Author : Rumana M Diggi Category : True Hausa Novels
a kullum wannan nake tunawa na shiga damuwa domin bansan yanda zaku kasance nan gaba ba. Wata ƙila abbinku ya auro mai imani mai jin tausayin ku. Wata ƙila kuma ya auro mara imani wacce bata jin tausayin ku. Domin kuwa Ni inaji a jikina bazanyi Tsawon raiba"
Ammi ta ƙarashe maganar hawaye na gudu a kumatunta.
"Haba ammi dan Allah ki daina wannan maganar a gaskiya ammi maganar nan ta tsorata Ni sosai ban masan abinda ya kawo wannan maganar ba. Dan Allah ki daina kuka ammi idan ba so kike mushiga damuwa ba gabaɗaya harda Abbi.
Kuma in sha Allah kece zaki riƙamu da hannayen ki ki aurar damu da kanki".
Ƙarar bugun kofar da taji ne ya katse mata tunanin da take kamar wacce ta farka daga bacci haka ta zabura, domin gani tayi kamar jiya-jiya abun nan yafaru.
Mum daketa faman buga kofa amma shiru ankasa buɗewa, abun yabata mamaki sosai amma dayake mace ce mai yawan uzuri yasa bata kawo komai a ranta ba, ta juya tabar wajen.
Parlour ta nufa tanaso ta ji abunda ya faru Yanzun nan domin kuwa tasan idan taga khulud zata gayamata koma menene ya faru, saboda sanin cewa ba wanda ke kuntatawa leeya a gidan sama da khulud.
Shigowa tayi parlourn tana ƙwalawa khulud kira har ta iso tsakiyar parlourn bata daina kiran khulud ba kuma bata ganta ba.
Khulud shiru-shiru ba magana har mum ta juya zata fita sai ta jiyo Muryar khulud tana cewa "gani anan mum naje kitchen ne na ɗauko juice cup, lafiya?"
Khulud tayi maganar a takaice.
A hasale mum ta amsa mata da faɗi
"lafiyar ce ta kawo haka, me kikayiwa leeya?"
"Wacece leeya kuma?" Khulud ta tambaya.
Rai a matukar ɓace mum tace"menene haka khulud Ni sa'ar wasanki ce?"
"Awww, mum kice min ƴar talakawan nan ƴar tsince-tsince a titi kho, inaga kamar itace leeya, ba komai nayi mata ba. Wanki na bata naga kamar tanaso tayi mini wasa da hankali shine na tuna mata da asalin ta idan ta manta Kamar dai yanda kika sani Nima na sani pa, ma ya sani".
Cikin matukar jin haushi da ƙuna mum ta ɗaga hannu zata mari khulud sai taji an riƙe mata hannu ta baya.
Da sauri ta waiwayo domin ganin wanda ya riƙe mata hannu "leeya, ki sakammin hannu na koyawa wannan yarinyar hankali kinji".
"Ah ah mum kiyi hakuri dan Allah nice silar komai, kuma nice banada gaskiya ki ƙyaleta dan Allah karki daketa mum, wallahi nice ma wacce yakamata a daka saboda nice banada gaskiya"
"Ki koma part ɗinki" shikaɗai kawai mum ta faɗa ta juya tare da barin wajen.
Khulud sake da baki take bin mum da kallo yayinda ta rasa mezatayi domin ta huce haushin mum da leeya da takeji.
"Dan Allah kiyi hakuri khulud, wallahi Ni bada wata manufa na faɗi maganar nan ba. Inason yin wanki da gaske ba nayi bane dan rainin hankali ko wani abu kiyi haƙuri dan Allah"
Leeya tayi maganar tana haɗe hannayen ta biyu alamar roƙo.
Juice ɗinda ke hannun khulud ta watsawa leeya gaba ɗaya tare da jan tsaki tabar wajen.
Gaba ɗaya mayafin leeya da kayan da ke jikin ta suka ƙara jiƙeya bayan ruwan hawaye da suka jiƙe ta.
Durkushewa tayi tana ƙara sakin kuka har tayi mai isarta kafin ta tashi ta shiga ciki da niyar yin wanka ta chanja wasu kayan.
A ƙofar ɗakin khulud mum ce tsaye tana Kwankwasa ƙofa, Daga cikin ɗakin kuma khulud ce zaune a ƙan gado tana cika tana batsewa.
"Waye bakin kofar? Ko waye ya tafi bana buƙatar ganinsa".
"Khulud mum ce buɗe kofar".
"Bana son ganin ki mum, je ki riƙa Sabuwar ƴarki, naga har kina rungumanta,
tafi dan Allah ina buƙatar na kaɗaita banason damuwa"
faɗin khulud da har yanzu bata buɗe kofar ba.
"Zaki iya daina waɗannan maganganu ku buɗe kofar ko yah?"
"No mum, bazan buɗe ba ki tafi kawai. Leave me alone, go away".
Juyawa kawai mum tayi da nufin ta tafiya, domin kuwa tasan tunda khulud tace bazata buɗe ba kowa yazo ba buɗewan zatayi ba.
Tun daga wannan lokacin khulud bata ƙara ko leƙowa waje ba har safiya ta waye sai misalin ƙarfe biyu na rana sannan ta sakko falo.
Zaune a parlourn leeya ce, sai faman wasa take da kayayyakin wasan khulud.
"Imagine" khulud ta furta cikin ranta lokacin da take ƙarasowa gaban leeya.
"Ke mena ke gani haka meyasa kika ɗaukar min taddy kina wasa da ita har kin isa" khulud ta faɗa a hasale.
"Barka da safiya ƴar uwata kin tashi Lafiya, mum ce tabani tace nayi wasa dasu" leeya ta faɗa tana miƙawa khulud hannu alamar su gaisa.
"Kada ki ƙara kuskuren taɓa komai nawa a gidan nan wallahi. Get out!" Khulud ta faɗa cikin tsawa, bangazar leeya khulud tayi da kafaɗarta har leeya ta faɗi ƙasa, "get out of this house ki koma inda kika fito" khulud ta kuma faɗa har tana sa ƙafa tana shurinta alhali kuma ta bangajeta ta faɗi ƙasa.
"But mum tace ke ƴar uwatace nima ƴar uwarki ce" leeya ta faɗa cikin muryar kuka, tana miƙewa daga kwancen da take.
"God forbid that we're sister's, get out" cewar khulud cikin wata irin tsawa tana yarfe hannaye.
Rushewa leeya tayi da kuka ta fita parlourn ta nufi hanyar fita baƙi daya daga gidan tanata kuka yanda ta iya.
Fitar ta ɗakin yayi daidai ta sakkowar mum daga sama tana cewa "khulud meya faru, me kika yiwa leeya kuma, me kika yimata nace?"
"Mum how dare she play with my toys, ita wace da zan ajiye abu ta ɗauka har tayi wasa dashi, kuma tace ke kikace ta ɗauka tayi wasa dasu" cewar khulud tana kallon mum tarrrr.
"Menene a ciki, it's Toys saboda ta ɗauka matsala ce" mum ta faɗa tana fita parloun bata ma jira cewar khulud ba tabi bayan leeya a guje.
Ita kuwa leeya tana fitowa harabar gidan, fitowar ta yayi daidai da wangale kofar gate ɗin da mai gadi yayi da alama za'a shigo da motane ciki.
Kafin mai gadin ya ankara ta wuce ta gabansa a guje ko takalama babu a kafarta, doguwar rigace a jikinta sai niƙab ɗinda ke sanye a fuskar ta ko mayafi batada shi akanta gashin ta a fili.
Da gudu mum ta ƙaraso wajen tanayiwa ma'aikatan gidan alama dasu bi leeya baya su dawo da ita, kafin wasunsu su ankara tuni leeya tayi nisa da gudun da takeyi.
Mum ta ƙaraso bakin gate ɗin sai numfarfashi take.
"Mum-ulud lafiya?" Cewar papu da yake fitowa daga mota tun driver baiyi packing ba.
"Justice wallahi leeya ce ta fita aguje ba wanda yasan inda zataje gashi batada ko takalma, gashi tana kuka sosai koda ta fita.
sannan kuma ko mayafi babu a jikin ta, dan Allah justice ayi wani abu kasan mutane basuda kyau Yanzu" mum takai ƙarshen tana sauƙe ajiyar zuciya da sauri domin kuwa a gajiye take ɗan gudunda tayi yanzu.
Juyawa papu yayi tare da yiwa driver izni daya tuƙa motar su bi bayansu.
Leeya kuwa har wannan lokaci gudu take faman yi, kuma ba alamar gajiya a tattare da ita, sai kukan da take yi ƙaɗan kaɗan idan ta juya baya taga dandazon ma'aikatan gidan da suka biyota, sai take gani kaɗan ne babu tsakanin ta dasu.
Wani irin wawan birki a jaa gabanta, wanda yasata dakatar da gudun da takeyi amma bata daina kuka mai sauti ba.
Buɗe kofar motar papu yayi fuskar sa ɗaure tamau kamar wanda bai taɓayin dariya ba yace" ke shigo mota".
Girgiza ƙanta tayi alamar bazata shigo ba ta juya zata ci gaba da gudu sai ga sauran ma'aikatan gidan sun ƙara so, suka cirata sama sannan suka sakata cikin motar suka rufe rufff......✍🏼
BAYAN WUYA....
By RUMANA M DIGGI
EP...13
____________Shigar ta motar keda wuya tayi shiru ta nutsu kamar ba ita ba, har aka ƙaraso gidan ba wanda yace kanzil tsakanin papu da leeya har driver.
Koda suka iso gate ɗin gidan mum na tsaye tana jiran isowarsu.
Ana buɗen marufin motar leeya ta zabura zata ƙara guduwa mum tayi wufff ta riƙeta ita da wani ma'aikaci da ya lura da guduwa takeso ta yi a karo na biyu.
"Leeya me kike shirin yi ki ne wai ki nutsu mana"
faɗin mum tana ƙara riƙe leeya.
"A nutse nake mum dan Allah ki sakeni na tafi na koma can titi na dinga tsince-tsince dana sabayi, dan Allah ki barni in tafi" Cewar leeya tana ƙara rushewa da kuka.
Gigitacciyar tsawa papu ya daka mata yana yimata nuni data koma ciki.
Da gudu ta shige ciki tana cigaba da rizgar kukanta.
"Hajiyata wai me akayiwa yarinyar nan har haka? Naga baruwanta ai, kuma naga kamar tanada haƙuri. Me aka yimata har haka"
"Wallahi justice ita da khulud ne, khulud ce ta zageta sosai kuma ta koreta gidan nan amma ka barni da ita kawai"
mum ta faɗa tana shigewa cikin gidan.
Shima papu ya rufamata baya suka shige baki ɗaya.
Zaune a parlour khulud ce ta ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya, sai wani girgiza ƙafar take tana faman kaɗa kai. tana ganin mum ta shigo ta miƙe da sauri zata bar parlourn.
"Khulud!!"
Mum ta kira sunan ta da ƙarfi. "Meyasa bakida hankali ne wai, ina kika ɗauko wannan mugun hali, Ni ko mahaifinki ko yayanki wakikaga yana irin wannan halayen na wulaƙanta ɗan adam. Allah da kanshi ya karrama ɗan adam har ke wacece da kika isa ki wulakanta shi"
"Ok mum kina supporting ɗin ta kenan"
"Could you Shut up, shut up"
mum ta faɗa cikin tsawa tun kafin khulud ta rufe bakin ta.
"Hajiyata kiyi hakuri abi komai a hankali kinji" faɗin papu yana dafa kafadar mum.
Da sauri khulud ta hau sama har tana haɗawa da gudu kamar zata banke mum.
"Ka gani, ka gani ko justice duba kaga bankeni fa tayi, takalman da ke kafar mum ta ciro ta wurga wa khulud. Amma baikai ga samunta ba domin har tayi nisa da tafiyar ta.
Bayan khulud papu yabi shima suka bar mum a parlour.
Da gudu khulud ta banki kofar ɗakinta ta rufe, dai-dai lokacin da papu ya iso.
saurin binta yayi a ɗakin tun kafin ta saka key, kan sofa taje ta jingina shikuma papu ya zauna kusa da ita ya riƙo hannun ta yana faɗin.
"Khulud my kid, nasan abune mai matukar wahala ki karɓi leeya a matsayin ƴar uwarki nasani, amma inaso ki gwada. Tana da kirki, gashi ba ruwanta batada matsala. Tana bukatar taimakon mu, bazamu watsarda itaba tunda munada abunda zamu taimake ta. Ko kin manta papunki shima da yanda ya fara, da ba'a taimako Ni kaina bazan kai hakaba. Please my kid inaso kiyi hakuri ki karɓesu dan Allah, yanzu na dawo daga makarantar akayimata registration itama ta fara zuwa makaranta kamar sauran 'ya'ya"
papu ya faɗi yana shafa kan khulud.
"Pa, nifa bance karku taimaketa ba. But i don't want her in this house, she's dirty girl and very, very, poor girl pa. Idan mutane suka sha ruwa suka jefarda robar ruwa, itace take tsinta tana siyarwa, a gaskiya bana buƙatar ta a gidan nan pa"
Khulud ta faɗa tana kara jingina kan sofa.
"Ki daina maganar nan mamana, itama mutum ce kamar mu, ba ita ta tsarawa kanta yanda takeso ba. Allah ne ya tsara mata kuma haka nan yakeso ya ganta gabanin shigowar mu rayuwar ta. Saboda haka ba yanda ta iya da ƙaddararta. Akwai wani darasi na rayuwa daya kamata ace kinsani, kuma kin fahimta",
dogon numfashi papu ya jaaa sannan ya sauke yaci gaba da magana "wanda kika gani talaka a yau, wata rana shi zaki gani ya zama mai kud'in da ya kere kowa idan Allah yaso. Sannan kuma kiga ya taimaki talakawa harma wasu masu kudin.
Ina so ki yi tunani akan haka kinji.
"Okay pa"
"Yawwa my kiddo Allah yayi albarka, sannan wani abu guda daya"
"Menene shi papu?"
"Kiyimin alkawari bazaki ƙara kwatanta yin abunda kikayi a dazu ba".
"Okay pa"
"Ba okay ba so nake naji kince kinyi alƙawari"
"Nayi alƙawari bazan ƙara kulata ba idan har ba ita ta shigo gonata ba, amma idan ita ta shiga lamarina na rantse bazan rangwanta mata ba"
"Nasan leeya bazata shiga lamarin kiba idan har ba ke kika sakata ba in sha Allah"
Taɓe baki khulud tayi sannan ta furta "kudai kuka sani" ta mayar da kanta ta kwanta.
Miƙewa papu yayi yabar sashen gaba daya ya koma nasa.
WASHE GARI, ya kama ranar Monday, ranar da ko wane ɗalibi yake hanzari da gaggawa domin ya shiga school.
Sakkowa take daga kan steps cikin tafiyar ta ta nutsuwa, jikinta sanya yake da uniform rigar half gown. Sand colour mai ratsin brown colour. Sai kuma suit data ɗora kan rigar kalar brown, a gefe daya na suit ɗin kuma ɗan karamin badge logo ne da aka liƙa mai tambarin school ɗin wato BUSY BRAIN INTERNATIONAL ACADEMY SULEJA.
Sai kuma wuyanta dake sakale da neck tie mai kalar red and white, sai kuma ɗan ƙaramin hijab ɗinda ta saka White colour ne da iya kacinsa kafaɗarta kawai.
Niƙab ne sanya a fuskar ta brown colour shima, wanda ya bayyana dara-daran idanun ta, da kallo ɗaya idan mutum yayi musu zai tsorata ko yayi tunanin ba mutum bace.
Cover shoe ne a ƙafarta sai kuma socks ɗinda ke sanye a kafar tata kalar brown mai dauke da logo na school ɗin.
"Masha Allah" mum ta furta yayinda leeya ta ƙaraso dainin area
"ɗiyata kinga yanda kikayi kyau, kamar ke kaɗai akayiwa uniform ɗin nan wallahi"
Cikin tsananin farin ciki mara misali da leeya ke ciki ta durƙusa har ƙasa tana gaida mum.
Mum ta amsa mata ita ma cikin farin cikin ganin sun zama sanadin shigar marainiyar Allah cikin farin ciki
"ki zauna kiyi breakfast kinji, kafin ƴar uwarki ta fito domin ita bata yin breakfast a gida saidai idan taje makaranta"
"Nima fa banaci mum wallahi bana jin yunwa" leeya ta faɗa tana miƙa hannu ta ɗauko lunch bag ɗin da aka siyamata"
"Kizauna kici abincin ki kada kije yunwa ta dameki" cewar mum tana zuba abincin a plate.
"Allah mum bazan ciba idan mutum ya cika cin abinci tunda safe yana toshe ƙwaƙwalwa kuma kona shiga class bazanyi karatuba saidai bacci tunda na ƙoshi. Kinga ko gwanda ma kar inci yanzu"
leeya ta faɗa tana kallon khulud da take sakkowa yanzu. Papu kuma yana bayanta.
Ƙarasawa leeya tayi da sauri gaban papu ta gaida shi kamar yanda tayiwa mum sannan ta waiwayo ga khulud tace
" hi sis, ya kikaga uniform ɗin nan sunyimin kyau kho, kinga yanzu school din mu daya muyi haƙuri mu zauna lafiya, muyi karatu, mu taimakawa juna, mu farantawa mum da papu rai kinji please "
Ja da baya khulud ta fara yi a kidime tace
"what!??, menake shirin gani pa, mum, kuna nufin school ɗin mu ɗaya kenan a BUSY BRAIN INTERNATIONAL akasakat?
no, no, pa wannan bazai taɓa faruwa yazaka min haka pa"
ta faɗa cikin tsananin hasada, kamar ta fashe da kuka.
"My kid menayi miki kuma".
"Pa, makaranta ɗaya kasaka wannan yarinyar tare Dani, no pa you're bringing down my personality. Cewa khulud tana yar fe zufa.
"Stop this please, bakiji yanda tace miki bane. Bakyaso kisakamu farin ciki ne, na sakaku school dayane saboda inaso shaƙuwa ta shiga tsakaninku, bakyaso ko a school ɗin a dinga cewa ga sistern ki nan bakyaso?"
"No, no pa, wannan bazata taɓa zama sister na ba har abada, ta dauke soyayyar mum daga gareni, yanzu kuma soyayyar ka papu takeso ta ɗauke daga gareni. No!!!"
Khulud ta faɗa tare da barin parlourn ta nufi mota da gudu tana kuka.
Idanun leeya na cikowa da kwalla ta kalli papu tace" pa, mum dan Allah ku yafemin wallahi ba ason raina haka take faruwa ba, wallahi a yanzun nan idan akwai abunda nafiso bai wuce naga mun zauna lafiya da khulud ba, dan Allah kuyi hakuri"
"Ba komai zo muje driver na jiranku"
papu ya faɗa yana wucewa gaba leeya kuma tana bayansa.
"Mum mun tafi sai mun dawo"
"Allah ya baku Sa'a leeya Allah ya tsare kinji"
"Ameen ya ilahi mum, bye bye"
Nan suka tafi suka bar mum ita kaɗai a gida.
SAI MISALIN 2:00pm na rana suka dawo gidan, ko da suka shigo mum ta tsaftace ko ina na gidan har ta kammala girkin ta na rana.
Leeya ce ta fara shigowa gidan da gudunta taje har gaban mum cikin farin ciki take magan;
"mum ambamu classwork yau kuma score na 10/10"
ta faɗa tana fitowa da book ɗin daga cikin school bag ɗinta.
Karɓar littafin mum tayi tana dubawa, sai murmushi take. Daidai lokacin da papu ya shigo riƙe da hannun khulud ya ƙaraso wajen.
"Barka da dawowa justice, kaga fa ɗiyata taci marks 10/10 a class work ɗinda aka basu yau" cewar mum tana miƙawa papu littafin.
"Masha Allah" gskiya kinyi ƙoƙari LEEYANA HAMRAZ AWAIS amma aƙara kinji ɗiyar mum" papu ya faɗa yana miƙawa mum littafin bayan ya duba.
"Kinyi ƙoƙari sosai, kuma zan miki kyauta kinji"
"Nagode mum" leeya ta faɗa fuskar ta ɗauke da yalwataccen annuri.
Zaune suke kan daining mum, papu, khulud sai kuma leeya. Abincin su sukeci hankali kwance ba wanda ya damu da wani.
Papu yakai dubansa kan khulud yace
"my kid ɗazu naga leeya ta nuna mana score ɗinta amma ke banga kin nuna nakiba"
"Pa, malamin mu yace sai gobe za'a bamu litattafan mu"
"Kin tabbata?" mum ta tambayi khulud.
"Yes mum, sai gobe yace mana"
"Ki tabbatar kin kawo littafin gobe nagani"
"Okay mum".
Basuyi wata gardama ba domin leeya da khulud ba class ɗinsu ɗaya ba leeya tana ss2 ne khulud kuma ss1 take.
"Justice gaskiya leeya tayi ƙoƙari she's very brilliant"
Spoon ɗinda ke hannun khulud ta sake da ƙarfi tana sauransu.
Mum kuma tayi kamar bata jita ba, shima papu haka dama can bai kula tayi haka ba itama leeya ɗin bata kula ba. Mum ce kaɗai ta gane abunda hakan ke nufi.
"Ehhh gaskiya tayi ƙoƙari sosai wallahi amma dai ki ƙara kan haka kinji leeyana"
"In Sha Allah pa, Nagode sosai".
"My kid meyasa bakya cin abinci?"
"Nothing pa, I will eat"
"Hmmm" kawai mum tace banda haka bata ƙara faɗin komai ba.
Har suka kammala cin abincin ba wanda ya ƙara faɗar komai
KhUlud ce ta fara tashi daga wurin sannan sai papu.
Mum da leeya su suka tattara komai da aka 'bata a wurin. Leeya ta kar'ba ta wuce kitchen ta wanke.
Bayan ta kammala wanke-wanken ne ta fito ta koma part d'insu sannan tayi wanka tayi sallah.
School bag d'inta ta janyo daga kan bedside drawer ta fito da littafin ta da aka bata assignment ta d'akko sannan ta fita balcony din gidan.
Zaune take kan ɗaya daga cikin kujerun da ke wajan sai lissafi take da