Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
nufo baba ilu tana faɗin.
"Baba ilu Wallahi na yi iya qoqarina amma abu dayane rashin Sa'a"
"Subhanallah, wallahi Hajiya nima bangaren nan nawa hakane, babu wata hanya ta fita gidan nan da ta wuce gate, sai kuma idan katanga mutum zai tsallake"
Leeya na shirin magana taji qarar waya, da sauri ta dago wayar don ganin wanda ke kira. Duk da tasan kiran bazai wuce mum ba.
Hannu na rawa ta daga kiran.
Gaisawa sukayi Sosai cikin farin ciki da kewa kamar kullum.
Kamar zata gayawa mum abunda turab yayi mata sai kawai tayi shirunta.
"Mum ina su meenal?"
Daga dayan bangaren kuma mum tace "meenal ai sun wuce tun jiya, yanzu khulud ce kawai a gidan nan"
"Allah sarki shikenan su meenal sun tafi....?"
Murmushi mai sauti mum tayi tace "sun tafi amma zasu kawomuku ziyara in sha Allah kinji"
"Yawwa mum dan Allah nace kinsan inda aka ajiye Aleena da zohal?"
"Ehh to wallahi bansan address din gidan nasu ba, amma dai suma cikin garin ne saidai address ya bambanta, karki damu zan tambaya miki justice idan ya dawo"
"Yawwa mum Nagode, ina gaida papu"
"Zai ji, kuma kiyi haƙuri zamuzo zuwa ranar asabar kinji"
"Tau amma mum ai yaune lahadi"
"Eh sati mai zuwa nake magana"
"Tau yayi mum Allah ya kaimu lokaci"
"Ameen ya rabbi"
"Mum Dan Allah idan khulud tana kusa ki bata wayan mu gaisa"
"Okay bani mintuna biyu na kaimata wayar parlour ina kitchen"
"Tau shikenan mum" leeya ta faɗa batare da ta yanke wayar ba.
Mum na fita taci karo da Khulud zata shigo kitchen din ta domin taya mum aiki.
"Mum ina zakije haka...? sai sauri kike"
Mum na dariya tace "Khulud ke zanje na kaiwa waya leeyanah ke magana"
Cikin matukar farin ciki Khulud ta daka tsalle ta karbi wayar sai murna take.
Sallama tayi mata, itama ta amsa mata.
"Khulud ki fita fili Magana zamuyi"
Khulud kuma jin haka ya saka da fita daga kitchen ta sauka har parlon qasa.
"Ina jinki sister me"
Cewar khulud tana tattaro dukkan nutsuwarta wuri ɗaya.
"Khulud dan Allah sirri nakeso muyi dake bana so ki gayawa kowa maganar nan kinji,,,,,dan Allah!"
"Hummm, sister leeya me kike tunani, Wallahi bana tunanin Ni inyi magana dake kuma sannan inje in gayawa wani koh wata........! don Allah kar ki saka wannan a ranki kinji"
"Nayarda dake, kuma na yarda da abunda kika fada, kinsan me??"
"Sai kin fad'a" cewar Khulud.
Leeyana kuma ta zage ta fara bawa Khulud labarin duk abunda ya faru tsakanin ta da turab bata rage mata komai ba har binciken da sukayi a cikin gidan ita da baba ilu.
Bawai dan turab yana matsayin yaya ga Khulud ba, ko ba don haka ba wallahi ya bata tausayi matuqa. Har hawaye ta kusa yi domin tuni idanunta sun sauya kala.
Mamaki sosai tasha wai turab ne yake durqusawa wata domin ta soshi, wanda 'yan mata 'yan gayu suke ribibinsa, wanda ko wace mace take burin ta sameshi amma ga leeyanah ta samu har take wasa da damarta.
Khulud bata ji tsoron komai ba ta fara nunawa leeya kuskuren ta na qin karbarsa da tayi.
"Ke zafaran yakeso, kuma kema shi kike so. Amma aka aura masa qanwarki, kuma yayi na'am da haka, yanzu suna nan zaune cikin aminci da kwanciyar hankali. Jiya sai da mukayi video call dasu, kingansu gwanin birgewa kamar masoyanda suka dauki lokaci mai tsawo a tare, a ransu komai ya wuce.
zafaran ya riga ya dauki qaddararsa da Allah ya d'ora masa ta rashinki. Domin taimako da jihadi.
Leeyanah wallahi idan ya-Turab ya rasaki mutuwa zaiyi! Kinsan ya-Turab yana dauke da ciwon zuciya mai tsanani, Wanda yakai limit dinda idan yaga abu ya kwallafa ransa gareshi bai samu ba komai yana iya faruwa dashi, ke turab yake so kuma ke ya saka ran samu.
Koda akayi list din sunayen ku aka je masallaci inda za'a daura aure ba sunan ki keda turab aka sanya ba, fahad da zohal aka saka, Aleena kuma da ya-Turab aka sanya, ke kuma da zafaran.
Amma sanin babbar matsalarda hakan zai haifar ya saka dad qarami ya bawa zafaran hakurin Rashin ki, ya kuma nuna masa irin mummunan halin da turab zai shiga idan ya rasaki ke, wata qila ma ya rasa ransa ta dalilin haka, kuma ya qara jaddada masa amintarda ke Tsakanin su, take hankalin zafaran ya tashi duk ya tsorata yana gani kamar duk abunda zai faru ya riga ya faru tunda an riga ankai sunayen masallaci.
shikuma dad qarami da ya fahimci Zafaran ya tsorata ta kalaman sa ya sakashi fadin "wannan ba matsala bane zafaran ai zamu iya zuwa gaban limamin mu nemi da ya bamu takardar mu gyara.
Haka dad qarami da zafaran suka koma masallaci suka sami limamin ba tare da sanin papu ba suka mayarda auren akan ke da kuma ya-Turab, shikuma ya karɓi Aleena matsayin matarsa, ko da kika ga papu ya shigo hargitse lokacin da aka daura aurenku ba don komai bane sai don yana ganin ba a yiwa zafaran adalci ba tunda aka hana masa aurenki. Kinji wannan shine silar sauyawar komai, wayasan inda ya-Turab ya tafi yanzu. Wata qila ma baya Nigeria Allah kadai yasani.
Tun jiya mum na ta kiran wayarsa amma ba'a d'aga kiran. Kuma ma ai Da Baya cikin Nigeria number dinsa bazata je ba idan an kira"
Leeyana da jikinta duk ya gama yin sanyi, tausayin ya-turab ya mamaye ko'ina a cikin jinin jikinta tace "Khulud dan Allah karki sanarwa da su mum da papu ki taimakamin kinji, wallahi na gane nice mai laifi dana kasa saurarensa, amma in sha Allah za'a gyara dan Allah ki turamin da number dinsa yanzu, kinji Please" ta fad'a kamar zatayi kuka.
Khulud kam harda hawayenta tana jinjina girma da iko irin na sarkin sammai bakwai, wai ya-Turab ne da kansa yake duk wannan saboda mace.
Leeyanah kuma tana zaune tayi zugummm, ta rasa me zatayi taji dadi duk ta rasa abunda ke damunta.
Qarar shigowar saqo taji da sauri ta daga wayar, ganin number ce ya saka tayi copying, ta shiga gidan kira tayi dialing da sauri.
Har kiran ya katse ba'a daga wayar ba, haka taci gaba da kiran har ta gaji amma ba'a dauka. Dole tasaka ta hakura ta dakatar da kiran.
Washe gari ma haka ta wuni sukuku batada aiki banda kiran wayar amma kuma duk abu daya, ba amsa ba respond.
Sosai leeyanah ta sauya,,,,,,,,,, tunani duk yayi mata yawa ko abinci bata iya ci, ta ma daina girka abinci gaba ɗaya balle taci.
A safiyar kwana na uku ne misalin ƙarfe 2 na rana, leeyanah ce zaune a parlour ta gyara ko'ina na gidan, kwance take kan sofa ta kurawa wuri ɗaya idanu.
Wayarta dake hannunta ta d'ago ta kira number ɗin turab amma a kashe take, a kwanakin nan bata da aiki banda kiran number din sa tun lokacin da aka tura mata numbar ɗin sa har yau bata bada tazarar minti d'aya ba wajen kiran number ɗin sa da aka bata, tun tana kiran numbar ba'a dagawa har takai yanzu idan ta kira tana jin ta kashe.
Knocking taji anayi, amma bata ko kalli wurin ba taci gaba da abunda take, sosai ake kwankwasa gidan.
Dan guntun tsaki tayi kafin ta miqe ta isa ga kofar dakin, a hankali ta fara bude kofar.
Tsaye su biyu hannunsu sarqafe da juna fuskokin su dauke da yalwataccen murmushi.
Leeyanah kuma ganin ƴar uwarta tsaye gabanta kamar a mafarki ta daka tsalle ta rungume ta cikin farinciki.
Sosai taji dadin ganinsu gwanin birgewa.
Janyota tayi suka shigo ciki, har zata rufe parlourn Aleena ta dan zaro idanun tace "kinbar mijina waje faa, haka zaki tarbemu kenan"
Leeyana cikin mamaki ta kalli kofar parloun domin ita shaff ta manta tare suke da zafaran "kinga wallahi na manta fa, muje ki shigo dashi"
Bud'e kofar leeyana ta kuma yi sai ga zafaran tsaye fuskar nan tasa a gimtse ya zuba hannayensa a aljihu.
Leeyana ma tana dariya ta iso inda yake tsaye tace "in-low kayi haƙuri wallahi ganin yar uwata yasa na manta ka"
Zafaran kam ko kallonta bai yi ba kuma bai kalli Aleena yace "to idan na yan uwane ni da nake bare sai in tafi kho, tunda ganin ƴar uwarki ya saka kin manta da mijinki, ke kuma ganin qanwarki ya saka kin manta da yayanki" ya fada yana mayarda kallonsa ga leeyanah.
"Waye yayanah?" Cewar leeyanah.
"Ni mana" zafaran ya bata amsa.
"Uhmm--hmmm, bakaji ba dan Allah, qanwata fa kake aure, lallai ma"
"Tau kice bangaren kika dauka, dan son girma"
"Eh mana, waye bayason girma to"
"Ni mana" zafaran ya fad'a yana nuna kansa.
Dariya sukayi gaba ɗayansu suna shigewa cikin parlour.
"Ikon Allah" Aleena ta faɗa lokacin da suka shigo parlon gaba daya.
"Menene?" Zafaran ya tambayi Aleena.
"Broth O duba kaga komai na parlorn nan da namu iri dayane, har komai fa" ta faɗa tana qara waro idanunta waje kamar wata qaramar yarinya.
Dariya ta bashi sosai har sai da ya dara sannan yace mata "hakane wallahi beauty ki duba kiga can muka zauna mukaci abinci dazu koh, har kika bata min jiki da miya"
"Ehh wallahi ugly nan ne, kaga ma ga sauran miyar can a qasa banyi mooping ba"
"Ohh ni, beauty yaushe zaki daina qarya dan Allah"
"Sai ka daina ugly"
"Ni na ke qarya kho" zafaran ya faɗa yana jefamata pillown da ke hannunsa daidai lokacin da leeyanah ta shigo dauke da ruwa da drinks zata kawo musu.
Ajiye musu tayi kan Centre table dinda ke tsakiyar parlourn ta juya zata koma bedroom.
"Leeyanah!" Zafaran ya kira sunanta da asalin muryarsa wacce babu wasa a ciki.
Jin haka ya saka ta mayarda hankalin ta gaba daya gareshi ta amsa masa "na'am"
"Zoki zauna" ya faɗa yana nuna mata wurin zama.
Komawa tayi ta zauna tsamm tana sauraren abunda zai fada.
"Me yake damunki?"
"Bakomai" leeyana ta faɗa muryarta na cracking.
"Leeyanah saboda bani na aureki ba bazaki iya gayamin damuwarki ba, amma wannan ra'ayinkine ban taɓa tunanin akwai ranar da zaki iya boyemin damuwarki ba, wannan ba asalin leeyanahr okene bace, ba leeyanar ammi da abbi bace ba asalin leeyanahr da take kiran okene bace ta gayamasa damuwarta, ba leeyanar da bata qaunar ganin okene cikin damuwa bace, ba asalin leeyanahr da ke zuwa ta nemi okene domin ta gayamasa damuwarta bace. Aleena kitashi muje, muje kinji ba gidan nan bane gidan yar uwarmu wacce bazata iya boyemana sirrinta ba, ki tashi muje kinji" zafaran ya fad'a idanunsa duk sun kad'a sunyi jajir.
Leeyana kuma da kuka ya kwace mata tayi saurin shan gabansu cikin kuka take fadin"hakika duk leeyanar ku ce wannan, kuma bakuda wata leeyana wacce ta wuce muku Ni, ya-zafaran kazo ka zauna na gayamaka damuwata, nasan zakayi ala wadai dani, zaka yi tirrrr da haleena, ban kasance mai fahimta da tunani ba, wallahi ya-zafaran ban kasance mai tausayi ba, dan Allah ina ya-Turab yake in roki yafiyarsa"
Cikin tsananin tashin hankali ganin yanda leeya ke kuka kamar zata shid'e Zafaran yayi mata umurni da ta zauna, da kyar suka samu ta zauna ta daina kuka kuma.
sai hawaye ne ke zubowa a hankali.
Fuskar nan tata ta qara wani jaaa ga idanunta sun qara fito da asalin kalarsu ta blue mai dan haske.
"Leeyana ki nutsu dakyau kimin bayanin abinda ya faru da turab, wallahi shine babban dalilinda ya kawomu gidan nan, domin tun washe garin ranar da kuka tare nake kiran wayarsa amma ba'a dauka, nayi tunanin nikadai ne yake yiwa haka, sai na kira fahad na sanar masa turab baya daukar wayana bansan laifin da na masa ba, amma shi ya gwada kiransa ya ga ko zai daga kiran. Kamar yanda yamin haka yayiwa fahad gashi bamu san address din gidan nan ba, kuma muna ta kiransa don ya sanar damu amma ya ki daukar kiran mu, ganin haka ya saka fahad ya ari wayar makwancinsa ya kira numbern dinsa da wayar amma duk abu ɗaya ake nunawa.
Ba shi kadai ba har ni ma na kirashi da wata wayar amma bai dauka ba, tsakanin jiya da yau kuma muna ta kiran wayar a kashe.
Shine muka yanke shawarar zuwa gidan nan mu duba ko lafiya, duk da muna da sanin abu ne mai wuya lafiyar ta kasance.
Nayi shawarar sanarwa da mum wannan lamari sai Fahad ya dakatardani domin bamu da tabbacin lafiyar ce ko akasinta. Amma duk da haka sai da muka kira dad qarami ya bamu address din gidan nan, bani kadai ba har fahad ma zaizo nasan suna hanya yanzu haka.
Meyake faruwa ne leeya, babban abunda ya tayar min da hankali shine da kika tambayeni ina turab, Ni a nawa ganin nine wanda ya kamata nayi miki wannan tambaya kho?"
Leeya na sharar ƙwallah ta kwashe labarin duk abunda ya faru tsakanin ta da turab ta sanarwa da zafaran, hatta fahad da zohal da suke shigowa sai da jikinsu yayi sanyi, Allah ya gyarawa Fahad da Zafaran mutane ne masu dauriya da babu abunda zai hana su suyi kuka.
Musamman ma kalamansa na karshe daya faɗa, sosai gaban zafaran ke duka idan ya auna maganganun turab a mizani tunani, kalmomine masu kamar wasiyya.
"Allah ya kiyaye ka kar ka cutar da kanka turab, Allah ya bayyanaka, Allah ya tsareka a duk inda kake Allah yasa kada kayi yunkurin hallaka kanka"
Zafaran ya fad'a a zuciyarsa da ta yimasa nauyi sosai, tausayin turab ne danqare a ciki..........................................✍🏼
46.
__________________Sallamar fahad ce ta ratso wurin bayan shirun da ya gifta na dan lokaci.
Sai zafaran ne yayi karfin halin amsa masa.
Ko kaɗan zohal bataga rashin daidai da leeyana tayi ba idan ta tuna abubuwan da turab ya dinga aikatamata a can baya, hasali ma tayi mata dai-dai, babban abunda ya saka zohal taji ba dadi shine a can baya haqqoqin turab ba ko daya akan leeya, amma a yanzu kam sun rataya, a nan ne kawai zohal taga laifin leeyana da wautarta.
"Kaji komai kho Fahad? Yanzu menene abun yi?" Zafaran ya fad'a yana sauke jajayen idanunsa akan fahad dake shirin zama.
"Leeyana!"
"Na'am ya-fahad"
"Kiyi hakuri kinji, banga laifinki ba nima. Duba da yanda turab ya dinga aikatamaki abubuwa babu ko duba gaba, tun a farko yasan yana sonki amma zuciyarsa ta umurceshi da ya boye soyayyar har zuwa wannan lokaci...... yanzu gashi lokacin yazo kuma ba nasara kho, hmmm haka qaddarar take wallahi. Ki kwantarda hankalinki kinji, ki daina kuka. In Sha Allah komai zaizo ya wuce kamar ba'a yi ba.
Leeyana bata amsa masa ba sai jijjiga masa kai da take alamar tana jinsa kenan.
"Yawwa ina so in tambayeki kuma"
'dago da kanta tayi ta kura masa idanu alamar shi take sauraro.
Fahad kam sai da ya tsorata lokacin da idanunsa da nata suka sar'ke. aikuwa da sauri ya janye nashi yana ci gaba da magana.
"Leeyanah......! da misalin karfe nawa turab ya dawo gidan nan?"
"Misalin karfe goma da ashirin" ta bashi amsa a dakile.
"Gud, koda ya shigo kinji alamar yana tare da mutane ko wani motsi daga can wajen gidan?"
"Gskiya banjiba, hasali ma Ni ban san shigowar sa ba. Sai dirar abu kawai naji a gabana yasa na tashi daga baccin da ya fara fizgata a lokacin"
"Dirar abu kamar me kenan?"
"Abunda ya dawo dashi a shopping leda, wallahi idan nace nasan ko meye qarya na maka domin ba ma wannan ne a gabana ba"
"Okay, da zai fita dakin ya tsaya daukar wani abu misali takarda haka, ko kuma makulli ko waya ko wani abun daban"
"Ah'ah ba abunda ya tsaya dauka, kuma tunda ya sanya kansa bai sake waiwayoba ya fita"
"Da zai fita kinji qarar tashin mota ko kuma qarar bude kofar gate ko kuma wani abu makamancin haka"
"Ah ah, amma dai naji qarar bude kofa, sai dai bansan ko wace qofa bace saboda ba qofa daya bace a gidan nan"
"Bayan ya rufe kofar bedroom din kikaji qarar bude wata kofar"
"Ehh" ta faɗa da tabbacin haka a fuskar ta.
"koda kukazo gidan nan kun tarar da mai gadi"
"Ehh akwai mai gadi tun kafin muzo ma, haka ya gayamin. Sannan kuma ya gayamin ba wanda ya fita a daren ranar tunda Aunty Rafa'at ta tafi, sannan ita Aunty Rafa'at tana tafiya ba jimawa motar sa ta shigo gidan. Mai gadin kuma ya gayamin tunda aka ajiye motar ba'a taɓa ta ba har yanzu"
Ɗan murmushi fahad yayi domin a Duk lokacin da yake hango nasara a aikinsa yanayin irin wannan murmushin da yake gani kamar kwarin gwiwa ne gareshi.
*Masu karatu karfa ku manta fahad babban lauya ne mai matsayi da dama, kuma lauyan gwamnati wanda ake damawa dashi. Bincike kuwa ba abu bane mai wuya a wurinsa"
"Zafaran!" Fahad ya kira sunansa a tsanake.
"Na'am fahad kai nake sauraro"
"Nasan idan aka shigo da su mum cikin maganar nan dole zasu shigo da 'yan sanda domin bincike, nikuma a yanayin aikina idan aka shigo min da yan sanda aikin ba zaiyi yanda akeso ba"
"Yanzu ya kake so ayi?" Cewar zafaran.
So nake ka kira dad ƙarami ka tambaye shi su waye suka yi ginin gidan nan, nasan zai gaya maka ginannen sa ya siyeshi, to idan yace maka haka sai kace ya aramaka zanen gidan akwai abunda kakeso ka duba nasan ba zai maka musu ba domin kaima kayi masa hallarci. Yanzu fa hurry up please bamuda lokaci kaje suleja yanzu urgent please Allah ya tsare hanya"
"Amma fahad meye alaqar zanen gidan nan da kuma 'batan turab" cewar zafaran da mamaki.
Mikewa fahad yayi ya tattako har inda zafaran ke zaune ya dan bubbuga kafad'ar sa yace"zakasan amfanin haka abokina, yanzu ka tashi ka karbo mana zanen kawai"
"Amma Meyasa sai naje har kaduna akan karbo zanen gidan nan, naga nima zan iya zana hoton gidan ko daga waje nake, balle ace ina kwana cikinsa ina tashi. Domin kasan ba abunda ya bambanta da gidan sa da kuma nawa gidan har kayan dakin ma. Sannan kuma wace irin mantuwa ce ta shiga kwakwalwar ka, kai da kanka da ka sanardani dad qarami yana nemana na fitar masa ta taswirar wani kamfani da yakeso ya gina a Imo"
"Wallahi thummma tallahi na manta man zafaran, dan Allah kazo muje gida yanzun ka dauko instruments a fara fitar da zanen nan wallahi ina hangen wani abu amma abun bazai tabbata ba har sai an fitar da zanen gidan nan"
Mikewa sukayi suka fita parloun ba tare da sunyi sallama da matayen nasu ba, suma su leeyana a ta bangarena su ba wata doguwar fira, jimami da tausayi duk ya cika zukatansu.
A bangaren su zafaran kuma babu jimawa suka dawo dauke da duk wasu kayan amfani da zasu