BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   49 / 61

144K to 147K   out of 180.4K words

kansa a kafadar ta ya lumshe idanun sa.
Juyowa tayi gareshi lokacin da ya kwantar da kan nasa taji shi rad'au, da alama bashida lafiya ne akwai abunda ke damunsa.

Sake godiya da tazbihi tayi acikin ranta tana qara godewa Allah daya albarka ceta da wadannan yara.

"Allah ya kara shiryamin ku, Allah ya raya ku bisa tafarki madaidaici" ta fad'a a fili duk suka amsa da "Ameeen"

"Fanaya Rawaan Hahmeed, ina miki murna da samun 'ya'yan 'yar uwarki cikin koshin lafiya, Allah ya rayasu ya qara hadin kanku, Allah Ubangiji ya jikanta ya yafe mata kurakuranta yakai haske kabarinta" cewar papu yana kallon fanaya.


"Ameen ya rabbi justice, godiya maras adadi. Allah ya jikan faheema da kuma sauran muminan da suka rigamu gidan gskiya"

Kowa ya amsa addu'ar mum sai papu ne kadai da ya yi zurfi a cikin tunanin da yake.

Magana mum ta fara yimasa sai dai hankalinsa baya wurinta. Kallon ta ta mayar ga baban twins wato dad qarami fuskar ta dauke da damuwa tace "baban twins dan Allah kabani labarin abinda da yake faruwa da justice na kasa gane masa tunda ya dawo gidan nan sanin ba haka muka saba ba, kana ganinsa kasan yana dauke da damuwa, meyake faruwa"

~Awanni biyu da suka gabata~

Tafe suke su biyu kadai sai kuma driver a cikin wata rantsatstsiyar farar mota sai kyalli take kamar madubi idan ka tsaya kusa da ita.
Sunci ado dakyau komai nasu iri daya ba abunda ya banbanta kama daga kalar shigarda sukayi. Motar tasu tayi packing ne a harabar babban central mosque dinda yake gaba da unguwar su kad'an, duk wanda ya gansu yasan suna cikin farin ciki da nishadi.
Fitowa sukayi lokacin da motar ta yi packing suka nufi cikin masallacin juma'a mutane ma sai tururuwa suke ganin lokacin sallah ya gabato.

Dad qarami ne ya kalli papu fuska dauke da fara'a yace "Justice meyasaka ka hana yaran nan zuwa masallacin nan?"

Shima papu da murmushi a fuskar sa ya bashi amsa "Nafiso ayi komai yanda na tsara, bana so a sami kuskure shiyasa na dakadardasu daga zuwa masallacin nan suje na gaba da nan idan aka daura auren sai a sanar musu"

"To amma justice abokansu fa da suka gayyato"
"Kowa ya zauna a daura auren a gabansa mana, ai wannan ba matsala bane in yaso idan an gama sai su kirasu a waya, kuma ma duk abokansu da suka gayyato idan suka ganmu ba wata magana ai"

"Tau shikenan Allah ya sanya alƙairi ya sa hakan da muka yi shine daidai"

"Ameen ya rabbi" papu ya fad'a daidai lokacin da suka qaraso kofar shiga Masallacin.

Fara gaisawa sukayi da mutane har suka isa inda zasuyi sallahr, basu jima da zama ba aka tayarda sallar juma'a, bayan an idar ne kuma aka fara gabatar da adadin auren d za'a daura.
Nan limamin ya fara karanto sunan yaran da za'a daurawa aure da kuma mazajen da zasu auresu ciki harda su leeyanah.
Sunan da aka d'aura na karshe ne da kuma wanda aka ambata a matsayin ango ne ya saka papu mikewa ba shiri ya fita Masallacin kamar wani zararre.

Duk irin iskar da ke faman kad'awa sakamakon bishiyoyin lim dake zagaye da masallacin bai hana papu jin zufa da zafi na kwararo masa ta ko'ina a sassan jikinsa ba, sai sharce zufa yake yana fifita da hularda ke kansa fad'i yake yana cewa;

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, taya wannan auren zai yiwu. Taya wannan babban al'amari ya faru.
Idan na aikata haka na so kaina, meyasa zan 'bata farin cikin mutanen dayawa akan na farantawa kaina Ni d'aya tak ya subhanallah.
Allah ka sanya wannan lamarin yazo da sauki ya rabbi kana gani bani na aikata haka, taya duk wannan zai faru alhali ba haka na bayar ba......" Yana cikin yin zancen ne a fili yaji an dafa kafad'arsa ta baya.

Juyowar da zaiyi ne yayi ido biyu da gahees dafe da kafad'arsa, tun kafin gahees yayi magana papu ya tare shi da fadin "wallahi ba Ni na aikata ba, to wa zaiyi haka gahees, dan Allah ka sanardani zuciyata gaf take da sarewa domin kunya ce danqare a ciki, don girman Allah ka sanar dani wani abu"

Murmushi dad ƙarami yayi yana bubbuga kafad'ar papu a hankali yace "kwantar da hankalin ka justice, kanaso mu kashe kan mu da kanmu ne, idan har ina da abu kuma samun abun bai fi qarfi na ba wallahi zan iya sadaukarda shi ga yarona saboda yayi farin ciki.
Ina tunani kamar ka manta d'ana yana dauke da wannan cutar kho, kasan Ni likita ne, kuma a bakina kuka fara jin cutar da yake dauke da ita, shin saboda na boye ban gayamuku illar abunda kuke shirin yi bane yasa ku bazakuyi tunani da kanku ba, kasani danmu yana dauke da cutar (BPD) borderline personality disorder, wannan cutar cutace mai hadarin gaske Justice. Nasan duk yanda zanyi maka bayani bazaka gane ba, amma zan takaitamaka ko da zaka iya fahimta, borderline personality disorder the mental health disorder marked by intense emotions and unstable relationships.
People with BPD often fear abandonment and have difficulty managing their feelings. They may struggle with self-image, impulsive behavior, and mood swings. requires professional help like therapy to manage symptoms and improve quality of life.

Wannan ma'anar cutar kawai na baka, lokacin da kuka fara kawoshi kaga wasu alamomi a tattare dashi kho, tun a lokacin naso sanar maka da illolin cutar nan ganin hankalin ka baya kwance yasa nayi shiru har zuwa lokacin da wani abun zai taso.

This disorder makes a person very sensitive emotionally. They need constant care and can get very upset if things don’t go their way. Stress and negative feelings can seriously affect their mental health.

Justice d'a namiji ɗaya tak Allah ya baku, kuma yana dauke da wannan babbar larura shin bazaku tausayamasa ku nema masa farin ciki da kanku ba, kwantar da hankalin ka muje gida yanzu"

Dad ƙarami ya fad'a yana rike hannunsa zuwa mota, jikin papu yayi sanyi sosai da jin abunda dad qarami ya fad'a, yasan gaskiya ce ya fad'a, to ya zaiyi shi kansa yasan yaso kansa da yawa duk da ba shi ya sauya komai ba, amma ga Dukkan alama aikin dad qarami ne.

*Wannan shine abunda ya faru a masallaci wurin daura aure, kuma ana kammala wa dad qarami ya kira yaran gaba ɗaya ya sanar musu an daura aure, tsakanin zafaran da kuma turab ba wanda yayi gigin tambayar matar da aka aura masa domin sun fahimci kamar ran dad qarami 'bace yake.

"Allah sarki, to Allah ya sanya alƙairi a auren nan, kuma Allah ya bada zaman lafiya. Dan Allah ina neman wata alfarma guda d'aya rak" cewar mum tana shafa kan Aleena dake kwance a cinyarta.

Dad qarami da ya harbo jirgin ta yayi saurin cewa "yawwa, iyayen zohal sun tuntuɓeni maganar daukar amarya. Na yanke shawarar a abuja zasu zauna gaba ɗaya, kuma a sababbin gidajena dana gina kwanakin nan, na saka an gyara ko'ina kuma an

Na saka furnitures sun sa komai a ciki, ga address din gidajen kowa a cikin ku ya dauki arear da yakeso ya zauna da iyalansa idan kun gama dubawa sai ku sanarda ni a fara shirin tafiya"

cewar dad ƙarami yana miqawa Fahad da zafaran da kuma Turab wasu takardu, da alama sune takardun address din.

Dubansa ya kuma kai ga yaran yace, "Rukhshanah, ko kuma dai nace Aleena, my sweet daughter ki tashi kije ki fara shirin tafiya gidan mijinki kinji yar albarka" dad qarami ya fad'a da shigar rarrashi.

Da kuka sosai ta tashi da gudu ta nufi mummy-neesah ta rungume ta tana faɗin "mummy dan Allah kice na fasa auren, Wallahi bazan iya tafiya na barku ba Please mummy kicewa dad a fasa dan Allah, fannah mayah kuna gani za'a rabamu banason tafiya dan Allah" da gudu suma fannah da mayah suka nufo inda take suka rungumeta suna kuka da magiya akan afasa da auren.

Dariya ma suka bawa kowa dake wurin "aure kam an riga an daura ai" cewar dad qarami cikin ransa.

"Dad kace ya saketa har ta girma, wallahi munyi alqawarin idan ta girma zamu kai ta da hannunmu ba ma sai ya zo ba"

A wannan karon kam papu ya kasa riqe dariyar sa har sai da yayi sannan yace"to ai ba anan garin yake ba, bakiji ance Abuja zasu zauna ba, means mijin d'an Abuja ne kho?"

"Ehh" twins suka fada kamar wasu qananun yara.

"To sai munje da ita rukhsha, idan mukaje sai mu nuna masa qarama ce bata girma ba, a saketa sai ta isa aure zaku kawota da kanku"

"Eh papu, wallahi a gayamasa haka munyi alqawari, kuma damu za'a je muyi masa alqawari da kanmu"

"No my twins basai anje daku ba, in sha Allah yanda mukaje da ita lafiya haka zata dawo lafiya. Kunga lalla'ba shi za'a yi yayi sakin, wata qila idan mukaje da ku zai iya qin yarda da abunda mukazo masa dashi, zai yi tunanin kamar mun tara masa mutane ne".

Ba dan sun so ba suka amince ayi tafiyar ba tare da su ba, amma a tabbatar cewa an dawo musu da rukhshan su gida yau.

Da kyar da sudin goshi suka amince har ita Rukhshanah din, inda aka umurci leeya itama taje ta shirya babu 'bata Lokaci, kuma a cikin tsatstsauran hukuncin dad qarami yace ba wanda zaije abuja acikin yaran, iyayen yaran kawai aka kira suyi rakiya.
Aunty saknah da kuma aunty Rafa'at qannen su papu mata kenan.

Aunty saknah aka had'a ta da Rukhshanah da kuma Mummy-neesah domin rukhsha taki yarda su rabu da mummy ko nan da chan.

Ita kuma leeya aka had'a ta da aunty Rafa'at kad'ai, domin mum bazai yiwu taje ba tunda da ita za'a je daukar matar fahad wato zohal.

Sai a lokacin da aka gama tsara komai dad qarami ya kalli mum yace fadi alfarmar da kikace kina so ayi miki.

Cikin d'an jin haushi mum tayi murmushi kawai tace "baban twins kenan kuci gaba da aikinku kawai daga baya mayi Magana"

Murmushi shima yayi kaana ya umurci Aunty saknah da kuma Aunty Rafa'at suje su taya yaran had'a kayayyakin su.

Leeya kam sosai take kuka kamar ranta zai fita ga Khulud itama da take jin leeya kamar wani bangare na jikinta a yanzun nan, take ji ina ma ace yanzu ne zasu fara rayuwa, sai gashi lokacin da komai ya bayyana, a lokacin kuma aka rabasu.

Id ganin Khulud na kuka Sosai gwanin ban tausayi ya sakashi fita daga parlorn, haka kurum yake ji bazai iya jure ganin hawayenta ba.

Yana fita parloun ya nufi wani bangare na gidan ya sami wuri ya zauna, kiran number din ta ya fara bugu hudu ta dauka.
Tun a cikin wayar ya fara rarrashinta har sai da yaji tayi shiru ta daina kuka.

Awanni kad'an aka gama hada musu komai nasu, sannan su haji-mainah da mum da kuma maman twins da su Aunty saknah suka zaunar da su sukayi musu nasiha sosai akan hakuri da kuma juriya a zaman aure, nasiha sosai sukayi musu mai ratsa jiki, tun lokacin da aka fara yimusu nasihar suke zubarda hawaye har aka gama ana shirin tafiya.

Da gudu leeya taje ga mum fanaya ta rungume ta tare da fashewa da wani irin kuka mai ban tausayi.

mum kuma hawaye take kawai murmushi kwance a fuskar ta tana yimata magana a hankali yanda ba kowa yake iya jiyota ba, "kiyi hakuri kinji, in sha Allah nan da sati ɗaya komai zai daidai ta. Naso a d'aga wannan tafiyar kafin a shiryaku, a gyara ku. Amma kuma naga kamar baban twins baya son hakan yanzu shiyasa nayi shiru kawai, amma nan da sati ɗaya in sha Allah komai zai daidaita zamuje har Maiduguri da ku kusan dangi, suma su sanku kinji 'yar albarka, Allah ya baku zaman lafiya mai dorewa da mijinki, Allah ya baku hakurin zaman aure ya albarka ce ku samu tsaftatacciyar zuri'a"

Leeya da kuka yaci qarfin ta qasa cewa komai tayi sai kuka take yi har Aunty Rafa'at tazo ta ja hannunta tana rarrashinta suka wuce mota.
tana tafiya tana waigen su mum da su meenal, khulud, fannah, da mayah, Aneesa da kuma badariyyah.

Suma suna tsaya sunyi cirko-cirko abin murna ya dawo kamar na kuka.

Misalin ƙarfe shida na yamma suka dauki hanyar Abuja, leeyanah kaɗai Sai aunty Rafa'at sai kuma driver da zai kaisu.

A hanya ma leeya bata daina kuka ba abun ka da farar fata fuskar ta tayi jajir kamar gauta, aunty Rafa'at kam sai d'ari-d'ari take, domin da ba'a gabanta mum ta rungume ta ba babu abunda zai saka ta shigo mota d'aya da ita ba, taso tayi tambaya amma kuma ganin ana uzurce yasa tayi gummm da bakinta, hatta driver kallo ɗaya yayi wa fuskar leeya ya rud'e domin ya haqiqance aljana ya dauko shiyasa yaketa sheqa gudu babu daddaukawa domin ya tserar da ransa.
Itama aunty Rafa'at sai zancen zuci take domin ko leeya da kanta zata faɗa mata cewar ita ba aljana bace bazata yarda don tasan babu inda za'a sami halittar dan Adam mai kyau da tsari haka kuma a kirata da mutum.
"Idan mutum ce wane irin kyawu Allah ya bata haka".

Da misalin ƙarfe bakwai na yamma suka karaso, da yake an kwatantawa drivern estate ɗin yasa bai wani sha wahalar ganewa ba.

Wani tangamemen gida ne da ya amsa sunansa gida, tsayi fadar kyau da tsari irin na gidan bata lokaci ne domin bazai fad'u ba sai wanda ya gani da idanunsa.

Packing yayi a madaicin packing space din gidan, da drivern da mai gadi suka shiga da kayan da su leeya sukazo dasu.

Leeya kuma tana bacci bata ma san sun iso ba sai ji tayi ana kiran sunanta a hankali.

'Dago jajayen idanunta tayi ta kalli aunty Rafa'at tace "Aunty mun qaraso ne?"

"Eh mun qaraso leeyanah, kinata bacci"

"Wallahi aunty bansan zuwan baccin ba ina ta tunanin mum"

"Allah sarki, aikuwa mun qaraso fito kiga gidan ki leeyana, gidan da muke miki fatar kasancewa har qarshen rayuwarku"

Jiki a sanyaye ta zuro qafarta waje gabanta na duka uku-uku, kasa d'aga 'kafar tayi nan take ta fashe da kuka mai sauti.

Tana tunani barkatai a zuciyarta, shikenan yanzu nan zata ci gaba da rayuwa, ba mum, ba zohal ba papu, ba Aleena kuma.
Ga sabuwar amintacciyar ta meenal itama babu ita.

Haka taci gaba da zance a zuciyarta sai kuka take. Abunda leeya ta manta shine Aleena da zohal duk a abuja suke domin suma anan aka basu estate.

Tunowa da hakan da tayi ya saka ta d'an tsagaita kukanta sai matsar ƙwallah kawai.

Aunty Rafa'at kuma sai ban baki take tana bata hakuri da guntayen nasihohin manzo Sallallahu alaihi Wasallama.

Miƙewa tayi ta fito daga motar jikinta duk ba kwari ta fara takawa sannu a hankali tana kallon yanayin tsarin gidan a fakaice.

Har suka isa Tsakiyar kasaitaccen parlorn ta ba wanda yayi magana a tsakanin su.

Sai dai kafin ta shiga Aunty Rafa'at ta umurce ta da yin Addu'o'i daban daban wadanda manzon Rahma yayi umurni dasu a daidai wannan yanayin na sabuwar rayuwa.

Aunty Rafa'at ta sha mamaki sosai ta kuma ji dadi ganin yanda leeya ta dinga karanto Addu'oin neman tsari da kariya da kuma samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidan aurenta.

Nan aunty Rafa'at taji leeya ta qara shiga ranta, kuma ta qara yaba hankalin ta da nutsuwarta.

Komai na parlourn tsaf-tsaf gwanin ban sha'awa, kuma tsarin parlourn yayi dai-dai da mace mai tsafta kamar leeya domin komai na parlorn adon fari ne sol da ratsin golden ba sosai ba.

Zama sukayi cikin daya daga kujerun furnitures din da akayi order daga Saudiyya gwanin kyau kamar ka sace ka gudu.

Leeya na zaune ta kasa d'aga kanta, sai 'kullawa da kuncewa take cikin zuciyar ta.

Aunty Rafa'at kuma tana zama ta shiga kitchen ta d'akko cup da ruwa masu sanyi ta bawa leeya.

"Bana sha, na qoshi aunty" leeya ta fad'a cikin sanyinta.
"Leeyanah Please dan Allah karki saka damuwa cikin ranki, wallahi da nice ke babu wani abu da zai baqantamin rai a fad'in wannan duniyar yanzu, kinga na farko sama da shekaru goma kuna gararamba baki San dangin mahaifiyarki ba balle na mahaifinki, sai gashi yau da rana tsaka Allah ya bayyana miki su cikin tsatso mafi albarka da asali da Dattaku.
Sannan abu na biyu yau Allah ya d'aga darajar ki, burin ko wace mace ganin wannan rana, ke kuma gata nan kingani. To me zai hana ki nunawa Allah farin cikin ki a fili da kuma 'boye leeyanah?. Please karki zama mai butulcewa da ni'imominsa ki zamo mai yawan godiya a gareshi kinji"

"In sha Allah Aunty zan kasance mai yawan godiya da ni'imominda Allah ya yimin".

"Nice gurl, haka nakeso naji kin fad'a, ga ruwan kisha kinji" cewar Aunty Rafa'at tana miqamata mug din ruwan sanyi.

Karɓar ruwan tayi ta dan sha kadan sannan ta ajiye.

"Muje na nuna miki bedroom dinki" Aunty Rafa'at ta faɗa.

Mikewa tayi tana binta a baya har suka isa wani tangamemen bedroom kyakkyawan gaske kamar cartoons aka bawa yin decorations komai na dakin kyakkyawa ne.

Kamar yanda parlour yake haka nan bedroom komai na cikinsa fari ne mai ratsin golden.

Kan wawakeken farin royal bed din ta ta qarasa ta zaune gefe daya ta zabga uban tagumi.
Har ga Allah idan tambayar ta za'a yi meya sakata cikin damuwa batada takamammiyar amsar da zata bayar.

Qarar kiran waya ne ya shigo wayar aunty Rafa'at, sai a lokacin leeya ta tuna da wayanta.

"Allah sarki, wallahi na manta wayana suleja" ta faɗa a zuciyarta.

Sai da kiran ya kusa katsewa aunty Rafa'at ta daga kiran da sallama da kuma murmushin ta duk a lokaci daya.

"Okay, kin kwatanta masa kenan,,,,,,,,,"Allah ya sa zai gane wurin. Dan Allah banda bata lokaci, kinsan ango ya kusa qarasowa yanzu,,,,,,,,"ok Nagode sai na iso,,,,,,,,, Ameeen ya rabbi" Aunty Rafa'at ta faɗa tana ajiye wayarda ke hannunta.

Dubanta ta kai ga leeyanah dake zaune ta tsurawa wuri ɗaya idanu kamar ruwa ya chanyeta tace "leeyana zan tafi gidan aunty hajaarah, dayake ba'a sanar dake a gida ba kho? Zan tafi yanzu dan kinga dare ya soma yi har karfe tara ta gota, kinga kho ya kamata in tafi, kuma ma gidan da zan sauka suna nan suna jira nazo"

Murya na rawa kamar wacce zata fashe da kuka tace "Aunty tafiya zakiyi ki barni dan Allah ki bari Zafaran yazo kinji, banzo da wayana ba kuma koda nazo da wayar banada number dinsa balle na san inda yake

49 / 61