Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
da ma can sun saba yin magana.
Mamakine ya kusan kasheta ganin shi ɗin ne da gaske ya furta mata.
"Akwai zafi ko?" ya sake furtawa a karo na biyu.
nan ma bata cemasa komai ba domin kuwa har yanzu gani take kamar ba da ita yake ba.
Taɓe baki kawai yayi sannan ya fara aikinsa.
Farantin ya ɗauke daga wurin ya kuma dauke ruwa da cup ɗinda ya ajiye.
First aid box ɗin ya ɗakko ya ɗorata kan Centre table ɗin da ya ajiye.
PAIN RELIEVING GEL, ya ɗakko daga cikin akwatin ya miƙa mata "karɓa ki shafa duk inda kumburin yake"
Hannu biyu ta saka ta ƙarɓa, tare da buɗeshi ta fara shafawa a hankali, kuma ta shafa ko ina duk inda tasan ya kumbura.
hannun sa ya miƙa mata alamar ta bashi Tata.
Ita kuwa ta ɗauka Cream ɗin da yabata yake nufi ta bashi, sai ta saka hannun nata mai ciwo ta miƙa masa cream ɗin duk a zaton ta shi yake nufi.
Bai ko kalli abunda take miƙa masa ba ya riƙe hannunta dai-dai inda yake ciwon, wani irin zabura tayi da sauri zata miƙe ya saka ƙafarsa ya take mata tata kafar "ina zakije idan na sakeki ki zauna bana son shashanci" turab ya faɗa fuskar sa ba ko ɗigon fara'ah.
Komawa tayi ta zauna tana jan wani wahalallen numfashi tana saukewa.
Sake dai-dai ta hannunsa yayi a wurin yana sake murzawa haɗi da lankwasa hannun wani gefe. Da sauri ta saki ihu tana miƙewa zata tashi, sake danne mata ƙafa yayi da tasa ƙafar amma a wannan lokacin kam bai sa ta tsaya ba.
Miƙewa yayi tsaye shima yana ci gaba da jan hannun, itakuwa bata fasa da janye hannunta ba tare da yin duk addu'ar da tazo mata a baki.
Turab kam ko a jikinsa domin shi a rayuwarsa ya tsani irin haka, bayason mutum mai raki ko kaɗan domin a ganin sa raki kawai take, ciwon bai kai da tayi irin wannan kukan ba, abun ya dawo kamar kokawa tsakanin su domin tana janye hannayenta ne shi kuma yana ƙara riƙo hannun ko a jikinsa aikinsa kawai yake baya ma duba yanda take kuka.
Jin abun yayi yawa ya saka mum sakkowa tazo parlour "Turab meye haka kuma, gyara tarkaɗene wannan ko kuma gayya, bafa soja bace kasaketa ta huta ai ko tsayuwarnan zata sakata jin zafi balle gashi ka haɗa mata biyu, gata a tsaye kuma baka sassauta mata ba" cewar mum tana janyo leeya jikinta.
Leeya ko tanajin kanta a jikin mum ta ƙara fashewa da kuka tana ƙara lafewa a jikinta.
Turab da haushi ya kusa kashewa yace"kinga mum ni na tafi idan ta kammala kukan da ba gaira ba dalili ki ƙara shafa mata wannan" yafaɗa yana nuna mata wani magani "domin Ni bazan iya tsayawa kallon wannan abun haushin ba ɗan wannan ne zatazo tanayiwa mutane irin wannan kururuwa sai kace wacce ake zarewa rai " cewar turab yana haɗa kayan da ya baje na first aid box ɗinsa.
"Turab wannan ne bakomai ba, duba kaga yanda hannun baiwar Allah ya zama abun ban tausayi. Kuma kai kazo kana gyara mata ba ko sassauci haka, ai dole yarinya ta yi kururuwa"
"Yanzu mum wannan ne zai saka mutum ihu har haka, wallahi ni da badan kinzoba sai hannun nan ya dawo daidai kome zatayi ta daɗe batayiba"
Cewar turab yana barin parlourn.
Washe gari tun da sassafe leeya ta tashi hannunta duk ta sache da kumburin da tayi sai dai sauran ciwo da yake yimata, kaɗan kaɗan, sosai tayi mamakin wannan domin bata zaci hannun zai sache da wuri haka ba, kuma gashi yau tayi aikin da ta jima batayiba saboda ciwon da hannun ke yimata.
Bayan ta kammala gyara bedroom ɗinta ta fita ta gyara parlou, sannan ta shiga kitchen ta haɗa breakfast.
"Leeya, wai meyasa bakyajin magana" ta tsinkayi Muryar mum dake tahowa.
"Mum barka da safiya"
"Leeya, waya sakaki yin wannan uban aiki"
"Mum, wannan aikin ne wani aiki harda za'a..."
"Harda za'a yi me, jiya jiyan nan fa kika gama kururuwa kamar wacce ake yankawa jiki"
Tafin hannunta ta saka ta rufe fuskarta alamar taji kunya kai kace mum ganin ta take.
"Wallahi mum shine bai sassautamin ba, daya bini a hankali da bazaki ji ko tari na ba balle nayi ihu"
"Ai ba'a bin mai irin ciwon nan a hankali, saboda ciwo ke fitarda ciwo da ba'a yi haka ba da kumburin bazai sache ba, yanzu dai kije ki zauna daining ki jirani khulud ta fito, shima turab ya fito. Duk suna chan zaune kema kije kizauna kihuta kinji"
"Haba dai mum, kedai ki barni na ƙarasa ladata kawai dan Allah"
"Idan ladace wannan ma da kikayi ai zaki samu ladar kije ki huta Kinji"
"Mum, nifa ba gajiya nayiba saboda haka kije kawai dan Allah "
Mum tayi tayi ta hanata aikin amma furrrr taƙi kuma ta hana mum ta saka hannuta a aiki.
"Mum har kin kammala breakfast ɗin" cewar turab dake zaune a wurin.
"Ban kammala ba, leeya ce tace naje zata idar da ladar ta"
"Wacece leeya mum? Badai wacce hannun ta ke ciwo ba kho"
"Ita wallahi"
"Ikon Allah, ba'a taɓa hannunba fa har yanzu duk abunda kikaga munyi jiya, ba gyaran targaɗen akayi ba, maganin kumburi ne aka sakamata. Kuma idan ma zaki tambaye ta har yanzu hannun nayi mata ciwo kawai dai babu kumburin idan kika duba yanzu, amma hannun yana nan da ciwon, kuma idan ta cika yin aiki dashi zai iya janyo wata matsalar daban kuma"
"Tau ya za'a yi tunda ta dage sai tayi"
"Ke! me kike anan da bazaki tashi kije ki tayata ba" turab ya faɗa yana mayarda kallonsa ga khulud.
"ya-Turab wallahi ban iya aikin nan da takeyiba, Nima yimin akeyi"
"Kamar ya baki iya ba" Turab ya faɗa da mamaki.
"Eh yaya wallahi ban iyaba" khulud ta faɗa a tsorace saboda tasan sarai zai iya aikamata da duka daga inda yake.
"Mum, ya akayi aka bari yarinyar nan ta lalace haka, taya kamar khulud za'a ce bata iya aikin gida ba, wanda ya kamata ace itace zata koyawa wasu a yanda take yanzun nan" cewar turab a faɗaceh. "Tukunna ma dai Mum ina ƴar aikin gidan nan?"
"Ka tambayi khulud gata nan"
Wani irin wawan kallo ya jefamata da sauri tace
"Yaya ankoreta"
"Kamar ya ankoreta dayammah nake nufi"
"Eh, yaya ankoreta tunda jimawa ma yanzu"
"Laifin me tayi aka koreta"
"Marina tayi"
"Mari?"
"Eh, shine papu ya koreta".
"Ya koreta ko kikasaka ya koreta" mum ta faɗa
"Mum, ban fahimci ita ta saka aka koreta ba, kina nufin saboda khulud aka kori dayammah gidan nan?"
"Wallahi saboda ita aka koreta"
Gigitacciyar tsawa ya daka wa khulud "ki tashi ki shiga kitchen, kicewa yarinyar nan nace ta dawo ki kammala aikin, kuma wallahi idan naga ba daidai ba sai kin yabawa aya zaƙinta"
Jiki na rawa khulud ta tashi, ba halin kuka da tayi kukan ko zata rage domin da mum ce ko papu suka mata haka, da tun tuni ta rushe da kuka.
"Ke kin kammala" khulud ke tambayar leeyanah
"Na kammala da kinyi hakuri ai, da Yanzu ma zan fito"
"Ke dallah malama rufewa mutane baki ko angaya miki yunwa ce ta kawoni wurin nan"
"Allah ya baki hakuri" shi kawai leeya ta furta ta ɗauki hot water a flask tayi tafiyarta.
Khulud kuma ta dauko ragowar kayan ta biyota itama.
A daining suka iso kusan lokaci ɗaya, leeya ce kawai tayi sallama, khulud kam ko tari batayiba, tun kafin su ajiye kayan turab ya dakawa leeya Tsawa"ke waya sakaki yin aikin da kikayi"
"Ba wanda ya sakani"
"Ke kika saka kanki kenan"
"Eh, na jima bana aiki da hannun nan ne shiyasa yau danaga ta sauka nace bara na taɓa wani aikin"
"Ba wanda ya saka ki kenan, to waya gayamiki hannun ya warke, iya maganin kumburi aka saka masa kuma kinga ya sauka amma ba'a saka maganin targaɗen ba. Saboda haka idan aka gama break fast za'a gyara zaman ƙashin"
Haka kawai ta tsinci kanta da faɗin"ya-Turab ai hannun ya warke gaba ɗaya"
Murmushin gefen baki yayi cikin wani salo irin nasa yace" okay ya warke ko, ba inda yake miki ciwo"
Jijjiga masa kai tayi alamar
"eh"
Wata wawuyar harara ya ɓalla mata nan take tace"eh, ba inda yake min ciwo yanzu ko ina lapiya Ƙalau nake jinsa"
"Okay" cewar turab daidai lokacin da papu ke sakkowa shima
Yana ƙarasowa wurin duk suka gaidashi,
"lafiya ƙalau, leeya kinji sauƙin hannun naki kho, Jiya nake tambayar mum ɗinku ta gayamin ashe kinyi missing step ne kika yi targaɗe"
"Eh wallahi, papu amma ai jiya ya-Turab ya gyaramin targaɗen kuma hannun ya warke gaba ɗaya" leeya ta faɗa tana murmushin yaƙe.
Kusa da kujerar da mum take papu ya zauna sannan sai khulud ta zauna kusa da tashi, sai kuma turab dake zaune kusa da khulud, sannan sai leeya dake zaune gefen turab itama.
Serving ɗinsu mum tayi gaba ɗaya suka fara cin abincin suna fira jefi-jefi.
Papu ne ya fara barin wurin yayinda khulud ta zama ta biyu.
Aka bar wurin daga mum, turab da kuma leeya.
Bayan haka kuma leeya ta tashi ta bar wajen itama kafin su kammala sannan ta dawo ta haɗa kayan da aka ɓata taje ta wanke.
Bedroom ɗin ta ta koma sannan ta shiga toilet tayi wanka ta fito.
Mirror sit ta janyo ta zauna sannan ta shafa duk abunda take buƙata ta shafawa jikinta.
Ƙarar wayarta taji a can gefe alamar shigowar saƙo.
Da sauri ta janyo wayar ta buɗe saƙon domin tasan zohal ce, kuma da ita kaɗai take communicate.
gaba ɗaya sim ɗin ma number mutum uku ne haɗi da itane ya zama huɗu.
Daga mum, papu sai zohal.
Cikin matukar mamaki ta tsaya tana ƙara karanta saƙonda taga an turomata da baƙuwar number.
"Amincin Allah ya tabbata gareki sarauniya ta, barkanki da wannan lokacin, ina fata kina cikin ƙoshin lafiya. Allah yasa haka (Ameen thumma), jiya kinyi kyau sosai kuma kunshinshi yaya jaa gwanin ban sha'awa, sai dai naga kamar hannunki daya batada lafiya kho? To Allah ya sauwaqe ya baki lafiya my dream girl nayi missing din zazzakar Muryar nan taki kinj, take care byeee".
Ta daɗe tana maimaita karatun saƙon nan kamar mai yin hardan shi, "wayakeda number nan ?" Leeya ta tambayi kanta a zuciyarta.
Kiran number tayi saidai abunda ya bata mamaki number a kashe take.
Ta kira a ƙalla sau biyar amma abu ɗaya ake gayamata not reachable.
Goge sakon tayi taci gaba da aikinta.
Kayan ta ta saka material Yard kalar brown mai haske ɗinkin ya karɓi jikinta sosai, tayi ɗaurin da ta sabayi wanda ake kira A'isha Buhari.
Sannan ta ɗaura niqab ɗinta ta fita.
Bata saka mayafi ba ta fita hakan nan yanda take saboda tasan ba wanda zata tarar a parlourn yanzu.
Sakkowa tayi daga kan stairs cikin tafiyar ta ta nutsuwa, a hankali take takawa harta ƙara so daining area, tsayawa tayi chakkk da tafiyarda take sakamakon ƙamshin turarensa data jiyo amma ta kasa tantance inda ƙamshin ke fito.
Ci gaba tayi ta tafiyarta kawai domin tana tunanin ko ya fita yayi shiyasa kamshinsa baibar parlourn ba har yanzu.
Tana isa daining ta tararda kayan yanda tayi tsammanin ganin su.
Haɗa su tayi wuri ɗaya ta ɗauki waɗanda zata iya ɗauka ta nufi kitchen area dasu, dayake bawata tazara bace tsakanin kitchen da daining yasa kayan basu takurawa hannun da yake mata ciwo ba.
Mirɗa handle ɗin kofar kitchen ɗin tayi, sai ta saka kafarta ta tura kofar a hankali har ta buɗe iya yanda zata iya wucewa, tana shiga bata isa koina ba sai gaban kitchen sink ta zube kayan ta fara wanke wa, cikin nutsuwa take aikin ta, bata kula da komai sai aikinda take.
"Ke, baki iya sallama bane da zaki shigo kamar bakiga mutum ba" cewar turab cikin masifa.
Da mugun tsoro ta juya domin batayi tunanin jin muryarsaba kamar a sama taji muryar tasa domin kuwa da darene ba abunda zai hanata guduwa.
Muryarta na karkarwa tace"wallahi ya-Turab banganka bane shiyasa, kuma na sha'afa gaba ɗaya na ɗauka nayi sallama ai"
Ta faɗa kanta a ƙasa tana saiti da turab dake zaune kan fabric sitter ɗaya jal dake kitchen ɗin.
"Ki miƙomin juice a fridge, shinazo na ɗauka dama"
Bata furta komai ba ta nufi inda fridge yake ta buɗe "wane kalar juice za'a ɗakko maka" ta faɗa jikinta sanyaye.
"Apple juice" ya bata amsa
Apple juice ta duba ta ɗakko tare da zuwa gabansa ta ajiye masa, sannan ta dawo ta ɗauki cup shima taje ta kai masa.
"Kinfi ƙarfin ki zubamin juice ɗin ne"
"Kayi hakuri dan Allah, bara na zuba maka"
Robar juice ɗin ta buɗe tare da tsiyaya masa"ya isa ko a ƙara"
Ko kallon ta baiyiba yaci gaba da danna wayarsa kamar bai san da ita a wurin ba.
"ya-Turab Gashi nan na saka" ta faɗa tana niƙa masa kofin.
"Ajiye shi anan" cewarsa yana nuna mata wani ƙaramin tables ɗinda ke gaban fabric sitter ɗin da yake zaune.
Hannunta ta miƙa da nufin ta ajiye juice cup ɗinda ta tsiyaya masa, ba zato ba tsammani taji ya riƙo hannun ta daidai inda ke yimata ciwo.
A ruɗe ta fara jan hannun iya ƙarfin ta domin tsananin azaba da takeji, amma ina yafi ƙarfinta saboda haka ya fara lankwasa hannun tare da jan hannun iya yanda zai iya.
"Dan Allah ya Turab kayi hakuri, wallahi na ɗauka wannan table kake nufin na ajiye maka juice ɗin ka"
Baiko kulata ba yaci gaba da aikin sa, wani mai ya fito dashi a aljihun sa.
Sannan ya sakkamata hannun ta tare da faɗin "wallahi idan kika kuskura kika fita kitchen ɗin nan, ko kuma naji kukanki wallahi saina ɓata miki rai" ya faɗi maganar kamar dai yanda aka saba fuskar sa ba ko ɗigon Annuri.
Dayan hannunta ta saka tare da riƙe bakinta domin ta kasa tsaida kukan da take.
Tsawa turab ya daka mata da faɗin"rufemin baki sai rakin tsiya, ɗazu dana tambayeki a daining cemin kikayi hannunki ya warke ai, yanzu meyasa kika kuka, means ƙarya kika min kho?" Turab ya faɗa yana tsureta da idanunsa.
"Wallahi Ni banyi tunanin taɓa hannun za'a kuma yiba, kuma ma dalilinda yasa ban gaya maka gaskiya ba banaso na kushe abunda kayi ne saboda idan mutum yayi maka magani kuma ya tambaye ka jikinka, bazaiji daɗi ba idan ka faɗa masa saɓanin waraka"
"Angayamiki bansan abunda nake bane, ko kin ɗauka ni sha-sha-shan mai magani ne da bansan abunda nake ba, nagayamiki maganin kumburi na sakamiki ba'a taɓa targaɗen ba, domin da hannun bata kumbura ba iya targaɗen za'a gyara, amma dana tambayeki kika gayamin har targaɗen ya warke. Da tun jiya kin kwantar da hankalinki da anyi komai lapiya angama, Yanzu ma hakane ko ki tsaya ayi lafiya ko karki tsaya sai an gyara, yafimiki ma ki kwantar da hankalinki kiyi dauriya na gyara miki kiyi tafiyarki"
Wani irin kwarin zuciya ne yazo mata jin abunda ya faɗa, takeji a ranta ko ya taɓa hannun bazata ji komai ba balle tayi ihu kowani abun daban.
"Shikenan ya-Turab ga hannun" ta faɗa tana ƙara miƙa masa hannunta.
Maganin ya shafa a hannun nata, kafin ya fara gyara mata targaɗen, leeya kuwa ko tari batayiba saboda ta fahimci idan ka nuna bazaka iya bane yake yimaka yanda yakeso, amma idan ka tsaya shima zai bika a hankali.
Saida ya kammala komai da komai tukunna ya fito da wasu tablet sachets kati biyu.
"Karɓi waɗan nan kije ki sha biyu yanzun nan, idan akayi la'asar kisha biyu, sannan ki sami wuri ki kwanta ki huta. Domin hannun ma yayi tsami sosai saboda kin jima da buguwa kuma kika ƙi yin magana balle a dubamiki"
Karɓar maganin tayi tare da furta"nago.....de...sosai" ta ƙarasa maganar kuka na kwace mata domin harga Allah hannun zogi take yimata, ji take kamar an tsinketa daga jikinta.
Taɓe baki turab yayi haɗe da jefa mata wani kallo yana ɗaukar juice ɗinsa tare da barin kitchen ɗin.........✍🏽
BAYAN WUYA.......
By RUMANA M DIGGI
EP.24
____________juyawa tayi tare da nufar sink domin ta kammala wanke-wanken da ta fara.
Amma inah hannun yana yimata ciwo sosai sai taji gaba ɗaya bazata iya kammala aikin ba.
Magungunan da aka bata ta ɗauko tana barin kitchen area ɗin,
Bedroom ɗin ta koma kaana ta ɗakko maganin da tazo dashi ta balla ko wanne biyu sannan ta hadiya da Ruwan da tazo dasu.
Kan Royal sopa ɗinda da ke bedroom ɗin nata ta zauna taɗan kishin giɗa nan da nan kuwa bacci ya tafi da ita.
TURAB.
Zaune yake kan bed ɗinshi sai faman bincike yake a system ɗinsa,
Daga can gefe kuwa waya ce ke faman ruri alamar kira na shigowa, ɗaukar wayar yayi yana karawa a kunnensa.
"Hello, zafaran"
Banji abunda ake faɗa daga cikin wayarba amma da alama magana ake yimasa saboda yayi shiru alamar yana sauraren sa kenan.
"Okay ba damuwa in sha Allah, zankira fahad na gayamasa, sai mu shirya tafiyar. Yanzu haka ma ina shirin tafiya sati mai zuwa"
Har yanzu banajin abunda ake faɗa a wayar amma naji turab yana cewa
"zanje Kuwait ne, zanyiwa wasu aiki tun wancan satin suka kirani sakamakon sojawansu da aka harba har wuri huɗu mutum ɗaya ne aka ceto rayuwar sa, su kuma sauran ba wani ci gaba shine suka bibiyi page Dina suka min Magana, wai likitocin Kuwait ɗin sun kasa. Ina ga a kwanan nan zan tafi saboda aikin urgent ne gaskiya idan banje da wuri ba za'a iya rasa wasu daga cikin su"
"OKAY tau ba damuwa, idan aka saka tafiyar da wuri dani za'a je in sha Allah, gaskiya wannan lewar ta wahalarmin da abokina",
OKAY tau sai anjima. Turab ya faɗa yana ajiye wayar.
Cigaba yayi da aikinsa, ji yayi kamar ana knocking din kofa "Yes" ya furta cikin husky voice ɗin sa.
"Shigowa khulud tayi ɗakin"ya-Turab mum tace nazo na gyara maka ɗaki"
"Saboda ke sha-sha-sha ce kuma ba'a koyamiki sallama ba kho"
"Yaya, nayi knocking fa"
"To knocking da sallama ɗayane khulud, meyasa kike abu kamar wata ƙaramar yarinya, wai meya ɓataki haka ne, Ni wallahi kuna