BAYAN WUYA BOOK COMPLETE BY RUMANAH M. DIGGI.txt

Author :  Rumana M Diggi Category :  True Hausa Novels

Chapter   20 / 61

57K to 60K   out of 180.4K words

ƙanwarkace kaji ba-indiye, kuma FANNAH sabuwar ƙawatace a can muka haɗu da ita ɗazu".

"Ban faɗa miki sunana bane ? karki ƙara kirana ba indiye ni Bahaushe ne, bakiji nama fiki iya hausa ba" cewar fahad cikin sigar wasa.

"Hmmm, a yanda kace kenan. Amma aini zan iya ɓatarda kai ɓattt a cikin Hausa".

"Haaa, yaro baisan wutaba sai ya taka, nikam bazaki iya ɓatardani a hausa ba, tun kan a haifeki nake ɓatar da manyanki balle ke".

Ƴar siririyar dariya zohal tayi kaana tace "to ka ɓatar dani nagani".

Fahad ya kalleta shima cikin dariyarsa yace "dakin tafi inda bakisani ba kuwa ɓacewa zakiyi kuma idan kinyi gardama kije india kigani".

Dariya suka kwashe baki ɗaya kai idan ka gansu zakace sun shekara da sanin junansu.

"Byee, zan tafi ana jirana" cewar zohal tana tafiya.

"Okay, Nagode sosai mrs, fahad take care please"

"Mekace?, zohal ta faɗa tana waiwayo shi.

"Cewa nayi sai anjima bahaushiya".
Murmushi kawai tayi tana tafiya batace masa komai ba.

Leeya kuwa tunda tabar wajen hankalinta ya kasa kwanciya haka kawai takejin tsoron baƙon balarabe na ratsata.

Ji tayi an dafa kafaɗarta ta baya, da sauri ta waiwayo ganin zohal ce yasa ta sauke ajiyar zuciya.

"Bestie ramawa kikayi kho, shine kema kika tafi kika barni. Yayi miki kyau".

"Sorry bestie zohal, wallahi nima bansan meyasa nake matukar tsoronsa ba kuma wallahi hankalina.ya kasa kwanciya har yanzu".

"To, sbd me kikejin haka" cewar zohal.

"Allah bansaniba nima, kuma ba abunda ya taba haɗani dashi amma wani abu ya taɓa haɗani dashi zo muzauna na faɗa miki.
A can gefe sosai suka samu a filin taron suka zauna ba mutane sosai a bangaren domin yanda akayi decorations ɗin ne yazo da haka, saboda yanda aka yi tsarin ajiye kujerun ko daga ina kk indai kana zaune wurin to zaka ga wanda yake gaban ka komai nisanku dashi.

Hakama wanda yake gaba zai ganka, kamar yanda Turab da sauran mutanen da ke tare dashi suke ganin kowa, kowa kuma yana ganinsu.

Labarin duk abunda ya faru tsakaninsu da turab ta kwashe ta gayawa ZOHAL har sa'adda suka haɗu dashi a kitchen.

"Ikon Allah, kice ya-Turab shine dalilin jin ciwon da kikayi a hannunki"

Ɗaga mata kai tayi Alamar "ehh"

"Tabb amma kuwa naso naga yanda zaigyara targaɗen da hannunsa" cewar zohal tana yimata murmushi.

Saida hantar cikin leeya ta kaɗa jin abunda zohal ta faɗa, domin ita ta manta kwata-kwata da mum tace ta sameta idan an kammala taro.

"Zohal, ya zanyi wallahi inajin tsoron bawan Allahn nan bazan iyaba gwanda muje asibiti kawai"

"Idan ya kasa kenan, amma idan zai iya gyarawa kinsa ba wata asibitin da zakuje, ballema nasan zai iya wanda yake likitan sojoji ai gyaran ɗan targaɗen da kikayi ba komai bane a wajensa"
Zohal ta faɗa daidai lokacin da mai gabatar da taro ya fara magana..........✍🏼






BAYAN WUYA.....










By RUMANA M DIGGI





EP.21

__________Bayan doguwar addu'a da aka saurara a bakin wani shehin malami da papu ya gayyato.

Sai kuma karatuttukan Alqur'ani mai girma da aka bayarda dama duk wanda zai iya yafito yayi, Mutum daya ake bukata bangaren maza, haka kuma bangaren mata.


Ganin ba wanda ya miƙe cikin mata yasaka Leeyana tashi, daidai lokacin da ZAFARAN yabar wajen sakamakon kiran wayarsa da akayi.

Tafiya take cikin nutsuwa har ta isa wurin da ake gabatarda karatun.

A gaban wanda zai bada mic ɗin ta tsaya, mutumin kuwa yana ganin ta ya miƙa mata ta fara karatun. Karatu take cikin sanyi da zaƙin muryarta, cikin suratul Maryam.

Hankalin kowa ya karkata izuwa karatun da take wurin yayi tsit bakajin sautin komai saina karatun ta, sosai ta birge mutane domin kuwa wasu da za'a bi tasu kamar tayita karatun nan har lokacin kammala taron yayi.


TURAB kam tunda ta taso bai ɗaga kansa ba balle ma yasan wacece. duk da shima karatun yayi masa daɗi sosai, domin kuwa har lumshe idanun yake yana bin karatun a hankali cikin zuciyarsa.

Yanda ta karanta wata aya a can ƙarshe bai masan lokacin da ya ɗaga kansa ya ƙuramata idanu ba. Lokacin da ta bada mic kuwa duk mutane sukayi kaffara cikin birgewa.

Har ta sauka daga wajen anata kallon ta, tare da yaba muryarta da kuma iya karatun Alkur'ani mai girma.

Zohal kuwa daɗi kamar ya kasheta jin yanda ake yaba bestien ta.

Bayan haka kuma, mai gabatar da taron ya miƙawa papu mic, shima yayi jawabi, daga nan kuma aka Bama mum , itama tayi nata. Sai kuma wasu daga cikin family suma sukazo zukayi guntun jawabi, daga nan kuma aka bawa zafaran da Fahad, daga su kuma aka miƙawa mai gayya mai aiki wato TURAB K. WAASIB.

Bayan dogon jawabi da yayi shima, da irin nasarorin da yasamu a gayyatar da aka yimasa a kasashen waje, da kuma award, award ɗin da ake bashi a matsayin kyaututtukan yabo da godiya.
Yana cikin jawabin ne idanun sa suka sarƙe dana leeya, wata irin muguwar faɗuwar gabace ta ziyarceta yayin da taga ya dalla mata wata uwar harara.
Da sauri da sauke kanta ƙasa tana mamaki sai zancen zuci take, "kenan mutane duk ƙarƴa suke da suke faɗin idanuna tsoro suke basu, amma gashi shi yakalli cikin idanuna har ya harareni, wallahi badan nayiwa ammi babban alƙawari ba da ayau ɗin nan saina kalli madubi" koda leeya takai daidai nan a zancenta ta ɗaga kanta ta kuma kallon turab.

Amma a lokacin ba ita yake kallo ba. Sosai mutane sukayiwa turab kyautuka daban daban, haka ma mum da papu ana yita saka masa albarka, har aka kammala taron daidai lokacin da Turab, zafaran, da kuma fahad suka sakko, suka shigo Mutane ana gaisawa da sauran family da suka iso da baya.

Koda leeya ta kula da haka sai tayi sauri ta shiga cikin taron mutane domin ta ɓacewa ganinsa, tafiya take tana waige-waige cikin tsoro taji ta bankin wani abu, da ƙarfi ta juyo da nufin taga abunda ta banka. Numfashin ta ne ya tsaya chakkk, tayi suman tsaye sakamakon ganin Turab a gaban ta, tazarar da ke tsakanin su bata wuce taku biyu ba.

Idanun ta takai can gefe inda ta jefarda wayar da ke hannunsa, da sauri ta duka ƙasa da nufin ta ɗakko masa wayar. Hannunta na hagu ta saka domin ɗayan hannuta ne bashida Lafiya.

Cikin ɓacin rai Turab ya saka ƙafarsa ya takemata yatsu, wani irin ihun azaba ta saki domin kuwa ji tayi kamar yatsunta basa jikinta.

Durkushewa tayi zaune domin ta ma rasa abunda zatayi "Dan Allah kayi hakuri wallahi da zafi" cewar leeya muryarta na rawa saboda tsoro, ga kukan da ke neman cin ƙarfin ta.

"Kin taɓa ganin inda akayiwa mutum ɓarna, kuma a masa wulaqanci" cewar turab yana murtuƙe fuska.

"Wulaƙanci kuma, Ni na isa na maka wulaƙanci? Wallahi da ason rainane bazan yi maka ɓarna ba ƙaddara ce kawai Ni danasan zamu haɗu wallahi bama zan biyo hanyar nan ba".

"Saboda ga dodo kho, da kinsan zaki haɗu dani da baki biyo nan ba kho. Dan kin rainani ki bankeni har wayana ta faɗi sannan kuma kisaka hannun hagu zaki ɗauko waya ki bani, ai ko kyauta zaki ban bazaki bani da hagu ba, balle ni nakeda wayana saboda haka bazan karɓa da hannun hagu ba". Turab ya faɗa yana janye ƙafarsa daga hannunta.

Janye hannun tayi a hankali ba tare da ta ɗauki wayar ba, kana ganin niqab ɗin ta zaka gane hawaye take, hannunta na dama da yayi sundul ta ta ɗauki wayar dashi da yake bazata iya ɗauka da hannun kaɗai ba sbd kumburin ta yayi yawa, yasa tasaka ɗayan hannunta ta tallafawa wa ɗaya ta miƙa masa wayan.

Karɓa yayi tare da yin ƙofa yabar wurin. Ita kuwa leeya yana barin wajen ta ƙara fashewa da kuka domin kuwa tana ganin cewar zamansa a gidan ba ƙaramar wahala zatasha ba, shikenan idan ba'a wurin mum da papu ba, ba inda zata sami sanyi, domin ulud batason ta ko kaɗan haka shima baƙon balaraben nan daga gani baya ƙaunarta.

A bangaren zohal kuwa tayi neman leeya har ta gaji bata ganta ba, kuma ta kira wayanta sai taga ashe bataje da wayan ba domin gata nan a cikin jakarta.

Tashi tayi daga inda take ta fara ta fara zagayawa cikin mutane.
"ZOHAL KHALIL GIRAH" taji ankira sunan ta daga nesa da ita kaɗan.

Dakatawa tayi tana jiran ƙarasowar wanda ya kira sunan nata.

"Ba-indiye" zohal ta faɗa tana washe fararen haƙoranta lokacin da Fahad ya iso wajen.

"Ke nifa na gayamiki ba ba-indiye bane, tun ɗazu inata neman ki ban ganki ba" cewar FAHAD.

"To nema kuma, Allah yasa lafiya" zohal ta faɗa tana gyara tsayuwar ta.

"Eh, to dama dai za'a ce, amma alfarma ɗaya zaki min" cewar fahad yana ɗaga yatsansa alamar (ɗaya)kenan.

"Ohk, Allah yasa zan iya"

"Zama ki iya, precious queen" fahad ya faɗa fuskar sa ɗauke da ƙayataccen murmushi.

"To nikuwa zohal a ina na zama queen waya bani saurauta".

"Anan" fahad ya faɗa yana nuna saitin zuciyar sa.

"Thooo, Allah sarki. Yaushe hakan ta faru kuma" zohal ta faɗa da cikin barkwanci.

"Hmmm, kedai bari kawai zuciyar fahad tayi nutso, har ta noce q begen wannan sarauniyar daga ɗazu, zuwa yanzun nan".

"Allah sarki, aikuwa ka shigo fadar sarauniyar da takeda sarkin da ke mulkin fadar zuciyarta" faɗin zohal tana janye idanun ta daga kallonsa.

"Da ace hakane, da zuciyata bazatamin ƙarya ba, Saboda na yarda da zance da zuciya ta taymin akan wannan kyakkyawar sarauniyane yasa nazo mata a bawa, bawai sarki ba".

"Hmmm" kawai zohal ta faɗa tana cewa" da ace bawan jarumine ba abunda zai hana saraunyar ta ƴan tashi ya dawo a gefen damarta".

"Domin tabbatar da bawan jarumine yasa nake so kizo ki rakani".
"Ba damuwa muje"
"Yau Hausa girl, ko kefa"



A bangare ɗaya kuwa mum-fanaya ce zaune a wani gefe cikin filin da aka kammala walimar, sai kuma mummy-neesah wato mahaifiyar twins sai kuma su kansu FANNAH da MAYAH da RUKHSHANAH harda NU'AIM sai kuma khulud dake zaune gefen mahaifiyarta sai firar yaushe gamo suke.

FAHAD ne ya iso wajen bakinsa ɗauke da sallama zohal kuma tana biye dashi, saida suka kusa isowa ta kula da mum harda fannah, cikin tsananin farin ciki take tafiya har ta manta da rakiya take.

Jin sallamar da fahad yayiwa su mum ne ya sakata dakatawa da tafiyar da take.
"Zohal ina kuka shiga keda ƙawarki tun ɗazu aka yita ɗaukar photo amma bangankuba" cewar mum-fanaya tana duban zohal.

Zohal zatayi magana fahad yayi caraffff yace"mom itace sarauniyar da nace muku ta sace zuciyata, gatanan ZOHAL KHALIL GIRAH ƴar nan garin ce, ita nakeso kuma ita zan aura idan har kun yarda itama ta yarda, to ba makawa itace matata In sha Allah, zohal ga iyayena nan da ƙannena shine na tarasu a nan na nunaki a gabansu".

Wata mahaukaciyar kunya ce ta kama zohal domin har ga Allah batayi tunanin haka ba,
da bazata biyoshi anan ba domin su mum zasuga rashin kunyarta da yawa.

Sosai mum tayi farin ciki da haka, koba komai zohal ce yarinya mai kyau ga hankali da nutsuwa, ga yawan barkwanci.
Miƙewa mum tayi ta ƙaraso ga zohal ta rungume ta domin ta fahimci kunya takeji.

"Lallai mummy ke bazaki taso ki rungumeta bane, shine kika bar mum ita kaɗai" cewar fahad yana tallafe ƙeya.

Robber cup, mummy-neesah ta ɗauko dake kan table ɗinda suke zaune ta jefa masa tare da faɗin "bar nan mara kunyan banza".

Juyawa yayi aguje yana dariya yabar wajen.

Zaunarda zohal mum tayi kusa da ita, zohal kuwa kamar batasan mum ba saboda kunya ko daga kanta ta kasayi balle tayi wani kwakkwaran motsi.

Mummy-neesah kuma sai kallon zohal take tana murmushi domin kuwa taganta nutsatstsiyar budurwa ga kyau da ɗie kuma ga kunya.

Ta ido mum da mummy sukayi magana sai mum ta mayarda kallonta wurin twins tace fannah ki tashi ki rakata ta wuce.

Da murmushi a fuskar fannah ta miƙe ta kama hannunta tace "aunty na muje na rakaki kho"

Gwalalo idanu zohal tayi domin da ba domin ganin su mum ba sai tayi magana.

Suna fara tafiya FANNAH tace "yadai matar yayana, kinga mun ƙara haɗuwa a karo na biyu kho, haɗuwar mu ta gaba kam in sha Allah kinzama cikin familyn mu kenan, wannan kyawun da kikayi Ni nasan sai kinyi catch, daga shigowar yayana kin kwamushe masa zuciya"

Zohal na shirin magana wayar fannah tayi qara, picking call tayi ta kara a kunnenta "OKAY" kawai FANNAH ta faɗa tana katse kiran.

"Nan zamu bi" cewar FANNAH sunayi wani ɓangaren.

Surutu kawai fannah keyi ita kaɗai zohal kam loma ta ɓace a bakin ta domin ta kasa furta komai.

Komai FANNAH tace sai kaga zohal tayi murmushi kaɗai har fannah itama ta fahimci kunyace kawai zohal keji. Kuma itama abun ya birgeta.

Ita kuwa zohal Allah-allah take kawai taga leeya domin ita kaɗai takeda muradin gani a daidai wannan lokacin.




"Ya-fahad gata nan".

Maganar da fannah ta faɗa kenan data tsamo zohal daga tafkin tunanin da ta tsunduma.

"Subhanallah" zohal ta faɗa a mamakance domin ita har ga Allah batasan sunzo wurin nan ba.

"Maimakon ace bawa ya tsorata sai kuma naga sarauniyar ce da kanta keda alamar jin tsoro".

"Cikin sanyin murya zohal tace" idan bawan yakai tantiri ne ake jin tsoron sa, yanzu kam idan ma akwai wani suna da ya wuce tantira to dole a baka sunan domin kuwa duk ka gogemin harda"

"Uhmm, shikenan kawai yanzu tunda bawa yayi nasarar kwamushe zuciyar Sarauniya sai ta bada kai bori ya hau kho".

Ɗan rankwafarda kai zohal tayi sannan tace"ga kan a kira borin ya hau kho"

Dariya suka kwashe baki ɗayansu, daga nan kuma fira ta wanzu tsakanin su. Idan ka gansu zakayi tunanin laila ne da majnoon saboda ƙauna.







*******
A bangaren leeya kuma tunda abun ya faru tabar filin taron ta koma cikin gida, sashensu ta shiga tare da cire kayan jikinta tayi wanka sannan ta canja kaya, ta saka rigar yadi mai shara-shara mara nauyi, sai kuma ƙaramin mayafin da ta ɗauka ta yafa bayan niqab ɗinta data saka.

Parlour ta sauka ta zauna kan 3sitter sai faman tunani take, har bacci ya ɗauketa.


Tana kwance a wurin tsawon awanni biyu, dayake kuma babu hayaniya sosai a parlourn ko mutane ma ɗaɗɗaya ne ke shigowa, ga kuma tarin gajiya dake jikin ta, shiyasa ta dauki tsawon lokaci tana bacci.



Kaso chasa'in cikin ɗari da sukazo taron duk sun tafi, domin babu waɗanda ke nesa sosai sai irin familyn su dake Maiduguri.
A cikin waɗan da suka wuce kuma harda su mummy-neesah da ƴan ukunta da kuma NU'AIM.

Shikuwa fahad yana nan bai tafi ba, dama a abuja yake aikinsa domin shi babban lauyan Shari'a ne. Kamar dai papu, amma ba matsayinsu ɗaya da papu kowa da nasa.




Baqinda suka rage kuwa sun koma a masaukin da aka basu Ya rage saura ƴan gidan kawai Sai kuma zohal.




Turab kam tun karfe shida na yamma suka ɗau hanya Abuja shi, zafaran, dakuma Fahad.


A hanyarsu ta zuwa ne fahad ke yita basu labarin zohal, wanda tun sa'adda aka kammala walimar ba abunda yakeyi face zancen ta tun suna amsa masa har suka fara yimasa banza.

Zafaran ne ke tuqin fahad kuma yana kusa dashi, sai turab dake back sit.

"Yawwa, zafaran nace ba wani zance kan batun wancan yarinyar? Saboda naga tun yanzu fahad ya fara yimana gorin budurwa".


"Kaidai bari kawai man Tk ba wani labari, wallahi Ni inaji a jikina yarinyar nan tana inda na baro yanzu".

"Inda ka baro kuma zafaran, suleja kenan?"
Gyada masa kai yayi alamar "Eh, haka nake tunani domin inajin alamarta kamar tana suleja Yanzu haka"

"Ah ah dai abokina, kadaina saka wannan a ranka idan har labarin da kabani kan wannan yarinyar gaskiya ne to mezai kawota har nan suleja" Turab ya faɗa yana jijjiga kai alamar tunanin zafaran ba daidai bane.

Fahad ne ya ɗago kai yana kallon abokin nasu cikin tausayawa ya dafa kafaɗarsa yace" Zafaran kayi hakuri, ka daina saka damuwar nan a ranka, in sha Allah zamu tsaya tsayin daka muyi iya ƙoƙarinmu wajen nemo maka cikar burinka. Ka saka wannan a ranka indai har ka aminta da abotarmu".


Wasu zafafan hawayene suka zubowa zafaran har yakai ga ya faka motar gefen titi ya kifa kansa kan steering motar.

Cikin tausaya Turab ya buɗe motar ya zagayo mazaunin driver, tare da janyo zafaran,

fahad kuma ya koma inda zafaran ya tashi wato driver sit.

Shikuwa Turab ya dawo dashi back sit domin ya rarrashi" haba abokina, dan Allah kayi hakuri mana Please, musani akwai zafi kuma duk wanda ya tsinci kansa a halinda ka tsinci kanka dolene a tausaya masa. Kuma mun tausayamaka harga Allah, to meya rage".

"Haƙuri" Fahad ya faɗa yana ci gana da driving ɗinsu.


"To kayi hakuri dan Allah, in sha Allah munyi maka alƙawarin kasancewa dakai har zuwa lokacin da zaka samota, wallahi danasan wannan labarin Muhsin zai gayamaka a ɗazu da ban bari ka amsa wayar ba, domin na lura tun lokacin da ya gaya maka labarin nan nutsuwa ta kau daga jikinka"

Cikin raunananniyar murya Zafaran yace" Tk nifa nasakashi ya bincika min, kuma da yayi binciken yasamo amsa har ya gayamin, to menene laifin Muhsin tunda Ni na sakashi. Amma kuma har yanzu jikina baya bani akan bayanan sa inaso inje dakaina in gani, Fahad ka shirya mana jirgi gobe zamu ɗau hanya in sha Allah"

"Zuwa ina zafaran, dan Allah Zafaran banda gaggawa mubi komai a sannu, domin nida kaina nayi binciken sakamakon da Muhsin yazo mana dashi a yanar gizo, faruwa abun shekara biyar zuwa shida ne, domin har ansamu wasu sun maye gurbin waɗancan da aka kashe a arear da abun yaFaru, yanzun nan Bama da tabbacin itama kanta tana raye ko ta mutu, domin a yanda masu rahoto sukace ba wanda aka samu da rai a cikinsu".

Runtse idanu zafaran yayi da ƙarfi yanajin yanda kalaman Fahad ke sauka a zuciyarsa kamar ana

20 / 61