Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
matar aure zaki shigo dakina me kikazo yi"
Turab ya faɗa ranshi yayi ƙololuwar ɓaci.
Sosai ta tsorata da ganin matashin balarabe a gaban ta saboda tsabar tsoro tama rasa abunda zatace sai idonunta masu ban tsoro da ta tsureshi dasu.
Tsawa ya kuma daka mata saidai hantar cikinta ta kaɗa. da gudu tabar ɗakin, baima kulaba kawai ji yayi ta wuce ta gabanshi babu shiri.
Gudu take ko kallon gabanta batayi, sai kawai tayi ta faɗi kan stairs.
Tayi missing step ta bata kula ba har ta faɗi hannuta ya daki bangon wurin kanta kuma ya bugu a ƙasa, ƙara ta ƙwallah domin ji tayi bazata iya tashi daga wurin ba.
Mum dake zaune a parlour tana waya taji ƙarar da leeya ta kwala, da sauri mum ta ƙara so wajen "subhanallah leeyana lafiya" mum ta faɗa tana kokarin miƙarda ita.
Cikin tsananin azaba ta miƙe tsaye a daddafe ta sauka daga kan stairs ɗin.
"Sannu Leeya, ya akayi kika faɗi har haka"
Cije bakinta tayi cikin tsananin wuyarda take sha yayinda tazo lankwasa hannunta da kyar ta furta"mum nayi missing step ne".
"Ayya sannu ina ke miki kiwo yanzu" mum ta faɗa tana dudduba jikin leeya.
"Ba inda ke min ciwo mum kawai kaina ne ya ɗan bugu kibani maganin ciwon kai"
"Anya kuwa ba inda ke miki ciwo banda kanki, idan akwai wani wurin ki faɗa ko asibiti ne aje kokuma a kira Turab ya dubaki"
Jin an ambaci Turab yasa ta tattaro duk wata dauriya ta azawa kanta ta miƙe tsaye da kyau tace "No mum dan Allah kar akirashi a bari ya huta yanzun nan ga ya dawo, ki barshi ya huta pls mum Dan Allah. Kibani maganin ciwon kai kawai inaso naje na kwanta"
Leeya ta faɗa cikin ƙarfin hali, domin kuwa da ana ganin fuskar ta da za'a a fahimci tanajin ciwo a cikin jikinta.
Magani da ruwa mum ta kawo mata ta sha, godiya tayiwa mum daga nan ta koma bedroom ɗin ta.
Tana isa ta faɗa kan gadon ta wani wahalallen bacci yayi awon gaba da ita..............✍🏼
BAYAN WUYA......
By RUMANA M DIGGI
EP.18
___________sai kusan karfe huɗu da rabi, na yamma ta farka daga baccin, koda ta farka bata jin karfin jikinta ko kaɗan, ga uban zugi da hannuta ke yimata. A daddafe ta shiga toilet ta ɗauro alwala ta fito.
Tana kaffara sallar mum ta shigo ɗakin tazo ta dubata, sai da ta jirata ta sallame sallar la'asar tayi addu'a. Sai a sannan mum ta kalleta tace" leeyana sannu da jiki ina fatardai Kinji kin ji sauki kho"
"Ehh mum wallahi kuwa naji sauƙi sosai alhmdullillah".
"To Masha Allah, ai haka nakeso naji, kin ci abinci kuwa?"
"Ah, ah mum banciba amma bana jin yunwa, inaga sai zuwa dare zanci".
"Ok to Allah ya kaimu"
"Ameen summah ameeen mum, nagode sosai".
Ficewa mum tayi daga ɗakin. Tana fita leeya tayi kwanciyar ta kan sallahyar da tayi sallah.
KADUNA....
"Okay ba da damuwa Dr. Insha Allah za'a yi yanda kace, amma yanzu menene abun yi batun transfer da muke nema"
Daga cikin wayar aka amsa masa da cewa" batun transfer wannan ma ba matsala bace idan kun tashi kawai kuzo, duk ranar da kukazo za'a baku"
"Ok tau Dr. Muna ƙara godiya sosai Allah ya saka da alƙairi"
"Ah ba komai karka damu, Nima Nagode sai anjima"
"Yawwa to mujima Lafiya" faɗin dad yana katse wayar.
"Hajiya kinji yanda muka yi dashi kho" cewar dad yana kallon mummy.
"Ehh naji Alhaji, amma kuma me ka gani game da cewa da yayi taci gaba da shan magungunan, anya kuwa wannan cigaba ne kuwa? Naga kafin ta fara shansu duk bata irin haka. Amma tana fara amfani dasu komai ya taɓarɓare"
Shiru yayi na wasu mintuna kamar bazaice komaiba"Nima abunda nagani kenan hajiya, ai shiyasa nayi shawarar mubar ƙasar nan da ita, amma yanzu kinga komai ya kusa zuwa ƙarshe tunda abunda mukeyiwa jira yazo. Gobe ne taron walimar idan an kammala kinga shikenan ba saura, sai muje can BHOPAL ɗin a gwada nasu kho, duk da nasan za'a sami nasara da ci gaba in sha Allah".
"Tho Alhaji, idan mun dawo sai a fara shirin tafiyar ba damuwa".
Daga haka ba wanda ya ƙara faɗar komai kan maganar nan, fira ta ɓarke a tsakanin su.
A chan bedroom kuwa Rukhshanah ce da FANNAH da MAYAH.
Rukhsha kuwa sauƙi ya samu sai surutu take zubawa kafin anjima ta riƙice ta daina cewa komai, kuma ta daina sauraren komai dama haka take tun lokacin da ta fara shan magungunan ASHMED HOSPITAL.
"MAYAH kice gobe zamuje naija state kenan wow, ba dama waya ganmu" cewar Rukhshanah tana fito da kaya.
Dariya MAYAH ta kece da ita tana faɗin"wallahi kuwa gobe akwai chasu, Please RUKHSHA yanda kike chocolate colour ɗin nan mai wahalar samu, ki matsa ki samamana guy ɗan suleja Kinji".
Wata uwar harara Rukhshanah ta watso mata kafin tace" ai ke zancewa yanda kike da ƙirar ƴan indian nan ki taimaka ki samamana, gobe fa akwai kallo zanga yanda maza zasu dinga somewa da ganin ƴan india a gabansu".
"Hmmm, lallai kho sweet Rukhsha harda su zolaya kenan ba komai mun gode, ke kho twiney bakyacewa komai lafiya kuwa. Faɗin MAYAH tana kallon FANNAH.
"Nima abunda nake shirin cewa kenan fa MAYAH amma kika rigani, meyake damunkine sweet FANNAH.
"Uhhhhhm nikam ba abunda yake damuna kawai naga kuna maganar samarine, Ni kunsan ƙaramace ban isa ba shiyasa ban shiga batun nakuba".
Dariya suka kwashe da ita gaba ɗaya, domin har ga Allah itama FANNAH ta bama kan ta dariya da abunda ta faɗa.
"Yanzu dai ba wannan ba, batun yarinyar nan khulud take ko wah?"
Rukhshanah ta tambaya tana jiran amsarsu.
"Kedai bari Rukhsha wallahi idan muka baki labarin yarinyar nan zaki sha mamaki, da dad ɗin mu da papunsa yaya da ƙani ne mahaifi, da mahaifiyarsu duk ɗaya da dad. Amma wallahi karkiso kiga wulaqanci da take mana idan mukaje gidan, kamar ba familyn gidan bane mu" cewar FANNAH.
"Hummm, ai wallahi twiney ke kike hanani kirbamata uban duka, tunda kinga a part ɗaya muke idan mukaje gidan ga bedroom ɗin ta ga namu, amma wallahi yariyar nan idan mukaje bata yarda ta kwana part ɗin nan saidai taje parlour ita kaɗai ta kwana"
"Twiney kenan, wallahi kinga duk wannan da kike gani bawai banaso ki daketa bane, ina tsoron abunda zaije ya dawo ne. Mu mukazo gidansu, bamuda ikon mu daketa har cikin gidansu duk abunda tayi mana, kuma Ni banga ma amfanin mu daketa ba domin damu da ita duk abu ɗayane. Bazai yu a taru azama ɗaya ba dole akwai banbanci saboda haka indai duniyace gata nan ita zata karantar da ita".
"Gaskiyar kice sweet FANNAH amma kuma wannan ai rainine. kikace akwai shekara ɗaya harda wata uku tsakaninku da ita kho, means kune yayanninta kenan" Rukhshanah ta faɗa cike da tsanar halayen khulud.
"Ehh wllh mune yayanninta, amma kinga twiney ce ke janyo mana raini wurinta. Tunda kinga komai tayi cewa take a ƙyaleta"
"Hmmm, kedai ki bari kawai. gaskiya gobe saina koyawa yariyar nan hankali idan ta shiga gonata, lafiyarta idan bata kulani ba Nima ba ruwana da ita, bazan kulata ba shikenan. Ni wulaqanci ne banaso kawai" fadin Rukhshanah.
"Sweet Rukhsha kenan, ai twiney ce bazata barki ba. Tsoron ta yayi yawa, amma ki bari kigani kawai Allah ya kaimu goben"
Haka sukaci gaba da firarsu, da kuma yanda gobe zata kasance garesu idan Allah ya kai mu.
*K. MANSION, SULEJA NIGERIA*
Misalin ƙarfe 2:13am na dare Leeya ce kwance a bedroom ɗin ta sai faman murƙususu take.
Wani irin mirdawa cikin ta ke yimata har yanda baza'a misaltaba.
Sai matsar kwalla take cike da azaba.
Haka take duk ƙarshen wata sai tasha wahala tukkuna kafin tayi period. Sosai cikinta ke yimata ciwo,
Idan kuma mirɗan da yake da ciwo ya dan sassauta sai ta sami lipton mara sugar da kuma paracetamol ta hada tasha, shine abun zai yi sauki.
Yanzu ma haka ta duba ba Lipton a ɗakinta gashi kuma Lipton kawai zata samu tayi amfani dashi.
To anan ne zataji sauqi.
Miƙewa tayi cikin ƙarfin hali ta yanke shawarar fita ɗakin nata taje kitchen ko zata samu.
Laluba fuskar ta tayi taji da niqab din ta yana nan bai fita ba, domin a yanda takejin raɗaɗin ciwon hannunta da kuma cikinta dake yimata azabar ciwo sai taji kamar ba mayafin a fuskar ba shine dalilin da yasa ta laluba fuskar ta tah.
Wayarta ta fara dudduba wa cikin duhun dakin tana lalubawa, har hannunta ya sauka a bedside drawer ta janyo wayarta. Da haske screen tayi amfani ta dakko wani niqab ta sauya domin ruwan hawaye ya jika wanda ke fuskarta.
Wardrobe ɗinta ta buɗe ta janyo dogon hijab har ƙasa tasaka kan rigar baccin da ke jikinta, a hankali take tafiya har ta sakko ƙasan parlourn da jan kafa da dafar bango. Kana ganinta kasan ba lafiya take ba saidai kho karfin hali.
Parlourn tsittt ba motsin komai, kuma bakajin ƙarar komai saina agogon da ke like a bango parlourn.
Tafiya take kamar mai sanɗa tana waiwaye, kamar wacce tazo yin sata.
Tana isa kofar kitchen ta fara buɗe kofar a hankali, ƙarar buɗe kofar yana tafiya a hankali, har ta bude kofar gaba daya. Sannan ta shige kitchen ɗin.
*****
A daidai wannan lokacin kuma Turab ne zaune a dakinsa sai faman aiki yake da system. Domin kuwa bayajin bacci ko kadan, hasali ma yafi jin dadin aiki tsakar dare yanda ba hayaniyar komai.
Sosai yakejin yunwa domin tun Abincin da sukaci a restaurant bayan dawowarsa airport har yanzu bai saka komai a cikinsa ba, ko fita ma baiyiba yau gaba daya
Mikewa yayi ya rufe system dinsa, sannan ya fita ɗakin.
down stairs ya sakko da nufin shiga kitchen ya samu ko Noodle ya dafa domin bayajin zai iya bacci idan bai ci abinci ba. Hasali ma yunwar ce ta hana masa jin baccin amma yasan daya koshi shikenan. Saboda baya wasa da Cikinsa ko kadan.
Hanyar da zata sadashi da kitchen ya nufa shima, da mugun mamaki ya kara kurawa kofar idanu wacce ya hango ta wangale kuma da alamar akwai mutum a ciki tunda gashi har hasken da ke ciki yana iya hangowa.
"To waye a ciki" Turab ya faɗa a zuciyarsa.
Kashe fitilar wayansa yayi yaci gaba da tafiya cikin sanda har ya isa daff da ƙofar inda yake hango leeya da duk abunda take.
Ita kuwa leeya bayan ta gama hada Lipton din tasha, sai ta jinginar da bayanta da kitchen cabinets domin ita kadai tasan abunda takeji.
Sake dauko kofin tayi ta kafa a bakin ta zata kuma kurɓa Lipton ɗin, kamar daga sama taji ance,
"wacece ke?"
Wata masifaffiyar kaduwa da tsoro suka ziyarceta a lokaci daya har ya haddasa mata sakin Lipton cup ɗinda ke hannun ta jikinsa, ruwan Lipton ɗin masu ɗumi suka zuba a jikinsa kuma sun taba ko'ina a gaban rigar sa.
A matuƙar tsorace ta fara kuka, muryar ta na rawa kamar mai iƙina tace "dan Allah kayi hakuri wallahi naji tsoron ganinkane, saboda banji motsinka ba harka shigo nannnn kuma......."
Bai jira ta ƙarashe maganar taba cikin tsananin bacin rai da takaici ya fara matsowa kusa da ita,
ita kuwa tana ja baya har takai ga bango. Kuma ba yanda zatayi ko dogon motsi ta gagara yi.
Sosai ya matso kusa da ita har suna iya jin numfashin juna, hannayensa biyu ya saka gefen damanta dana hagunta ma'ana (ya sakata tsakiya kenan).
Cikin matukar ɓacin rai yace" wacece ke, ki buɗe fuskar ki. Kece dazu na kamaki kina Min bincike a ɗakina kho wallahi sai kin gane kuskuren ki, Ki buɗe fuskar ki nace" ya faɗa cikin ɗaga murya.
Ƙara mannewa da bango tayi domin tana ganin ko buɗe fuskar zata yi bazata iya ba saboda sunyi kusa dashi sosai, kuka ta fashe dashi domin kuwa tana ji shikaɗai zatayi a wannan lokacin ta sami sauƙi.
"Rufemin bakin ki wallahi kona cire shi" ya faɗa yana ƙara tamke fuskar shi.
Da sauri ta gimtse bakinta har ta saka hannayen ta biyu ta rufe bakin ta, taji ciwon sosai da hannunta daya ke yimata zogi sakamakon amfani da tayi da shi ciwon ma kamar ƙara daɗuwa yake yi.
"Zaki buɗe fuskar ko me kike jira Ni abokin wasan kine da zan tsaya ina maki magana kamar ba dake nake ba" cewar turab a hasale.
Ba zato ba tsammani kawae yaji ta banke hannunsa ɗaya tafita wajen da gudu tana dafe da cikinta.
Ran sa yayi ƙololuwar ɓaci bisa wannan abun da tayi masa"Ni hmmm, lallai kuwa saidai idan bakya gidan nan amma wallahi sai kin gane dani kike zancen".
Turab ya faɗa yana fitowa daga kitchen ɗin domin yunwar da yakeji tama tafi saboda tsananin ɓacin rai.
Washe gari kuwa tunda sassafe Turab yayi sallama da mum zaije Abuja gidan Abokin sa dasuke can Mexico a tare, kuma ya faɗamata har fahad ɗin dad ƙarami ma yana can tun jiya, shiyasa yakeso yaje. Jiya duk sun takuramasa da kira.
"Me kake cewa ne Turab mun tara mutane za'a barsu ba uban gayya"
"No mum, nifa bawai ina nufin naje naƙi dawowa bane sai an kammala taron, ah ah wallahi ko kaɗan inaso naje muyi shirin mu a can idan lokacin farawa yayi sai muzo da shirin mu gaba ɗaya tunda kinsan Ni banida wasu abokai da suka wuce su, kinga kuwa komai suka shirya akai zan zauna tunda nima ina shiryawa su bi abunda nace"
Turab ya faɗa yana gyara zaman hular da ke kanshi.
"Okay, tou ba damuwa aje lafiya, Allah ya tsare hanya.
Kamar ya tambayi mum wacece yarinyar nan mai niqab dayaga tana yimasa binkicen kaya jiya, kuma ya kuma ganin ta a kitchen jiya da dare.
Wata zuciyar tana gayamasa kar yayi wannan tambayar domin mum itama zata iya jefa masa wata tambayar akan yarinyar. Haka dai ya bar zancen a ransa yana hasashen ranar da zai ganta ya koya mata hankali, amma kuma yana tunanin kamar matar aure ce kuma tunda ya ganta da niqab.
"To matar wa" ya faɗa a zuciyarsa.
"Magana kake?" Mum ta tambaya
"Ah ah" ya faɗa a takaice.
"Kayi sallama da dad ɗin ka"
"Tun a masallaci"
"Okay, sai ka dawo" cewar mum tana nufar ɗakin khulud.
Knocking kofar tayi, kafin ta shiga. Zaune ta tararda ita a bakin gado sai famma danna waya take kuma da alamu brush kaɗai tayi batayi sallah ba domin kuwa ba alamar alwala a jikinta.
"Mum, barka da safiya"
"Yawwa, kinyi sallah kuwa"
"Ah, ah tukunna dai, banyiba"
"Meya hana?" Cewar mum tana haɗe fuska.
"Wallahi mum harna shiga toilet nayi brush, ina shirin na fara alwala naji shigowar saqo a Whatsapp ɗina, koda na fito na duba na tarar ashe ƴan group ɗin mu ne na school suka fara maganar shirin da za'a yi idan muka kammala makarantar"
"Bani wayar, wallahi dama nayi gudun wannan saboda nasan za'ayi haka dama, wanda bai mayarda hankali ga ibadarsa ba, kuma bai mayar ga karatunsa ba shine za'a siyawa waya, ai saidai komai ya ƙara lalacewa. Kiban wayar nace"
Kamar zatayi kuka ta ɗago tace" mum don Allah kibar min wayana wallahi Ni yanzu na riga na saba da ita ko minti ɗaya bazan iya yi ba wayar nan ba, balle kice karɓeta gaba ɗaya gaskiya mum bazan bada ba".
"Ok ki riƙe ta a hannunki kinji, Ni bazan iya karɓar wayan ba. Amma ai turab zai iya karɓa kho".
"Innnallillahi wa'inna ilaihirraji'un mum Dan Allah kidaina haɗani da wannan mara imanin ɗan ki, wallahi mum idan bakya sona papuna yana sona, kuma wallahi idan kika saka ya-Turab ya dakeni wallahi saina faɗawa pa, na rantse kuwa da Allah"
"Hmmm khulud kenan duka kuwa kam sai dai idan kin bada wayar nan, Amma muddin wayar nan na hannun ki wallahi saina haɗaki dashi Kuma ba abunda zai hanamasa dukanki"
Kuka harda hawaye takeyi ta ɗakko wayar ta miƙawa mum tana faɗin" ga wayarnan na baki, ai dan an ƙarɓi waya ba raina aka karɓa ba. Ga ƴar masu gida an karɓemata waya, amma wata banza ƴar bola da titi ƴar tsintuwa Ambarta ta riƙa waya. Wallahi da an kammala taron nan sai mun fita da pa, yasiyomin wata tho a zo a ƙarɓa idan an ganta" khulud ta faɗa tana shikegewa toilet tare da banko ƙofar........✍🏼
________Bayan sun yi masa rakiya ne suka dawo ciki, gidan ba wani babban gida bane domin ɗaki ɗaya ne jal, sai kuma banɗaki da kuma wurin da suka killace dabbobin da suke kiwo.
A can cikin ɗakin kuma sai suka ware wani ɓangare da zasu kwanta kafin dare.
uchi kam yasami abokiyar surutu,
Da yake shima dai mutum ne mai sakin fuska da son yara kuma gashi da surutu sosai, sai kuma aka haɗe da an dace domin kuwa indai surutu ne ya taɓo Aleena ba'a dai cewa komai.
Ita kuma Nnene tana chan tana shirin ɗora girkin dare, leeya kuma sai tayata takeyi dama ita chan bata dama wajen son aiki musamman idan na abincine,
Leeya ta maida hankalinta sosai kan aikin da suke ko ba komai tanaso ace ta iya girki kala-kala ko a ecoco haka suke zama ita da ammi tanata koya mata abincin yarbawa yanzu gashi tanaso ta iya na igbo.
"Nnene wannan kuma menene"?
"Fufu" ta bata amsa fuskar ta ɗauke da murmushi
"Fufu kuma Nnene"
"Ehh a yaren igbo ana kiranshi fufu, a wani yaren kuma ana kiranshi (cassava dough) Amma bansan ya ake kiransa a yaren kuba"
Ƴar dariya leeya tayi cikin jin daɗin samun amsar ta datayi sannan tace a yaren "mu kam ana kiransa (Rogo)"
dariya suka ƙara kwashewa da ita suna cigaba da aikinsu.
★
"Uchie dariyar me su Nnene sukeyi ? Aleena ke tambayar uchie.
"Shina gani budurwa wata ƙila tsokanace kawai dan muyi magana, kinsan me muyi kamar ma bamusan dasu ba"
"Ah ah uchie muma mu rama dariyar mu, kawai haka kawai zasuyi mana dariya muna jinsu mu kyalesu mu rama kawai"
"Tau taya zamu rama"
Uchie ya tambaye yana gyara zamansa.
"Bara kawai muma mu kallesu yanda suka kallemu, sai kawai mu fashe da dariya.
Kallonsu kawai uchi da Aleena sukayi sai suka kwashe da dariya harda rike ciki.
Abunda ya bawa su leeya mamaki kenan, ganin haka kawai suka kallesu suka kwashe da dariya. sai sukayi tunanin kodai aikin da sukeyine ya sanya su aleena dariya. sharesu kawai sukayi sannan suka ci gaba da aikin su, ba wanda ya ƙara kula wani tsakanin su Nnene da leeya da kuma uchie da aleena.
Saida Nnene da leeya suka ƙare girkin nasu tsaff kafin suka bar harabar Wurin da sukayi girkin, hadarine