BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   60 / 61

177K to 180K   out of 180.4K words

da sanin haihuwar batazo ba, jiya har taraba mum ta tafi taga 'yarta Aleena kuma ta kaimata kayayyakin da aka had'a mata na shirin haihuwa, sosai qabilar su zafaran suka tarbi mum kamar ba kirista ba.

sun saki jiki da ita Sosai har suka ta'ba fira kafin mum tayi musu sallama ta biyo flight ta dawo.





*
Mintuna kadan turab ya qara kira ya sanarmusu da isowarsu, bada jimawa ba mum ta haɗa tawaga harda su papu akaje tarbarsu.

Mamakin kowa ya bayyana lokacin da sukaga yanda leeyana ta chanja, haqiqa ko da ka santa dole zakayi gardama akan ba ita bace.

Duba da yanda ta sauya gaba daya, tayi wani irin sihirtaccen kyau.

Babban abunda ya qara bawa mutane mamaki Ganin yanda cikin leeya yake, wasunsu ma zasu iya rantsuwa basu ta'ba ganin cikin irin nata ba.
Gashi nan dai abun sai wanda yagani.

Bayan kwanaki hud'u da zuwan su aka shirya gagarumin bikin sunan zohal da jaririjarta.

Sosai farin ciki ya cika ahalin musamman mummy-neesah yanda mutanensu sukayi mata karah.

takanas mutanen india sukazo bikin, kuma suka sakawa yarinya suna.

A ranar da ake bikin Halloween na cika shekaru biyu da rasuwar nahaifiyar mummy-neesah, a kuma ranar ne aka haifi jaririyar zohal.

Saboda haka yasaka mummy-neesah ta roqi fahad akan yayiwa mahaifiyarta wato kakarsa takwara da 'yarsa da aka haifa.

Cike da tsantsar farin ciki ya amince domin shima shawarar hakan yake a ransa sai kuma Allah ya saka mummy-neesah ta fahimci tunaninsa.

Ranar suna kuwa yarinya taci sunan babba a cikin familyn su fahad aka sakawa jaririyar suna (GULNAR) sannan fahad ya baiwa ahalin gidan Khalil girah damar zaɓen sunan da zasu sakawa yarinyar a matsayin nickname.

"Ifrah.....!"

Shine sunan da fahad ya maimaita a bakinsa lokacin da zohal ta gaya masa sunan da suka za'ba.

"Masha Allah, Allah ya rayamana GULNAR mai sunan manya a india, a Nigeria kuma ifrah. Ina matuqar qaunarki ifrah. Ina godiya ga Allah da ya bani mahaifiyarki. Allah ya qara bani ikon kiyaye haqqoqin ku"

"Ameen" zohal ta faɗa cike da jin dadin kalamansa.








*
A bangaren su Aleena kuma tun daren jiya take fama da naquda, sosai zafaran ya damu ganin yanda suka hanamasa kai ta asibiti. Duk wannan yana cikin qa'idodinsu, kuma hakan shine al'adar su kuma suna girmama al'ada matuq, ba qaramin abu bane yake sakasu su karya dokar al'ada.

"Samanta, ya kamata ki saka baki a maganar nan, tunda nasan inne najin maganar ki. Kar 'yar mutane ta mutu a hannun mu"
Zafaran ya fad'a yana durkushe gaban wata tsohuwa mata.


Murmushi tayi kafin tace masa "kar ka damu, bazata mutu ba. Kaga ai anata kula da ita. Haihuwar ce batazo ba kawai amma bana fatar mutuwa agareta gaskiya, domin tanayin naqudar yanda akeso tanada dauriya sosai"

"Haba samanta, taya mutum yana cikin matsanancin hali irin wannan zakice na kwantarda hankalina ina matsayin mijinta, wallahi idan ta mutu sai iyayenta sunyi Shari'a damu, kinga mahaifiyarta ɗaya ma da kyar ta barta gidan nan, kuma har da jaddada muku tayi komai ya sami yarinyarta sai ta yi Shari'a daku koda komai da ta mallaka zai qare"

(Ummasalima yake nufi)


Tsohuwar da yake kira da samanta na shirin magana sukaji kukan jarirai na fitowa daga cikin dakin da Aleena take.

Tare suka tashi aguje suka nufi dakin, sai dai iya samanta ta sami shiga, zafaran na gab da zai shiga aka rufo qofar da sauri.

Wani mugun duka ya kaiwa qofar cike da jin haushi. Sanin tunda suka rufe bazasu bude masa ba.
Hakan ya saka ya koma gefe yana jiran fitowar su.

Bayan tsawon mintuna arba'in sai gashi an bude masa kofar, aikuwa kamar za'a qara rufemasa ya shiga dakin da azama.

Bakinsa ne ya kasa rufuwa ganin matarsa gatanan kwance an tsaftace ta har turare aka kunna a dakin da kuma yara biyu kwance cikin kyakkyawar shiga ta kayan jarirai masu kyau da mum fanaya ta sako a cikin kayayyakin da ta kawo musu.

Bai isa inda yaran suke ba har sai da ya gama yiwa Allah kirari a zuciyarsa kafin yakai hannu ya d'akko daya daga cikin yaran.

"Kagani kho, matarka tagwaye ta haifa mace da namiji kyawawa dasu" wata mata ta fad'a tana murmushi.

Shima murmushin yake kafin yakai yaron saitin bakinsa yayita koro masa Addu'oin da manzo Sallallahu alaihi Wasallama ya umurta ayiwa jarirai idan aka haihu.

Bayan ya gama ya d'akko mace ya yayi mata itama.

sosai yarinyar ta shiga ransa lokacin da yayimata 'kuriiiiii.....!!!!! Yana kallon ta ganin yanda take cikakkiyar kama da ammi mahaifiyar Aleena.


Batare da 'bata lokaci ba ya fara kiran mutane yana sanar musu, su mum kam baki har kunne baramma ummasalima da ta fi ji da Aleena.

Aikuwa kwana uku da haihuwa suka dawo taraba sukaci gaba da kula da ita, saura kwana ɗaya jal ayi biki mutane suka fara yin tururuwa daga wurare daban-daban.

Leeyana ma da kyar ta iya zuwa dha har turab yace suyi zamansu tunda yanzu tafiyar ma da kyar take saboda girman cikinta.

Amma sai mum tace abarta tazo kawai bikin yar uwarta guda..! Yakamata ace ta halarta.

Hakanan ta tafi cike da dauriya da kuma tarin gajiya, har zohal da ifrah sun zo, ifrah kam an fara wayo kamanninta da mahaifinta na fitowa sosai duk wanda ya ganta zai yi tunanin indiyawa ne iyayenta, har ta fi su fannah da mayah zama cikakkiyar ƴar india tun daga gashinta idan mutum ya kalla.

Zafaran ya sami abokansa sukayi shawara kafin yaje ya sanarwa mum shawarar da ya yanke game da sunan da za'a sakawa yara, tayi na'am sosai ta qara martaba qimar zafaran a zuciyarta.

Ranar suna sai ji sukayi ana sanarwa, a bangaren iyayen zafaran sun sakawa yara suna, haka ma bangaren zafaran da dangin uwar yara sun saka sunan su suma. Kuma duk sunyiwa yaran yanka.

danginsu zafaran sukayi yankansu yanda yake a al'adar su, namijin yaci suna (DUBEM) macen kuma (CHIDINMA).

a bangaren zafaran kuma ya sakawa yaransa suna da kansa macen sunansa (FAHEEMA) namijin kuma sunansa (HAMRAZ)

wasu hawayen farin ciki ne suka zubowa Aleena tana qara jin soyayyar mijinta na rasa ko'ina a sassan jikin ta, Sosai mutane sukayi mamaki domin babu wanda yayi tunanin haka, leeyana ma taji daɗi sosai, tun lokacin da fara ganin yaran suka shiga ranta musamman ma macen dake kamada amminsu sak.

A lokacin da taji an saka sunan kuma taji ta qara qaunar yaran fiye da tunanin mai hasasowa.

Haka akayi biki lafiya aka qare kowa ya koma gida.

bayan wata biyu leeyana ta shigo watan haihuwa a yanda aka basu IDD.
Tun farkon shigowar wata leeyana ke fama da matsanancin zazzaɓi tanajin naquda akai akai kafin wani lokaci ta nemi naqudar ta rasa.

Babu yanda turab baiyiba akan mum ta barshi ya fita da ita waje amma taqi yarda.

Kwanaki uku da wannan wata ranar Alhamis leeyana ta tashi da naquda mai tsanani, tun da sassafe suka kinkimeta suka kaita wata private hospital.

Kwanan su ɗaya da awanni ana abu daya, leeyana ta jigata sosai, haqiqa duk wanda ya ganta dole ya tausayamata.

Allurorin tada naquda babu kalarda ba'a yimata ba amma abun yaci tura.

Nan likitan ya sanarmasa ya zama dole ayi mata c's da gaggawa, idan kuma ba haka ba za'a iya rasa babyn ko kuma ita kanta.

Jin haka ya saka turab ya saka hannu tare da yimusu transfer din kudin da za'a buqata bayan an gayamasa adadinsu.

Likitan na shirin sanarda sauran likitocin da yake aikin c's tare dasu.

wata nurse ce ta shigo office din da sauri.

"Sir kazo, da alama haihuwar ce tazo, amma gskiya akwai matsala domin matar ta kusa kasawa"

Wata mummunan faduwar gaba ta ziyarci turab lokacin da yaji kalaman nurse din na karshe, fuskar leeyana kawai ke fadowa aransa ya na qara nema mata sauqi wurin Ubangiji.

Fita likitan yayi da sauri tare da yiwa turab magana akan suje dakin jira su jira.

Haka nan jiki babu kwari suka koma dakin jira sukayi jugum jugum suna sauraren hukunci rabbil izzati.


Bayan shigarsu dakin da kamar awa daya saiga nurse d'aya ta shigo dakin fuskar ta babu fara'a ta miqa masa baby boy din da ke lullube cikin tsadadden lallausan towel.

Da sauri mummy-neesah ta taso domin mum fanaya da turab duk basu san shigowar matarba sunyi nisa a cikin tunani har sai da sukaji mummy-neesah na fadin

"masha Allah tubarkallah hajiya fanaya leeyana ta sauka"

Da sauri mum da turab suka miqa hannu lokaci daya su qarbi babyn, sai kuma ga nurse din nan ta dazu ta qara shigowa da yaro daya, qarbar wanda ke hannun mummy-neesah mum fanaya tayi, shi kuma turab ya nufi nurse din sam bakinsa ya kasa rufuwa, cikin madaukakin farin ciki ya furta

"twins......?!"

Ko rufe bakinsa bai yiba ga wata nurse ta shigo da wani baby a hannunta.

Turab kamar ya nutse saboda farin ciki ya karbi yaron daya yana fadin "duk namu ne"

Nurses din suka amsa masa da "kwarai kuwa, duk 'ya'yankune, Allah ya azurtaku da samun yara maza har uku a lokaci daya"

Sosai idanunsa suka chanja launi jaaa ya maye gurbin fari.

Miqawa nurses yaran yayi batare da 'bata Lokaci ba ya durkusa qasa hannunsa sama kamar mai addu'a kafin yayi sujudul-shukhur, ya dade a haka sannan ya d'ago ya karbi yaran yayi musu addu'a, car keys ya fitar guda biyar ya miqa musu da kuma katinsa da address dinsa.

"Wannan tukuicinku ne, idan anjima ku kirani wannan kati nane kuyi sending account dinku, sannan wannan address dina ne inda zaku zo ku dauki motocin"

Mamaki sosai ya rufe nurses din, ansha haihuwar yara uku a hospital din nan amma ba'a taɓa samun wanda ya karramasu kamar wannan mutumin ba.

Su Mummy-neesah ba bakin magana ko wannensu ya ɗauki yaro daya sai kire kiren waya suke suna sanarwa.


"Ya jikin matata" turab ya tambaya.

"Jikinta da sauki, ta samu bacci tana resting room sai idan ta tashi sannan zaku ganta"

Kafin kace me tuni mutane sun cika Asibitin sai tururuwa ake, har 'yan jarida da gidan talabijin.

Yara kam son kowa qin wanda ya rasa, kyawu ne ya had'u da kyau, domin ko turab ba baya ba kyakkyawane na gaban kwatance mai zubin larabawa, leeyana kam ba'a magana.

Tuni leeyana ta farka amma jikin bai sake yanda akeso ba, sai da yamma liqiss aka sallamesu suka koma gida, sosai Mutanen su na Maiduguri suka bada gudunmawa, baramma ummasalima tayi namijin qoqari, kamar yanda tayiwa Aleena. Haka tayiwa leeyana ko wane yaro sai da tayi masa set din akwatuna, ya zamana ta kawowa yara set uku kenan, mamansu ma haka.

Mum fanaya har rasa bakin godiya take idan ta kalli abunda ummasalima tayi, baiwar Allah sai tace mata ba komai yiwa kaine ko bayan haka Leeya da qanwarta marayu ne kuma ga zamanda sukayi da mahaifiyar su.

A bangaren turab fahad da zafaran sun dage sun hana masa siyan ko tsinke, duk wani abu da kukasan ana sakawa jarirai sai da suka saka shida ko wannensu bibiyu kenan, hatta akwatunan da ake kawowa su zafaran sukayi, da aka fara shigowa da kaya sai da kowa ya riqe baki ganin irin kayan da zafaran da Fahad suka kawowa yaran abokinsa kamar a kamfani.

Mutanen da ke gidan basu qara shiga mamaki ba sai da suka ga anshiga da qosassun raguna guda uku da manyan shanu biyu masu matuqar girma da wani babban raqumi ɗaya wanda a nufin su a yankawa yara ranar suna.

Turab kam harda kukansa domin bai taɓa tunanin haka ba, duk da shima yayiwa yaransu amma ko kusa baza'a had'a ba.

A cikin kayan kuma aka gano makullin mota har uku a baiwa yara, Tuni gida ya dauki ihu da shewa.

Turab kam ya rasa tayi domin wannan yafi qarfin ayi masa godiya, tunaninsa da wace kalma zai yi amfani wajen Bayyana musu farin cikin sa.

Mum ta kirashi batun sunan da za'a sakawa yara amma yace ya riga ya sakamusu suna kawai ranar suna yake jira.


Jin haka ya saka mum ta bar zancen domin tunda taga haka tasan baya so ta sani shi yasa tayi shiru da bakinta kawai.


Su ma su fahad sun tambayeshi batun sunaye ya gayamusu ai leeyana ta riga ta sakawa yaran suna, kuma bazai iya musa mata ba.

Zolayarsa suka fara yi cikin wasa, samm abun bai masa zafi ba domin sun saba da irin haka.


Zafaran ya shaidar wa da mutanen da yakamata su san yau Aleena zatazo bikin suna.

da kuma sauran families dinsa. Sanin ba wata matsala ya sanya mum ta saka aka gyara masu bangare d'aya a gidan.

Sosai mutane suke gangaro domin anshirya gagarumar waleemah wacce za'a hade yaran wuri daya ayi musu waleemar duk da ba wata tazara a tsakanin su, banner turab ya saka aka yimasa a sirrance mai dauke da sunan jaririyar Fahad, da kuma yaran zafaran da kuma nasa yaran.
Ranar suna kuwa tunda sassafe mutane suke kasa kunnuwa suji sunan da za'a sakawa yara.

Sai misalin ƙarfe goma na safe maroqa suka fara kida da roqa.

"Allah ya raya 'yan uku tagomashin albarka, yara masu halin Dattaku Da tausayi, yara jinin arziki da wadata. Yara qanana renon manya jikokin Khattab waasibudden ministan shari'ar uban turab, kakan turab. Ina gaisuwa gareka kakan 'yan uku jikokin albarka, gahees uban fahad kakan Fahad, mun kowa gaisuwar mu gareku qabilar chochawa, gaku da d'a zafaran gakuma farin jika zafaran kun samu Allah dai ya barma kowa nasa"

Marokan suka faɗa suna nufar gaban families din zafaran, aikuwa suka fara zuba kudi har sai da aka riqesu, sun birge mutane sosai yanda suka fidda dan su kunya.

Wani mutum yazo yayiwa maroqi ɗaya rad'a a kunne, gyaran murya yayi yana qara saita speaker a bakinsa ya fara da fadin.

"An nemi mu ambaci sunan jikokin albarka, 'ya'ya uku chas maza.

"na fari sunansa (zafaran, ambashi laqabi da Akhram) sannan na biyu sunansa (turab ambashi laqabi da Afeef) sai kuma na ukunsu, nasan kun sanshi. Amma kuma domin fitardaku kokonto yasa zangayamuku....! Na ukun sunansa (zafaran, amma laqabin sa shine Aslam).
Yara dai sun ci sunanyen mahaifansu.

Sosai wuri ya ɗauki ihu da shewa, zafaran da Fahad da kuma turab suna zaune a balcony sunsha dressing kamar sababbin angwaye, zaune suke suna cin kalaluwan abincin da aka had'a musu hatta su samanta iyayen zafaran sai da sukayi musu kalar girkinsu suna ci sai faman santi suke sukaji sanarwar da maroqan keyi.

"Man Zafaran kaji abunda nake jiyowa kuwa.......?"

Fahad ya yi maganar da alamun tambaya.

Ka sah kunne Zafaran yayi yana jiyo yanda ake faman sakawa yaransu albarka.

"Naji kamar sunayenmu mutanen ke fad'a kho.....?"

"Eh nima haka naji wallahi"

"Kenan sunayen mu aka sakawa yaran?"

Fahad yayi magana yana kallon turab da son jin qarin bayani,,,,,,

ko kallonsu baiyi ba ya miqe ya zura takalmansa yayi tafiyar da lokaci ɗaya.
Miqewa sukayi suma suka bishi suna yimasa magana amma yaqi kulasu har suka iso filin da mutane suka yawaita kuma anan ne makid'an da maroqa suke.

Ganinsu ya saka kidan ya kara tashi da qarfi ana yimusu kirari, hakan ya saka 'yan uwa da abokan arziki suka fara shigowa filin suna yimusu ruwan kudi.

Meenal da Khulud da kuma zohal dauke da yaran uku ko wacce a cikin su tana riqe da ɗaya suka iso cikin filin"

Fahad da ya kula dasu da sauri ya qaraso yana washe baki yace "ina little Fahad yake...?"

Kallon kallo suka fara yi domin kamannin yaran daya ba mai iya bambancewa a cikinsun.

Fahad da ya fahimci haka sai ya juya ya kira turab da zafaran sukazo.

"Nunamin ina little Fahad a cikin su"

Dariya turab yayi kafin yayiwa su meenal alama da hannu su zo.

yatsun yaran ya fara dubawa ɗaya bayan ɗaya har ya gama dubasu tsaff.


"Khulud je ki miqawa Fahad na hannunki shine Aslam little Fahad.........

"Meenal ki miqawa zafaran shine Akhram little zafaran"

"Kenan na hannuna ne Afeef Little Turab....?"
Zohal ta tambaya da mamaki.

"Eh, na hannunki Afeef ne"


Sosai mamakin abun ya kamasu, Khulud kam da ta kasa shanye mamakinta sai da tayi magana tace "ya-Turab ya akayi ka gane yaran nan da wuri haka, har fa gardama muke nace na hannuna ne Afeef domin shi yafi kama da kai"

"Ah ah na hannunki shine Aslam gskiya, wannan dake hannun zohal shine Afeef"

"To Amma........ya akayi ka gane haka bayan babu wani banbanci tsakanin su....?"

"Tun ranar da aka haifesu danaga kamarsu tayi yawa sosai na saka aka qeramusu zobunan azurfa, ko wanne zobe yana dauke da harafi daya na farkon kalmar sunansu, ba ma su kadai aka yiwaba har Ifrah da CHIDINMA da kuma duben duk anyimusu ban natsu bane da naje dakaina na kaimusu nasu suma"

Zafaran na dariya yace "amma ba sunan nan ka saka ba kho...?"

"No Ammi da Abbi na saka sai dai sunan nasu yanamin dad'i a baki shiyasa na zaɓi na dinga kiransu haka"

Godiya fahad da zafaran sukayi masa sosai suna qara jin qaunar junansu.

Kar'ba yaran su meenal sukayi suka koma cikin gida bayan anyi pictures.

Lafiya qalau akayi waleemar yaran nasu baki daya, ifrah, CHIDINMA, duben sannan da 'yan uku Aslam da akhram da kuma Afeef.

A banner da memo da calendar wacce turab ya raba duk haka aka sakawa yaran suna da kuma pictures dinsu matsu matuqar sha'awa da daukar hankali.

Bayan shekara daya, komai na gidan ya dawo normal hankalin kowa ya kwanta domin kuwa har an aurarda yara da yawa a familyn kamar dai Khulud da meenal da kuma twins.

fannah a gombe tayi aure. mayah a cikin garin kaduna, meenal ma a kaduna tayi aure.

Idrak kam ya sami buɗi sosai arzikinsa ya ha'b'baka domin idan za'a zano sunan shahararrun matasa masu kuɗi a cikin garin suleja sunansa zaizo na uku koma ya fito na biyu.

Sosai mum fanaya ta dinga rokon papu akan ya auri Dayammah ko ba komai sun zauna tare da ita sun santa da kyawawan halaye, kuma idan yayi hakan ya taimaka. Da kyar ta samu ta shawo kansa ya amince aka dauramasa aure da Dayammah.

Hakan ma ya qara saka Papu yin kwakkwaran bincike akan fairozha, amma aka shaidamasa ai ta dade da mutuwa, kwatsam rana ɗaya akaga gidanta da suke tsafe-tsafensu ya kama da wuta ba'a fitarda komai dake numfashi ba a gidan, aka gayamasa yanzu shekara daya da wata biyu da kwana biyar kenan.

domin wannan al'amari ba qaramin yawo yayi a jarida ba shiyasa aka kasa manta kwanan wata.

Sosai Dayammah tayi mamaki domin idan ta auna da kyau kenan ranar da ta bayyana labarin su wurin mum da sauran mutane ne haka ta faru, aikuwa da tasan wannan shine had'arin da fairozha take magana akai da tuni ta dade ta fallasa asirin kungiyar.


Leeyana, da Aleena, da kuma Idrak Papu ya tara gaba ɗaya tare ta alqalai domin

60 / 61