BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   46 / 61

135K to 138K   out of 180.4K words

bata nan ba.

Ban sameshi a kofar dakin ba, sai alamar tafiyar danaji ya wuce sashensa, da sauri na bishi har ina hadawa da gudu.

Turussss nayi lokacin da na isa tsakiyar dakin hilwah, bakinsa kawai naga yana motsi amma duniyar da nake a halin Yanzu bansan wani abu mai motsi da zai yi magana na ji ba.

Neelah yayar mahaifiyata ce kuma uwa d'aya uba daya, ita kadai na sani a garin calaba.

Da kyar na sami zarafin magana da sarka-kakkiyar murya nace "hilwah me ya sa sami neela, itace kwance haka? Mutuwa tayi? Hilwah neela ta rasu ne? Naga sai matattu ake rufewa har fuska, ko sanyi takeji hilwah?, ko kuma zazzaɓn ta ne ya tash......?"

Bansan a wane yanayi hilwah ke ciki ba nidai naji sautin Muryar sa kamar nesa dani sosai yana fadin.

"Dayammah sai kunyi hakuri kinga illar Rayuwa kho, ga yanda rayuwa tayiwa neelar ku, yanzu shikenan babu ita a wannan duniyar mai cike da tarin rud'ani, yanzu gashi mun kwana da ita amma bamu tashi da ita ba,

Dayammah na kira mahaifiyarki da sauran danginku na gayamusu abunda ke faruwa, sannan kuma na gayawa wasu daga cikin makwotanmu, kiyi hakuri kinji rayuwar kenan muda muke tsaye akan gawarta yanzu, wata rana wasu ne zasu tsaya akan tamu"

Daga haka hilwah bai qara fad'ar komai ba ya shiga toilet ya dauro alwala ya fito yayi sallah raka'a biyu sannan ya dauki chazbi ya fara salati gaban gawar neela.

Ina mamaki sosai yanda koda wasa banji hilwa ya tambaye ni fairozha ba, nikuma ganin bai tambayeni ba bai saka na ce masa komai ba game da haka, ina zaune a wurin sai kuka nake mai sauti da marar sauti duk wanda yazo yinsa kawai nake.

Lokacin da aka kira sallahr asuba hilwah yamin umurni akan naje nayi sallah, fita nayi na d'auro alwala nima na dawo dakin, har a wannan lokacin hawaye basu daina zuba a idanuna ba, ina tunanin yanda su maharaz da hamraz zasuji labarin mahaifiyarsu mafi soyuwa a cikin zuciyoyin su ta rasu ba'a gabansu ba.

Shigowa nayi da sallama dauke a bakina na nufi sallahya na tayarda sallah, bayan na kammala nayiwa neela Addu'oin neman gafara da afuwa wurin sarkin da ke kashewa da rayawa, tun kafin na tashi daga inda nayi sallah mutane suka fara shigowa gidan rututu, kafin kace me mutane sun cika gidan, nayita rarraba idanu ko zanga fairozha, amma ko mai kamada ita banganiba.

Har aka suturta neela za'a kaita makwancinta babu Ita babu alamar ta, kirana akayi domin nayi mata addu'a, kuka yaci karfina sosai har bansan abunda nake ba.

Sai riko mutanen da suka dauki gawar neela nake ina kuka wai ko zasuji tausayina su fasa tafiya da ita, amma sai aka sami waɗan da suka fini karfi suma suka rikeni har aka fita da gawar cikin gida.

Durkushe wa nayi ina kuka sosai, duk da zamana 'yar fari a wurin mahaifiyata bai hanata rarrashina a agaban mutane ba.

Sai da akayi kwanaki biyar da rasuwar neela sannan kowa ya watse a gidan, mahaifina da mahaifiyata sunyi duk yanda zasuyi akan na dawo gida muci gaba da zaman mu tunda neela bata nan yanzu, nikuma nace bazan iya ba, ni su barni a nan zan yi zamana.

Da dai suka dage akan sai mun tafi sai na saka kuka, hilwah kuwa yana ganin haka yace su tafi zai maidani da hannunsa.

ko yaushe mamaki na bai wuce na yanda ya manta da 'yar sa ta cikinsa ba.

Ina tsoro ace wani mummunan abu ya faru da ita, kuma bana jin dadin ganin yanda hilwah ke nuna halin ko in kula akan lamarin nan.

Ba yanda iyayena suka iya tunda hilwah yayi magana, haka suka hada kayansu suka tafi ba tare dani ba.

Ni kadai na kwana a dakinmu yau, sakamakon duk bakin da nake kwana da su da sukazo gaisuwa sun tafi.

Wani abun ban tsoro da mamaki shine koda na tashi na tarar da fairozha a gefena tana kwanciyar ta hankali kwance.

Cikin matukar tsoro da shakku na ja baya daga kusa da ita, a hankali na sauka daga kan gadon na dawo gefen ta, sai da nayi shawara da zuciyata kafin na fara ta da ita ina kiran sunanta.

"Fairozha ki tashi, ina kika shiga? Meyake faruwa da ke ne, kuma yaushe kika shigo gidan nan? Fairozha kin san neela ta rasu kuwa, neela ta tafi ta barmu fairozha?" Na faɗa kuka na kufcemin.

Miqewa tayi zaune tana yamutsa fuska da alama ma baccin dadi yake mata "dayammah,,,,,,,,,,kikace neela ta rasu kho? Hmmmm nasan da rasuwar dayammah! da ma baki wahalar da bakinka wajen gayamin wannan ba" cewar fairozha.

"Amma kinsan da mutuwar fairozha kika bari har aka fita da gawarta gidan nan baki ganta ganin karshe ba, dan Allah me ya faru dake kika koma haka fairozha?"

Maimakon tayi magana sai kawai naga tayi murmushi sosai har haƙoranta suka bayyana, sake juyar da murmushin tayi izuwa kuka, nan ta cusa kanta tsakankanin cinyoyinta ta fara kuka kamar ranta zai fita.

Banyi yunkurin hanata ba sai ma qara ci gaba nayi da kukan nawa, sai da mukayi mai isarmu kafin fairozha ta fita daga dakin.

Ni kuma na shiga toilet din dakin namu nayi alwala na fito na tayarda sallah ta, fitarta dakin bansan ya sukayi da hilwah ba domin na tabbatar wurin sa taje.

Bata sanar dani inda taje ba haka hilwah bai sanardani ba, kuma bansan abunda ta gayamasa ba dayasa banji ya taso da maganar ba.

Sati biyu tsakani gidan ya dawo kamar bashi ba, komai na gidan ya sauya abubuwa a wurin fairozha kam sai abunda ya k'aru, zata iya wata daya, biyu........ bata gida.

Sosai hilwah ke kula dani da karatuna, kuma yana kula da kasuwancinsa, hatta su Hamraz da maharaz dake denmark yana kula dasu iya gwargwadon iyawarsa.

Amma duk wannan da ake ko da wasa banji yana ambatar fairozha ba, sau ba adadi idan nayi nufin yimasa maganar ta sai naji kamar an dauremin harshe duk sai naji na kasa fad'in komai a kanta kamar aikin asiri ko tsafi, ni hankalina ma yafi karkata da haka.

Kamar da wasa kuma sai gashi muna lissafa ranakun da suka ragewa su maharaz da hamraz a chan kasar denmark.

kwanaki sai zuwa suke suna shud'ewa har muka cimma ranar da aka diba musu zasu dawo Nigeria.

Da misalin ƙarfe goma sha biyu na rana jirgin su ya iso, a lokacin kuma na gama shirya komai na gidan nan.

Tsawon shekaru hud'u ne da tafiyar su, kuma idan za'a auna yayi daidai da lokacin da neela ta rasu kenan.

Kunga kenan basu san da mutuwar ba, na gyara komai na gidan tsafff, kuma na girka musu abinci har kuma sashensu duk na gyara dah ma can ban cika barin shi da datti ba ko dan gudun irin ranar nan.

Ina zaune tsakar gidan nikadai ina jiran dawowarsu naji an kwala sallama da karfi.

Fuskata dauke da walwala na fita da dan saurina domin na tarbesu, maharaz kawai ya tsaya shi kuma hamraz muna gaisawa kadan ya wuce ciki yana kiran sunan neela cikin d'aukin ganinta.

Jin haka ya saka idanuna suka ciko da kwallah har ta zubo, da sauri maharaz ya iso gareni tare da rike kafaduna yana jijjigani;

"Kanwata Lafiya? Meya sameki ko dai bakiji dadin ganinmu ba ne kike kuka?"

Jijjiga masa kai nayi alamar ba abunda yake nufi bane, domin a yanda nakeji kukan yanaso ya ci karfina.

Yana shirin sake tambayata sai ga hilwah ya shigo gidan,

"Maharaz meya faru ne?"

"Wallahi hilwah bansani ba nima na shigo ne yanzun nan tazo ta tarbemu, sai kuma naga ta fashe da kuka haka kawai shine nake tambayarta ko lafiya?"

Juyawa hilwa yayi gareni ya fara tambaya ta abunda ke faruwa, nikuma bansan yanda zan yi masa bayani ba domin ga dukkan alamu ma bai sanar da su mutuwar ba tunda naga haka daga garesu.

"Muje ciki maharaz" hilwah ya fada yana nuna masa kofa alamar mu wuce.

Shigewa mukayi har a lokacin maharaz bai saki hannun na ba, kuma bai daina tambayar abunda ya sameni ba.

Gab da zamu shiga parloun hilwah ne muka ci karo da hamraz yana fitowa.

"Hilwah neela bata san mun dawo bane naji gidan shiru ko sun fita ne?"

"Muje ciki hamraz" cewar hilwah damuwa shimfid'e a fuskar sa

Shiga sukayi gaba ɗayansu, hilwah bai bawa kowa damar magana ba har sai da sukayi wanka sukaci abinci sannan suka dawo parloun suka zauna.

Bai 'boye musu komai ba na duk abunda ya faru game da mutuwar mahaifiyar su, sunyi kuka sosai kamar ransu zai fita domin shi hamraz kusan zaucewa ma yayi.

sake tambayar sa fairozha sukayi, sai ya shaida musu cewa tana nan cikin koshin lafiya, kuma itama zai sanar dasu labarin ta nan gaba.

Basu kawo komai ba, domin suna tunanin kamar tana hannun wasu daga cikin danginsu ne, duba da tayi rashin mahaifiya.


Haka mukaci gaba da zama a gidan cikin kwanciyar hankali, shakuwa mai karfi ta shiga tsakanin mu da maharaz har kuma ta juya ta zama soyayya, mun fahimci junanmu sosai inda yaje da kansa ya sanarwa da hilwah abunda ke zuciyoyin mu, hilwah yaji dadin zancen nan sosai babu 'bata Lokaci yaje ya sami iyayena ya gayamusu, suma sunyi farin ciki matuqa. inda aka umurci hamraz daya nemo matar aure ayi aurenmu lokaci daya dashi, amma ya nuna cewa shi bai tashi yin aure ba akwai abubuwa da dama a gaban sa da yakeso ya kammala.

Ba'a tilasta masa ba, kuma babu wani 'bata Lokaci akayi bikin mu da maharaz aka gama.

Sashen mahaifiyar sa neela mai rasuwa aka gyaramin na tare, kuma sashen yana kusa da na hilwah sosai, kusan ma duk gini daya ne kofofi ne kawai a rarrabe.

Hilwa ma Ya so ya tashi ya koma wani sashen amma maharaz yace masa idan har ya tashi saboda mu, to muma zamu tashi mu bar wurin ba koma tunda ya ki yarda ya zauna a kusa damu.

Da kyar dai muka samu yayi zamansa a sashen. Bayan wata shida da aurenmu, abubuwa sun chanja sosai yanda ba'a misali.

Rayuwa ta tsanan ta mana sosai, sai mutuwar ban al'ajabi ake a cikin danginmu yau idan kaji an dauki wannan, gobe sai kaji ta wancan mun rasa wace irin annoba ce ta fado mana.

Gashi yau mun wayi gari da 'batar hamraz , dashi muka kwanta bacci, amma gashi mun wayi gari an nemeshi an rasa.

Hilwa kuma tsawon sati shida kenan yana fama da jinya, anje asibiti anyi magani har an gaji ko hagu babu ballantana dama.

Wani babban abokin kasuwancin sa da ake kira WAASIBUDDEN KABEEL shi yake jinyarsa, shikuma maharaz yana can yana fama da neman d'an uwansa gidan television da na Radio.

Ina zaune a parlour abun duniya duk ya isheni na jiyo murya daga can dakin hilwah yana kirana cikin muryarsa irin ta majinyata.

Da azama na mike na shigo dakin da sallama a bakina, mijina maharaz na gani zaune a gefensa ya zabga tagumi da alama bai ma san zuwana wurin ba.

Abokin hilwah waasibudden ne ya tsayarda tunaninsa ta hanyar kiran sunan sa.

"Maharaz"

"Na'am Abba"

"Dayammah kho" abokin hilwah waasibudden ya fada yana tsureni da ido.

"Eh,,,eh" na fada murya na rawa.

"Kunsan dalilin da yasa mahaifinku ya taraku anan"

"Shi muke so sani Abba"

"Yawwa, kunga waɗan nan takardu" ya fada yana nuna wasu takardu dake ajiye a gefe daya.

'Daga kai mukayi alamar mun gani. Yaci gaba da fadin "ku sani na kiraku ne dan ku zama shaida,,,,,, wadan nan takardun sune kadarar mahaifinku da dukiyarsa gaba d'aya.
duk wasu kamfanoni nashi da masana'antunsa da kuka sani da wanda baku sani ba akwai su a wurin nan, kuma ya bani sune amana na ci gaba da juya masa su har zuwa lokacin da 'ya'yansa zaku buqaci komai ya dawo hannunsu. Kuma Ni waasibudden kabeel ina rantsuwa da girman Allah zan rike alƙawari, bazan yarda naci hakkinku ba koda kwayar zarra wannan alqawarin tsakanina ne da Allah, da kuma ku da zaku tsaya shaidata a ranar gobe kiyama idan naci amarku" abokin hilwah waasibudden ya fadi haka idanunsa na tsiyayo da ruwan hawaye.

Ba wanda bai zubarda hawaye ba a wurin hatta shi hilwah dake halin jinya sai an kwantar a tayar.

"Maharaz nasan kana cikin rudani da tashin hankali yanzu ganin yanda matsala ta taru tayi maka yawa,
ga mahaifinka kwance cikin matsananciyar jinya, ga kuma dan uwanka da aka nema aka rasa, nayi tafiya mai nisa daga barno zuwa nan calaba, kuma nasan baka sanni ba, koh da ka sanni nasan ka manta dani tsawon shekarun da ku ka d'auka bakwa nan bakasan inda nake rayuwa ba.
saboda haka gobe ka shirya muje can na gabatar da kai ga iyalaina da kuma nauyin ku dake kaina, dan Allah karka ce baza je ba domin jinkirin mu a wannan lokacin shine babban tashin hankalinmu. Da kasan abinda ke faruwa bazakaso mu kara kwana ɗaya ba tare da munje barno ba.
Amma ka ci gaba da addu'a kaji, Allah ya kaimu gobe lafiya"

Daga haka ya sallamemu muka tafi, rayukan mu duk ba dadi kowa da abunda ya dameshi, washe gari tun da sassafe abokin hilwah da mijina maharaz suka d'au hanyar zuwa barno, nayi kuka tuburan ji nake kamar bazan sake ganinsu ba, ko su su mutu kokuma Ni mutu.

Komawa nayi sashenmu zuciya ta na min zafi, zama nayi na rasa makama da abun yi, na rasa wane tununi zanyi da haka har bacci ya ɗaukeni.......................



A can cikin ɗakin hilwah kuma kwance yake kamar yanda ya saba kullum sai kiran sunayen Allah yake a zuciyarsa domin baya magana a fili tun lokacin da ciwon ya sameshi. Yana cikin hakane yaji wani sauti mai qarfi ya ratso cikin dakin, sekonni biyar da faruwar haka yaji dirar wani abu mai nauyi ta gefensa.

Baiyi niyar ya juya ba haka kawai yaji zuciyarsa na matsa masa akan sai ya juya, juyawar da zaiyi ne idanunsa suka sauka akanta.

Cikin matukar tashin hankali yake kokarin yin magana duk da yasan abune mai matukar wahala taji abunda zai faɗa amma yayi karfin halin kiran sunanta.

"Fairozha ina kika shiga tsawon wannan shekaru?" Bai yi zaton taji abunda ya fad'a ba, shi kansa masani ne akan baya magana tsawon watanni domin ko yayi ba jinsa ake ba shiyasa ya daina yi gaba ɗaya, ko yanzu bai sani ba ko fairozha taji abunda ya ke cewa.

Da sassarfa ta fara tafiya har ta zo inda yake, zama tayi kusa dashi ba tare da ta kalli inda yake ba.

"Hilwah ka yafemin da abunda zan fada maka, nasan wa'adin ka ya kusa.
yanzu hakan nan shi yasa nazo in sanarda kai abunda ke faruwa wanda nasan ba ku san dashi ba"

sai da ta ɗan sauke ajiyar zuciya a hankali kafin ta d'ago kai ta kalleshi tarrr tace "hilwah na shiga kungiyar asiri!, kuma Ni na kashe neela, itace sadaukar wa ta ta fari a kungiya, kuma Sannan duk mace-macen da ake a cikin danginmu ni nake bada su, sannan kuma ni na 'batarda hamraz saboda ba yanzu bane lokacin da zamuyi amfani dashi ba, hilwah kasani wannan ciwon da kake nice silar sa amma lafiya Ƙalau kake gabanin wannan" fairozha ta fada babu tsoron komai, kuma babu wata alama ta nadama a tattare da ita.

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, fairo,,,,,,zha dan,,,, Allah me kika ra,,,sa da zaki,,,,,,,shi,,,gga kungiyar asiri" ya fada kalmomin na neman kufcemasa.


Murmushi mai sauti tayi wanda ya bayyanar da duk hakoranta tace "hilwah sai yanzu kake tambayar me na rasa dha can da kake daukar 'ya'yan ka maza kake kaisu kasar waje suyi karatu ka taba tambaya ta abunda na rasa? Sai yanzu dana daukesu ne kake tambaya ta"

Fairozha dan Allah me mukayi miki a wannan duniyar da muka cancanci irin wannan sakayyar, fairozha mu muka haifeki fa karki manta wallahi hakkin mu na iyaye a wurinki da kuma hakkin mutanen da kika kashe basu ji ba basu gani wallahi bazai barki ba"

"Wallahi hilwah ko a yanzu na mutu banada takaici ko haushin mutuwata, babbar fansa ta akanku ne kuma na riga na dauka hmmmm amma Ni kaina nasan lokacin mutuwata bai yi ba sai na karasa aikina, kasan menene aikina?"

Bata jira cewar sa ba taci gaba da faɗin, d'an ka maharaz da ka aika da babban amininka waasibudden suje barno sun isa lafiya hanyarsu ta zuwa, amma ina maka rantsuwa da gunkin tsafinmu abun dogaronmu d'an ka maharaz bazai dawo garin calaba da rayuwa ba, sannan shima waasib da ya shiga gonata wallahi bazai girbeta da dad'i ba........."

Tun kafin kafin ta kai ga karasa fadin abunda zata fad'a wani mugun tari ya turnike hilwah, har idanunsa na rufewa suna budewa, cikin matukar karfin hali yayi kalmar shahada shikenan yace ga duniyarna.

"Dama nasan ko ciwon nan bai kasheka ba maganganun da na gayamaka zasu karasaka, ki shigo ki shafe gawarsa domin babu wannan hilwah sai dai wani" fairozha ta fada tana mayarda hankalin ta ga kofar shigowa dakin.

Wani irin rawa da mazari jikina ya fara yi domin banyi zaton ta san dani a wurin ba, tun lokacin da ta shigo dakin ina la'be ina sauraren ta duk a zatona bata ganina.

Wata tsawa ta qara dakamin har sai da 'ya'yan cikina suka yamutsa da gudu na shigo dakin ba shiri, babban abinda yabani mamaki shine babu fairozha babu alamar ta a cikin dakin iya gawar hilwah ce kawai.

Cikin kuka na isa wajen gawar sai dai tsoro ya hanani aikata komai, naji tsoro sosai rayuwa kenan wai hilwah ne kwance matsayin gawa innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un.

Na dade akan gawarsa ina kuka mara sauti nayi har sai da nayi mai isata, wayata na laluba tare da dannawa maharaz kira, saidai tana nunamin inda yake ba network, nayi iya kokarina inga nasamu wayarsa amma abu d'aya ake fad'a tun dazu.

Mutanen unguwar mu suna gudun mu, tsoron mu sukeji gani suke kamar akwai Mayu a cikin mu sakamakon yawan mace-macen da akeyi a cikin danginmu, fairozha ta ja an shafa mana bakin fenti, ta dalilinta ne komai yake faruwa har haka.

Hankalina yayi mugun tashi, bansan yanda zanyi da gawar hilwah ba. nasan abu ne mawuyaci su yarda da suturta hilwah su kai shi makwancinsa.

Mikewa nayi da sauri na fita gidan, duk inda nasan akwai majalisa da ake zama a unguwar tamu sai da naje na rokesu, wasunsu ma ba bari suke in karaso inda suke ba, daga sun ganni sai kaga suna gudu.

Inda naje na karshe kuwa harda jifana sukayi da duwatsu, kuka mai kara na fashe

46 / 61