Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
turamiki saƙo baki taɓajin ya takuramiki ba balle ki ɗauki mataki, kuma kina da damarda zaki sauya sim card amma bakiyiba, a duk lokacin da ya turamiki saƙo sai kinyi yunkurin kiran numbern da ya turamiki saƙo da ita amma bakya samu, kuma zaki bibiyi number domin mayar masa da martani, sannan kuma jiya daya turamiki saƙo har ya baki damar yin magana dashi abu ɗaya kika fara tambayar sa waye shi, saboda shine a ranki.
Da baya ranki wani abun zaki tambaya ba wannan ba, sannan kuma jiya kasa bacci kikayi saboda ya baki zaɓi biyu da zaki yi domin jagoranci zuciyar ki, kuma Sannan yanzun nan tunaninsa ya hanaki magana ma balle a je ga batun wani abun daban.
Gayamin duk wadannan alamomi basu baki cewa kina sonsa ba, da bakya sonsa duk wannan zai faru ko kuma idan bakya sonsa zaki barshi ya ci gaba da kutsowa cikin rayuwarki, da bakya sonsa duk wannan bazaki bari ya faruwa ba domin kinsan duk yanda zakiyi ki yakiceshi daga cikin rayuwarki"..................✍🏽
BAYAN WUYA........
By RUMANA M DIGGI
EP.32
_______________khulud ta ƙarashe maganar cike nutsuwa da tunanina.
Leeya kuwa jin abunda khulud ta faɗa yasa ta fara ji kamar da gaske ne ta kamu da soyayyarsa to waye shi?.
"Khulud kinga fa bansan ko waye ba to taya zan yi SOYAYYA da wanda bansaniba"
"Duk da haka ai, idan kin fahimci bayaninsa cewa yayi zaki sani idan lokacin sanin yayi kiyi hakuri ki jinkirta kiga iya abunda zai iya yi"
Haka dai khulud ta dinga ba Leeyana shawarwari da kuma bata haske kan wannan lamarin har takai leeyana ta amince ɗari bisa ɗari ta faɗa soyayyarsa ne, domin kuwa duk wanda yaji bayaninda khulud keyi a wannan lokacin yasan gaskiya take faɗa. Kuma ba yanda zatayi dole ta aminta da ta faɗa soyayya.
"Yanzu abunda za'a yi ki rubuta masa sakon barka da safiya da tattausan lafazi kinji"
"Ni wallahi khulud tsoro nake ji"
"Ki aiwatar da abun da zuciya ɗaya kawai ki fitar da tsoron komai a ranki, rubuta kawai"
"Okay"
Zama tayi dakyau tare da yin guntun tunani kafin ta tsara masa morning text massage.
Cikin mintuna ƙalilan aka mai da mata da reply ɗin saƙon da ta aika kamar yanda tayi nata cikin tattausan lafazi, da kuma godiya mara adadi, domin duk bayan layi ɗaya na saƙon sai ya gode mata.
Khulud kuwa tana ganin haka ta saka shewa da tafi tana faɗin "shikenan ƴar uwata ta faɗa soyayya to Allah yasa kin shiga a Sa'a ta" ta faɗa cikin sigar zolaya.
Pillow ta dauka tare da jefa mata, da gudu khulud ta fita ɗakin tanata dariya.
Bayan sati biyu.
Haka al'amura sukaci gaba da tafiya, khulud da leeya sun haɗa kansu sosai Tamkar ba su ba. Domin a Yanzu kam khulud ta canja halayenta sosai ba wanda zaiyi tunanin khulud ɗin yanzu itace ta baya can farko.
A ɓangaren leeya da masoyinta kuwa soyayyar su tayi ƙarfi sosai har mamaki ma takeji yanda akayi wannan lamarin ya faru farat ɗaya, sosai suke bawa junansu kulawa da muhimmanci tare da tsaftatacciyar soyayya mai ma'ana. Saidai duk wannan a rubutun sakonni kawai ya tsaya bawai fili da fili ba.
A can gefe kuwa tsakanin kulud da idrak sai abunda ya ƙaru a soyayyar da khulud ke yimasa.
Sosai sayyid yake yiwa khulud son ransa kuma ba abunda zata iya yi domin ita ta nema. Shima id ba'a barshi a baya ba wajen nunawa khulud ita ba kowa bace, kuma ko a gaban kowa zasu iya yimata duk abunda suka ga dama. Sosai su raudha da amrah suke damuwa akan wannan, domin kuwa a shawarwarin da zohal ta bata ta gayamata ta faɗawa abokanta ko suma zasu rage faɗan da sukeyi dasu sayyid, amma a duk lokacin da amrah ko raudha suka ga an yiwa khulud wani abu mara daɗi to sai sun mayar da martani ga su sayyid hakan kuma zai janyo wata masifar daban. Cikin ma Sayyid yana ragawa mutuncin da ke tsakanin sa da reemah ne da abunda zai yimusu har ma baza'a iya faɗa ba.
Bangaren turab kuwa ba abunda ya ragu saidai ma abunda ya ƙaru domin ya tsananta musu sosai ga kuma dokokin masu tsauri daya kafa musu, domin kuwa basuda ikon amfani da wayoyin su idan yana gidan ko sunyi da ɓoye ta yanda bazai gani ba.
Yau juma'a 24 ga watan nan kuma hakan yayi daidai da saura sati ɗaya kacal ayi bikin auren ZOHAL KHALIL GIRAH da angonta FAHAD GAHEES WAASIB.
Yaune kuma familyn su mum suka hallara na nesa dana kusa Domin gudanar da taron da sukeyi duk lokacin da za'a yiwa wani ko wata daga familyn aure dama haka Al'adar familyn take.
Sosai mutane suke taruwa domin kuwa Ni abun har mamaki yake bani, Mutanen nan da suke zuwa sun ninka waɗanda suka zo walimar ya turab sau uku, domin a wannan karon har mahaifiyar su papu, da ƴaƴanta mata da suke zaune a garin barno sai da suka zo, haka ma ƴan uwan mum da dama sun zo taron.
Khulud kuwa sai nan-nan take yi da ƴan uwanta musamman ma Sa'aninta da waɗanda suka ɗan girme mata a shekaru kamar dai ni.
Ko ƴan uwanta da sauran iyayenta sunyi farin cikin sauya warta domin a can baya basa zuwa gidan nan idan ba irin haka ta taso ba, shiyasa ko walimar da akayiwa ya-Turab basuyi irin wannan yawan ba saboda kowa yana gudun wulaqanci ne daga khulud.
Zaune muke a parlour inda dangin su mum suketa nishaɗinsu sai ɗaukar photo suke, Ni kuma ina zaune a gefe kusa da su khulud sai fira sukeyi cikin nishaɗi ita da ƴan uwanta su kusan huɗu itace cikon ta biyar sai ni danake zaune kusa dasu.
Daga can gefe kuma wasu mutane ne zaune daban amma duk a cikin su ɗayace ta fara tsufa sosai irin tsufan nan, amma dayake masu kuɗi ne sai tsufan bai wani bayyana yanda za'a fahimci komai da komai.
Wasu matane kusan su uku suma suna kewaye da ita sai fira suke yi ankawomata abubuwan fruit a gabanta sai ɗauka take ɗaɗɗaya tana gutsurawa a hankali, bayanta jingine da wani ƙatoton sofa pillow mai taushin gaske.
Nikuma sai kallonsu nake ina mamakin wace matace wannan domin har mum naga sai bata kulawa take sosai.
Daga can naji muryar matar tana cewa"ke baiwar Allah bakya magana ne kinyi shiru sai kallon mutane kawai" matar ta faɗa Muryar cike da Dattaku.
Murmushi nayi kaɗan wanda nasan bazata gani ba, nayi ne kawai saboda hakan ɗabi'a a tace.
Saina sunkui da kaina ƙasa bance mata komai ba.
"Zo nan" na ƙara jin muryarta tana yimin alama da hannu danazo wurin ta.
Da sauri na miƙe na zo gabanta tare da durkusa har ƙasa nace "barka da yamma anzo Lafiya"
"Ah lafiya ƙalau ya maigidanki"
Ƙara ƙasa dakaina nayi daga can kuma naji muryar khulud cikin muryarta tana dariya tace hajiya babba wannan fa batayi aure ba, sa'ar su meenal ce"
"Aww, ba matar aure bace nikam na ganta da niqab ai nayi tunanin matar aure ce"
"Tohm haji kidaina tunanin haka domin ita ba matar aure bace"
"To ke kuwa shine kikayi shiru cikin sa'an ninki bakya magana kije can ki shiga cikinsu kuyi fira mana"
"Kedai haji rabuda ita batason zama a familyn mu ne tun ɗazu Aneesa da Badar ke yi mata magana tazo ayi fira da ita taƙi har meenal ma tayi magana amma taƙi ta zo tayi magana"
"Khulud naji baki sakani a sahun mutanen da sukace tazo muyi fira ba karta riƙeni a rai tace nikaɗae ce bana so ta zauna cikin familyn mu". Wata kyakkyawar matashiyar yarinya ta faɗa daga cikin ƴanmatan da ke zaune tare da khulud su biyar.
"Haji har Airah ma ta faɗa tace leeya tazo muyi fira" khulud ta faɗa tana ƴar dariyar da ta bayyanar da fararen haƙoranta tare da kallon budurwar da tayi maganar.
Leeya kuwa jin yanda ƴan matan suka yita magana kan tazo cikinsu yasa ta miƙe ta koma wurinsu.
"Yawa ko kefa, yanzu ai zaki fi sakewa kho"
"Hmmm, kedai badar ki barta kawai wallahi surutu ne da ita amma kinga nan tayi shiru kamar ba ita ba"
"Ai irin wannan kana ganin su kasan basuda yawan magana" cewar wata budurwa dake daman leeya.
Haka sukaci gaba da firrarkinsu, da dariye-dariye har aka kira sallahr la'asar.
"Ku tashi muje muyi sallah kho"
"Wai su meenal an musulunta yanzu an fara sallah"
"Da can ba musulma bace"
"Ah wace ni baza'a ji mutuwar sarki a bakina ba" cewar khulud cikin tsokana.
Miƙewa sukayi Dukansu leeya ta kalli khulud tace "khulud wacece matar nan data tashi yanzu" ta faɗa tana nuna datijjuwar matar da ta kirata ɗazu.
"Ah bakisan haji bane hala ke ba a familyn nan kike ba?" Aneesa tayi tambayar da mamaki.
Leeya zatayi magana caraffff khulud ta karɓe da faɗin "ƴar ƙawar mum ce, amma mahaifiyarta ta rasu"
"Allah sarki, ƴan matan suka haɗa baki wajen faɗin haka, fuskar su na Bayyanarda tsantsar tausayi.
"Menene sunanki hala, Ni sunana meenal"
"Leeyana sunana"
"Sannu leeyana, Allah yayi mata Rahma kinji, Allah yasa ta huta"
"Ameen, Nagode sosai"
"Karki damu anzama ɗaya, tambayar da kikayi waccan matar da kika gani kakarmu ce itace mahaifiyar papu, da dadyn Kaduna, kuma duk nan jikokin tane banda waccan" ta faɗa tana nuna Airah.
"Okay, to ita menene sunanta?"
"Wake nan?" meenal ta faɗa ta sigar tambaya.
"Wannan"
"Okay wannan Airah sunanta, kuma mahaifiyarta ce jikar haji ba ita ba, duk nan da kika ganmu ƙanen mahaifiyarta ne"
"Ok Allah sarki, Allah ya ƙara haɗa kanku"
"Ameen" suka faɗa baki ɗaya, yayinda Airah ke faman hararar meenal.
"Wallahi Airah bakida kunya kingani bake bace sa'ar yina, ya-safiyyah ce Sa'a ta"
"Hummm, wallahi shine matsalar ƙaramin yaro ya haifeka, Ni kunga tafiyata idan baku tashi ba sister kekam zo muje kinji bar waɗannan dama ba damuwa sukayi da sallah ba" Airah ta faɗa tana jan hannun leeya.
"Kambala'i mu zaki gayawa haka bin na gaba dai bin Allah" khulud ta faɗa tana bin Airah da gudu sauran ma suka rufamata baya kamar ba ƴan mata ba.
Ko bayan shigar su ɗakin saida suka taɓa fira kafin wasunsu sukaje sukayi alwala, aneesa da Airah ɗakin leeya suka bita.
Inda meenal da badar kuma sukaje ɗakin khulud.
Bayan sun kammala sallarh ne suka haɗu gaba ɗaya ɗakin leeya, sosai sukaji daɗin haɗuwar su inda wata mata ta zagayo ɗakin tace kowa ya shirya karfe uku daidai za'a fara meeting ɗin, ba jimawa da fitar ta sai suka jiyo murya ta waje kamar Muryar Mayah ce tana kiran sunan meenal.
Isowarta kenan sai taga maman su meenal ɗin ta tambaye ta ina meenal take sai aka gayamata suna part ɗin nan.
Ita kuwa bata da haƙurin wulaqanci shiyasa ta tsaya bata ƙarasa ciki ba domin bataso su tada masifar da suka sabayi ita da khulud, idan sau goma zasu haɗu sai sunyi faɗa sau goma mayah kenan, amma idan fannah ce ba ruwanta da duk abunda khulud keyi domin ba saboda ita take zuwa gidan ba. Itama Rukhshanah batada haƙuri ko kaɗan a wannan bangaren duk FANNAH ta fisu sanyin hali.
"Meenal ke nake kira fa rainin wayo kuma kinyi banza kamar bakya jina" mayah ta faɗa cike da masifa.
Tana shirin juyawa sai taga khulud tafe tana tunkaro ta, gyara tsayuwar ta tayi dakyau tana jira taga dame yazo, domin ta ƙudurta a ranta ko mummy zata daketa a gaban mutane indai khulud tayi mata maganar banza ko raini sai ta wanke mata fuska da maruka.
Fuska ɗauke da murmushi khulud ta karaso wurin tana faɗin "twins saukar yaushe"
Duk da ganin yanayin da khulud ke ciki bai saka mayah ta murmusa ba, ƙara tamke fuska tayi tace "khulud meenal nake nema, ko sunanki kikaji na ambata"
"Ah ah baki ambaci sunana ba amma nake gani da Ni da meenal duk ɗayane a wurinki kho"
"Kowa daban a cikin ku kuma kowa da halinsa" mayah ta faɗa tana juyawa zata tafi.
Hannunta khulud ta riƙo tare da faɗin "ya kamata ki ajiye duk abunda kikeji a ranki mayah, ki daina ƙullatata a ranki domin kuwa hakan bashida wani amfani, nasan kinyi mamaki kwarai da gaske da kika zo kika sameni tare da ƴan uwana kho, Badar, Aneesa, Airah, da kuma meenal, sai kuma baƙuwar gidan nan namu wato Leeyana wacce yanzu ta wuce baƙuwa ma saidai a kirata da ƴar gida, duk muna tare sai nishaɗi mukeyi. Nasan nayi miki kuskure a can baya bama ke kaɗai ba da ma sauran mutane da dama amma dan Allah kiyi haƙuri ki yafemin na gane kuskurena, domin wannan ɗabi'un nawa da halaye mara kyau su suke neman jefani tsaka mai wuya, dan Allah ki yakemin na tuba kinji ƴar uwata".
Sosai jikin Mayah yayi sanyi nan da nan ta rungume khulud tace;
"na yafemiki ƴar uwata nima dan Allah ki yafemin a can baya kuruciya ce ke damun mu amma a yanzu munsan ciwon kanmu ba abunda zai ƙara shiga tsakanin mu in sha Allah, Allah Ubangiji ya ƙara haɗa kanmu"
"Ameen" khulud ta faɗa kwalla na kwance a idanunta.
"Muje ciki" ta sake faɗa hannunta na riƙe dana mayah.
*******
Hajiya mainah waasib wato (haji-mainah) yanda mafiya yawan ƴaƴanta da jikokin ta ke yawan kiran ta da haka ko kuma su kirata da (hajia babba).
mahaifiyar papu da dadyn Kaduna wato maihaifin twins da Fahad, suka ɗaina ƴaƴa maza da Allah ya bata, Khattab waasib shine babban ɗanta wato mahaifin TURAB da KHULUD.
inda gahees waasib ya zamo ɗa na biyu a gareta kuma shine yake biyema Khattab a shekaru. Daga kansu Allah bai ƙara bata ƴaƴa maza ba, sai ƴaƴanta mata su uku, saknah waasib,
itace mai biyewa mahaifinsu fannah tanada ƴaƴa huɗu ɗaya mace uku maza, macen itace Safiyyah wato mahaifiyar Airah, sai kuma fawzan, sha'aran, da kuma fideer shine auta.
Sai kuma rafa'at waasib kanwa ce a wurin Saknah waasib ita ce sherunsu suka kusa da juna domin a haihuwa daga saknah sai ita tanada ƴaƴa biyu mata Badar da Aneesa sune sha'anin ulud,
sai kuma ƴar autar haji mainah wato ubaidah, itace ƙanwarsu gaba ɗaya, ƴa ɗaya gareta mace sannan sai namiji ɗaya macen itace meenal (Ameenah) kuma itace babba sa'ar Leeyana, sun girmewa su ulud shekaru biyu zuwa uku, sai kuma ƙaninta waasib wanda aka mayarda sunan mahaifinsu kuma kakansu alhaji waasib sai ake kiransa da suna Little.
*Mahaifinsu Alhaji waasib kabeel, dan asalin jahar barno ne kuma a can yake zaune da iyalansa aiki ne ya mayarda Khattab a Abuja, daga nan kuma ya samawa ƙaninsa gahees aiki a Companyn da yake aiki da takardunsa na karatu cikin nasara kuwa ya samu aikin domin takardunsa nada kyau sosai, a ƙa'idar Companyn duk shekara ana tsintar mutane daga cikin ma'aikatan Companyn suje su wakilci Companyn a ƙasashe da dama domin tattauna dasu game ta yanda tsarin Companyn ke tafiya, haka ta kasance a shekarar aka zaɓi mutanen da zasuje harda gahees waasib, kuma a india ne za'ayi taron, ba'a wuce sati ɗaya da maganar ba ya koma gida barno ya sanarwa da iyayensa, amma a zahirin gaskiya yaji tsoron yanda ya sami mahifinsu waasib kabeel cikin matsananciyar jinyar da ta kamashi a kwana biyu kaɗai duk ya sauya kamanni, sosai hankalinsa ya tashi gaba ɗaya gwuiwoyin sa sunyi sanyi da ganin halinda mahaifinsa ke ciki har yace ya fasa tafiyar, da kyar aka samu aka rarrasheshi da magana mai dadi aka shaida masa Khattab zai ɗauki hutu yazo yayi jinyar mahaifinsu, ta hakan ya yarda yayi tafiyar, Khattab babban ɗan kasuwane har a ƙasashen waje gashi kuma cikakken alƙali kuma minister of judiciary.
Bayan tafiyar gahees kullum sai yakira gida yana tambayar jikin mahaifinsa ana gayamasa yaji sauƙi, ba rana da Ubangiji da zata fito ta faɗi ba tare da yakira yaji halin da mahaifinsa yake ciki ba. Da kalaman da yake samu ne suka saka ya kwantar da hankalinsa ya fara aikin da ya kawoshi a nan India, a kuma wajen aikin ne ya hadu da neesa wato mahaifiyar twins asalin ƙabilar ta urdu ce saidai su musulmai ne basa bautar gumaka daga nan kuma ya kira gida ya sanar musu da cewa ya sami matar aure, sosai sukayi masa farin ciki da fatar alƙairi, ba jimawa ya aureta lokacin da suka kammala aikin da ya kawoshi India.
Kwana uku tsakani suka dawo gida NIGERIA, sosai yayiwa iyayensa da ƙannesa da yayansa tsaraba, bayan haka kuma ga tsarabar mata ba-india daya kawo musu.
ƴan uwansa sunyi murna sosai kuma sun karɓi neesah hannu bibbiyu, sai dai wani tashin hankali da gahees ya tarar gida aka gaya masa tun bayan tafiyarsa da kwana ɗaya mahaifinsu waasib ya rasu, kuma an zaɓi a ɓoyewa masa ne saboda aikin da yake yi sunsan idan suka gaya masa bazai zauna ba balle yayi aikinda yakai shi.
Ranar gahees yayi kuka sosai kamar wani mace, rarrashi kuwa ba kalar wanda ba'a yimasa ba sai da yaci kukansa ya ƙoshi sannan yayi shiru.
Haka rayuwa taci gaba da tafiyar musu, sosai suke kula da mahaifiyarsu duk da suna nesa da ita amma hakan bai saka ta saka tunani a ranta ba domin iya gwargwado suna kula da ita.
Bada jiwa ba gahees ya koma kaduna da iyalansa domin yaci gaba da kula da harkokin Companyn su na Kaduna.
Shikuma papu a lokacin yana zaune a Abuja, sai daga bayane khulud ta ƙeƙashe kan itafa garin suleja takeso su koma da zama tun ana ɗaukar maganar ta matsayin wasa saboda a wannan lokacin ƙaramar yarinya ce sosai har sukaga abun nata ya wuce gaban tunanin su, domin haɗa kayanta tayi wuri ɗaya kan zata bar gidan idan basu koma garin da takeso su zauna ba.
Anyi rarrashi har aka gaji batayiba, papu kuma baya ƙaunar ganin abunda zai taɓa khulud domin sosai yake sonta yake kuma jin tausayinta sakamakon larurar da take fama da ita, tanada ciwon zuciya wanda dashi aka haifeta.
Ciwon zuciyan mai tsanani idan ya tashi sai an fita da ita waje domin baya barinta a Nigeria saboda tana zubarda jini sosai hanci da baki harma kunne, tana cika shekaru tara ne alamomin ciwon asthma suka bayyana gareta, domin kuwa sosai numfashi keyi mata wahala a duk lokacin da ciwon ya tashi, kuma ciwukan biyu zasu iya tashi a lokaci ɗaya.
Da wannan dalilin ne yasa papu ya sangar tata sosai baya taɓa bari ayi mata wani abu da zai ɓata mata rai, ko kuma ta nuna tanason abu bata samu ba a kasa yimata duk baya