Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
taru ku mata bugun hatsi ko zata dinga baku girman naku"
"Kamar kina kusa Aunty zainab yi tafiyarki kawai kar ki damu"
Badar na gama faɗin haka Aunty zainab mahaifiyar Airah ta fice dakin ta janyo kofar ta rufe ta saka padlock.
Dariya suka fara yi ƙasa-kasa, suma sun kagu bata tafi ba tana tafiya kuwa suka dora inda suka tsaya.
Da misalin ƙarfe goma sha biyu na dare mai gadi yaji ana kwankwasa kofa kamar a mafarki. da karfi ya zabura yana kara murza idanu.
"Waye anan yanzu?" Ya faɗa cikin murya irin ta masu jin bacci.
"Turab ne". Mai gadin yaji ambashi amsa daga waje.
Tsoro, sauri, mamaki, duk suka zowa mai gadin a lokaci ɗaya
Yana taku a hankali yana kara dallara hasken fitilar sa bayan duk hasken da yake wurin na electric bai hanashi saka hasken fitilar sa ba.
Dan leqa wajen yayi kafin ya fara zare luck din a hankali.
"Baba wai tsoro kakeji mune fa, ai dare bai yi ba sosai har ta yanda zakaji tsoro" fahad ya faɗa daga wajen gidan domin ya gane nufin mai gadin.
Zare key mai gadi yayi ya buɗe karamar kofa "Alhaji karami lafiya cikin daren nan"
"Lafiya qlau, nazo ganin mum ne"
"Allah sarki to shigo" mai gadin ya faɗa yana hamma.
Turab ya fara wucewa sannan zafaran, da Fahad suka rufa masa baya.
Ba kowa a parlour kuma bakajin motsin komai sai na agogo.
"Man ka duba yanda muka zo muka sami gidan nan zaka iya rantsuwa da Allah karfe ukun dare ne"
"Eh wallahi kuma fa yanzu ne 11:50 amma babu wani mahaluki mai matsi a gidan nan sai cikin bacci"
"Ikon Allah to kaje ka fito zamu jiraka a parlour" fahad ya faɗa.
Juyawa turab yayi inda zafaran ke zaune ya jingine kansan ga sofa idanunsa a lumshe ya dafe saitin zuciyar sa kamar dai kullum abunda yakeji idan ya shigo suleja.
Girgiza kai kawai turab yayi bai ce komai ba sannan ya wuce part ɗin mum, knocking ya farayi a hankali.
Kuma a daidai lokacin mum na zaune kan sallayah tana tazbihi taji knocking.
Alama tayi kamar tana sallah, shikuma yana jin haka ya gane sai ya dan dakata da knocking din mintuna uku tsakani yaji tace "waye?"
"Mum turab ne ki buɗe kofar"
"Turab kuma lafiya daga ina kake yanzu?" Mum ta faɗa a dan tsorace.
"Mum ki buɗe Please, Kamar yanzu na fara shigowa gidan nan da dare"
Mikewa tayi taje ta bude masa kofar, da ido take binsa har ya isa ya zauna.
"Mum nazo ganinki ne daga kaduna muka zo, motar mu ta tsaya hanya sai da muka kira gida can kaduna aka kawo mana ita sannan aka kira bakanike yazo ya tafi da dayar data lalace. Yanzu kuma Abuja zamu wuce cikin daren nan kuma inada abunda zan dauka a cikin dakina shiyasa na biyu ta gidan nan da sai gobe zamu zo, yanzu haka ana jirana a parlour badai kuna lafiya ba?"
"Lafiya qlau muke, amma dan Allah ka daina tafiyar dare turab wallahi tanada had'ari sosai baramma yanzu da duniyar ta zama sai a hankali"
"Mum kiyi mana addu'a Allah ya tsare kawai, Bara na tafi sai da safenku"
"Allah ya tashe mu lafiya, Allah ya tsare hanya"
"Ameen" ya faɗa yana barin dakin.
Hanyar da zata sadashi da part dinsa ya nufa, wani mugun tsoro ne yaji ganin mutum ya wulga ta gefensa, amma a ɗan nesa dashi.
Da sauri yabi bayan mutumin domin bai iya tantance mace bace ko namiji.
Sai da ya kusa isa daff sannan ya gane mace ce kuma ya ganeta leeyana ce domin kayan bacci ne a jikinta masu nauyi riga da wando.
Mayafin da ya hango ne lokacin da ta juya domin itama taji alamar kamar ana biye da ita, sai dai bai bari ta ganshi ba, ta juya taci gaba da tafiyarta.
"Me kika fito yi cikin daren nan" ya faɗa muryarsa wasai kamar yanda yake magana da kowa.
Juyowa tayi a tsorace zata gudu ya cafko hannunta, a fusace ya kuma faɗin "tambayar ki nayi amma kike kokarin guduwa, me kika fito yi nace"
Bata wani ji tsoronsa sosai ba kamar yanda take a baya domin tayi imani da can baya ne da yanzu hawaye sun wanke mata fuska.
"Ko bazaki yi magana ba ne"
"Zanyi, ba komai na fito yi ba na kasa bacci ne yasa na fito kuma bana jin dadin zama wuri daya kar tunani yamin yawa"
"Meya hanaki bacci?"
"nima bansani ba baccin ne dai nasan bana ji"
"Shine kuma bazaki iya zama a part ɗin ku ba harsai kin fito nan ko ba mutane a can"
"Akwai, bazan iya zama bane domin su duk sunyi bacci nikuma bazan iya zama ni kadai ba"
"Saboda me?"
"Tunani zai iya min yawa"
"Tunanin me?"
Kallonta ta mayar kan hannunta da kuma nasa dake riqe da juna, shima ganin tana kallon hannunsa ya saka ya kalla.
Da sauri ya saki hannun nata, yana yarfe nashi.
"Ki koma sashen ku"
Tana shirin magana ya kuma daka mata tsawa, da sauri har tana haɗawa da gudu ta bar wurin ta koma part dinsu.
Part dinsa ya wuce shima yayi abunda zaiyi sannan ya koma parlour suka dau hanyar Abuja cikin daren nan.
Washe gari tunda asuba kowa ya tashi aka fara gyara gida tukunna bayan sunyi sallah, sannan aka fara shirin girke girken snacks da kuma juice wanda za'a bukata a wurin dinner.
Leeya kam kiran wasu tayi daga cikin daliban catering dinsu Domin su tayata hada wasu abubuwan domin ita ta zama mr.chief a gidan gaba daya, sai da gari ya fara wayewa wadanda leeya ta kira suka iso suka hadu suka fara aikin.
Sosai yanayin gidan ya sauya sai kamshi ta ko'ina.
Mafi yawan ahalin ango idan zasuje biki a gidansu Amarya suna zuwa da abincin su ne wanda zasu rabawa baƙin da suka zo dasu, da kuma wanda zasuci su kansu basai sun jira an basu abinci a gidansu amarya ba. shiyasa su mum sukayi komai nasu a gida.
Koda karfe goma sha daya na safe ta buga duk sun kammala aikin abincin da zasuyi, suka fara shirya wani abun daban kuma.
A boss quarter na gidan kuma mum neesah ce zaune tana shirya wa.
"Mummy Dan Allah nima zan fita"
"Fannah kina gani ga Rukhshanah nan bata jin dadin jikinta idan kika fita dawa zaki barta"
"Mum muje da ita nima bazan iya fita na barta ba"
"Rukhsha zaki iya fita?"
"Mum kuje kawai idan nu'aim ya tashi da bacci zan gayamasa kuma cikin gida, zan iya zama nikadai, bana son hayaniya ne da zan biku ai ina so na sami relief ne da maganin da nasha idan na walwale zaku ganni, idan kuma ban fito ba sai idan za'a je dinner zan fita"
"Okay Allah ya baki lafiya"
"Ameen, sweet fannah ki gaidamin da mayah kinji"
"Zataji sweet rukhsha Allah ya baki lafiya"
"Ameen sai kun dawo"
Daga haka rukhsha da mayarda kwanciyar ta su kuma suka fita.
Koda Lokacin sallahr azahar yayi mutane a gidan ko magana ba'ayi aka sanar musu da zarar anyi sallahr la'asar kowa ya shirya motoci zasuzo.
Su khulud kam har sun shirya, meenal da leeya tuni suka wuce gidan su zohal, bayan kowa yayi sallahr la'asar ne aka fara shigar da kaya Boot, basu wani dauki lokaci ba suka kammala kowa ya tafi, har haji da sauran mutane ba wanda aka bari hatta rukhsha da batada lafiya.
"Ina ne venue din?"
"Royal elegant center, idan kunzo ku kirani ko ku kira zafaran wayan fahad ma na hannun sa"
"Ok sai kunzo, Allah ya kawoku lafiya"
Daga haka turab ya katse wayar, sannan yaci gaba da shirin sa.
Angwayen sunyi kyau sosai kamar su ukun ne ake daurawa aure, wankan farar shadda sol sukayi wacce akayiwa aikin hannu cikin tsari, kayan iri dayane su duka uku turab zafaran da kuma fahad, tsarin yanda aka dinka kayan nasu ne kawai ya bambanta.
Pics sukayi kafin daga bisani suka dau hanyar Royal elegant event center inda a nan ne ake gudanar da taron dinner party din.
A bangaren su leeya suma sunyi kyau sosai, musamman leeya da zohal, farin material suka dinka suma, dinkin ne kawai ya bambanta amma koman su iri ɗaya itace babbar qawar amarya.
Sultanah kuma da sauran familyn su zohal sunyi kalar ankonsu daban.
Suma su meenal da sauran familyn su fahad sunyi nasu daban.
Wurin yayi tsari sosai sai dai amarya bata iso ba tukunna, suna can an killacesu wuri daya har sai ango ya fara zuwa ya zauna.
Shigowar mc kamar da minti ashirin sai ga angwayen sun iso sai kamshi suke bazawa, mc ya fara kirari aka saka waqar aure yana binta ana yimasa liki har angon yazo ya zauna sannan su turab da zafaran da sauran abokansu suka juya suka tafi.
Bayan haka kadan sai ga zohal itama ta shigo da kawayenta, itama haka mc ya mata ya saka waqar auta waziri ta amarya ya fara bin waqar, qawayen amarya kuma suna yimasa liqi harda dollers, ganin haka ya saka aka fara ihu da tafi kan amare sun fara buge angwaye tun kan a fara.
Leeya na shirin isa wurin sai mum ta kirata da waya, da sauri ta janyo Sultanah tace "sulteey ki isa da ita ta zauna mum na kirana ina zuwa yanzu"
Fita tayi fili inda babu surutu sosai sannan ta amsa wayar.
"Okay, suna waje yanzu, tho bara na shigo dasu"
Daga yanayin yanda take waya na tabbatar wasu akeso ta shigo dasu hall din.
Fita tayi ba jimawa ta dawo da ba'ki, an fara gudanar da taron cikin tsari kuma anabin komai daki-daki.
Amarya da ango kadai ne zaune a can saman step, mc kuma a down.
Mc ya fara magana cikin d'aga murya yace.
"Bayan dogon jawabi da muka saurara a bangarori biyu na dangin Amarya dana ango, yanzu kuma zamu fara kiran babban yaya kuma aboki ga ango wato Turab k. Waasib dan Allah ku bashi hannu"
Nan family ɗin sa suka fara tafi da ihu wasunsu kuma suna video din fitowar sa, wasu kuma suna bin waqar da aka saka da muryoyinsu.
Fitowa yayi shima ya tsaya inda yaga kowa yana tsayi idan zai yi magana ya fara magana yanda ya kamata, sai da ya yaba halayen abokin sa daga karshe ya godewa Allah da kuma adadin mutanen da zukazo taron, ya kuma yiwa Amarya da ango addu'a da fatar alƙairi.
Sosai mutane ke murna har ya sauka wurin sannan zohal ta fara wurga idanu domin bataga leeya a wurin ba, leeya kuma tana tare da mum tun dazu itama mum bata zauna ba sai fama da 'baki suke.
Mc ya dora da cewa "yallaɓae turab k. Waasib mun gode sosai, munji bayanin ka kuma muna fatar Allah ya amshi addu'ar ka, yanzu kuma zamu kira babbar kawar amarya, amintacciyar ta, kuma yar uwarta wato leeyana Hamraz Awais, dan Allah ku bata hannu"
Wani mugun zabura da zafaran yayi har sai da ya bawa turab da sauran abokansa tsora, miƙewa yayi tsaye hannu na makyarkyata bakinsa na rawa yake nuna musu da yatsansa ya kasa furta komai sai rawa jikinsa yake sosai har kafafunsa suka fara gazawa dashi, tuni mutanen da ke wurin suka fahimta zaka iya faduwa ko yaushe, akayi saurin zaunardashi amma ya kasa zama sai nunawa yake bakinsa na rawa idanunsa kuwa tuni ruwan hawaye suka fara ambaliya, makoshinsa na sama da kasa da alama dai magana yakeso yayi amma ya kasa.
"Le!!!_ _ _le!, ita_ _ _ce!" Ganin yahaka ya saka suka zaunar dashi da karfin su suka daddafeshi.
Rukhsha na zaune ta d'ora kanta a cinyar mummy-neesah taji ankira wani suna,
"Leeyana hamraz Awais, wannan wane irin suna ne kamar na taɓa jinsa"
"A ina?" Mummy-neesah ta tambaya Rukhshanah.
"Wallahi mummy ji nake kamar nasan sunan nan" ta faɗa tana miƙewa zaune.
Ganin leeya ta hau step din da ake tsayawa ayi magana ya saka rukhsha fizgewa daga rikon da mummy tayiwa hanneyenta ta mike tsaye tana nuna leeya baki na rawa ta furta "Yahyah-leeya" daga haka ta sulele kasa idanunta suka kikkife kamar wata gawa ta daina motsi, su fannah da sukaga abunda ya faru da gudu suka iso burin ko kallon gabansu basayi sai buge abubuwan da ke gabansu suke sunata kuka da ihu har suka iso wurin,
Da sauri suka dafata suna kuka, mayah tace "innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un mummy me akayiwa sweet rukhsha meya sameta, mutuwa tayi mun shiga uku mummy"
Tuni wurin ya hargitse domin kuwa zafaran ma an kasa gane makarinsa da kyar aka samu mutane kimanin goma suka fita dashi hall din, aka sakashi a mota turab ya tafi dashi.
Leeya ma da sauri ta janyo zohal ta fita da ita wasu daga dangin zohal din suka sakata mota suka tafi da ita domin mutane cewa sukayi anyi kisan kai yanzu-yanzu a hall din nan,
Gaba ɗaya hankalin kowa a tashe yake wasu harda guntayen hawaye,
Fahad ma da sauri yayo kan rukhsha suka kinki meta suka sakata mota aka wuce asibiti da ita, mum kuma da leeya da badar suka shiga wata motar khUlud tayi driving dinsu suka bi bayan su mum neesah a asibiti.
Tuni labari ya isarwa su papu da dad ƙarami suma suka dauko hanyar zuwa abuja domin su a gida aka barsu.
Suna isa asibitin aka karbesu emergency don ganin halin da rukhsha ke cikin twins kam sai kuka suke kamar ransu zai fita duk a tunaninsu mutuwa tayi.
Mummy-neesah da fahad sai rarrashin su suke amma suka ƙi yin shiru,
Mum fanaya da badar da kuma leeya na isowa asibitin suka ci karo da turab.
"Mum Lafiya, meya kawo ku asibiti waye ba lafiya?"
"Kai zamuyi wa wannan tambayar turab"
"Mum zafaran ne wallahi ya dan samu shock tun dazu bai farfaɗo ba"
"Subhanallah, a wane room yake"
"Male side room 27 akwai abunda zan karbo Chemist, wa kuka kawo"
"Wallahi kanwar fahad din nan Rukhshanah, itace ba lafiya itama haka kawai akaga ta fadi ta daina motsi"
"Subhanallah tana da aljanu ne?"
"Wallahi muma bamu sani ba inaso inkira maman twins ne ta kwatantamin inda suke"
"Shikenan mum Allah ya bata lafiya, bara na yi sauri na dawo zanzo in Allah ya yarda.............................✍🏼
EP. 41
_____________________kiran mummy-neesah mum tayi ta kwatanta mata dakin da suke.
"Mum kuje ciki wata ƙila gida zan koma ko kuma na kira meenal tazo muje gidan su zohal"
"Saboda me bazaki shiga ba leeya?"
"Mum tsoro nakeji bana son shiga asibiti wallahi" leeya ta faɗa kamar zatayi kuka.
"Okay tau karki damu kajirani na duba jikinta nazo mu koma gida yanzu nima inaso naje naga ko su haji sun koma gida, amma ke wa zaki bi ki koma suleja yanzu ana shirin yin magariba"
"Shikenan mum kije ina nan ina jiranki, badar zaki iya shiga kho?"
"Ehh Nima zan shiga in dubata"
Khulud batace komai ba suka shige gaba daya ita kuma leeya ta koma ta jingina da motarda suka zo.
Bata jima da tsayuwa wurin ba ta hango turab yana zuwa idan take fuskar sa ɗauke damuwa.
"Leeyana, me kike a nan"
Karo na farko a rayuwarta da wannan bawan Allah yayi mata Magana cikin kwanciyar hankali.
"Bana iya shiga asibiti tsoro nakeji"
Yasan ana samun irin haka dama, akwai wasu mutanen da basa son shiga asibiti ko kadan idan ba dole Ba.
"Zo muje na bude miki mota ta ki shiga ciki ki zauna kafin su mum su fito tun da naga motar nan a rufe take kuma baki amshi key ba"
"Ah ah ya-Turab kaje kawai Nagode zan tsaya anan na jirasu"
"Okay normal, idan kin fi son haka, zan shiga nima na kaiwa abokina magani ana jirana"
"Sai ka fito" ta faɗa bata ko kalleshi ba, shima bai kara kallonta ba yayi tafiyar sa.
Shigar mum fanaya ɗakin yayi daidai da farfaɗowar rukhsha taga sumanda tayi.
Da sauri su mummy-neesah da fahad da sauran likitoci sukayo kanta.
"Nnene! Yahyah-leeya nagani itace wallahi" Rukhshanah ta faɗa murya a dakile idanunta rufe hawaye na bin gefen kuncinta.
Da sauri mummy-neesah ta kara kunnewanta saitin bakin ta ko zataji abunda take faɗa.
"Leeya! Yahyah-leeya leeya kece" rukhsha ta faɗa tana riko mummy-neesah.
Da sauri mummy-neesah ta dago ta kalli fahad tace da karfi "fahad Rukhsha ta sami lafiya, wallahi taga wani abu da ta taba sani kayi sauri kaje mota ka dauko allura nan da aka bamu a Bhopal ka kaiwa likita yazo ya mata"
Da sauri fahad ya fita dakin ya nufi inda suka aje motarsu da sukazo asibitin.
*_________
Idan baku manta ba a can baya na gaya muku an fita da rukhsha waje can Bhopal India, sunje anyi mata magani kuma sun gana da likitan qwaqwalwa har ya bata magunguna da allura daya tak, wacce ya shaida musu duk lokacin da taga wani abu da ta taɓa sani gabanin ciwon ya sameta idan har taga wannan abun kuma ta taɓa saninsa, da zarar ta farfaɗo da sunan abun a bakinta a yi mata allurar nan.
Tun daga lokacin duk inda mummy-neesah zata tafi da allurar take zuwa. tayi mata kyakkyawan wuri a cikin motarsu kuma ba wanda baisan inda allurar take ba don gudun bacin rana shine yanzu take gayawa fahad kan yake ya dauko.
*___________
Mum fanaya kuma jin Rukhsha na surutai wanda mafi yawan abunda take fadi a cikin maganganun da take sunan leeya ne yasa ta matso kusa sosai domin ita kanta ya rufe gaba daya.
"Hajiya fanaya dan Allah wacece leeyana danaji ankira sunanta dazu a wurin dinner, haƙiƙa tana da alaqa da wannan yarinyar Rukhshanah"
"Nima nayi mamaki sosai maman twins, amma bana tunanin leeya tasan Rukhshanah din nan gskiya, bazan ki ta taki ba bara naje na kirata tazo muji, amma kin gayamin yanda akayi kuka sami yarinyarnan meye zai hadata da leeya itafa leeya Lagos ta fito"
"Wallahi nima shine abunda yake bani mamaki, duk dai yanzu ba wannan ba dan Allah idan leeya din nan tana kusa ki kira mana ita musan wani abu daga wannan yarinyar"
"Tau shikenan Bara na kirata tana waje"
Fita daga dakin mum fanaya tayi, har kuma lokacin rukhsha bata daina magana ba idanunta a rufe sai hawaye suke sosai.
Mum fanaya na fita sai ga fahad ya shigo, ya mikawa mummy-neesah allurar da ya ɗakko.
Karba tayi sannan ta umurce shi daya kira likita, likatan na zuwa tayi masa bayanin komai nan take ya karbi allurar yayi wa Rukhsha, ko cire allurar bai yi daga jikinta ba tayi bacci.
A bangaren mum fanaya kuma tana fita tayi dialing number din leeya domin bata ganta a inda ta barta ba.
Ita kuma leeya tana tsaye jikin motar har wannan lokaci sai taji kiran mum ya shigo wayanta, ta dauka wucewa zasuyi yasa ta sauke ajiyar zuciya da karfi.
Sannan ta daga wayar "Na'am, ina wurin da mukayi packing ɗin mota,,,,,, ok tau gani nan zuwa yanzu"
Tana gama faɗin haka ta mayarda wayan cikin jakarta ta juya