BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   38 / 61

111K to 114K   out of 180.4K words

sanni dasu".

"Shikenan dai Yanzu muje ki zauna zaifi tsayuwar nan"

Ba musu ta bi bayanta har suka zauna kan shimfida, gaisawa sukayi sosai inda khulud ta kasa nutsuwa saboda kunya da kuma tsoron abunda zai biyo baya, tana tuna munanan kalamai da zagi da cin mutunci wanda tayiwa baiwar Allahr nan. Ita a yanzu ma ji take kamar idan tayi maganar id dayammah ta cemata ba gidan yake ba ko kuma tace mata ba ɗan ta bane.

"Tunanin me kike haka Hajiya ƙarama inata magana bakiji ba"

Firgigit ta zabura kamar wacce ta tashi daga nannauyan bacci ta sauke tagumin da tayi tare da ajiye numfashi mai tsawo sannan tace "dayammah kinsan abunda ya kawoni gidan nan?"

"Shi nake so na sani hajia ƙarama"

"Wallahi bansan ke zan tarar a gidan nan ba, har ga Allah Ni bansan nan kuke zaune ba, dan Allah inaso na roƙeki wata alfarma ɗaya kafin nakai ga faɗin buƙata ta"

"Ki faɗi ko menene hajiya ƙarama, muddin zan iya yi to sai na aikata miki ita"

"Dan Allah dayammah na roƙeki ki dubi girman Allah da Manzonsa ki yafemin duk wani laifi dana taɓa yimiki a rayuwar nan wallahi kinji na rantse wallahi na canja hali ki yafemin"

tun kan ta ƙarasa dayammah ta tari numfashin ta da faɗin "duk wannan Maganar ta riga ta wuce yanzu hajiya ƙarama, kuma abunda ya wuce bai kamata ana taso dashi ba kiyi maganarki kawai karki damu da wannan, kuma wallahi indai ni kika yiwa laifi na yafemiki duk wani abu da kika yiman duniya da lahira. Allah Ubangiji ya yafe mana ga baki ɗaya".
"Ameeen ya ilahi" khulud ta faɗa a sanyaye sannan taci gaba da faɗin

"Nan ne gidansu idrak?"

"Idrak!!" Dayammah ta faɗa kamar a tsorace.

"Eh, idrak manaf nake magana nan ne gidansu"

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un, Hajiya ƙarama dan Allah karkice fréri laifi yayi miki, dan Allah ki sassauta masa Wallahi baisan Matsayin ki bane da bazai......"

"Ba abunda kike nufi bane dayammah, na kamu da sonsa ne kuma matsananciyar soyayyarsa sosai, sai dai shi idrak bani bace gabansa, wallahi babu rokon da banyimasa ba amma ya ƙi amincewa da soyayyata dayammah zaki yarda idan nace miki na durƙusawa idrak da gwiwoyina saboda ya soni. Ni nasan amanar ki ce ke bina, nasan duk abunda nayi muku ne da sauran ma'aikata amanarku ke bina ku yafemin dan Allah kice idrak yasoni dan girman Allah" ta faɗa tana wani irin kuka mai ban tausayi kamar ba ita ba.

"Shine kika biyoni har gida, kikazo ki haɗani da mahaifiya ta, Annah dan Allah na roƙeƙi ki fitar da bakinki cikin wannan maganar, wallahi khUlud bata cikin tsarin matan da nakeson aura kwata kwata batada halayen kwarai, Annah khulud batada mutunci bata mutunta kowa hatta malamai bata mutuntawa balle ɗalibai, Annah ta, dalilinsu ne saboda sunga iyayensu manya ne agari aka koreni inda nake faci kuma su sukazo har wurina suka cimin mutunci suka wulaƙanta sana'a ta, daga baya kuma suka saka iyayensu suka tada ni daga rumfar da nake samun abincin da muke sakawa a bakinmu Annah. Shin kina farin ciki da wannan yarinyar ta zama surukarki Annah, inajinki Annah ki faɗamin, Tun Sa'adda kuka fara magana da ita ina jinku ina nan bakin kofa tsaye ina jinku idan na fahimta wannan itace KhULUD K. WAASIB wacce kikayi aikatau gidan su shekarun da suka shuɗe, Annah wannan yarinyar ita ta ruguza farin cikin ki, ita ta tarwatsa plain ɗin da kika jima kina haɗawa har nazo na samu kinyi nisa, Annah ta dalilin wannan yarinyar ne muke zaune cikin matsanancin talauci da Rashin hujja mai ƙarfi, annnah ta dalilinta ne muke zanune cikin tauyewar rayuwa, daba dan itaba da yanzu komai yana zuwa daidai yanda aka tsara, da badan ita ba da yanzu mun haɗa karfi da karfe da mahaifinta mun ruguza shirin da fairozha ke shiryawa, da mahaifinta ba azzalumi bane da yanzu......"

"Dakata id, ya isa haka, mahaifina ba azzalumi bane baya zaluntar kowa" khulud ta tare shi a tsawace cikin kukan da yaci ƙarfinta, sai da ta ɗan daidaita numfashin ta dake ƙoƙarin tsayawa sakamakon ciwon ta na asthma da ke kokarin tashi sannan taci gaba da faɗin,
"kayimin adalci id, nace kayi min adalci.
saboda inasonka, kai kuma baka sona bashi zai saka na zamo sillar waɗan nan abubuwan ba, sannan ka tuna shekaru sunja yanzu. Kuma nayi imani da yanzu ne bazan taɓa aikatawa dayammah wannan ba nasani! Ka gayamin menene farin ciki a cikin Rayuwarku dana tarwatsa, menene plain ɗin ku dana ruguza, menene?, wallahi duk wannan abun da kake magana akai bansan dashi ba, abunda nasani kawai na saka an kori dayammah a gidan mu tare da karyar ta mareni alhali bata mareni ba, kuma nayi hakane kawai saboda banasonta a cikin gidan mu a wannan lokacin, kuma bayan haka ba'a barta ta tafi haka ba sai da aka biyata ladar aikin da tayi shin menene laifina a cikin wadannan abubuwa daka lissafa"

"Kinaso ki sani khulud!?, na ce kinaso ki sani" ya faɗa cikin tsawa da fushi "to kije ki tambayi mahaifinki dan wannan maganar ba taki bace ta mahai....."

"Idrak!!!!" Dayammah mahaifiyar sa ta kira sunansa ƙwallah na cika mata idanun.

"Annah dan Allah ki dakata na faɗa mata, har sai yaushe abun zai tsaya Annah, kinada shaidodi da yawa da zasu tabbatar da haka, meyasa? Me yasa bazakije ki sameshi kuyi magana ta fahimta ba Annah, tsoro kikeji"

ya faɗa yana takowa gaban mahaifiyar tasa, "bakyaso yasan laifin mu ne ya shafi mahaifinsa Khattab har fairozha ta kasheshi, bakyaso yasani, bawai ina kwaɗayi bane Annah ta.
nima inaso ki samu farin ciki da kwanciyar hankali kamar yanda mahaifiyarta ke ciki, duba kiga Annah har bauta kikayi musu tsawon shekaru duk baki aikata komai akai ba, kin kasa yimusu bayanin komai dan Allah a tsayarda abun haka kinji mahaifiyata dan Allah nake rokarki akawo ƙarshen komai".

Da sauri khulud ta zube kasa kan gwiwoyinta gaban dayammah domin ita gaba ɗaya kanta ya rufe, maganar kisa, me idrak da mahaifiyarsa suke boyewa, dama akwai sanayya tsakanin mahaifin ta da mahaifiyar idrak, innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un meyake Mala'ikun faruwa.

A gaban Annah dayammah ta durkusa tana kuka tace "dan Allah ku taimaka ku fitar dani duhu dayammah menene tsakanin ku da pa, me ya aikata muka. Nasan mahaifina baya cuta kuma bayason a cuceshi, wallahi inada tabbacin idan ma cutar ku yayi bada saninsa bane, yakamata kuje ku sameshi ku yi masa Magana domin a Tsawon shekarunda naji kuna faɗa Maganar ba karama bace dan Allah kije kiyi Magana dashi, wallahi nasan ko mum bata san da wannan ɓoyayyen al'amari ba, koda bazaku gayamin ba shi kuje ku gaya masa ku daina kallonsa da laifin da baisan ya aikata ba". Juyowa tayi ga id ta kallesa da rinannun idanuwanta da sukasha kuka tace "id kayarda Dani wallahi bansan su amrah sun saka an tadakai rumfar da kake aiki ba na rantse maka da Allah, kuma wallahi ko ranarda mukaje inda kake aiki ɗin nan Ni ban saka bakina ba, bamu taɓa samun saɓanin da Raudha da Amrah ba sai ranarda suka yimaka wannan abun, kuma tun daga ranar na daina sakar musu fuska, wallahi danasan an tada kai bazan zuba ido ba, dan Allah kayi haƙuri kaji in sha Allah zanyi Magana da papu ya samamaka wani aiki".

Wata gigitacciyar tsawa ya daka mata har saida kayan cikin ta suka motsa "fitar muna daga gida!" Ki tashi ki fita nace ko gidan kune nan".

Da sauri mahaifiyarsa ta kalleshi tun kan tayi magana yace "Annah kiyi shiru".

"KhUlud! Ki fita daga gidan nan tun muna shaida juna wallahi" yana faɗin haka yayo kanta da sauri ta miƙe ta fita daga gidan ranta na mata ƙuna.

Motar ta ta koma domin tun zuwansu kofar gidan ta bama driver kuɗin adaidaita tace masa ya tafi kawai zata jima a gidan.

Tana shiga motar ta ɗan jingina bayanta a sit ɗin motar, ta ɗaga kanta sama wasu zafafan hawaye na gangarowa a fuskar ta.

Ji tayi ambuɗe motar an shigo sai dai bata buɗe idanun ta ba kuma bata motsa daga yanda take ba.

"Meya sameki kike kuka?" Taji sanyayar muryarsa ta dira a dodon kunnenta.

Da sauri ta ɗago kanta sai dai tana ido huɗu dashi ta sake fashewa da matsanancin kukan da tayi a baya.

Da sauri ya dafe kansa, saboda tsorata da yayi da ganin yanda take kuka, kuma shi a Duniya ba abunda yafi tsana kamar sautin kuka musamman ma na mace, a can baya kullum da dare sai annahnsa tayi kuka sosai sannan take iya kwanciya, kuma baisan Dalilin haka ba, idan ya tambayeta dalili kuma tace masa zai sani ko ba yau ba.

"KhUlud ki dakata dan Allah, nine fa idrak ki faɗamin menene dalilin kuka har haka, bayan kuma gani"

"Id nasan abunda ya zo dakai nan, kazo ne ka bini gidan mu kaga mahaifina ko, dan Allah menayimaka da ka tsaneni haka id"

"Shhhhh" ya faɗa tare da saka ɗan yatsansa a bakinsa alamar tayi shiru "karki sake faɗin na tsaneki khulud ni ba wanda na tsana, ban iya ƙiyayya ba kuma bansan yanda ake ba, ban iya tsanar mutum ba balle na tsaneki, ki kwantar da hankalinki kinji in sha Allah komai yayi fine, yanzu kije gida zanzo na sameki muyi magana kinji, kiyi shiru ki daina kuka banason kukan mace yana sakani ciwon kai mai tsanani"

"Ah ah Id, idan har da gaske kake abunda kake faɗa sai dai kazo muje gidan yanzu, domin idan kace zakazo, ka faɗa ne kawai banada tabbas kaga ko gidanmu baka sani ba, kuma gashi banada number ka ma dan Allah ka biyoni muje"

Murmushi yaƙe ya danyi wanda ta gaza gane ma'anar sa yace "nidai kije kawai ai ni nace zanzo kho, kinga ban shirya zuwa gidanku ba yanzu amma dai zanzo kinji kar ki damu"

"Kar na damu! Kar na damu fa kace id, Dan Allah gayamin yanda zan hana damuwa yin tasiri a raina bayan bana cikin zuciyarka da Rayuwarka"

"Ni na faɗa miki bakya raina da zuciyata, na gargaɗeki a karo na Farko ki daina amfani da Maganar da kikeji ranki na raya miki, kije gida sai nazo"

"Dan Allah to ka bani number ɗinka" ta faɗa tana zaro dalleliyar wayanta daga cikin jakarta"

"Banida khulud, da inada wayan da na baki number na saboda a halin yanzu danasan komai nafiki bukatar number ɗin wani da yake gidanku"

"Ina wayanka take?"

"Na gayamiki banida, kwana biyu kenan da suka shuɗe, Annah batada lafiya na siyarda wayan nayi mata magani, domin inda nake samun kuɗin maganin kun saka an toshe min"

"Dan Allah id kayi hakuri, wallahi banida masaniya, ka karfi wayan nan tawa bara na cire sim card dina idan naje gida zan saka a wata wayar kayi amfani da wannan, duk ranar da kaje gidan mu sai na baka wata sabuwa"

Sosai ya haɗe fuska kamar bashi ba, yace "kinaso muyi faɗa"

Hannu ta saka ta dafe bakinta tana zare idanu tace "banaso sai dai idan kai kakeso zuciyata ta buga shikenan"

"Taya zan so zuciyar ki ta buga tun yanzu bayan ban gana da mahaifinki ba, idan zuciyar ki ta buga wazai min iso"

"Babu" ta faɗa ba tare da ta gane takamammen abunda yake nufi ba.

"Tau kije gida sainazo"

Daga haka ya buɗe kofar motar ya fita, da ido kawai ta bishi har ya shiga gida sannan ta tayar da motar ta ta tafi ranta yana washewa a hankali.







Bayan ya shiga gidan ya karaso kusa da mahaifiyar shi ya zauna sannan ya ɗora kansa kan cinyoyinta yace;
"Annah naje kuma nayi mata magana na rarrasheta har ma na gayamata zanje gidan su kinji Annah ta, in sha Allah bazan zama butulu mai Rama alƙairi da sharri ba, wallahi tun farko da nasan ita ƴar gidan hajiya fanaya ce bazan yi mata haka ba, ki yiwa Allah karki ƙara zubarda hawayenki a kan wannan kinji"

"Allah yayi maka albarka fréri, haƙiƙa ko dan mahaifiyarta taci muyi mata ragowa".

"Amma Annah dan Allah idan bazaki damuba inaso in tambayeki"

"Ina jinka frére faɗi tambayar ka idan na sani zan gaya maka"

"Annah" ya kira sunanta da nutsuwa sannan yaci gaba da faɗin "Annah ya akayi hajiya fanaya ta dawo rayuwar ki bayan sun koreki daga aikin gidan batare da sunga ne wa idanun su laifin da kika aikataba, taya ta dawo rayuwar ki har ta taimakawa karatuna nakai har haka?"....................✍🏻
















Ep. 39














______________________sai da Annah ta ɗan niiisa sannan ta kalli idrak ta fara bashi labarin yanda komai ya wakana a lokacin da khulud ta saka aka koreta a gidan.

"Bayan na fito da kayan da nasan nawane a gidan kamar yanda Alhaji wato mahaifin khulud ya umurce Ni, na fito dasu wajen gate din gidan na tsaya, sai sharar hawaye nake saboda bansan inda zanje ba, tun farkon zuwana garin suleja lokacin kana yaro karami sosai baka wuce shekaru biyar ba a duniya, a hanya na haɗu dasu hajiya fanaya kazo tsallaka titi suka buge ka da mota, su suka daukeka harma ni mukaje asibiti, ita hajiya ita ta biya kuɗin da aka yimaka magani har sai da ka warke gaba ɗaya sannan suka daina yimana hidima bayan kudin da suka bamu masu dan yawa.

An sallamemu a asibitin suka saka mu a motarsu muka nufo cikin gari.

A cikin motar take tambaya ta inda zasu saukeni, sai nake gayamata labarina cewa Ni bakuwace bansan kowa ba, kuma bana da miji rana ɗaya aka nemeshi aka rasa, ta tausaya min matuƙa inda take tambayata zan iya yin aikatau.

Na amsa mata cewar zan iya, tace min ba damuwa muje gidansu sai tayi magana da mijinta itama, da wannan maganar muka tsaya, sai dai abunda ya bani mamaki shine da mukaje gidan mai gidan shima ya tarbemu hannu bibbiyu kuma ya amince amma da sharadin idan ƴarsa bata yarda da zamanmu a gidan ba bazamu zauna ba, na yarda akan hakan nima sai addu'a nake Allah ya sa kar yarinyarnan ta ƙi amincewa,

Cikin ikon Allah yarinyar na zuwa aka tambaye ta ta amince amma da qyar da sudin goshi, sai da aka haɗa da rarrashi da komai kafin ta yarda na fara aiki a gidan, wulaqanci yau daban, na gobe daban a hannun yarinyar.

Bata sonka ko kadan a lokaci, ta Dalilin hakane yasa na mayarda kai makarantar kwana kaci gaba da karatunka, a kwana a tashi har wannan kaddara ta faru yarinyar nan khulud ta saka a ka koreni a gidan, dana fito na rasa inda zanje, dama can bansan kowa ba, ina zaune dan nesa da gate din gidan najiyo karar wayata da alamu kirana ake, nayi mamaki sosai ganin hajiya fanaya ce mai kiran nawa na daga ina goge hawaye, kuma ina saurar abunda zatace "hello, dayammah kina jina"

"Eh ina jinki hajiya, wallahi Ni ban mari khulud ba, hasali ma ban taɓa nufin dukanta ba, tun zamana a gidan, ko magana da tsawa ban taba yimata balle musu, balle har nakai ga d'aga hannu na mareta"

"Nasani dayammah, nasan baki aikataba kuma ki kwantar da hankalinki kinji, justice ya d'auki zafi sosai kuma ya riga yayi rantsuwar cewa bazaki koma gidan da sunan aiki ba"

"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un" na fada ina ƙara sakin kuka.


"Yi hakuri ki daina kuka, yanzu kina ina?"

"Ina Wurin bishiyar nan ta lim wacce ke kallon gidan naku"

"Okay karki damu, kiyi zamanki anan zan aiko da shuraihu driver yazo yakaiki gidan da zaki zauna, na saka ya binciko karamin gidan haya unguwar tsohon bariki inda zakici gaba da zama amma sai kinyi hakuri, saboda unguwar tsohuwa ce gaskiya, kuma cikin nasara ansamu gidan, sannan ki karɓi number ɗinsa idan yazo, duk abunda kike bukata ki kirani a waya ki sanardani, idan kuma bazaki iya ba shi ki kirashi ki gayamasa sai ya faɗamin, koda bakyayin aiki a gidan mu idan wa ta yayi lokacin da ake biyan ma'aikatan gidan nan za'a dinga fitar miki da kasonki kamar yanda ake miki lokacin kina nan, kuma zan dauki nauyin karatun yaronki harya kammala baki daya, kuma zanyi masa tsaye ya sami aikin da zai dogara da kansa bayan ya kammala karatun karki damu, sannan kuma na saka muku abinci a boot din motarda shuraihu zaizo da ita, kiyi hakuri kinji Allah ya sauwaqe sai anjima"

Doskarewa nayi da wayar a kunnena domin na rasa da wane baki zanyiwa hajiya fanaya godiya, ban ankara ba sai ji nayi an katse wayar, sake danna wa nayi da nufin in mayarda kiran tare da kokarin tattaro ƴan sauran kalamaina wajen yimata godiya, sai ganin mota nayi a agabana.

Shuraihu ne ya fito yayimin bayanin komai nikuma na shiga motar, duk abunda Hajiya fanaya ta faɗa ta cika, kuma har free scholarship din da kake gani kamar ka samu wallahi saida da tayi ruwa da tsaki kafin daga bisani ka samu".

Dayammah ta faɗa tana kallonsa.



"Gaskiya Annah wannan hajiya fanaya tanada kirki sosai, wallahi Allah danasan itace ke dauke da nauyin mu tsawon waɗan nan shekaru da ban kwatanta yiwa khulud haka hakaba, duk wani jinin Hajiya fanaya bai cancanci tozarci daga garemu ba, amma meyasa fairozha ke ƙoƙarin ganin bayan ahalin waasib kabil?"

"Ba yanzu yakamata kasan labarin fairozha da mahaifinka ba idrak, amma ka kara hakuri lokaci yana nan tafe"

"Annah, har sai yaushe zamu tsaya jiran lokacin, a yau ba gobe ba Annah, zanje na sanarwa da Khattab waasib asalin mu*

"Ban amince ba idrak, wallahi ban amince kaje gidansu ba yau da nufin bayyanar da ko mu su waye, domin kafin waasibudden mahaifin Khattab ya rasu ya gayamusu ko wacece ta yi masa asiri, mainah matar waasibudden tana gidan Khattab yanzu haka kuma tasan da labarin fairozha, kana tunanin idan munje bazasu kamamu a matsayin munsan abunda fairozha ta aikata ba".

"Shikenan, amma banaso ki saka kanki cikin damuwa ko ɓacin rai saboda wannan abun danayi, kinji dan Allah" ya faɗa ya na yin fuskar tausayi.

Shafa kansa tayi kaɗan tace"shikenan, bazan saka ba Allah yayi maka albarka kaji"

"Ameeen ya rabbi annah bara na fara aikin girkin dare kho"

"Kullll, karka sake ka shiga madafah na gayamaka, duba kaganka fa wai a ce kana girki da girman nan naka"

"Haba Annah, idan banyi ba waye zai yimiki, ai banace zan dinga yi kullum bane idan jikinki ya warware gaba ɗaya shikenan ai

38 / 61