BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   32 / 61

93K to 96K   out of 180.4K words

mutum ya cika tsufa sai bacci yayita yimasa yawa a kullum kamar dai yan da jarirai suke"

"Uhmm--hmmm nikam banida masaniya amma kaje ka tambayi wanda kaji suna faɗin maganar"

daga haka ta koma kan sopa tare da yin kwanciyar ta ƙyaleshi, sai dariya yake ganin yanda tayi da fuskarta..................✍🏽


















BAYAN WUYA.........













By RUMANA M DIGGI








EP.34









______________miƙewa yayi yabar ɗaƙin bayan yayi cokali biyu na abincinda yagani kan Centre table, dayake ba yunwar yake ji sosai ba shiyasa bai tsaya yaci da yawa ba.

A ɓangaren su Airah kuwa suna faɗawa ɗakin ko wacce su ta zube kan gado tana maida numfashi da ƙarfi saboda gudun da sukayi ga kuma tsananin tsoro take cike falll a ransu.

"Gaskiya uncle turab bashida mutunci wallahi matarsa kam ta shiga uku dan sai taga ta kanta"


"Ke Airah ki rufawa kanki asiri, turab kawunki ne fa gwanda muma idan yaji muna zafinsa zai iya mana da sauƙi ba kamar ke da yake ƙanin mahaiyarki ba dukan Kawo wuka zai yimiki"

"Wallahi Badar sai an faɗi gaskiya, ai ko iyayena sukejin rashin gaskiya sai an faɗa balle shi dayake ƙanin mahaifiyata"

"Menene rashin gskiya a ciki Airah, sabida yaga kuna rawa yayi muku magana shine yayi rashin gaskiya"

"Tau Aunty meenal nadaina tunda kinyi magana amma ko gobe yayi irin haka sai na maganta nikam, tun sa'adda nayi wayo ba ranarda nasan nazo gidan nan na tafi ba tare da uncle turab yaci ubana ba, ina ga wannan ne na fari wallahi"

Haka dai sukaci gaba da maganganun su kowa na sabgar gabansa.

Turab a ɗakinsa da misalin ƙarfe takwas da rabi na dare papu ya kira wayarsa, da mamakinsa ya ɗaga wayar domin tunda yayi tafiyar nan papu bai taɓa kiransa ba, kuma a duk lokacin da aka zauna family meeting duk wanda baya kusa sai ankirashi video call a ajiye wayar inda zaiga komai har ayi a gama yana ji kuma yana gani.

Amma a wannan karon kam papu baiyi masa hakaba, kuma ya hana kowa ya kirashi, tun tafiyarsa yake ganin wani abu mai kamada fushi daga mahaifinsa, haka ma jiya kamar wannan lokacin yana ƙasar Europe sai saƙon Aunty Safiyyah yagani wai papu na yi masa kiran na gaggawa a Nigeria.


Daya tambayeta ko lafiya, jiki a sanyaye sai tace masa "wallahi turab nima bansan dalilin kiran ba, kuma na tambayeshi ko lafiya yace ba yanzu zan san maganar ba sai komai ya kammala, Allah dai yasa lafiya"

"Ameen aunty Safiyyah, amma wallahi abun nan yaban mamaki to saboda me papu bai kirani da kansa ba saidai yakiraki kigayamin saƙon"

"Allah masani turab, kaidai kashirya gobe kazo gida, irin wannan kiran ba'a sanya domin bakasan abunda zakaje ka tarar ba"

"Haka ne Aunty Safiyyah Nagode, Bara naje nayi Booking flight gobe da sassafe zan dawo in sha Allah".

Sake sauke ajiyar zuciya yayi tunawa da yayi da maganar da sukayi jiya da shi da Aunty Safiyyah, saidai kafin ya kai ƙarshe a tunanin sa har wayar ta ƙatse.

Da sauri ya maida kiran amma tuni ba papu ya riga shigowa
"Assalamu alaikum"

"Turab kazo ina neman ka a sashena yanzu"

"In sha Allah gani nan zuwa papu"
Kittt papu ya kashe wayar batare da ya ƙara cewa komai ba, wannan ne ya ƙara tabbatar masa da cewa papu fushi yake dashi.
"To menayi masa, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un"
"Wazaka tambaya amsar tana wurin sa ai tun da kai bakasan kayi masa laifi ba" wani ɓangare na zuciyar sa ya faɗi haka.

Miƙewa yayi da sauri cikin tashin hankali ya nufi part ɗin papu, domin har ga Allah shi bayason fushin mahaifansa, a garesa hakan babban asara ce a wurin yin ibadarsa domin wani hadisi na Manzo Sallallahu alaihi Wasallama yana cewa "ridallahu fiii ridal-walidi, sakhɗullahi fiii sakhɗul-walidi" ma'ana (yardar Allah tana tare da yardar mahaifa, hakama fushin Allah yana tare da fushin mahaifa" idan kuwa mahaifanka sukayi fushi dakai babu shakka Allah zaiyi fushi dakai, idan kuwa Allah yayi fushi dakai kana cikin azaba.

A nutse ya shiga ɗakin tare dayin sallama, a fuska idan ka kalleshi kuwa kamar ba abunda ke damunsa, saidai a karkashin zuciyar sa kuwa damuwace fall ransa domin baisan abuda yake faruwa ba.

Shiga yayi ɗakin bakinsa ɗauke da sallama, su uku ya tarar a ɗakin haji, mum sai kuma papu.
A gaban haji yaje ya zauna amma a ƙasa saiti da ƙafarta, gaidasu yayi baki ɗaya duk suka amsa masa, saidai papu kam yana amsawa ya ɗauke kai fuskar nan tasa a haɗe.

"Haji, don Allah laifin me nayiwa papu wanda bansani ba" turab ya faɗa ɗauke da damuwa.

"Waƙa a bakin mai ita tafi dadi shi zaka tambaya ai tunda gaka nan ga shi"

Miƙewa yayi cikin nutsuwa ya taka har gaban papu ya durkusa "papu, babanah, dan Allah idan nayi maka laifi ina neman afuwa da gafara a gareka, dan Allah ka yafemin duk da nasan Ni banyi maka laifi ba, amma kayi hakuri idan wani abu nayi kake dubin shi matsayin laifi na roƙeka da sunayen Allah tsarkakakku mahaifina"

"Abu turab!" Papu ya kira Asalin sunansa a tsanake, yana kuma kifeshi da idanuwa.

"Na'am papu"
"Kasan anyi family meeting"
"Nasani, kuma naga anyi sanarwa a group tun Kafin ayi"
"Good, kasan me aka tattauna kuwa"
"Eh nasani, kan maganar auren fahad ne"
"Nice, but shi kaɗai kasami!?"
"Eh, shikaɗai nasani gaskiya, kuma NASAN kaso chasa'in daga cikin ɗari na taron dan wannan maganar akayi shi"

"Sauran kason fa"

"Gskiya bansan sauran ba"

"Turab ka saurareni sosai kaji abunda zan faɗa maka, jiya anyi maganganu da dama a wurin taron da akayi, kuma mafi yawa daga cikin maganar anyita ne saboda kai"

"Saboda Ni ku....."

"Dakata" papu ya katseshi ta hanyar ɗaga masa hannu.
Da sauri kuwa yayi shiru kamar bashiba, papu ya ci gaba da faɗin;

"mafi yawa daga cikin family sunyi korafi kan zamanka a haka har yanzu ba aure, ƙannenka da ƙannen ƙannenka duk sunyi aure, da aka lissafa ku, ku biyu ne zuwa uku kuka rage da ya kamata ace yanzu duk kunada iyalai, kuma duk a cikin waɗan nan da suka rage gaba ɗayan su ka girmemusu.

Duk sa'anin ka wasu suna ƴaƴa biyu wasu kuma uku, amma kai gaka nan zaune ba aure. Wasu zasu iya tunani rayuwar banza kakeyi da wasu ƴammatan waje tunda kakai lokacin da Yakamata ace kaima kazama magidanci amma kuma hakan bata kasance.

Na rantse da girman rabbi bakasan iya kunyarda naji a wurin ba, domin kuwa dole sai wani yayi zarginka da aikata mummunan abu a waje, wasu kuma zasu dubi da saka hannun mu a ciki.

Babban abunda ya baƙatamin rai wai ashe mahaifiyarka ta taɓa kiranka da batun auren nan amma sam kaƙi yarda, akace maka meenal kace bakaso, akace Aneesa itama kace ah ah, ga fannah, ga mayah, duk kaƙi yarda, da ma wasu daga cikin ƴan uwanka. Turab so kake ka shafa min baƙin fenti a idon iyayen wadannan yara, kuma ina matsayin babba a garesu.
Turab!!!!?" Papu ya ƙarashe maganar tasa ta karshe cike da sanyi.

"A yi hakuri papu in sha Allah wani abu nakeda nufin naƙarasa da yarda Allah idan na ƙara sa zan fito da matar aure, kuyi hakuri ku ƙara bani lokaci"

"Ba wani lokaci da zamu kuma baka turab wannan shine lokaci na ƙarshe saboda haka mun riga mun yanke hukunci"

"Hukuncin me kuma mum!?" Turab ya tambaya cike da tashin hankali.

"Mun zaɓa maka matar da zaka aura turab, kuma ba shawara muke baka ba umurni ne, inma kaso ko karkaso ruwan kane, idan kuwa kaƙi wallahi saidai ka changer wata uwar bani ba"

"Nima saidai ka canja wani uban bani ba, zan iya yimaka alfarma ɗaya idan kanaso kaje ka auro matarda ka zaɓarwa kanka daga baya idan ka kammala abunda zaka yi, amma wannan kam sai anyi in sha Allah Indai ba gawata ke magana"

"Subhanallah" ya faɗa a fili.

Papu kar Allah ya nunamin wata rana da zaku shata min layi na ketare, wallahi na yi na'am da zafinku koma wacece, na amince ɗari bisa ɗari duk abunda kukayi akaina kunyi daidai kuma na gode sosai Allah ya saka muku da alƙairi Allah yasa ku ganmu yanda kukeso"

A can cikin ransa kuwa tsoro ne da fargaba fal, "wannan shine dalilin da yaran nan suka dawo gidan nan saboda a haɗa aure, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, ya Allah ka sanya wannan zabin ya zamo alƙairi a gareni.
Ya rabbbb, wa nake da tabbacin itace aka zaɓarmin meenal banason meenal ban taɓa sonta ba, hakama mayah tayimin ƙanƙanuwa banasonta, Badar ma ƙaramar yarinyace Sa'ar ulud, Aneesa kuma batada tarbiyya, Airah ƴar Aunty Safiyyah ce ba aure tsakanin mu, khulud ƙanwatace bama zan sakota ba to wacece a cikinsu ya Allah!"

Ya faɗa a zuciyarsa tare da dafe kansa dake yimasa azabar ciwo kamar zai tsage.

Muryar haji ce ta dawo dashi hayyacin sa, sakamako tambayar da tayi masa "Abu Lafiya dai kho, anata yimaka magana kamar wanda ke bacci"

A hankali ya ɗago rinannun idanuwansa da sukayi masa nauyi sosai ya kalleta, "bakomai haji, ba abun da ya sameni na ɗan shiga tunani ne kawai banji kuna yimin magana ba"

"Ka shiga tunanin matarda aka haɗaka da ita kho"

"Eh haji dan Allah wacece aka haɗani da ita" ya faɗa muryarsa na karkarwa.

Shafff ya manta da mum da papu dake zaune a ɗakin domin kuwa shi kaɗai yasan abun da yakeji a zuciyarsa.

"Karka damu kaji, kar ka saka komai a ranka domin kuwa iyayenka sunyi namijin ƙoƙari wajen yin tunanin haɗaka da yarinya mai hankali da nutsuwa, ga tarbiyya ga kunya, ga ilimin addini sosai, wallahi ka ƙara godewa Allah da ya saka iyayenka sukayi tunanin haɗaka da Leeyanah a matsayin matar da zaka aura"

"What!!???, haji kinsan me kike faɗa kuwa wannan yarinyar ce aka haɗa ni da ita,
Itace mum da papu sukeda muradin na aura?, impossible haji, wannan bazai taɓa yiwu ba"

"Kamar yanda bazai taɓa yiwu mu kuma sakaka a jerin wanda muka haifa ba"

Sai a lokacin ya tuna duk abun nan dake faruwa mum da papu na zaune basu fita ""ya subhanallah, na rantse da Ubangijin talikai na karɓi zaɓinku mum, wallahi ku yarda Dani"

"Ka tafi" papu ya faɗa yana dafa kafaɗarsa, domin kuwa ya hango abun nan dayake hangowa a cikin idanunsa a duk lokacin da yake cikin halin tashin hankali"

( karku manta fa turab soja ne, kuma cikakken likitan Sojojin ƙasashen waje, saboda haka ana iya fahimtar abubuwa da dama a cikin ƙwayar idanun su, musamman ma idan suka faɗa wani hali).

Juyawa yayi kawai baice uffan ba har ya fita ɗakin, tafiya kawai yake baya ma kallon gabansa duk inda ya samu jefa kafarsa kawai yake, idanunsa ma ba sosai yake iya bude su ba saboda sunyi masa nauyi sosai, ikon Allah ne kawai ya ƙaishi sashensa.

A ɓangaren su khulud kuwa tunda suka shigo sashen ba wanda ya kuma fita, har aka kira sallahr ishah suna nan, sai bayan an idarda sallahr ne meenal ta fita da nufin ta zubowa leeya abinci taci, dalilin haka kuwa tun kafin ma turab ya gansu suna rawa ita leeya bata jin daɗin jikinta, saidai bata nuna ba sai yanzu ne da yaci ƙarfinta har ya kaita kwance.

Duk jikinsu yayi sanyi, sunyi zugum suna zagaye da gadonda take kwance duk sun zuba mata idanu ganin yanda take makerketar sanyi, kuma bayan sun rufa mata blanket har biyu, amma ba abunda ya rage.

"Badar kije ki dubo dan Allah idan su mum sun gama Maganar da suke ki gayamusu leeyanah batada lafiya"

"Bara naje na duba, amma yanzun nan naga Aneesa ta fita bansan ko can zatajeba"

"Okay tau ɗan jira, inaga can zataje domin duk ta fimu shiga damuwa" cewar MAYAH

"Haka ne, kinsan Aneesa tanajin tsoron mara lafiya gani take kamar mutuwa zai yi a gabanta" badariyyah ta faɗa tana kafe kofar ɗakin da ido.

"Allah sarki, in sha Allah leeya bazataje ko'ina ba"

"Allah ya ƙaddara haka"

"Ameen suka faɗa baki ɗaya har khulud daketa faman hawaye tun ɗazu.

Da ƙarfi suka waiwayo domin ganin wanda ya banko ƙofar ɗakin.

"Aneesa lafiya kike kuwa, saboda me zaki shigo bedroom a haka kamar wacce aka biyo za'a kasheta" cewar badar cikin jin haushin abunsa aneesar tayi.

Muryar Aneesa na cracking tace"kunsan me, yanzu zan shiga sashen papu najiyo maganarsu daga ciki, har haji da mum duk suna cikin ɗakin"

"Me kikaji suna faɗa a cikin ɗakin?"

"Khulud, ji nayi haji nata faɗar ya-Turab yayi dace sosai ya sami mata mai hankali ga nutsuwa ga...."

"Mata kuma Aneesa kodai bakiji da kyau ba, yaushe ya-Turab yayi budurwa har ana maganar mata bamuda labari"

"Mtswww yanzu Aneesa kan wannan ne zaki shigo haka duk kinbi kin tada mana da hankali"

"Hmmm, Mayah kenan ya zakiyi idan akace kece matar ya-Turab"

"Nop Aneesa banason irin maganar nan kinji, turab yayana ne kawai kuma ɗan uwana, Saboda haka ba wani mata ko aure"

"A misali ne fa kawai, kuma tambaya nayi miki kuma mu ƙaddara yana sonki fa, bawai baya sonki ba"

"Kidaina misalin dani domin koda a mafarki hakan ta faru sai na ƙaryata mafarkin duk da nasan mafarki ba gaskiya bane amma sai na ƙara karya tashi domin haka bazata taɓa faruwa"

"Tau mu kaddara bake bace wata ce ya kike gani zaman nasu zai yi"

"Tabb, ai koda yana sonta ɗin dole sai tayi hakuri dashi sosai, domin ya-Turab zuma ne ga zaƙi ga harbi. A ganina kawai macen soja ce zamansu zai yi daidai idan allurarsa ta sojawa ta motsa itama ta motso da tata shikenan saidai acee Allah ya sauwaqe"

"Idan yana sonta kenan koh, idan suna soyayya" Aneesa ta faɗa.

"Ehmana, ai dama sai anason juna ake aure" sukaji muryar Airah tana faɗar haka.

"Yawwa, to ya zakuji idan akace muku matar da aka bama ya-Turab basu taɓa soyayya ba, hasali ma bai santa ba, kuma koda yasanta bai taɓa ganin ta ba, basu taɓayin maganar da ta haura mintuna biyu ba"

"Saidai addu'a kawai amma wannan lamarin zai yi mata wuya sosai wallahi, amma Hausawa sukace bayan wuya sai daɗi maybe tasha wahala wajen gane kansa daga baya kuma ya dawo kamar bawanta, wata ƙila kuma mukadaine bama samun sauqi a wajensa zai iya yuwa matar ta samo kansa sosai"

"Hmmm, wallahi khulud bana tunanin haka, ki duba kiga yanda ya wulaƙanta meenal a gaban kowa saboda ta nuna masa so, shin meenal ta cancanci hakan a wajensa koda ba ɗan uwanta bane ai akwai hakkin masoyi, domin mai ƙaunarka ya gama maka komai a rayuwa"

"Hakane Aneesa, mudai muna fatar wannan da aka zaba masa tayi dauriya da taurin zuciya domin idan ba haka ba zaman bazai yi daɗi ba"

"Kunsan wacece za'a haɗa da ya-Turab kuwa"

"Ah ha sai kin faɗa" cewar Badar.

"Leeyana" Aneesa ta faɗa tana nuna leeya dake kanan naɗe a kan bed ko ina na jikinta sai rawa yake.

"What" suka faɗa a tare kamar haɗin baki.

Meenal ce tazo ta gaban Aneesa ta wuce dauke da farantin da ta sako wa leeya abinci. Kan side drawer ta ajiye farantin.

Kaff a cikinsu ba wanda ya iya cewa komai, kowa da abunda yake saƙawa a ransa.

Leeya kuwa numfashin ta ne ya tsaya chakkk, halin ciwo ne kawai yasa batayi wani ƙwaƙƙwaran motsi ba, domin duk firarsu tun daga farko har ƙarshe ba abunda bata jiba sai abunda suke faɗa yanzu, yanzu kam duk hankalin ta yabar jikinta.

Addu'ar ta kawai Allah yasa mafarki take duk abunda taji ba gaskiya bane, tana fatar haka a ranta.

Komawa sukayi suka zauna gaba ɗaya domin kuwa al'amarin yafi gaban wasa ba wacce ta iya cewa komai daga cikin su, sun rasa me zasuyi tsakanin murna da jimami, leeyana ƙawarsuce koba komai zasuyi farin ciki idan abun farin ciki ya samu, koda ba ƴar uwarsu bace ai akwai haƙƙin zama wuri ɗaya.

Turab kuma yayansu ne dole suyi murna a duk lokacin da wani abun alƙairi ya sameshi, kuma suyi baƙin ciki a duk lokacin da abun baƙin ciki yasameshi, wannan kam saidai su kirashi abun alƙairi domin aure rahmace mai lulluɓe da alƙairi, amma ba halin yin murnar a yanzu saidai ko daga baya.

Meenal ce ta kalli leeyana cikin tausayawa halin da take ciki tace "Leeyana tashi ga abinci kici kinji"

Cikin Muryar da take nuna alamun mai ita na dauke da zazzaɓi mai zafi tace "meenal da gaske ya-Turab aka bani a matsayin mijin da zan aura"

Meenal da ta fahimci idan tagayawa leeya gaskiya komai zai iya faruwa a yanayin nan da take ciki na mara lafiya yasa tace "ah ah ba gskiya bane kinji, wasa ne suke kawai suna zolayarki ne kawai, ina zaki iya da soja kuma litana sojoji leeya, wannan ai sai irinsa kinga ƙwarya tabi ƙwarya kenan" meenal da faɗa cikin ƴar dariyar da kanaji kasan iya laɓɓanta ne.

Miƙewa leeya tayi zaune meenal na taimaka mata har ta jingina ta ga kan gadon ta yaye mata blanket din da ta rufa dashi ta barmata shi iya gwiwoyinta.

Haƙiƙa duk wanda ya kalli leeya zai fahimci tsananin tsoron da ke cikin zuciyarta sakamakon wannan maganar da taji su Aneesa nayi, meenal dake kusa da ita sosai takejin ƙarar bugun zuciyarta ta karfi kamar ganga.

Meenal ta fara bata abincin tare da yimata kalamanda zasu kwantar mata da hankali koba komai tana bukatar su domin batada lafiya, a hankali har ta fara ƙoshi.

Sannan ta gayawa meenal cewa ta ƙoshi, magani meenal ta ɗakko a can parlon ƙasa ta dawo tare da ɓallawa ta bata, bako gardama ta karɓi maganin tasha, ta maida kwanciyar ta.

Su kuwa khulud suna fira jefi-jefi suna yimata ya jiki kuma, mum ce ta shigo ɗakin tare da yimusu sallama duk suka amsa mata suna gaida ita.

"Ina leeyanah" ta faɗa tana rarraba ido a tsakanin su.

"Mum leeyana na kwance batada lafiya tun safe" khulud ta faɗa tana nuna leeya dake kwance kan bed bacci ya fara kwasarta sai dai wannan karon ba rufe dake ba.

Da sauri mum ta isa gareta tare da dagota "leeya bakida lafiya har haka, meenal meyasa bakuzo kun gayamin batada lafiya ba, za'a bar

32 / 61