Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
watsa masa ruwan wuta "yanzun nan bama da tabbacin tana raye, ko ta mutu"
"Ah ah Fahad lewa bata mutu ba, bazata mutuba in sha Allah, sai munyi Aure kuma mu haifi ƴaƴa da izinin rabbi"
zafaran ya faɗa wasu hawayen na ƙara gangarowa a kumatunsa.
Sake dafashi turab yayi yana cewa "ba'a san namiji da ragwanta ba abokina, anason namiji da juriya, wannan halin daka tsinci kanka ka yarda jaraftace kawai. Idan lewar ka ta mutu shikenan ba abunda zamu ko kuma kai zakay...."
"Lewa bata mutu ba, inaji a jikina bata mutu ba, domin muhsin daya gayamin ya faɗamin ƴan harin sun tafi da ƴan matane da ƙananan yara, kaga lewa mace ce kuma karamar yarinyace a wannan lokaci" zafaran ya tari numfashin Turab tun kan ya ƙarasa zancensa.
"Shikenan, ƙaddara da gaske ne ma sun tafi dasu, a ina suka kaisu?, a ina zasu tafi dasu?, me zasuyi dasu ?, zafaran! Duk kana da amsar wadannan tambayoyi?. Magana fa ake ta shekaru shida baya, shekaru shida fa ba kwana shida bane zafaran dan Allah kayi hakuri kasawa zuciyar ka salama in sha Allah komai zaiyi fine kaji abokina.............✍🏽
BAYAN WUYA......
By RUMANA M DIGGI
EP.22
____________K. MANSION SULEJA NIGERIA.
"Nayi farin ciki sosai da Allah ya haɗaki da fahad zohal, haƙiƙa zanfi kowa farin ciki idan haka ta kasance, kuma zanyi iya ƙoƙarina domin ganin hakan ta kasance. Fahad mutum ne mai sauƙin kai ko ban faɗa ba ma kin gani, shi ba kamar Turab bane halayensu nada bambanci sosai, dan Allah kiyimin alkawari ɗaya zohal"
mum ta faɗa tana kallon zohal dake zaune gabanta. Leeyana kuma a gefen.
"In sha Allah mum, ki faɗi kowane alkawarine indai har zan iya to zanyi miki shi da yardar Allah"
"Zaki iya zohal, kan maganar fahad ne. A matsayin da fahad yake kai na aiki yanzu ya kamata ace yanada iyali ko dan kula da wasu abubuwa, amma kuma kinga babu iyalin. Sosai mahaifiyarsa tayi farin ciki da Wannan zancen da ya zomata saboda har tabar garin nan zancen ki muke, domin bata ɗauki maganar da wasa ba.
Shima fahad ɗin haka, saboda hakane ma ya kawoki wurin mu, kuma bari kiji mahaifinsa yace a shaidamiki idan kun sasanta kanku sati mai zuwa zaizo da kansa suje suga mahaifinki, kuma su nemi auren ki. Shiyasa ma na zaɓi na gayamiki tun yanzu domin ku fahimci juna dashi. Amma me kika ce game da haka?"
"Nidai bazan ce komai ba mum, saidai nace Allah yayi mana jagora, kuma ya shige mana gaba, yasa hakan ne yafi zama alƙairi"
"Ameeen zohal, Ubangiji Allah yayi muku albarka, ki tashi kije ku tattauna ta ƙawarki nasan abunda kike matuƙar buƙata kenan, domin alamun ki duk sun nuna. Kije ku tattauna tunda mun jira turab har yanzu bai dawoba"
"Mum ina ya tafi" leeya ta tsinci kanta da yiwa mum tambaya.
"Yaje Abuja ya raka abokansa, kuma yace min yau zai dawo, naga har yanzu bai dawoba ina ga ko can zai kwana"
Miƙewa zohal tayi tana faɗin "mum zan tafi amma zan dawo gobe in sha Allah, leeya kuma zamuyi magana ko a wayane, domin dare yayi yanzu karfe goma na neman shuɗewa, leeya zan kiraki da waya gobe mayie magana in sha Allah"
"Leeya ki tashi ki rakata gate zanyiwa driver magana yakaita gida"
"Ah ah mum, ki barshi kawai dana fita zan kira gida na faɗamusu ko Aunty zainab ce zatazo ta ɗaukeni ko kuma a turomin driver".
"zohal kenan ita zainab ɗin bataso ta hutane da zaki saka a tasota yanzu daga unguwar ku tazo nan ɗaukarki, ai tunda ga drivern gidan ki bari ya saukeki gida kawai"
"Tau mum, ba damuwa. Nagode sosai Allah ya huce gajiya"
"Ameeen, sai da safenki, kuma karki manta dan Allah idan kinje gida ki gayawa mahaiyarki saƙona ko ki turamin da number ta kawai"
"Tau in sha Allah mum zan tura miki tun kan na ƙarasa gida ma"
"Okay, sai na jiki".
"Muje bestie" zohal ta faɗa tana wucewa gaba, leeya kuma tana biye da ita.
Fira suka ɗan taɓa a ƴar tafiyarda sukayi kafin su iso wurin da drivern ke zaune Tare Da mai gadi, nan suka tarar dashi sai fira sukeyi a tsakanin su suma.
Suna isowa wurin suka gaidasu cikin girmamawa, suma suka amsa musu cikin girma.
daidai lokacin da ake ta faman danna horn a bakin gate.
Da sauri mai gadin yaje ya buɗe kofar, wata baƙar mota ƙirar Benz ta shigo gidan, ta gaban su leeya motar ta wuce.
leeyana da zohal suke, ratse gefe domin su bawa motar damar wucewa.
Parker motar akayi daidai inda suke tsaye. Daga can ɓangaren driver kuma ya buɗe motar ya fito yana nufosu, dayake ba wata tazara tsakanin su domin zagayowa kawai zaiyi motar ce ta shiga tsakani su.
akwai hasken electric solar a wajen yasa suka gane ko waye.
"Fahad me ya dawo dakai suleja kuma yanzun nan!?" Zohal ta faɗa da mamaki.
"Zohal ce ta dawo dani wallahi zuciyata ta kasa samun sukuni, shiyasa na sake dawowa. Wata ƙila idan nayi firar dare dake zan samu sauqin abunda nakeji a kanki, gaba ɗaya soyayyar ki na neman rikitani zohal anya kuwa ba lauje cikin naɗi" Fahad ya faɗa da alamar wasa.
"Hmmm, har mashi akwai cikin naɗi Fahad" kaga nifa har na manta da wani fahad"
Zohal ta faɗa fuskar nan tata babu yabo ba fallasa.
Da sauri fahad ya dafe ƙirjinsa ya jingina da motar da ƙarfi.
"lafiya" cewar zohal tana ƙara jaa baya kamar wacce taga wani abun tsoro.
"Zohal, kin manta dani fa kikace, wallahi so kikeyi ki illa ta zuciya ta da waɗannan kalaman naki kawai, a yanzu kam na fara ganin alama kan abunda abokaina suke faɗamin, haƙiƙa na zurfafa sosai a soyayyar ki, kuma sun faɗamin idan kika gane haka zaki iya amfani da wannan damar ki cutarda zuciyata zohal. Don Allah na roƙeki idan bakya sona tun yanzu ki faɗamin karki saka ni faɗawa mawuyacin hali na roƙeki Please"
Fuskar zohal ce ta sauya sosai zuwa wani yanayi mai wuyar fassara, fushi, ɓacin rai, hasala, zuciya. A wanda yake kallon fuskar ta zai fahimci duk wadannan abubuwan.
Tafiya ta farayi cikin isa da taƙama harta matso gab dashi, tsayuwa tayi sosai tana ƙara murtuƙe fuska tamkar ba itaba.
Duk abun da yake faruwa akan idon leeya, duk da batasan ta soyayya ba, amma ta fahimci irin tsananin soyayyar zohal dake cikin zuciyar fahad, sosai kalamansa suka bata tausayi, duba da yanda ya marairaice, mamakin zohal ne cike tabbb a cikin ranta domin a tsawon zamanta da ita a ƙalla zasukai shekaru biyu da watanni.
Bata taɓa sanin ta da halayyar wulaƙanci ba, kuma tasan zohal sosai tanada son mutane, koda bata sonka bazaka gane ba saboda bata nunawa. Amma sai gashi yau a gabanta zohal na neman wulakanta wani, bayan kuma tasan zaman ɗa yake a wurin mum.
"tabbas idan na bari zohal ta wulaƙanta fahad ban kyautawa kaina ba kuma bazan taɓa yafewa kaina ba akan haka.
koba komai shi ɗan adam ne wanda ya cancanci karamci a ko'ina, gashi kuma shi musulmi ne cikakken, daɗin daɗawa kuma zaman ɗa yake a wurin mum, haƙiƙa bazan bari kiyi abunda kikeda niyyaba zohal" leeya ta faɗa a zuciyarta tana dakawa zohal tsawa.
"Ki dakata daganan zohal" cewar leeya tana yowa kanta.
A daidai lokacin turab kuma ya banƙaɗo marufin motar kamar zai ballashi domin kuwa ya hangi wasu abubuwa biyu daya kasa bambancewa a cikin ƙwayar idanun zohal tsakanin soyayya da ƙiyayya.
Turab ya fitone da nufin ya janye abokinsa domin yana gani baza'a ci zarafin fahad ba a dalilin soyayyar macen ma dayake gani a idonsa bata kai ba balle ta kawo, domin idan ta shi
ne wallahi zohal ko kallo bazata isheshiba.
Cakk suka tsaya su biyu yayinda suka ji abunda zohal ke ƙoƙarin faɗa "fahad me kace? In faɗa maka idan banasonka kace?.
Zuciyar fahad na bugawa da sauri sauri kamar ganga, Muryar sa kuma na rawa cikin fargaba da kuma tsoron amsar da zata fito daga bakin zohal yace
" ehh, idan bakyaso na ki gayamin, wallahi nayi miki alƙawarin zan fita rayuwarki, kuma zan manta dake kamar yanda kema kika manta Dani".
"Abu na farko inaso ka buɗe kunnayen sosai kaji abunda zan faɗa maka, FAHAD G. WAASIB, ZOHAL KHALIL GIRAH na sonka, kuma tana ƙaunarka, soyayya zohal a gareka ka gaskiya ce, ba abunda zai sauya haka. Kuma Ni zan zamo matarka in sha Allah, mu rayu tare cikin so da ƙaunar juna saboda Allah" Lumshe idanunu ta yi a hankali kamar bazata buɗe ba taci gaba da faɗin;
"A Rayuwar nan tawa ban taɓa jin wani abu ya shiga raina ya sami wurin zama sosai ba sama da soyayya ka, nasan kanasona fahad kuma nima ina son ka, domin inada tabbacin da za'a auna girman soyayyar ka dake zuciya zatafi taka yawa.
A lokaci ɗaya soyayya ke shiga cikin zuciya ta ratsa jiki da jinin wanda ke ɗauke da ita, haka soyayyar ka tayimin fahad. A farkon ganina da kai kaima idan zaka fahimta zaga gane yanda na kusa loosing control saboda ɗimauta da nayi, kai baka gane ba?, nasan ka gane Fahad saboda gane War da kayi ne ya janyo hankalin ka kaymin magana.
A tashin farko da kaymin magana ba soyayya ko ɗigon soyayyata a zuciyarka, sai bayan mun rabune ka faɗa halin da na faɗa tun a farko, kasan yanda zuciya tayita azalzata akanka kuwa, wallahi fahad da ace ban ƙara haɗuwa dakai ba, da bansan yanda zuciya ta take ba halin yanzu" murya a tausashe ta ƙarashe maganar da faɗin "Abu na ƙarshe fahad na roƙeka kazo mu haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tabbatar da maganar da abokanka suka faɗa ba gaskiya bace.
Idan ma zata kasance gaskiyar to kaine zaka yi amfani da girma da kuma adadin soyayyar da nake maka ka illa tamin zuciya,
Ina ƙara baku haƙuri gaba ɗayan ku da kukayimin kuskuren fahimta harke bestie, kuyi hakuri duk ku yafemin Ni wallahi ko kaɗan ba abunda yake raina ba kenan"
Zohal tayi maganar tare da dunkule hannayenta alamar roƙo.
daga nan bata ƙara cewa komai ba tayi tafiyarta ba wanda kuma ya dakatar da ita domin kalaman ta sun sanyaya jikin kowa dake wurin sosai.
Sake jingina jikinsa yayi a sanyaye a jikin motar tasu, ya ɗaga kansa sama kamar maison tunano wani abu, domin kalaman zohal sunyi masa daɗi sosai yama rasa me zaiyi yayi farin ciki "ina zataje" fahad yayi tambayar while kansa na sama, kuma yana jingine a motar.
Leeya ta fahimci da ita yake shiyasa bata jira kowa ya amsa masa ba domin tasan ita yake tambaya tunda tare ya gansu.
"Gida zataje"
"Wazai kaita gidan ko a ƙafa zataje saboda abun hawa zaiyi wuya a unguwar nan"
"Driver ne zaije ya kaita, nasan yanzu haka tana nan waje shikuma drivern gashi can yana fitar da mota daga parking space" leeya ta faɗa tana kallon wurin.
"Tk bani carkey zanje na kaita".
Sai yanzu hankalin leeya ya dawo kan wanda aka kira da Tk wato (Turab Khattab).
Wani irin tsalle zuciyar ta tayi ta faɗo yayinda tayi arba da fuskarsa, "baƙon balarabe" ta faɗa a cikin ranta.
juyawa tayi da sauri har tana harɗewa a yafiyarta saboda tsananin tsoron sa.
Turab kam tsaf ya fahimceta domin shima bai ankara da ita a wurin ba saida bayan angama komai.
Wani irin haushi ne ya turnuƙeshi, a yanzu kam ya gane tsaff yarinyarnan tsoronsa take, "tukunna ma wacece wannan yarinyar?"
"Amsar tambayar ka tana hannun mum" fahad ya faɗa yana shigewa cikin motar.
A zaton turab a zuci yayi maganar sai bayan Fahad ya amsa masa ne ya gane a fili.
Juyawa yayi ya tafi abunsa, ita kuma leeya har tayi nisa a tafiyarta.
Shigowa yayi a parlour bakinsa ɗauke da sallama, da mamakinsa bai tararda kowa cikin parlourn ba. Harya taka stairs da nufin hawa sama sai ga mum zata sakko.
"Dama kai nake zaman jira wajannan tun ɗazu, nayi tunanin a can zaka kwana ai".
"Jirana kuma mum, Allah dai yasa lafiya"
"Lafiya amma ba lau ba"
"Subhanallah, waye bashida lafiya mum"
"Wallahi ƙanwarkace da ɗan sami buguwar ƙashi".
"Allah sarki ina khulud ɗin take"
"Hmmm, khulud ce kaɗai ƙanwarka".
"Ah ah mum, suna nan dayawa ma kuwa, amma dai gaskiya banji daɗi ba, nasan ma daga cikin baƙine kho, yanzu shikenan za'a ce daga zuwa walima sai dawowa da ciwo"
"Tau wannan kam ai ba baƙuwa bace ƴar gida ce"
"Ƴar gida kuma ba khulud ba"
"Eh, ba khulud bace, khulud kam inaga tashige bacci tun ɗazu"
"Wacece mum?"
"Leeyanah"
"Leeyanah" ya maimaita sunan a bakinsa, ɗan jimmm yayi yanaso ya tunano inda ta taɓajin sunan na"
Ya ɗauƙi tsawon seconds sittin a haka kafin ya ɗan jijjiga kansa kaɗan hadi da jin guntun tsaki.
"Akwai matsala ne"
"No mum, nataɓa jin sunan nan a wani wuri, amma na kasa tuna wurin"
"Okay inaga a gidan nan ne"
"Maybe" ya faɗa yana komawa cikin parlour.
Bayan ya zauna da alama dai jira yake wacce batada lafiyar tazo yace "mum, niko inada tambaya"
"Tambaya kuma tame turab"
"Mum, wacece wannan yarinyar mai saka niqab"
"Leeyana" mum ta bashi amsa a takaice.
"Okay, amma mum ita ƴar waye a familyn mu"
"Ba ƴar familyn mu bace, amma dai zata zama in Sha Allah"
"Ba ƴar familyn mu bace kuma?" Cewar turab da alamar tambaya.
"Eh, ba ƴar familyn mu bace, ƴar gidan hajiya saknah ce, ƙawata marigayiya wacce ta rasu a shekarun baya nasan kasanta ai, inaga kamar ma kana nan lokacin da nake nema a bani yarinyar"
"Eh, ina nan mum, kuma nasan da rasuwar, amma mum ita wannan ba zuhra bane sunanta"
Murmushi mum tayi irin na yarda da kai tace"saidai idan ka manta amma ba zuhra bane sunanta LEEYANA ne"
"Okay, to meyasa take ɓoye fuskar ta, tayi aurene"
"Ah, ah batayi aureba"
kwashe labarin komai dangane da saka mayafinda da leeya keyi a fuskar ta, mum ta bawa turab kamar yanda leeya ta gayamata. Har ita kanta mahaifiyarta bata yarje mata tasan fuskar ta ba sai ranar da za'a ɗaura mata aure koma idan an ɗaura"
"Eyeeh, mum kina nufin kice itama kanta bata san fuskar taba kenan"
"Tabbas itama batasan fuskar ta ba, saboda hakane take kiyayewa kanta, domin batasan nufin mahaifiyarta nayin haka ba".
"Gaskiya mum, abun akwai ban mamaki, to Allah dai ya sauwaqe".
"Ameen" mum ta faɗa tana ƙwalawa leeya kira.
Kamar kullum ta fito cikin tafiyar ta ta nutsuwa, kanta a ƙasa saidai wannan karon kam ta sako hijab saman rigar da ke jikinta.
Zuciyarta sai duka take, gaban mum tazo ta durkusa har ƙasa
"Mum, gani"
"Kije ga yayanku can yana jiranki, ya duba miki hannun ki Kinji"
Miƙewa tayi cikin sanyi ta nufeshi shikuma turab ko inda take bai kalla ba kai kace baisan da zuwanta wurin ba, harta ƙaraso kusa da shi ta zauna a ƙasa har kuma wannan lokacin bai ɗago ya kalleta ba, itama bata ɗaga kai ta kalleshi ba, kuma bata cemasa uffan ba.
"Mum, Bara naje na dakko first-aid box ko, akwai wani cream ta zan shafa mata a hannun".
"Ok kaje ka dakko, bara na hau sama kafin ka dawo, leeya ki tsaya ki jirashi kinji banda raki" mum ta faɗa tana ɗan murmushin wasa.
Daga kanta tayi alamar taji abunda mum ta faɗa, yayinda Turab ya tashi yabar wajen itama mum tabi bayansa.
Babu jimawa yadawo hannunsa ɗauke da wata karamar akwati.
Daining area yaje ya ɗakko ruwa masu sanyi sosai, da kuma ƙaramar kujera daining sitter.
A gabansa ya ajiye kujerar tana fuskantar sa, sannan ya buɗe ruwan ya tsiyaya a cup, ya kuma ɗakko akwatin a gabansa yabuɗeta gaba ɗaya, wani farantin ya fito dashi daga cikin akwatin,
kaana ya fito da cream ɗinda zaiyi amfani dashi ya ajiye kan wani ƙaranin Centre table ɗinda ke tsakanin sa da kujerar da ya ajiye.
Har a lokacin leeya bata ko ɗaga kanta ba balle tasan abunda yake.
Wata uwar Tsawa ya daka mata yana faɗin,
"ke so kike nazo na ɗagaki na zaunar dake kan kujerar nan ko me, da kika wani zo kika sakani a gaba sai kace mai neman yafiya"
Bata furta masa komai ba ta miƙe kawai ta zauna kan kujerar.
Farantin ya janyo har gabanta kan Centre table ɗin, sannan ya janyo cup ɗinda ya saka ruwa shima har kusa da inda hannun ta yake
"gashi nan ɗauki ki zuba ruwan nan a inda ya kumbura, ruwan sanyi ne sosai, kuma zakiji ba zogi idan kika zuba ki daure kawai ki zuba kada ki damu da abunda zakiji.........✍🏽
BAYAN WUYA....
By RUMANA M DIGGI
EP.23
_____________ɗayan hannunta da baya ciwo ta ɗauki cup din dashi sai ta tara hannunta ɗaya mai ciwon a farantin da ya ajiye mata, ta fara zuba ruwan.
lokacin da ruwan suka fara sauka a hannunta saida taji kamar tayi ihu da sauri ta runtse idanun ta tare da cije gefen lips ɗinta na ƙasa.
"Sannu" taji ya furta mata muryarsa wasai kamar