BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   42 / 61

123K to 126K   out of 180.4K words

zata bar wurin.
sai ganin mum tayi har ta kusa karasowa.

"Lahh mum da kin bari nazo ai"
"Ba komai ai Ni gani nan nazo, yauwa nace kin taɓa sanin wata yarinya Rukhshanah sunanta"

"Rukhshanah?" Ta maimaita sunan a bakinta, "bansantaba gaskiya, amma inajin sunan a bakin mayah, amma lafiya meyasame ta?"

"Wallahi itace batada lafiya, kuma itace ta suma a hall, yanzu ta farfaɗo tana ta kiran sunan ki"

"Ni kuma!?" Ta faɗa tana nuna kanta. "Muje to"

Sun juya zasu tafi kenan sukaji horn din mota a bayansu.
"Mum su papu ne" leeya ta fada domin ta gane motar.

Bin motar sukayi baya sai da tayi packing sannan papu da dad ƙarami suka fito suka gaisa da juna.

"Ya me jiki?" Cewar dad ƙarami.
"Alhmdullillah me jiki da sauƙi"
"Ta farfaɗo?"
"Eh ta farfaɗo amma abun akwai ban mamaki tunda ta tashi take kiran sunan wannan yarinyar"
Cikin mamaki shima dad ƙarami ya kalli leeya yace"kinsan ta ne leeyana?"

"Ah ah dad wallahi ban taɓa ganin ta ba amma wata kila ita ta sanni nice bansan ta ba"

"Ah to mu shiga ciki mana" Papu ya fada yana wucewa su kuma suka rufamasa baya.

A bangaren Fahad gaba ɗaya komai ya shafe a tunanisa.
"Turab" ya furta a ransa.

Miƙewa yayi da sauri zai fita mummy tace "fahad ina zakaje"

"Mummy zanje na kira wayan turab ne, wallahi na manta gaba ɗaya bansan inda suke ba yanzu, inaga ma koda wannan abun ya faru basa cikin hall din nan"

"Allah sarki ya kamata gaskiya kaje ka kirashi"

Yana fita yayi ta wata hanyar daban, wayarsa ya ciro yayi dialing number ɗin turab.

"Subhanallah, meya faru? Meya same shi"

Fahad ya faɗa lokacin da turab ya daga wayar.

"Shock kuma, akan me? Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un yanzu kuna ina"

"Okay wane asibitin, gayamin gani nan tafe yanzu"

"Ahhh ikon Allah muma muna asibitin wallahi, wane room ne?"

"Okay gani nan zuwa"

Tun bai kammala wayar ba ya nufi sashen da aka gaya masa nan aka kwantar da zafaran.
Da sallama dauke a bakinsa ya shigo dakin, zafaran ya farfaɗo yana jingine da gadon da mug a hannusa yana kurfa tea a hankali.

"Sannu zafaran ya jikin?" Fahad ya tambaya yana daddafa goshin sa.

"Da sauki fa, Ni lafiya kalau nake tun dazu ina ta so kazo na sanar maka"

"Me zaka sanar dani?"


A can bangaren su leeya kuma suna shigowa dakin da Rukhsha take mummy-neesah ta tarbesu da murmushi kwance a fuskar ta.

"Sannunku da zuwa anzo Lafiya?" Ta fada tana kallon su Papu da suka shigo Abuja yanzu.

"Hanya alhmdullillah, ya me jiki?"

"Me Jiki da sauki alhmdullillah sai godiyar Allah, gata can tana bacci"

Mummy-neesah ta fada tana nuna gadon da Rukhsha take, sai dai basa ganin fuskar ta domin ta juya kanta ta bangon dakin su kuma suna daga bayanta.

Wuri suka samu suka dan zauna, minti biyar tsakani ba wanda ya kuma cewa komai.

Fannah da mayah, khulud da badariyyah tuni aka kira driver yazo ya mayar dasu gida domin fannah da mayah sun kasa daina kuka hankalin su ya kasa kwanciya shiyasa aka mayar dasu gida.

Miƙewa suka ga leeya tayi da karfi tana toshe bakinta tare da ja baya lokacin da Rukhsha ta dan motsa har ana iya ganin rabin fuskarta.

"A...A...Aleena, mum wannan Aleena ce ba Rukhshanah ba, ba itabace Rukhshanah Aleena ce ƙanwata mum, mahaifi da mahaifiyar mu daya wallahi itace kuzo ku gani"

Leeya ta fada tana jan hannu mum fanaya zuwa gadon da Rukhsha ke kwance kamar wata zautacciya.

Mummy-neesah da dad kam suka doskare a tsaye sai bin leeya suke da idanu duk abunda take.

Papu ma kallonta yake cike da madaukakin mamaki, suna isa gadon leeya ta saka hannu ta sake juyo da fuskarta yanda kowa zai ganta.

Sake ja da baya tayi kamar mai jin tsoro ta kuma cewa "Aleena, kece dan Allah ku taimaka ku tadani idan bacci nake aleena ta riga ta mutu wanda ya mutu kuma baya dawowa ai" cikin matsanancin kuka take fadin haka ta juya zata bar dakin da gudu taji an riko hannuta ta baya.

"Yahyah-leeya ina zaki tafi ki kuma barina, wallahi nice Aleena ban mutu ba, mu ke muka d'orawa mutuwa tun a farko"
Aleena ta fada itama cikin hawaye.

Da gudu leeya ta yo kanta ta rungume ta suka sake fashewa da kuka.

Buɗe kofar dakin akayi kanajin sautin bude dakin kasan wanda ya bude ta baya cikin kwanciyar hankali.

Turab ne farko, sai kuma fahad ya biyo baya sannan sai zafaran.

Cirko-cirko sukayi suna kallonsu leeya dake ta sheka kuka har tsawon wani lokaci.

Miƙewa Rukhshanah wato (Aleena) tayi da karfi tana kokarin gasgata abunda idanunta ke gane mata, fizge drip dinda ke daure a hannunta tayi tana kokarin kara gudun hawayenta.

A kafff dakin ita kadai ta lura da shigowar su turab.

"Bro O, kai ne yaushe ka dawo meke shirin faruwa? Daga ina kake ina Nnene da uchie na"

Kamar wani zaki haka zafaran ya tsallako inda suke domin shi harga Allah har yanzu bai gasgata leeya yake gani a gabansa ba, wai harda budurwa.

"Leewa, leeyana! Ina kika shiga tsawon lokacin nan" zafaran ya faɗa yana riko hannayenta, ruɗanin da ya shiga ya saka shi mantawa da inda yake kuma a gaban su wa yake har ya riqa hannun leeya a gaban kowa.

Kamar wanda aka zubawa ruwan dalma haka turab yaji lokacin da zafaran ya rike hannayen leeyanah, da sauri ya rumtse idanunsa yana jin d'aci da radadi a zuciyarsa.

Dunkule hannayensa yayi da sauri ya kaiwa iska naushi yana jaa da baya idanunsa a rufe.

Fahad kuma ganin haka ya sakashi rike turab da sauri ya zaunar dashi.

Da sauri dad ƙarami da mummy-neesah da kuma papu suka yo kan turab da yake neman fita hayyacinsa.

"Papu leeya ce, mum meyasa tun a farko kika ki gayamin gaskiyar asalin inda kuka sami leeyana meyasa mum? Kince min ƴar aminiyarki ce mai rasuwa, alhali a bincinken da nayi babu wata alaqa tsakanin leeyanah da ita ƴar Aminiyar taki, gashi yanzu mum, ga abunda wannan abun ya janyo"

"Me kake nufi turab, kwata kwata ban fahimci inda zancenka ya dosa ba, wai menene haka ya kukeso kwakwalenmu su dauki wannan abun, wallahi gaba daya kaina ya rufe na rasa gano bakin zaren" cewar mum tana matsowa inda suke.

A bangaren zafaran kuma lokacin da ya riko leeyana har razana tayi da ganinsa sosai domin tafin hannunta ta saka ta dafe fuskar ta da kwayar idanunta da suka bayyana a cikin mayafin da ta sako.

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Okene kaine dan Allah ku tadani daga mafarkin da nake, ku maida ni duniyarmu ta asali, meke shirin faruwa damu"

Bata idar da fadin abunda take shirin faɗa ba kamar wacce ta tuna wani abu ta wafce hannayenta daga rikon da zafaran wato okene yayi mata ta koma inda Aleena ke tsaye hankalinsu duk a tashe tambayoyi ne falll a ran duk wani mahaluki mai numfashi a cikin mutanen da ke dakin.

"Budurwa nasan an kashe uchie tun a gabana ina Nnene take?"

Kamar wata zararriya kafin rukhsha ta bude baki tayi magana tuni leeya ta sake dira gaban zafaran.
"Taya iyayenka suka bar ka ka musulunta okene, dama karya kayi mana da kace kasar waje zaku koma, meye amfanin kin gayamana gaskiya dakayi"

"ki Zauna a nan leeyana, Fahad miko min mug da ruwa masu sanyi, karɓi kisha"

Karɓar mug din tayi kamar yanda aka umurceta tasha, sannan ta kuma zabura zata tashi, "ki zauna nace" mum ta kuma daka mata tsawa.

"Ki bita a hankali hajiya fanaya, kina ganin lamarin nan kinsan ya girmewa tunaninta, maganar kisa fa ake, babban abunda nakeso na sani shine alaqarsu su ukunnan. Amma duk wannan ba maganar da zamuyi anan bane muje gida yanzun nan"

"Turab baya cikin nutsuwa mum inaga kamar ma ya daina motsi wallahi"
Sukaji muryar fahad daga bayansu yana magana.

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, wai meyake shirin faruwa damune, kaje ka kira likita yanzun nan"

Da gudu fahad ya fita har yana tuntuɓe.

"Hajiya ku tafi da yaran nan suleja yanzu, mu zamu zauna da turab din, kuje waje driver yana nan wanda ya kawomu, mu idan muka tashi sai fahad ya dawo damu"

Mummy-neesah da mum fanaya, da kuma leeya da Rukhsha suka dauki hanyar komawa suleja tare da driver, amma har a wannan lokacin leeya bata dawo cikin hayyacinta ba komai take ganinshi kamar a mafarki, a back sit ta zauna ta ta haɗe kai da gwiwa har suka isa gidan batayi magana da kowa ba.

Ita kuma Rukhsha tana jikin mummy-neesah tana bacci har suka karasa domin itama allurar da aka yimata bata ida saketa ba, a ƙa'idar allurar ma ba'a tambayar mutum komai ko ayi masa magana har sai yayi 24hr allurar na zaga jikinsa.

A asibiti kuma papu ne da dad ƙarami sai kuma fahad, zafaran, da turab dake kwance a yanzu ya farfaɗo.

Dad ƙarami ne ya kalli turab da murmushi kwance a fuskar sa yace "son meke damunka haka wanda mu kanmu bamu sani ba kana neman sake tada mana hankali bayan wanda muke ciki?"

"Dad nasan kuna matukar son farin ciki na, kuma kunaso kuga na rayu dad, amma wallahi bana tunanin rayuwata zatayi tsawo idan babu leeyana a ciki, wallahi ina matukar sonta, na rantse da girman Allah idan leeya bata aureni ba zan iya mutuwa, dan Allah ku taimaka kuji tausayina" turab ya faɗa gwanin ban tausayi.

Wani irin azababben faduwa gaban zafaran yayi da sauri ya kalli inda turab ke kwance jin abunda yake faɗa, kamar a Sa'a kuwa idanunsu suka sarke.

Mikewa turab yayi hade da fizge drip dinda ke daure a damtsensa ya karaso gaban zafaran idanunsa duk sun firfito waje saboda tsananin tashin hankali da yake ciki.

A gabansa ya durƙusawa tare da riko hannayen sa gaba ɗaya.

"Abokina wallahi ina sonka so na tsakani da Allah wanda Allah ya yarda abokai su yiwa junansu, kuma kaima nasan kana sona, wallahi a rayuwata ban taɓa tunanin akwai Ranar da zatazo na zautu dalilin soyayya ba, zafaran wallahi summah tallahi ina son leeyana na kasa yarda da cewa yarinyar da kake so muke neman ta tare dakai ita zata hana zuciya ta sukuni, alal haqiqa nasan soyayyar ta na zuciyar ka, kuma nasan abu ne mawuyaci ka fitar da ita a ranka, banso kaina ba Muhammad zafaran Areyola amma wallahi na tabbatar da na Fika bukatar leeyana a rayuwata, infact itace Yarinyar da iyayena suka zabamin matsayin matar aure. na rokeka da girman Allah da darajar fiyayyen halitta kayi hakuri ka fitarda Leeya a ranka, wallahi duk tsawon wannan lokacin da muka ɗauka muna Neman leeya banyi tunanin ita ce yarinyar da kake nema ba saboda baka taɓa furtamana Asalin sunanta ba, ko Ranar da mum ta fara gayamin sunanta saida nayi dogon tunani ko zan iya tuna inda naji sunan amma na kasa, I'm so sorry to say Zafaran wallahil Azeem ina son leeya har cikin rainah" turab ya karasa maganar yana durkushe gabansa.

Jiki a sanyaye zafaran ya miƙe daga zaunen da yake idanunsa sun sauya kala zuwa jaaa jajir hawaye kwance zaiyi magana fahad yayi saurin shiga tsakaninsu hannunsa ɗaya rike da turab daya rike da zafaran yace;
"Dad kuzo muje gida please, wallahi sam wannan maganar bata dace da ko'ina ba sai a gida, dan Allah kuzo muje gida gaba ɗaya ayi komai a gama"

"Shikenan muje gida kawai" cewar papu.

Dad ƙarami ne yazo ya riqa hannun Zafaran shi kuma fahad yana riqe da na turab kamar wasu kananun yara har suka isa mota gaba dayansu suka dauki hanyar komawa suleja tare. fahad ne kan gaba, kuma shi yake tuka motar.


SULEJA STATE.
K. WAASIB MANSION.


Zaune take a tsakiyar gado ta nannade kafafuwanta ta cusa kanta tsakan ka nin cinyoyinta tana fitar da sautin kukanta a hankali cikin dusasshiyar murya wacce bata fita sosai saboda tsananin kuka da kuma shakewa da muryar tayi.


A gefenta kuma meenal ce da kuma Khulud sauran yaran duk basa dakin iya su biyun ne kawai.

""Leeyana kiyiwa Allah ki daina kukan nan haka, wallahi kuka ba shi bane maganin matsalar, domin da kuka yanada mafita da tun awa uku da suka gabata ansamu mafita don Allah kiyi haƙuri ki daina kuka haka"

"Meenal ya zanyi da rayuwata? Daga na fita wannan sai wannan meyasa ya-Turab bayada adalci a rayuwarsa, da tun farko ya karbi zabin da aka yimasa da ba haka ba, inason Okene da dukkan zuciyata, wallahi tun kafin ya musulunta ina mafarkin zama da shi, me yasa bai Bayyana ba sai a wannan lokaci, Meyasa ya-Turab bai furta yana so da qaunata ba saida yaga asalin masoyina na gaskiya ya fito, bazan taba yarda ba meenal, kuma bazan taba butulcewa alkairin da iyayensa sukai min ba"

"Gaskiya wannan lamari Akwai daure kai, to shi ya-Turab yana sonki tun farko ko kuwa dai sai yanzu ne dayaga asalin masoyinki ya fito yasa yake nuna kamar yana sonki"

"Wallahi meenal Ni har banason tunawa da wasu abubuwa na baya da ya-Turab yayimin, amma Ni ban taɓa rike shi a rai ba, kawai dai yarda da shi ne bazanyi ba"

"Ki dinga hakuri kawai kinji, Allah ya sauwake yanzu ki tashi muje parlour abincin ki na can tun dazu, kuma har yanzu hankalin mum da haji bai dawo akanmu ba domin wannan yarinyar rukhsha na bacci tun da suka dawo nan, kuma ya-Turab da ya-zafaran duk suna kwance a asibiti"

Cikin zallar tsoro leeya ta dago kanta daga jinginashi da kan gado da tayi ta kalli meenal tace "me ya samesu?"

"Tho wallahi muma dai bamu sani ba, amma dai ankira haji an sanar mata suna hanya, dha niyyar ta ma taje abuja yanzun nan har sun shirya zuwan kuma aka gayamata ba sai tazo ba domin suna hanya"

"Allah ya qara tsare gaba"

"Ameen"

Meenal da khulud suka faɗa.

Tun zamansu a wurin khulud bata ce komai ba saboda bataso tayi magana cikin wannan lamarin domin abun ya fi karfin ta, duk yanda tayi Magana za'a ce tayi son kai tayi.

"Ku tashi muje parlour" khUlud ta faɗa tana miƙewa tsaye.

Miƙewa sukayi suma har leeya suka wuce parlour.

A parlourn kuma haji ce zaune da shirinta sai kuma mum da kuma mummy-neesah.

Shigowar su leeya yasa suka dago gaba ɗaya.

"Leeya kizo idan kin kammala cin abinci" cewar haji mainah.

Daga mata kai tayi cikin nuna alamun maganar ma tana yimata wahalar fita.

Daining suka wuce su biyu kaɗai ita da meenal. Zama sukayi meenal tayi serving dinta, amma har tayi ta gama leeya bata sani ba saboda ta na zaune ne kawai hankalinta baya wurin ta zabga uban tagumi ta zubawa wuri daya idanu.

"Leeya ga abinci nan ki ci don Allah kar ki sakawa kanki tunani da damuwa kinji Please"

Kamar wacce ta farka daga nannauyan bacci haka leeya ta mike tsaye "meenal ina kanwata Aleena, wallahi na manta da tana gidan nan tun shigowar da muka yi ban ganta ba"

Dafa kafaɗarta meenal tayi sannan ta mayar da ita zaune tace cikin tausasan kalamai "ki zauna kici abinci kawai, leeya rabonki da abinci tun karfe goman safe fa, kici idan kin gama zamuje ki ganta bacci take yanzu"

"Meenal waye ya mayarwa Aleena da suna Rukhshanah, alhali Abbinmu Aleena ya saka mata?"

"Sai idan kin gama cin abincin ne zamuje muyi magana dasu kinga yanzu bazai yiwu muje inda suke ba tare da kinci abinci ba"

"Shikenan zanci, amma wallahi bana ma jin yunwa kuma saboda ke zanci"

"Tau kici koda bakyajin yunwa hakan ma ba laifi"

Zama tayi ta fara kai spoon din abinci a hankali kamar bata son ci, a zahirin gaskiya cin abincin kawai take batasan ya tasting din abinci yake ba turashi kawai take ya zamarmata kamar dole.

"Na ƙoshi" ta faɗa tana sake mikewa tsaye.
"Karɓi ruwa kisha"
"Na koshi" ta kuma fadi murya a sanyaye.

"Muje ki kaini in ganta don Allah, wallahi inada tarin tambayoyi danake so nayi mata"

Parlour suka koma sai dai basu tarar da kowa a parlourn ba.

"Su mum basa nan, kuzo muje dakinmu ki kwanta ki huta idan suka dawo zan kiraki kizo muje ki gana da kanwar taki"

"No meenal, ba nada gajiyar da nake bukatar hutu yanzu i need to meet her please"

"Okay muje part ɗin mum, bansan takamammen inda zan ganta ba gaskiya, amma kinga idan muka tambayi mum zata gaya mana"

Part ɗin mum fanaya suka shiga sai dai basu tarar da ita a dakin ba, sake dawowa master parlour sukayi amma kuma har yanzu ba wanda suka samu a parlour.

Parloun kasa suka sauka shima basu tarar da kowa ba, suna shirin fita part din ne sai ga mum da papu sun kunno kai, da sauri leeya ta dan tattaro yar sauran nutsuwarta ta gaida shi tayi masa ya hanya kuma ta yi masa ya masu jiki"

"Meenal kuje part din haji ki raka leeya yanzu a can zata kwana"

"Okay mum, muje leeyana" meenal ta fada tana riko leeya suka fice daga part din.

Sashen haji suka wuce direct, mugun faduwa gabanta yayi ganin turab da zafaran da kuma fahad suma zasu shiga sashen na haji-mainah.

Da sauri ta soke kanta kasa sosai har tana hardewa da tafiyarda take tanaso tayi saurin barin wurin.

"Leeyana!?" Ya kira sunanta da kausa sasshiyar murya.

Kamar wacce akeyiwa lugude haka ta keji gabanta na da ka da karfi.

Ci gaba tayi da tafiya bata tsaya ba kuma bata wai wayo ba, meenal ma na iya kokarinta taga ta tsayarda ita, daga karshe ma fizge hannunta tayi ta ci gaba da tafiyarta ita kaɗai.

"Leeyana ki tsaya magana zanyi dake". still bata tsaya ba taci gaba da tafiyarta.

"Don girman Allah ki tsaya"

Chakkk ta tsaya bata kara ko taku daya ba har ya iso daf da ita meenal na ɗan nesa dasu, zafaran da fahad ma suna biye da su da ƴar tazara kaɗan.

Tsayuwar sa ya gyara sosai tare da zuba hannayensa gaba ɗaya a cikin aljihu, yaci gaba da kallon ta a yanda ta tsaya ma'ana ta bashi baya kenan baya ganin fuskarta, bayanta kawai yake iya gani.


Magana ya fara yi, kuma a yanda yake magana ba wanda baya jin abunda yake faɗa, har meenal da zafaran, da kuma fahad.


"Leeyana, nasan zakiyi mamaki sosai idan na gayamiki sirrin zuciyata akanki, wallahi tun ranar da na fara ganinki na kamu da matsananciyar kaunarki, wanda hakan ya haifar min da illa sosai a rayuwa ta, wallahi leeyana da a ce bana shan magani akai-akai da yanzu ba wannan maganar ake ba, ina bada abun sadaka a masallaci, ina kuma rabawa mabukata domin komai ya zomin da sauki, ina pretending sosai akan komai na rayuwata domin ba wanda ya san da haka, ina cikin addu'ar samun mafita ne iyayenmu suka kiramu suka hada aurenmu, a

42 / 61