Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
sauri leeya ta ɗago kai zatayi magana sai kawai ta fasa maganar batace komai ba ta mayarda kanta ƙasa.
"Leeya bakiji justice na Magana dakeba"
Ƙara ɗago kai tayi karo nabiyu domin shafff ta manta bata amsa masa ba.
"Lahh papu Dan Allah kayi hakuri wallahi a zatonda nake ma na amsa maka, bara ma naje yanzun na kaimata ai".
"Ah ah ki bari ki gama kawai batajin yunwa ai, baki ji abunda tacewa mum ɗinku ba"
Daga nan ba wanda ya ƙara faɗar komai har suka kammala cin abinci. leeya ce kaɗai zaune a daining area taci abinci sosai ta ƙoshi, sai kuma ta haɗa wa khulud nata Kamar yanda papu ya umurce ta tayi.
tana gama haɗawa ta tashi taje ta kaimata.
Tura kofar ɗakin tayi bakinta ɗauke da sallama, gabanta na duka uku-uku, domin haka kawai takejin tsoron khulud sakamakon abunda tayi mata yanzu.
Ba kowa a ɗakin, ɗan ƙaramin table dake gaban fabric-bed sofa ta ajiye babban faranti da ta sanyo mata abincin,
Exercise book ɗinda tagani kan bed ta nufa tare da miƙa hannu ta ɗaukeshi, ta fara buɗewa
"Allah sarki khulud, ta faɗi a assignment ɗin nan, da ace ina nan lokacin da tayi shi dana taimakamata dan naga kamar bata fahimci topic ɗin nan ba"
Duk da ƙarar buɗe ƙofar da taji hankalinta bai kawo ta daga kanta taga waye ba domin gaba ɗaya hankalin ta nakan littafin khulud na mathematics da take buɗewa.
Wani irin wawan fizga khulud tayiwa littafin ta da ke hannun leeya
"what are you doing?"
"Nothing"
Ɗan waro ido khulud tayi domin batayi tunanin leeya najin turanci ba, amma sai ta ɓoye mamakin ta dan kar leeya ta fahimta. Cikin tsiwa da bala'i irin nata ta fara magana,
"What do you mean by nothing, what are you staring at my book? By the way, who gained the you access in to this room without knocking?"
"Papu ne yace na kawo miki abincin ki"
"Then you bounty yourself access?, nagayamiki kifita harakata a gidan nan amma kin ƙi kho, ki tashi ki ɗauki komatsan da kika shigo dasu kifitar min ɗaki"
"Allah ya baki hakuri" shi kawai leeya ta iya furtawa sannan ta ɗauki farantin da ta shigo dashi ta fito, sosai taji ba daɗi abunda khulud ta yi mata amma ta kuɗuri niyar yin hakuri da koma meye.
Leeya na fitowa daga bedroom ɗin khulud ta dawo daining area ta haɗe kaf kayayyakin da suka ɓata ta shiga kitchen ta wanke su fess, kaana ta dawo ta gyara daining ɗin tsafff kamar ba'a ci abinci kanshi ba.
tana gamawa ta koma ɗakin da aka bata shima ta gyarashi, toilet ta shiga ta ɗauro alwalar sallar la'asar tazo ta tada sallah, tana fara sallahn ne sai ga mum ta shigo, bakin gadon ta zauna saida leeya ta kammala sallah sannan tayi addu'a
"mum barka da yamma"
Da murmushi a fuskar mum ta amsa mata
"yawwa barkan ki dai leeya, ya gajiyar aiki kuma? Naga duk aikinda kikayi, gaskiya kinyi ƙoƙari. Allah yayi miki albarka"
"Ameeen ya rabbi mum Nagode sosai"
"Idan kin gama abunda kike kiyi wanka kizo muje shopping ki zaɓi Kayan da kikeso na sakawa"
"Tau in sha Allah idan nayi wankan zaki ganni mum Nagode sosai, Allah ya saka muku da alƙairi"
" Ameen amma ki daina yimana Godiya haka mana ki ɗaukemu matsayin iyayen ki, ba komai zamuyi miki kina yimana Godiya ba kinji"
"Uhmm tau mum zan gwada na ga ko zan iya dainawa kamar yanda kikeso"
"Ki tashi kije kiyi wankan ina nan ina jiranki bara naje na gayawa khulud itama ta shirya"
A ɗan razane leeya ta ƙara kallon mum jin da khulud za'a fita, sai takeji kamar tace bazata iya zuwa ba amma idan tayi haka kamar ta watsa musu kasa a ido.
"Akwai matsala ne? Naga yanayin ki ya changer ko bakyajin daɗi ne"
"Ah ah mum ba komai kawai na tuna da iyayena ne"
"Allah sarki, kiyi hakuri kinji ki dinga yi musu addu'a kinji ɗiyata"
"In sha Allah mum, Bama su kaɗai ba har da ku"
"Madallah dake ɗiyar albarka, Allah ya karɓa"
"Ameen mum"
Daga haka mum ta tashi tabar bedroom ɗin na leeya.
********
Khulud kuwa tunda leeya tabar bedroom ɗin nata ta fito main parlour ɗin gidan inda ba sahun mutane ko hayani ya,
ita kaɗai a katafaren parlourn wanda ya gaji da haɗuwa, sai kai da komowa take tana kumbura, sai dunkule hannu take tana kaiwa iska naushi kamar ta fashe takejin kanta.
kan royal chair two sitters taje ta zauna tana tare da jingina kanta tana huci kamar wani bakin kumurci.
"Mamana lafiya meya faru" kamar daga sama taji muryar papu da shigowar sa kenan parlourn yanzu.
Tanajin papu ne kuwa ta fashe da kuka tana faɗin
" pa, Ni ka kyaleni kaji, ba ka sami wata ƴar ba, ka manta Dani, Wai har ni za'a aikowa wannan ƙazamar yarinyar ta kawomin abinci na da zanci, ai basai kun yimin haka ba idan kun gaji dani ku gayamin kawai na koma can kaduna wajen maman twins ai ita tana sona kuma su FANNAH DA MAYA ma suna sona kuma UNCLE-JIF ma yana sona sai ku gayamin in koma wajen masoyana tunda ku kun sami wata ƴar nima naje na sami wasu iyayen"
"Haba mamana meye na kuka kuma, dan Allah kiyi shiru ki min bayani abunda ke faruwa waya taɓamin ke, ummm mamana wanene gayamin kinji shalelen papu"
"Pa, ba ku bane kuka kawo waccan talakar yarinyar ƙazama da ita, mai tsince-tsince a titi wai ita ce zaku kawo gidan nan matsayin ƴar gidan nan, kuma ta amsa sunan gidan, haba pa wannan ba adalci bane wallahi nidai gaskiya saidai ku zaɓa ko ni ko ita"
"What!?, ko, ke ko ita fa kikace mamana wane kare da buzun kure, ai ko kusa baza'a haɗa ba kiyi haƙuri kawai zamane na ɗan lokaci kafin a gano danginta, muna nan muna bincike yanzu haka ana gane dangin nata zamu miƙata garesu, shikenan matsalarki ta ƙare?"
"Ehh pa, sai kuma wacce zatazo daga baya"
"Ah ah my kiddo ai bama fatar matsalar ta ƙara zuwa"
"Okay"
"Abunda nakeso dake Yanzu Ki tashi kije ki shirya mum ɗinki na jiranki"
"Mum tana jirana a ina? Me zanyimatane pa?"
"Ba komai zaki mata ba shopping zakuje"
"Okay pa, zan shirya yanzu, ina dai fata bata wannan yarinyar zamuje ba kho?"
"Haba dai mamana da ita zakuje mana, Tau ae itace za'a yiwa shopping ɗin kayan sakawa, kinga batada wasu kayan da zatasa"
"God forbid, pa wallahi bazamuje da itaba saidai ta tsaya idan munje muyi mata shopping ɗin tunda kun nace kan sai anyimata"
"Okay ba damuwa mamana indai don wannan ne, ki shirya kuje kawai Bara naje naga mum ɗin taki na gayamata abunda kikace"
"Okay" daga haka ulud bata ƙara cewa komai ba ta juya tabar parlourn, shikuma papu ya hau sama inda mum take.
LEEYA
Tana nan zaune a bedroom ɗin nata tsawon minti goma sha biyar da shirin ta amma bataga mum ta shigo ba.
miƙewa tayi ta fita daga ɗakin, cikin tafiyar ta ta nutsuwa take takawa har ta isa kofar bedroom ɗin mum, tana Isa kofar ta jiyo Muryar papu yana gayawa mum abunda khulud ta faɗa.
daga can cikin ɗakin mum ce tsaye hannun ta riƙe da jaka papu kuma yana zaune
"yanzu don Allah justice haka za'a zubawa wannan yarinyar idanu tana abunda taga dama, yanzu fitar da zamuyi da wannan yarinyar Leeyana ne siyamata kayan sawa shine khulud zata ce baza'a fita da ita ba? kai kuma ka yarda ka biyemata to gaskiya bazai yiwu ba dole sai an tafi da leeyana ta zaɓi kalar kayan da take so gaskiya"
A tsawace papu ya amsa mata maganar da;
"Bazaiyu ba fanaya, kije da mamana kawai ai itama ta iya zaɓen kayan, amma bazaiyu khulud ta faɗi magana a ketare ta ba, kin san da bana son matsala, bana son matsala, musamman ma idan ga mamana zata faru......✍🏼
BAYAN WUYA....
By RUMANA M DIGGI
EP.11
________Dafe kai mum tayi tanajin kwalla na taruwa a idanun ta.
"shikenan justice kuje da kaida ita ɗin kuyi shopping ni bazan jeba kuma leeya ma bazataje ba ku barmu gidan"
Hannun mum papu ya riƙo ganin kamar ranta ya ɓaci har tana hawaye.
"hajjaju fushi kikayi?"
"Menene abun fushi justice? ba fushi nayiba naga bai kamata abar leeya ita kaɗai a gidan nan ba tunda itama ƴa ce kamar yanda mamana take ƴa, idan har baza'a fita a bar mamana ita kaɗai a gidan nan ba, to itama leeya bai kamata a fita a barta ita kaɗai ba tunda itama ƴace".
Jikin papu yayi sanyi sosai da jin abunda mum ta faɗi shima kanshi yasan gaskiya ce mum ta faɗa to amma ya zaiyi tunda ƴar gaban goshi bata yarda ba "yanzu menene abunyi hajiyata"
Faɗin papu yana riƙo hannun mum da murmushi mai sanyi domin kuwa yasan ranta aɓace yake kawai bata nuna bane.
"Hmmm, wannan kam ai sai aje a tambayi mai gidan kho"
"Wacece kuma mai gidan?"
"Ulud mana justice!, naga yanzu itace da gidan ai".
"Hajiyata kenan, meya kawo wannan maganar kuma, ai Ulud ɗin kanta da bazarki take takawa, kiyi haƙuri kinji, nasan ranki ɓace yake a ya.nzu, amma kiyi hakuri ki gayamin abunda ya kamata yanzu"
"Toh tunda abun ya zama haka a fasa fitar kawai"
"A fasa fita kuma!?"
"Ehh mana"
"Haba hajiya idan aka fasa fitar ai leeya aka tauye saboda da abun wani gwara ace naka"
"Hakane amma kasan idan akace aje da khulud kawai ita leeya bazata ji daɗi ba, koda bata nuna mana ba nasan zataji abun a ranta"
"Tau menene abun yi yanzu shi nake tambayar ki"
"Akira leeya kawai tazo ta zaɓa sai ayi online shopping kho?, kaga shikenan ba wata rigima".
"Nice, gaskiya wannan shawarar tayi yanzu abunda za'a yi kije ki kira leeya tazo ta zaɓa da kanta kho".
Leeya da tunda taji papu ya dakawa mum tsawa ta bar wajen a tsorace ta koma bedroom ɗin ta tanata sharɓar kuka, domin tasan saboda itane papu yayiwa mum tsawa, alhali koda tazo gidan ba haka ta tararda suba.
Ƙarar buɗe kofar da taji ne yasa ta ɗago kanta, mayafin ta gaba ɗaya yayi sharkaf da hawaye
"subhanallah!!, leeyana, Lafiya? Meyafaru ne kike kuka?"
"Mum kaina ke min ciwo sosai bazan iya fita shopping ba, kuje da khulud kawai sai ta zafamin kayan"
Tada ita mum tayi tana jeramata sann
"ki tashi muje asibiti kinji, bara na ɗauko carkey na kaiki asibitin kinji"
"No mum, kiban magani kawai nasha, bazan iya fitar yanzu bane, amma kiban magani idan nasha banji sauƙi ba daga baya sai muje asibitin"
"Da hanzari mum ta bar bedroom ɗin, ta koma nata sashen ta ɗauko mata magungunan zazzaɓi, ta kawo mata
"karɓi kisha maganin idan kinsha sai ki kwanta ki sami relief kinji"
"Okay mum Nagode sosai Allah ya saka miki da alƙairi"
"Ameen ɗiyata, wannan ba komai bane Allah ya baki lapiya, idan kinji sauƙi zuwa yamma sai ki zo ki duba kayan da kikeso ayi online shopping ba sai mun fita ba kho"
"Tau mum ba damuwa, ai bama saina zaɓa kayan ba kawai ki dubamin waɗanda suka yimiki duk zaɓinda kikaimin shine nawa"
"Yawwa ƴar albarka, Allah ya baki lafiya"
"Ameen mum".
Bayan fitar mum ɗakin, leeya ta sauke nannauyan ajiyar zuciya domin kuwa ba wani zazzaɓi da takeji, tayi hakan ne saboda kar mum tagane taji maganganun su da papu domin kuwa mum zatayi tunanin kamar laɓe takeyi musu.
Mum kuwa tana fita ɗakin ta je ta sanarwa da papu abunda ke faruwa, sosai papu ya tausayawa leeya musamman ma da yaji mum ta faɗamasa halin da ta tarar da ita
"Hajia fanaya kina ganin kuwa haka da akayi yayi? Ya kamata abar mai ciwo gida kuwa, ki tashi a kaita asibiti kawai, ko kuma a kira Dr. jif yazo ya dubata a gida"
"Bantari numfashinka ba justice, amma ina gani abari kawai zuwa yamman idan mukaga ba sauƙi sai akira Dr. Jif ko a akaita hospital gaba ɗaya"
"Okay ba laifi Allah ya sauwaƙe, Ni zan fita office domin akwai wasu files da nakeso na cike, Turab ya sanardani lokacin dawowarsa, domin lokacin da naje visiting ɗinshi ba'a saka musu date ɗinda zasu dawo ba, kuma in sha Allah yau result ɗinsu zai fito ki sakashi a addu'a don Allah"
"In Allah yaso kuwa zan cigaba da yimasa addu'a domin kullum yana cikin addu'a ta saidai na ƙara masa"
"Tau Allah ya karɓa"
"Ameen"
Iya shi kaɗai mum ta faɗa bata ƙara cewa komai ba, har papu yafita ɗakin.
"Natafi" papu ya faɗa yana fita daga ɗakin.
"Allah ya kai lafiya, ya tsare justice"
"Ameen ya hayyu ya qayyum"
KHULUD
Tunda papu ya gaya mata saƙon mum ta koma bedroom ɗin ta tayi wanka, kaana ta shirya tsaff cikin ƙananan kaya riga da skirt, sai kuma band kalar skirt ɗinda ta saka, tayi parking gashinta duk da ba yawa ne dashi ba amma tana bashi kulawa sosai.
zaune take a parlourn ƙasa gaba ɗaya, ta ɗan jaaa lokaci a wurin ba wanda yako gifta parlourn, har kusan yamma.
Sai da ta gaji da zama ta tashi ta koma ɗakin ta, kuma batayi tunanin zuwa ta kira mum ɗakinta ba ko kuma ta duba idan mum tana lafiya, bata yi tunanin yin haka ba domin tana ganin kamar ba ita ke buqatar fitar ba.
tana zaune sai mamaki take abunda ya hana mum fitowa har tayi tunanin mum tayi tafiyarta ne shiyasa bata ganta ba.
Zumbur ta miƙe ta nufi part ɗin mum ta duba kar tunanin ta ya zama gaskiya, wato mum ta tafi da leeya ta barta.
Ita kuwa leeya baccinta ta kwasa saida ta ƙoshi ta tashi lokacin da aka kira sallar la'asar, banɗaki ta shiga ta ɗauro alwala Sannan ta dawo bedroom ɗin ta shimfiɗa sallahya kaana ta kabbarta sallahr ta.
Cikin nutsuwa tayi sallarta har ta gama tayi addu'a, bayan ta kammala ta tashi ta ɗauko tsintsiya da parker ta share bedroom ɗin, sannan ta gyara gado tayi mopping ta saka air freshener da kuma turaren tsintsiya. Part ɗin gaba ɗaya ya game da ƙamshin ɗakin ta.
Banɗaki ta shiga tayi wanka, bayan ta gama wankan ne ta ɗauro mayafin ta kamar dai kullum, sannan sai towel mai ɗan girma da yakai har ƙaurinta ta fito.
Tana buɗe ƙofar ban ɗakin kuwa taga mum zaune kan fabric sofa sai murmushi take.
"Mum ina wuni"
"Lafiya ƙalau leeyana, ya ƙarfin jikin?"
"Alhmdullillah mum, jiki kam yayi sauƙi fa nikam ae na warke ma zance"
Da murmushi a fuskar mum tace;
"ai kuwa naga sauƙin, tunda gashi na ga kin gyara ɗakin nan tsaf kamar ɗakin amarya"
Murmushi mai sauti leeya tayi itama tace;
"mum ai ban so kizo yanzu ba naɗauka ma kina can kina hutawa ne kawai da saina gyara ko'ina na gidan nan sannan in shiga kitchen inyi mana abincin dare ni kaɗai kuma bana so kowa ya tayani"
Idanu mum ta zaro waje cikin alamun mamakin abunda leeya tace
"duk wannan aikin keka ɗai, ai ba hauka akeyi ba da zakiyi haka inahhh"
"To bara kigani mum idan banyi ba yanzu ma tashi zanyi"
Mum zatayi magana leeya ta tari numfashinta da faɗin
"dan Allah mum karkice bazan yiba Wallahi inason aiki sosai, na riga na saba ne idan banyi ba bana jin daɗin wallahi"
Fuskar mum ɗauke da damuwa tace
"Bawai na hanaki aikin bane ki bari idan kika ji sauki sosai jikin ki ya warware sannan sai kiyi duk aikinda kike so ba wanda zai hanaki, amma ki duba kiga yanzu fa bakida lafiya"
Leeya na shirin magana sukaji ƙarar buɗe kofa da ƙarfi, waiwayawa sukayi gaba ɗayansu kafin mum tace
"mamanah menene haka zaki shigowa mutane bako sallama kuma ki banko ƙofa haka kamar mai shirin dambe"
"Mum kardai kice faɗa kike min a gaban wannan talakar yarinyar ƴar talakawa, ba komai na shigo yi wannan ƙazamin ɗakin ba, naje part ɗinki ne ban ganki ba nayi tunanin da ita akaje shopping ba dani ba, bayan naje ban ganki bane na dawo part ɗin nan anan naji motsinku shine dalilin shigowar danayi ɗakin nan, dabadan shiba bansan abunda zai kawoni nan ba ehee"
Khulud na gama faɗin haka ta sake fizgar kofar ɗakin tayi ficewarta, second ɗaya, biyu, uku ba wanda yace komai tsakanin mum da leeya sai ƙofar suka kafe da idanu kamar masu neman wani abu
"leeyana!"
"Na'am mum".
"Dan Allah leeya kiyi haƙuri da abunda mamana take miki wallahi ƙuruciya ke cinta da kuma sangarta ta da papunku yayi, dan Allah ki ɗinga ƙarfafa zuciyar ki akan komai da khulud zata miki, wata rana ba wannan maganar za'ayi ba, kawai hakuri ne da wuya amma da kinyi zakici ribarsa in sha Allah, kinga kece babba akanta, nasan kin girmemata wannan bata wuce ƙanwarki da aka kashe ba, dan Allah ki dinga hakuri kinji ƴar kirki"
"Lahh wallahi mum ba komai aini bana ɗaukar wannan komai, wallahi ban taɓa riƙeta a rai ba, don Allah ki daina ban haƙuri ai sai inji kunya wallahi"
Leeya ta faɗi maganar da fara'ah a fuskar ta.
Sosai mum taji daɗin jin hakan daga leeya
"Allah ya miki albarka leeya, ina ma ace khulud ma haka halayenta suke kinga sai kuyi zamanku lafiya, ba wani tashin hankali. Ni ina ganin ba wani abu da zai dameni a faɗin rayuwar nan, sai idan na tuna da ƴan uwana"
"Ƴan uwanki kuma mum!?, meyafaru dasu!?".
"Hmmm Kamar yanda ƴan bindiga sukazo suka kashe kowa naki, Nima haka sukazo a Maiduguri amma su mutanen da sukazo ƴan boko haram ne suka kashe mahaifiyata da kuma ƙanina, amma mahaifina da sauran wasu daga cikin dangin mu sun samu sun tsira"
Mum ta ƙarashe maganar kwalla na zubo mata.
A ƙiɗime leeya ta sakko daga kan bed tazo kan sofa inda mum take, bata masan lokacin da ta fara goge mata hawayenta ba.
murmushi mai cike da ma'anoni mum tayi sannan ta buɗi baki tace
"hawaye nake kho?"
A duk lokacinda na kwatanta bada labarin nan to nasan bazan ƙare badashi ba tare da nayi hawayen ba, saboda abun yana cimin rai, wallahi yana cikin raina"
"Mum Dan Allah kiyi hakuri kinji, yanzu kika ƙare ban hakurin naga hawayenki sai ƙaruwa suke mai makon ace sun ragu, amma ƙaruwa naga sunayi dan Allah kiyi hakuri ki daina kukan nan, Allah ya saka mana ga azzaluman mutane wallahi ko bamuyi magana ba ma sai Allah ya saka mana, saboda haka ne nake roƙonki ki fitarda komai a ranki"
"In sha Allah ɗiyata,