kam ta kuduri aniyar kiransa tunda saura kwana biyar kacal a daura auren.
Da dare Misalin ƙarfe goma ta kirashi, yana kwance bacci na fizgarsa a hankali yaji qarar kiran waya.
Bai duba lambarba ya d'aga kiran. Lokacin da muryarta ta doki dodon kunnensa sai da ya zabura.
"Mafarki nake ko gske leeyana kece, Allah sarki sama da wata daya bana ganin ki, kuma banajin wannan Muryar. Sai yau kika tuna dani"
"Lahhh, haka ma zakace saboda na kiraka kho"
"Awww gori kike min saboda kin kirani, to ki kashe wayarki bana buqatar kiran na ki"
'kitttt ta kashe wayar tana jin haushin kanta, on ready tasan mutumin nan d'an wulaqancine dama ta sani da bata kirashi ba wallahi.
Tana cikin zancen zuci ne taji qarar ringing din waya, dago wayar tayi tana dubawa,.ganin baƙuwar number ya sakata ɗaukar kiran.
"Kinga yanzu Ni na kira ki ba wani gori da zaki min"
'kayataccen murmushi tayi kamar yana kusa da ita tace "ni dama can ba gori na maka ba kawai naga kanaso ka dauramin laifi ne"
"Ah ah na isa in dauramiki laifi, rufamin asiri kinji 'yar nan" ya fad'a cikin sigar wasa.
Dariya sukayi gaba ɗaya cikin nishadi, daga nan fira ta 'barke a tsakanin su har ta manta da gargadin mum. Da kalamansa ya bugo cikinta ta gayamasa inda take zaune tsawon lokaci.
Wanda mum ta gargadeta akan kada ta sanar masa, shafff ta manta sai bayan ta gayamasa ne ta tuna da haka.
"Yanzu dama tsawon lokacin nan kina gidan Aunty Rafa'at, ance rashin sani yafi dare duhu amma wallahi ko yau nabi ta unguwar na shiga gari......! Shiru yayi bai idarda fadin abunda yakeson fad'a ba Sakamakon jin kiraye kirayen sallahr asuba ta aka farayi.
"Wai kana nufin kiran sallahr asuba nake ji?"
"Abun mamaki" turab ya faɗa yana dariya.
Kuka ta fashe dashi ala dole ya hanata yin bacci.
da kyar ya samu tayi shiru suka ci gaba da fira kafin lokacin zuwansa masallaci yayi.
Idan ba farin sani kayiwa leeyana ba, ba lallai ka iya gane ta ba sakamakon gyaran da ta samu daga kwararrun turawa.
Jikinta yayi sumul babu alamar 'kurji ko kuma tabo, tayi mugun fari tassss, fatarta sai shining take da wani 'kyalli mai daukar ido. Fuskar ta sai sheqi da walwali take tayi wani smooth gwanin kyau. Idanunta sun qara fito da ainihin asalin rikitacciyar colour dinsu mai matuqar daukar hankalin wanda yayi tozali dasu.
Magungunan mata kam ba'a magana dan mum da ummasalima zage wa sukayi suka samarsu da komai na wannan bangare.
Qamshi kuwa duk idan ta wuce sai ta barshi domin gyara suka samu sosai daga dangin nasu a Maiduguri, sosai aka tsumasu da humrah kala daban daban. Ita kanta dadin qamshinta take ji balle wanda yazo kusa da ita.
Kwance akan makeken bed dinda ke amsa sunan nata a gidan aunty Rafa'at take, waye ce manne a kunnuwanta sai murmushi take ta rungume pillow a jikinta da alama tanajin dadin firar da take a waya.
"Wallahi nidai na gaji da jiran rushewar katangar nan da
mum ta saka mana tsakani"
Narkarda muryar ta tayi cikin shagwa'ba tace "Allah nima na gaji da jiran ganin rushewar katangar nan ina son ganinka sosai"
"Really......?"
Yace yana murmushi mai sauti.
Turo baki tayi kamar yana kusa da ita tace "not really, partially"
Ta faɗa tana murgud'a baki.
Sosai yake dariya har tana iya jin yanda yake dariyar "haba uwar gidan turab, ya da wannan maganar haka?"
"nice uwar gida?"
"Eh mana"
"Awww kana shirin yin amarya kenan.....!?"
"Ehhh, amma ba yanzu ba" yayi maganar cikin sigar wasa.
"Allah nidai banaso ka daina" ta yi maganar a shagwa'be kamar zata fashe masa da kuka.
"Tau naji kina ina haka......?"
"Ina bedroom....."
"Me kikeyi a bedroom....?"
"Kwanciya kawai..!"
"To ki sakko qasa"
"Bazan sakko ba..! Akwai rana da zafi nikuma banason rana yanzu"
"Bakyason rana? Ko mijinki zaki gani baza ki iya sakkowa ba"
Miƙewa tayi da sauri cikin madaukakin farin ciki tace "da gaske dan Allah T-heart..!?
"To kizo ki gani mana"
Da sauri jiki na rawa ta ajiye wayar ta buɗe wardrobe ta fito da wata doguwar rigar abaya deep blue da mayafinta ta sanya.
Light make up ta d'anyi abunka da baka saba ba, sosai kyawunta ya fito kamar 'yar sarkin aljanu saboda tsananin kyau.
Plate shoe black ta saka ta fita kamar tayi fiffike ta isa inda yake.
Zaune yake cikin motarsa a compound din gidan ya tsurawa kofar parlourn idanunu.
Kusan dauke numfashinsa yayi lokacin da ya hango ta tana zuwa.
Sai godiya da tazbihi yake yiwa Allah da zai mallakamasa wannan halitta mai daraja.
Sai da ta kusa isowa inda motarsa take ya fito, fuskokin su dauke da yalwataccen murmushi.
Leeyana kam ji tayi kamar ta tafi da gudu ta fad'a jikinsa, idanunsu sar'ke cikin na juna tayi hanyar parloun ba'ki kafin tayi masa alama da hannu ya biyota.
Murmushi yayi yana kad'a key din motar sa ya bi bayanta.
Cikin nutsuwa suka zauna, idanunsa akanta.
Fridge ta nufa ta dauko masa drink ta miqa masa tana gaidashi.
Kar'ba yayi ya sha sannan ya amsa mata gaisuwar da tayi masa.
Lumshe idanunsa yayi yana fadin "Alhmdullillah, Allah ina godiya da ka bani dama da iko na ci gaba da rayuwa, yau nine a gaban leeyana a matsayin wanda zai aureta"
Ganin yanayinsa ya chanja yana shirin kuka ya saka ta ɗora yatsarta akan lips dinsa"shhhhhhh"
A hankali ya fara buɗe idanunsa ya dora cikin nata bugun zuciyoyinsu na tsananta.
Cikin wata irin murya da bata ta'ba ji turab yayi amfani da ita ba saboda sanyinta yace "idanunki launin shudi mai haske, sai farin da ya zagayesu kamar sabuwar tatacciyar madarar shanu, sunada wani sirri a cikinsu wanda Ni kadai na iya fahimtar haka, ubangiji ya yi halittar sa dole na yaba"
Murmushi mai sanyi tayi masa wanda sai da dimples din ta suka lo'ba sosai tace "adadin mata nawa ka gayawa haka....!?"
"Tabbb aikuwa sai dai idan an sami calculator, domin bazasu lissafu ba haka kawai"
'dan basarwa tayi tace "okay yayi kyau, kayi qoqari ai" ta faɗa tana qoqarin mikewa.
Da sauri ya riqo hannuta ya zaunar da ita kan cinyoyinsa yana dariya yace" I'm sorry my gurl, ke kadai na taba gayawa haka, kuma ke kadai ce na fara so a rayuwata. Da ke kadai na tsara rayuwata"
Ya fad'a yana riqe kunnuwansa da hannayensa biyu.
Murmushi mai sauti tayi, ta d'an jaa kumatunsa tace "baka laifi"
"Da gaske kho my queen..? Nima fa bakya laifi a wurina wallahi. Ko da bana da lafiya da naji anaso a kamaki da laifi bazan iya yaqi da su bane da sai kinga jarumta"
Dariya Sosai tayi tace "waye jarumi..?" Tayi tambayar cikin tsokana.
Murmushi yayi shima yana shafa kwantaccen gashin kansa zuwa sajensa yace "Ni mana"
"Kai waye to..?"
Hannunsa ya daga yana d'ago kanta suna fuskantar juna yace "Ni angonki, masoyinki...!, mai qaunarki, mai burin zama dake har abada, mai qaunar ganin farin ciki da nishadinki, wanda zai hana hawayenki zuba muddin yana da rai da lafiya, kece a cikin zuciyata, rayuwa ta....! Ke kadai, ke dai leeyana.....!"
Murmushi tayi hadi ta danna masa light kiss a kumatu"thanks for loving me T-heart"
"Me too precious...!, ya maganar sadakin ki ne?"
"Ka ga Ni ka bada abunda Allah ya hure maka kawai, da badan ba'a yafe sadaki ba da sai ince na yafe maka, ni burina kawai musami zaman lafiya da yarda da juna da kuma fahimtar juna, amma kuma Annabi ya fada cewa "koda tsalle mace tace kayi sau daya shine matsayin sadakin ta, to har a wurin Allah sadakin kar'ba'b'be, dan haka mafi qanqantar sadaki, mafi albarkacin aure"
"Wallahi shiyasa nake qara jinki a raina precious, amma kuma akwai kyautatawa a tsamin mu kho....?
Dan haka ga makullin mota nan na baki halak malak, motar kuma tana waje tun kafin isowa ta nan na saka aka kawota.
Wannan kuma zoben diamond ne, sannan kuma akwai brief case a mota 20millions ne zan bada matsayin sadaki, Allah ya sa banyi rowa ba"
Zatayi magana ya dora yatsarsa akan lips din ta yace "no argument......! Just obey
Kinwuce ki ce komai a wannan da na yimiki precious,,,,,,kece burina, idan ban miki ba wazan yiwa....? dan Allah karki ce komai, just accept it"
"I accepted, Nagode sosai yalla'bai..! Allah ya saka maka da alkairi, Ubangiji ya sanyawa aurenmu albarka ya bamu zuri'a dayyiba, Allah yasa ka gama duniya da iyayen mu lafiya"
"Ameeen ya rabbi precious me, then gobe zanzo na amshi passport dinki domin ba'a qasarnan zamuyi first night ba"
Ya fad'a cikin tsokana.
Remote dinda ke hannunta ta d'an doka masa a gefen fuska ya goce yana dariya.
"To yanzu me kaki shirya mana na bikin da zamuyi"
"Kamar me fa....!?" Ta fad'a idanunta akansa.
"Kamar su dinner, da lunch da sauransu"
"My T nifa gskiya bana son bidi'ah"
"Tabbb.... Chief military health service zai yi aure ba tare da Nigeria ta sani ba, impossible. Bama Nigeria ba hatta qasashen ketare zamuyi inviting, kinga da farko za'a daura aure anan suleja, sannan muyi waleemah a abuja.
Zamuyi lunch a Greece, muyi dinner a Jordan, Arab woman's a Egypt, sai kuma muyi love show a London sannan mu wuce Spain muyi honeymoon muci amarcin mu"
Baki ta turo gaba cikin shagwaɓɓiyar murya tace"Allah nidai banaso"
"To naji bakyaso, mu fasa da love show din da za'a yi a London......amma gskiya sauran sai anyisu"
Zatayi magana ya ɗora hannusa a bakinta yace "shhhhh mu komai namu cikin tsari da ilimi da wayewa zamuyi,
Bazamu yi abu any how ba, zamuyi komai a nutse cikin kwanciyar hankali batare da munyi bidi'ah ko mun sa'bawa Allah ba in Sha Allah kinji...!
Jiki a sanyaye ta d'aga masa kai.
"That my precious gurl, I really love you" ya faɗa yana manna mata Peck a goshi.
"Love you too my T-heart"
"Yawwa kuma na bawa mum 5millions a hada miki kayan fitar biki, sauran kayan lefe kuma idan munje honeymoon za'a had'a.
Godiya take masa sosai da hidimar da yake yi da ita, sun jima a tare suna fira cikin kwanciyar hankali da nutsuwa da kuma tattauna yanda bikin zai kasance.
Sun ɗauki tsawon lokaci kaana suka rabu da tsananin kewar juna.
Yana fita daga gidan ya fara neman layin mutanen da zasu yimasa komai a biranen da zasuyi programme sai da ya tabbatar angama komai sannan ya sanarwa dasu fahad da zafaran.
Sosai suke murna da jin haka, lokaci yayi da zasu nunawa abokinsu qauna suma.
Passport din yan gidansu ya kar'ba da kuma sauran families, dana zafaran da matarsa....... sannan fahad shima dana Matarsa.
A can biranen kuma angama shirya musu komai hatta kayanda zasu saka, date kawai akejira.
Shirye-shiryen biki kuma kullum anata yi, domin wasu manyan iyayen su leeyana a Maiduguri sun fara zuwa kamar su ummasalima da sauran mutane.
Sosai k. Waasib families ke shirye-shiryen biki, sanin auren ne na fari a gidan, kuma shine babba, mafi soyuwa a wurin iyayensa. Dangi kuwa na nesa dana kusa duk suna halarta sai hidindimu ake.
Mum kuwa da Papu sun saki bakin aljihu sai fitarda kudi ake yanda kasan gidan ake 'kerasu.
Ummasalima kuma daga Niger republic ta d'akko wacce zatayiwa amarya 'kunshi, ai kuwa aka d'and'asamata jan lallen solatif wanda yafito maroon colour sharrr hasken fatarta ya qara fita kamar balarabiya.
Gashinta kuwa yasha gyara sai wani qamshi da kyalli yake abunka da mai gashi. Aka yimata tsoraye guda biyu ta suka kusa ta'ba 'kugunta.
Sai wani farin haske gashin ke fitarwa. Idan ka ga leeyana a wannan lokacin zakayi tunanin labaran asali ne.
Wani bangaren kuma ta wuce balarabiya, don idan ganinka na fari ne da ita batada wani bambanci da aljana saboda tsantsar kyau da tayi, duk inda ta juya sai wal-wal take tana kyalli da d'aukar ido.
Sosai daurin Auren TURAB KHATTAB WAASIB da matarsa LEEYANAH HAMRAZ AWAIS ya sami halarta manya mutane daga kasashe daban-daban na sassan duniya, kama daga presidents, commissioners, governor's, manyan lauyoyin kasa da manyan likitoci, da kuma manyan ƴan kasuwa 'yan nigeria da kuma wanda ba Nigeria ba. Manyan limamai da mukama manyan ma'aikatan tsaro na qasa.
Sosai sojojin qasar Mexico sukayiwa turab kara musamman ma mutanen da ya yiwa aiki. Key holder suka yimasa mai zanen bindiga da kuma tambarin qasarsu, sai kuma can gefe suka saka hoton turab dana leeyana tare da sunayensu.
Masu aikin jarida da gidan tv kam kamar su akayiwa taron domin duk motsin da mutum zaiyi zai ga ma'aikatan jarida ko na tv a bayansa suna qoqarin jin ta bakinsa.
K'arfe biyu da rabi dai-dai, dubannan miliyoyin jama'a suka shaida daurin Auren DR.TURAB KHATTAB WAASIB da kuma sahibar Amaryarsa LEEYANA HAMRAZ AWAIS, akan sadakin zunzurutun kudi har millions ashirin da kuma dallelen makulin mota qirar Benz, da zoben diamond....................✍🏼
48.
_____________da sauri ya rumtse idanunsa ya cije gefe daya na lips dinsa yana dafe saitin zuciyar sa.
Wasu hawayene suka gangaro daga cikin idanunsa, lumsassun idanunsa ya fara bud'e wa yana jin abun kamar a mafarki.
Hausawa sukace idan farin ciki yayi yawa yana saka hawaye, musamman lokacin da zuciya mai cike da buri ta sadu da muradinta........!
irin wannan yanayi ne turab ya shiga lokacin da yaji an shafa fatihar daurin aurensa da leeyana.
Sosai farin cikinsa ya kasa boyuwa har sai da hawaye ya gangaromasa.
Mikewa yayi yana hamdala. Wata tawagace ta tunkaro shi tare da ma'aikatan gidajen rediyo da talabijin dai-dai lokacin da ya durkusa yayi sujudul-shukhur.
Sosai mutane suka shiga mamaki da sha'awar abinda yayi, da wani irin sauri fahad da zafaran suka rungume shi.
Shima zafaran hawayen yake tunda aka d'aura auren leeyana da turab kuma ya rasa dalilin yin hawayen gwanin tausayi.
A can gida kuwa leeyana ce zaune a babban dakin da yafi ko wane daki girma a gidan papu.
Zaune take gaban mirror tana saka sarqa.
Wata farar basudaniyar matace tsaye akanta tana gyara mata gashinta, domin ba'a samu akayimata kitso ba saboda yanayin tsayin gashinta ba yanda za'a yi masa kitso.
tsayinsa ta kuma santsinsa yayi yawa.
Daga Sudan aka dauko wacce zata rinka yimata gyaran gashin da kuma kwalliya har a kammala bikin.
Yanzu ma tana tsaye ne ta gama shiryata, ba wata kwalliya da aka mata saboda yanzu zasu wuce Abuja inda za'ayi waleemah.
Meenal, Badar, Aleena, Aneesa, Airah da twins da kuma bestin ta zohal duk suna zaune a dakin wasunsu na cin abinci, wasu kuma suna shiryawa. Wasu kam pictures sukeyi abunsu.
Leeyana na zaune an gama gyaramata gashin har dauri ma an yimata. Bakin less ne mai fulawas golden da red.
Ɗinkin half boo-boo ne a jikinta wanda ya kwanta a jikinta Sosai ya fito da tsadaddiyar kalar fatarta.
Tsayi fadar kyawunda leeyana tayi bata lokaci ne, wani jan net na amare basudaniyar matar ta yafa mata sai zuba kyalli yake.
Hill shoe ta saka suma kalar ja ne, sosai takalman suka dauki qafarta da kyakkyawan red henna din da ke qafarta.
a hankali take takawa domin bata iya yin tafiya dasu ba, idan mutum ya gani kuwa zai yi tunanin kamar salon tafiyar ne haka.
Qamshinta kuwa sai da ya cika sashen gaba ɗaya tun kafin ta tashi gaban mirror.
Qarar kiran waya ya shigo daidai lokacin da basudaniyar take daura mata tsadadden agogon hannu na mata.
Cikin sanyin ta ta d'aga kiran ganin turab ne ya saka ta d'aga da sauri.
"Kice alhmdullillah kinji matata, yau kinzama matata da gaske kuma duniya ta shaida haka, ina sonki leeyana dan Allah karki barni kinji...!" Ya fad'a muryarsa na cracking alamar kuka yakeso yayi.
"Alhmdullillah,,,,,,,,alhmdullillah,,,,,,, Alhmdullillah" ta fad'a sau