BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   57 / 61

168K to 171K   out of 180.4K words

mata Irin haka.

"Kice na tashi mana Please gimbiya ta" cewarsa yana d'an langwa'be kansa gefe daya yanda yayi maganar kamar da gaske bawa ne a gaban uban gidansa.

"Tohm ka tashi kaji, ai dama ba Ni na saka ka ba"

Mikewa yayi shima ya zauna sukaci gaba da firarsu ta masoya kamar ba abinda ya faru, sai da aunty Rafa'at ta fahimci dare ya soma yi sannan tazo ta sanarmasa, haka bayaso ya tashi ya koma zuciyarsa cike fal da tunanin Leeya ɗin sa.

Washe gari haka suka shirya cikin farin ciki kowa yana mararin ganin ƴan gidan su.

Haduwa sukayi wuri daya gaba dayansu bayan sunyi sallama da larabawan Egypt, sosai amarya da ango suka sami kyaututtuka domin kuwa ba inda ba'a san turab ba a qasahen nan da suka zauna kwana d'ad'd'aya.

Misalin k'arfe biyu da kwata suka dauki hanyar shigowa Nigeria.

A Nan gida Nigeria kuwa sai shirye-shiryen dawowarsu ake, families duk sun qara taruwa, sosai ake qaunar ahalin gidan Khattab waasib saboda tausayinsa da yawan kyautar sa da kuma saurin fahimtar mutane. Uwa uba ga kuma sanin darajar jama'a.

Misalin ƙarfe hud'u da kwata daidai jirgin su yayi landing, nan aka tura drivers babu b'ata lokaci suka dawo da su.

Sai da suka huta sosai kafin fahad da zafaran da kuma matan su harda shi turab din suka koma abuja.

Bai saka ransa da ganin leeya a koda yaushe ba shiyasa bai damu da haka ba.

Dawowarsu Nigeria da kwana biyu shirin su na tafiya spain ya kammala.

Kusan motoci hud'u aka tafi dasu filin jirgi na ƴan rakiya kawai, bayan motocin su fahad da wacce su Khulud ke ciki.
Tun a cikin mota leeyana ke kuka, turab kuwa jin kukanta yake har bangon zuciyarsa da 'bargo, dole tasa ya kyaleta don bashi da yanda zaiyi ne saboda yawan mutanen da ke tare dasu.

Allah-Allah kawai yake su shiga jirgi....!

Misalin ƙarfe 1:30 na rana aka kira sunansu, sosai ta rungume mum da Aleena tana kuka sai da kyar aka rabasu, mum ma kukan take yi.

Gab da zasu shiga jirgi ne zafaran ya dagawa turab hannu alamar ya tsaya.

Tare da fahad sukazo wajensa bayan sun gama bankwana suma, "afuwan Chief turab, na manta kyautarka ne ban baka ba. Amma dan Allah kar aje Kasar turawa a manta damu"

Murmushi mara sauti yayi kafin yace "idan na mantaku na manta kaina zafaran, kune Ni a wannan rayuwar banada kamarku idan kuka cire mahaifana da matata, kaga ba yanda za'a yi na mantaku"

"Kar ka damu muma munsan ba abu mai yuwa bane, yanzu dai ga wannan, karka bud'e anan sai kun isa inda zakusha soyayya"

Sake fadada murmushin fuskar sa yayi yana qara gode musu tare da fatar alkairi.

A bangare na musamman suke, iya sune sai kuma ƴan kayayyakin su duk da ba wasu kaya suke da su masu yawa ba.
Inda aka ware musu a jirgin kuwa bambancinsa kaɗan da d'aki.

Addu'a yayi sosai kafin su shiga, suna shiga kuwa ya zaunar ta ita ya kwanto da ita jikinsa ya matseta tsamm, tisue ya zaro yana goge mata hawaye ba tare da yace uffan ba yana ci-gaba da bubbuga bayanta alamar rarrashi.

Ita kuma ganin jirgi na d'agawa yasa ta qara qanqameshi sosai sakamakon wannan shine shigarta na Farko"

"Sorry dear..... kiyi hakuri kinji. Komai zai wuce zakiga kamar ba'a yi ba....! Ya fad'a cikin sanyin murya mai kamada rarrashi.

A hankali ta daga kanta ta kalleshi suka hada idanu, da sauri ta mayarda nata idon qasa.
Wani irin nauyi da kunyarsa takeji, ga wata faduwar gaba dake ziyarta ta akai akai, tsoro da kunya duk suka taru suka sami mafaka a cikin zuciyar ta.

Lura da haka yasa ya shafa kanta kadan yana sauke ajiyar zuciya.
Wani madanni ya danna akan kujerar da suke zaune, nan take kujerar ta juya ta zama makeken gado.
Kwantar da ita yayi, sannan yayi mata pillow da cinyarsa yana shafa kanta.
Kasancewar da gajiya a tattare dasu yasa Bacci yayi awon gaba dasu.

k'arfe takwas da mintuna goma sha biyar na dare jirgin su ya sauka a Babban Birnin spain.

Jin tsayuwar jirgi da kuma qarar na'urar da take shaidar haka ya saka turab ya gane sun iso.
Ganin har yanzu tana bacci bata farka ba ya dan shafa gefen fuskar ta.
A hankali ta buɗe idanun ta dake cike da bacci ta saka a cikin nashi "mun qaraso...?" Ta tambaya cikin sanyinta.

Murmushi ya sakarmata da fadin "eh hajajju mun qaraso kinata bacci kho"

"Da nikadai nayi baccin zakace haka, sau nawa ina farkawa ina ganinka kana baccin kaima"

"Thom naji,... Amma dai yanzu na rigaki tashi"

Murmushi tayi itama bata qara cemasa komai ba, hannunta ya riqo suka sauko a hankali cikin natsuwa.

Suna fitowa aka fara watsa musu wasu fararen furanni masu matukar qamshi.

""Abun mamaki" ta faɗa a fili ganin mutane masu tsananin yawa, kuma duk kayansu iri dayane da alama kayan ma uniform ne.

Murmushi ya sakarmata tare da kashe mata ido daya. Wani lallausan farin carpet aka shimfida musu sukabi ta kansa har suka isa gaban motocin da akayi packing.

Mutanen da ke tsaye kusa da motar kuwa suna ganin sun qaraso daff dasu suka dinga bud'e wasu qananan Cage's sai ga tsuntsaye kala daban daban masu wani sauti mai dadi.
Sai zagayasu suke suna wake-wakensu na tsuntsaye............

Ba leeya da ta fara shigowa ba, hatta turab daya jima a cikin wadannan mutanen sai da ya kamu da sha'awar irin wannan tarba da suka yi masa. Shikam me zaiyi ya biya waɗan nan bayin Allah.

Ita kuma leeya mamakine fal ranta, ya akayi turab yayi suna har haka ta inda ko'ina ya tafi sai an ganeshi gashi da dimbin masoya. Ikon Allah, taci gaba da fad'a a zuciyarta.

Har a Cikin motar anyi decorations da balloons gwanin birgewa, a bakin wani makeken gida suka yi packing.

Wani Bature ne ya fito da kayansa na sojojin kasar ya bude musu gate suka shiga cikin compound din gidan.

Gidan babba ne sosai irin gidajen nan ne turawa masu dogon gini da muke gani a film.

Fitowa tayi tana murmushi tana kallon ginin gidan har ya shige gabanta yana tafiya bai kula da ya yi mata nisa ba.

Ita kuma bata masan abunda ake ba ta saki baki tana kallon gidan, chak taji an d'aga ta sama....! bai direta a ko'ina ba saib a tsakiyar babban parlourn gidan gaba ɗaya.

"Masha Allah" leeya ta furta a hankali tana sakkowa daga jikinsa kuma. "Gidan nan yayi kyau my King....."

Tsadadden murmushin sa ya sakarmata tare da fadin "Nagode Allah tunda gidan nan yayi miki, muje kiga ko'ina"

Cikin zumud'i ta bishi suka fara zagawa lungu da saqo na gidan 6 bedrooms ne a gidan kuma shahararru, babu wanda bayada kaya a cikin dakunan kuma duk kayan tsadaddu ne na turawa iyakar ganin idanunka.
Sannan 4 parlours, sai kuma 3 kitchens da kuma 2 daining area's.
2 laundry rooms, and 6 bathrooms, sai swimming pool da garden, sai kuma 6 prayer-rooms.
Gidan ya tsaru sosai domin tsayi faɗin tsaruwar gidan bata lokaci ne, babu abunda basu tarar a gidan ba, daidai ta tsinke akwai a gidan komai ya saka anshirya masa tun kafin yazo.

5 rooms gaba ɗaya kayan gyara da shafe shafe ne a ciki har kayayyakin make up.

Wasu rooms guda hud'u kuma duk kayan sakawa ne manya da qanana kuma nata ita kaɗai.
Shoes and bags kam ba'a magana kamar kaje Company.

Babban abunda ya daurewa leeya kai shine komai da ta gani size dinta ne, kuma ita dai tasan basu ta'ba magana akan haka ba.
Cike da mamaki ta kalle shi da faɗin "sadaukina..., ya akayi kasan sized dina haka....?"

Murmushi mai sauti yayi yana laqato hancinta yace "taya bazan san sized din matata ba...."

"Amma harda......"
Kasah qarasawa tayi domin wata kunyarsa da ta lulluɓe ta.

Shikuma daya gane abunda take son fad'a yace"har da su mana, ya ma za'a yi na kasa sani. Idan bansan naki ba nawa zan sani....?"

Idanunta kam tuni sun chanza kala, hawaye duk sun taru tana murmushi take kallonsa;
"duk domin ni kayi wannan sadaukina....?"

A hankali ya d'ago fuskar ta suna kallon juna, hawayen yake shima yace "wallahi idan ina da ikon cire rayuwa dana cire tawa na baki leeyana, ina sonki Sosai Allah shaida haka, ina yimiki halattacciyar soyayya wacce nake fata Allah ya sanya mu a aljanna saboda ita, kamar yanda yayiwa laila da majnoon alqawari. Ya-turab loves you much Leeya" ya qarashe maganar sauran hawaye na gangaro masa.

"Nagode, Nagode sosai jarumi nah, Allah ya sanya alqairi da albarka a zamanmu..." Ta fad'a kukan ta na qara tsananta.

Shima kukan yake sosai ba mai rarrashin wani a cikinsu "yau nine a gabanki a matsayin mijinki leeyana! Ashe zanga wannan rana mai cike da albarka a cikin rayuwata, ashe dama zan mallakeki ki zama tawa, zama na har abada leeyana....?, dama zamu zama d'aya mu zauna a qarqashin inuwa daya, wallahi ban taɓa zaton haka ba, na riga na cire raina da samunki a cikin rayuwata leeyana.....!" Ya qarashe maganar cikin matsanancin kuka.

Itama kukan take sosai tausayinsa kuma na qara shiga zuciyar ta, "damah ace baka yi zaton haka ba ya-Turab, wallahi nima inasonka, wanda ban tashi gane hakan ba sai lokacin da ka fad'a mummunan hali ta dalilinah, ka yarda soyayyata a gareka gsky ce, kuma wallahi bana fatar Ganin ranar da zamu rabu da idanuna ko mutuwa zamuyi ina fatar ta fara daukata domin Ni nasan bazan jure rashinka ba uban 'ya'yana"

Rungume ta yayi tsammm ajikinsa yayi ajiyar zuciya, bubbuga bayanta ya farayi "sorry matar ya-turab guda ɗaya jal, kuka bai dace da kyakkyawan idanun Nan naki ba a daidai wannan lokaci, dan Allah kiyi hakuri kidaina zubarmin da wadannan hawayen naki masu daraja, wanda nayi alqawarin indai inada rai da lafiya bazan ta'ba bari su zuba ba, Dan Allah kiyi hakuri kinji, Yanzu ki tashi muje muyi wanka muyi sallah kinji"

Goge hawayenta tayi tare da tashi tsaye, miqewa yayi shima yana shirin bin bayan ta.

"Ina zakaje....? Kayi zamanka kawai nasan toilet ai ban manta hanyar ba"

"Wanka zamuyi tare mana...."

Ido ta zaro waje kamar zasu fado qasa tace "wanka da kai da wah....?"

Yana dariya yace "dani da matata mana, Annabi yace hakan yana qara dankon qauna"

A shagwa'be take kallonsa irin kallon nan da yake narkemasa zuciya kamar zatayi kuka tace "nidai a'a Please, ko zamuyi ba yau ba kabari wata rana kaji" ta fad'a tana kashe masa ido ɗaya.

"Hummm,,,,,,tau shikenan kije kiyi ke ka d'ai idan kin fito sai nima nayi. Kinsan bana so na sakaki abunda baki niyyar yi ba"

"Na sani my happiness, Yanzu zan dawo in sha Allah I love you" ta fad'a cikin 'kayataccen murmushinta tana yimasa alamar heart da yatsunta ta wuce toilet. zuciyar ta cike fal da farin ciki.

Shigarta ba jimawa ta fito, koda ta fito parlourn bata tarar dashi ba, bedroom din da ke passing sosai da parlourn ta shiga domin tana tunani shima yana ciki.
Tana shiga kuwa taji motsinsa a bathroom, wardrobe ta bud'e ta fito da wata doguwar rigar bacci mai dan kauri wacce ta kaimata har qasa, kuma ta bud'e sosai bata d'ameta ba.
Babban hijab ta ciro shima har qasa ta sanya saman rigar, sannan ta shimfida sallahya tana jiran fitowarsa.

Ganin har yanzu tana jin motsin ruwa da alama bai gama wankan ba ya saka ta bud'e wardrobe ɗin da ta kasance mallakinsa domin kaf kayansa dake parlorn a ciki suke ta fito masa da jallabiya, sannan ta fesa masa turare mai sanyin qamshi. Idan ba kusa kake Sosai dashi ba bazakasan ya saka turaren ba ta ajiye masa akan bed tana jiran fitowar sa.

Sai da ya ɗauki mintuna uku bayan haka kafin ya fito. Yaji dadi sosai dayaga ta shirya sannan shima ta fito masa da nashi kayan.
A gaggauce ya saka sannan yace "muje" yana nuna mata qofa.

"Bakaga na shimfida sallahya ba"

"Ni ba'a nan zamuyi sallah ba, zo ki ga"

Ba musu ta bishi a baya suka fi ta bedroom ɗin, suka shiga wata 'yar siririyar kofa
qofa sukagani gani zagaye da wani daki da akayi gininsa da gilashin azurfa.
Babban zanen dakin kha'a, bah ne a kofar dakin, a samansa kuma anyi jera wasu qananan tasoshi guda biyu daya kan daya sannan akayi alamar wata da taurari a samansu.
A harabar kuma lallausan grass carpet ne shimfid'e, sai wani haske mai kyalli da ya zagaye dakin gaba d'aya.

Leeyana har sauri take ta isa cikin dakin domin ganin wane irin daki ne wannan.

"My love! Wurin nan yayi kyau wallahi tun Kafin na shiga"

Murmushi ya sakarmata hannunsa na cikin nata yace "mu shiga ki gani tukunna"

Ba musu ta biye masa suka shiga dakin "Masha Allah, shine abunda take furtawa a fili da zuciyarta.
"Mijinah Allah ya baka ladar kowace ibada da zamuyi a wurin nan"

"Ameen ya rabbi matata, ke kuma Allah ya baki ladar ibadar da zakiyi a wurin nan"

Lallausan Italian carpet ne mai alamar kha'ah'bah da aka saita ta a qeeblah leme a fadin dakin, kai tsaye zaka iya kiransa masallaci.
Amma ganin irin tsarin da akayimasa yasa idan ka gani shiru zakayi da bakinka kawai.

Bangare d'aya na dakin bayada wani banbanci da masallaci. Bangare d'aya kuwa decorations akayimasa sosai aka fitar da wurin saka litattafai.

Inda ba komai a wurin sai tarin littafan addini da kuma Alqur'ani mai girma. Harda littatafan tarin annabawa.

Ga kuma daddad'an kamshi dake fitowa wanda leeya bata san daga ina qamshin ke fitowa ba.

"Masoyi, anan zamu dinga yin sallah kullum kho"

"Eh, amma ba anan kadai ba, ko wane bedroom yana da irin wannan dakin. Kinsan anan ba musulmai sosai kuma babu masallatai. Shiyasa na gina wannan kinga kiran sallah ne kawai bazamuji ba, amma muna shigowa masallaci"

Idonta akansa tana murmushi mai sauti tace"gsky mijina kai na daban ne, Allah ya qarawa zuciyar ka imani"

"Ameen" ya fad'a yana dai-dai ta tsayuwarsa itama ta gyara tata tsayuwar.
Sallolinsu sukayi cikin nutsuwa bayan sun gama ya dafa kanta yana kwararomata addu'ar da manzon Allah yayi umurni ayi.
Bayan ya gama yimata addu'ar ya fara yimata tambayoyi akan addinin ta.
Babu wani abu da ya tambayeta wanda bata bashi amsa ba.
Cikin tsananin farin ciki da alfaharin samunta ya rumgeta yana yaba mata sosai akan riqo da addini da tayi, yaji dadin hakan sosai.

"Yanzu kuma muje muci abinci kar in barki da yunwa mu koma Nigeria ace ban iya kiwo ba"

Dariya ta yi sosai har haqoron ta suka bayyana, ba zato taji ta ajikinsa.

D'aga ta yayi tsammm har suka iso daining area. Zama yayi tare da d'ora ta akan cinyarsa.

Mamaki Sosai ya rufe leeya har ta kasa cewa komai ganin abinci kala-kala a jere har mamakinta ya kasa boyuwa.

"Mamakin me kikeyi......!?"
Ya fad'a cikin sanyi da nutsuwa.

"Abinci...." ta fad'a tana nuna tari abincin da ke zube sama wawakeken daining table ɗin "waya dafa.......?" Ta kuma tambaya da mamaki.

"Robot...! Akwai su da yawa a gidan nan kuma kowa da aikin da yake, waɗan da suka shirya abincin nan su biyu mace da namiji"

Zatayi Magana ya ɗora hannunsa akan lips din ta "shhhhhhh,,,,,,,,kice Abincin tukunna, zaki san komai daga baya kinji. Wannan lokaci bana tambaya bane na abinci ne kawai"

A baki ya dinga bata abincin har ta gayamasa ta qoshi, sannan shima yaci ya qoshi.

Wani remote daga gefe ya dauka ya dannah wani wuri. Sautin na'ura suka faraji da alama magana take.
Jimm yayi yana saurare kaana ya kuma dannawa.
Robot biyu taga sun jero cikin tariyar su. Suna isowa suka tsaya har saida ya qara danna wa kaana suka fara aikin tattare kwanukan da aka 'bata.
Leeya kam banda mamaki har tsoro ya shigeta sosai, sai da turab yayi mata bayani sannan ya bata remote din tayi amfani dashi, Sai a sannan tsoronta ya d'an ragu.

Bayan sun gama komai ya kuma ɗaukar ta chakk ya rabata da qasa suka doshi wani daki ba wanda suka shiga da farko ba, wanine na daban.

Cikin nutsuwa ya kwantar da ita kan gado ya juya ya fita batare da ɗayansu yace uffan ba.
Tana daga kwance ta miqe a hankali ta kashe bulb din dakin ta kunna bedside lamp.
Kafin kace me nannauyan bacci yayi awon gaba da ita abunka da wanda ya kwaso gajiya.
Cikin baccinta kamar kuma a mafarki taji zafafan sak'onninsa na shigarta.
Hakan yasa ta bud'e lumsassun idanunta dake cike da bacci.
Ta dan tsorata da ganinsa domin ita dai tasan koda ta kwanta baya dakin, sai farkawa tayi ta ganshi.
Da kyar cikin kasalalliyar murya ya furta "na katsemiki bacci kho, kiyi hakuri kinji"

Tana shirin yin magana ya matsa kusa da ita sosai cikin ƴar nutsuwar da ta ragemasa ya hade bakinsu wuri daya ya fara kissing dinta.

Sun dauki tsawon mintuna talatin suna abu ɗaya har ya janyo blanket ya rufe su, bayan ya karanta addu'ar da Annabi ya umurci kowane namiji da yayiwa matarsa a lokacin da suka hadu shimfiɗa daya.

A daren ne turab ya sami nasarar mayarda leeyana cikakkiyar mace, kuma qima da darajar ta suka qaru a wajensa.

Har aka kira sallahr asuba tana qanqame a jikinsa, ko wane motsi nata idan tayi zakaji ya kira sunanta yana sanya mata albarka.

Da kanshi ya kaita toilet ya gasata sosai sannan yayi mata wanka, a daddafe tayi alwala ya nad'ota cikin towel ya dawo da ita kan bed.

Leeyana kam jikinta yayi mata tsami sosai har wani zazzaɓi mai zafi ya rufeta.
Da kansa yayi mata komai, shi ya ciro mata kayan sawa ya sakamata sannan ya dauketa suka tafi prayer-room sukayi sallah ya dawo da ita.
Saman bed ya ajiyeta sai sannu yake jeramata ita kuma kunyarsa duk ta rufeta.
Matseta yayi gammm a jikinsa sannan ya ɗora bakinsa dai-dai kunnenta ya fara karanto mata surorin Alkur'ani cikin zagin muryarsa kamar Balarabe haka yake karatun.

Itama a hankali ta fara bin karatun nasa har bacci ya dauketa, dama hakan yakeso yanaso tayi bacci ta samu ta huta.

Aikuwa tanayin bacci ya janyeta daga jikinsa a hankali ya sauka kan bed din ko dogon motsi baiyiba gudun kar ya tasheta.
Kayan da duk suka bata ya tattara gaba ɗaya ya tafi laundry ya wanke su tasss sannan ya saka a Drayer ya busardasu.

Bayan ya gama kuma ya shiga ciki ya umurci robot dinsa da su hada musu lafiyayyen breakfast.

Nan da nan kuwa suka fara aikin, parlour ya dawo ya zauna haka kawai yake jinsa wasai, zuciyarsa cike da farin ciki.

system dinsa ya saka gaba ya fara aiki sakamakon yayi kwanaki bai ziyarci shafukansa ba.
Fridge ya kalla yaga nisansa dashi kuma gashi yana buqatar ruwa.
Murmushi yayi lokacin da ya tuna remote na hannusa. Ciro shi yayi daga cikin aljihunsa tare da dannah shi.
Ba jimawa sai ga robot ya iso gabansa.
Magana

57 / 61