Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
mutanen a wannan lokacin tana kasa ba wanda ya daga kansa ya kalleta a cikinsu balle ta gane su waye.
Rigar tanada dogon hannu mai fadi wanda ya rufe har yatsun hannayensu, kuma a gaba da bayan rugar anyi wani tambarin kan bakar mage da jini.
Hakika mutanen nan sunada ban tsoro sosai duba da yanayin da suke ciki, duk suna durkushe ne sun sunkuyar da kansu gaban wata matar daban. Sun dauki tsawon mintuna biyar a haka.
Matar ta fara daga kanta, daga nan kuma suka fara dagowa suma daya bayan daya.
nidai ina zaune ina kallon ikon Allah, domin kuwa bana iya ta'buka komai ina jina zaune ne kawai ba tare da na san abunda ke faruwa ba.
Gabana ne yayi mugun faduwa ganin fuskar da na taba sani shekaru talatin da biyar baya, duk da ba ganin ta nake ba amma hakan bai hana na gane ta ba domin tana zuwar min a duk lokacin da mummunan mafarki zai riskeni a cikin baccina.
Ina so na furta sunan ko iya fatar bakina ne amma na kasa, ji nake kamar an dauremin harshe.
Mikewa tayi ta fara tafiya har sai da takai gaban matar da nake gani a kujera ita kadai, kuma nake kyautata zaton itace babba a cikinsu.
Naji tsoro sosai lokacin da naji matar da ke zaune ta budi baki tayi magana, cikin tsawa da daga murya tace da karfi.
"Fairozha!, ya zama dole ki ja kunnenta sosai ki gargadeta akan abunda take nufin yi, domin idan kika kuskura kika barta ta idar da nufinta rayuwarki da ta sauran ƴan kungiya na cikin haɗari, ya zama dole ta manta da maganar bada labarinki, labarin maharaz da hamraz da kuma waasibudden, da sauran mutanen da jininsu ya gushe akan dodon tsafi Black cat, idan kuwa kikayi sake ta bayyana babu abunda ya shafeni bayan hukuncin da zaki dauka daga wurin black cat, kuma zan miki nawa sannan yan kungiya suyi miki nasu tunda kika yi sake asirinsu ya fita. gata na kawo miki ita kija kunnenta naga tana shirin warga za mana shiri"
Cikin ladabi da biyayya irin tasu ta matsafa ta kara sunkui da kanta kasa tace "kiyi hakuri the Queen, ki yarda DAYAMMAH tanada kafiya sosai, na rasa me zan yi domin naci galaba akanta, kinsani mai girma black cat ya hana mu tsaface jininta da tuni ba wannan maganar ake ba amma zamu gargadeta a karo na karshe"
"Ya rage naki, nidai kinji abunda na fada miki".
"Naji the Queen, kuma nabi nayi biyayya"
Banajin komai da suke fadi, bawai dan suna nesa dani ba. Kuma Nima ban san dalilin da yasa banajin komai daga maganar da suke ba, gani nake bakunan su na motsi kawai amma bana jin ko d'iif.
Kamar yanda sautin aradu ke shiga a kunnuwan mutane haka naji murya mai kara da amsa amo tana min magana a lokacin da na daina ganin komai a dakin saboda tsananin duhu ko tafin hannuna bana iya gani.
"Dayammah ya zama dole ki janya kudurinki nason to na mana asiri, idan har kinaso kici gaba da rayuwa to dole ki manta da fairozha, dole ki manta dani dayammah, Ni fairozha naci dubu sai ceto, ja dani ba karamin aiki ba ne a wajenku, na gargadeki sau ba adadi amma kin kasa fita rayuwata, wallahi da badan Black cat bai bani damar shan jininki ba da tuni ba wannan maganar akeba. Amma duk da haka bazan barki ki ki tafi a banza ba" Muryar ta faɗa tare da daukewa d'iif.
Muni mugun zugi taji a cikin tafin hannayenta da kafarta har sai da ta kurma uban ihu.
"Dayammah lafiya?" Taji Muryar hajiya fanaya na tambayar ta.
Da karfi ta buɗe idanunta ta kallesu duk tayi sharkafff da gumi.
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, meke faruwa dani yanzu fa naga fai........" Bata karasa faɗar abunda zata faɗa ba ta manta da komai.
"Ke kawai muke sauraro dayammah"
"Wallahi hajiya banada nutsuwar da zan iya bada labarin komai yanzu, amma idan za'a sami Kur'ani a kusa inada bukatarsa don Allah ko zan sami nutsuwar zuciya"
"Leeyana je dauko mata Kur'ani" hajiya fanaya ta fada tana kallon leeya.
Ita kuma dayammah ta mike da nufin tayi alwala, da mugun sauri ta zauna tana kallon kafafunta da tafukan hannunta.
Sosai hankalin ta ya tashi ganin yanda aka raunana ta, sake yunkurin mikewa tayi amma ta kasa gaba ɗaya, ganin haka ya saka suka tambaye ta ko lafiya.
"Lafiya ƙalau" ta fada da karfin hali.
Miƙewa id yayi ya tako gabanta shima tare da rike kafafuwanta yana duddubawa,
"Annah meke faruwa?"
"Ciwo naji idrak, kagani kamar yankan wuka kho?"
"Ban ga komai ba Annah, me kikeji a wurin" ya faɗa yana shafa tafin kafafuwan nata.
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, idrak ka daina tabawa baka gani yanda kake taba ciwo" ta fada kamar zatayi kuka saboda tsananin azabar da takeji.
Hakan kuma yayi daidai da ƙarasor leeya wurin da Kur'ani a hannunta.
Karbar Kur'anin dayammah tayi daga hannun leeyana, duk da bata da tabbacin cewa zata iya rika Kur'anin da hannunta yanda takeji.
Cikin ikon Allah kuwa tana rika Kur'anin da hannunta taji ta daina jin komai daga azabar da hannun ke yimata.
Sake gyara zaman ta tayi ta bude Kur'anin da ke hannunta ta fara karantawa dallah dallah, duk shiru sukayi ba wanda ya kuma cewa komai har sai da ta kammala karanta surar da ta bude.
Anan taji komai ya dawo mata yanda takeso, amma tambayar ta anan shine ya akayi taga wasu abubuwa kamada mafarki, ko kuma almara.
Cikin mintuna kalilan komai nata ya changer kamar ba ita ba, to me hakan yake nufi, shin fairozha ta gani ko kuma mafarki take, idan fairozha ce ya akayi su mum basu ganta ba? Idan da gaske komai ya faru meyasa idrak baiga yankan wuka da fairozha ta yimata ba, idan kuma mafarki ne yaushe tayi baccin???
"Ya Allah ka fitardani cikin wannan sarkakiya"
Ta fada a zuciyarta.
Tun kafin wani ya sakeyin magana dayammah ta ci gaba da faɗin.
"Tun ranar da na baro asalin mahaifata nakeda buri da addu'ar Allah ya hadani daku" ta faɗa tana kallon hajiya fanaya ido cikin ido.
"Allah yaga zuciyata kuma yaga abunda nake nufi a cikinta, yasaka ina sauka garin nan daku na fara cin karo, cikin isarsa da ikonsa ya kawo qaddara a tsakanin mu ya saka kuka kadeni da mota, har na dawo ina aiki a gidan ku, duk da a farko bansan cewa ku nake nema ba sai daga baya na gane hakan bayan naji Asalin sunan alhaji.
Anan na gane kune mutanen da nazo nema cikin garin nan, domin in samu bayyana wa Alhaji wani bakon al'amari, kuma shi kansa alhajin yanzu idan aka tambaye shi yana da matsananciyar bukatar son ya sauke nauyin dake kansa"
"Dayammah wallahi ban fahimce ki ba, me kike so ki sanardani game da maganar nan da kike fad'a Yanzu"
Dan murmushi tayi kafin tace"ba damuwa zaki gane komai in sha Allah, ki bari idan Alhaji ya dawo kawai zaku fahimci komai"
"Tau shikenan, Allah ya mai da shi lafiya, kuma Allah yasa muji alqairi"
Ameen suka fada gaba daya, dayammah kuma ta dora da fadin;
"Nasan baku san wanene mahaifinku ba kho, kuma nasan babban abunda ke cikin ranku a yanzu bai wuce ake kunsan asalin wanene mahaifinku ba, to karku damu domin mahaifinku mutumin kirki ne, kuma bai baro danginsa da mahaifarsa don ra'ayin kansa ba, wallahi sakashi akayi bayin kansa bane.
Asalin garin da mahaifinku yake shine calaba, kuma can yake zaune da iyayensa da sauran danginsa.
Ni matar dan uwansa ce wato maharaz domin na gayamuku mahaifinku ba shi kad'ai aka haifa ba su tagwaye ne, sune na fari, sannan sai kanwarsu dake biye musu a haihuwa sunanta fairozha, a gidansu na tashi nake rayuwa tun kafin auren mu da maharaz. Mahaifiyarsu wato neela kanwace a wurin tawa mahaifiyar, kuma akwai zumunta mai karfi tsakanin mu dasu.
Ganin haka ne ya saka mahaifiyar su maharaz wato neela ta nemi mahaifiyata ta mayar Dani gidan nasu naci gaba da karatuna tare da yar wajenta fairozha.
Mahaifiyata bata nuna rashin amincewarta ba, kuma ta nuna mata wannan ba komai bane.
Ba jimawa nayi shiri na koma gidansu maharaz naci gaba da zama gidan da bayada bambanci da gidanmu, saboda komai zan yi a gidan mu, zan iya yinsa a gidansu.
Mahaifinsu hilwah mutum ne mai karamcin da alkunya Dattijo ne mai kamala, gashi kuma mutum ne wanda Allah ya azurta da dumbin dukiya sakamakon sana'o'in da yake dasu a gida Nigeria da kuma kasashen ketare, bai gaza da karatun mu ba kuma yana kwatanta adalci a tsakanin mu domin bazan fitarda kaina a cikin 'ya'yan gidan ba saboda komai yake musu nima yana yimin. wani lokacin ma sai ayi min abu su ba'a yimusu.
A lokacin fairozha bazata wuce shekaru goma sha hudu zuwa sha biyar ba, babban abun ban haushi game da rayuwar fairozha shine rashin godiyar Allah da kuma tsagwaron hasada da kyashi da kuma bakin cikin ganin wani ya ci gaba, kullum idan aka kwatanta yiwa wani alqairi a gabanta ko waye bazata bari ba, fairozha bata alqairi, kuma bata yarda ayi alkairin a gabanta.
hamraz da maharaz kuma sunada kusan shekaru 17 zuwa sama. A lokacin ne suka kammala karatun su har ana shirya yanda zasu ci gaba da wani karatu.
Batare da hilwah ya nemi shawarar d'aya daga cikinsu ba ya yanke shawarar turasu kasar DENMARK suci gaba da karatunsu a can.
Fairozha bataji dadin wannan lamari ba ko kadan, duk da suma basu so aka rabasu da qasarsu ta gado ba. Sunso a barsu cikin danginsu suci gaba da karatunsu amma hilwah ya ki amincewa da batun su.
Cikin 'yan kwanaki aka shirya komai na batun tafiyar su, hakika fairozha bataji dadin wannan lamarin ba, kuma ba yanda batayi ba akan ta hana tafiyar amma Allah yaso faruwar haka , har ita kanta ta dage kan da ita za'a yi tafiyar amma abun yaci tura tunda bata kammala karatunta na secondary ba.
An shirya musu komai na batun tafiyar su washe gari zasu wuce denmark din.
Ita kuma fairozha ta rasa abunda ke yimata dadi Saboda tana ganin taci baya idan ta bari wannan lamarin ya faru.
Me zatayi domin domin ta hana tafiyarsu??
Maganar da take faman nanatawa kenan tun daga fitowar alfijir din yau har yanzu da muke kusan karfe uku na rana.
Mikewa tayi cikin mutuwar jiki da kasala domin ita abun ya zamo mata kamar jinya.
Sai da ta lura sosai da hilwah baya nan dakinsa, sannan ta shiga cikin d'akin da sand'a cikin ikon Allah ba wanda ya ganta har ta shiga ta rufo kofar.
Bedroom ɗin hilwah ta wuce kai tsaye tana shiga bedroom din ta nufi inda yake ajiye takardunsa masu muhimmanci, 'yar karamar kit ce ta akwati kuma an sakamata key, wani irin mugun haushi ya turnuketa ganin an sakawa kit din makulli.
Juyawa tayi da nufin ta fita, wata zuciya ta ce mata "meyasa zaki fita bayan kinsan inda yake ajiye makullan sa"
Da sauri ta juya bayanta,,,,,,, idon ta kuwa suka sauka kan wata 'yar karamar jakar da hilwah ke saka makullan sa.
Bata san da wane makulli zatayi amfani ba domin bude kit din da aka saka takardun da take nema, duba da haka ne ya saka ta je da makullan gaba daya, kuma da d'ad'd'aya ta dinga gwada makullan har dai ta samu wani daga cikin makullan ya bude kit din akwatin da takardun komai suke ciki a gidan .
Murmushin mugunta tayi lokacin da ta bude kit din idanunta suka sauka akan takardun da take nema.
Ba tare da shakka ko tunanin komai ba ta d'ebi takardun gaba ɗaya waɗan da tasan zata bukata ta 'boye su sosai a jikinta sannan ta mayarda komai inda ta dauko kamar ba'a ta'ba ba.
Fita dakin tayi cikin tsananin farin cikin samun nasara da tayi sannan ta nufi bayan d'akunan gidan gaba ɗaya.
Ajiye takardun tayi gefe daya, sannan ta kuma dawowa cikin gida ta shiga kitchen ta dauko ashana ta fita.
Bata zarce ko'ina ba sai gaban takardun nan, tana zuwa ba wata-wata ta kestawa takardun wuta, nan da nan kuma wutar ta cinye takardun gaba d'aya kamar basu taba wanzuwa ba.
Tsinsiya ta d'akko ta tsaftace wurin har da zuba ruwa ta wanke tass kamar ba'a yi komai a wurin ba, sannan ta koma cikin gida hankalinta kwance, zuciyar ta fal da farin ciki.
Bayan dawowar hilwa gidan tare da maharaz da hamraz ya kaisu sunyi bankwana da yan uwa da abokan arziki sannan suka dawo gida, tun lokacin da hilwah ya shiga dakinsa ya tabbatar da akwai abunda ba daidai ba a dakin.
Kiran maharaz da hamraz yayi domin suzo su fara hada kayayyakin da zasu bukata a tafiyarsu.
Sai da suka nutsu sosai kafin suka hada kayan ba wata rigima, kuma suka kwantarda hankalinsu duk abunda zasu bukata idan sunje suka sakashi a cikin trollyn su.
Washe gari tun da sassafe suka tashi suka dora daga inda suka tsaya domin tafiyar tasu karfe tara da minti sha biyar na safe zata kasance.
'yar karamar jakar da hilwah ke saka makullan sa ya d'akko tare da fito da wani karamin mabudi da yafi kowanne karanta.
Direct inda ya ajiye kit ya nufa tare da zare mata padlock bayan ya saka mabudi.
Ido ya zaro cikin mamaki ya kalli hamraz da maharaz yace "ku kuka ɗauki takardun da na saka anan"
Suma ɗin kallon mamaki suka bishi dashi domin maharaz ma bai gane nufinsa ba hamraz ne kawai ya sami damar amsa masa.
Inda ya samu damar gayamasa basu suka dauka ba, sosai abun ya bashi mamaki domin shi dai a saninsa nan ya sakasu, kuma ya tabbatar nan ya sakasu tunda shi ya saka da hannunsa harma ya rufe da kansa.
"Ikon Allah" ya fada tare da talla'be ha'ba.
"Hilwah ka kira neela ka tambaye ko sun gani" maharaz ya fada yana dakatawa da aikin saka kaya trolly da yake.
Mikewa hilwa yayi ya fita dakin ba jimawa suka dawo tare da ni da neela da kuma fairozha.
Sai da muka shigo dakin hilwah sannan aka sanar mana da dalilin kiran.
"Bayan fitar mu gidan nan akwai wanda ya shigo dakin nan?" Hilwah ya tambaya.
Jin kowa yayi shiru yasa na kalli gefen da fairozha ke zaune domin yau gaba daya ita naga ta shigo ta bangaren nan hatta neela ma ban ganta ba.
"Hilwah fairozha ta shigo dakin nan yau gskiya" na fada ba tare da tunanin komai ba.
"Me kika dauka a nan fairozha?" Hilwa ya tambayeta yana kafeta da idanu.
Murya na rawa cikin tsantsar rashin gaskiya tace "hilwah nazo ne naga ko kana ciki na kara jaddada maka magana ta akan nima zan bi maharaz da hamraz denmark"
"Amma kuma mahaifiyar ki ta riga ta gayamiki ba inda zakije kho, Ni dama kin kammala secondary ne da zan iya hadawa har ke ma ku tafi Ni wannan ba wata matsala bace, Amma kiyi hakuri zuwa wata shekara kinji"
"Shikenan hilwah ba damuwa zamu hakura har wata shekaran domin ba ni kadai zan hakura ba"
"Hummm fairozha kenan, to idan dayammah kike dubi ai ita bata da sha'awar yin nisa da gida"
"Ba dayammah kadai ba, hatta su Hamraz da maharaz din da aka fifitasu akanmu sai sun hakura domin na 'kona takardun su gaba daya dana gani cikin wanchan akwati"
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, me kikayi haka fairozha, Ashe baki da hankali? Yanzu toshewar kwakwalwarki da hankalinki har sun kai ki aikata irin haka?" Neela ta fada cikin tsananin bacin rai mara misali.
Kafin hilwah da sauran mutanen da ke dakin suyi wani yunkuri tuni neela ta dira kan fairozha, dukan ta kawai take ta ko'ina batare da tunanin abunda hakan zai janyo nan gaba ba.
Da kyar suka 'ban'bare neela daga jikin fairozha bayan tayi likiss har bata iya yin kuka.
Sosai hilwah ya rufe neela da fad'a inda ya nuna mata illar yin haka, kuma ya shaida wa su maharaz da hamraz su kwantar da hankalinsu tafiya ba fashi domin takardun da ta kona basu bane original duk copies ne.
Sunyi farin ciki sosai da jin haka, fairozha kuma kamar ta hadiye zuciya ta mutu, Babban abunda ya hanata tasha maganin kwarin jiki shine son daukar fansa"...............
"Fansa kuma? Wurin wa zata dauki fansa?????"
Aleena ta tambayi dayammah lokacin da ta kai daidai nan a bayanin ta.
"Wurin mahaifiyar ta neela?"
"Taya zata dauki fansa......? saboda ta daketa akan laifin da tasan ta aikata, kuma ma ita ta faɗa da kanta"
"Ki saurara kiji yanda komai yazo karshe"
"Okay ina sauraren ki" cewar Aleena, wato (Rukhshanah)
"Bayan sati biyu da faruwar wannan komai ya dawo daidai domin su Hamraz da maharaz sun jima da tafiya karatunsu can denmark, shekara hudu zasuyi kafin su dawo, kuma har wannan shekara hudun su kare ba zasu zo gida ba sai dai aje musu.
Komai ya ci gaba da tafiya kamar yanda ake dha, fairozha ma duk ta manta da komai kamar ba'a yi ba.
Amma wani babban al'amari dake dauremin kai dangane da ita, d'aki daya muke kwana, kuma a gado d'aya, a duk lokacin da zan farka cikin dare bana ganinta a dakin. Tun abun baya damuna har yazo ya fara damuna.
Idan nayi yunkurin sanar da wani sai naji harshena yayi nauyi sai kawai nabar abun a zuciyata.
A wata rana cikin ranakun da bazan manta ba, Ko da muka tashi da safiya sai muka tashi da jimami a zukatan mu, neela ce ta tashi da zazzabi mai zafi, tunda sassafe kuma hilwah ya dauketa suka tafi asibiti, wuni daya a asibitin suka dawo gida.
Taji sauki sosai kamar ba itace aka fita da ita gidan ba ko motsin kirki bata iya yi yanda akeso.
Hatta aikin gida neela ta ki bari nayi Ni kadai, sai da ta tayani a wunin ranar, dama can ita fairozha bata cika yin aikin gida ba.
Sai da muka kammala komai da komai har abinci dare da komai mukaci sannan ta koma sashen ta nima na shigo namu sashen.
Bada fairozha mukaci abincin dare ba, dama can bata wani damu da abincin ba sai idan hilwah da neela sun takuramata.
Nayi mamaki kwarai da gaske dana dawo dakinmu bansameta ba, "to ina fairozha taje yanzu?" Na tambayi kaina ba tare da na ajiye mai bani amsa ba.
Saida da nayi addu'a sosai kafin nan na kwanta bacci barawo bansan lokacin da ya saceni ba.
Can cikin baccina kamar a mafarki naji muryar hilwah na kiran sunana, a firgice na tashi zaune ina murza idanuna ko da mafarki nake, sunan fairozha naji ya sake kira cikin tashin hankali na bud'e kofar na fita ban ma kula da fairozha na gidan ko