Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
da dare na jita tana waya har tana cewa ita ta gaji da aiki a gidan nan saboda ana takura mata bata samun lokacin kanta balle ta samu lokacin ɗanta"
"Da gaske ne abunda khulud ta faɗa?" Papu ya tambayi dayammah.
"Wallahi ba gaskiya bane Alhaji na rantse maka da Allah gaba ɗaya jiya banyi waya da kowa ba ƙarya take min"
"Ni nake miki ƙarya? Talaka dake zanyiwa ƙarya wallahi pa, ba ƙarya nake mata ba"
"Kinason aikin ki kho?"
"Ehh wallahi alhaji inason aikina"
"Okay tau yazama dole idan kinason aikin ki, ki kula dashi idan ko ba haka ba gaskiya zan sallame ki"
"Pa a koreta kawai tunda har ta fara gayawa mutane ta gaji da ganinta a ƴar aiki"
"Wallahi alhaji bantaɓa faɗar maganar nan ba"
"Nidai nagayamiki idan kinason aikin ki riƙe da kyau, My kid lemme get car key to go out and eat something again"
"Thank you my pa"
Tashi papu yayi daga wajen, ya rage saura khulud da dayammah kaɗai
"Hajiya ƙarama dan Allah meyasa kika aikatamin haka bayan kinsan Alhaji bayason ayimai ƙarya kuma gashi ke kinyi mai ƙarya, kinsan bani na aikata abunda kikace nayi ba"
"Uuuhhhm Ni na aikata, Ni na zuba ruwa a soup ɗinda kika haɗa Saboda alkawarina ne saina saka pa, ya koreki a gidan nan, tunda idan nace nayi yanda nakewa sauran ma aikata akanki mum bazata bari ba, amma kijira kigani Ni KHULUD KHATTAB WAASIB bana magana biyu, kinzata wasa nake kho? This is just the beginning, zanyita yin abubuwan da zaki gwammaci ki bar gidan nan da kanki basai an koreki ba that's promise"
"Kiyi hakuri dan Allah wata rana sai labari, yau gare ka gobe kuma ga wanin ka, hajiya ƙarama ki ƙara hakuri kawai komai yanada lokacin watarana zaki nemeni ki rasa, da badan ƙaddara ba da bansan inda zaki ganni ba balle ki wulakanta Ni"
"Mtswww can ta matsemiki ke kika san waɗan nan ni bakya ko gabana, balle na wani da mu da abunda kike faɗa"
"Khulud ɗin papu ki tashi ki cire uniform ɗinki tukunna sai mu tafi kho"
"Ah ah pa, Ni sai na dawo zan cire uniform, yunwa nakeji sosai bazan iya tsayawa nacire uniform ɗin nan ba"
"Dan Allah hajiya ƙarama ki cire na wanke miki kafin ki dawo, kinga gogewa ka kawai za'ayi"
"Mtswwww kinga dayammah kifita harakata wallahi idan ba haka ba zaki gane kurenki. Pa, let go Please yunwa nakeji"
"Dayammah ki bari idan muka dawo sai ki je kiwanke mata ɗin kinji, yanzu kinga yunwa takeji bazata iya tsayi ta canja kaya ba"
"Tau Alhaji babu damuwa Allah ya dawo daku lafiya"
"Ameeen"
Tana nan zaune a parlour har mum ta fito ta sameta zaune ita kadai kuma ba aiki take ba "dayammah me kike jira a nan?"
"Ahhh hajiya babu komai, ina jiran su hajiya ƙarama su dawo ne na wanke mata uniform shikenan na ƙare aikina, saboda inaso na gama da wuri ne fita"
"Ina zakije?"
"So nake naje na duba ɗana a makarantar su, kinsan jiya aka kawoshi asibiti ba lafiya, kuma ɗazun nakira malaminsu bai ɗaga waya ba, shine nakeso naje na dubashi idan na gama aikina"
"Tau ai kin gama aikin kho, ko meya rage, akwai wani abu da baki yibane?"
"Ehh hajiya nagama, wankin uniform ɗin hajiya ƙarama kawai ya ragemin"
"Wane uniform kuma? Badai waɗan da ke jikinta ba"
"Ehh hajiya su"
"Dayammah kenan wankin uniform ɗin khulud sune zasu hanaki zuwa duba yaronki, dan Allah tashi kije kawai hala sauran uniform ɗin nata ba wankakku bane?"
"Ehh hajiya wankakku ne amma..."
"Amma me ki tashi ki tafi kawai kinji bara na ɗauko tsarabar mara lafiya"
"Nina tsayarda ita mum, Ni nace tajirani" khulud ta faɗi maganar tana shigowa parlourn da leda a hannunta pa, kuma yana biye da ita.
Bata ƙara faɗar komai ba ta wuce bedroom ɗin ta.
Dayammah kuma ta bita a baya har suka isa bedroom ɗin ta, khulud bata tsaya ba sai da takai kan gado sannan ta zauna gefen gadon.
Dayammah kuma ta shigo bakinta ɗauke da sallama, khulud ko ɗaga kanta batayiba balle ta amsa mata.
Ɗan wuri ta samu ta tsaya tare da kafe idanun ta waje ɗaya saboda tasan komai tayi zai zamo laifi wajen khulud.
Buɗe ledar da ta shigo da ita tayi tafito da hollandia yoghurt tare da pizza, ta fara ci.
Harta gama cin abincin bata kalli dayammah ba balle ta saka ran zata yi mata magana.
Baby taddy ta ɗauko ta fara yimata tawai tana wasa da ita kamar bata san da mutum a wajen ba
"Hajiya ƙarama ke nake jira dan Allah ki cire ki bada na wanke miki"
"Okay kibari idan nagama wasa sai na cire nabaki"
"Haba hajiya ƙarama wallahi inada uzurin fita kibari idan kika cire uniform ɗin sai kici gaba da wasan"
"Nace miki ban shirya ba idan zaki jira ki jira, idan bazaki iya ba ga hanyar nan"
"Kina nufin na tsaya ina jiranki har sai kin ƙare wasa sannan ne zaki ban uniform na wanke miki"
"Mtswwww so if you can't wait for me them you go and came back later"
"Dan Allah hajiya ƙarama karkiyimin haka kicire kibani kawai wallahi fita zanyi idan kuma nadawo nagaji wallahi saboda tafiya mai nisa zanyi"
Tsaki ta kuma ja sannan taci gaba da wasan ta batace komai ba.
Cikin jin haushin abunda khulud tayi mata, ta kama neck tie ɗinta da nufin ta cire mata uniform ɗin ita kuma khulud ta riƙe hannuta"
Wani sakaran ihu khulud ta ƙwala har takai ga mum da papu sun shigo ɗakin da gudu
"menene haka" papu ya tambaya a harziƙe.
"Pa marina tayi sannan ta shaƙemin wuya wai saita kasheni tunda na saka kayi mata faɗa"
Khulud tayi magana tana dafe da kumatunta haɗi da matsar kwalla.
"Dayammah khulud kika mara?"
"Wallahi na rantse da Allah Alhaji ban mareta ba ban yimata komai ba"
"Ƙarya zata yimiki ne ki duba ki ga yanda take kuka fa"
"Pa wallahi ta mareni bana ma gani da idon nan nawa na bangaren dama"
Da sauri mum ta zagaya tare da riƙeta tana jijjigata kamar wata ƙaramar yarinya.
"Wallahi pa bana gani da idanun nan sau biyu ta mareni"
"How dare you slapped my daughter in our house, kina matsayin ƴar aiki zaki zo har gidan mu ki dakarmin ƴa, yazama dole kibar gidan nan yanzu-yanzu" papu yafaɗa cikin ɓacin ra.
Da sauri mum ta miƙe zatayi magana"karki sake kice komai hajiya fanaya na riga na yanke hukunci, ko don bake akayiwa haka ba shiyasa kike nema ki kareta, to wallahi na riga na gama magan dayammah bazata zauna a gidan nan ba tunda har tayi tsaurin idon dukan ƴata a cikin gidan na"
Kamar yanda papu yace mum bata furta komai ba, dayammah ke kuka kamar ranta zai fita tana rokon papu da khulud suyi hakuri.
"ki tafi na riga na gama magana ko so kike na kira a fitar dake gidan nan"
Jiki na rawa ta tashi ta fita ɗakin domin kuwa papu yaɗau zafi ba kaɗan ba, ganinsa a haka ya tsora tarda ita sosai, shiyasa tayi gaggawar tashi ta fita ɗakin, tana fita kuwa tanufi part ɗin da aka ware mata agidan ta fito da duk abunda tasan nata ne tabar gidan tanata kuka, ma aikatan gidan da dama sunji ciwon barin dayammah gidan yayinda wasu suke cike da murnar barin gidan da tayi.
Zaune a parlour mum ce da papu sai kuma khulud da suka sakata tsakiya, papu sai leka fuskarta yakeyi yana duba idanunta.
"Mamana nace kizo muje hospital a duba idanun nan kinƙi"
"Ni bazanjeba pa, tunda ta riga ta cuceni da dai ramamin za'a yi a hospital ɗin danaje amma tunda ba ramamin za'a yiba ni bazan je ko ina ba gaskiya"
"Justice nifa har yanzu zuciyata taƙi aminta da wannan lamarin, wai dayammah ce zata ɗaga hannu ta mari khulud gaskiya nidai ban yarda ba, da dai ka tsaya kayi bincike kafin ka yanke hukunci"
"Hey idan ma batayi, yau ɗin tayi ƴarmu bazata yimana ƙarya ba tunda bata saba yimana ƙaryan ba, kinga kho bazatayi ba saboda mutum ɗaya idan baki yarda da abunda tace ba sai kiyi shiru da bakin ki" papu yayi maganar a hasale.
"Ke da gaske kike ta mareki"
"Ehh mum Wallahi da gaske nake marina tayi har sau biyu, kuma wasu lokutan idan bakwanan dukana take sannan tace idan na sake na gayamuku ta dukeni saita yanka Ni"
"Kinji kho, kinji ma har dukanta takeyi idan bama gidan nan kuma tana barazanar zata yankata, na rantse bazata dawo gidan nan ba, kuma bazata ƙara aiki a gidan nan ba"
papu ya faɗa yana wucewa part ɗinsa fuuuuu kamar shi aka mara ba ulud ba.
"I'm so sorry mamanah, bayan mari me tayi miki?"
"Marina kawai tayi mum"
"Ya idanun yanzu?"
"Suka kawai nakeji sunayimin yanzu mum"
"Kiyi hakuri kinji"
"Okay mum"
"Na ajiye miki wani abu mai kyau muje ɗakina na baki"
"Thank you mum"khulud ta faɗa tana murmushi mai bayyanar da haƙora.
"Ur welcome my baby" faɗin mum tana rungumo ulud a ajikinta.
* * * * * *
LEEYA...
Kwance take a inda tayi bacci tunjiya,
wato bakin titi kusa ga wani ɗan karamin gida, juye-juye ta farayi yayinda hayaniyar mutane da kuma na abin hawa suka fara dira a kunnuwanta.
tashi tayi daga kwancen da take ta buɗe idanun ta tarrr kan inda ta tsinci kanta a yanzu kuma.
"Yanzu a nan na kwana"
"To wazaki tambaya ai kinsan nan kika kwana tunda kin tashi kinga kanki anan"
Wata zuciyar ta bata amsa.
Addu'ar tashi daga bacci ta karanta sannan ta miƙe tsaye.
Zaninda ta kwanta da shi ta yaye,
kana ta kaɗe kurar da ke kan zanen ta ninke shi ta maidashi cikin jakarta.
Randar ruwa ta hango gaban gidan da ta kwana, tana hangota ta nufi ranar ta tsoma kofin da tagani ciki sannan ta ɗibo ruwanda ke ciki.
wata ƙaramar gora ta janyo ɗan nesa da ita kaɗan ta zuba ruwan a ciki sannan ta koma chan gefe inda mutane basa hangota sosai sai tayi alwala, bayan ta kammala alwalan ne ta dawo inda ta ajiye jakarta sannan ta fito da sallahya ta shimfiɗa ta tada sallah.
cikin nutsuwa tayi sallarta har tagama ta zauna ta fara azkar.
Gama azkar din keda wuya zazzaɓi mai zafi ya rufeta.
anan inda tayi sallah nan ta kuma kwanciya sannan ta ƙara janyo zani daga cikin jakarta ta lulluɓe jikin ta dashi, domin har sanyin zazzaɓi ya kamata.
Wata farar mota ƙirar RANGE ROVER ce tayi parking dai-dai inda leeya ke kwance, sauke glass ɗin motar akayi yayinda matuƙin motar tausayin ta ya kamashi yaɗan cije lips dinsa kaɗan, kana ya girgiza kansa a hankali.
Kamar mai nazarin wani Abu.
Ya ɗauki ƴan sekonni yana nazarin leeya kafin ya tuƙa motarsa yayi gaba.
Tana nan kwance a wajen har rana ta hudo ta fara taɓata, anan aka samu masu imani da sukazo suna tambayar abunda yasa take kwance anan kuma cikin rana, sai take gayamusu batada lafiya ne shiyasa.
Cikinsu aka sami wani bawan Allah da yaje yasiyo mata magani harda abinda da zata ci.
Godiya tayi masa sosai inda mutumin bai tafi ba har sai da yaga taci abincin tasha magani.
Sannan yayi mata iznin ta tashi daga nan ta koma ɗan gaba da gidan kaɗan saboda nan ne ba rana sosai.
Kayan ta ɗauka gaba ɗaya tare da barin wajen ta koma inda mutumin ya nuna mata taje chan taci gaba da zaman ta.
A Kwana a tashi har ta share tsawon sati ɗaya da kwana biyu, alhmdullillah jikinta yayi sauƙi sosai idan ka ganta ma zakayi tunanin ita ce ke zazzaɓi a kwanakin da suka gabata ba.
A tsawon waɗan nan kwanaki da ta ɗauka ba wanda ta samu ya taimake ta ko kuma ya bata abinci.
Ita take siyawa kanta komai na bukatar ta har kuɗin suka ƙare ta rasa yanda zatayi.
Shine ta yanke shawarar ta fara tsintar goruna tana saida wa, da kuɗin nan da take samowa da su take cin abinci.
Yauma ta shirya ne da nufin taje tayi tsintar goruna domin ta samu abunda zata ci, tsaye take bakin titi tsayuwar ta kuma yayi daidai da lokacin da akayiwa wasu motoci alamar da su dakatar da tafiya.
cikin wurin ta kutsa ta fara tsintar wasu abubuwan da tana da tabbacin zata sami inda zata siyar dasu. Ta gaban wata mota ta wuce da nufin ta ɗauko wani abun data hango. Mace ce mai tuƙin motar.
Matar da ke tukin kuma tana ganin leeya ta gifta ta kafeta da idanu sosai kamar mai nazarin wani abu ajikinta.
A back sit kuma na motar wata ƙaramar yarinya ce sanye cikin school uniform ɗin ta, glass ɗin back sit ɗin yarinyar ta sauke ta fito da emptyn gora ta jefota waje.
Sakamakon lura da tayi da kallonda matar da suke tare keyiwa LEEYA.
Aikuwa leeya na ganin an cillo gora ta rugo aguje ta ɗauki gorar tare da sakata cikin buhun da take yawo dashi.
"Mum what are you staying at? we are just parked hare and you don't traffic, please can we go home I'm really tired" faɗin yarinyar da ke tare da matar da ta zubawa leeya idanu kawai.
"I'm sorry my kid nima haka kawai na tsinci kaina da kallonta wallahi" glass ɗin motar ta ɗaga ta tayar da motar sukaci gaba da tafiya.
"Mum"
"Na'am mamana"
"Me abunda kikayi yake nufi?"
"Wane abu kuma"
"Saboda me muka tsaya kina faman kallon yarinyar chan bayan kuma an bada damar ko wace mota ta wuce?, she's dirty girl, kuma almajirace fa"
"Common, ki daina mana my kid bana jin daɗin irin ɗabi'un nan naki"
"Mum, how can you be concerned about total strangers, mum ke ba talaka bace taya zaki damu da lamarin talakawa"
"Khuludddd! Please ki gane Allah shi yake ba kowa mana"
"Okay mum amma gskiya ki daina irin haka banaso, idan kika ci gaba da kallon wasu talakawan haka ai za'a yi tunanin ko a cikin dangin mu akwai talakawa, especially yarinyar nan mai mayafi danaga kin tsurawa ido yanzu"
"Yi hakuri my kid bazan ƙara kallon suba kinji, are you happy now"
"Uuuhhhm maybe, let's go home"
Tana gama faɗin haka mum taja motar suka bar wajen.
*******
Tsaye take jikin wani baho da aka zuba shara bakin wani gida, hannunta ɗaya riƙe da buhun da take saka gorunan ta, ɗayan hannun kuma riƙe take da guntun siririn ice mai dan tsawo da langwasa tana tonon sharar da ke cikin babban mazubin shara da ake ajiye wa,
duk abunda tasan za'a siya idan ta ganshi a sharar saita sakashi a buhu.
Haka takeyi tsawon wuni, taje nan ta dawo chan har sai da ta sami abunda zata ci. Bayan ta tsinci abunda zata tsinta a wurin sai tayi gaba, saida tayi tafiya mai nisa a unguwar kafin ta cimma wani makeken gida.
"Masha Allah, gskiya wannan gidan kam ya haɗu Allah yasa masu shi su more"
Leeya ke maganar a zuciyar ta.
ƙara saurin tafiyar ta tayi lokacin da ta hangi bahonda ake zuba shara har biyu bakin gidan kuma suna cike maƙiil.
Da sauri ta isa tayi tsince-tsincen da zatayi,
sosai ta sami abubuwan ta a wurin ba abunda ta bari sai wanda bata amfani dashi domin kuwa buhun da tazo dashi ya cika tabb har ta samu igiya ta ɗaure idan bukatar hakan ta taso.
Tayi farin ciki sosai da faruwar wannan al'amari harta ƙudurce a ranta kullum idan ta taso da wajen da take kwana bazata ƙara biyawa ta ko'ina ba, nan zata riƙa zuwa tana kwasar kayayyakinta.
Har zata juya ta tafi ta hango ɗayan bahon na shara irin wannan a guje ta isa wurin da ɗayan bahon yake,
Isarta wajen yayi daidai da fitowar wani garjejen mutum mai gadin gidan.
Mutumin ya kalleta ya daka mata tsawa,
"ke!, me kikeyi anan?"
"Ba komai ba, kayan bola nake tsinta"
"Ƙarya kike yi ɓarauniya ce ke, shiyasa kika rufe fuskar ki dan kar a gane ki, mai yuwa ma kece kika sace ƙaramin generator da aka kunna a masallaci jiya, da ga gani bakyada gaskiya gashi ko Magana kin kasa".
Kuka ta fashe dashi jiki na karkarwa, duk ta tsorata da jin an laƙa mata sata daga isowarta wurin, sata ma ba ƙarama ba, Karo na farko taji danasani ta mamaye mata zuciya.
"Wallahi thumma tallahi bani bace, bani bace ni ba ɓarauniya bace, wallahi bamma taɓa zuwa nan ba sai yau, Ni Bama ƴar garin nan bace, ban san ma wane gari ba ne wannan na rantse da Allah"
"Ohhh ba ke kika ɗauka ba"
"Ehh wallahi ban ɗauka ba"
ta faɗa tana kaɗa kai alamar ehhh.
"Tau tunda bake bace kije kiyi abunda ya kawoki kiyi sauri ki tafi"
"Tau na gode, nagode sosai"
Ta faɗa tare da nufar bahon sharar da gudun ta.
Mai gadin kho yana ganin haka ya janyo bulalar doki ya nufeta gadan gadan, dayake ita bata ganinsa saboda ta juya baya ne, shiyasa bata ganshi ba sai jin saukar bulalar take ajikinta ta ko'ina.
Ihu ta fara yi tare da neman taimako, kuka take iya ƙarfinta.
Da sauri mai gadin ya juya baya sakamakon ji da yayi an buɗe gate ɗin gidan da karfi.
"Kai!, Lafiya me yarinyar da kake duka tayi maka?"
"Alhaji irin waɗan nan yaran basai sunyi laifi ake dukansu ba saboda ɓarayine ire irensu"
"Meta ɗauka yanzu?"
"Me zata ɗauka dai, amma bata ɗauki komai ba tukunna"
"Kai wane irin sha-sha-sha ne dazaka kama yarinyar mutane kana duka batare da tayi maka laifin komai ba" faɗin matar gidan da ke ƙarasowa bakin gate ɗin yanzu.
"Ayi hakuri Hajiya Babba, nazata itace ta sace generatorn da aka ɗauke jiya" mai gadin ya faɗa yana sosa kansa.
"Ka taɓa ganinta anan ne?"
"Ah ah bantaɓa ganin taba"
"Kana nufin cewa yaune na farko da ka ganta anan"
"Ba shakka hajiya babba yaune na farko da na fara ganinta a nan"
A tare papu da mum suka furta
"kai wane irin wawane, yau ka fara ganin ta a nan shine zaka mata wannan dukan kamar ba wata dabba ko dabbarce ayi mata irin haka. wannan wane irin zalunci ne haka, ga yarinya ƙarama"
"Bata ma motsi wallahi" cewar papu yana ƙarasawa inda leeya ke yashe duk ta galaɓaita.
"Zo ki kamata mushiga da ita ciki, kai kuma wallahi idan ƴar mutane ta mutu sai kasan abunda zaka gayawa hukuma" mum ta faɗa cikin tashin hankali.
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, taya zata mutu Alhaji wallahi ni ban kasheta ba ɗan kaɗan na doketa, wallahi dukan nan bazai kasheta ba, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un yau na bani na lalace Allah ka taƙaitamin wahala"
mai gadin ke magana yana kuka kamar me.
"Tsurawa leeya idanun mum tayi kafin tace Allah sarki nagane yarinyar nan justice"
"Kin gane ta kuma?"
"Ehh wallahi na ganeta"
"Keko ina kika santa"
"Jiya na ganta ɗan